Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels https://chat.whatsapp.com/DBGH2dTWEfmBB7Gi0BgrJ8 *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ DAFIN ZUCIYA ✍️✍️By Fateema Bintu Hussain Page 1 Bismilahi Rahamanir Rahim Ameerah Kwance Suke a Wani Daki Wanda Kai Tsaye Za a Kirashi Da Dakin Awaki Itada kaninta Ameer Muna Cikin Barci Mukaji Saukan Ruwa Me Sanyi. "Dan Ubanku Bazaku Tashibah?' Bakowa Ke Wanan Maganar Ba, Wata Matace Wadda Akalla Zata Kai Shekara 37 zuwa 39 Take Wanan Maganan Matar Abee ce Muna Kiranta Da Ummah Afirgice Muka Tashi Dama Inda Sabo Mun Saba Da Masifarta Dama Mun San Aikin mu Muna tashi Muka Dauki Butiki Muka tafi Diban Ruwa Saida mukayi tafiya me nisa muka iso wajan deban ruwan Wanda Kai Tsaye Za a Kirashi da korama, Saida muka cika komai na gidan sanan nayi aikin da zanyi dama shi Ameer bawani aiki yake iyawaba sabida yunwa, muna ji muna gani suna karyawa itada yaranta amma Bata damu ta bamu komai bah, Ameer yanata kuka na lallashesh. "nace ka kadaina dora rai Kan abinda bazaka samubah." Nan nafita barah dama na sa bah na sa mu ma na abinda zamuci bayan nagama komai ne mukafita dama wanine wajin zaman mu inta tunanin rayuwarmu ta baya ko Ina Amminmu da sauran Yan uwanmu, ina cikin tunani naji leka a jiki na ya Ashe hawayene Ameer "yace Nima zanyi kuka idan Baki dainah bah." ______________________ Najeriyan amer Phatacurt Eshan zaune yake Kan kujera mai juyawa Yana tunanin kalar ta addancin da akeye a kasar Nan, abin yayi yawa Yana tunani yadda za a kawo ƙarshen wannan bala'in a kasa. Ahmad ne ya shigo ya na ta sallama bejiba Saida ya kaimai duka yayi fargita! ya mike tsaye " a a Man tunani mai ka keyi? kardai ansamar manah aunty." messsss ya Bata Rai "Allah ya kiyaye Ni Banga kalar matar da Zan aura bah." nikam nace tofah __________________ Ameerah Muna nan zaune a waje har abee yadawo Amma bai ko kallemu ba Ameer ya kalleni zaiyi kuka na garigiza Mai Kai nace. "ka daina damuwa insha Allah komai zai zo karshe bayan wuya sai dadi." Shin meye dalilin shigar ameerah da Ameer wanan Hali Kuma Ina ammi da Yan uwanta? in sha Allah zakusan ko Mai nan gaba, please share and comment DAFIN ZUCIYA ✏️By Fatima Binta Hussain✏️ https://chat.whatsapp.com/DBGH2dTWEfmBB7Gi0BgrJ8 *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne ys kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️* _________________________________________________Bismillahir rahmanir Rahim Page 2 _________________________ Haka muka ƙaraci Zaman mu Amir yace min "Yunwaa Ya ce min yunwa ya ke ji." Haka na tafi Bara, Na sha Wuya Kafin Na samu ɗan Abinci na bawa Amir. Nace "Gashi nan Ka ci." yace "Ke fa? Na ce Mai "Yace Kawai." Allah Sarki Dan Uwa Sai Da Ya Ragimin Duk Da Yana Karamin Yanada Wannan Hankalin Dama Tun Muna Tare Da Ammi Take ko Yamana Kasoma Dan Uwanka Abinda Kaki Soma Kanka Ina Cikin Ci Sai Na Tuna Da Ammi Wani Hali Take Ciki Itada Yan uwana. , Ina Cikin Wanan tunanin Na ji Saukar Bulala Umma Cetake cewa. "Don Ubanki Ba za ki Tashi ba?" Na Tashi Na Shiga Gida Kayan Futsarine Na Yaranta. __________________________________"Eshan. ya ce ma Ahmad "Wato Kai Dan Iska Bakaga Matar Aure ba?" Ahmad "Don Allah Kabar Wanan Maganan." Ahmad Ya yi Dariya Yace "In sha Allah Sai Soyayya ta wahalar Da Kai." Suna Cikin Fira Aka Nuna Wani Labarai Da ya D'au Hankalin Su An Shiga Dutsinma Daki Jihar katsina An kwashi Mutane An Kona mawasu Gidaji Anyi Ma Yara Faɗe Duk Wani Me Rai Dayake Jihar Katsina Hankalinshi Atashi Yake Ganaral Eshan Sabuda Tsabr Bacin Rai Duk Wani Abu Da Yasamu Jifah Yake Dashi. Ammi ce Zaune Take Tana Tunanin Yaran Tan Wani Hali Suke Ciki A hanun Matar ________________________________Amira Da Amira Suna Zaune A Dakin Su Amira Na Kowa Ma Amir Karatu. Sai Ga Abbi Ya Shigo Dakinmu Muna Ganin Shi Hankalin Mu Ya Tashi Muna Tunani Ko Zai Koremu ne Sai Muka Kama Kuka Maganar Abbi Ce Tasa Na Kalle Shi. "Kuyi Hakure Allah Yana Tare Damu Sai Ya ka sa Magana Sai Kawai Yace Min. "Ku Shirya Gobe Za ku Fara Zuwa Makaranta." Haka Na ji Maganan Kamar A Mafarki Nace "Da gaske Ka ke?" Kawai Sai ya Share hawayen Da Ya zubu Mashi Sai Jikin Mu Yayi Sanyi. WASHE GARI Bayan Mun Sherya abbi ya ba mu Kayan Makaranta Mu ka sa. Mun Fitu Kenan Sai Ga Umma Don Bakin Ciki Haka Ta Watsamin Ruwa Ta Hauni Da Duka ______________________________Kai Duniya Wai Idan Bake Ki ka Haifi Yara ba Sai Ki ta Zalintarsu Humm Wallahi Kalar Sune Allah yake D'agawa In sha Allah Nan Gaba Za ku San Komai _____________________________Share And Comment please DAFIN ZUCIYA ✏️By Fatima Binta Hussain✏️ https://chat.whatsapp.com/DBGH2dTWEfmBB7Gi0BgrJ8 *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️*. Bisimilahi Rahamanir Rahimin Page 03 _________Bayan Ya tafi Office Ya ka sa yin Komai, ya rasa Me Yake Damunsa tun da ba ga Yaransa Cikin Wani Hali Ya Kasa Tabuka Komai, Wani Lukacin Idan Ya Zauna Da ya Fara Tunani Yaran Shi Ko Matar Shi Da Ya saka Ba Tayi mashi Komai Ba. Da Ya fara Wannan Tunani Sai yaji kamar an jefe Shi Da Wani abu. Kamar Mara Lafiya haka yake komawa. GENERAL ESHAN Ahmad Yace "Kai ka san k'asar Nan wani abun ma dasa hannun manyan kasa acikin wani abun." General Eshan yace" ni kuma nayi Alkawarin sai na kawo K'arshen wanan ta'addacin a k'asar nan." ni kam Nace" Allah Ya bada Sa'a. Amira Wani kalar zazzabi me zafi ya rufeta" saka ma kon dukan da tasha ɗazu. Amir ne ya je maƙota ya samomin magani bayan Nasha ne barci ya ɗaukeni Allah sarki. Dausin Alhaji Abuja wani mugun daji ne bayan unguwar, saman wani dausi wani ƙasurgumin boka ne, zai ne kan wani tabarma. wasune su biyu Suka Shiga wajin bokan su na ma shi kirare Suka farayima. "bokan na gurungu shugaban shedanu.' wata mahaukaciyar dariya bokan yayi cikin dariya yace "la'ananu na san me yake tafe da ku." ya nuna D'aya daga cikin su yace "wannan aikin na ki ba zaiyuwubah Yaran ana masu addua sosai Kuma Suma suna yi sai dai ki ci ga ba da wahalar dasu Kuma kisani za suji Dadi Nan Gaba." "ke kuma Ladidi magananr kisheyarki ankusa Gama aiki akanta zaki yankama aljani bak'in rago." (Waiyazubillalah) Nan dai Suka tattauna maganah akan yar da za su ga komai yayi dai-dai. Wayar Eshan ce Tayi Kara Ganin sunan me Kiran ne yasa shi yin saurin ɗauka. "Assalamualaikum." jin salamar mamin shi yasa ya sauke ajiyan zuciya. yace" Mami I miss you." tace "son yau she za ka zo?" maimakon ya ba ta amsa sai yace Mata" Ina farha?" tace "ga ta nan ta nata cigiyanka." yace "a bata waya ta gaisheshi." tace" Yaya yaushe za ka zo?" yace Mata "sati me zuwa." wata uwar ƙara ta saki tace "Allah ya ka wo ka lafiya." daga haka sukayi sallama BOKA "za a kawo boka na gurungu nawa ne kudin aikinka?" yace "sai Aljani burum ya fada." yace ma Umma "ke Kuma La anananiya akan aikin Mijin"ki za ki daina sallah tsawon sati ɗaya. (wa iyazubillah) tace "angama." suka fita sunayi Mai kirari koda za su fita Sai da su kayi Mai sujjadah (yaAllah ka tsaremu) kamar yadda Su ka sugu wata ba za' Kali gabas ba a juyama Allah baya a Kama shed'an (wa iyazubillah )ya Allah ka tsare mu DAFIN ZUCIYA ✏️By Fatima Binta Hussain✏️ https://chat.whatsapp.com/DBGH2dTWEfmBB7Gi0BgrJ8 facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️*. Page 4 Amira yau dai Allah yasa sai munji makaranta bayan Abbi ya kaimu ana kaini aji 5 Amir Kuma aji 3., Naya ƙawa me suna Hafast, Kuma tanada kirki sosai, antashi mu karfi 2:30 sai munyi sallah a makaranta ake tashi Ina dawowa na dauki tallan manja. haka rayuwa yacigaba da tafiya ammice Zaune, da Yan uwana dasuka kaimata ziyara suna magana akan halin da mukiciki.********************************************* ASALIN SU AMIRA asalinsu Yan garin Funtuwa ne dake jihar Katsina, sunan abbi Usman' i karatu Bai samu aiki ba, sai ya ci ga da da noma. Yana kuma sa na'ar kayan kamshi irin su citta tafarnuwa kanimfari da sauransu, ya hadu da Ammi a bayan ungiwarsu inda Suka Fara soyayya har manya Suka Shiga maganan. Sunan Ammi Aisha Abubakar itama tayi karatunta Amma daga sekandiri ta tsaya Amma a bangarin na addini sai dai ace alhamdulilahi Don tana dashi sosai haka Abbi yanada ilimi Don har koyarwa yakeyi su abi sun sa san ta kan su Nan akayi maganan aure bayan an yi aure inda aka kai Ammi gidansu abbi gidane babban gida suna Zaune lfy ahankali Ammi ta Fara fahintar wasu abubuwa daga family din Abbi sabuda anyi shekara biyu Bata haihu ba. ( Humm mutane na mantawa da Allah yake bada haihuwa sai su daura ma mutum laifi ) abi yace "ma Ammi ta daina damuwa haihuwa Allah yake badawa." Haka suka cigabada rayuwa bayan shekara biyar Ammi ta samu ciki zukuga murna wajan wayan Nan bayin Allah sunba cikinsu kulawa har yakai watan haihuwa. Ammi taci wahala inda ta haifi danta namiji ranar suna yaro yaci Usman watu sunan abbi anacemai Ammar da ganan haihuwa ta bude Ammi nada Yara biyar Abbi yasamu aikin cotu a Abuja inda suka dawu Nan suna zaman, su cikin kwanciyan hankali Ammi ta Kara haihuwa namiji daganan aka haifeni bayan Ni ta Kara haihuwa mace Dana miji bayan sekaru Mauna Zaune cikin amince da son Yan uwanmu, wata rana tafiya ta Kama Abbi zaiji garin gausu daki zamfara anan ne Abbi ya hadu da umma bazawarace tanada yara hada manya, Abbi ya nuna Yana so ba Bata lokaci akasa biki Amma Abbi Bai fada Mana ba sai da ana saura kwana uku biki, ya fada Mana Ammi Bata tada hankalinta bah Tasan Allah Yana tare Damu bayan aniyi aure daga nan ne muka Fara ganin sauyi tare da Abbi, baidamu da yabamu abinciba babu ruwan shi ko munci ko bamuci bah, su Yaya suke fita aiki suna samamana abinda zamuci wata rana abbi yasai gida yace amarya zata koma ita Kuma tace saidai ta tafi da nida amir Nan ne, Ammi tace Bata yarda ba ako abi yasaki Ammi yace tawuce ta barmai gida, Ammi ta hada kayanta da su Yaya suka tafi Funtuwa, inda mukuma muka tafi sabon gidan abbi, daganan ne muka Fara shiga wanan Hali abi Bai damu damuba ya na gani zata dafa abinci Bata bamu Kuma baya iya yimata magana. Wannan shine labarin Amira da Amir. Eshan Yauce ranar da zaizu gida karfi 12: 00pm. Jirginsu ya sauka a airport din Abuja ablkin shine yazu dau karshi abudulahi Yana fituwa daga jirgin sai yaji an rungumeshi. Abdullah ne ya amsai Mai kayan shi suka shiga mota Kai tsaye asokoro Suka nufa inada gidansu yake. wani hadandan gidani ya hadu iya haduwa su na zuwa bakin get me gadi ya wangali masu gidan ya salam ba a magana. Abdullah Yana aji yeshi yawuce akan anjima zai dawo. shikuma ya wuce cikin gida. wani babban falo ne Wanda ya ga ji da haduwa mami ya gani Zaune Yana shiga ya rungumeta. suan cikin gaisawa Farha ta shi go itama Suka gaisa. yace "Bari na shiga na yi wanka." Part ɗin shi ya nufah Yana zuwa komai an gyarashi wanka ya shiga Yana fito Yana goge jikin shi Sai ga yusurah ta shigo yusurah wata diyar ƙawar Mami ce wadda ta mutu akan sonshi shi kuma baya son ta Don shi Bai shir ya yin aure Ba ko da ma auren zai yi ba zai iya auren ta ba, Tsawa ya da ka mata da gudu tabar dakin tana fita tahau motar ta Kai tsaye gidan su tanufah . AMIRA Yau ta kama litinin mu na tashi mu kayi abinda za m uyi muka tafi makaranta bayan mun dawu ko kayan makaranta bamu cire ba naduki tallah na fita na ɗanyi ciniki Amma haka ta Kamani tayi min duka, ai ban jiba yawona natafi naci kuka nah na koshi natashi muka tafi islamiya dayake amir ya rigani dawowa Dana dawo Naga amir a waji na tambaye she meyaki yima kuka yace "ai Umma ce tarufi gidan." tace "saidai mu kwana a waje." Nan muka Zauna munata kuka Babu me taimakon mu, Amir yace "min yaunwa yake ji." haka natafi Bara na sa mo Mana abinci bayan munci muka kwanta abakin kofar gidanmu Sai da wani makocinmu ya dawo ya kaimu gidan shi. DAFIN ZUCIYA ✏️By Fatima Binta Hussain✏️ https://chat.whatsapp.com/DBGH2dTWEfmBB7Gi0BgrJ8 *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️*. Page 5 Yusurah tana isa gidansu kai tsaye ta fara kiran "Mom! Mom! Mom!" wata matace tafito warda kana ganin ta Kinga Yar duniya. Yasurah ta fa ɗa jikin ta. ta saki kuka mom na tambayar ta me ya faru sai kuka take da kyar tafaɗa mata abinda ya faru. Nan Mom ta bata Haƙuri tace ta "shirya gobe za su je wajin gagara badau da kanshi Zaizo yace yana sonta." Amira Yau Alhamis mun tafi makaranta yan ajinmu su kayi ma malamin English laifi, yace idan aka tashi sai kowa ya ga ma tafiya zamu tafi bayan an tashi Amir yanzo mutafi nace yayi gaba idan yaje gida ya yi ma umma bayani. Sai wajin karfe 3:40pm muka dawo gida dana faɗa mata abinda ya faru sai cewa tayi natafi yawan iskanci, Za ta yi maganina taka Mani da duka da wani karfi ta buga min a kafa nan fah kafa na ya kumbura kuma bata damu da halin da Niki cikiba, Kwana na biyu a kwance ba a kai Ni wajin me gyara ba ina ta fama da ciwo sai da taga ai ita tayi ma kanta sanan tafa ɗama abbi Eshan Bayan tafiyar yusurah yayi yan shafe shafe shi sanan yafi falo suka kara gaisawa da mami sanan. yace akawo mai abinci bayan yaci abinci suka ci ga ba da fira da mami suna cikin fira aka kira sallah ya tafi masallaci a masallaci ya hadu da Abba suka gaisa suka shiga gida suka dasa fira ana cikin fira Abba ya kale Eshan, Yace "wai son yaushe zakayi aure?" aikam ya ɓata fuska Abba yace "ya dai?" shefa basu gane bane ba ba ya son ana yi mai maganan aure ya tashi ya tafi daki yana tafiya Abba ya kalle mami yace "anya kam yaron nan ba aljanace ta aure shi ba?" Mami tace "lokacin ne baiyi ba." shekam yana shiga ɗaki ya kira Abdullahi. Umma Yau taka mah zasu koma wajin boka sun ji sun iske bayanan. Yusurah yau suka shir ya tafiya wajin boka san da suka ji sun samu mutane dayawa don haka Sai da suka jirah sai bayan la'asar sanan suka samu ganin boka suka shiga wajin boka suka fada mai abinda ya ke tafe dasu yabasu wani ƙwali yace tasa da sun hada ido da Eshan da kanshi zai dinga Binta kamar bita zaizai. Amira Bayan an kai ni wajan gyara aka ce na kare nan aka tambaye? me ya sa me ni? Nace "faɗu wa nayi a makaran ta na bege." nan aka yi min kamu har fitsari sai da na yi don azaba aka ce bayan sati mu koma muka koma gida yau sati ya zagayo mu ka ma wajan me gyara aka ce be yiba Na sha wahala sosai don har yanzu ina fama da ciwon kafa. Umma Yau suka koma wajin boka sunyi sa a yana nan. yace ma Ladidi "ina ragon? da za a yan kama Aljani?' Ta ce "ba ta sa mu ba sai dai ta ba da kudin." boka yace "zata bada dubu hamsin." nan ta ba da. ita kuma umma tace "ya maganan mu?" ya bata wasu magunguna. yace "gashinan." da wanda zata sa mai a ruwan wanka da wanda zata samai a abinci nan dai yayi surkulinshi ya ba su koda zasu fito ta baya suka kuma fituwa bayan sun mai sujada (waiyazubillah). Yusurah Yau ta shirya ta tafi gidan su Eshan bayan sun gaisa da mami ta tambaye ta ina Eshan? tace "yana daki." Kai tsaye ɗakin shi ta nufa ta shiga ta iske shi yana bacci ai kam ta ta sheshi. yace "waye?" tace "haba masoyi nice fah." aiam yakai mata wani wawan mari da gudu tabar dakin tana fito tashi ga mota tasha kukan ta akan hanya ta taga me ruwa ta kira shi zata siya ai kam ta manta da kwalin da tasa suna hada ido da me ruwa yace "masoyiya." nan fah hankalin ta ya tashi ta faisgi mota aguje tayi gida tana zuwa tace ma megadi kada yabar ko wa yashi ga tana gama magana sai ga wannan me ruwa ya biyo ta. yace "ya ki ke guduna masoyiya?" da gudu tayi cikin gida tana ihu me gadi ya hana shi shiga ya bangaje shi ya wuce yayi cikin gida da gudu. DAFIN ZUCIYA ✏️By Fatima Binta Hussain✏️ https://chat.whatsapp.com/DBGH2dTWEfmBB7Gi0BgrJ8 *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️* Bisimilahi Rahamanur Rahim page 6 Eshan bayan Abdullahi yazo yace "yadai naga ranka ya ɓac" yace "daga zuwana an fara yimin maganan aure." Abdullahi yace "eh mana aida gaskiyar Abba mana kai ka fiso Kaita zama tuzuro." Eshan yama kai mai harara yace "wallahi ka kama kan ka idon ba hakaba kasan sauran." AMIRA Yau abi zai tafi umara bayan tafiyan Abbi muka ci ga ba da fuskantar rayuwa wani Lokacin abamu abinci wani lokacin a hanamu yau Abbi ya na da kwana bakwai da tafiya yaune kuma umma tayi ma Amir wani duka wanda har ya suma saboda yaji yace abincin da tasama yaran ta. YUSURAH Yusurah bayan ta shiga gida wannan me ruwan ya

Chapter 1 of 14