Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
daddare bayan naci abinci na gama aikina kawai na dauko wayata na kunna data banbi takan WhatsApp na shiga Facebook nafara duba posting din mutane na dariya in dariya na tsaki inyi tsaki. Tun budemin account da Walida tayi kullin sena hau facebook sai dai ba na magana da kowa banma taba shifa inbox dina ba, kusan kullin sena duba posting din mutumin har yazame min jiki dan posting dinsa masu ma'ana ne ko joke yai inka duba sosai sai kaga abin anfana. Nakanyi commenting sosai aduk post dinsa wanda na rasa abin cewa kuma nakanyi liking. Yau ina zaune bani da data kawai dai inabin previous post ne na mutane ina kallo sai dai nai nai gabaki daya suyi loading sunqi iya goman farko ne kafin Data ta ta qare kawai inbox na shiga inda ban taba gwada shiga ba sai yau tsawon wata biyu da fara chat dina. Duba mutanen da suka min magana na shiga yi kamar me naga nashi manar sai dai nai nai ya bude yaqi hakan yasa na gane rashin data ne kudi na ciro daga account dina ta waya na kira walida. Pls ya zanyi ne insai data tawa ta qare tai dariya eyye ai dayake data ce yau kin kirani tunda kikai waya baki taba kirana ba nai dariya to ni kirana kike eyye nan ta basar ta fadan yadda zanyi. Kashe wayar nayi na sai Data din dan ganin saqon nasa sallama ce afarko sai qanwata shine kikaqi karbar request dina ko dan murmushi nayi duda kuwa bansan me yasani ba sauri nayi naje nai accepting dinsa. Na koma nace amsoryy yanxu naga saqon sai dai me naita jiran replay shiru. Sai da aka kwana uku sannan ya turo tun daga time din muka saba sosai harta kai ga ya amshi wayata dan yace shi yana japan yana karatu mukan gaisa hakan yaqara qarfafa shaquwarmu saidai abu daya ke hadani dashi in yace yazo hutu yaushe zamu hadu saima inkashe wayar indena hawa online gabaki daya sai na dedaici ya koma. Yauma din tambaya ce qanwata kwanaki da yawa kin dena hawa online inna kira ki bata shiga ko dannace miki na dawo kenan nai murmushi kawai dan bani da amsa din bashi. Bai cika tambayata abinda ya shafi personal life dina ba duda shi yakan dan fadan wani abun da ya shafeshi duda ban cika cewa komi kaiba. Online na hau na bashi haquri mukasha firarmu. Zaman gidan Salma ya fara gundurata gashi inaso inma yah nasir magana kan karatuna dan alissafina yanxu shine dedai lokacin da ya dace ace an fara admission duda nasan ba lallai insamu jami'a ba tunda nasan banyi post UTME ba sai dai nakasa. Yau aunty Salma suke final paper murna take sosai duk yan nima ina tayata ji nake dama nice ita da sassafe taimin salma ta tafi makaranta. Sai yamma liqis ta dawo daga makaranta ina zaune ina sana'ar chat dina ta shigo ta fada kaina tayani murna little sis exam tayi dadi kai anman nayi murna fatan Allah yasa adace tace amin kamin tace kuma Allah yasa afara asa'a nakalleta kawai bance komi ba. Washe gari Tace in shirya zamu unguwa na shirya cikin doguwar riga yah nasir yazo ya tafi damu tafiya muke sosai mamaki na shiga yi ganinmu a BUK Aunty salma ta juyo ta kalleni kina mamaki ko nai saqare ina kallonta ta miqon takarda surprise na karba ina bude emblem din admission letter ce tawa bansan sa'adda na saki qara ba inamasu godiya. Screening Mukaje ranar kam munna ba'a magana kowa yaganni yasan ina cikin farin ciki nan naqara san yayan nawa ashe shima yasan abinda nakeso wato in zama engineer godiya har gajiya yai da yimasa. Bayan convocation dinsu anty salma ta koma gida qanwarta da batafi sa'a ta ba tazo itama tare zamu fara karatu inda ita zatayi MBBS su suna tsohon makaranta mu muna sabuwa. Watanmu daya da fara lectures akayi bikin aunty Salma sai yanzu na gane alaqarsu da yaya Nasir ashe budurwar Amininsa ce da shi yake can university of ibadan yana koyarwa shi yasa yah nasir kular masa da ita har kaduna mukaje gurin bikin tai ko murna sosai. Akan hanyarmu ta dawowa be naita sheqa amai ga zazzabi lokacin cikina watansa uku da wasu kwanakin hankalin yah nasir shida farida ya tashi sosai asubuti mukaje inda aka bashi tabbacin ai ciki gareni hankalinsa ya tashi danni ban fada masa ba agida kuma baiji ba dan bai taba tambayar inda nake ba. Zuwa yai ya titsiyeni in fada masa gaskiya wayamin nan nafada masa ai dalilin korata da akai kena yaita fada me yasa tun farko ban fada masa ba ai da tuni ya zubar nidai nai shiru dan daman zubarwar ne banaso ayi. Da muka koma gida yai yai inyadda azubar naqi ya haqura ya qyaleni kawai. Shine ya dauko min ummi diyarki dan min akace akace tunda ga ciki ga karatu ita kuma farida itama ba zama ta cikayiba tunda tare yawanci ma muke fita nakanma rigata dawowa wataran aiki duk yabi yamin yawa. Karatu yana zuwa mn da sauqi dan ba qarya ina gane abu indai an koyan gashi kuma yah nasir na iya qoqarinsa na koyamin. Lokacin da muka fara lectures na rage chat cikina bai fito ba sai dai yana dan ban wahala haka nake jurewa akwai wani malaminmu maisuna Abbakar tun gani na dashi na farko naji inasansa sai dai shi din irin malaman nanne da ko dariya baya yi magana ma kamar siye yake sai yaga dama yakeyi ni kadai nasan me ke damuna game dashi. Ko gaisheshi nayi sai yaga dama yake amsawa kallo ban isheshi ba balle insa ran zai soni inna koma gida bani da aiki sai kuka in dare yayi musanman duk lokacin dan cikina ya motsa na tuno da malaminmu sai kukana da tsanar yah mahfuz ta cikan rai dan nasan babu tayadda za'ai yasoni balle ya aureni tunda masu mutunci da basuyi cikin shege bama suna nuna masa so abanza. Lokacin da na haihu yah Nasir yasama yaron mahfuz ni kuma azahiri na tsani me sunan shi yasa nace da nawane ni Abbakar nasa masa bai ce komi ba yadai qi kiransa da Abbakar sai mahfuz yace in yaro ya girma ta zabi sunan da yake so. Sati biyu da haihuwar Abbakar yah nasir ya kawon takardar gidan da muke ciki ya bani yace yanzu yazama nawa watansa guda da siye so dama yake sai na haihu nai nai ya karbi abinsa yace ina inya mutu kuma ina zani nai murmushi kawai dan baisan inada kudi da yawa ba. Koda yake lokacin da mahaifinsa ya bani ATM dina yace kudadena suna ciki in ina buqata ba wanda ya sani dan yasan halin matarsa ko sauran yan uwansa bai fadawa ba. Yadai min kwatance inda wani abokinsa yake yace sauran abubuwa na da inda zan sami mahaifiya duk innaje zan samu dai dai ni ban taba bi takan hakan ba dan ban dauki abin da mahinmanci ba. Lokacin da nahaihu ne Abokina Abbakar ha facebook ya takura sai mun hadu dole na nemi izinin yah nasir ya yadda dan daman yasanshi dan har gausawa sun tabayi munyi dashi zaizo inbashi shawara dan nasaba bashi shawara yaji dadinta sai dai yace alokacin yafiso muhadu face to face dan matsalarsa babbace. Lokacin da na fita dan ganinsa sai ganinsa nai da yah mahfux wanda daman yace min da amininsa zaizo dan yasha fadamin kusancinsa dashi abu nagaba da ya tsoratani shine ashe shine lecturer dinmu danake masifarso. Koda na koma daki na shige nakira tah nasir na fada masa komi yazo ya kori yah mahfux da Abbakar matsayin besansu ba duda dakewa kawai yai. Lokacin da rikicin yah mahfux yai qarfine kan waini masoyiyarsa ce yasa yah nasir samo wani amatsayin mijina kanni bani bace ummun da yasani dole hajiyarsa ta yadda yasamu tabuwa. Ganin rikicin mahfux yai yawa yasa yah nasir yanke shawarar aurena duda cewar yasan da nasan irin san da yakema Farida fada mata ne kawai beba danni ya tambaya kan yanake gani nace ai sun dace sosai yace kar in fada mata sai yagama nazari kanta saidai kawai ya bijiromin da batun aurensa. Naqi yadda danni harga Allah matsayin yaya na daukeshi saidai shawarar da qawayena suka ban na amince zan aureshi dan na yadda bazasu ban shawara mara kyauba dan tun farkon fara karatuna na basu labarina duka sun tausayamin bakuma su sauyamin ba bankuma tabajin sun fadawa kowa va hakan yasa na yadda dasu sosai. Sai dai mahaifiyar yah Nasir taqi yadda qarshema sai cewa tayi ina ita ai aure dole in auri Mahfuz ni kuma ganin haka yasa cikin daren na baro kano ummi tace muzo nan. Innar Ummi ta nisa gami da share hawaye kiyi haquri Na zargeki kan abinda baki aikata ba ummu tai dariya bakomi inna ai hakan shi ke nufin ke uwa ta gari ce inna tai murmushi kawai. Wasa wasa Abbakar ya gama karade maradi da yawo yau kwana uku anman ko alamun ummu babu gashi ko hotonta bashi dashi hausar yan garin ba cika ganeta yayi ba gashi su basa jin turanci ma sai France suke ji abin duniya duk yabi ya ishe shi hankan yasa yau ya yanke shawarar barin maradi zuwa wani garin Kasuwar grand marshé ya fara shiga dake nan maradin danyin siyayya yan abinda ba'a rasa ba ya siya abinka da namiji bai wata iya siyayya ba ya fito ya koma unguwar da ya sauka mai suna kawo acan yabar duk kayansa sai abinda ba'a rasa ba ya dauka ya tambayi kwatancen tasha yai can. Mota ya hau da yaji ana kiran niyame niyame bai wata tambaya ba yai shigewarsa shidai burinsa bai wuce yaga ummu ba yakusa minti talatin cikin motar kafin ta cika su yi gaba. Ita ko ummu inna ce ta dafa ta tace to yanxu ummu zuwanku nan kina ganin shine dadai ummu ta gyada kai to anman me yasa baki nemi wanda mahaifinki yace ki nema ba ada ban niyar nemansa ba to lokacin da naso nemansa sai na tuna da abinda Abbansu mahfuz yace min. Mutumin lauyansa ne yakuma fada masa duk sanda na nemishi hakan na nufin da wata matsala to ko gidan da su yah Nasir suke ne asaida dan cireni daga matsalar dan gida nawa ne to ni kuma tun kanma ahaifen suke cikin gida tayaya zance injanyo abinda zaisa subar gidan. Inna ta gyada kai ai da sai kije kimasa bayani ba matsala bace kinaso ne kawai yakaiki gun mahaifiyarki ummu ta share hawaye kamin tace innar ummi ada inaso inje gunta da burina kullin bai wuce inyi candy inje inganta ba dan Baba mahmud wanda yake ayanxu babba agidanmu yasha fadamin zai kaini Jordan innai candy kafin ashiga tsakani na da duk yayun babana yakai yakawo cikinsu ba wanda yasan da zamana ko ya damu dani. Inaso inga ummata duda ita bata damu dani ba tunda tun randa ta tafi tabarni kafin ta yaye ni bata kuma nemana ba saidai inna banasan inje in tada mata da hankali inna kinsar ba uwadda zata so ace yau diyarta ta haihu dan ya girma kuma bada aure ba inna ta rausayar da kai haka ne ummu. Amma ga shawara kinsan kudi duk yawansu ana anfani dasu dole su qare kuma in sun qare baki da na baima mijina da sirikata zasu koreku ne ni kuma bazanso haka ba mai zai hana kuje cikin zender ku sassaro kaya inyaso sai kizo kike saidawa irinsu mai magi gishi fulawa dasauransu ki dinga sai dawa tiya tiya rabin tiya kai har gwangwani. Ummu tai murmushi nagode inna da kika fahince ni kika yadda in cigaba da zama daku gobe sai muje nida meron inna ta miqe ni bari inje in dora sanwa. Washe gari da wurwuri ummu suka fita su gwaggwo harda bada sauti alhalin ko ficika vata bada ba. Siyayya sosai ummu tai suka hawo qurqura ta dawo dasu sai yamma liqis suka shigo unguwarsu mai suna unwala, daki gwaggo ta baima ummu wanda zata zuba kayan nata bayan ta vata tsarabar da tayo mata. Zaman ummu gidan babu wata matsala dan sau da dama ma ita take bada abinda za'a dafa hakan yasa kakejinsu shiru ko fada malan musa ya dena dan zatonsa karyayi ummu ta tattara tabar gidan. Shi ko Abbakar duk yabi ya gaji tun yana baza ido yaga anzo har ya gaji yai bacci sunyi azahar ahanya anman har lokacin basu isa niyame ba. Awarsu goma sha biyu a tafe kafin sukai niyame garin ya birgeshi dan yafi maradi kyau da girma da anan tasha aka saukesu kafin ya fito daga motar. Sai da ya fito daga motar sannan hankalinsa yadan tashi sai alokacin yafa tuna bashi da masauki ga gajiyar da yai sosai shi ba abin ya koma maradi ba wannan uwattafiya haka. Can ya hango me shayi tafe irin buzayennan yai saurin kiranshi sai da yasha shayin wajen kofi hudu dayake irin qananun kofunanne sannan yadanji dadi ya bashi kudinsa shi kuma yai gaba inda yaga taron matasa gurin wani me saida kasa kasai. Sai da aka dan watse ya masa salma sun gausa kafin mutumin yace anman dai ke daga nigeriya kike ko Abbakar yai murmushi eh mutumin yai dariya haba koda naji ai daga jin maganarki na huskanta yanzu ina anki zuwa hakanna na cikin almuru. Abbakar ya nisa nazo neman qanwata ne da tazo nan sedai bansan inda zan sameta ba gashi na gaji da yawa wallahi kuma bani da masauki. Mutumin yai dariya ayya ayya seki jirani in kammala sai muje can gidana na in baki masauki Abbakar ya washe baki aiko da na gode sosai. Anan sukai sallah kafin mutumin ya goya Abvakar a mashin dinsa sukai unguwar francophonie wadda nanne mazaunin mutumin me suna muntari. A gofar gida ya saukeshi ya shiga gida yafi minti biyar sai ga yaro da tabarma ya shimfida masa ya sauna kafin mutumin ya fito da kwanuka a hannu tuwone na gero da miyar kadi ba lefi tuwon da dadi gashi da zafinsa hakan yasa Abbakar yaci ya qoshi. Adakin zaure inda qanin mutimin ke kwana anan aka sauki Abbakar din. Kwanar Abbakar biyar agarin nan yaje dik inda zaije sai dai ya rasa gano ummu hankalinsa duk ya tashi sai yanzu yagane bawai zuwa niger dinne wahala ba face gano inda take gashi kusan kullin sai ya kira wayarta wadda Ahmad ya bashi anman akashe. Sun saba sosai da muntari da kuma qaninsa Basiru yau suna zaune suna fira duk hirar ummu ce basiru yace anman me yasa baki zuwa zender nemanta tunda naga lokacin da zani fara zuwa nijeriya tacan mukabi ta magarya kuma abokina yace min duk yawanci masu zuwa Niger ta mota tacan suke bi. Miqewa Abbakar yai ai sai in tafi ma yanzu muntari ya ruqoshi ki bari gobe maje gyada kai kawai yai ya koma ya zauna. Adaki kuwa ji yake kamar gari bazai waye ba shi ji yake kamar yaga ummu ya gama. Da sassafe ya kintsa suka rakashi tasha ya hau motar maradi dan sai anje can kafin ya hau motar da zata sadashi da zender sai da ya shiga mota ya leqo yana qara musu godiya sai da motarsa ta tashi sannan suka bar tashar shi kuma muntari yai gurin sana'arsa wato saida fina finai danshi har kano yasani dan yana zuwa sayen fin qofar wanbai. Kusan irin tafiyar da sukai kafun su zo niyame sukai yanzu ma sai dai yanzu awa goma sha daya sukai. Nasaukinsa yai inda yabar kayansa dake maradi nan unguwar kawo dan yagaji sosai. Washe gari ya hau haramar yin zender duk ya bi ya rame abinka da wanda bai saba wahala sosai ba. Ita ko ummu sana'a ta karbu dan yawancin unguwanni dake nan magarya sun san da zamanta dan ita din kayanta da sauqi sosai ko akasuwa dake birni inkahe yadda take saidawa zaka samu dan ita ba ta riba take ba ta kawai juya kudin take. Yanxu takai takawo daga unguwar Ghana, Sabon gari , tudin wada , un franco,mayanka , gawo da gamdji, gawon kolliia, château, kai inma akace duk garin magarya ba'ai qarya ba..inka anbaci sunan gidan malan musa da ake sai da komi sai ankawoka har gidan. Yau wasu kayayyakin sun qare hakan yasa mero da ummi zuwa zender sayowa inda ummu da ummi suka shirya dan zuwa can niyame sayen kaya dan inna tace niyame anfi samunsu da arha sai dai nisa kawai. Gurin innar mero ummu tabar Abbakar dan yaba musu quya kuma komi yana ci. Amaradi su ummu suka fara sauka anan tasha. Abbakar yana cikin mota inda kwandasta ya shiga gami da bugun motar alamar muje fara tafiyar mota kamar ance ya dago ya hanqi wata kamar ummu ita dince ya fada sai dai cikin mota yagansu motarsu taja da gudu rasa abinda ke masa dadi yai shi ba abin yace asaukeshi ba anya kai ba ita bace abinda keta kai kawo aransa kenan. Sunyi wajen awa bakwai a hanya kafin su isa zender nanma agajiye suka isa dagyar yasamu hotel yakama anan din yau kwanansa takwas gashi ko alamun ummu babu gashi sati biyu yacema hajiyarsa zaiyi kawai. Sai da ya huta atashar da yake basu da nisa da kasuwar dole can ya nufa dan ko zai sami abinda zai ci dan wani irin hotel ya sauka basa baima mutun abinci. Acan kasuwar ya rasa mai zaici can ya hango wani mai shayi yai gurin yana kurbar shayin da yake da zafi sosai. Ya dago kenan suka zo wucewa ta gabansa indai ba gizo idansa ke masa ba wannan yarinyar itace mai ma ummu raino tabbas itace kenan yar niger ce kome ya fada gami da miqewa, buzun ya ruqoshi kudina malan ya ciro ya miqa masa. Saurin shan gabansu yai har yana dan haki sukai saurin tsayawa cikin fada mero ke fadin malan lafiya ummi ce ta dan firgita dan tasanshi azatonta ma shine Mahfuz dan vatasan mahfuz din ba. Yi haquri baiwar Allah ya fada gami da kallo ummi ina ummu take ta hade rai ni bansanta ba yadan kuma kallonta kafin ya basu hanya su shige....... Zanci gaba insha Allah [1/13, 4:18 PM] 🅰️ " AXEEX✌🏻 D'🅱️🅾️Y😎: _POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚 [1/13, 4:19 PM] 🅰️ " AXEEX✌🏻 D'🅱️🅾️Y😎: *ABBAKAR* *PAGE 130---140* Sai da sukai dan nisa ummi ta dubi mero wannan shine wanda antina ta baki labari ta gwalo ido to me yake anan bakiji yana cewa ina take ba nemanta yaso yi mun shiga uku mero tace kafin tace kinga zo muje mucewa dan bala ya kawo mana kayan gida zo mu tafi. Abinda basu bani ba Abbakar buye yake dasu har sanda suka gama yima dan bala bayani sukayi hanyar futa daga kasuwar. Gun dan bala ya koma suka gaisa kafin yace yanaso yakaishi inda zai kai musu kayan dan bala bai kawo komi aransa ba zatonsa ko irin masu sayen kayan da ummun ke sai dawa ne. Suna tafe a mota dan bala na masa surutun kaima kaima kaji labarin sauqin hajiya ko shi dai eh kawai yake cemasa har suka iso qauyen magarya. Su kuwa su ummu acan suka yanke kwana dan basu suka gama siyayya ba sai dare jafin su taso suzo maradi ma dare yayi sannan daga nan qara wata uwattafiyar zuwa zender dole sika yanke shawarar kwana gidan wani qanin malan habu mijin inna dake nan unguwar lazare dake nan niyame din. An shisshigar da kayan dan bala yaja mota yai gaba ummi sin rigasu isowa tama dan jima agida dan harta dora girki danshi Abbakar kan su tawo saida Dan bala ya qarasa sayayyar. Wata yarinya ce ta fito daga daya gidan dake kallon inda aka shisshigar da kayan riqe da Abbakar ahannunta duda magariba tayi sai da ya ganeshi dan akwai nefa saidai irin jan kwannance bakuma ta cika haske ba. Zo yace mata tai sauri taje ya amshi yaron dan tabbatarwa ta miqa masa ba musu ya sunansa yace tace Abbakar yadan rungume taron yaiko lif ajikinsa ya miqa matashi jeki ki kiramin ummamsa tai dariya ai batanan tun safe suka tafi niyame sai gobe zata dawo. Tausayin yaron ya cika shi ace yaro dan qarami haka babarsa ta tafi tabarshi harta iya kwana. Ganin baice komi ba yasa yarinyar shiga gidan sai dagowa yai yaga bata nan yaci gaba da zamansa a qofar gidan har malan musu ya dawo. Sai alokacin ya tsaidashi suka gaisa kafin Abbakar ya dora daman nine mahaifin Abbakar dan da suke zaune a gidanka malan musa yadan waro ido da gaske eh yace yajashi cikin gida to me yasa suka barka anan biyoni ciki ba musu ya bishi ciki suka shige. Kai tsaye dakin inna malan musa yai ya fada mata komi itama ta hau murna ai wai tunda matarsa take da kudi ai sai yama fita kudi sukam karensu ne ya yanke sa'a. Ummi najinsu ta kuma leqo ta ganshi hankalinta inyai dubu ya tashi ta rasa meke mata dadi ta kuma kasa fitowa duda futsarin da ya matseta. Gwaggo ce ta je ta dauko Abbakar ta dangashi ahannun Abbakar babba tana fadin Allah sarki dan albarka ashe da uba nasa muke wadin shege ne dan kawai uwatasa nada kudi yasanya bamu wadi gabanata Abbakar yai dan yaqe kawai tausayin yaron da mahaifiyarsa na cikashi. Washe gari wajen goma na safe gwaggo tai tabi gidaje tana cewa azo aga baban dan ummu aikuwa akaita zuwa. Su kuwa su ummu basu suka dawo ba sai wajen biyar na yamma duk a gajiye suke daga ita har inna sai da aka gama shigo musu da kayan kafin su shigo gwaggo na zaune ummi a gefenta tana mata tsifa. Anan suma suna zauna ummi da gwaggo na musu sannu da isowa sai da suka ci abinci sukayi la'asar kafin gwaggo tacewa ummu jiya mijinki yazo atsorace ummu ta ce mijina eh gwaggwo tace yanxu yana ina inji ummu yadan fita shi da dansa. Dansa kuma eh danki mana ummu ta miqe badai Abbakar nawa ba eh shi kenan nashiga uku an gama dani hankakin inna ma ya tashi to wazaizo har yace shi ne mijin ummun harya dauke mata yaro komdai masu garkuwa da mutanene tunda kowa yasan uwar yaron nada kudi. Sallamar da sukaji yasa ummu saurin juyawa danko mafarki take intaji muryannan tasan me ita zata kuma iya gane muryarsa cikin maza dari. Shi dinne riqe da Abbakar dinta akafada da alamu ma yayi bacci tasaki ajiyar zuciya gami da fadin Malan kaine ya akai kazo nan waya fada ma

Chapter 8 of 15