yake sosai alamun yunwa yakeji yadda yakesha da kuma tunanin da zuciyarta ta tafi yasa batasan sa'adda hawayen da suka cika mata idanu ya zuboba.
Jitai an dafata ta baya tai saurin jiyowa Hafsa ce kinsan tun dazu muke nemanki ina su fatima inji maryam assha kukan me kike haba ummu ki dinga ragema ranki damuwa pls inji maryam ke wallahi kina da matsala nasan duk bazai wuce kan exam din yauva kawai ki shateta exam luck ce kawai inji hafsa to Allah ya bamu sa'a su suna waje jen fais muje nace su jirani.
Suna tafe hafsat na selfie da dan surutanta intayi wani tauawo ummu tayi musu su biyu wani ta jawo maryam, yayin da maryam ke faman tambayar ummu wace amsa ta samo a questions din yau wasu ummun ta bata amsa wasu kuma tai shiru.
Sun yi photocopy din inda fatima da amina suka wuce toilet na CIT mosque basu jima ba suka dawo.
A bus stop suka hadu da halima da sauran frnds dinsu sun hau mota tare yan hanya sun sauka ahanya yayin da su suka sauka a old side din sch din tasu dan can ne gun da zasu.
Sinyi rashin sa'ar samun duk wanda sukaje nema hakan yasa kawai ko wannen su ya wuce gida kan zasu hadu ran alhamis.
A gida ummu ta rasa me ke mata dadi dan tun randa Abbakar ya titsiyeta batajin dadi ita ba abin ta fadawa Nasir ba tsoronta daya kar yaje ya ballo mata ruwa abinci ma ba koyaushe take ci ba ko tahajin yunwa data fara ci zataji ya fita aranta.
Ran alhamis da sassafe ummu ta shirya tai sch dan sunyi zasu hadu dasu hafsa 10 na safe.
Basu wani makara ba sukazo duda kuwa ta dade da zuwa Fatima ce last din zuwa suka dunguma sai math department sunyi rashin sa'ar samun wanda sukaje gunsa bayan sun tambayi maqocinsa ko zaizo ya basu tabbacin zuwansa suka koma qasa dan jiransa.
Zaune suke sina hira sama sama yayin da karatin paper din dazasuyi yau yafi qarfi maman humaira ce ta dauko wata paper suna dan tattaunawa akai dagowar da Aisha zatai taganshi yazo suka miqe dan bin bayansa.
Faduwar da Hafsa tai ne yasa har isarsu bakin office din basu bar dariya ba ganin office din abude yasa su shiga taitayinsu suka jira na ciki ya fito kan su shiga.
Bayan sun gaisa cikin hade rai ya ce lafiya me ya kawoku paper dinta Aisha ta nuna wadda ya rubuta not recorded ya amsa da Id dinta ya shigar yayin da fatima tace complain gareta ya karba yana dubawa.
Ya dago a fusace haka na koya muku tai tsuru tsuru ya miqo mata paper dinta yayin damaman humaira tamiaqa tata itama fadan yasa hafsat na gefe tana dariya qasa qasa.
Ganin da taske ficewa zaiyi yasa Fatima yin qarfin halin qara miqa masa nanto sir bakamaka ba ya karba ya soke sir but ka makawa wasu dedai yai tsaki itama ya maka mata
Sir wai zaka bada attendance inji wa ni nai attendance ne a class dinku gabaki daya sukai tsuru tsuru pls ku fita sauri nake.
Aisha ce ta miqa nasa sir nima baka makan nanba kuma nan nayi dedai ya amsa tsaki yaja kowa ma ban maka masa ba nankuma mene sir gashi nan miqo mata takardarta yai pls kumuje nan sawa kikai wallahi sir bafa sawa nayi ba zakace nasa Dallah muje yaje suka fice gabaki daya rai abace.
Sunfi minti goma suna mita yayin da ita dai
ummu bakin naganarma babu jitake kamar tai kuka dan ita bama tayi test dinba gashi exam din se a hankali shi yasa takejin su mitar dadi ma suke.
Se wajen sha biyu maryam tazo suka bata labarin yadda sukai da malamin tai ta dariya kafin su juya akalar firar zuwa karatu.
Sai qarfe Daya da wani abun suka bar old side zuwa new side inda zasuyi exam dinsu ta yau suna tafe a mota suna fira yayin da kadan kadan suke taba muraja'ar abinda suka karanta.
Gidansu Abbakar Hajiya ce ta shigo dakin dan nata da sallama ya dago daga kan computer din gami da dan matsar da ita ya amsa sallamar bata zauna ba tace leqowa nai inga ko lafiya tunda kazo gaisheni banji motsinka ba bakuma kazo kace min ka fita ya yadan sosa qeya gami dayin murmushi yanzu nake shirin fita ina da jire dalibai wajen qarshe biyu da rabi inata faman duba wani assignments ne dana baima yara tai dariya yayi kyau ai gwara ka hanzarta yanzu shabiyu ta kusa ya miqe ahto bari in wanka ta fice shi kuma ya shiga toilet.
Saida ya shirya sannan ya sakko Abinci kadan yaci dan baya san cin abinci da yawa inzai fita yana kuma san zuwa gidansu mahfuz yasan indai time in cin abincine sai haniyar mahfuz tasa yaci abinci ko baya so.
Hajiya ni zan wuce harka shirya eh to Allah ya yemaka amin hajiyata ta fada yana yin gaba.
Haryakai bakin falon ya dawo waiko hajiya ina wannan mara kunyar take tai dariya maza taji kana ce mata mara kunya ta tafi exam af fa hakane tacemin jiya sunada paper yai waje.
Yana shirin barin main falo din wanda dagashi sai farfajiya suka shigo Kadija ce qanwarsa wadda take aure a Zariya sai yaranta guda uku nan danan fara'arsa ta qaru a'a manyan baqi yaran sukayo kansa suna ihuuu uncle uncle ya daga su dai dai kafin su rungumo juna shida sister din nasa suna yaushe gamo ciki ya bisu dauke da qaramin data ke goyo ina hajiya ma na ganinsu murnarta ta qaru.
Yaran sukayi kanta da gudu qaramin ma yasa ihu saida ya saukeshi shima ya fada kanta ohni hashina yarannan so kuke ku qarasani Abbakar yai saurin cewa ku daga mun uwani karku karya min ita a'a kaga malan ka qyalen yan jikokina su mori kakarsu suka juyo suna masa gwalo suka saka daria gabakibdaya.
Keda me gidanne yake tambayar qanwar tasa a'a mu kadaine sai zamu tafi zaizo sai su gaisa da hajiya ok yayi kyau yadan kalli agogo opps zanyi latti inna dawo dai koma mene ne ma tattauna ya miqa mata hannu sukayi musabaha kamar yadda al'adarsu take sun riga sun saba to sai nadawo to yah sai kadawo da labari naga alamu ko tai dariya kaidai bari kawai sai kadawo nagama duk kayi baqi dama can baqin nake kinga sai nadawo ya fice aiko Malan qarami ya taso da gudu yabi bayansa yana kuka uncle uncle mamanshi tai saurin daukoshi ta dawo dashi ciki.
Ko gidansu Mahfuz din baijeba ya wuce sch dan yaga ya makara.
Wayarsa ce ta fara qara time in da suke raba booklet ga student ya migama malama zainab dan basu ina zuwa sunan ummi mabiyar autarsu ya gani kan wayar towo ya fada yasan yanzu ai yakamata tana exam room yai saurin dagawa cikin kuka take magana yah ina cikin matsala subhanallahi mene badai malpractice aka kamaki dashi ba ko tai saurin goge hawayen kamar tana kusa dashi kaji kuma yaya Abinda banyi da ba zanyi yanzu.
Sai yanzu yadanji normal to mene wallahi yaya ina cikin matsala kana ina ne ni ina chemical engineering ok ganinan bata jira cewarsa ba ta kashe ya tsaya kawai yana kallon wayar kome wannan yar rikicin ta jawo musu kuma oho dan ko autansu baya abinda take kai tama zama tafi autan tabara hajiya kuma tai ta goya mata baya kodan shi autan baya qasar ne oho.
Minti biyar sai gata kamar wadda tai gudu tai futu futu da ita kallo daya yamata daga ajin da yake yaja tsaki sannan ya kuma yima malamar da suke kula da daliban magana pls ina zuwa.
Waike lafiya kika dokan kira haka tasa kuka yah na mance ID dina kuma sun hanani shiga towo ni me kike so na miki yanzu ta kamo hannunsa so nake kaje ja roqesu nasa Bala yaje ya karbo min to se ki bari yakawo ai.
Dan Allah yah kaji qaina kasan in aka fara fitowa bazasu barni inyi ba yai shigewarsa ajin ni nace ki dinga sakaci gobe kya rage lalaci da mantuwa aikuwa ganin ya shige ajin ta fashe da kuka.
Wajen minti biyar saiga malan Mansur yazo ya shiga ajin suka gaisa kafin su fito tare tasan mansur lecturer dinsu ne saidai yah nata bai taba ce mata yana da aboki a faculty dinsu ba balle department din datake kullun sai dai ya dinga cewa ta dage tai karatu danshi ba abinda zai iya mata.
Ya dagota yawwa gashinan abokina zaije ya rakaki anman wallahi inkina irin haka karma ki yi tunanin kinsanni tai tsalle tama mance a inda suke ta fada kansa that's why i love u mansur yace muje kina kuma makara tai saurin saukar da ido qasa wai taji kunya tabi bayansa suka wuce.
Duk abinda suke ummu na kallonsu ta tagar ajin da suje wani abu yazo ya tsaya mata arai ita kadai tasan mene kawai ta cigaba da rubutunta.
Ta gama rubutunta tas tana kuma dubawa na kusa da ita ya mata mgn juyowar da zatai tace me kace a idon Abbakar aikuwa yayo waje submit yace sorry tace bazaki bayar ba kena no ba hk bane ko ki bayar ko ki cike form dinnan ya miqo mata malpractice form tai saurin bashi tana singing out hawaye na bin idanunta ita kadai tasan hawayen me take dan bawai na anqwace bata gama bane.
Tunda ta fito take kuka har Aisha ta fito dagyar suka sa tai shiru ita da halima azahiri kenan anman a badini tai shiru ne kawai bawai dan taji nasihohinsu ba dan sanin bata da wata mafita inma kukan ta cigaba dayi shirun ma shine mafi alkairin kawai.
Sunfito suna masallaci danyi la'asar su tafi gida Hafsa ta dube ta idonnan yai fayau dashi tana riqe fa Abbakar Allah ummu mutumin can sanki yake wa kenan malan Abbakar mana taja tsaki maryam tace mene haka hafsa da aurenta fa yanzu in mijinta yaji yace mene haka nefa na mance ai wallahi kinyi sa'ar miji me sanki gashi me kyau halima tai dariya a'a Hafsa kimana shiru karkisa yanzu muga ta miqe ta hau jibgarki kinsan kishi gabaki daya sukai dariya inka dauke ummu da kana kallonta kasan yaqe take.
A old side Hafsat tace ita zata ta amso wata takadda Aisha tace tunda muka fito nakira mam nace mata munfito nidai na tafi to sai gobe suka hau dan sahu ita da ummu da fatima da halima halima ce ta fara sauka a danja su kuma aka wuce dasu.
Halima na sauka ummu ta dubu Aisha inasan magana daku ina cikin matsala wallahi but me yasa tun dazu baki fada mana ba to yanzu munajinki no inaso mu samu guri ne anman yanzu ki ba sai gobe.
Gobe kuna kun mance an gama exam ah hakane tacema dan sahu pls tsaya anan ya tsaya daidai legal college of islamic studies ku fito what kinafa ji nace miki na ce mam na tawo pls ina buqatar shawararku ne da gaggawa.
Aisha tadan tsaya jim tana tunani me adai daita sahun yace zaku saukanne ko mu wuce fatima ta fito tana juyar da fuska wai ita kar wani fa tasani yaganta ta sauka a qofar sch din akai gulmarta gida ummu ta miqa masa kudi Aisha bata da zabi ta fito.
Sun nuna ID dunsu na BUK sun kuma yi sa'a anbarsu sun shiga cikin kujeran da aka tanada dan zaman students na bakin bishiya suka zauna.
Ai kuwa suna zama ummu ta fashe da kuka dagyar tai shiru saida Fatima ta miqe kinga inbazaki fada mana ba ni zan tafi ta rugo hannunta alamar ta dawo ta zauna.
Ta komo ta zauna ina cikin wani hali mene ya faru munce ki dena wannan damuwar kinqi.
Yah nasir ne matsalata me ya miki inji Aisha fatima ta dafe qirji badai cewa yai kibar masa gida ba in wannan ne ai me sauqi ne to mene suka fada cikin tsoro.
Wai cewa yai yana sona mtssss suka ja tsaki atare to saime ke ba abin farin cikinki bane mutumin da duda yasan komi game dake ya dauki kasadar riqeki duda yasan hakan zai iya rabashi da iyayansa yadauki nauyinki ya rufa miki asiri kika zo cikin Abbakar nanma bece komi ba ya dauki ragamar komi to mene ba damuwa.
Cikin kuka tace ni banasansa indai so na aure ne what ummu kinsan me kika ce kuwa eh nasani to wa kike so in bakya sansa Abbakar suka mike gabaki daya arazane suka maimaita Abbakar eh shi wai wane Abbakar din lecturer dinmi ba thermodynamic badai wanda ya koroki yauba eh shi ni shi nakeso nayi nayi na cire abun araina nakasa.
Tabdi kin dauko dala ba ganmo inji fatima Aisha tace haba ummu karki zama butulu mana ta ture hannunta da ta dafata ni shi kadai nake so shi kadai nake gani shi kadai ne burina shi kadai nake gani dashi na shirya rayuwata gabaki daya pls ya isa haka fatima ta fada cikin fushi bansan shirme wallahi........
[12/31/2020, 5:52 PM] 🅰️ " AXEEX✌🏻 D'🅱️🅾️Y😎: _POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚
[12/31/2020, 5:52 PM] 🅰️ " AXEEX✌🏻 D'🅱️🅾️Y😎: *ABBAKAR*
*PAGE 70---80*
Haba ummu kiyi tunani mana ai kinsan ko da Abbakar ba abokin Mahfuz bane babu ta yadda za'ai ya yadda ya aureki kina ganin yadda yan mata masu aji ke faman sansa kuma ya sani bawai be sani ba anman ya sharesu.
Ki daurewa zuciyarki karki zama butulu Yah nasir be cancanci haka ba yacancanci duk wani karamci daga gareki ya miki duk wani halacci na rayuwa kidaure ki sake tunani wallahi.
Nifa ba cewa nayi bazan aureshi ba ni wallahi amatsayin uba na daukeshi koma uwa da uba na taya kuke ganin zan iya zaman aure da wanda nakema kallon iyayena.
Daurewa zakiyi ahankula inkika ce kin amince kuka fara soyayya tuni zaki mance da a ina kika ajiyeshi kina kallonsa haka simi simi zai baki mamaki dan irinsu sunfi sanin takan mace batasan sanda tai dariya ba wallahi baku da dama ko kadan.
Sunji dadi datai dariya yawwa ko kefa ki dena yawan kuka da damuwa kisama ranki dangana yanzu ki daure in yazo ki fada masa bacin yai fushi ya dena zuwa kingani ko duk haqurin bawan Allahn nan.
Yanzu ki kirashi ki bashi hakuri kice kin amince wa ni tab inba bazan iyaba kuma tunda ya hanani kiransa iyanzu sabida yace yana gida ok to ki bari sai dare lokacin ya shiga daki tai jim tana tunani kinga inbazaki iya kiransa ba ki tura masa saqo kawai to shikenan sai na koma gida.
Shi kuwa Abbakar tun da ya qwace paper din ummu yana kallon ta time inda take singing hawaye na bin fuskarta jiyai kamar ya bita ya rarrasheta ko ya goge mata hawayen saidai ba dama.
Yar firar ma dasuke da daya malamar duk sai ya kasa ransa gabaki daya ba dadi yaji sai faman fada kawai yake qarshe ma tasauran student din karbewa yai danji yai gabaki daya ya tsani ajin.
Futowar da zasuyi hangota tana faman kuka ana bata baki nanma jiyai kamar yaje yashiga sahun masu bata bakin yadai dake kawai.
Sai mangariba ya koma gida shima dan kar hajiyarsa taji wani abu badan yaso ba dam jiyai gabaki daya baisan hayani yama mance da qanwarsa tazo duk dokin da yake na yaje ya dawo su kwashi fira ya tafi.
Saida ya shiga falon yama tuna hakan yasa ya fada da murmushin fuskarka ya shiga da fara'a.
Tana ganinsa ta quntse fuska inba nayi fushi ba aikasan da zuwanmu shine sai yanzu zaka dawo yazo ya zauna kujerar dataje inba bakiyi fushi ba ya fada yana irin yadda tayi tasa dariya Yaya ta fada shima yasa dariya qanwa bari in shiga in rage kayan jikina sai in sauko to se ansakko.
Danqaramin danta yasa kuka ya daukeshi ya daukeshi sukayi saman tare yana masa fira irin tasu ta yara.
Tare suka sauko yana dauke dashi da alawa ahannunsa aikuwa yana direshi mai bi masa ya sauko daga kujerar da yake faman game ya kwace alawar ya tura baki aikuwa ya tsanyara kuka dasauri Abbakar ya juyo OMG this boy me aka ma ya fara nuna yayan nasa da alawa abaki.
Ah wahid ya zama babban kwabo yai saurin miqa masa alawar wasa nake masa fa suka sa dariya dan wahid bayasan ace masa babban kwabo dan zatonsa kwabon wani abu ne marar kyau.
Shima wata Abbakar yadauko a aljihu ya miqa masa yakoka yana tsalle thank you uncle dayan ma ya taso ya miqa masa sai muskilin nasu baya maga sai yaga dama mutane da yawa nacewa Abbakar yayo musanman babansu danshi yace duk danginsu babu muskili aikuwa ganin anbawa kowa ba'abashi ba ya zumburo baki ya huro hanci sai hawaye da sauri Abbakar yai gunsa haba nawan mene na kuka kuma yai shiru to shikenan ya goge masa hawaye.
Ya bude alawar ya vashi to ungu kaga takama ni na bude maka ya miqe zai koma ya zauna ya riqo rigaraa ahankula yace thank you uncle yai dariya kawai.
Hira suke sosai gabaki dayansu har hajiya tace kunga ni na gaji saida safenku duk an miqe sai ummi yah Zainab sai da safe inkika biyewa yah Habu saiku kwana anan ya kalleta wato yau rashin mutuncin naki kaina ya koma ko.
Tai dariya ai tunda kasa nai kuka asch na yah Habu zan dinga cewa tai daki da gudu ya kada kai yana dariya dan in ummi ce komaima zatayi shi yamayi mamaki da ya dawo bata sa hajiya ta cakcakeshi va dan yasanta da sharri.
Zainab ce ta juyo daman tun dazu wallahi nakesan muyi magana ya kalleta me ne kuma daman Babansu wahid ne nace masa inasan in koma sch in cigaba da karatu qeme me ya hanani yai saurin kallonta to me kike nufi yaji kika yo kome.
A'a ba yaji nayo ba wallahi kawai ziyara ce nadai fada ma ne dan Allah ka roqarminshi ya yadda ehto ba roqarsa zanyi ba zan saneshi muyi magana in ya yadda to inbe yadda ba ki haqura masters dinki ya isheki keda ba aiki kike ba ina jarin dana baki kwanaki tahau sosa qeya duk sun qare ko tai dariya kawai.
Shikenan kibari inasa ran shigowar kudi na kayan gonata danake na sayar zan yi qoqari in bude miki dan qaramin store in kikai maintaining dinsa ya isheki rayuwa mijinki ba abinda ya rageki to yah na gode.
Sauran daya maganar inajinki yah dan Allah kafadan meke damunka duk kayi baqi ka rame yai dan murmushi me kuwa ke damuna kawai yanayin aikine kullin cikin jele daga han zuwa old site daga can zuwa new site ba dole mutun ya rameba anman yah anman qarya nake ko a'a ni ba haka nake nufi ba.
To tashi muje ku kwanta kar gobe yarannan su tashi da wuri su hanaki bacci kanki yazo yana ciwo ta miqe ta sabi yaro guda shima yadauki biyu qananan ta tashi babban suka wuce dakin da zasu kwanta saida ya kwantar mata dasu ya mata saida safe ya wuce dakinsa.
Zaune take tana ta faman rubuta saqon da zata tura masa tana gigewa ta rasa me zata tura mai qarshe dai ta rubura
_Assalamu Alaikum
Yah nasir barka da dare daman cewa nayi na Amince Alkah ya bamu zan lpy_
Gabaki daya tama kashe wayar tahau kuka bayan ta tabbatar saqon ya tafu.
Yana kwance idonsa akan fanka shi kansa besan tunanin me yake ba yaji alamar shigowar saqo a wayarsa kamar kar yadauka ya duba yadai daure ya miqa hannu yadauko.
Ganin sunan ummu yasa shi miqewa ya zauna tunkan yaga saqon yai saurin budewa duda ba wata magana bace me yawa sai saqon ya masa dadi sosai jiyai kamar yai tsuntsu yaje ya tabbatar ita dince ta turo ba kuskure bane.
Yaso tashi da wuri saidai kasantuwar bai kwanta da wuri ba yasa sai wajen tara da rabi ya tashi.
Wanka ya fara yi shi kansa baisan meyasa yake dokin zuwa ganinta dinba besan me yasa yake ta dauko kaya yana sauyawa ba duk dan ya burgeta duda yasan tasanshi batun yauna.
Shadaya dedai ta masa a gidan ummu Farida ce a farfajiyar gidan tana karatu abokiyar zaman ummun tana ganinsa ta saki fuska sir barka da zuwa yadan hada rai sau nawa zance a dena cemin sir dunnan a gida tai dan murmuahi sorry sir kika kuma yai shigewarsa ciki ta biyo bayansa tana dariya.
Yai saurin cafe Abbakar ko ince mahfuz da ya rarrafo zuwa bakin qofa yana bin ball insa ya ko tsanyara kuka dan besan waya daukeshi ba Nasir yai saurin juyo da fuskarsa haba yaron babansa jin muryar nasir yasashi yinshiru yana ganowa a hannunsa yake ya bangale da dariya alamar farinciki.
Dan rigima wato da bani bane shikenan sai ayita kuka ko Ummi da ta zo daukansa tasa dariya itama lah yah nasir ashe zakazo yai dariya ce miki akai da nadena zuwa a'a nadai ga kwana biyu baka zuwa ne suka shiga falon gabaki daya har Farida.
Wallah yah nasir nayi missing inka da yawa eyye ko eh mana inji Farida duk ganina da kike a sch ta dan rausayar dakai bayan a sch din nuna wa kake baka san mutane ba Allah ko eh mn inka wani hade rai to shikenan maida wuqar zan dinga dariya sukai dariya baki daya.
Ta miqo masa littafi Allah tun jiya nake karanta nan nakasa pls koyan yakarba ya duba eyye wato duk lecture din da muku bakima gane ba tadan juyar da kai time inne inajin bacci to ynx ma ai inna miki cewa zakiyi bacci kike ji dan Allah yah nasir to shikenan bari sai anjima.
To wannan fa ta miqa masa paper a'a banda wannan ai assignment na baku pla yah inkika isheni ko sauran bazan koya miki ba wai ina Ummu ne ta dan fita ne nasan yanzu zata dawo.
What ina taje mene anfanin ummi da na kawo mata tace batasan aiken ummi bata rufe vaki ba Ummun ta shigo ya hade rai daga ina kike naje shago ne ko dan kinga kwana biyu bana zuwa shi yasa kika tsiri futa yawo.
Idonta yai rau rau kamar zatai kuka haba yah nasir kasan bana maka qarya to me yasa baki aiki ummi ba naga batasan zuwa ne what no bawai qi take ba aikenne kamarta dole taji kunyar zuwa wane irin aikene ta miqa masa always ya gani oh basai ki fadanba da wake sayo muku tadan turo baki to inama muka ganka bacin ka dena zuwa yadan sosa kai aishi kenan.
Farida ta miqe tai waje yah bari inje inci gaba da karatuna ummi tasa hannu zata dauki Abbakar yako sa qara Nasir ya ce jeki abinki kyaleshi tai ciki.
Ummu ta zauna yah ina kwana lafiya kalau yace ya dannawa ta kalli Abbakar ganinan ai.
Jiya sai naga saqo tai murmushi ashe ma shi ya kawoka yai dan murmuahi dadinsa da ita akwai bawa mutun amsa haka nace miki shi ya kawoni to yaya rabonka damu kwana nawa bakiga exam ake a sch ba bani da time inkuma nakai dare kinsan hajiya tai dan murmuahi batare da ta amsa ba.
To anman yah kana ganin family dinmu zasu yadda da aurenmu yai dariya gami da sauko da Abbakar to aiko basu yadda ba abinda nasani ni shine dolene su yadda tunda kin yadda ta kalleshi ya daga mata gira.
Fira sukai sosai sai da aka kira sallah ya miqe bari in sallah ya fice.
Haka kawai ummu kejin takaicinsa ya ragu aranta haka kawai takejin hirarsu ta
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 4 Chapter of 15