Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
abu ya hadashi da Abbakar ya daddakeshi sai ta masa rashin kunya. Data girma mutunci ya shiga tsakaninsu karatu ma da Abbakar ya tafi waje karatu shi yake koya mata dan basa shiri da mahfuz ko kadan dan ta ganshi yanashan taba ita kuma indai kanashan taba ta dena ganin girmanka yayin da mahfux mutun ne me dan banzan san girma. Jeki kice ya shigo tai waje suka shigo tare Aisha ta dauki qaramin Abbakar sukai cikin dakin ummu Nasir ya zauna yana sun sun da kai. Sun gaisa kafin hajiya tace yanxu Nasiru dan zaka shigo gidannan shi ne sai anma iso da wani kema yadan sosa qeya yana murmushi yayi kyau yanzu yaushe rabonka da gidannan ina zaton tin haihuwar zainab ta farko da tazo wankan gida ya sosa kanshi gami da sun kuyar da kai wallahi abubuwa sukamin yawa. Eh haka ne shi yasa ai kake iya zuwa katsina ziyara yai dariya ni kuma ga hanci ga baki baka iya zuwa sabida abubuw sun maka yawa can dinma saifa aiki yakaini uhum tace ai shikenan. Tinda yanzu na dauko qanwarka ai dole in ganka Allah hajiya ba haka bane Nadiru kenan ta fada gami dayin shiru. Daman magana nazo muyi to inajinka kan mene kan karatun ummulkairi ne ok inajinka. Kinga tayi nisa yanzu ace saita sake jamb ta jira admission kamar abin beba shi ne naga tunda anyi sa'a ta dawo ba'ayi exam ba mai zaisa ta koma ko co tasamu ta gyara nan gaba. Haka ne kayi magana zanma mijin nata magana yawwa yace wasuma sunyi test anman na roqesu zataje su mata inyaso inta koma sai taje din abinda bata ganeba sai shi Abbakar din ta koya mata bama sai ya koya mata ba in qawayenta sun kasa in yaso saita kiraka to yace gami da miqewa ya dire handouts din da ya shigo dasu gashi sai abata wadanda ta siya kan hutune sai wasu kuma wanda malamansu suka bada ne na sayo mata godiya hajita tai yai waje ransa fal farin ciki danshi daman burinsa ummu tasamu inda ake santa. Sai yanma su Aisha suka tafi tunda ansan da zuwansu daga gidajensu. Koda ummu taji batin komawarta makaranta tai ta murna tanama Yayanta addu'a nasir koma ince uba dan ita aranta jinsa take yafi qarfin matsayin yaya gareta saidai uwa da uba. Washe gari sai gasu Hafsa ita da Ahmad Ahmad ummu tai murna sosai suka sha firarsu anan su ummu suka tafi suka barshi dan zai koya mata wasu abubuwan da bata ganeba cikin wanda taga yah nasir ya rubuta mata zatai test. Ummi (me aikin ummu) dan tun dawowarsu Abbakar ya maida ita sch duda kafin su gudu ma Nasir yasata dan basu barta a niger ba shigowa tayi sanye da kayan islamiyya ta qaraso inda suke karatun tana washe fuska da yake tasan Ahmad sosai lokacin suna zuwa buk namata namatansu ummu kenan kullun yana cikinsu baifi sa'ansu ba ko su ya girme musu da kadam shine kuma captain dinsu. Mutuncinsu da ummu ya fara tun wata rana baya zama a baya suma su ummu haka saidai suk qawayenta sun gudu gida kan bazasu ji GSP ba tace ita kota koma gida ba kowa zamanta zatai. Ta shigo theatre din inda ta aje jakarta sai dai ya sauke yai dare dare kan kujerar aikuwa cikin fada ta qarasa sai dai ganin captain ne yasa tadan sassauta captain pls tashi kaban gurina yai banza da ita ga malami a ajin ko tsoronsa bataji ba ta kuma magana katashi nace yace bazan tashi va wani yace ki fuce eyye yana murguda baki dan ya iya abubuwan mata da yawa. Malamin yace dakai da ita duk kuyi waje ta jiyo anman malan yimum shiru nace kuyi waje ya miqe pls sir harsun kai waje malamin yace ku dawo ga kujera can abaya guda biyu kuje ku zauna ya nuna baya. Ummu tai can gefe yace madan guri guda nakesan kuzauna ta dawo tana turo baki Ahmad na hararta sai dai kamin atashi har fada ya koma fira dan Ahmad surutunsa yai yawa ko sati ba'aiba duk insa ya gansu sai yaje yana tsokanarta wai ta fiye fada har suka saba sosai ya zama amininta bama aboki ba tun qawayenta na tsokanarta mai aboki namiji kodai kodai har suma din ya zama abokinsu dan shi din mai saurin sabo ne kasantuwarsa duk yan uwansa mata yasa baijin komi dan yana cikinsu. Ummi ta dan durkusa ta gaidashi ya amsa yana murmushi maman Abbakar andawo tai dariya eh to sannu da zuwa ina tsarabar guduwa ta rufe fuska abinka da yarinta batafi goma sha biyu ba zan kawo maka ai na dauka bazaka zoba yai dariya to gashi na baki mamaki tai ciki tana dariya. Sun ci gaba da karatunsu ummi ta dawo riqe da kaya irin na yan niger gashi tace ya amsa yana dariya duk wannan eh tace to na gode tai ciki abinta. Ya kalli ummu Allah diyar nan taki tayi kinga da ace na isa aure ai bada nan ba ummu tasa dariya kaifa shaqiyancinka baya kadan. Allah da gaske nake to banda abinka kana shekara sha takwas wazaima aure yadan hade rai ashirin dai au haka ne kaka tsoho kawai ki dinga ragen shekaru da girmana da mutuncina sukai dariya baki daya kinga fa dagaske nake ya za'ayi ina ciki fa to kabari ka qara hankali in naga zanbaka sai inba eyye wato yanzu bani da hankali suka saka dariya baki daya. Hakan yai dedai da shigowar Abbakar a mota aikuwa idanunsa kan ummu dake faman sheqa dariya wani malolon takaici yazo masa wuya gami da kishi afusace ya bude motar yai gunsu shi kansa baisan me zai yimusu ba in yaje anman yasan tabvas bazasuji da dadi ba.... [1/13, 4:20 PM] 🅰️ " AXEEX✌🏻 D'🅱️🅾️Y😎: _POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚 [1/13, 4:21 PM] 🅰️ " AXEEX✌🏻 D'🅱️🅾️Y😎: *ABBAKAR* *150---160* Ransa duk a bace yayo gurrin baiyi shi kansa baisan yana da kishi irin haka ba sai yanxu ganin ummu da wani da daga nesa bai gano ko wane ba. Sai da yazo dan kunya ta kamashi ganin Ahmad dan yasanshi abokin su ummun ne qoqari yai ya qaqaro murmushi kamin ya qarasa din, Ahmad na ganinsa yai saurin sauko daka kan kujera yana fadin lah sir sannu da zuwa Abbakar yadan saki murmushi kamim yace ah Ahmad yau kaine a gidan namu yai dariya eh tun daxu muka zo dasu Hafsat su sun tafi nima nakusa muna dan yin abunda zatai test ne ok yayi kyau yace. Ya maida kallonsa ga ummu yace shine baki fadan zaki fito farfajiya ba ko tai masa banza ince dai baki tafi yawo ba da sunan raka qawaye hawa mota ta juyar da kai tana fadin to sabida me zan fada maka qasa qasa take maganar eyyi me kika ce tace cewa nayi ai naga na fadawa hajiya ok ya miki kyau ya koma gurin motarsa. Ahmad ya dubeta ashe daman kinsanshi baki taba fadanba tai dariya bansanshi ba kawai dai ashe shine frnd dina da nake fadama na facebook kai dan Allah kice chat ya hadaku tai q wayasan masa baifa taba ganina va time in muna chat kai da gasqke ka mance su haka nefa. Bama kasan wani abu ba ya kalleta yana fadin mefa wai nan mijina ne wai mijina ne ya tafa hannu gami da riqe haba kai dan Allah tai dariya Allah ya shiryeka ka dinga abu sai kace mace. Nan ta bsshi labarin komi har aurensu tunda daman tuni yasan tarihinta ya kuma tafa hannu ai mukam kice A abagas zamu sameta a course dinsa tai dariya ai seku dena karatu shima yai dariya. Ko da Abbakar ya shiga ciki Hajiya ta masa maganar batun Nasir yace ina sam shi yadda ba tunda ummu matarsa ce ba wani karatu da zata ci gaba wanda tayima ya wadatar. Aikuwa hajiya binsa kawai tai da ido ganin ta miqe zai tafi dakinsa ne tace Habu zonan ya dawo ya zauna . To bari kaji wallahi kayi kadan ka hana yarinyar nan karatu dan zalunci inma kana ganin kudine bazaka iya biya mata ba ni zan dauki nauyinta balle kuma tanada yaya wanda zai dauka yai shiru. Maganar aurenka in dan kana aurenta ne kake ganin bazaka barta tayi karatu ba to hanya mafi sauqi ka sawwaqe mata Inada wanda zan bata yai saurin kallinta a'a hajiya bama sai ankai ga haka ba tai tsaki gami da yin dakinta. Acan kuwa gidansu maganar aurensa tai nisa dan tuni hajiyarsa ta gama magana da aminiyarta zasu hada auren zumunci tsakaninsu badan komi yasa aminiyar amincewa ba sai dan sanin halin diyarta. Duda cewar tasan halin mahfux sai dai tasan da cewar yafi yarta nutsuwa nesa ba kusa ba. Dan yarinyar tata takai matuka wajen rashin mutunci dan in iskancin ta da rashin mutuncinta ya motsa har gida take kawo qato inko ta bar gidansu sai anganta. Bakomi yasa salma yadda da aurenba sai dan daman tun da tana san mahfuz dan yana cikin mazan da take so shi yasa koda mum din ta tazo mata da tanaso tai aure ta fara fada jin wazata aura yasa ta hau murna ta rungume mum dinta gaskiya mum kin gama mun komi da kika neman auransa. Mum din tata tasa dariya cike da farin ciki yawwa yar gari. Kinga kafin ai aurannan sai mun gama dashi dan tuni na gama da uwassa so nake kiyi zaman farinciki gidan aurenki dan haka dole musan yadda mukai sai abinda kika ce masa suka tafa kai kace ba uwa da 'ya bane. Shiko mahfuz ko kadan baya wani farin ciki da auren kawai dai yana dan shassharewa ne dan kar hajiyarsa ta gane. Shi kadai yasan me yake shiryawa dan ya qudiri aniyar kwato dansa kota yaya ne. Zaune yake shida lauya dinsa yace wai mansur yaushe zamu fara zaman kotunnan ne wallahi na qagu inga yarona jikina nafiso da ya fara magana ya fara da kirana baba ba wani qaton kawai ba mansur yai dariya yanzu mahfuz aminin nakane qaton kawai yaja tsaki kaga gyara maganarka ba amini na bane. Ya dafashi da zanbaka shawara kabi da kadaure ka janye qarar nan inaganin in yana gun Abbakar ai kamar yana gunka ne mahfuz ya daga masa hannu kaga malan in bazaka iya kareni bane ka fadan in canja lauya a'a ni ai shawara na baka ba komi. To yanxu yaushe zamu fara shiga kotun mansur yace eh yau dai akace za'a kai mata san masu ok ai gwara ayi ayi. Hajiya na zaune Badaru ya shigo hajiya anada baqo to jeka kace ana zuwa ta dubu Abbakar jeka kaji waye ya miqe yai waje. Mutumin yace daga kotu nake ina san ganinmatar gidan towo kotu lafiya dai ko lafiya kalau kirata. Ya dawo yama hajiya bani ta fito yace hajiya kece ummulkairi tace eh nice to gashi ya miqa mata takarda ta mece inkin duba zaki gani. Abbakar ya amsa ya duba sammaci ne ankai ummu qara kan ta riqema Mahfuz yaro ta baima wani ya dafe kai oh my God ya fada hajiya tace mene ya miqa mata takardar ta karba jiki na bari. Ganin meke ciki ne yasa ta saka salati yanxu abinda mahfuz zai mana kenan sika koma ciki hankali tashe ganin ummu ta tawo dan basa son tamasan me ake ciki *Amina-yarzazzau Oumyasmin AeshaKabir Safiyya kabir da Fatima Ahmad wannan page in naku ne kunfi kowa san wannan littafin ina godiya sosai Abbakar ma na godiya, Ummu tace itama a miqo mata saqon tata godiyar gareki, Mahfuz kam cewa yayi agaisheku da kyau dakyau, Nasir kam tsabar Farin cikin yadda kuke san littafin murmushi ya hanashi yin bayanin saqonsa* Ciki sukai kowa da tunanin abinyi Hajiya ce tace Habu miqon wayata yai saurin miqa mata sunan Babbar yaya ta hau kira bugu biyu aka dauka. Tsohuwa barka da rana aka fada daga daya bangaren tai dariya wadda inkana kusa da ita kana kallonta kasan yaqe take dan ranta duk a cakule yake. Dan rikishi miqama uwarka wayar Sudai yasaki qara kai Hajiya zagina fa kikai itama tai dariya ai nima kasan ba tsohuwa bace ko, Sudais kenan jikan Hajiya na biyu, maza ni kai mata inasan magana da ita jitai ance Hajiya na karba ok sai da ta gaida Umman tasu kamin ta ce umma kiyi Hakuri nayi nayi subar daukan wayata in ankirani anman indai sukaga kece sai sun dauka. Hajiya bata bata amsa ba tace in Abbansu ya dawo inasan ganinku baki daya to umma fatan lafiya, lafiya qalau kamar yaushe kenan kike san muzo yau ko gobe da sassafe to insha Allah zamu zo mu duka kike san gani ko mu biyu a'a banda yara tam se munzo sukai sallama. Hankalin Babbar yaya duk ya tashi dan Hajiya bata musu neman gaggawa haka kawai, Hakan yasanya ta kammala komi da wuri mijinta kawai take jira. Koda ya dawo abinci kawai yaci dan ita bama taci ba saida ta tabbatar ya qoshi yana shirin zama kallo kamar ko yaushe tazo ta masa bayanin kiran hajiya yako hau fada kinsan da kiran tun dazu da na dawo baki fadanma yanxuma nasan ta gaji da jiranmu ita dai tai shiru kawai. Maza dauko gyalenki muje ta miqe tana qwalaw Nurat babbar yarsu kira ta fito da gudu mum gani daukon gyalena a daki ta kawo mata tana sanyawa tana mata bayani. Nurat ki kula da qannenki bankuma san duka kinji ko zamu fita bazamu dade ba gidan hajiya zamu in 10 tayi kuje ku kwanta to mum Dady yace zansa tijjani in 11 tayi ya kashe gen to kai sudais kazo muna futa ka rufe qofar shigowa nan shima to yace. Sai kun Dawo Nurat tace gami da komawa kujera tai kwanciyarta tana ci gaba da karatun littafin da take na Aisha Kabir a wattpad mai suna Step mother ( Aziza's Story) danma writer din tana bata haushi bata cika update da wuri ba anman duk sanda tayi sai tasa ta mance da haushin da takeji dan zata kawo chapter mai dadi data fi ta da. Yaya babba ce zaune ita da mijinta gaban hajiya suna kwasar gaisuwa ganinta lafiya qalau gasu maryam duk zaune suna fira yasa yaya Babba samun kwanciyar hankali. Bayan sun gaisa ne Hajiya ta kuma kai dubanta ga ummu tace wannan itace Bilkisu babbar yayar su Habu wannan mijinta ne ummu ta kuma durkusawa ta kwashi gaisuwa duda dazun ta gaidasu, Hajiya ce ta baima su maryam harda ummu umarnin su koma daki zata gana da diyarta. Maryam ce takaima Abbakar qarami sura zata daukeshi yana kan Cinyar hajiya yako sa kuka shi bazai bitaba Hajiya tace qyaleshi maryan ta watsa masa harara gobe kace zaka bini ko kallonka bazanba sukai mata dariya baki daya. Idon hajiya nakansu ummu sai da tada sun haye sama ta dawo da idonta kan su bilkisu nan ta musu bayanin komi gami da basu takardar sanmacin. Mubarak kai nakesan ka zama lauya dinmu inso samune banasan ko kadan yarinyar nan taje kotu tam shikenan hajiya anman inaga kamar zuwanta zai iya zama dole anman dai bari muga kamun ludayin shari'ar. Yaya babba tace anman dai mahfuz bai kyauta ba zan je in sameshi gobe ko zai janye shari'ar Abbakar da tun dazu yake sauraronsu baice komi ba sai yanxu ai yaya dama kin gyaleshi wallahi ta watsa masa harara kai ba abin kunya bane wasu sujiku a kotu dashi to aishina ya rufe idanunsa ya mance da alaqarmu, daquwa ta watsa masa ungo nan inshi san zuciya ya rufe masa ido sai kaima ya rufema. Gobe zanje insha Allah ai kowa nasan sulhu yawwa kije in inji Hajiya dan wallahi inajin tausayin yarinyar tana cikin matsaloli da yawa tayi qanqanta dudu batafi sekara sha tara ba yan biyu inzan iya tunawa sun girme mata. Washe gari da wuri Yaya babba tazo gida anan ta aje motarta tai gidansu mahfuz tai sa'a alokacin zai fita yana ganinta ya washe fuska kai kace ba abinda ya shiga tsakaninsu da qaninta itama ta saki fuska suka gaisa bayan futowarsa daga mota. Tace Allah ya temaken ban daki gurbi ba gurinka nazo towo to mushiga ciki a'a namma ya isa zatonta ko hajiyarsa tasa shi kai qarar dan bataso ta hanashi janyewa basshi namma ta isa taja ta zauna a teburin me gadin su. Yanzu mahfuz abinda kai ka kyauta kenan ya kalleta da mamaki kamar ba abinda yai yace ni kuma me nayi ta kalleshi sosai kamin tace yanzu bakasan me kayi ba eh wallahi yayi kyau tace. To Bari in fada maka daka kai amininka kotu mana ya dafe qirji ni kuma me yamin zan kaishi kotu ta kalleshi da mamakin yadda yake maganar kamar besan yayi ba. Ka mance kace ya riqe maka yaro oh ya fada haka yace miki shi nakai ni wallahi bashi nakai ba ai komai yamun ya wuce in kaishi qara tai dan murmushi ai kamar shi kakai tunda ka kai matarsa yai shiru kamin yace ni wallahi bashi nakaiba ko sunansa babu cikin qarata. Ok naji bashi kakaiba kayi haquri ka janye qarar in yaso inkayi aure sai yaron ya dinga zuwan maka hutu kaga yanxu ko yayeshi batai ba. Ina wallahi baxan janyeba ace nida yarona sai dai yadinga zuwa min hutu to ni so nake in amshi yarona tun kan ayayeshi inasan jinsa kusa dani ajikina akullin inasan ya taso da qaunata. Yaya Babba ta gyada kai ai shikenan se aje kotun inga me baka yaron yanajin nauyinta hakan yasa cikin qunquni yace ai kota yaya ne sai na amshi abina. Bataji mai yace ba tai gaba kawai..... Waye Abbakar Alhaji ukashat Fadal shine sunan mahaifin Abbakar haifaffen garin kano ne unguwar yakasai komi nasa yayi shi ne agarin kano wato girma karatu duk a kano yayi su. Yayi karatun likitancinsa inda ya fara aiki anan Muhammad Abbdullahi wase hospital, Fiddausi daliba ce cikin daliban sch of nursing kano practical ya kaisu asibitin sannu a hankali shaquwa ta shiga tsakaninsu da da Dr Ukashat har ta kai su ga aure. Shekararsu guda da aure ta sami ciki ita din mutunce me laulayin tsiya hakan yasa da kanta ta ajiye aikin da take dan tuni ta kammala school of nursing in. Sai dai tun haihuwar diyarsu ta fari basu qara haihuwa ba san duniya suka dorawa Bilkisu tun basa damuwa har suka fara damuwa. Bilkisu na primary 1 suka kuma haihuwar namji yaci sunansa Abbakar yayarsa ke kiransa da Habu sai dai yaro nada shekara uku bilkisu na primary 4 yaro ya koma tai ta kuka cikin ikon Allah fiddausi ta kuma samun ciki lokacin da ta haihune Aka maida masa da sunan marigayi Abbakar. Abbakar nada shekara biyu fiddausi ta kuma haihuwar mace ta ci sunanta zainab. Abbakar nada shekara hudu zainab biyu bilkisu sha biyu tana Jss one yanzu kam arziqi sosai ya zaunawa Ukashat dan asibitinsa ya bunqasa sosai gami da shahara a ko ina a nigeria dan tuni yai asibitinsa mai zaman kansa inda kwararrun likitoci ke aiki cikinsa, makarantar koyon jinya ma tuni ya kammala gininta kawai jira yake amasa register ta fara aiki. Su Abbakar basa futa sai dai in Bilkisu zata makaranta ta tafi dashi ajinsu daya da Muktar yayan mahfuz shima yakanzo da Mahfuz Nasir na aji daya sai dai su mahfuz basa zama a ajin yara sai gurin yayyensu zamansu aji daya su kadai ne sa'anni yasanya shaquwa ta sosai tsakanin Mahfux da Abbakar. Hartakai in ba islamiyya mahfuz zaita kuka sai ankawoshi gidansu Abvakar danshi Abbakar bayasan zuwa gidansu mahfuz danshi mahfuz irin yarannanne inyaga agidansu ne yaita dukan yaro inko agidansu Abbakar ne sai dai suyi ta wasa. Lokacin da suka isa shiga sch baban mahfuz yakaisu makaranta tare aji daya Mahaifin Abbakar yaso cire Abvakar Fiddausi tace ya kyaleshi kar baban mahfux yaji ba dadi. Abbakar da mahfuz abokaine sosai sai dai hakinsu ya vanbanta dan shi mahfuz ya cika rawar kai duk yan iskan aji da sch insu abokansa ne. Suna jss 3 aka haifi maryam su Abbakar murna kamar me. Tuni makarantar mahaifinsu ta fara aiki kudi sun qara zauna musu sai dai ko kadan Abbakar ba irin yarannan bane masu nuna su wasu ne. Da suka shiga SS ne ya zabi science mahfuz art yakeso sai dak bayasan rabuwa da Abbakar hakan yasa ya haqura da art din ya shiga science. Bilkisu babanta ta gada dan medicine take tana lecel 4 aka mata aure . Zainab na Jss 3 Abbakar Ss3 yayin da maryam primary 1 Hajiya nada wani tsohon cikin Alhaji ukashat yai hadari kan hanyarsa ta dawo wa gida daga kaduna sai gawarsa aka kawo gida kuka gurinsu kamarme. Kwana uku da rasuwar Hajiya Fiddausi ta haifi yaranta guda biyu macen ta fara haifa da kwana biyu wank ciwon ya taso dan agida ta haihu ko asibiti basu je ba ta kuma haihuwat namiji. Abbakar ko kadan bayasan yayi medicine math yake so ko engineering hakan yasa da suka fara medicine aka tafi yajin aiki yasa kawonsa ya masa komi na tafiya japan karatu yai sa'a dagyar Hajiyarsu ta yadda. Lokacin da ya samu mahfux da batu ya yadda shima zashi sai dai daya fadawa wani abokin shaye shayensa yace kar yaje haba Baba kaima kazama mutumin kanka mana ace kullin sai abinda guy dincan yace zakayi yaita zigashi har ya yadda....shi kuwa salim badan komi yake zugar ba dan sanin in Mahfuz ya tafi babu mai siya masa kota yar lasa ce wato kwaya. Samun Abbakar yai ya fafada masa Hajiyarsa taqi yadda Abbakar yace zai sameta yace kar yaje nima inasan koda sau daya ne inma mahaifiyata biyayya Abbakar yaji dadi dan zatonsa shiriya tasamu abokin nasa. Duda Abbakar basa tare da mahfuz anman komi yai sai ya fada masa lokacin Abbakar ya kirashi tayashi murnar kammala masters insa ne Yakr fada masa abinda yai ma ummu batare dajin komi ba zatonsa Abbakar ma bazaiji komi ba kamar su salim da sukai ta sara masa. Saidai Abbakar fada yai ta masa har saida mahfuz yai danasanin fada masa. Yaya Babba da zainab ke kula da Dukiyar mahaifinsu asibiti da makaranta sai dai lokacin da zainab ta samu miji tai aure a katsina abubuwa suka dawo kan yaya babba duka hakan yasa Hajiya tilastawa Muktar auta yin karatun likita tunda shi namiji ne tashi Abbakar yaqi. Koda ya kammala secondary ya tafi india yin medicine ummi tagwai insa take law maryam pharmacy. Ci gaban labari Ranar da aka saka za'a zauna a kotu yazo ta kuwa cika ba lefi duda bakowa yasan da qarar ba. Lauyoyi sun bayyana kansu inda maga takarda ya karanto bayanin qara kamin shari'a ta fara gudana. Bayan bugawa da lauyoyi sukai tsakaninsu aka daga qara zuwa sati biyu ba tare da tabbacin wazai nasara ba cikinsu dan ko wanne kwararrene. Yaya Babba ce tazo gida tana fadawa Hajiya abinda mijinta yace dole sai sun kai ummu kotu da ita da Nasir dan sune shaidun fyade ya mata dagyar hajiya ta aminta. Bikin mahfux kam yai nisa dan gobe ake saka ran daurin aure yayin da shi tuni ya mance dan hankalinsa gabaki daya ya tashi ganin kamar bazasuyi nasara ba. Yau akai za'ai zaman kotu dagyar Nasir ya yadda zaije sai da ummu da hajiya Hajiya da yaya babba sukai ta roqonsa ya yadda yaje. Bayan saurarun shedu da DNA da akai aka tabbatar yaro na Mahfuz ne alqaliya tai gyaran murya kotu tai tsit kowa nasan jin me zata zartar. Tace ina mahfux ya miqe ina yaron da ake qarar kansa shima ummu ta miqe gashi ranki ya dade ina uwattasa tace nice. Miqa masa shi ummu ta kalli alqaliyar alamar in miqa masa kamar yaya tace nace ki miqa masa shi ko ummu ta qara qanqame yaronta police mace ce ta amshi yaron ta miqawa mahfuz dake faman washe baki ummu ta zube gurin tana kuka....... [1/13, 4:21 PM] 🅰️ " AXEEX✌🏻 D'🅱️🅾️Y😎: _POST BY GROUP OF HYPE

Chapter 10 of 15