Bugu hudu ta qari ringing dinta baza'a dauka ba sai ana biyar dinne aka daga cikin tsiwa take fadin wai waye haka ya isheni da kira na tsani irin haka ka kira sau daya sau biyu ba'a daga ba basaika haqura ba.
Eyye sannu maras mutunci to uwar mijinki ce taja tsaki in uwar mijina ce ai ba ita ke aurena ba sannu salma yanxu rashin mutuncin naki har ya kawo kaina aiko ba mahfuz kike aure ba na fice rashin mutunci gurinki balle duk asirin da muka rufa miki, wa kul hajiya kima dena cewa kun rufan asiri ai in bazaki ce na rufa muku asiriba na auren dan iskan yaronku zaifi kyau kice mun rufawa juna asiri tunda kinsan duk iskanci na banyi dan shege ba, ban kuma yi zaman prison ba.
Yanzu salma ni kike fadawa haka ai kedin ce naga kina neman kawo qabli da ba'adi yayi kyau daman ai gado kikai ni ban dana inaso muyi magana tsaki taja mai qara mtttwwwww gami da fadin au baki da number dinsa in da tana kunne aikinsan babu ta yadda za'ai in kiraki ko.
To yanzu yana hutawa ne banasan atakura masa zaki iya kiransa anjima bata jira cewar hajiyar ba ta kashe wayar.
Bin wayar da kallo hajiya tai ranta na quna wato rashin mutuncin salma har kanta.
Wayar Batulu ta kira bugu daya ta daga aminiyar ya akaine cikin fada hajiyar mahfuz ke magana ba wata amininyar yanzu batulu rashin mutunci da asirinki har kan yarona vatulu ta riqe ha6a kai kace tana gabanta tace haba Aminiyar me yafaru haka ai kema kinsan babu ta yadda za'ai inma mahfuz asiri to mene ribata ai dashi da salma ni duk daya ne me ya faru ne kike irin wannan batun.
Nan ta kwashe komi ta fadawa Hajiya batulu itako sai salati da tafa hannu na munafirci take haba Aminiyar sai kace bakisan halin salma ba aikinsan rashin mutuncinta harni ma yiwa take batun kuma mahfuz ai kinsan se ahankali zai huce balle yaga kinqi goya masa baya ya daukaka qara ya amso yaronsa shiru hajiya tai kamin tace kumafa haka ne.
Kiyi hakuri zan kirata zan mata fada bazata sake ba suka taba fira kamin suyi salama.
Hajiya Batulu ce ta hau kiran diyar tata bugu daya ta daga suka ta6a fira duk kan asire asirensu ne kamin hajiya batulu ta dora.
Dazun muka gama da mutuniyarki ta fadan duk yadda kukai sedai inasan ki kirata ki bata haquri ki kuma barmata yaro yana zuwa gunta.
Kai infa basshi kika ce eh kema kinsan ita din ba daga nanba duda ni nasata ahanya anman kinsan sau da dama dan koyo yakan iya fun malaminsa nafiso se itama an kama mana ita ta dena zaton asiri muka nasa in ba haka ba kuwa zata iya ruguza mana komi.
Allah momey ina kishin inganshi da mace to ai ita uwassa ce kuma banda abinki mun riga mun musu farraqu abunda zai dunga mata na rashin mutunci sai tafiso kar yazo Allah umma kishi nake, tsaki hajiya batulu taja tace ke wace irin mutunce kima rasa kishin wa zakiyi sai uwassa to umma ita ba mace bace.
Kinga nace ki kirata ki bata haquri inba so kike in cire hannuna akanki ba to zan kira ta kashe sukai sallama.
Mahfuz na zaune yana musu gugar kaya ta shigo tana fadin honey ka kuwa kira hajiya ya dago yana sakar musu murmushi eh mana jiyafa munyi waya tadan hade rai kasan wace hajiyar nake nufi.
Akwai wata hajiya da na ke kira da ya wuce hajiyarki tadan saki rai kadan a'a hajiyar ka nake nufi ya hade rai in kirata in mata mene.
Haba nawan mahaifiya ce fa kadai daure ko sau daya ne ka dinga kiranta ta miqo masa wayar pls call her ya amsa yana wani shasshan qamshi shi kenan zan kirata dan ke tai murshin jin dadi.
Bugu daya ta daga haba mahfuz yanzu ka kyauta gabaki daya ka gujemu kofa bikin Nasir bakazo ba bakuma ka turo matarka ba sai anan ya samu damar magana, a'a hajiya ni ne ya dace nazo ban kuma ga damar zuwa ba matata adena samin ita cikin matsal tsalun gida ni kika haifa ba ita ba ya kashe wayar.
Rashin mutuncin Mahfuz kullun yawa yake yayin da matarsa kullin cikin sake shiri take ganin dagaske za'a kwace mata yaronta yasanta hajiyar mahfuz ko ta kan mahaifiyar salma abokiyar zuwa gurin bokayenta ba tai zamfara gurin hatsabibin bokanta.
Qarya da gaskiya bokan ya fadawa wa hajiya tahau tazauna daram komi ya hada mata kai tsaye gida ta koma.
Washe gari gidan mahfuz tai dan ai watar sa aikinta baya nan ta shiga ciki daman haka taso dan tasan ahalin yanzu yafi ma matar tasa rashin mutunci.
Sai dai me shiru falon kamar ba kowa cikin kujera ta tusa daya cikin asirin nata bata taba zuwa gidanba tun kawo salma sai dai tasan gidan sosai hakan yasa ta miqe tai dakin da ke kallonta kai kanta ke da wuya ta dawo da baya abin ya mugun daga mata hankali bata gazgata abinda ta gani hakan yasata qara komawa sai dai me abinda ta gani gaske ne.
Bawai gizo bane Salma ta gani da wani qato ba mijinta ba wato mahfuz suna sa6ama Allah hankalinta yai matuqar tashi sosai.
Dakin ta fada hankali tashe ganinta yasa mutumin yin waje dasauri salma ta bishi ta ruqoshi haba Darling mene haka atsorace yake ka kintsa se ka fita ba abinda zata iya mana.
Mamaki ya cika hajiya ai ku shi dai tuni ya fice hajiya ta kwadawa salma mari gami da jawota waje ashe iskancinki ba iya fatar baki bane haba salma da aurenki aka.
Anan falo hajiya keta surfa bala'inta tama mance da me yakawota gidan dan nata.
Ai kuwa Mahfuz na dawowa Salma ta miqe cikin kuka ta fada jikinsa tana fadin hajiya tazo ta mata duka abinka da aikin asiri tuni ya hau ya zauna hajiya me ya kawoki gidana nan hajiya ta hau masa bayani komi har halin da ta tsinci salma budar bakinsa sai cewa yai yanxu hajiya dan kawai kinajin haushi na shine sai kinma mata ta sharri.
Hajiya ta hau rantse rantse dan ya yadda da gaske take yace pls hajiya kije gida ganinki na qaran takaici wallahi dan kece kawai anman babu wanda zai daki salma in raga masa kema inkika ci gaba da zama zan iya sauya ra'ayi.
Ba shiri hajiya tabar gidan ranta bace har wani jiri take ji.
Gidansu Abbakar
Ummu tace gidanmu kuma bayan wannan da muke ciki yai dan murmushi kamin yace ai kinsan ba wannan gidan nake nufi ba namu mu uku nida ke da takwara na ko shima yasamu qanne ta sunkuyar da kai ganin ya bata kunya yasa shi sauya maganar da fadin.
Wai me yasa bakya hawa facebook account dinki tace haka kawai kuma inna kira number din dana sanki da ita bata shiga tace ai ta bata tun kan na tafi Niger, to da wacce kike anfani babu tace.
Miqo masa ta hannunsa yai ungo kafin in siyo maki wata ta kalleshi yamata kwarjinin da bazata iya cewa a'a ba ta amsa.
Tace ka buden se kin amsan tambayata wacce tambaya ta tambaya yaushe zamu tare anamu gidan tai dan murmushi kamin tace sai randa hajiya ta yadda.
Ya kuma mai maitawa haka kika ce ko tai shiru yadan dubeta kadan kamin yace waini yaushe qanwata ta facebook me magana, fira da barkwanci ta koma miskila ne tai dariya ai daman ko waya muke ni kasan ba magana na cika ba basshi achat din yai dariya wato haka ne ta gyada kai nasan me zanyi ya dauki Takwaransa dake kan cinyarta ya bude qofar sukai cikin gida.
[1/13, 4:24 PM] 🅰️ " AXEEX✌🏻 D'🅱️🅾️Y😎: _POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚
[1/13, 4:25 PM] 🅰️ " AXEEX✌🏻 D'🅱️🅾️Y😎: *ABBAKAR*
*PAGE 180---190*
*Pls kusani a addu'a wallahi bani da lafiya sosai ni kadai nasan me nakeji dakyar ma nayi muku wannan zaku iya jina shiru kwana biyu*
Abun duniya duk ya ishi Abbakar gashi dai yanajin haushin mahfuz sakamakon abinda yai tayi bacin mugun kishinsa da yake ji sai dai kunsan in akace abotar gaskiya wacce take ta tsakani da Allah ko me mutun ya maka wannan san sabida Allah kullin yana nanne.
Gabaki daya ya damu musanman ganin anyi bikin Yah nasir ba Amininsa ya kuma tambaya yah Nasir yace masa wayasan masa tun lokacin yakesan zuwa gidansu sai dai yana tsoron jarrabar Hajiyarsa dan inta mahfuz ne daman sun saba suyi su shirya.
Yanke shawarar zama abakin lokonsu yai ko zaiga aqallah wucewar Aminin nasa dan tabbacin lafiya yake sedai yau kwana hudu babushi bare labarinsa.
Zaune yake gaban hajiyar Mahfuz duk ta rame tai baqi yadda ta amshe shi ya bashi mamaki dan yayi zaton da fada ne sai wani nan nan take dashi.
Sun gaisa yake tambayarta mutumin me makon ta bashi amsa kawai sai ta fashe da kuka yai yai tai shiru taqi sai da tai me isarta cikin shessheqa take fadin Habu haqqine ke cina nakuma san bana kowa bane saina ummulkhairi da iyayenta.
Shi dai da ya samu tai shiru ya danji dadi kadan duda zuciyarsa cike take fal da tunanin me yasamu Aminin nasa "nace uhum Abbakar kenan Allah ya baka zuciya me kyau"
Hajiyar mahfuz bata boye komi game da halin da mahfuz ke ciki ba harda wanda data je gidan ta tadda matarsa, sai dai bata fada masa zuwa gurin bokan da taiba da dalilin zuwa Hankalin Abbakar ya tashi yasan mahfuz yana shaye shaye dan baya boye masa komi anman baya bin mata shi yasa lokacin ya fada masa game da ummu yaita masa fada yanzu tsoronsa daya kar matarsa ta saka masa cutar wannan zamanin.
Nan yaita lallashin hajiyar yana bata haquri yasamu ta dan dawo nutsuwarta kamin ya dora yanzu addu'o'i yakamata ayi tayi masa zansa a masallatai da makarantu ki yawaita masa sadaka da niyar Allah ya karya koma mene taji dadi sosai dan ita tama mance da batun addu'a din.
Kai tsaye gidan Nasir Abbakar ya nufa ya sanar dashi duk yadda sukai da hajiya shima hankalinsa ya tashi ya yadda da shawarar Abbakar tun daga lokacin su ka duqufa sosai ko sallah ce ta kai Abbakar masallaci sai ya roqi asa abokinsa a addu'a.
Sannu a hankali farraqun da aka masa da hajiyarsa yaji ya tsani zuwa gurinta ya kau dan yanzu yana zuwa sosai fiye da da, duda har yanzu cike yake da tsoron matarsa gidan nasu ma aboye yake zuwa.
Da zuwan da yake ne Babban wansu muktar yai anfani tofin da yake masa azam zam ya hada da dabinon ajuwa indai yazo se yasha in yaqi dole suke masa.
Awayo a wayo yayan nasa yake nusar dashi sallah dare in addu'o'i kamin kwanciya bacci da neman tsari dan shi din ba daga nan bane yasan illimin addini sosai kawai dai irin ansani ne bashi da anfani tunda ba'a aiki dashi.
Sannu ahankula tsoron matarsa ya fara barinsa har mamaki yake in yaga tazo ta tsaya masa aka tana bashi umarni kawai kallonta yake sedai ya kasa daukan mataki.
Hankalin Salma da hajiyarta yai mugun tashi ba kadan ba ganin har Niger sun kai sunan mahfuz gurin hatsabibin bokansu wanda duk wanda suka kai ya gama yawo anman kulin abubuwa qara tabarbarewa suke.
Yau sunyi da matarsa zaiyi tafiya zuwa university of ibadan dan yin wani abu murna take sosai dan ta gaji dashi sosai gashi tsoro ya hanata kawo kowa dan daya fita yake dawowa.
Wanda zasuyi tafiyar tare ke fada masa su bari se gobe hakan yasa ya wuce gidansu suka taisa da hajiya sukai yar fira kafin suyi sallama ya wuce gidansa.
Da ace nasan mahfuz yasan me zai tadda da tabbas da bazaiyi sha'awar zuwa gida ba hankalinsa yai matuqar tashi idanunsa duk ya rife bema san me ya rarumo ba yai kansu.
Duka kawai yake babu qaqqautawa ganin zai ita kashesu yasa kwarton yin ta maza yai waje a miliyan ya koma kan salma dake gefe a rakube tama kasa motsawa duka kawai yake tai mata lilis dagyar ta rarumi zanin gado ta arta aguce.
Biyota yai yana ci gaba da duka yana fadi Allah ya isa tsakani na dake na sake ki saki uku har farfajiyar gidan dagyar me gadi da driver suka riqeshi ita dai data samu tai waje adai daita ta hau se gidan ubanta.
Agurin Mahfuz ya zibe yana kwasar kuka shi kadai yasan abinda yakeji yanzu ransa bai taba yadda cewar inkayi zina da wata mace se anyi da wacce take mallakinka ba sai tau matarsa ta sunna kuka kam yayi shi bakadanba tausayin yaransa mata ya kamashi innalillahi wa'innailaihi raji'un yake fade kawai Allah ka temake ni katsayarmin iya nan wallahi nayi nadama ya Allah karka dorawa yarana abinda ni nayi sanbatu kawai yake.
Gidan ji yake gabaki daya ya zame masa kurku ku ba abinda yake gani sai matarsa da wani gidanma gabaki daya ya bari yai gidansu.
Cikin kuka yake fadawa hajiyarsu komi baima qarasa ba suka jiyo masifa a waje da sauri hajiya ta miqe tai waje Hajiya Batulu ke ta sirfa masifa salma na bayanta.
Fadi take ina Karimar take wallahi dukan da dan iskan yaronki yama yarinyata akanki zan rama mata ganin hajiyar yasa tai kanta gadan gadan aikan daga hannu tai zata zuba mata wayar dake hannunta aiko muktasir yako riqeta kul bazai yiwu kizo mana gida dan rashin mutunci kice zaki dakar mana uwa ba kinyi kadan.
Kamin ya qarasa tasakarma Hajiyar tasu nari itama taji kuwa an dauketa dashi wa zata gani mahfux ne namfa yaran suka mata lilis ita da salma sai da hajiya taga zasuyi kisa tasa baki suka kyalesu.
Hajiya batulu fadi take wallahi, Wallahi sai kinyi danasanin ni kika ma haka kinsan da cewar gabaki daya a tafin hannuna kike shirya karbar sakamakonki, hankalin hajiyar mahfuz ya tashi dan tasan me take nufi su kuwa yaran ina suka sani fadi suke abar mana gida yayanmu ya rabu da bunsurar yarinyarki ya wuta da kuda.
Kai tsaye maqabartar dan dole ta nufa daga gidansu mahfuz din yaron da ta baima aikin binne binne tace duk ya je ya haqo mata ya kawo mata yace an gama.
Inda ta sa aka kai na tsohuwar rijiya ma duk aka ciro ta tara shirgin asiri tim gabanta ta zuba musu kalanzir gami da kunna ashana tuni suka hau ci da wuta.
Tasaki wata dariya Wallahi hajiya karima dani kike zancen kin riga kinyi sake da kika bari ni nasan sirrin komi naki waike uwar san jiki sedai ki bada kudi ni inje miki gun boka inkuka miki aikin yadda nasa aka binne na haqesu yadda naje nayi miki kike rayuwar fantamawa kike mulkar kowa gidanki to kuwa kinyi kadan.
Tun safe hankalin Hajiyarsu mahfuz yai mugun tashi ganin Baba tijjani da baba usman matsayinsu na qannen mijinta me rasuwa da sukazo gaidata suke tambayarta ina Ummulkairi ne basu ga tazo gaidasu ba wato tunaninsu game da yar qanin nasu ya dawo yanzu in mahmudu ya dawo me zata ce masa wato wanda yake me matsayin babba gidan yanzu.
Tasan ko mijinta be kaishi san diyar qanin nasa ba.
Ilai kuwa yana dawowa yaran kowa yaje ya masa barka da dawowa yana ta zuba idon ganin diyar tasu sedai shiru bayan yai wanka yaci abinci ya debo tsarabarta yayo bangarensu wato bangarensu Hajiya karima tunda anan yasan take tun rasuwar mahaifiyarsu.
Dakinta ya shiga sai dai yadda yaga dakin ya tabbatar babu mutun aciki duk yayi qura yai cudun cudin.
Tun yayansa nada rai basu cika shiri da karima ba hakan yasa take shaskarsa afusace ya futo yake kwala mata kira ta fito da sauri ina kuka maida yarinyar nan cikin rawar murya take tambaya wace yarinya fa.
Cikin fada yake magana zan tambayi wata yarinya bayan ummulkairi ta gurin Yasir hankalunta yai mugun tashi tama rasa amsar bashi dan gabaki daya ta gama rudewa.
Nasir ne ya shigo jin rikicin da ake hankalinsa ya tashi daqyar ya samu kawun nasa yai shiru ya zauna ya masa bayanin komi game da ummu har aurenta yanzu sedai bai fada masa wata aura dinba.
Hankalinsa yai qololuwar tashi yanzu duk yaushe hakan ta faru bamu sani ba yama akai haka cikin kuka hajiya ke fadin abin duk tayi ya miqe yana salati wallahi karima kinban mamaki ashe zaki iya haka nasan duk bazai wuce kan wannan gidan ba da yake mallakinta to gabaki daya kinja muku kowa gobe zai bar gidan daman ai ba namu bane muna zaune dan iyayenmu ne yanxu tunda suma basa raye se abarma me gida gidanta.
Gidansu Abbakar
Sabo sosai da shaquwa me qarfi ta shiga tsakanin Abbakar da ummu kullin suna farfajiya tare duda yawanci da maryam ko ummi ake karatun anman kallonsu kawai kai kasan da masoya ne masu san junansu iya so.
Duk yadda Abbakar yai yayi da hajita tace ina itafa babu zancen tarewa yanxu dole se ummu ta gama katatu ganin da gaske take yasa zuwa ya sami kawunta ya rattaba masa komi.
Aikam yasha fada kanyin aure bada saninsu ba yaita bashi haquri yace zaije ya sameta yaje ya fadowa nasa kawunnan yace to.
Gidan qaramin kawunsa yaje ya fada masa dan yasan inyaje gidan wan babansa dukansa ne kawai bazai ba dan mutumin kwai fada.
Shima kawu Barau din da bai cika fada ba yau ya ta6a dakyar Abbakar yai ta bashi haquri har ya yadda zaije ya fadawa wan nasu.
Aiko dakyar yasha kan yayyen nasu suka yadda zasu saka baki akan auren dan nasu.
Hajiya ta yadda ummu zata tare da sharadin dole aje dangin ummu su san da batun auren ba musu suka amince.
Gidansu Mahfuz
Washe gari da sassafe Baba mahmud ya tara qannensa ya fada musu komi harda hukuncin da ya yanke sun yadda kan jibi iyanzu sun bar gidan agurin ma wasu cikinsu suka fara kiran motar da zata kwasar musu kaya.
Ba wanda bai jin jina halin da ummu ta shiga ba da tausayinta agurin suka yanke shawarar sanya cigiyarta dan nasir bai fadi inda take ba zatonsu ta bace yanxu, hankalinsu bai qara tashi ba sai jin abinda mahfuz yai wasunsu ma ji suke kamar su dakeshi tada kam yashashi harda masu cewa basu bashi tunda ya rasa wanda zai ci mutunci sai yar uwarsa.
Abbakar ne yazo gidan kan kawunnansa nason zuwa ganin su baba mahmud yai mamakin ganinsu gabaki daya mahfuz nafaman kuka.
Ada baba mahmud yace sedai in wani satin anman jin yace kan ummulkhairi ne yace su zo yau da yanma kawai.
Tarba sosai suka samu duda gidan a hargitse yake kowa na qoqarin hade kayansa ne sosai hankalin su Baba mahmud ya tashi kanjin har wani aure akama ummu bama da saninsu ba.
Budar bakin Baba mahmud se cewa yai ai ina maganar tarewa bai taso ba yadda akayi mata dole barin gidan nan ina da tabbacin dole aka mata aka mata aure dan haka kawai kuce ya bata takardar ta yarinyar mu nada gata in ta sami wanda take so to lokacin zamu aurar da ita.
Komi suka ma Abbakar bayani game da yadda sukai da iyayen ummulkairi aikam hankalinsa ya tashi sosai da kansa yaje yasamu baba Mahmud aikan rufe ido yai kamar be sanshi yahau yazauna sakin ummu dole gida Abbakar ya dawo ya sanar da hajiyarsa.
Itama hankalinta ya tashi taje har gida ta sami baba mahmud sun gaisa cikin mutunci ta masa bayanin komi yai murmushi fiddausi kenan nasan kun mana da kuka riqe mana yarinyar nan anman hakan baya nufin zamu biya ku tukwici da yima yarinya auren dole dan kawai danku nasanta.
Duk yadda hajiya taso ya fahinta ya kasa fahinta haka ta tawo gida rai babu dadi.
Ganin yayi duk yadda zaiyi ne kan sakin ummu Abbakar yaqi yasa yanke shawarar zuwa har gidansu Abbakar din ya dauko ummu ya kuma sanar musu tabbas qara zai shigar indai nanda kwana uku bai kawo sakinba.
A gidansu Abbakar tabar yaron nata Abbakar gurin hajiya dan ta yaye mata shi.
Ummu tai mamakin ganin gidan da ya kaita can unguwar karkasara me makom nan naqotansu Abbakar bata tambayi dalili ba dan ranta duk babu dadi bataso barin gidansu Abbakar ba tayi sabo sosai dasu bana wasa ba tanajinsu aranta anman batasan nunawa kawun nata iyakarsa.
Komi sabo aka saka mata adakinta ita da Abbakar dinta ahankula tadan fara sabawa da zaman gidan babu inda take zuwa dan anyi hutun sch balle tasa masoyinta a idanunta ko bacci basosai take ba cikin tunaninsa take.
Bata taba zaton tanasansa haka ba sai yanzu dan ada tana qoqarin yakice shi zatonta bazai taba santa ba anman yanzu da ta riga ta saba dashi ta saba fira dashi ya koya mata sansa ji take raba ta dashi kamar ta'addanci ne babba sedai ita batasan me zatai ba.
Satinta biyu gidan baba mahmud yaje ya amso Abbakar qarami dan ganin ummu taqi sakewa zatonsa ko rashin yaronta ne tunda Nasir yasanar masa tanasan dan dayawa.
Kwana biyu yaron ya saba da kowa dan baida rikici musanman gidan da yake da yara sunzo hutu jikokin gidan sai warkajaminsa yake abinsa.
Tunda ummu tazo gidan bata ta6a farin ciki irin na yauba taji dadi sosai Baba mahmud ne yazo yafada mata ta shirya zasu Jordan can gurin ummanta tai murna ba kadan ba.
Nan ta shiga hada musu komi dan gobe ne tafiyar ita da Abbakar dan su uku zasu tafi daga ita sai danta sai baba mahmud.
Yanzu abu daya ke damun ummu rashin masoyinta Habunta anman indai fannin iyayene duk cikin yayun babanta kowa nan nan yake da ita danma taqi sakewa dasu kamar da.
Sun shiga mota ta tuno ta dauki wayarta ta turawa Abbakar saqo pls izini zamu jordan a samu a addu'a afadawa hajiya.
Baba mahmud na kallonta tai kamar be ganta ba yace kawo yaron jeki kice ma kadija ta baki saqona tace tota miqa masa yaron tai ciki ya dauki wayar yana duba saqon.
Har ya turo amsa Allah yasaukeku lpy abar sona dan Allah kiyi wani abu kar a rabamu pls ajiye wayar kawai yai ganin ta tawo.
A Jordan
Bayan sun sauka mota ta daukesu sai gidansu ummanta kowa yaji dadin ganinsu musanman kakanninta sai washe gari aka dibesu zuwa gidan umman nata.
Tunda ta shiga falon ummun nata kishi ya rufeta ummanta ce jikin bango a hoto sai yara suma larabawa uku manne jikinta mijinta gefe tai saurin dauke idanunta daga hoton duk inda ta duba sune.
Yan matan biyu masu kama da ita suka fito dan ganin su
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 12 Chapter of 15