waye ganinsu yasa komawa ciki da gudu dan kiran momy dinsu suka fito tare har namijin wanda da gani shine qarami befi 9years ba kishi ya rufe idon ummu hawaye ya fara kai kawo aidonta.
Wato ummanta ta ma mance da tana da yarinya a Nigeria tayi aure ta samu wasu ita ta badda marainiya ba uwa ba uba tunda ta yayeta ta tafi bata kuma nemanta ba.
Danta ta sura taja baba mahmud mu tafi nafasa banasan ganinta muje Kawai take fada tana kuka ganin bazai tafi bane yasa sakinsa tai gaba.
Dasauri umman nata tai gunta dan tana dan fahintar hausa ba sosai ba ta ruqota gami da dorata a kafadarta tana lallashi dakyar tai shiru.
Haba ummu kin taba ganin inda uwa ta mance da danta kina raina babu yadda zanyi ne.
Yaran sukaita kawo mata abu buwa wasu duk hotunan tane jiki tana qarama sunata murnan ganinta seda ta kula sosai taga ashe hoton farko ma kana shigowa shi zaka gani kamin nasu dukansu itace rungume jikin umman nata da alamu ma ranar da zasu rabu ne tadan share hawayenta kamin tace cikin harshen turanci dan larabcinta be kwari sosaiba.
Anman mum me yasa haki kuma wai wayata ba.
Ummu babu ce tasa tun bayan dawowata daga qasarku babana yai rashin lafiya sosai duk abinda muke dashi dana gadona duk ya qare gurin jinya har bashi muka dinga amsa qarshe ya rasu.
Shekara daya da rasuwarsa na auri babansu Nasrin shi ba wani me arziqi bane da zai iya daukan nauyi na inzo nageria albashi nama haka muke hadawa gurin kula da yaranmu da iyayenmu dan da nasa iyayen da nawa duk suna buqatar temakonmu.
Ummu ta kuma rungume ummanta tana qara bata haqurin fahintarta bai bai.
Koda Dahir ya dawo bakowa falon sai ummu yana ganinta ya ganeta dan yasan basu da dan uwa baqar fata sai diyar matarsa bayan mugun kama da sukai da matar tasa.
Da sauri ya qaraso ya rungumeta yana fadin ummulkhairi ya kuma dubon fuskarta dadi ya cika ummu tabbas ummanta bata mance da ita ba tunda har mijinta da akasan larabawa da kishi yasan da ita.
Watanta guda cif taji dadin zama dasu sosai soyayyar uwa kam se yanzu tasan me ake nufi da ita dabadan tanasan mijinta ba babu yadda za'ai ta yadda tabi baba mahmud Nigeria.
Sunyi shawara dashi kan tanasan kudinta na account dinta ya cire mata zata baima ummanta dan ta fusksnci suna wani hali tunda ita ba abinda take dasu ya amince.
Aikam tasha albarka dakyarma umman nata ta yadda suka amshi kudin haka ummu ta tawo suna kewar juna.
Nigeria
Ummu ce biye da Abbakar yana ihu shi baza'a masa wanka ba ya 6oye jikin baba mahmud yai saurin dagoshi mutumin lafiya dai kake yawo ba wando se nasa anma kaciya ko baisan kaciya ba yasa dariya baban ya nuna masa gurin nan zansa a yanke ya tsanyara kuka ummu taja ta tsaya turus ganin abinda ke faruwa.
Hajiyar mahfuz ce tsaye tana kuka tana roqon baba mahmud ya batta taga ummu zata nemi afuwa, ganin ummu tayo gurin zata zube qas ummu ta dagota tana girgiza kai alamun a'a.
Umma ni na yafe miki karki durkusa min ha juma da mancewa da komi hajiya taita godiya harda daukan Abvakar taita masa wasa.
Tun daga lokacin ba'a sati sai hajiya tazo gidan se alokacin ummu tajiashe kowa yabar gidan taje taita roqon baba mahmud dakyar ya amince kowa ya koma gidan tace ita indai gida nata ne to kowa ta bar masa bangaren da yake bangaren Abbanta kawai takeso da kakarta.
Farin ciki ya dawo gidan kowa nasan ummu Abbakar qarami haka kowa nasansa ko yaushe yana gun hajiyar mahfuz.
Mutun daya ne ko kallonsa ummu batayi shine mahfuz dan sosai ta tsaneshi danma yanzu yana yawan shiga sabgar danta komi ya samu sai ya kawo masa yaron shima bini bini uncle mahfuz a bakinsa abinda kedan rage mata haushinsa kenan.
Ummu zaune gaban baba mahmud daman zancen rabuwar aurenki ne nayi shiru da batun zuwa ki dawo daga jordan wani satin zamu fara zaman kotun.
Tama rasa me zata ce hankalinta ya mugun tashi ko bakiji bane to kawu Allah ya kaimu ta miqe tana tangadi dan jin jiri na qoqarin kwasarta tana shiga daki ta fashe da kuka.
Yau aka dawo da Abbakar daga gidansu Abbakar babba daqyar ya dawo danshi in ya je guri dagyar yake yadda ya dawo sabida sabo seda Abbakar babba yai masa dabara ya tafi yanata kuka.
Baba mahmud ya bita da kallo kamin ya miqe yai cikin gida dan dauko Abbakar za'a masa kaciya dan sanyi yazo.
Kai tsaye gurin ummu yai da yaron ya tsaya abakin qofa jeka ka kiramin ummanka ya shiga da gudu yana fadin mome tizo mamu afi anguwa tai saurin goge hawayenta ta dubi yaron.
Ya mata kyau sosai jitai kamar tace abar kaciyar se ya kuma girma tadai daure muje to yasa kuka auke shi wai ta daukeshi tai dariya dan rikici gami da daukansa.
Har mota ta kaishi gami da shafo kansa suka fice yana daga mata hannu.
Yara da yawa an musu kaciyar a idansa yaga suna fitowa yadda yake ganinsu yasa shi fara kuka.
Hankalin masu kaciyar yai mugun tashi ganin yadda yake bleeding abin ya wuce hankali dole suka futar dashi daga dakin zuwa dakin temakon gaggawa.
Likitoci sun duqufa kansa tuni suka gano ai haemophiliac ne jini duk yadda sukai ya tsaya yaqi gashi babu allurar da ake musu masu cutar a asibitin se ma anje zariya babu tabbacin ma kan aje yana raye.
Jini na zuba ana qara masa wani yaron yayi mugun jiqata rai ahannun Allah hankalin baba mahmud ya tashi tuni ya buga waya zuwa gida.
Ko ummu va'a fadawa ba suka bayyana a asibiti harda su Abbakar kowa ya tausaya ma yaron kowa ya damu dan yaron ya shiga ran kowa.
Minti talatin tsakani Abbakar ya rasu dedai da baba mahmud duk dakiyarsa seda ya zubda hawaye dan mutuwar ta dakeshi kai kace wani babba ya rasu.
Su kansu ma'aikatan sunji mutuwar dan dan awannin da yaron yai gurin kamin fara kaciyar yadda yake da faran faran da surutu har sun saba.
Komi Baba sani ne yayi aka basu gawar sukayo gida dan baba mahmud ya kasa komi gani yake kamar qarya ne yaron be mutu ba yanzu yanzufa suke wasa da dariya dashi ina shibqarya ne be mutu ba......
*Alhamdulilah jiki yau sauqi nagode sosai da addu'oinku gami da fatan alkairi*
Kai tsaye gida akayi da gawar ba wanda bai share hawaye ba cikinsu musanman ma wadanda suka ga yaron ayau da jiya se abin yake ta dawo musu sabo.
Ba abinda mahfuz yake se sharar hawaye haushi da tsanar kansa duk sunbi sun masa yawa shi ne sana diyar zuwan yaron duniya yaso ace yaron ya girma ya masa gata sedai gashi yama tafi besan waye mahaifinsa ba, ya kuma share hawaye lokacin da ya tuna ganinsa da yaron na qarshe.
A wasa yake masa magana my boy yau agurina zaka kwana ko ya maqe qeya a'a ni yau gurin dady na zani to ai nine dady naka yasa dariya kai uncle dina ne dady na biyu dadyn aunty farida(Nasir) da dady me sunana, bemasan sun iso gidanba seda Abbakar ya ta6ashi yai saurin futowa daga motar.
Gawar ce riqe hannun Abbakar ji yake kamar yaron zai farka yasa masa kuka kamar ko yaushe yace se ya bashi alawa kwallah ta tawo masa wadda ya kasa tareta, mahfuz yai saurin Amsar gawar shi kuma ya goge hawayensa.
Nasir kam ya kasa komi qafafunsa ma gabaki daya sunyi sanyi inbanda soyayyar uwa daban take to da nace ba wanda yafi nasir san yaron koda yake ko ummun batakaishi shaquwa da Abbakar dinba, shi har yanzu baima yadda wai yaron ya mutu ba jira yake kawai yaji sunce masa ya farfado.
Se kace ba dazu da safe ne da yazo gidanba yaga yaron yanata wasansa har dazai tafi yake masa wasa dady yau zamu unguwa da baba yace zai sayon kayan dadi cikin tsamin murya ta yara yake magana wadda seka zauna dashi zaka fuskanceshi.
To nima aragen kayan dadi yai dan jim sedai inzaka siyon wasu se insamma ka yai dariya ya lakuce hancin yaron kaji me wayo to naqi wayon naka shima yaron yasa dariya gani yake kamar alokacin abin ke faruwa bema san sanda shi kansa ya saki murmushi ba.
A bangaren Baba mahmud aka ajiye gawar dan anan za'a masa komi ba tare da wani 6ata lokaci ba aka dora ruwa baba mahmud ya kawo likkafani dan akwai da yawa adakinsa.
Ita kuwa ummu baiwar Allah tun lokacin da tasaka Abbakar amota takejin wani iri har dago mata hannun na baibai da yake mata ta kasa mantawa ji take kamar taje daukoshi in ya qara girma ayi kaciyar har motar ta fice bata denajin ba dadi ba duda yaron yasaba mata haka anman yau se takejin daban kodan za'a mai kaciya ne ta fada aranta gami da komawa bangarenta.
Tun dawowarta gidan bata shiga ko ina sai taje ta gaishesu shi kenan se karatunta kawai tasa agaba se kuma in yaronta yanan ta kunna musu kallo ko yaita mata hirarsa ta yara.
Tunani kala kala ya dabaibaye mata zuciya hakan yasa ta miqe ta shige daki danyin walaha kamar yadda ta saba.
Bayan ta idar ne ta dan kwanta danta huta batamasan sanda bacci yai gaba da ita ba.
Se wajen sha biyu ta farka adan firgigit ta farka tai saurin yin falo dan tasan yanzu Abbakar andawo dashi tasan yanacan yanata zuba shagwabar tasa daman qaqa balle an masa kaciya ita kam yau gurin Hajiya zai kwan dan bazai hanata bacci ba abinda take ta ayyanawa arai kenan.
Ganin falonta wayam yasata yin murmushi tasan yana gun hajiya kodai ta mahfuz ko kuma ta bilkisu wato matar baba mahmud.
Gyalenta ta dauka tai waje kai tsaye bangaren su mahfuz tai duda batasan zuwa sosai sedai takan danne dansu yadda dagaske ta haqura komi ya wuce din
Ba kowa anan ta danji wani abu aranta anman da ta tuna yadda kowa keji da Abbakar tasan kowa yana gurinsa hakan yasa ta juya zuwa 6angarenta.
Alawar da yafi so da madarar da ta hada masa tun safe kan inya dawo ta bashi ta dauka, dan tasan indai taje yaganta ko kasuwa ce gabansa se yasa kuka seta lallashe shi ta bashi alawar zai shiru.
Tunda taci karo da ummi qanwar Abbakar jikinta ta bata wani abu ta share tunaninta ko ran ummin ne a6ace kawai.
Tana shiga an kammala hadashi yaro yai tsawo kamar badan shekara uku zuwa hudu ba yai kyau fuskar nan ta kara haske kwance yake san6al kan tabarma kamar kai masa magana ya amsa.
Da sallamarta gami da fara'a ta shiga falon sedai yadda taga mutan ciki yasata tsayawa soro tai turus tana binsu da kallo.
Kowa ita ya zubama ido bawanda yai zaton ganinta ayanzu ta tsaya kawai tana binsu da kallo ta kasa gaba ta kasa baya ciki zatai ko waje.
Me makon taga yaronta yana mata kuka yana auke shi saidai ta ganshi kwance cikin siffar wanda ya mutu ina ita yaronta be mutu ba da sake abinda take fade cikin ranta kenan kama ce kawai Abbakar dina da ransa wallahi.
Jitai ana jan hannunta tai saurin kallon ko waye Nasir ne ta gani har gaban gawar ya kaita ya durkusar ta gami da saurin barin gurin dan baisan mai zaice mata ba.
Waye wannan take fade cikin daga murya kai kace bata sanshi ba ku fadin kuma karku cemin wannan yarona ne danni yarona da ransa.
Abbakar yazo ya riqeta ki nutsu ummu kar soyyar yaronnan tasa ki kasa fahintar gaskiya gabaki daya ta kasa kukan ma ta miqe gami da yin waje baba mahmud yace da hajiya subi bayanta.
Kai tsaye 6angarenta tayi ta dauko zaninta na atamfa guda biyu ta dawo inda gawar take abu kawai take kamar tababbiya.
Lulluba masa tayi ajikinsa gami da kinkimarsa daqyar tasashi cikin makarar yaran da aka kawo dan kaishi, ta kamo hannun baba mahmud babu ku yi saurin kaishi inda take mazauninmu na gaskiya gaggauta kaishi shine mun masa gata ta koma kansa gami da kuma bude fuskarsa ta shafata se alokacin kwalla ta kawo mata.
Tai saurin shanyeta gami da fadin Allah ya jiqanka yarona Allah yasa kaidin me cetonmu ne se munzo muma munan tafe ta miqe har taikai bakin qofa ta dawo ta dauke alawar da madarar da ta kawo masa da kayansa da aka cire masa tai waje.
Kowa ya cika da tausayinta kwallar su duk ta qaru.
Tsam ta rungume kayan inta tuna basu tai niyar saka masa ba yasa kuka sesu dan tare dashi ake za6o masa kayan sawa.
Tana shiga daki ta rufo qofa gami da tsayawa jikin taga tana kallo aka fito dashi akai waje dashi ba abinda ke bakinta se Allah ya jiqanka yaro na yayinda idaninta keta hango mata shi dazunnan da yake mata bai- bai zasu fita a mota yanzu gashi za'a fitar dashi a motarsa ta qarshe babu damar ya mata bai baidin.......
[1/13, 4:25 PM] 🅰️ " AXEEX✌🏻 D'🅱️🅾️Y😎: _POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚
[1/13, 4:27 PM] 🅰️ " AXEEX✌🏻 D'🅱️🅾️Y😎: l*ABBAKAR*
*190---200*
Tananan tsaye bakin qofa cike da tunani fal ciki bama tajin bugun da tun d'azu ummi mariqiyar Abbakar keyi.
Ita kuma ganin tayi bugun shiru yasa ta juyawa dan yin bangaren su Bilkisu kamar ance ta kalli jikin taga takai kallonta nan, antin tata tagani tsaye tai saurin komawa ta tabota tai firgigit takai duba inda taji an ta6atan.
Ummi ta gani tsaye riqe da sweet campo tana mata murmushi tai saurin zuwa ta bud'e mata qofar yarinyar tai ciki tana kwalawa Abbakar kira tana waqa ina kake ne dan kaciya da warin tusa nazo da alawata bani baka se kayi tusa me wari naji.
Ummu kasa ce mata komi tai tashige cikin daki ganin ta dube ko ina baya nan yasata fitowa anti ina aka kaimin baby na dan haka take kiransa kalli har tsarabar kaciya nayo nasa shine za'a kaishi wani gurin ni wallahi adawon da yarona ni da kaina zan iya kula dashi tun ganin gawar danta se yanzu taji kuka ya tawo mata na sosai.
Sosai ta fashe da kuka ganin kayan da ke riqe hannun ummi alawa ce, sai fan milk guda biyu da mangwaro irin katon nan duda tasan sunada su a fridge hakan besata siyo masa ba.
Saurin watsar da kayan hannunta ummi tai tayo gurin antin nata tana tambayarta me yasata kuka hakan ya qara sawa ta rushe da sabon kukan
Seda tai me isarta sannan tai shiru inda ita ummi ganin taqiyin shiru yasa ta tuni fashewa da nata kukan, ganin haka yasa ummu daurewa tai shiru.
Miqewa tayi taje ta zuboma ummi Abinci ta miqa mata ta kalleta da zimmar yin magana ta juyar dakai karki cemin komi kici abinci kawai tun jiya rabonki da abinci ina kallonki baki ci abinci ba kika tafi.
Seda ta gama ci sannan ummu tace kije ki kwa6e kayan in yaso sekije can bangaren baba mahmud ki zauna insan zama ni kadai bata kawo komi ranta ba ta miqe tai daki duda tanasan jin dalilin kukan antin tata sedai batasan ta kuma sata kukan.
Acan 6angaren baba mshmud ummi ta shiga tasha jinin jikinta ganin duk mutan gidan anan babu kuma alamar wai suna farin ciki ne.
Fadila ce yar gidan Baba kabiru ta mstso dab da ita ta dafata tace ummi ya haquri kumi ta kalleta soroso haquri kuma ta fada eh mana haqurin danmu wato Abbakar ta miqe wane Abbakar kuma.
Zee ta matso babyn ki mana da yake duk sun san haka take ce masa tai saurin barin falon rasa inda ma zata tayi kasa shiga inda ummu take tai tai bayan gidan tahau rusa kuka.
Iya shaquwa ta shaqu da yaron ashe bazai girma ta ga aurensa ba kamar yadda kullin take buri tun yana zanin goye ta saba dashi da masa komi har ya bude ido yai wayo yake kiranta da umma ashe dazu ganin qarshe tamai da zata tafi makaranta ta makara sun fito tana riqe dashi tai masa wanka ummu ta fito tana fada banace inkin makara ki dinga tafiyarki ba banishi nan ta amshe shi maza jeki ki shirya.
Ta fito ta biya ta dakin ummu yana zaune kan cinyar mumyn tasa suna za6ar kayan dazaisa tace anti ni natafi to Allah bada sa'a kije ki amshi kudinki gurin kawu to tace gami da lakace masa hanci baby se na dawo yasa dariya tai waje.
Jitai an dafa ta tai saurin goge hawayenta gami da juyowa Yah Abbakar ta gani ya komar da ita yazaunar shima ya zauna.
Haba ummi ki dena kuka duk me rai mamaci ne addu'a zaki masa ki kuma dena kukan kinga in momy dinsa taga kin tada hankalinki ita nata kuma tashi zaiti ki daure ko ita take kukan kiyi ta rarrashinta kinji ko to tace gami da kuma share sabon hawayen da yazo mata da sharje majinar a hijabinta irin na me kuka.
Yaita mata nasiha seda yaga tai shiru ya miqe yanzu kije can kisa taci abinci nasan tun safennan bata ci komi ba to tace ta miqe tai cikin gida.
Duk qawayenta sun zo mata gaisuwa har wasu cikin mazan ajinsu Ahmad har mum dinsa seda tazo dan ita har Abbakar din tasani.
Su Aisha ma kullin suna tafe kullin kuma basa gajiyawa da yima ummu nasiha duda tana qoqari sosai wajen boye damuwarta.
*Bayan wata hudu da rasuwar Baby Abbakar.*
Sannu a hankali ummu ta fawwalawa Allah ta riqi karatunta da diyar ruqonta duda wani sa'in takan tuna da yaronta sedai addu'a kawai take masa.
Yan abu daya ke damunta shi ne san mijinta wanda ala dole ake san rabasu gabaki daya baba mahmud ya hanashi zuwa gidan nasu.
In makaranta zata ya daukar mata driver shi ke kaita ya tsaya ko zatakai yanma ya dawo da ita gashi wannan semester din Abbakar din baya daukansu ko zuwa yai department dinsu sedai su kalli juna daga nesa dan bata isa tai masa magana ba dan in driver din yaganta kamar a idon Baban nata ne.
Zaune take gaban gaban iyayen nata baba mahmud ya fara da gyaran murya kamin ya kira sunanta, ta daga ido ta kalleshi yace ba komai yasa muka kiraki ba se dan mu gabatar miki da lawyer din da zai kareki a kotu dan munyi munyi da yaroncan ya sake ki ya qi.
Tai saurin daqowa ta kuma kallonsu wannan shine lawyer din wanda aka nuna yasaki murmushi gami da fadin sunana Barrister Bashir salman ni zan kula da shari'ar taku ta kuma kallonsa tama kasa magana gabaki daya ta rasa abin fade.
Ki tashi kije gobe ne zaman kotun zai fara in ana buqatar wani abu daga gareki zan kiraki to Baba tace dan bata cewa kawun ma ta miqe tai waje.
Tana fita kukan da ta kwace ya tawo mata tai saurin barin bangaren tana shiga falonta ta rushe da kuka...
[1/13, 4:27 PM] 🅰️ " AXEEX✌🏻 D'🅱️🅾️Y😎: _POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚
[1/13, 4:28 PM] 🅰️ " AXEEX✌🏻 D'🅱️🅾️Y😎: *ABBAKAR*
*200---210*
Jitai an dafa ta cikin sauri ta dago dan ganin waye ummi ta gani anti mene kike kuka dan Allah ki rage damuwa kinji tasa hannu ta goge mata hawayen da ya 6ata mata fuska.
Anti dan Allah ki fadan meke damunki ko addu'a ce na tayaki ba komi ummi kawai na tuna da baya ne.
Ummi tace anti kan Yaya Abbakar ne ko ummu tai saurin kallonta da mama ki ummi ta qara da cewa insha Allah bazasu rabaku ba anti.
Ummu cike take fal da mamaki wato tana ma ummi kallon yarinya, bata qara shiga mamaku ga seda taji ummin na fadin anman anti kince musu kina sansa ta kalleta sororo alamar me kike nufi.
Anti kema se kinyi wani abu ni inaji ajiki na bawai sunasan rabaku ba ne suna son ji daga gare ki ne sunasan suji kince karsu rabaku da bakinki.
Ummu tace to inba san rabamu suke ba me yasa gobe zasu fara zaman court narasa me yasa suke san rabamu na rasa me ya musu.
Ummi tace anti kiyi haquri ki daure kije kice musu kinasansa ina cewa sukai zasu rabaku dan suna zaton auren dole ya miki dan baki da gata yanzu inya sakeki se wanda kike so zasu baki indai haka ne kenan ko shi din kika ce kinaso zasu baki.
Mamaki fal ran ummu me yasa dani banyi tunanin haka ba da ita kallon yarinya qarama takema ummi ashe duk tana sane da abinda ke faruwa agidan nace "ummu kenan daman yawancin iyaye kan ma yaransu kallon yara qanana irin basu san komi bacin da wasu yaran sunfi wani babban fahinta da iya zance"
Ruqo hannunta ummi tai anti ki daure kije ki fada musu har bakin falon baba mahfud ummin ta rakota seda taga tashiga sannan ta juya zuwa gurinsu.
Da baba Bashir ummu taci karo yace ummulkairi ba yanzu kika bar nan bane tai saurin cewa eh Daman magana nakesan muyi to to yace ai se mu koma cikin tabi bayansa.
Sauran da suma suka miqe da zummar fita suka dawo suka zauna ganin ya zauna itama ta zauna yace tace zata fadi magana ne.
Baba mahmud yace munajinki ummulkairi tai ta maza gami da nemo duk nutsuwarta kamin tace daman roqarku zanyi dan Allah karku rabamu da shi wallahi inasansa.
Gabaki daya suka kalli juna gami da sakin murmushi kamin Baba mahmud ya dora kika ce kinasansa tai shiro da kinsan haka kikai shiru ai da bata kai ga haka ba ma.
Yanzu kije maganar shiga kotu anbarta zan nemeshi dan shirya yadda tarewar zata kasance jitai kamar tasa ihu dan murna ta miqe tana sun sun dakai yayin da fuskarta ke dauke da murmushin farin ciki.
Hartakai bakin qofa Baba mahmud yace ummulkairi tai saurin kintsa kanta dan niyarta tana fita tasa tsalle ta juyo inda wata matsala zaki iya samun ko wanne cikinmu kinji to tace tai waje.
Alhamdulillah take ta fade gami da dansa gudu tai bangarenta tana shiga ta rungume ummi tana murna.
Seda ta nutsu ta fara tunanin ko ta ya zata ma Abbakar albishir tunda yanzu bata da waya tun kwanan Babyn ta arba'in da rasuwa aka kwace wayar duk dan karsuyi waya da abin sonta.
Ummi kije gidansu Takwararki kice tazo inji ni ta tawo da wayarta to anti
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 13 Chapter of 15