Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
mata dadi koda tana sallah lokaci kadan kadan take dan murmusawa kodan yadda nasir kesan Abbakar dinta ne oho dan rabon da taga yaron na kyakyata dariya yanata warkajaminsa tun dena zuwan nasir abu kadan ma aka masa sai kuka kodan farin cikin danta zata haqura ta takurama zuciyarta taso nasir . Yana dawowa yace ni zan wuce sai kinjini yah mun gama abinci kazauna kaci inji ummi ok to kamar kinsan yunwa najeji tai dariya gami da komawa kitchen din. Farida ta shigo yana cin abinci yanzu yaya da abinci be tsaidaka ba shikenan karatuna yasha ruwa yai murmushi sorry mangofa ynx zamuyi. Sai da suka gama karatun Nasir ya musu sallama ya tafi cike da kewarsu ji yake kamar karya tafi. Gidansu Abbakar Wahidi ke ta faman kuka shi bazai tafi ba shi anan za'a barshi daqyar sai da yaga babansa yazo ya hau murna sannan ya yadda yabisu zainab sun tafi cike da kewar yan uwanta da ummanta. Shi kansa Abbakar sai yaji gidan wani iri dan dan kwana biyun da sukai agidan gwanin dadi kullin cikin hayaniyar yara hakan yasa zainab suna tafiya yace ma hajiya zaije waje sai dare zai dawo sao kadawo tace ta koma ciki. A teburin me gadinsu yazauna a qofar gida suka hau fira sai mangariba yabar nan din yai gidansu mahfuz dan ya kwan biyu bai ganshiba kamar yadda ya zata kamar koyaushe Mahfuz baya bangaren mazan gidan dole ya zayayo cikin gidan aikuwa abunda bayaso yan matan gidan sunata sha'aninsu waccan na zaune waccan na shanya ko wacce da abun da take bawai abubuwan da suke ke bashi haushi ba face shigarsu basa shigar kwarai indai sina gida duda kuwa abokan yaran gidan kowa shiga gidan yake haka mazan bakowa ne suke shaqiqaiba kawar da kai yai zai yi ciki. Ya jiyo Aisha na fadin lah yah Abbakar sannu da zuwa yadan saki fuska yawwa qanwarmu ina kuwa mutumin naje dakinsa baya nan lah ai yadawo ban garen hajiya tun rashin lafiyarsa yana nan ma yanzu ok to bari inje. Yana zaune a falon kansa kan cinyar hajiya Abbakar ya shigo ganinsa hajiya ta fada da murmushinta mahfuz ya miqe zaune a'a ai da kayi kwanciyarka dan gatan hajiya yai dariya zaka fara ko sun gaisa da hajiya ta miqo ai qwanda da kazo duk yabi ya damu kansa kan ummu ka masa nasiha nasan yafi jin maganarka akan ta kowa. Sun taba fira Abbakar ya miqe sukai masallaci agidan yaci Abincin dare sannan mahfuz ya leqa dakin hajiya zai tafi zan rakashi shima ya leqa hajiyarmu sai da safe au ba'a nan zaka kwan ba eh hajiya ban fadama hajiyata ba to agaisheta sai da safe suka fita tare. Sun dade a qarshen layi suna tattaunawa kan batun ummu kasan Allah Aminin in yau akace inada ciwon zuciya ba mamaki kullin cikin tinanin ummu nake bacci ma bayinsa nake sosai ba kai mahfuz kadaure ka cirema kanka damuwa kodan hajiya kasan yau in wani abun ya sameka tafi kowa tashin hankali haka ne shi yasa nake daurewa yawwa ka ci gaba hakuri kaji nawan sukai dariya gabaki daya gami da sallama suka rabu. Hajiya daman so nake muyi magana inji Nasir ta maida hankalinta kansa inajinka akan nefa yadan sosa qeya eh daman ta miqe kaga inbaka shirya ba inka shirya sai ka same daman hajiya tada miki zanyi na samu matar aure tai saurin juyowa da fara'arta da gaske kake eh hajiya wace kuwa wannan Hajiya ummulkhairin baba yasir what ta fada eh Hajiya alamar faduwar da sukaji yasasu juyawa da sauri Mahfuz ne zube da alamun yaji maganarsu ne hajiya tai gunsa da gudu itama hippp ta fadi a sume............. [12/31/2020, 5:52 PM] 🅰️ " AXEEX✌🏻 D'🅱️🅾️Y😎: _POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚 [12/31/2020, 5:53 PM] 🅰️ " AXEEX✌🏻 D'🅱️🅾️Y😎: *ABBAKAR* *PAGE 80---90* Rasa ma kan wazaiyi yayi ta maza yai yadauko ruwa yai kan Hajiya cikin sa'a ta farfado da tana bude ido ta tankade nasir tai kan mahfuz dake kwance tahau jijjigashi miqon ruwa mana ta fada cikin qaraji. Dasauri ya miqa mata ruwan ta hau shafa masa bai far fado ba da sauri Nasir ya daukeshi sai mota hajiya na biye dashi ganin haka yasa sauran mutan gida dake farfajiya sukayo kansu suna tambayar lafiya basu basu amsa ba suka bar gidan hakan yasa suma suka biyosu amota sai kadan aka bari agidan. Kai tsaye asibitin nasarawa suka wuce basu wani sha wuya ba dan babu marasa lafiya sosai a emergency din yau aka karbi mahfux din. Tun wajen awa guda da'aka shiga dashi dakin bada temakon gaggawa hajiya keta faman kai kawo tana hawaye babu yanda ba'ai da ita tazauna ba taqi da nasirma ya mata magana saita haushi da fada daqyar tai shiru shima dan nurse ce tazo tace ta ishe su. Ganin hajiya zata iya masa baki yasashi miqewa yabar gurin yai dan nesa kadan dasu dan yaga irin hararar da take sakar masa lokaci lokaci gami da tsaki da qwafa da take ja in suka hada ido. Doctor yana fitowa sukai kansa bai kulasu ba yai gun Nasir dan yasanshi aikuwa hajiya na ganin haka tabi bayansa tana fada yau naga mara mutuncin likita ya jiyo zai yi magana Nasir ya dafoshi Am sorry Abdul mum dina ce yadan saki fuska kadan gami da cewa Hajiya bawai na share ku bane kunsan irin haka namiji yafi karfin rai. Eyyye qarfin rai har yafi na cikin sa da nadauka nai naqudarsa ni nasan zafinsa dan haka zanfi kowa iya jure abinda ke damunsa dan in kula dashi ganin tadau zafi yasa Doctor din yace ai yamaji sauqi dan mun shawo kansa dakyar muka dai daita numfashinsa zaku iya shiga ku ganshi bata jira cewarsa ba tayi gaba. Nasir ke biye da ita saida suka zo dedai dakin ta juyo ta watsa masa harara me kuma zaka shigo kayi masa bai ce komi ba ya koma baya ya tsaya. Kwance yake idonsa a rufe da alamun bacci yake hajiya taja kujerar gefensa ta zauna gami da kamo hannunsa ta riqe yai saurin bude idanunsa zatonsa Nasir ne ganin hajiya yasashi fashewa da kuka ta hau rarrashinsa dakyar yai shiru. Da sassafe nasir yabar asibitin saida ya biya ta gida sannan yai wanka ya shirya yai gidan ummu acan yakarya sun dan taba fira kafin ya miqe ni zan wuce yah tun yanzu eh ummu tadan shafa kan Abbakar Allah ji nake kamar karka tafi yai saurin kallonta da alamun har zuciyarta take magana anman bai fasa cewa da gaske kike tai dan murmushi Allah kuwa to banda abinki ai kwanan nan sai kinmace in fita ta rufe fuska anya kuwa yai dariya ina nan dake. Har waje ta rakoshi ya miqo mata Abbakar yako sa kuka haba dan rigima yi shiru anjima zan dawo ya zura hannu a aljifu ya miqo masa alawa yako amshe yana kiciniyar budewa. Har ta juya yace aff ban fada miki ba gobe ba lallai inzoba tadan juyo sororo sabida me yah eh mahfuz ne ba lafiya jiyama a asibiti ya kwan tadan tabe baki ayya Allah bashi lafiya gami dayin ciki abinta abinka da dan uwa sai gabaki daya baiji dadin abinda tai ba aqalla ta nuna tadan ramu ya gyada kai kawai yai gaba. Ai kuwa da Nasir ya koma asibiti ya sha fada gun hajiya kan yasan dan uwansa ba lpy yai tafiyarsa yawonsa ba ita tai shiru ba sai da Mahfuz yace dan Allah hajiya kice ya fice daga dakinnan inna tanshi numfashina hadewa yake jin haka yasa yace ya fice. Wajen qarfe uku na rana Abbakar yazo shida Hajiyarsa da qannensa biyu mata sukaita fira da hajiya inda shima sukaita fira da amininsa. Kwanan Mahfux biyu ummusalma yayar Abbakar tazo dubashi aiko tasha qorafi dan sun saba sosai da Mahfux inma mutun ba sani yai ba zaiyi zaton Mahfuz ne qaninta ha Abbakar ba. Bakowa adakin sai Mahfuz da ummu salma aikuwa mahfuz yasa mata kuka daqyar ta rarrasheshi yai shiru tahau tambayarsa mene yahau bayani kan ummu ne yar gidan baba yasir yah nasir yasan ita nake so anman yace shi zai aureta tahau masa nasiha haba nawan kabari zamuyi magana dashi nasan baisan kanasanta va inda yasani da tuni ya aura ma ita Allah yasani nace kabar min komi a hannu na zan mai magana ya riqo hannunta nagode yayarmu. Sai dare ta bar asibitin shima saida Abbakar zai tafi ya tafi ita dan bada mota tazo ba. Washe gari ta kira nasir a waya har gida yazo ya sameta ta mai bayanin komi yai dan murmushi kafam ummusalma kenan ai duniya ko hajiya bata isa tasa in fasa aurenta ba lokaci yayi da mahfuz zai dena abin da yaga dama lokaci yayi dazai gane vawai komi kake so kake samu ba arayuwa, tai sakato tana kallonsa eyye tunda hajiya ma bata isa ba inaga ni yar karoro yayi kyau ta miqe ta bar falon shima ya kade rigarsa ya bar gidan. Kwanan Mahfuz hudu aka sallamesu sina zaune gabaki daya a falon mahfuz na kwance kujerar da Hajiya take Nasir ya shigo dauke da Abbakar dansa hajiya ta bishi da kallo gami da yaron wannan fa ya dubeshi dana ne what danka kuma eh hajiya dana ne da muka haifa da ummulkhairi ta miqe ashe nasiru haukan da kake cewa Mahfuz yayi ashe kai kayi yai dan murmushi hajiya aikinsan ba qarya nake ba kuma kinsan da hankalina. Mahfuz ya miqe qarya yake hajiya dana ne wallahi qarya yake kumin shiru da Allah injita ta fada ra qarfi sukai shiru baki daya kafin nasir ya fara magana eh hajiya ki yadda dani gama kamarmu nan kina gani da yaronnan sabida shi na yanke shawarar auren mahaifiyars dan Allah ki yadda in aureta kodan kare mutuncin bawan Allahn nan tai shiru kawai tana kallon yaron da yaketa faman wasansa tabbas kamarsu nan sosai jitai tsanar yaron ta cika mata rai sosai tai kansa zata takeshi mahfuz da yake atsaye yai kasa asume tai saurin yin kan danta. Sun samu ya farfado aikuwa ya hau kuka hajiya qarya Nasir yake yaronnan dana ne dan Allah karki yadda ya aure min mata wallahi inban aureta ba mutuwa zanyi Nasir dake zaune tun dazu ko motsi beba tun suman Mahfuz yana ta faman wasa da dansa yace aikuwa sai dai ka mutu Hajiya tahau rarrashinsa dagyar yai shiru tasa aka kai mata shi daki. Adakin rokonta kawai yake kanta yadda adaura masa aure da ummu tai shiru kawai da ace wani ne cikin yaranta ke faman kiran suhan wannan yar maqiyarta ta da tuni ta yi maganinsa dan dai kawai mahfuz ne. Haba mahfuz kayi tunani kwata kwata baku dace da ita ba ko kadan ya miqe haba hajiya inban dace da itaba da waxan dace zuciyata da gangar jikina ita suke so. Nasir ya shigo dauke da yaron yanata faman dariya yace hajiya ni zan mayar dashi kuma gobe ne za'a daura mana auren kawu nazifi ne wakilinta ni kuma nazama wakilin kaina banasan ko kadan kosau daya yarona yai kukan rashin uba nasan ban kyauta miki ba anman nan gaba nasan zakiyi alfahari dani tai zuru tana kallonsa tama rasa ta cewa wai yau nasirun da ko uhum baiso yaji yace shi ke fada mata baqaqen maganganu haka. Bai jira cewarta ba ya juya zai fita mahfuz yasa qara wallahi hajiya indai baki dakatar dashi ba ta auren masoyita wallahi yau zan kashe kaina tai saurin kiran sunan nasir yai gaba batare da ya tsaya ba tace nasiru wallahi ka qara taku daya Allah ya isa kuma sai ka biyani shayarwar da naima inyaso ka canja uwa yaja ya tsaya hawaye ya biyo idanunsa. Juyo nan ka kalleni ya juyo ya kalleta kasani ni uwarka dana haifeka hai haqudarka na shayarda kai na haramtama auren yarinyar nan inko ka aurenta Allah ya isa bazan kuma yafe maba ka kuma sani koda bayan raina ne. Jiyai kamar an sheqa masa ruwan zafi qafafunsa sunkasa daukansa yana qoqarin yada Abbakar a hannunsa zubewa yai qasa jabas hawaye na bun fuskarsa. Ummu ce ta fito daga daki tana kwalama ummi kira da sauri ta qaraso gani aunty ina Abbakar tace sun fita tare da babansa tun yaushe wajen magariba ta gyada kai kawai ta koma daki. Har kusan qarfe takwas bai dawo ba ummu ta kuma futowa wai ina yace zai jene farida tasa dariya Allah umma bakida kara indai akan wannan yaron naki ne tai kwafa gami da turo baki kuban amsa tukunna kafin afaramin qorafi ummi ce tace cewa yai zashi gidansu dashi zai nunama hajiya shi what ta fada tana zare ido mai yasa kuka kuka barshi baku fadanba ummi tace cewa yai bazai dadeba. Kuka kawai ummu ta fashe dashi gami da fadin shikenan nasan hajiya bazata barmin shi da raiba kuka take sosai farida na bata haquri. Zumbur ta miqe tai daki hijabi ta dauko da wayarta sai kudi dabatasan ko nawa bane ta zari jaka tai waje ummi taso muje tace bata jirata ba tai waje ummi tai saurin binta dan tunda tadan fara girma tadena cire hijabi ko ina dashi take shiga ko bacci zatai duk yadda su ummu sukai da ita taqi ita kunya takeji. Farida ce tai saurin miqewa ta ruqo ummu haba ummu ina zaki cikin daren nan zani inga halin da yaro na yake ciki ta riqeta dan Allah ummu ki rufa mana asiri karkije dan farine fa tai dan murmushi daga gani na takaici ne tace farida sakeni koma dan mene bazan zauna inaji ina gani akashemin shi ba wai da sunan kunya. Haba ummu aikin san babu ta yadda za'ai Yah Nasir yabari wani abun ya sami Abbakar kema kinsani ta gyada kai nasani Farida saidai nasan makircin mahaifiyarsa bata jira cewar Farida ba sukai waje ummi ta bi bayanta. Adai daita sahu ta tara sai da suka fara tafiya yace haija ina zamu ne sunan unguwar ta fada masa. Adai dai qofar gidan ya parker dan sahun yace hajiya mun iso ta ciro dubu ta miqa masa ya amsa ta juya tana kallon kofar gidan yace hajiya canjinki riqe tace ya juya yana murna dan be mamakiba ganin tamfatsetsen gidan da yasaukesu da alama yarinyar gidan ce ya fada. Gidan su Abbakar Tun jiya suke ta gyare gyare da kin tse kintse yau kam girki siketayi tun safe dan hajiya da kanta tashiga madafa ita da maryam da ummi dan yau muktar zai zo hutu da autan hajiya. Yadda hajiya ta zage tana ta hada kayan datasan yanaso koya kai mistake yanzu ta hau fada abinda ba sabonta bane haushi duk yabi ya ishi ummi dan duk fadanda hajiya dake yawanci akanta ne koya tai mistake. Sai kace ba ita ce take kuka lokacin da zai tafiba kishin sakun takan ya motsa. Tana sane cikin zobon da hajiya ta gama masa ta zuba zuma duda tasan bayasan zuma a abu me sanyi aikuwa hajiya ta hau fada har saida taji dama batasa ba aikuwa idonta yai rau rau kamar zatai kuka maryam ta faki idon hajiya ta mata gwalo nan da nan hawayen ya zubo hajiya kinganta ko hajiya ta cillama maryam harara fita idona maryam tunkan raina ya baci bansam tsokana ummi tasa dariya gami da mata gwalo zatai magana hajiya tace karki kawon qara aike kika fara shiru maryam tai tana hararar ummi dan tasan kobata ummi komi ba hajiya bazata mata magana ba dan duk gidan sun sani in abu ya hadaka da ummi dole kaine mara gaskiya sedai in ita da dan autane to dole ta dau rashin gaskiya. Sun gama komi sunyi wanka inda hajiya tai tafiyarta dan cewarta bazata bar dan lelenta ta jirasu ummi su bata mata lokaci wajen kwalliyarsu ta tsiya ba. Suma sun fito tsab shigarsu iri daya sunyi kyau sosai ummi tai daki da gudu tana kiran hajiya wayam ta gani gaji mai aiki ce take fada mata ai tuni hajiya ta tafi aikuwa ta zunburo baki tai waje tana bubbuga qafa ita ala dole taji haushi da Abbakar taci karo ya riqota yar kelen hajiya ya akaine ta kuma kumburo fuska ba hajiya ce ta tafi ta barni ba yasa dariya ba dole ta tafi ta barki ba mowanta zaizo kin zama bera tasa kuka yaya yai saurin goge mata hawayen da wasa nake muje inkaiku ta tirje ita bazata ba haba mowar hajiyarta kidaure muje kinji tawan ta dan murmusa yajata suka fice maryam biye dasu. Seda suka Abbakar ya amshi powder gun maryam yashafa mata kar yaroncan ya rainaki yaga kinyi kuka tai dariya tanasan yayanta sosai duda duk sauran yan uwanta haka sijeji dasu ita da autan hajiya shi yada suke tsula tsiyarsu se kace yara inda azahiri shekarunta ashirin cif kazalika autan hajiya twins ne ita dashi saidai ita aka fara haifa saidama takwana biyu akama hajiya CS aka ciroshi. Gabaki daya sunyi mamakin yadda autan hajiya ya girma inba kasani ba kai ka rantse shidin yayan maryam nema ba ummi bama. Tun saukowarsa ajirgi hajiya na hangoshi ta gilas sai washe baki take aikuwa suna fara tawowa suka fito inda zai hangosu ganin yan uwansa wanda rabonsa dasu shekara uku kenan yasa sanyi ya ziyarci ransa. Yana zuwa inda suke yai gun ummi wanda tunda ta hangoshi murmushinta yaqi tsayawa hajiya ta zuba musu ido eyya wato abun haka ne yar uwarka ka sani banda uwakka yasaki ummi yazo gun hajiya ya rungumeta yana cewa haba hajiyata aikema kinsan ke nafara gani kinsan kishinta ina kula wani ba itaba har in koma ana mita suka saka dariya baki daya. Agida ummi ce tai dakinta da gudu ta fito riqe da roba tace qanina bude bakinka yasha kunu waye qanin naki ta dubi Abbakar tace yaya dan Allah waye babba yai dariya gami da daga kai alamar tunani bari in tuna kai yaya ya auta shine auta ya daka tsalle yeeee tasa kuka yaya yai saurin cewa shine qarami tai dariya muktar ya amsa yakalla gami da tabe fuska wannan wace qazantarce ta gallah masa harara gami da amshe abunta tai ciki yai saurin bunta sorry babbar yaya ya amsa ya fara sha Vanana ice cream ce tamai dan yanasanta sosai. Sai da yai wanka yazo yaci abinci sannan suka hau hirar yaushe gamo yadinga basu labarin qasar waje basu ankaraba sukaga daya duk suka miqe sukai daki dan kwanciya. Anman hajiya ta daga masa hannu na riga na yanke wukunci dole agoben za'a daura mata aure anman bada kaiba da mahfux shi kuma yaron da kake cewa naka ne koma nawaye na qwaceshi na baima mahfuz tunda shi zai auru uwadda............ [12/31/2020, 5:53 PM] 🅰️ " AXEEX✌🏻 D'🅱️🅾️Y😎: _POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚 [12/31/2020, 5:54 PM] 🅰️ " AXEEX✌🏻 D'🅱️🅾️Y😎: *ABBAKAR* *PAGE 90---10* *Godiya gareku masoyan books dina inajin dadin yadda kuke karantawa gami da addu'o'inku garenk nagode sosai ina Alfahari daku* Wajen qarfe bakwai Babbar yayarsu ta iso gidan ganin duk suna bacci yasa tai kitchen ta hada musu kari ita da gaji da sauran masu aikin gidan tana cikin jerawa Hajiya ta fito itada ummi ummi ta daka tsalle yaya saikar yaishe tun jiya nazo kunyi bacci gami da durkusawa ta gaida Hajiya ummi tai waje. Wajen takwas aunty zainab tazo hajiya tai ta fada dan tace tasan ita tasa dole sukayi irin wannan sanmakon bacin tasan cewa batasan tafiyar duhu hajiya wallahi seda aka idarda asuba muka tawo ahab ai duk daya nan cikin wayo zainab ta basar da batun suka shiga wata hirar. Gabaki dayansu sun taru a falo suna fira Muktar ya sawko suka miqe suprise suka fada da dan qarfi yasauko yana murna sosai yaji dadin ganinsu. Durkusawa yai ya gaida hajiya da sauran yayyansa kafin yaya babba tace haba autana come give me a hug i miss u sosai ya manne kai bacin jiya kika qi zuwa taroni auni din kaima haka zainan tasa dariya zonan nawan ya juya qeya bacin kinmin buqulu naso yau inzo katsina ke kuma kika wani diro da sassafe gabaki daya suka sa dariya daman sun san halinsa ba'a iya masa fakar yaya babba yai ya fada kanta yana fadin suprise hug wayyo zai karyani ta fada ya miqe yana dariya zainab ta miqe yai dinning wannan suprise din badani ba akaini a baro suka saka mata dariya. Ita ko ummu gidan take bi da kallo yayin da wani abu dabatasan ko mene ba yazo ya tsaya mata a wuya ada tasa aranta tabar gidan kenan ko unguwar bazata qara zuwa ba sedai yau tanajin kome za'ai ba wanda ya isa ya hanata shiga. Kukan karen da taji yafara tashi yasa tai saurin dawowa daga tunanin data tafi ta fara buga gidan daga ciki me gadi yace waye ummulkairi ce ta fada bai dauki murya ha be kuma gane sunanba anman jin mace ce yasa ya bude. Qofar gidan cike yake da hasken wuta hakan yasa yana budewa ya ganeta yadan saki fuska a'a ummu daman kinanan idonta kuwa ya kuma cikowa da qwalla kamin tace baha Sale ina wuni ya amsa lafiya qalau ban taba zaton ganinki yanzu ba. Ta qaqaro murmushi wanda kana ganin kasan na yaqene nima baba ban taba zaton zuwa na nanba ya gyada kai kafin ya kuma magana tace Yah nasir kuwa yazo. Eh yazo da wani dan kyakkyawan yaro gabanta ya fadi cikin rawar murya tace ya fito dashi yace a'a tun dazu inanan banga fitarsa ba to baba bari mu shiga ciki. Bata jira amsarsa ba suka yi ciki. Kai tsaye bangaren yan mazan gidan tai gabanta sai faduwa yake zuciyarta fal tsoro ta dai daure ta shiga qofar da zata sada ta da gurin nasu. Ba qaramin mamaki abin ya bata ba ganin gurin shiru ba kowa dan ada saninta dedai wannan lokacin inkazo gurin cike yake da samari kowa na sabgarsa masu hira nayi masu chat masu tireni dan duk suna da kayan yi. Hakan yaqara tada mata da hankali da sauri tai dakunansu kai tsaye dakin da tasan na Nasir ne ta nufa ta tura a bude take sedai bakowa duk ta shiga ba kowa tabbas akwai abinda ke faruwa ta fada tai cikin gida. Ai kuwa afalo ta taddasu tsai tsaye sunyi jugun jugun hajiya nata zazzaga bala'i Nasir ta hanga can nesa azaune hawaye nabin kuncinsa Abbakar na gefensa yana ta faman wasansa a jikinsa ba abinda ya shafeshi sai lokaci lokaci yakan daga ido ya kalli Hajiya dake faman fada. Da sauri ummu ta qarasa ta suri danta gami da juyawa zata fita aiko mahfuz da sauri ya miqe cikin murna yayo gun ya rungumeta tai wani kukan kura ta tankada shi gami da bashi mari ya riqe gun yana kallonta dan gaskiya yaji zafin marin daga hannu yai zai rama kome ya tuna kawai yasauke hannun yana murmushi yaja tsaki gami da fadin kada ka qara kuskuren tabani dan akuya kawai. Murmushi

Chapter 5 of 15