Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ya kumayi yai gabanta ya durkushe yana kuka pls ummu kiji kaina duniya ke kadai zuciyata takeso nasani inban aureki ba mutuwa zanyi ta ja hannun ummi gami da fadin wallahi saidai ka mutu in dagani kadai muka rage aduniya to gwara in mutu ba aure wallahi inda zaka mutu zanfi kowa farin ciki ta juya zata fita. Hajiya tai saurin fizgota ganin cikin yaran nata bame iya tsai da ita tasa hannu zata fizgi Abbakar tana fadin inadai yaro jika nane dan haka baki isa kin fita dashi a gidan nanba kema kanki baki isa ki fita ba aure keda Mahfuz yazama dole. Fizge rigarta tayi gami da fadin wallahi ko gawata ta fi qarfin auren dan iskan danki tasa hannu ta mareta har ta daga hannu zata rama ta sauke gami da fadin wallahi kinci darajar yah nasir da sauri ta faki idonta tai waje da gudu ita da ummi Abbakar na faman sheqa dariya zatonsa wasa take masa. Mahfuz ne ya miqe zai bisu saidai jirin da ya dibeshi yasashi faduwa kasa tim da sauri kowa yayo kansa hajiya cikin tsawa take fadin ku bita ku bita dasauri su muktasir suka miqe sukayo waje dan nemanta saidai fa ina duban duniya batanan. Ita kuwa ummu tana fita abakin gate taji an rufe mata baki da tsumma haka ma Ummi cikin qarfi aka jawota zuwa dan dakin da ke qofar wajen tanata wutsil wutsil din so ta juya taga ko waye ina abu yaci tura.............. *Da yawa suna min test wasu nakan samu in amsa musu da wuri wasu kuma sai ya jima ina mai baku hakuri kan hakan dan bawai hakan na nufin wulaqanci bane saidai abubuwa sukamin yawa anman kusa aranku F.A.Ya'u mai san masoyanta ne ako ina suke* *Ban cika qorafi kan readers ba koma ince ni ban taba ba saidai wani abu da yadan fara batan rai dasu shine insun ma magana kadan dauki time baka amsaba wani dan rashin kyautawa irin tasa sai yafara zagi ko faden maganganu marasa dadi hakan bayamin dadi danshi rubutun online sa kaine kawai bawai rashin abinyi ba sai sha'awaryi dan kawai ina rubutu online bashi yake nufin duk sanda kaso ko kika so zaki min magana in amsaba dan kuwa inada abubuwanyi da dama masu mahin manci arayuwata fiye da rubutun online* *Readers kance writers basu da mutimci musanman na online sai dai kuma yawancin readers masu fadin haka asannu na gane sune marasa mutinci ta yadda suke zagewa su dinga cima mutun mutinci beji ba be gani ba.* Ruwa Hajiya ta shafawa mahfuz a fuska ya farka a gigice yana fadin hajiya karki barta ta tafi dan Allah inban aureta ba bazan iya rayuwaba hankalinta yai matuqar tashi. Malan ka ishemu da kuka da kasan kanasanta kai sana diyar barinta a gidan nan mansur ne ke fadin haka hajiya ce ta daka masa tsawa yai shiru yana dan qunquni. Shiko nasir jin su muktasir sunce basuga su ummu ba hankalinsa ya tashi dan tazararsu da futarta beci ace har ta bacema ganinsu ba. Miqewa yai zaiyi waje hajiya tace ina zaka mara san yan uwa dan uwanka na wani hali zaka fice yadawo jiki ba kwari ya zauna. Mahfuz ne ya miqe hajiya bari kawai inje gidan da take in roqota hajiya ta zaunar dashi kayi haquri yanxu dare yayi gobe maje da sassafe inyaso sema mu tafi da masu daura muku aure inma acan zata zauna ita taji shidai Nasir abin duniya duk ya isheshi ji yake kamar qirjinsa zai tsage zuciyarsa ta fito tausayin ummu duk ya cika masa zuciya. Gidan su Abbakar. Gidan cike yake da farin ciki kana shiga zaka san tabbas yau suna cikin farin ciki shi kansa Abbakar wasai yake jin kansa bakamar kwanakin baya ba da zuciyarsa take cikin kunci duda farin cikin da suke ciki yanzu koya ya tuna da ummu da nahfuz sai gabansa ya fadi dan baijin zai iya rayuwa batare da ummu ba saidai baijin zai iya auren matar da Amininsa yake masifar so yanajin zai iya sadaukar da komi akan abokinsa ada duda zatonsa natana da aure yanajin wataran zai iya aurenta tunda yayi yayi ya cire santa ya kasa saidai tun lokacin da ya gano ita mahfuz yake so yasa ma ransa koda zai mutu ya haqura da ita. Kamar kullin tun zuwan muktar hutu yau kwana hudu kenan gidan cika yake da yan zuwa sannu da zuwa dare yayi kowa ya miqe yai makwansa cikin shauqi da farin ciki haka shima Abbakar saidai yana tura qofar dakin ya nemi farin cikin ya rasa haka kullin yake dan da ya zauna shi daya shikenan tunanin ummu ne ke cika shi in bacci yake baccin cike yake da ummu ya rasa yadda zaiyi addu'a kullin yake kan Allah ya temake shi ya cire masa ita aransa anman kamar addu'a yake Allah ya qara masa santa. Juyi kawai yake akan gadon hawaye na bin fuskarsa yama kasa rufe idansa dan ko rufewa yai ita yake gani tana masa murmushinta me ratsa zuciya. Gidan su mahfuz da sassafe ya farka dan be niyar komawa ba bayan yin asuba saidai bacci barawo yai gaba dashi ko wanka be ba yai dakin hajiya dan dama ya dade da dawowa bangarenta. Qofar a bude take ya tura ya shiga ko taisheta beba tana zaune tana lazimi yace haji pls taso mu tafi ina tace yadan zaro ido kin mance gidan ummu taja tsaki kabari sai anjima dan ita dan kawai tana san mahfuz ne sosai shi yasa take iya haqurin jin sunan ummun dan batasan ransa ya baci anman a haqiqanin gaskiya ta tsani yarinyar sosai. Hajiya inbazaki ba ni zani ta miqe muje suka fice sai da suka biya gidan malan habu suka daukoshi shida almajiransa guda hudu masu jire masa dalibai dan daura auren. Bakwai dedai a gidan ta musu sunsha bugu kafin Farida tazo ta bude tana murza ido alamar bacci tana fadin ummu badai yanxu kika dawo ba sai dai ba ummu ta gani ba tadan zaro ido tana ja da baya. Hajiya da mahfuz da sauran mutanen suka shigo suka tsaya hajiya na bin gidan da kallo ba lefi yana da kyau sosai da kuma dan girmansa. Mahfuz ne ya daure yace ina ummulkairi pls Farida tace wallahi tun jiya da ta tafi dauko danta a gidansu bata dawo ba what ya fada pls karki mana qarya ta ce sabida me zan muku qarya. To me yasa baki nemeta ba taja tsaki kaji malan taya zaka zo ka isheni da tambayoyi. Nasir Hajiya ta kira tace ya sameta gidan ummu gin tana gidan da sassafiyar nan ya daga masa hankali hakan yasa yashararo mota ya tawo Allah ne kawai ya kawoshi lafiya. Koda yazo ake fada masa ai tun jiya bata dawo gidanga hankalinsa ya kuma tashi cikin tsoro da rawar murya yake tambayar Farida. Farida dan Allah ki fadan gaskiya da gaske bata dawo ba ta gyada kai cikin kwalla dan itama yanzu hankalinta ya tashi wallahi yaya bata dawo ba ta kirani bayan wajen awa uku da tafiyarta tace ai an dai daita komi yanxu dan haka a gidan zata kwana salati ya saka Farida me yasa baki kirani ba tace ai saida ta bani kai a waya ka tabbatar min hakane batunta innalillahi wa'inna ilaihirraji'un ni kuma Farida wallahi muryarka naji. Aikuwa mahfuz yai kansa ya shaqeshi yana fadin wallahi saika fito min da masoyita mugu kawai da sauri Nasir ya fuzfe wuyansa ya tankadashi baya kai malan bansan hauka kabarni inji da abinda ke damuna. Ita kuwa Hajiya can kasan ranta dadi taji da batan Ummu dan gaskiya batasan ko kadan danta ya aureta dan kawai ta fuskanci in bai aureta ba komi zai iya faruwa zai iya mutuwa. Wayarsa Nasir ya dauko ya fara kiran Aisha qawar ummu batare da la'akari da cewar ai safiya bace bugu uku ta dauka cikin muryar bacci tai sallama a gaggauce ya amsa bai jira tace komi ba yace Aisha ummu tazo gidanku kuwa ta gyada kai kamar tana gabansa tace a'a me ya faru fatan lafiya bai bata amsa ba ya katse ya fara kiran Fatima ita ma din haka ne duk wadda yake da number dinta ya kira ummu bataje ba. Jiyai qafafunsa sun kasa daukansa ya tsugunna gami da dafe kai dan yadd yaji yana sara masa. Duk inda suke saka ran ko ummu taje sunje ba ita ba dalilinta hankalinsu duk ya tashi sun rasa me zasuyi cigiya suka kai gidajen radio. Hankalunsu bai qara tashi ba sai da police suka tsinci kayan Abbakar da wayarta a wani kango da ake zube shara hijabin ummi anan dan gaba da qofar gidansu mahfuz din. Gidansu Abbakar Muktar ke magana yaya wai me nayima Yaya mahfuz ne tunda na dawo baizo ba Abbakar yai dan murmushi kwana biyu bai cika jin dadi ba inajin jikin ne ka bari anjima maje mu gano ko lafiya to yaya yace. Abi ne dan gidan zainab keta sukuwa kan muktar yanata wasansa ta sauko dauke da jaka Abbakar ya miqe ya amshi jakar qanwar an an gama shiryawa tai dariya bari yaya babansu Abi ne yace lallai lallai inshiryo in dawo gida nayi nayi yabari in sati biyu yaqi. Yadan zaro ido sati biyu tab ai kwana biyar dinma yayi qoqari wallahi inni ne ai kwana daya ma sai ikon Allah zakiyi tadan zaro ido tab kaji yayan nan kace kulle zakayi yai dariya no ba haka bane kawai dai ni atsarina ba zuwa akwana ko kai dare tab matarka ta banu koda yake kai ko yar budurwar ma baka da ita gabansa ya fadi ya tuno da ummunsa yai saurin cire sa din yaha fadin ba tawa bace azahiri yai dariya haka nace miki bani da ita. Ta zauna yawwa yayana nakaina fadamin ya miqe to sarkin san gulma bazan fada ba yai waje da kwatin nata dan kai mata mota. Wajen biyar Abbakar da muktar suka fito dan zuwa gidansu mahfuz bayan tafiyar zainab. Gidansu mahfuz. Yadda Abbakar yaga mutanen fidan basa wani nishadi kamar da kana ganinsu kamar marasa lafiya yasa yasha jinin jikinsa kasan tuwarsa mutun bame san shiga sabgar kowa ba yasa ya basar yai bangaren hajiya. Sun gaisa ba tabo ba fallasa ta fara tsokanar muktar a mutanen qasar waje haka ka girma jibeka kamar bakaine ka tafi kana dan tatsitsi sukai dariya gabaki daya. Abbakar ne ya miqe yai dakin da yasan mahfux ya koma yabar yajiya da muktar suna ta fira. Kwance ta taddashi yana kallon fanka sake faman wulwulawa wanda har Abbakar ya zauna mahfuz baiji shigowarsa ba. Saida ya tabashi ya dawo dedai ya muqe zaune Aminin yaushe kashigo yaidan murmushi yanxinnan tunanin me kake cikin kwalla yace ummu gaban Abbakar ya fadi to me ya sameta. Ummu ta bata what ya fada gami da miqewa yaushe me yasa baka fadanba cikin tashin hankali yake maganar mahfuz ya dafa shi kaima ka damu ko aminin nasani daman nasani Abbakar dina me damuwa da abinda na damu dashi ne. Wai garin ya ta bace din nan mahfuz ya bashi labarin komi hankalinsa ya tashi jiyai jiri na dibarsa yai saurin zama gami da riqe kai shikenan an sace masa ummunsa wataqilma yan yankan kai suka tafi masa da ita. Bai taba zato da tsanmanin haka yake san ummu ba irin tanzu yasan yanasanta da yawa anman yadda zuciyaraa ke bugawa hawaye na bin fuska bama yajin me mahfuz ke fadi yasa ya tabvatar indai ummu da gaske ta bace ansace ta komi zai iya faruwa gareshi. Miqewa yai zaiyi waje jiri ya dibeshi dishi dishi yake gani yai karo da bango nan yayo baya luuuu yai qasa mahfuz ya miqe yayo gunsa yana kiran sunansa......... [12/31/2020, 5:54 PM] 🅰️ " AXEEX✌🏻 D'🅱️🅾️Y😎: _POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚 [12/31/2020, 5:54 PM] 🅰️ " AXEEX✌🏻 D'🅱️🅾️Y😎: *ABBAKAR* *100---110* Cikin sauri ya dago shi mamaki ne ya kamashi ganin Abbakar na murmushi daurewa Abbakar din yai ya miqe sannu mahfuz take cewa kawai ya gyada kai badai kaji ciwo ba ko ya kuma yin murmushi haba yar wannan faduwar sukayi dariya duka Abbakar yai waje majfux na biye dashi. Muktar ne ya miqe yaya har ka fito eh naga magariba ta kawo kai saida suka gaisa da mahfuz shima ya masa tsiyar girma da yayi suka fito dan barin gidan. Tafiyama dagyar yake yinta dan qarfin hali kawai yai anman dishi dishi yakeji gashi har yanzu jirin be gama sakinsa ba. Masallacin sake qarshen lokon yai bari in je masallaci kaje ka fadawa Hajiya nashiga masallaci kartaga mun dade inyaso sekayo alwala ka tawo to yaya yace yai gida. Yana shiga masallacin ya zube ya dade riqe da kansa kafin ya iya kwantawa sai da ladan yafara kiran sallah ya miqe yana bin kiran sallah din yai waje danyin alwa. Koda ya yayo alwala dinma komawa yai ya kwanta yama rasa meke damunsa dan ayanzu bazai iya cewa ga abinda ke damunsa ba shi dai yasan kawai baya da lafiya. Ita kuwa ummu tana fitowa daga gidan rasa inda zata tayi tayi qofar gidan da gudu jin datai an kamota yasa ta kwalla qara jin qararta yasa aka rufe musu baki dakin me gadin gidan taga anyi dasu zullo kawai take tana qoqarin juyowa dan ganin waye ya riqeta ta kasa. Muryar baba me gadi taji yana fadin zan bude miki baki anman dan Allah kar kiyi qara gyada kai ta shiga yi alamar to ya saki hannunsa kafin tace wani abu yace karku fito ina zuwa. Gurin gadinsa ya koma ya zauna yana zama saiga su muktasir tambayarsa suka shiga yi koyaga ummu eh yace musu naganta sun hau wani adai dai ta sahu da yazo wuce oppps suka fada gami da komawa cikin gidan seda suka jima da komawa ya miqe yai dakinsa. Ummu ce cikin kuka take tambayarsa me yasa ya kawosu nan yai shiru kafin yace inda na barku kun fice tabvas kuwa zasu ganku su kamoku kuma dolene ki auri mahfuz din tadan kalleshi da mamaki wato duk yasan me ke faruwa. Kamar yasan abinda ke ranta yace tun wancan lokacin naso temakonki saidai bani da dama yanxu ki miqe zansa akaiku titi inyaso saiki koma inda kike da zama to tace masa gami da masa godiya yasa dansa yakaita har titi suka hau dan sahu zuwa gidan ta. Koda suka koma gida farida ta rufe gidan han yasa tabaima ummi Abbakar ta bude gidan tace su jirata a farfajiya tai cikin gidan. Ahankula ta ke tafiya hartai dakinta ta dauko ATM dinta da yan kayan Abbakar sai takardun secondary dinta da sauran takardunta masu mahin manci da kala uku na kayan ummi ko nata bata dauko ba takulle dakin tai waje. Saida ta kulle gidan sannan ta amshi Abbakar ta goyashi ummi ta kalleta anti ina zamu qauyenku tace can zamu can zan koma ummi. Shi ko Abbakar bayan an idar da sallah yaita roqon Allah yasa ummunsa tana da rai cikin qoshin lafiya ya bashi lafiya kodan yasamu damar nemota ganinta da jin tana cikin qoshin lafiya koda bata matsayin matarsa ji yake yafiye masa wannan batan nata. Sai isha ya koma gida bayan ya danji dadin jikinsa. Abun duniya duk ya isheshi gashi ba sch balle ta tambayi qawayenta da ya saba ganin su tare gashi shi bashi da number din kowa. Gidajen yada labaru washe gari ya kai cigiya gamida police stations yini daya tak duk yabi ya fada kana ganinsa kaga maras lafiya idanunsa duk yayi tsuru tsuru hankalin hayarsa gabaki daya ya gama tashi gashi tambayar duniya yaqi fada mata meke damunsa. Inma ta tambayeshi sai dai yai dariya yace haba hajiya nifa wallahi gaskiya na fada miki ba abinda ke damuna kedai kawai kike ganin na fada anman garau nakeji na. Mahfux ne zaune wani abu ne yabi ya tsaya masa arai ya kuma kasa gane dalili bakuma komi ke damunsa ba yadda yaga Abbakar gabaki daya ya kasa zaune yakasa tsaye yana wani nuna yafi shi jin zafin bacewar ummu yarasa dalilin Abbakar nayin haka. Yanke shawara yai na yaje yasameshi ya fada masa me yasa yake abinda yake kan bacewar masoyiyarsa. A qofar gida ya sami Abbakar yanajin radio ganin mahfuz yasa yasaki fuska gami da kashe radion sin gaisa gami da qara jajanta wa juna batan ummu. Maganar da mahfuz yai ne tai mugun baima Abbakar mamaki cewa yai Wai Aminin mene naka nawani ishisshirewa wajen nemo ummu jibi yadda kabi kawani jeme wanda duk ni ya kamata inyi haka matsayina na masoyinta me shirin aurenta. Dariya Abbakar yai masoyi manya ka mance ni kuma masoyinka ne aini me damuwa da abinda ka damu dashi ne mahfux ya washe baki hakane fa. Kuma banda abinka mahfuz ka mance ummu frnd dina ce da muka shaqu achat ko ka mance aiko dan shaquwarmu na damu ko mahfuz ya daure fuska bai shiru ba ya qara da cewa kuma kamance ita student dina ce wadda ada nasota kamar raina naso aurenta. Cikin fushi mahfuz ya miqe kai malan dakata bansan rashin mutunci haba dole ka damu mana tinda abar sanka ta bace Abbakar ya miqe gami da dafa mahfuz haba Aminin bakaji nace Ada ba yaje tsaki gami da ture hannun Abbakar din ya qara da cewa to tsaya kaji wallahi kama cire ta aranka inba haka ba zan rufe ido na cire amintar mu wallahi in cima mutinci kai barifa kaji akan ummu zan iya kawar da mutun wallahi. Ido kawai Abbakar ya bishi dashi yakasa cewa komi ganin yadda mahfuz ya mance da shi waye dinsa kan mace yahau ci masa mutunci. Atsaye ya barshi soro ro kawai yana kallon ikon Allah. Ita ko ummu sun hau dan sahu kan yakaisu tasha suna cikin tafiya ummi ta dubi ummu tace auty zuwa qauyenmu da matsala ta dubi ummin me yasa. Cikin kuka take magana wallahi in mukaje koro mu zasuyi me yasa sabida ummana bata gidan Abbana sai abinda umma rahane ta ce masa ita tasa aka kawoni ma aikatau shiru kawai ummu tai tama rasa abinda ke mata dadi. Can ummi tace sai dai mutafi magarya inda ummana ke aure ummu batasan sanda ta rungume ummi ba ta farin ciki. Me dan sahun har ciki yakaisu shi ummu ta roqa ta baima kudi ta kira farida ta bashi kan shine nasir kasantuwar tana bacci yasa bata dauki murya ba. Dubu hudu ta bashi yaita godiya suka shiga motar da sukaji tana kiran babura magarya saura mutun biyu da sauri suka shiga. Mota na shirin tashi tacema kwandas dan Allah ga dari biyar tukwici ga kakarbi wannan kasiyon sim da kati na sauran canjin ba shiri ya amsa ya tafi. Bai jima ba ya dawo dauke da sim da kati ta amsa tana godiya gami da cire na kan wayarta tasa sabon. Goma dedai motarsu ta tashi dan barin kano wani hawaye ne ya tawowa ummu dan gabaki daya bata taba zaton kwai rana irin wannan da zatazo mata ba ace wai ita take shirin guduwa tama koma wata qasar ba tare da sanin koma nata ba tunda magarya Niger ce wayyo ni ummu naga rayuwa........... Sunyi nisa sosai a mota masu bacci nayi masu kalle kalle nayi cikin masu kalle kallen harda ummu gabaki daya ji take ranta babu dadi ji take kamar tasa motar ta tsaya ta sauka. Duda kasantuwar garin yanayin sanyi gashi dare ne kukan tsin tsinye kawai kakeji gwanin dadi sai dai ita gun ummu ba abinda ke mata dadi baccin ma kwata kwata batajinsa juyawa gefenta tayi taga ummi nata sharar baccinta ta kalli hannunta inda danta ke maqale a qirjinta shima baccinsa yake har yana dan murmusawa akaro na biyu da tausayinsa ya cikata. Tun randa aka miqo mata shi cikin zanin goyo randa ta haifeshi bata qara jin tausayinsa irin na yau ba aranta take qara tausaya masa koya zai tsinci rayuwa inya girma ko zai iya jure qalubalen dake gabansa wata kwalla ce ta zubo mata tai saurin gogeta duda kasantuwar motar da duhu ba wani zaiga hawayen ba. A dai tashar babura suka yada zango inda da yawa a tashar zasu kwana dan daya tayi suma motarsu anan zata kwan kafin gobe ta tashi zuwa magarya. Ba haka ummu taso ba taso cikin daren nan subar Nigeria sai dai ba yadda ta iya duda hankalinta bai yi zaton wani zaiyi tunanin suna jigawa ba balle azo babura nemansu hakan yasa ta dan samu damar yin bacci. Da safe kafin mota ta tashi da yw na cikin motar tasu anan babura zasu sauka hakan yasa sai anyi lodi ummu barin ummi da Abbakar tayi ta fita dan nemo musu abinda zasu ci. Sai da taje ta ciro rabin kudin account dinta ta sayo kaya kala hudu duda ba wasu masu kyau bane sai dai sun fi babu. Sha daya dedai ta musu agarin seda suka hau mashin yaqarasa da su. Yanayin garin ba qaramin firgida ummu yaiba qauye ne sosai ji take daqyar zata iya rayuwa a garin sedai babu damar komawa tunda ita bata da kowa wanda suke natan su sika fara gudarta. Ai kuwa innar ummi tai murna sosai da ganinsu mijinta baya nan ya fice tun safe sai mahaifiyarsa sin gaisa cikin mutunci musan da ummu ta bata tsabar biredin da tayo musu tai ta godiya. Malan tanimu shine sunan mijin innar ummi ko da ya dawo shima yai murna da ganin su ummun ba dan komi ba sai shima anbashi tsabar biredi harda madara yaita murna yana sa albarka duk ya mance da kishin da ya debo ana fada masa diyar matarsa ce tazo. Yau satin su ummu biyu a gidan har sun fara sabawa da rayuwar garin dan hat ummu tai qawa me suna mero sun saba sosai dan mero mutince me san mutane kullin Abbakar na gunta hakan yasa ummu qara santa abinka da uwa kunsan ance in kanasan abin gurin uwa to kaso danta. Yau malan tanimu mahaifiyarsa ta zugeshi tas hakan yasa ya fito yanata tafka bala'i yaha kiran ummu ita da ummi da gudu ummi ta fito riqe da Abbakar ahannu dan ummu bata nan mairo ce ta jata zuwa niyame dan canzo kudinta daga na nigeria zuwa na niger. Kayan su yake watsowa waje ni na gaji da zamanku a gida tun ina kawaici na fiskanci baku fuskanta ba haka kawai bani nai cikin kiba ki dawo min gida da zama to wallahi bazai yiwu ba. Kuka take tana roqonsa ya yadda ummu ta dawo yaqi ita kuma inna ta qi ko fitowa daga daki balle ta bashi haquri ya kyalesu azahiri ba qin fitowa tayi ba kasan tuwar ummi yar fari kuma da sanin halin mijin nata yasa taqi fitowa dan tasan in tai magana zai iya hadawa da ita ya kora. Ummu ce tai sallama ta shiga ganin me ke faruwa yasa ta shiga da gudu aikuwa ya daka mata tsawa cikin muryarsa ta buzaye dakata daga nan kubar min gida ynx ynxunnan durqusawa tayi tana kuka tana roqonsa kinga malama wallahi sai kun tafi kinjini ko......... Nigeria Yau watan ummu guda kenan da bata har sun koma sch inda zasu shiga level 4 su Aisha duk sun sauya kullin tunaninsu ko ummu na lafiya gashi sinyi sabo sosai da Abbakar dinta da sunga yaro sai suga kamar shi. Zaune suke suna tattauna lecture din yau dan ta musu wuya wayar maryam tai qara ta dauka wata qara ta saki tana fadin ummu me yasa kika gujemu da sauri Fatima ta amshe wayar danjin wace ummun ce. Ke banza wallahi wayarku bata da anfani inji ummu na

Chapter 6 of 15