inasan mijin kar abinne minshi wallahi zan zauna koda gawarsa ne wallahi.
Seda Hajiyar Abbakar tazo sannan ta tambayi ina Ummu se alokacin suka tuna da ita ba shiri sukai can bangaren da suka barta.
Tana ganinsu tahau kuka da sauri Nasir ya qarasa ya ruqo hannunta cikin kuka take tambayarsa mijinta yaja hannunta se inda Abbakar yake.
Kwanan Abbakar biyu a asibitun malan su mahfuz suka gama komi dan kaishi can qasar waje inda za'a kula dashi sosai duda suma nan din basu gajiya ba.
Da ummu aka tafi dan duk yadda sukai kan ta yi haquri ta zauna taqi.
Satinsu uku a india Abbakar ya farfado sedai baya iya komi se kallo da ido kawai.
Watansu biyu a india Abbakar yaji sauqi sosai jiki yai kyau komai yana iya yi da kansa sa6anin da dasaidai ummu tamai in bata kusa mahfuz.
Lokacin da yaji ummunsa nada ciki murna yai sosai harda dagata yana juyawa da ita tai saurin kwace kanta tana dariya tana fadin rufan asiri kaida baka da lpy da dai zan iya ai da na daga ka.
Shaquwarsu da abotarsu da mahfuz ta dawo kamar da koma fiye.
Daga india jordan suka wuce can gurin mahaifiyar ummu taji dadi sosai seda suka mata wata guda suka baro jordan zuwa Nigeria cike da kewa.
Lokacin da suka dawo Abbakar yai kyau yai qiba kaikace bai jinya ba cikin ummu ma ya dan fara fitowa.
Seda ta tabbatar ya ji sauqi sosai sannan ta kawo batun 6oye mata ciwon sa da yai wato be dauketa da mahin manci ba cikin kuka take magana jin kukanta yake har cikin ransa.
Ya jawota jikinsa yahau lallashinta dagyar tai shiru ummu ban boye miki ba nayi zaton na warke ai na fada miki ciwon qodar da nake.
Abin mata da miji yaita bata baki harta haqura kan alqawarin ya dena boye mata damuwarsa dan mahfuz ya fada mata yawan boye abu ransa da cunkushe damuwa ya jaza masa ciwon dan shima se ya takura yake fada masa meke damunsa.
Shi din mutunne da baya fadin abinda ke damunsa duk girman takaici yakan kunshe shi cikin ransa ne yaita in abu yai yawa ne yakan danyi kuka shima a boye.
Watansu biyar da dawowa ummi ta haifi yaranta yan biyu duk maza murna gurin uban gayya Abbakar bafa a magana.
Ranar suna yara suka ci sunan mahaifin ummu da na Abbakar suke kiransu da Walid da Amir.
Suna akai sosai bana wasa ba anyi gayya sosai.
Akullim inta kalli yan biyunta ta takalli tafkeken hotonsu dake jikin bangon dakin wanda sukai ita da Abbakar da babyn ta da ummi me rainonsa setaga kamar shine ahannunta banbancin kawai wannan biyu ne shi kuma daya ne.
Lokacin da rai arba'in har Niger sukaje ita da Abbakar da ummi dan ko bayan Rasuwar Baby Abbakar bata maida ita ba.
Sosai suka sami kar6uwa abinda ya baima ummu mamaki shine gani jarin fulawarta ya bunqasa ba wai yanzu iya magarya da zender ba state da dama na Niger kanzo siye buhu buhu.
Wajen miliyan biyar innar Ummi ta bata wanda tai tara tarawa cikin riba qin amsa tayi tace innar tasa ayi borehole da masallaci a unguwar dan lokacin data zauna agarin taga yadda suke matsalar ruwa tace sadaqatujjariya ga mahaifinta da kakarta da babansu mahfuz.
Sauran riba kuma tace in an samu araba biyu a ajiye mata daya daya inna ta dauka.
Qawarta Fiddo tayi aure har ya mutu bataji dadin gidan mijinba ummu ta tawo da ita dan ta cigaba da karatu a Nigeri.
Har can inda akama Abbakar masauki a niyame suka je sunyi murna sosai malan musa yace oh ashe zaka tuna damu bayan shekara biyar da tafuyarka Abbakar yai dariya na tafi cikin gaggawa bamuyi sallama ba zanso zumuncin mu ya dore sosai yai musu alkairi sukaita murna.
Ummu tuni ta gama degree dinta dan hartai masters lauya din da baban mahfuz yace dukiyarta nagunsa ma tuni ta nemo shi ta amshi komi nata gami da masa kyauta.
Kamfanin qere qere ta bude gami da tallafawa yara masu kwakwalwa duk yaron dake da fasaha ta qere qere ummu kan daukoshi musanman mara gata ta kaishi makaranta me kyau ta bashi aiki kamfaninta dan baje irin tasa fasahar in ka kammala jami'a inkaga zakai aiki da kamfaninta to in kuma bazakai ba takan tsaya maka dan samun inda kake so sedai bata ta6a tsayawa mutun dan barin nigeri da sunan aiki.
Tuni su Aisha sukai aure suma duk da yaransu zumuncinsu kuwa se abinda ya qaru.
Zaman Fiddo gidan ummu yasa suka saba da mahfuz dan yanzu yana zuwa gidan harsuyi fira da ummu dan itama ta saki jiki bakamar daba da take kullin cikin daure masa fuska yanxu ta mance da komi ta kuma yafe masa.
Ansha bikin Fiddo da mahfuz sosai iyayen fiddo sukaji dadi yayin da take BUk tana karantar BSC nursing, lokacin yaran ummu shida haihuwa biyar maza uku mata uku.
Muktar qanin Abbakar ma ya dawo ya zama kwararren likita yazama shi ke kula da asibitin da mahaifinsu yabar musu gado.
Maryam qanwar Abbakar kuni ta jima da yin aure harda diyarta mace tana da wani tsohon cikin.
Ummi ma qanwar Abbakar tai aure ta auri muktasir qanin Mahfuz zumuncinsu kullin qaruwa yake.
Ummu diyar wato ummi yanxu ana level 3 yayin da tuni suka dedai ta kansu da Ahmad amin ummu jira kawai ake ta kammala asha biki.
Zaman auren ummu da Abbakar abune abin sha'awa ga kowa koyaushe cikin san junansu suke sedai kunsan ako yaushe aka ce aure dole ana samun matsaltsalu nanda can anman in ma'auratan suka iya zamantakewa ba mejin kansu.
*Bayan shekara Ashirin da biyar zuwa da bakwai..*
Duniya ba gurin zama bace tuni Hajiyar mahfuz ta jima da rasuwa, itama ta Abbakar din tsufa sosai kullin gidanta cike yake da jikoki harda tattaba kunne dansu Nur din yaya babba sun jima da haihuwa.
Yau jikinta yaqi dadi hakan yasa sukai asibiti da ita sedai kansuje ta rasu kowa yaji mutuwar nan sosai su Abbakar harda kuka.
Walid dan wajen ummu tuni suka dedai ta da Shukra yar gidan Aisha bayan wata biyu da rasuwar kakar tasu aka sha biki.
Shima Amir yar gidan mahfuz yakeso basu wani bata lokaci ba akai nasu auren.
Fatima kuwa tuni ta jima da mutuwa qawar ummu da Aisha wata sch mate dinsu a buk sedai ta bar diyarta daya wadda ummu ta dauketa take kula da ita duda kuwa dangin fatiman sunso su hanata da temakon Abbakar suka bata.
Itama Kairat din ta girma ansa ranarta lokaci kawai ake jira asha biki.
*Bayan shekara goma sha daya.*
Ummu ce zaune jikoki sun ke wayeta na yaranta dana gurin ummi da na gurin kairat sun cikata da hayani kowa da abinda ke fade daga wancan yace gwaggo kinga wane ko se wancan yace gwaggwo a ina kika ajiye min kazana.
Abbakar ya shigo duk an tsofe kannan ya furfure dan tuni yai ritaya yaransu ke musu komi duda kuwa ummu nada kamfaninta se abinda yai gaba shima.yanada nasa anman basa zuwa ko ina kamfanin ma kula musu ake dashi.
Ya dubeta sweetheart wai yaushe yaran nan zasu tafi ne ta dubesu kowa da abinda yake tai dari se nanda.sati uku what ya fada aikam iyayensu zan kira kowa yazo ya kwashe dansa haba ni nagaji abarnima in hutawa tsofa na da mata ta se ankawon jikoki tai dariya mu lokacin da muke kaima hajiya me tace yai dariya ita daban ai.
Na'im babban jikansu dan wajen ummi ya dubi kakan nin nasa yace kajifa wai Sweetheart har tsoffi sunsan love, Fadila yar wajen kairat tasa dariya bari kawai yah na'im ko kunya basa ji.
Eyye kingani ko yarannan samana ido kawai suke dole su tattafi Husain dan gurin walid yace ta6 ai ba inda zamuje Abbakar ya cilla masa lemar hannunsa kaji mara kunya to dole ku tafi Usman dan qarami da befi shekara hudu ba yazo ya fada kan Abbakar yana dariya.
Nana ma ta fada kansa Abbakar yace kai nidai na banu ummu yasa dariya.
An koma makaranta kowa ya koma gidansu anbar Abbakar daga shi sai ummunsa zaune suke yana shan fura kamar yadda al'adarsa take ya dan jawota jikinsa sweetheart ta ce na'am my D yaushe za'a kuma bada hutu nai missing din yaran nan tai dariya se bayan wata uku yai dan tsaki kamin yace.
Kai duniya ba komi bace ada mu biyu muke zaune muka haifi yaranmu sun tafi se jikoki suma tanzu sun tafi ta shafo gefen fuskarsa haka ne my D qarshe ma mutun shi daya zai dawwama akabari to Allah yasa mu cika da imani tace Amin ya kuma riqeta sosai ajikinsa sukai dan shiru na mintina kamin ummun tace my D yace na'am tace nagode.
Me akayi u support me alot yai dariya duty nane matsayin miji no need ki godemin tai dariya inasanka mijina shima yai dariya inasanki nima Allah yasa mu rayu a aljannah tare amin my D.
Alhamdullah nan nakawo qarshen littafin Abbakar.
*Abin lura*
_*Arayuwa muna buqatar yafiya gami da mantuwa kamar yadda ummulkairi ta mance da abinda mahfuz yai mata suka ci gaba da rqyuwarsu cikin jin dadi_
_*Mutun baya taba wuce rabonsa duk rintsi seka ci abinda Allah ya tsaga shine naka sannan zaka mutu inka nema baka samu ba to abinnan tabbas ba raboknka bane kamar yadda Abbakar har ansashi a kabari sedai kasantuwar rabonsa aduniya be qareba ya dawo ya ci gaba da rayuwa._
_*mutane da dama suna fadin me yasa bansama littafin suna Nasir ko ummulkairi ba sedai ni ina ganin Sunan Abbakar yafi dacewa da littafin Abbakar mutun ne me sadaukarwa kamar yadda yake ganin zai iya sadaukar da sosayyarsa ga aminsa._
_Abbakar mutun ne me iya tankwara zuciyarsa kamar yadda lokacin da zuciyarsa ta amince kan yin masha'a da ummu ya tankwarata yaqi yi duda alokacin tanada dama anman be hakanba se yazama mutumin kamsa kuma ni aguri hakan ya kamata mu zama masu danne san zuciyarmu in ba dedai bane._
_Abbakar mutunne me haquri da sanin ya.kamata duda kasantuwar rashin mutuncin mahfuz gareshi lokacin da mahfuz din ya shiga matsalar asiri shi ya shiga ya fita seda yaga yazama normal._
_Duda kasantuwar ummul kairi nada yaro bashi yai cikin ba bakuma da aure ta haifeshi ba anman hakan besa da sukai aure ya wulaqanta ta ba sannan kasantuwar yaron ba nasa ba baisa ya tsani yaronba yaso yaron tun kan yai nasa dan._
_Tabbas da zansa sunan wani ba Abbakar ba to kuwa na Nasir ne dan akoyaushe muna muqatar tausayi da san yan uwa muna buqatar muzamto jarumai alokacin da yazamto mana na baqin ciki._
_Nasir mutunne me san yan uwansa kulawa dasu ako wanne hali duda kasan tuwar farida yakeso da yaga auren ummu zak iya sauqaqa mata lamarinta ya akiye buqatar zuciyarsa dan ceto yar uwarsa._
_Nasir mutun ne da duk girman matsala yakan iya tattara nutsuwarsa guri guda kamin ya tunkareta kamar lokacin mutuwar baby Abbakar da shi kansa Habu din wanda kuna kowa anso yazamto mutun mai jarimtar nutsuwa a kowa ne hali._
_Miqama Allah lammuranmu akoyaushe shi yafi dan babu me maka abinda be ma ba zuwa gurin bokaye ba namu bane musanman mu mata komi kike buqata tashi cikin darw ki nema Allah na kowa ne zai baki duk girman buqata in kuwa kika riqi wani sa zaki qare cikin nadama kamar yadda Hajiya Batul tai._
_Kishi da yassada ba namu bane musanman kan yara inba haka ba zasu kaimu su baro kamar yadda suka kai Hajiyar mahfuz da shi kansa Mahfuz din danshi sharri dan aike ne in yaje ya dawo kan ka ke koma._
_Duk girman matsala in mukai haquri akwai sauqi kamar yadda ummu da tai haquri komi ya zamto labari_
*Godiya me tarin yawa ga duk wata ko wani da suka karanta fatan kukkuren da ke ciki za'a min afuwa ajizanci ne na dan adam.*
[1/13, 4:32 PM] 🅰️ " AXEEX✌🏻 D'🅱️🅾️Y😎: _POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 15 Chapter of 15