Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚 [1/13, 4:22 PM] 🅰️ " AXEEX✌🏻 D'🅱️🅾️Y😎: *ABBAKAR* *PAGE 160---170* Mahfuz yakai hannu ya amshi yaron tuni kotu ta hargitse da hayani kowa na fadin albarkacin bakinsa domin yau kotun ta cika sosai da yawa cikin mutanen kotun abu daya suke fade yake kuma basu mamaki wato wannan wace irin alqaliya ce wannan zalunci ne. Maganar da alqaliyar ta fara ne yasanya kotun fara yin shuru kafin daga bisani kuma tai shiru. Yanzu daman innace ka amshi yaron nan saika amsa ya kalli alqaliyar da mamaki, ina kai musulmi ne ko baka da labarin in mace ta haifi yaro a muslunci batare da aure ba yaron nata ne bana wanda yai cikinba. Kai wane irin azzalumi ne da har zaka ma yarinya fyade ta haihu kakuma zo ka kawota qara ko dan ita batasan haqqinta ba ta gaza kawoka qara. Wato kazo nan aqwace yaro abaka ko kai gaka uwa da uba na doka ko to abaka shi kamasa me ka kasheshi ko yai saurin kallonta da mamaki fiye da dazu eh mana kanasan karbar sa ka kasheshi dan karya girma ya zargeka da rashin kawoshi ta hanya dedai. Mahfux cikin fishi yake magana Haba malama wannan ai bayi bane zaki dunga mun sharri kawai dan kina alqaliya tsawa ta daka masa kai malan kasan a inda kake kotu ba sa'ar wasan ka bace. Sakamakon samun wanda yake qara da rashin ta ido da kotu saka makon haka kotu ta bada dama a sakaya shi nanda wata guda sannan yaro na mahaifiyarsa ne kotu ta masa katanga da yaron indai ba mahaifiyarsa ta yarje yaje gunsa ba. Duk yadda yan uwan mahfuz sukaso kar yai firxin na wata guda abin yaci tura dan alqaliyar iya wuya yazo tace da a qyaleshi gwara ta bar aiki. Har gida alqaliyar mai suna Salma tazo ta sami ummu tasamu karba ta mutunci sun gaisa da hajiya kamin ta fara bayaninta. Indai kun amince ni zan tsawa ummulkairi ta kai yaroncan qara kan cin zarafinta da yai na keta mata haddi tunda duk wata shedu munadasu na zaman kotun da mukai. Kafin hajiya tace wani abu ummu ta dora a'a ni zaman yarona agurina wallahi ya fiyemun komi na riga nakai shi qara gurin sarkin da baya zalinci nakuma san ko aduniya ko alahira zai saka min nagode sosai aunty sukai sallama ta tafi. Hankalin hajiyar mahfuz yafi na kowa tashi gashi gobe daurin aurensa abin haushi dik gidajen radio da tv sun nuna shi sakamakon rashin mutuncin da yai akotu balle tace ko tafiya yai. Ban garen gidansu amarya basu wani ji komi ba dansu burinsu kawai su aurar da salma gama ko wane ko sa samu su huta da halinta, itama bangaren Amarya bataji komi ba saima murna da tayi na rashin bashi shegen dansa dan mum dinta ta fada mata irin son da yake masa shi yasa tun kan tashiga gidan kishin duniya ta dora kan yaron, na biyu kuwa ta samu abinyi in ya mata gori zata rama da cewar ai gwara ita bata taba bursinba. Mahfuz duniya ta masa zafi ba abinda yake tunawa sai sa'adda police suka saka masa ankwa Abbakar yasa hannu ya amshe takwaransa dake hanunsa ya miqawa ummu. Gabaki daya yai baqi ya rame danshi mutunne da bai saba da wahala ba bakuma yasanta ji yake wata guda dinma taqi qarewa ji yake kamar shekara ce zaiyi ba wata ba. Sanye taje cikin baqar abayarta mai adon ja ta nada mayafin abayar akanta sai yar jaka mai dauke da littafanta gudu uku kacal ita ma jace sai dan duwatsun baqi jikinsu takalminta mai sauqin nauyi tai kyau sosai. Ummu kenan wadda ko wacce kwalliya tai tana mata kyau musanman a idan Abbakar wanda yanzunma tunda take saukowa ita da ummi qanwarsa yake binta da kallo gashidai shiga iri daya sukai anman gani yake ina ummu ai babu ya ita. Ummu doguwa ce bacan ba komi nata me kyau ne ita din bata cikin fararen fata bakuma za'a kirata baqa can ba tanada dai duhu irin na yan Nigeria wato duhunta me kyaune fatarta ma me kyauce idanunta yan madai daita wanda hancinta da baqinta sun dace da yanayin fuskarta kana kallonta zaka san ta hada jinsi da larabawa ko ka kirata irin fulanin asalin nan kamarta daya sa babarta saidai ita batayo hasken babar tata ba. Sai da suka zo dab ummi ta tabashi yah munata gaisheka bakaji ba ya dake irin karsu gane ita yake kallo yayin da tuni hajiya ta rafkoshi yace oh banji ba inadanjin bacci ne, ina zuwa haka zamu sch ne ok to ku jira in kaiku ya fada gami da miqewa. Ajikin motar suka tsaya yazo ya bude duk suka shige baya shima yai zamansa agaban motar yaci gaba da daddana wayarsa yayinda lokaci lokaci yake satar kallon ummu. Ganin bazai tafi bane yasa ummi qanwarsa cewa yaya muje ko ya juyo ya watsa musu harara baki dayansu muje ina? sch mana kai kace zaka kaimu ai, nace dai zan rage muku hanya ko suka kalli juna ita da ummu shi kuma ya ci gaba da danna wayarsa. Ganin da gaske bazai tafiba yasa ummu daurewa tace pls sir karmu makara asanyaye tai maganar yadan kalleta watoma agidanma kallom wancan lecturer din nasu na thermodynamic take masa yace au ai nazaci baku shirya tafiya ba ummu aranta tace lallai mutumin nan dan rainin hankali ne bamu shirya tafiya inba zamu shiga mota ummi ta miqe daga bayan ta koma gaba. Ko rufe qofar taiba ya tada mota ta jawota suka tafi, ummi ya fara saukewa a old campus dan zatai wani abu yaja yai tsawarsa ganin yana bata mata lokaci yasa tace pls dan Allah sir mu tafi. Ya leqo gidan bayan ni direbanki ne ya fada yadda yai yamata kwarjini hakan yasa ta fito ta shiga gidan gaba yaja suka tafi. Adai dai faculty insu ya paker ta bude kamin ta sauka ta juyo tace thank you sir ya ruqo hannunta da sauri ya juyo ta kalleshi ba sunana Sir ba, nakuma sanda kinsan da hakan dan haka akiyaye ya saketa tai waje dasauri. Su Aisha ta gani can gefe suna sheqa dariya harda tafi iyye kaga masoya wato abin har yakaiga adinga kawoki inkuma ankawoki a zauna a mota a kwashi love ta turo baki to 'yan sa ido masu zuwa lahira da qoqom danbu anayi kuna irgawa to ya ranku. Ahmad yace ransu fes birgesu kikai shi tasa suka kasa shiru Hafsat takai masa duka da littafinta kaifa dan is ne ah kinga yarinya dena iskantani da mutunci na har yanzu suka saka dariya baki daya. Yau kwanan mahfuz uku kenan da fitowa duk yai baqi abinci ma ba wani da dinsa yakeji ba kawai dai yana daurewa ya cine dan kan abin ya masa yawa ga yunwa ga rashin dansa. Ganin ya kwan uku ne bai maganar matarsa ba hajiyarsa ta sameshi adakinsa yana kwance da alamu tinani yake tace mahfuz magana nazo muyi ta Fahinta ya dago gami da jin gina da gadon to hajiya inajinki. Maganar matarka ce Naga tunda ka dawo bakamin maganarta ba adan razane ya kalleta mata kuma hajiya eh matarka danshi a zahirin gaskiya yama mance dawai za'a daura masa aure balle yasan an daura. Haba hajiya da wanne zanji da auramin wadda banaso ko kuwa da kwacen yarona da akai ta daga masa hannu kaga ni yimun shiru kai inbanda butulci naka yarinyar duda sanin kana da yaro shege ta yadda ta aureka kace aura maka ita tashin adalcine kai inbanda amincin dake tsakanina da uwatta aikasan kamin kasamu me aurenka saika shirya. Dan haka ina baka umarni kayi maza ka hada naka yanaka ka koma gidanka na court road dan can nasa aka kaima ita idanunsa sunyi jawur rannan abace ya miqe ya hau dibar kayansa. Ko sallama baima Hajiya ba ya fice daga gidan danshi yanzi haushinta yakeji gani yake ita ta cuceshi data sangarta shi ta nuna masa komi yayi dedai ne gashinan tasa yaje yai abinda sakayyarsa ke neman haukatashi. Gidansu Abbakar Yau shirye shirye suke sosai dan har su Nurat sunzo aunty zainab ce zatazo dan ganin amaryar yayan nata dan ita batasanta ba. Lokacin da tazone aunty zee tasha mamaki qanwarmu ashe kece amaryar tamu ummu ma ta mamaki aunty zee daman ke yar nance eh aure yakaini katsina kowa yai mamakin sanin juna da sukai. Aunty zee ta dubu Hajiya umma ai nasanta qanwar Yah Nasir ce kuma qawar Farida qanwar salma wato qannen mijinta Hajiya tace ikon Allah. Da yake duk gida daya suka zauna da su salman yanzu ma tare suke ra Farida ummu tai dariya kawai Abbakar yace a'a yanzu ta dawo nan daiko suka saka masa dariya baki daya. Zainab ta dubi ummu waiko in tambayeki ummu ta zuba mata ido alamar inajinki, Yah nasir kuwa ya fadawa Farida yana santa ummu tadan dubeta wato itama tasan yanasan Faridan a'a tace. Kai yaya Nasir da zurfin ciki yake wallahi tun yarinyar nan fa na Jss yake fama da santa yasha fadan yadda yakejin santa aransa anman ya kasa fada ai shikenan nasan me zan masa. Suna gama cin abinci ta kira Nasir din awaya Yaya na nafazo garin naku eyye watoma garinmu ko to ganinan zuwa gidan naku. Sun sha fira kamin zainab tace daman jaje zanma bikin Farida ya gabato sauran wata uku what ya fada yana miqe ina wallahi bazai yiwuba farida tawa ce ni daya. Yai waje zainab ta bishi a baya sedai kamin tazo ya fice a motarsa ita dai hankalinta duk atashe kar yaje yai wata baran baramar. Kai tsaye gidan Farida ya wuce ya dade baije ba dan yanzu ita kadaice hakan yasa gudun shedan ya rage zuwa duda ta ce masa qannenta uku sunzo mata hutu baida niyar zuwa. Kullin cikin kiransa take awaya ko a sch nunawa yake baisanta ba yama hanata zuwa office dinsa gabaki daya. Kai tsaye gidan ya shige yana kwala mata kira Basira na shanya tasanshi hakan yasa bata tsorata ba se ce masa datai tana ciki. Da gudu Farida ta fito yah lafiya kuwa cikin kwalla yake magana yanxu Farida kin kyauta min kenan kinsan da ke daya nakeso a duniya shine zakiyi aure ki barni ta kalleshi yah ban gane me kake magana akaiba yaushe muka taba maganar soyayya dakai. Ko kuwa nace inasanka ne what eh bakice kinasona ba anman aikin nuna ta zaro ido ni wallahi a'a kawai irin kulawa da wa da qanwarsa ce . Oho ke kika sani ni kawai abinda nasani ke din matata ce kuma dole koma wazaki aura a fasa ayi dani cikin dan murya me qarfi take magana wai yaya wane aure kake magana yaushe nace ma zanyi aure. Wayarsa da tun dazu ke ringing ya daga bema duba ko waye ba ya amsa muryar zainab ce cikin muryar kuka take fadin yah wallahi da wasa nake tsokanar ka kawai fa nake ba wani aurenta da aka saka. Kunya duk ta kamashi sun sun ya fice yabar gidan Farida na kiransa yai gaba ita dai tasan yaya nasir baya shaye shaye dasai tace ko ita ta fada masa qarya. Gidansu zainab ya koma anman kin gama dani kinsa nayi abinda banniya ba tasa dariya to ai kaga na temakeka kaidinne inata ka tsaya katsaya kai gaba ummu tai dariya ke kuwa aunty zee yaji zuciyarsa zata tafi gidan wani yace eyye kema harda ke ko suka saka dariya Abbakar mamaki yake daman tana magana da dariya haka. Gidan Mahfuz Duk ransa abace ya shiga gidan sai dai me yana shiga yaji yamanta komi ba abinda yake sai burin ganin matarsa ko rufe murfin motar baiba yai ciki ita kuwa gwanar daman su suka tunzuro Hajiyarsa ta koroshi dan tuni ko wanne aiki da bokansu ya basu sun kammala. A tsaye ya hangeta da wata arniyar shigarta suna hada ido wanda yaci kwallin boka yaji ya kasa koda motswa zuwa tai taja hannunsa sukai ciki gurin dinning area ta kaishi ta zuba masa lemon abarba da yasha magani ta miqa masa ya amsa ya hausha saida ya shanye ta zuba masa abinci yaci yai nak. Komi ya tafi yadda suke so dan basu wani sha wuyaba asirunsu ya kama mahfuz dan shi din ba gwanin ibada bane . Mahfuz ya zama kamar wani sauna sai abinda matarsa ta fada masa yake ta zama kamar itace mijin shi kuwa irin baiwar matarnan danma bazamu kirashi matarso ba. Rabonsa da gidansu tun randa ya baro sati biyu kenan ko wayoyinsa matarsa ta kashe cewarta ita bata gama cin amarcinta da angonta ba aiki ma dan dole take bari ya fita shima sai yasha kashedin in ya dade ko ya kula wata shi da ita ne gabaki daya tsoronta ya gama rufe zuciyarsa. Gidansu Abbakar Zainab ce tsaye suna magana da Hajiyarsu umma wai yaushe ne Amaryar zata tare nama yaya magana yamin shiru Hajiya tace se randa ya shirya inkuma be wasa ba wallahi sawa zan yasakar min ita tunda naga baya santa inyaso na bata sulaiman kai hajiya kema kinsan yah nasanta sulaiman da tunda ya taso yake qasar waje ai bazai yadda da auren dole ba au haka kika ce zakusha mamaki tai dariya kawai sikai sallama suka tafi. Soyayya tsakanin Farida da Nasir kamar sa hadiye junansu ko yaushe suna maqale awaya ko yana gidansu Abbakar dan tuni Farida ta dawo gidan da zama. Magana tai nisa aure saura wata guda duda farida taso sai tana level five yace shikam ya gaji da yaquri tanaji tana kallo ya mata fun qarfi. Rana bata qarya yau laraba ake kamun Farida su ummu ne manyan biki duda kuwa gogon nata baisan budirin da take ba dan ko ta kanta baya bi qarqari yazo ya dauki takwaransa girin hajiya su fice yawo dan yaron ya saba dashi sosai. Yau zasu wuce kaduna dan acan za'ai bikin dagyar hajiya ta barsu sun fito da akwatu suna zubawa a bayan mota ya shigo da motarsa idanunsa kansu yai parking ya qaraso. Ku ina zakune haka kuke jidar kaya cikin sauri ummi tace yah ka mance bikim yah Nasir to nan nan din sekun dibi kaya kai yah Kaduna fa zamu. Me kaduna ku ai yan uwan angone ba inda zaku munfa tambayi hajiya ya doka mata harara zaki matsa ko sai nai ciki dake tai cikin gida da gudu tana kuka ummu ta huro baki gami da qamewa wajen. Eyye sannu mara mutunci wayo ke bazaki bar gurinba ko tai masa banza wallahi ki kiyayeni ta kiyayeka ko kai ka kiyayeni. Hajiya ta fada suna fitowa da ummi kuma biki ne se sunje haba hajiya dan Allah nifa mijin tane anman kin hanani matata kuma kina nunan iko kanta ai inzata fita ya kamata ta tambayeni. Haba hajiya ta riqe iyye sannu me mata kai inkana da kunya kace matarka ce ka taba bata kwayar shinkafa eyye. To anman hajiya ai baki kawota gidana kinga na kasa ba me kace yace bakomi cewa nayi se sun dawo yai ciki hajiya tace dan nema ashe rashin kunyar qarya kake. [1/13, 4:22 PM] 🅰️ " AXEEX✌🏻 D'🅱️🅾️Y😎: _POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚 [1/13, 4:24 PM] 🅰️ " AXEEX✌🏻 D'🅱️🅾️Y😎: *ABBAKAR* *PAGE 170---180* Duda ummu taji dadin shigar mata da hajiya tayi can qasan ranta bata ji dadin zatayi tafiya me nisa ba tare da izinin mijinta ba duda shi din bai nuna wata kulawa na shi din mijin ta ne. Yau take daurin aure cikin wadanda sukazo kaduna har da Abbakar tunda suka iso yake baza idanu ko zaiga ummu amma bai ganta ba ko ya manta da mata basa fitowa gurin daurin aure oho. Su ummu se hotuna ake sha da angwaye wadanda suka shigo cikin gida bama tasan da zuwan Abbakar ba tai kyau sosai kai kace itama din amarya ce. Ummi qanwar Abbakar taxo ta riqota madan yaya fa zai tafi baku ko gaisa ba balle kuyi hoto ta dube ta wane yayan, Yah Abbakar au yazo ta fada eh to shida yazo be nememu ba se mu zamu nemeshi, ta dan dafata haba tawan ki daure badanshi ba danni to kije kisa ya shigo se muyi photon pls ummu ki temaka danni kije ki kirashi ummu tai jim kamin tace amman ummi..... Bata qarasa ba ummi tace pls harda dan rissinawa. Sai da ummi ta rakata har zaure ta tabbatar ta fita farfajiyar gidan sannan ta juya cikin gida. Ware idanunta ummu ta shiga yi dan su bata ikon hango ko gani Abbakar cikin dan dazon mazan da ke gurin. Baba mahmud da wasu yayun babanta ta hanga da sauri cikin murna tayi wajensu ta durqusa har qas ta gaidasu babu wanda ya ganota dan an riga da anmusu asirin farraqu nasu mance da ita da shafinta. Baba mahmud ne yaso ganota sai dai ya rasa inda yasanta kawai dai yanaji ajikinsa kamar ita din jininsa ce sosai suka gaisa taji dadi dan zatonta sun ganeta Baba mahmud harda zaro kudi ya miqa mata gashi a qara a hidimar biki ta amsa tana godiya duda bataji dadin rashin tambayarta ina take ba ko me yasa tabar gida. Shiko gogon nata kamar ance ya kalli qofar gidan idanunsa akanta kishi ne ya rufeshi ji yake kamar duk gurin kalle masa ita suke yayin da ya kasa dauke idanunsa akanta. Jikinta ya bata ana akallonta hakan yasa ta maida idanunta inda take zaton tanan ake kallontan hangensa tai jikin motarsa shida wasu su uku tai saurin qarasawa. Batasan me yasa ba lokacin da taje daf dashi ta tsinci kanta da yi masa murmushi, shima din ganin murmushinta da in ba daga nesa ba tanaima wasu bazaice ta taba masa ba ji yai kamar su kadaine awajen ya hau mata murmushi duk ya nemi fadan ya rasa. Yah barka da safiya tace barkanki dai daman naga baka shigo bane shine nazo in kiraka kazo muyi hoto da angwayen. Hoto kuma eh a'a ni gaskiya ban iya hoto ba balle cikin mata pls yah tarihine tai maganar cikin wani salo dama batasan tayi ba yayin da shi kuma baima sanda yace muje ba, tana gaba yana biye mata baya har suka isa gidan. Sunyi hotuna sosai wasu shida ita dasu ummi da su Nasir din ji yake dama ranar aurensu ce shida ummunsa da yafi kowa jin dadi har ya juya zai fita ummi ta tawo da gudu riqe da Abbakar qarami yah bakuyi dashi ba tace ya amsheshi ya tsaya za'a daukesu su biyu ummi ta tura ummu kuyi tare tarihine, su uku me hoton ya dauka ita Abbakar da takwaransa sunyi kyau sosai. Duk yadda akai da Nasir ango ya yafi yaqi yace ina shifa sai an bashi amaryarsa dole dole ya tsayar da Abbakar kan ya bari zuwa qarfe uku sai su tawo in andauko amarya. Su hudu ne cikin motar Abbakar keja ummu agaba azaune sai ango da amarya, Hirar ummu da Yah nasir da Amarya kawai kakeji yayin da Abbakar tuqinsa kawai yake dan bashi da ta cewa sai in Nasir ya sako shi ciki ne yake dan tofa tasa. An kawo amarya gidansu Nasir aka fara kaita ummu bata shiga ba a aqofar gida ta tsaya cikin motar Abbakar yai yai da ita kan tazo su tafi gida taita roqonsa ya bari ta kai amarya shi kansa mamakin kansa yake me yasa komi tace yake amin cewa uhum Abbakar kenan wato bakasan power of love ba kadan ma kenan. Su Farida se wani kuka take tun shugarsu har fitowarsu se kace ba ita ce dazun suketa kwasar fira a mota ba. Sun shiga kamar dazu ummu a gaba ita abaya sedai angon be shigo ba shima Abbakar yana daga waje ummu ta leqo ke mu dallah ki mana shiru ai kin fito daga gidan sirikan da kukan naki zai yau dara, Farida ta daqa mayafin gami da dan shan mur. Ke nice dallah din maza ki nitsu yanzu ni yayarki ce tunda ina auran wanki ummu tace ayi haquri aunty gyanbo sarkin san girma suka saka dariya baki daya, Ummi ta leqo ta taga anti Farida pls ki dena surutu ko yaya Nasir yazo kinga in kina magana ai bazamu samu kudin siyan baki ba kidan daure kiyi shiru awa daya ne kawai munje mun tafi, Farida ta kai mata duka ta jikin taga tasa dariya tai gefe. A mota ma da Nasir ya shiga kuka ta cigaba da yi abinta shiko yahau rarrshinta haba tawan ki daure kiyi shiru kar nima kisani kuka ko kunyar su ummu baya ji harda wani jawota jikinsa yana lallashe ita kuma taqi magana se shessheqar qarya take tana kuma lafkewa, ummu tai gyaran murya gami da daga waya tana fadin ummi albishirinki anbi umarninki ki shirya karbar masu kauri Farida tace to mugaye ce miki akai.....bata qarasa ba ummu tasa dariya maza ki tonawa kanki asiri itama tasa dariya. Ankai amarya da yake ba wani qawayen azo agani take da ba su ummu ne sai wata aminiyarta da suke buk tare su ummi sarkin san kudi tun aqofa ake radawa Farida kartayi magana intayi kuwa gidanta bazata dinga zuwa ba, ansamu abinda akeso dan dubu hamsin Abbakar ya lale ya bada dan Nasir din tun safe abokanansa sun tafi sai Abbakar din din da mansur duda duk qannene ga Nasir din. Duk masu rako amarya na kaduna wato yan uwanta a gidansu Nasir zasu kwana hakan yasa su Abbakar na fita ya dubi ummi yace to lashe money se a yunqura ayi gaba ko tace lah yah kora yace wah ni ban koreku ba kawai dai ta miqe bari to muje kar akoremun da dai yafi inji farida ta kamo kunnenta ta fada mata kai aunty Farida. Nace su Yah Nasir seda safe su farida uwar rawar kai kuma uhum to ba wani abin zance ba ita ma din seda safe ne asha amarci lafiya. Zaton ummu yah Abbakar ya tafi sai dai tsaye ta ganshi jikin motarsa ummi tai kamar bata ganshi ba ta shige motar mansur ita da wasu qannensa. Ummu ma tazo shiga taga ta cika ta dawo gurin Abbakar din bai ce mata komi ba ta bude ta shiga gami da kwantar da Abbakar dinta a baya. A dedai inda zai kaika ga bangaren da zai kaiga bangaren hajiya ya parker kagaba kadan ummu ta da juya ta dauko Abbakar qarami dake bacci ta riqe qofa zata bude yai locking din motar gabaki daya gami da ruqo hannunta tai saurin kallonsa a tsorace cikin sanyin murya yake magana kai kace bashine wannan Abbakar din data sani ba me fada da tsare gida . Ummulkairi dan Allah su yaya Nasir basu birgeki ba tai shiru be damu da shirunta ba ya kuma Fadin yaushe zamu tare muma anamu gidan ta kalleshi gida eh gidanmu........ Gidansu mahfuz Hankalin hajiyar mahfuz ya gama tashi musanman ganin anyi bikin Nasir an gama babu Mahfuz babu labarinsa tun tana tsanmaninsa harta dena hakan yasa ta kira number din matarsa danshi ko ankirashi akashe take.

Chapter 11 of 15