Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kasheka wallahi shine. Ala dole su hajia suka yadda tabbas Mahfux ya haukace hakan yada sukayi bail insa suka kaishi asibitin kula da kwa kwalwa. Duk wani bincike anyi anman ba'agano komi ba wato kwakwalwarsa normal take. Saidai yadda inyaga Nasir yake tuburan dole hajiya naji na kallo ta yadda ya haukace tasa hannu dan kaishi gidan kula damasu tabin kwakwalwa. Duk halun da ake ciki Abbakar baya da labari sai yau hankalinsa ya tashi danshi be yadda Mahfuz dinsa ya haukace ba. Kai tsaye asibutun ya wuce aikuwa mahfuz din naganinsa yahau kuka tausayinsa ya cika Abbakar yadda kwana biyu kawai yaga mahfuz din duk yai baqi ya rame kamar bashi ba. Ya hau rarrashinsa dan Allah amin kaje kacewa hajiya wallahi da hankalina Allah van haukace ba kai nasan zaka yadda. Yadda yake maganar yaqarama Abbakar kwarin gwiwa tabbas Amininsa da hankakinsa wata maqirqisa kawai aka shirya masa. Naji nayadda da hankali anman garin yaya me yafaru har aka kawoka nan ya bashi kabarin komi tabvas raina musu hankakin da yarinyar nan take ya isheshi yau zai maganin komi dan yanasan abokinsa yanaji yana gani baza'a mayar masa da Amini mahaukaci ba. Ya kwantarma da Mahfuz hankali kafin yq fito daga gidan masu rangwamen hankalin. Kai tsaye gidan Su mahfuz ya wuce baibi ta ko inaba yai bangaren hajiya abinda yake ba sabonsa ba shiga cikin falon gidan kai tsaye. Yai sa'a tana falo suka gaisa kafin ya mata jaje ya dora da fadin yanzu hajiya kina kallo za'a maida mahfuz mara hankali vazakiyi magana ba. Tai dan murmushi Habu kenan ai ba maidashi akaiba ya haukace din ne wallahi hajiya be haukace ba da hankalinsa haba dannan taya zakace be haukace ba mutumin da yake iqirarin kashe dan uwansa agabana fa. Yana ihuuu yana shine ajalunsa yace yai aure alhalin qarya yake masa yace yaganshi alhalin bamashi bane bakajin wannan duk ba alamomin hauka bane. Wallahi hajiya shi yagani tare muka ganshi taja tsaki daman ai abokin barawo barawo ina yabonka ashe kaima ka fara shan qwayar da yake sha nasan itace ta fara tamvayarsa inzaka tashi katafi to inkuma ansn zaka kwana sekayi tayi tamiqe tai sama dan wallahi kaima ban yadda dakaiba kar inje a afkamin. Ya miqe yabar gidan takaici fal cikinsa. Gidan da sukaje da mahfuz yai inda sukaga Nasir da ummun. Yaro ya aika amasa sallama da me gidan yaron ya fito wai baya nan can saigata tafito. Wake nemansa yai saurin dagowa daga daddanna wayar da yake dan ko a ina yaji muryarta sai ta gane nine ta fada. Tace oh baya nan sedai inzaka jira ok va matsala yace ta koma ciki. Ya kusa minti goma sha biyar mutumin ya parkee motarsa qofar gidan ga mamakin Abbakar ba Nasir vane anman yadan daurewa mamakinsa barka sannu ko yawwa kai kake nema na eh nine ok muje daga ciki ko suka shige. Bayan ya shiga ya fito riqe da yaronnan da kodaga bacci Abbakar ya tashi saiya ganeshi dan tabbatar da abinda ke masa yawo arai na shakku yasashi miqa hannu kawoshi. Ya amsheshi dadinsa da yaron kwai fara'a ya sunansa nahfuz yace ataqaice Allah sarki Allah ya rayashi amin yace ya miqo hannu ya amshe abinsa. Nikam Kamar nasanka wataqil kwanaki dai munzo da abokina mahfuz oh naganeku kune yan iskannan masu shigarwa matan aure gidako yadan cige lebe dan yaji zafin kiransu da yan iska dayayi yaidai basar ehto koma me kakiramu ni ba hayaniya nazo ba nazone dan inasan yin magana dakai da matarka. Ya miqe a fusace what dan mene inbazaka iyayi dani kadaiba to mata tata haramin alaik no maganece ta fahinta nakeso muyi kan abokina da kuka haukatar. Kaga nafiskanci haka daikinyi pls tashi kabar min gida tun kan kadaga hankalin matata pls give me a chance wai baka ji me nace maka bane ko sai na hadaka da police na sassauta maka ne dan kawai na fiskanci kafi abokinka kamala. Abbakar ya miqe yabar falon but kasani zan dawo kuma time in da zan dawo dole in magana da matar taka hakan kuma shi zai kawo qarshen matsalar nan na fada ma to muza nidakai dan halak ka fasa inji mijin nata. Tunda yahau titi tunanin muhawarsu da mutumin yake yasan babu ta yadda zai iya magana da matarnan indai mutumin nan nanan but za'a iya kamashi inyaje ya shigar musu gida suka masa ihuuu gabaki daya tunaninsa a cunkushe yake ya rasa mafita. Sauri kawai yake ya tafi sch ko breakfast din kirki beba ya bar gida. Ko a office ma jira yai kawai takwas tayi ya wuce inda zaiyi lecture dinsa ta morning bayan ya gama yace wadda aka kawon complain bata da lafiya tazo yau for her make up ya fice be jira amsar student dinsa ba. Aikuwa kamar tare suke yana shiga ta shigo riqe da babyn ta yadan kalleta ya kalli babyn zaki iya zama tace taja tazauna yai saurin murda makullin office din gami da zareshi ya zura a aljihu jikinta ya dau rawa ta mike ta daka mata tsawa koma ki zauna kika ce tak kome ya faru dake ke kika jawo yado gabanta dab da ita tana kallonsa yana kalkonta yazauna har yana iya jiyo faduwar gabanta suka hada ido ya daka mata harara tai saurin kawai da kai.......... [12/31/2020, 5:50 PM] 🅰️ " AXEEX✌🏻 D'🅱️🅾️Y😎: _POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚 [12/31/2020, 5:51 PM] 🅰️ " AXEEX✌🏻 D'🅱️🅾️Y😎: *ABBAKAR* *PAGE 45---60* Cikin kuka take magana pls let me go I beg ur pardon dan Allah, mtss yaja tsaki au daman ke kinsan Allah ne da har zaki hada wani dashi munafuka kawai taisaurin dagowa hawayen da ya cika mata ido ya gangaro. Inkinga kinbar office dinnan to Wallahi kin fadan ke wace taisaurin kallonsa yes kinmaji na rantse sir bangane ba all i know am ur student kawai nop ba wannan nake san sani ba ki fadan mene alaqarki da mahfuz, Ni dakuma Nasir ni bani da wata alaqa dakai balle su ok kin shirya ma kwana ananko. Ya shige toilet ya dauro alwala gami da fitowa ya tada sallah bayan ya idarne yaci abinci ya miqo mata sauran inkinyi niya kyaci ya sa hannu ya amshe babyn hannunta ya koma inda sallayarsa ke shimfide ya kwanta gami da dora babyn kan cikinsa ya lumshe idonsa hankali ba qaramin tashi yaiba ganin la'asar na shirinyi dagaske bazai barta ta tafiba. Wata irin yunwa takeji abinka da me jego but batasan cin abincinsa dan bata yadda dashi ba yadda ta fuskanci yau din kamar a buge yake dan dazu da ya daka mata tsawa ta kalleshi taga idanunsa sun wani sauya launi batasan duk bacin rai bane kawai. Dole in samu mafita naji zan fada ma alaqata dasu inkamin alqawarin barina in tafi ok inajinki ya fada batare da ya bude ido ba balle nuna concern innaji bayaninki ya gamsar dani mai zai hana inbarki ki tafi. Mahfuz cousin dinane what ya fada gami da saurin bude ido ta gyada kai alamar da gaske take eh causin dina ne so Nasir fa ya fada. Tai shiru oh baki shirya tafiya ba kenan ta kada kai cikin hawaye mijina ne ya miqe a tsorace sauran qiris babyn ya fadi ya tallafeshi mijinki ya fada eh ta fada oh i see. Shiyasa kuka hada kai kedashi zaku haukatan aboki ko dan kawai san zuciyarku dan zalunci pls kabarni in tafi na amsa naka duk tambayoyinka dan Allah. Naji zaki tafi but baki gama amsan tambayoyina ba baki fadan alaqarmu ba sir ni bamu da wata alaqa da kai banma sanka va sai a Bayero. Karfa ki rainan hankali nasan me nake am 30 so kinga na fice kizo ki rainan hankali inkasa gano wa taya zakice baki sanniba bacin kinsan frnd dina if i can recall ke kika fara turon frnd requires sai yanxu na gane hakan duk yana cikin shirinku ne keda Nasir. Sir kayadda dani bansanka ba eh naji baki sanni ba anman taya za'ai da aurenki ki dinga chat da wani harki dinga baima mijinki ku gaisa da wanin inbaya shirinku. Sir in zaka tuna time in four years back muna chat but inka tuna bama na nigeria muna waya da kai inka tuna na fada ma i never being to Nigeria even though my Father's relative gaba daya suna nigeria na turo ma frnd requires ne dan kawai inasan yan nigeria naga kai dan nigeria ne. Yai dan tsai yana tunani yes yatuna ok yanxu zamuje ki fadama iyayen mahfuz abokina da hankalinsa kafin inbarki ki tafi ta zaro ido what eh. Hawaye ya gangaro mata haba sir ba haka mukai dakai ba pls let me go kazamto me cika alqawari any way zaki iya tafiya yabude mata office din gami da bata baby ta wuce. Harta fita ta dawo sir make up test in tawa yaja tsaki pls sir tace kafin yace wani abu jeki i will think about it dan Allah sir ta kuma fade yaja tsaki gami da fadin oppps kije during exam ki amsa all question in yaso se kisa C.A a biyun zan gane thank you sir ta fada tai saurin ficewa. Wayarsa ya dauko ya danna recording din da yai nasu yana kuma sauraro at list yasamu evidence against ita da nasir dole yai wani abu he yas to expose them dan kare martabar abokinsa. Miqewar dazaiyi wayar ta fadi jiyai har cikin ransa faduwar wayar yaisaurin daukowa yai yai ta kunnu taqi oh my goodness ya fada yana dan dukan goshinsa memory din ya ciro yasa ada wayar sedai ba recording shedar yana kan wayar ya Allah ya fada gami da komawa ya zauna wani hawayen baqin ciki ya gangaro masa ya rafka uban tagumi yana tunanin abinyi......... Koda ummu ta fita daga office din kai tsaye ficewa tai daga sch din saida ta hau dan sahu sannan ta dauko wayarta tafara dialling din number din Aisha yafi sau hudu bata dauka va kawai sai ta kira Fatima ita ma same thing happen kawai sai ta zura wayarta a jaka. Saida taje gida sannan kiran Aisha ya shigi lafiya dai irin wannan kira haka bata bata amsa ba ta kuma tambayarta kina ina ne ke muke jira fa. Tun dazufa nake nemanku ban gankuba shine na tafi gida nakirama in ce muku na tafi gida se mun hadu gobe tsaki Aisha taja Fatima tai sautin karbar wayar cikin fada take magana anman wallahi ummu bakida muntuci inba rashin mutunci ba kinsan bazamu tafi ba sai mun jiraki kawai saikiyi tafiyarki ayi hakuri naga tun wajen fitowa ta banganku ba kofa office din ban shiga ba kutt bakishiga ba kika ce muna kallonki fa kika shiga munfi awa biyu baki fitoba. Ganin yadda Fatima ke fada yasa Aisha karbar wayar haba ummu taya zaki mana hk tsaya ma naji fatima tana cewa wai kince ko office din baki shiga ba No bata fahince ni bane kinsan ta da fushi inta hau bata tsayawa cin ribar zance zata hau fada. Cewa nayi ina shiga na fito fa baku dai kula bane ni kuma banyi zaton kuna nanba natafi masallaci nemanku da banganku ba na tafi gida anya ummu idanuna fa nakan office din kinsan dai karatu mukazo ko bataji komi kan maganar Aishan ba dan tasan ta da tsantseni da fadar gaskiya gama kowaye . Ki yadda dani abinda yakaini kawai nayi banmayi make up dinba cewa yayi in answering all question 2 for test in yaso 3 for exam ok yayi kyau yanxu kina ina ina gida ki yadda ina gida bakomi ki shafan kan Abbakar zaiji insa Allah sukayi sallama. Ta goge hawayen da ya zubo mata wani dacin rai na taso mata tarasa me ke mata dadi ji take inama batazo duniya ba ko inama ta mutu kafin a haifeta. Gidansu mahfuz Hajiya wai bakya ganin haqqin ummulkhairi ke dawainiya da dangin nan namu musanman nahfuz taja tsaki me muka mata da haqainta zai dawai niyada mu eyye mara mutunci. Gani naifa yah mahfuz ya haukace gashi an kasa gano me ke damunsa Hajiya tai shiru kin tunan wani abu nasan tabbas da sahannun uwar yarinyar nan a abinda ya same shi sai yanzu na fuskanta aljanu suka turo masa suka masa farraqu da dan uwansa maza kiramin doctor yusif. Yawwa Doctor so nake mahfuz ya dawo gida mu gwada ruqiyya tunda naga na asibitin ba sauqi kinsan nayi tunanin haka aqwada ruqiyya hakan za'ayi. Kiramin musa ummi ta miqe saigata ta dawo da musa yana biye da ita ya russina ya gaida hajiya gami da cewa gani. Yawwa musa so nake kaje kadauko min mahfuz a asibiti yadan fada da razana hajiya mahfuz eh shi so nake ya dawo gida mu masa na gida tunda na asibitin yaqi. Hajiya ya warkene ya fada cikin rawar murya inda ya warke ai dabazance ma zamu masa maganin gargajiya ba ko. Jikinsa ta hai kyatma anman hajiya taya zan iya tawo dashi cikin sauqi ina tuqi to me kake nufi yai zuru zuru da ido ummi yasa dariya wallahi hajiya da gaskiyarsa taya zai dauko mahaukaci a mota shi daya wanda yake cewa zai kashe mutane kawai ya shaqeshi. Hajiya ta cilla mata daquwa ungonan dan uwan naki ne mahaukaci to hajiya aiba qarya akaiba ok to naji ku tafi tare sai ki riqe masa shi ta zaro ido hajiya ni eh ke inkuma bazaki ba to kinsan ba ke daya na haifa ba tasan indai hajiya ta fadi haka to taki qololuwar jin haushi. Ta miqe muje ta hau sama ta dauko gyalenta hajiya mun tafi Allah ya kiyaye tace amin. Tunda suka fara tafiya ba wanda yacewa kowa ci kanka kowa zulluminsa taya iya tafiya da mahaukaci cikin mota. Koda suka isa sunje office din doctor usif sunyi cike cike kafina abasu mahfuz, yadda ummi ta ganshi ya daga mata hankali dan mahaukaci sak tagani ya tara uwar suma da gemu wanda dauda har tafara sawa ya koma jaja. Koda ummi taje dab dashi amai ne kawai batai ba sabida wani tsamin dauda da yake tace yah mahfux ka gane ni ya kalleta ba ummi bace tadanyi ajiyar zuciya aqallah ya ganeta. Lafiya me ya kawoki nazo mutafi ne nine nace miki inasan mu tafi yadda yake magana cikin fushi da fada ya tsorata ta a'a to ba inda zani pls yah kinga alamar wasa a idona. Ni nariga na yanke shawar qare rayuwata anan dan haka zaki iya tafiya yah kayi haquri kazo mu tafi kowa na kewarka qarya kike kowa yafisan Nasir gashinan sabida shi kowa ya mance dani kowa ya tsaneni kowa ya gujeni. Cikin sauri tace yah kayi haquri inkasa wa ranka kowa ya tsaneka ka cire hajiya tanasanka kullin burunta kasamu sauqi pls kazo mu tafi kodan hajiya. Miqewa yai yabi bayansu ummi ta fara yadda da batun hajiya anwa mahfuz da Nasir farraqu tunda gashi har yasama ransa anfi san nasir duda yana cikin hauka. Suna tafe tana kaf kaf dashi cikin mota dan tsoronta karya shaqo me tuqi ko ya bude ya fice yana fiskantar ta sosai kasantuwarsa bayan yai degree dinsa a fanni qere qere yaje yayi wani sabon degree din a psychology baisan sanda dariya ta kufce masa ba aikuwa gabaki dayansu ummi da musa hankalinsu ya qara tashi fuskantar haka ne yasa shi yin shiru. Agida ma kowa kaf kaf yadingayi dashi har suka isa sashen hajiya sai asannan ummi ta saki sanyayyar ajiyar zuciya aqallah sunzo lafiya. Baibi ta kan kowa ba ya shige bangarensu toilet ya shige ruwa me dumi ya hada yai wanka ya wanje jikinsa yakai sau goma still bedana jin wani iri ba haqura yai ya daura towel ya hau shaving din gemun ya rarrage sumar kansa sannan ya sake wanka aqalla yadanji dadi. Ya fito yana saka kaya ne hajiya ta shigo riqe da kofi ummi na biye da ita da flask gabaki daya sunyi mamaki mahfuz ya koma mutun sak hajiya tazauna gefen gadon ummi ta zauna gefen kujera. Saida ya kammala sakayan yazo ya gaida hajiya aqallah ta danji dadin ganinsa yanzu va kamar dazu ba ga tea kasha ko zakaji dadin cikinka ga danwake kuma sekaci yunwa yakeji hakan yasa be musa ba ya amsa yasha. Yanasan dan wake sosai hakan yasa ya karba da zumudi yahauci saidai taunar farko yaji ba dadi dan gabaki daya bakinsa ba dadi dagyar ya hadi a hankula ya furta Allah ya isa Nasir hankalin hajiya ya tashi tadai daure. Ganin ya ijiye yaqi ci ne ta kalleshi kadaure ka ci hajiya wallahi ba test daurewa zakayi kaci se ahankula komi zai koma normal. Ummi kije ki samo toka ki gasa masa nama da ita zai temakawa test din bakinsa to hajiya. Da yamma agun cin abinci kowa ya hallara har mahfuz inka dauke Nasir mahfuz yakai lomar abinci baki kenan nasir yazo yaja kujera ya zauna kamar koyaushe kujerarsa kusata da ta mahfuz ya sha kansa qanina yajikin naka ya tankade hannunsa cema akayi banda lafiya ne ya miqe fuuu yabar gurin. Koda Abbakar yabar office din gida ya wuce dan gabaki daya ransa ya baci yama rasa abinyi. Da Amira qanwarsa ya ci karo zata fita tace lah yah sannu da zuwa ya amsa yawwa ina zuwa haka da yamma yah zani gidansu khairiyya ne zamu dan tattauna yai dariya zadai asha gulma tai dariya wallahi yah ba haka ne kyaji dashi se an dawo yai ciki be jira amsarta ba. Gabaki daya mutan gidan na falo har masu aiki shima anan ya zauna bayan ya gaida hajiya yasa baki cikin firar da suke hakan ya rage masa kashi arba'in na bacin ran dake damunsa. Kiran sallahr magariba ce ta tashi kowa dan kawo farilla ya kai kayansa samansa kafin ya daura alwala ya fice. Daga masallaci gidansu mahfuz ya wuce baisan an dawo da mahfux dinba ganinsa ba qaramin dadi ya masa ba sun tattauna kafin suyi sallama har ya fita ya dawo. Ban fada ma ba wani abin takaici nan ya zayyana masa komi cikin takaici Abbakar ke bashi labarin mahfuz ya goge hawayen da yazo masa ba komai Aminin Allah ya kawon mafita amin Abbakar yace. Kasan me inji mahfuz sai kafada Abbakar ya fadi ni wallahi bawai gidan mahaukata da aka kaini ne matsalata va babbar matsalata itace San ummu da kullun ke qaruwa cikin raina ko nayi yunqurin cireta araina abu kamar. Yana daya daga abinda yasa nake jin haushin yah nasir da ya aureta ni wallahi yanxu ji nake da rashin ummu gwanda abanni in dawwama gidan mahaukatan. Abbakar ya dafa shi se haquri taka qaddarar ce a haka uhun ba qaddarata bace nasani haqqine ke bibiyata tunda Allah ba azzalumin sarki bane yana sakawa wanda aka zalunta kadena sa haka aranka ka ci gaba da qoqarin mancewa da ita ni zan wuce kar hajiya taga na jima. Yana barin inda mahfuz din yake ya share hawayensa wanda tun dazu suke san fitowa yana jarumtar riqesu shi kadai yasan azabar da yake ji na san dalibar nan tasa dauriya kawai yafi amin nasa. Ashan gida ma bayan yaci abinci yaje gurin motsa jikinsa jiyai duk jikinsa ba kwari dakinsa ya shige ya rasa abinyi wayarsa ya dauko ya hau kunnawa ko Allah zaisa ta kama amman ina tace batasan zance ba tsaki yaja yahau gado ko Allah zaisa yadan samu bacci. Baccinma gabaki daya yaqi zuwa daya rufe idanunsa ummu yake gani tana masa murmushinta da yake qara mata kyau agunsa yarasa wace irin zuciya gareshi me nacin tsiya da take jawo masa masifa kala kala ace dik yan matan dake sansa takasa kallonsu sai matar wani. Ganin da gaske idanunsa basu shirya yin bacci ba yasa ya miqe yashige toilet dinsa ya dauro alwala ya hau nafil filun. Yau lahadi ba inda Abbakar zaije hakan yasa ya fito babban falo dan yin fira ko zai samu ya raje kewar da ke damunsa. Hira suke sosai inka ganshi bazaka taba cewa yana cikin damuwa ba danshi din akwaishi da jarumtar boye damuwa duk girmanta shi yasa ko hajiyarsa take cewa yana da zurfin ciki. Yau litinin yanada kula da masu jarrabawa qarfe biyu hakan yasa tun asuba da yasamu bacci ya debeshi yai me isarsa dan ya dade be yi me dadin sa sai goma ya farka yai wanka sannan ya sauka danyin breakfast dinsa. Bakowa a falon sai kwanukan abinci dake kan dining da alamu nashi ne kawai saida yaci sannan yaje dan gaida hajiyarsu. Tana kishin kide tana tasbihi suka gaisa kafin yace hajiya mu zamu fita tadan gyara zama to Allah ya kiyaye ya tsare ya amsa da amin cikin jin dadi. Gidansu mahfuz ya wuce sun dan taba fira da hajiyar sakamakon mahfuz din na wanka a hankula ya fara sako mata da maganar ummu aikuwa nan danan ta hau wato mun samu ya mance da maganar shine zaka zo ka tayar mana da ita to ahir dinka. Sin sin ya miqe yai dakin mahfuz din dan jiransa. Wai mahfuz in tambayeka mana inajinka in har ka yadda ummulkhairi ba matar nasir bace me yasa sukayi qaryar aure mahfuz yai shiru na dan lokaci kafin yace waya fada maka ban yadda ba ni wallahi na yadda matarsa ce. Kasan kawai meke ban mamaki seka fada inji Abbakar kawai ina mamakin me yasa yah nasir yakesan dole sai ya haukatani ta hanyar nunan bashi nake gani innaje gidan matar tasa. Abbakar yai dariya ba dole ya haukata ka va fansa suke dauka shida matarsa mahfuz yai danshiru na wani lokaci yes u are right wallahi se yanxu na gano dalili wato ya zabi mace kan dan uwansa. To wallahi tunda haka ya zabarma kansa ni nasan nafishi santa to zan nuna masa hauka sedai kowa ya rasa dan wallahi kashe shi zan yau bako gobe ba ya miqe ya zari wuqar dake kan kayan marmarin dake bed side drawer yai waje yana huci............ [12/31/2020, 5:51 PM] 🅰️ " AXEEX✌🏻 D'🅱️🅾️Y😎: _POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚 [12/31/2020, 5:52 PM] 🅰️ " AXEEX✌🏻 D'🅱️🅾️Y😎: *ABBAKAR* *PAGE 60---70* Da sauri Abbakar ya riqoshi yajawo shi zuwa ciki haba mahfuz kasan nasan da hankalinka pls act serious ma katsaya ka saurareni ya amshe wuqar. Ni ban yadda ummu matarsa bace mahfuz ya zaro ido what bafa ka yadda ba kace eh ban yadda ba to sabida me sabida kawai ban yadda ba ayanzu banda hujja anman ina ji ajikina ba matarsa bace kawai suna maka haka be dan ka fita daga rayuwarta. Ka yadda dani karka yi abinda zakayi danasani a hankula komai zai koma dedai haka yaita tausarsa har ya samu ya sauko. Fatima ce riqe da paper din test dinsu tana faman mita wallahi dedai nayi mutumin nan zai kansilemin dan Allah Aisha kalli nan ba haka ake ba ta kalla to ba gwanda keba nida ba'amin recording bafa to ba inkin kai masa zai miki ba. Pls ku rakani nai photocopy din paper dinnan suna tafe fatima na mita yayin da Aisha itama keyin tata kan rashin mata recording duda yake lefin tane na rashin saka reg. Number dinta. Ita dai Amina ba abinda take fadi se maganar absent da aka saka mata a last exam yayin da ummu tai shiru ita kadai tasan abinda ke damunta gabaki daya ta dena jin dadin sch din kawai tana daurewa ne. Kinsan Allah maidama mutumin nan zanyi jibi fa ko makamin nan beba yaushe zaki kaimasa ya shigar miki Fatiman ta tambayi Aisha ko yau ne sai muje inasan zuwa can chemistry lab ma ok se muje gabaki daya. Sunyi rashin sa'ar samun me photocopy hakan yasa suka kira sauran frnd dinsu kan suzo su tafi daga nan zasu viya suyi ahanya. Sun hadu a CIT inda student dinnan suke graduating se murna suke se anan ummu tadan ji sukuni aranta dan ita din mutunce me san taga mutane sun kanmala karatu musan man data ga yara qanana se taji dama ita ce. Tuni qawayenta sunyi gaba ta tsaya sakato tana kallom masu bikin sunata selfie yau batazo da me rainonta ba bata da lafiya koda zasu shiga exam sai wata yar level 4 ta roqa ta riqe mata Abbakar shine ya matso alamar ya tashi tai saurin sakkoshi ta matsa gefe dan bashi abinci. Da yake yafara shan kamu shi take bashi sha

Chapter 3 of 15