Sis Lina kuka sukai tayi itada laya, dakyar aka samu Laya tadena kuka kuma takicin abunci wai sai an kaita gurin Abbi”. Girgiza kai Alina tayi tana nufan su.
Hannu tasa ta janyo Laya tay wani firgiga ta tashi tana matse idanu. Kallonta Alina tayi tana kallon har cikin idonta ganin yanda take wani murza ido, tana kallonta tasan ba baccin gaske tayi bah, iya shege ne kawai da neman magana.
Janyo gashinta tayi tana kaimata duka a baya. Yanka ihu tayi tana tsalle tareda shafa bayan nata kamar wanda aka zubama garwashi. Tamke fuska Alina tayi tana janta tana fadin “ Wallahi Laya idan baki rabudani da wannan rashin mutuncin naki bah wlh saina zaneki. Kinsan bana daukan shit dinna naki koh”.
Dan tsayawa Laya tayi tana kallon face na Alina, ganin face din nata bada wasa takeyi bah yasa ta turo baki tana buga kafa. Kitchen ta jata suka shiga ga takeouts nan packages dayawa an jerasu. Sakinta tayi tana bubbude takeouts din. Biryani rice da garlic sause hadeda chicken drums ta dauko mata tace suje.
Palour suka koma ta ajiye mata akan center table tace tazauna taci. Zama tayi sannan ta dauki spoon tafara kaiwa baki da sauri da sauri, kana gani kasan yunwan takeji amma take wannan iyayin.
Alina kuwa itama biryanin ta dauka ta cire garlic sauce din ciki ta dauki pack na chicken nuggets ta koma palourn. Kan table ta ajiye sannan ta matsa inda Ummi take. A hankali tafara kiran sunan Ummi, dan juyi Ummi tayi tana bude idanunta dasukayi suntum tana kallon Alina.
Dan smiling Alina tayi mata sannan tace “ Ummi tashi kici abunci yanzu zansa ayi ordern abubuwan dazamu bukata sai kiyi wanka yanzu babu mai, in kinci sai kiyi sallah”.
Gyada mata kai tayi sannan ta mike jikinta duk yayi sanyi, miko mata pack din Alina tayi da spoon tafara ci ahankali ahankali bakinta duk ba dadi. Saida taci kusan rabi sannan ta ajiye Alina ta tashi ta dauko mata ruwa da akayi stocking a freezer ta kawo mata daya ta mikama Raya daya Laya daya.
Pack da Ummi ta ajiye ta dauka itama tafara ci, ko spoon goma batayi ba ta ajiye tasha ruwa ta tashi. Wayarta sabuwa ta dauka tayi list na abubuwa da suke bukata ta turama Henry.
Daukar laptop din tayi sannan tahau sama ta shiga bedroom dinta ta kwanta kan bed tanajin gajiya na ratsa jikinta. Message ne ya shigo wayarta ta dauko sabuwar tana dubawa, saidai babu komai a ciki. Wani tunani ne ya fado mata tay saurin daukar tsohuwar. Aiko message ne ya shigo gashinan An rubuta Unknown Caller ba number a jiki bakomai.
Shiga setting na wayar tayi taga still layin nata a blocked yake, so babu daman a kirata ko a turo mata message ya shigo. Fita tayi ta shiga message din da aka turo ta shiga.
Message ne aka rubuta kamar haka “ Missing me already? My Lady”. Da stickern white heart a karshe. Wani dum taji kirjinta yayi tana kara karanta message din. Yana nan dama? Yana nan yana bibiyanta kenan?
saimun hadu monday insha Allah. zan kara yawan pages din.
For more information ga wattsapp number na 09157578540
Wasan sarƙaƙiya ( Game of puzzle)
By Aryaah Riyad..
Book one 1….
Chapter 11…
Stars talented writers..
Jin hayaniya kasa kasa a cikin kata yasata dan motsi da idanunta. A hankali kuma tafarajin hayaniyar na karuwa kamar a cikin kanta akeyi yasata saurin bude ido. Saurin maidasu tayi tana runtse sakamakon wani haske dau daya daki idon nata. A hankali ta bude idon tana kyaftasa kadan kadan.
Bin dakin dateke tayi da ido ganin dakin wani fari fat yasa ta gane a ward room take. Face din mamah ce ta gani dab da nata ta kura mata ido tana kallonta. Itama kallon nata ta tsaya yi tanason ta gano mekuma yakawota nan dakuma abunda mamah keyi a ciki.
Smiling mamah tayi mata sannan ta matsa ta dauki waya tana kiran Dr. Katherine. Kawar idonta Yazrin tayi daga kallon mamah tayi yunkurin dagowa daga kwancen datake. Wani azababben zugi da bayanta yadauka kamar an zuba mata wuta akan bayan yasa ta koma dawani gudu ta kwanta bayanta ya bugu da gadon wani sabon azabar ya daketa.
Take idonta ya cicciko da hawaye tana runtse su da garfi kamar hakan zaisa tadena jin zafin. Tadade a haka har saida mamah ta taba mata hannu. Da sauri ta bude ido suka hade dama mamah. Cikin tausashiyar murya mamah tace “ Yazrin ya akayi? Jikin ne?”. Dan mamaki ne ya kama Yazrin dan rabon da mamah tay mata magana a sanyaye dakuma kulawa haka harta manta.
Gyada mata kai tayi dan bamatason yin magana. Still bayanta zafi yakeyi. Shafa kanta mamah tayi sannan tace “ sannu kinji. Yanzu Katherine zatazo saitayi miki alluran bacci kawai ki koma baccinki zuwa gobe zakiji duk ciwukan sun warke”.
Sai a lokacin brain dinta ya tuno mata da abunda yafaru. Face din Hajiya Marwa datatuno yasa ta sauke wata nannauyiyar ajiyar zuciya tana tuno irin zalincin datayi mata. Mamah kamar tasan abunda take tunani dasauri tace “ Yazrin ki yafe ma Marwa, kinsan wani lokacin kishinta kamar hauka yake. Kowaye akace za’a mata kishiya zata iyayin abunda yafi wannan. Idan daddynki yazo ki bashi hakuri karya yimata hukunci mai tsanani. Kodan bakomai nan gaa zata zama abokiyar zaman ki”.
Yazrin jitayi kamar ta mutu kawai a gurin ta huta da bala’i. Dama tasan hakan zata faru. Matar nan batada hankali kwata kwata baima kamata ace tana yawo cikin mutane hakanan bah. Asibitin mahaukata yakamata a garkameta kowa ya huta. Ga yanda mamah ke kare mata yazrin taji wani zagi a zuciyanta. Yanzu ita mamah bama taji zafin abunda akayi mataba take depending Hajiya marwa.
Bataga irin rashin imanin data gwada mataba har take da bakin tace taba daddy hakuri kar ayi mata hukunci. Sannan bama su fasa aura ma ridwan itaba. Lallai kuwa sosuke su kasheta kawai dan idan har zata iya yimata haka a yanzu datake gidansu toh abunda zatayi mata idan takoma chan zaidai a fitoda gawanta kenan.
Tsabar takaici ma rufe idonta tayi tareda juya kanta karma mamah tay tunanin zata hakura. Dan wlh bazata hakura bah idan daddy baiyi mata hukunci data gamsu dashi bah toh wlh ita zatayi. Saitasa Hajiya Marwa ta zubar da wannan kibar dake jikinta da tashin hankali da idanunta kamar ta surukar shaidan. Kwafa mamah tayi ganin yanda Yazrin tay banza da ita ta juya kai alamar bama zatayi ba kenan.
Dr. Katherine ce ta shigo dakin suka gaisa da mamah sannan ta karaso inda take. “ good morning Yazrin. How is your body”.
Dan smiling tayi mata sannan Yazrin ta dago ta kalleta. Mayar mata da smile din tayi sannan ta ansa mata da fine daba wani fitowa yayi bah tanajin makwogwaronga kaman sahara dessert a bushe.
Gwaje gwaje tafara yi mata wajen 10 minutes sannan tay wajen cupboard ta bude ta debo wasu allurai da bandages da wasu kayan dressing din. Tun kafin Dr. Katherine ta karaso Yazrin idanunta suka kara cikowa da kwalla tana bin tray na abubuwan da ido kamar taga wani aljanin akai tsoro fal idonta. Tana karasowa ta ajiyeshi a gefen bed din ta dauki allura guda daya ta budeshi sannan ta dauki ruwan alluran ta zuko a syringe din tana juyowa kan Yazrin.
Kuka sosai Yazrin ta fashe dashi tana yarfe hannu idanunta kafe kan allurar dake hannun Dr.Katherine. Dr. Inda sabo ta saba dan bama tayi kamar tasan me Yazrin din keyiba ta kara matsowa tana damkar hannun Yazrin na hagu.
Aiko fitsari ne kawai Yazrin batayi bah jin ta riko mata hannu. Damke idonta tayi hawaye na sunturi akan face dinta tana karanto duk wata addu’a datazo bakinta. Mugun tsoron allura takeyi da inba dan ciwon dake bayanta bah bazata bari ayimata alluran nanba kome takeji kuwa.
Jin shigar alluran cikin fatar hannunta yasa ta wani dauke wuta baki daya ta sume. Girgiza kai Dr. Katherine tayi tana kallonta, saidai taji dadin hakan tunda zatayi mata duk sauran alluran batareda ta tashi kota juyyuya bah bare ta fama ciwonta. Gama mata alluran tayi sannan ta juyata ta cire bandages dake bayanta dayake kamar an daye fatar abun babu kyan gani.
Babu jini ko daya sannan baiyi ruwaba infact yama bushe dan maganin da aka samata dakuma yimata alluransu chinese medicine ne mai bala’in karfi dakuma aiki. Kwana uku zuwa hudu ciwo yake warkewa a fili saidai still zaina zafi nadan kwanaki.
Wanke ciwon tayi daya shafe duk bayan dan babu inda babu ciwon a jiki sannan ta shafa mata maganin tayi dressing dinshi cikin bandages taja mata hospital gown dake jikinta da akasa mata jiya ta rufe bayan.
Maidata tayi ta kwantar sannan ta dauko ruwa ta shafa mata a face dinta. A firgice ta tashi tana rike hannunta da akayi mata alluran akai. Dr. Katherine ce ta cire mata hannun tana fadin “ Yazrin kidena movement dayawa kibar bayanki ya warke, inba hakaba karin alluran za’ayi tayi tunda bakyason ki warke, sannan ga magungunanki nan danace za’a kawo miki dama gobe dasafe zaki fara sha banda yau saboda alluran da akayi miki”. Gyada mata kai Yazrin tayi sannan ta maida hannun ta ajiyesu tana sauke nunfashi.
Ficewa tayi mamah ma tabita daidai nan Faryal yay sallama. Dagowa tayi dasauri yana shigowa face dinshi dauke da wata shagwababbiyar smile. Batasan sanda wata yar dariya ya kubce mata ba ganinshi sanye da manyan kaya ba usual English wears dayake sawa bah.
Har inda take ya karaso sannan ya bude hannuwanshi alaman hug. Hararanshi tayi ganin harya fara tsokananta kotayaya zatayi hugging dinshi oho. Maida face dinshi yayi serious yana taba wuyanta donjin temperature dinta. “ My baby ya jikin? Kinsan banma san bakida lafiya bah sai yanzu. Daga fada nake Sheikh Uncle Abduljabbar yake fada mun bakida lafiya”.
Gyada mishi kai tayi tana kare mishi kallo ganin kayan dake jikinshi “ kaikuma yau ya akayi kasa manyan kaya? Ni dana ganka nazaci wani malami ne ustaz wallahi”. Harara ya wurga mata yana dan tsaki tareda kara kallon jikin nashi. Da gangar tafada hakan dan bayason ace mishi ustaz. Dariya ta kwashe dashi ganin yanda yawani tamke face.
Adan gefen ta yazauna face dinshi yay wani iri yana bude baki ya rufe kamar maison fadin wani abu yakuma fasa. Tana ganin hakan tagane me yake son fada. Ita tama manta Faryal dan Hajiya Marwa ne. Kwata kwata basuda wani kamancece niya a tsakaninsu. Sannan bawai tana ganinsu tare bane ko dan shima faryal din yafi zama tareda Ridwan dan mai zama da Hajiya Marwa ko yayanta wani zubin gudunta sukeyi.
Sunkai wajen 5minutes kafin Faryal yajuyo ya sauke idonshi kasa murya a sanyaye yace “ Yazrin Dan Allah idan Uncle Abduljabbar ya tambayeki me za’ayi ma Hajiyar mu kice kin yafe mata. Ya fadawa oldman dina cewa zaisa Ayi mata duka dari ba daya a farfajiyar masarauta. Ina baki hakuri dukda nasan abunda tamiki bata kyautaba amma bazan iya kallon mahaifiyata a cikin wannan halin bah”.
Rufe idonta tayi dan bataso yamaga wani abu a idon nata. Batajin zata iya yafewa Hajiya Marwa. Kodan saboda karta kara tunanin yimata wani abu dan idan har tabari aka rabuda ita toh next abunda za’tayi mata saiyafi wannan. Tunani takeyi yanda zatayi da Faryal. Dan koma yayane saidai ta tambayan mata sassauci amma dole bazata yafe mataba. Wani tunani ne yafado mata kawai tace mishi toh.
Wani ajiyar zuciya ya sauke sannan yace mata thank you. Cigaba da hira sukayi suna tsokanan junansu. Mamah ce ta bude kofa ta shigo hannunta rike da jakar yazrin data mantoshi a East Wing. Wani bugawa zuciyanta yayi ganin jakar. Ita tama manta gabadaya Jakarta batanan. Ga book din a ciki.
Tunani tafarayi Allah yasa babu wanda yagani abunda ke ciki. Jikinta ne yafara rawa ganin mamah na kokarin bude zip din. Wani irin tari tayi dayasa mamah yin saurin juyowa ta kalleta. Ganin mamah ta juyo yasa kawai ta cigaba da tarin sannan ta daura hannunta akanta tana jujjuya kai. Sakin jakar mamah tayi tayo kanta Yazrin na kallon yanda Abubuwan dake jakar suka fito harda book din sakamakon zip din da mamah ta bude.
Kara karfin tarin tayi tana danna kanta tareda shura kafarta tana addua aranta Allah yasa hakan zai daukema mamah hankali daga kanta. Faryal dayaso yagane dagangar takeyi yasa yajuya yakalli mamah yace taje takira Dr. Katherine. Aiko da sauri mamah ta fita dayake wayarta bata hannunta.
Tana rufe kofar kuma yazrin tay saurin mikewa dayasa wani azaba ya ziyarci brain dinta saidai bata bi takan hakanba dan gwara komai akan Mamah tazo taga wannan book din. Faryal tsab yagane matsalar dasauri ya mike ya dauke book din ya mayar cikin jakar sannan ya maida har wayarta dake ciki ya rufe tareda kawo mata jakar.
Nannauyar ajiyar zuciya tasauke tana kallon faryal kozataga wani abu a face dinshi. Dan smiling kawai yayi mata a normal voice yace “ Yazrin amma bandani kike boyewa wannan abunko? Mekike yi da book dinnan?”. Kwantawa takoma tayi dakyau tana jin yanda jikinta ke ansa mata bayanta nawani radadi tana sauke ajiyar zuciya.
Qatar…
A bangaren Alina kuwa Tunda ta kurama text dinnan ido bata fitaba har barci ya dauketa. Bata tashi ba saida safiya tayi tafara jiyo kuka daidai kunninta. Tsaki tayi tana mirginawa saura kadan ta fadi daga gadon tay saurin komawa tana salatin tashi daga bacci.
Waro idonta tayi kan inda takejin kukan Laya ce kwance daidai gefenta tana rera kuka face dinta ba ko digon hawaye sai idonta dayayi raurau tana kallon Alina data tsaya kawai tana kallonta. Duk zamanta da Laya bata taba sanin iskancinta yakai hakaba sai yau kodan da bata biyota ko ina ne oho.
Mikewa tayi ahankali tana mika sannan ta nufa inda kayanta yake still a cikin akwati ta bude. Girl belt ta dauko ta nufo bed din Laya naganin abunda ke hannunta ta tashi da gudu tana ihu ta fita daga dakin. Kwafa tayi tana binta ta fita daga dakin tasan bai wuce gurin Ummi zataba.
Aiko tana fita tashiga dakin dake opposite nata Raya tagani a zaune kan bed tana kurban tea Laya daidai tana bude toilet tareda fadawa ciki. Dawo da kallonta kan Raya tayi da itama ita take kallo. A nutse Raya cikin sassanyar muryarta tace “ good morning Sis Alina. Yau bazamu school bah?”. Gyada mata kai Alina tayi tana mata smiling. shiyasa take son Raya akan kowa a gidan. Yarinyan kwata kwata batada problem ga nutsuwa kamar ba karamar yarinya ba.
“ Raya ina Ummi?”. Nuna mata kofar toilet Tayi da mamaki Alina ke kallon kofar toilet din dake datse kamar zataga wani abu a ciki. Indai hakane kenan Ummi naciki Yarinyar nan Laya tashiga kenan?. Lallai yau saita zaneta da batayi niyyan ta daketa ba dagaske kawai tsoro tayi niyyar bata amma wallahi saita gyara mata zama yau.
A hanzarce ta nufi kofar tareda knocking tana jiran ansa saidai shiru babu wanda ya ansa mata. Dawo da kallonta tayi kan Raya da itama toilet din take kallo “ Sis Alina Allah tana ciki, naga shigarta saidai tun dazu ta shiga ko bacci takeyi a ciki.
Wani dum taji akanta batai wata wata ba ta bude kofar dan babu key a ciki. Laya tagani a kasa tana rungume da Ummi dake a kwance warwas a kasan kamar wanda babu rai a jikinta.
Da gudu Alina ta karasa ciki tawani finciki Laya data daurama Ummi nauyi tayi gefe da ita. Hannunta tasa a kasan hancin mamah tanaso taji ko akwai nunfashi saidai bataji alaman dakwai ba. A hargitse tayi saurin saka kanta kan kirjinta jikinta yahau rawa tana son jiyo ko akwai heartbeat shima babu.
Hannunta dake rawa tasa ta kamo face Ummi tana tapping dinta tana kiran Ummi, Ummi kitashi saidai jin jikinta yadau sanyi yasa tay baya da sauri tana girgiza kai. Ina bazai yuba wallahi takasa ma motsawa. Da sauri kuma kamar wanda aka finciketa ta mike ta kunna tap ta taro ruwa a hannunta tazo ta shafa mata a face saidai shiru babu wani motsi ko alaman zata tashi, mikewa tayi tay waje Raya dataga a halinda ta fita yasa ta nufa toilet din itama.
Kasa ta sauka tana skipping stairs din kafarta sun mata nauyi dakyar take gudun ta fice dace ta nufi boys quarters. Kofar tafara knocking a haukace tana kiran sunan Henry saidai shiru babu ansa. Tura kofar tafarayi saidai a rufe take gam gam.
Da sauri kuma ta koma sama ta nufi dakinta remote na motarta da dauko sannan ta koma dakin Ummi ta shiga toilet din tareda yunkurin dagata saidai banda kanta babu abunda ta iya dagawa jikinta yayi nauyin gaske.
Cikin murya dake shakale tayi kan Raya Da Laya dasuka rungume juna suna kuka tace “ kuzo ku tayani dagata Raya zoki rike hannunta muje a kaita hospital”.
Tasowa duk sukayi suka zu tagefe da gefenta suna tayata dagota saidai tayi nauyinda bazasu iya dagata su kadai ba.
for more information ga wattsapp number na 09157578540
Wasan Sarƙaƙiya( game of puzzle).
By Aryaah Riyad..
Book one 1…
Chapter 14…
Stars talented writers…
Karan kamar ana bude gate yasa Alina mikewa dasauri ta fita daga cikin toilet din. Windown ta nufa tana kallon wanda yashigo. Ganin Henry ne yasa taji wani farin ciki ya ziyarce ta. Kwala mishi kira tafarayi daga nan yay saurin dagowa face dinshi cike da mamaki.
Magana tayi mishi akan yazo da sauri aiko bai bata lokaci ba dan yanda yaganta a hakan yasan babu lafiya. Cikin yan mintuna ya hawo Alina tace “ Henry Ummi ba lafiya. Munkasa daukanta dauko mana ita mutafi hospital Karta mutu”. Tana maganan muryanta ha hardewa.
Cikin tashin hankali yake kallonta ta nunamishi toilet din ya shiga ya daga Ummi chak shima yanajin yanda jikinta yay sanyi. Da sauri yayi kasa da ita Alina ta bishi. Harta kai kofa ta juyo tazo inda su Raya suke still a toilet din suna kuka cikin daga murya tace “ Kukuma bazaku fitoba? Mutafi mubarku kenan?”. Da sauri suka tashi suka bita kafansu babu ko takalmi.
Cikin Truck car din ya bude ya ajiye Ummi a bayan motar Raya ta shiga ciki. Alina a gaba ta shiga Laya ma ta shiga gaban suka zauna su biyu. Shiga motar Henry yayi ya tada motar gate ya bude suka fita a guje ya figi motar. Straight wani babban Private hospital da ake jidashi a kasar suka nufa wajen 10 minutes suk isa suna tafe Alina na juyo da idonta ko zataga Ummi na motsi saidai shiru.
Bai gama parking bah Alina ta bude kofar ta dira saura kadan ta fadi. Kofar baya ta bude ta fitoda Raya Henry yazo yadauki Ummi suka shige cikin hospital din.
Nurses ne suka dauko stretcher akasa Ummi akai aka shiga da ita Emergency Care Unit. Wasu hawaye ne masu zafi ke fita daga idanun Alina. Batamasan me takema kukan bah, ko dan halin da ummi ke ciki ne kokuwa, saidai batayi karaba ko kaga mutun na jijjiga irin na kuka. Hawaye ne kawai ke zubowa.
Sun shafe wajen 2hours a waje anan suna jiran fitowansu kowannensu hankalinshi a tashe kafin a fito da ita. A stretcher aka fito da ita jikinta a rufe tun dagakan kafanta har zuwa kanta. Wani faduwa gaban Alina yayi ganin yanda tafito da sauri ta nufi doctor dake fitowa shima. “ Doctor meke faruwa?, meya sameta?”.
Tsayawa doctorn yayi ya kalleta sai kuma ya juya yaci gaa da tafiyanshi. Da sauri ta sha gabanshi ta tsaya tana hada rai tareda maimaita mishi tambayan.
Shima hada rai yayi kana gani kasan bawai yanason yin maganan bane yace “ kije nurses zasu miki bayani inada abubuwan yi”.
Wani kallo tamishi cikin kulewa tace “ wannan wani irin rashin mutunci ne? Nurses ne zasumin bayani? Kai meya hanaka kayimin bayanin sannan ka tafi inda zaka?”. Kallonta yatsaya yi ganin bazata rabu dashi ba kawai yace “ Heart dinta yasamu problem. Sai an mata transplant amma yanzu an ceto rayuwanta. Tanada nanda sati biyu idan har ba’a samu heart da za’ayi mata sauyi dashiba zata rasa ranta”. Yana fadan hakan yajuya yawuce.
Wani sankarewa tayi agurin kamar wanda tayi suman tsaye. Tana rasa mezatayi kanta ya kulle gabadaya. Bata taba tunanin irin haka zata faruba. A hankali ta juya tabi inda nurses suka wuce da Ummi. Saidai a maimakon taga sun sakata a daki sai taga sun ajiyeta a wani dan corridor kamar waiting room.
Karasawa tayi ta tsare nurse daya da bata riga tabar gurin ba, a fizge tace mata “ ya kuka barta anan? Ina ward room din?”. Kallonta nurse din tayi wani sama da kasa sannan cikin wulakanci tace “ Oh, ai batada daki a hospital dinnan, in kina neman mata daki saidai ku fita waje ki ajiye ta gurin masu gadin asibitin. Nan yafi dacewa dak..”. Bata bari ta karasa ba tawani dauketa da mari jikake tas. Kafin hannunta ya sauka ta dau dayen shima ta kara daukarta da wani marin a dayen kuncin.
Bude baki nurse din tai zatay ihu ta daga hannunta takai mata wani marin a baki saida jini ya fito daga bakin nata hakori daya nafadowa. Sulalewa kasa nurse din tayi tana kama bakinta tama kasa ihun idanunta na zubar hawaye fan ji tayi kamar an maka mata wani karfe a bakin.
Sauran nurses da yan mutanen dasuke a harabar gurin ne sukayi saurin zuwa inda suka suna janye Nurse da Alina ta daka. Head nurse na cikinsu tayi wani kan Alina kamar zata daketa. Alina bata ko motsa daga inda takeba tana kallon matar ido cikin ido. Henry ne yayi saurin zuwa gurin shida wani doctor.
Doctor ne yace ta biyoshi office sannan yace nurses din sukoma aikinsu. Binshi tayi suka tafi office din nashi Henry kuma ya tsaya inda Ummi take tareda su Raya. Suna shiga ta samu guri ta zauna shima komawa yayi ya zauna yana kallonta. “ Miss Alina bazan miki boye boye bah, yanzu muna cikin Emergency Care muna kokarin cheto rayuwarta infact muna gwaje gwaje don gano yanda za’a samu zuciya dazatayi daidai danata akayi waya daga Minister na Health na Qatar cewa kada mu sake tabata daga wannan ceto ta damukayi. Sannan kada mubata daki ko prescriptions, dan haka ba laifin mu bane bazamu iya bujure order ba”.
Kuwait
A bangaren Yazrin kuwa saida tadanja lokaci tayi tunanin yanda zata ansa ma Faryal sannan ta fara bashi labarin abunda yafaru har ta yanke shawaran ta dauki littafin, “ Amma Faryal banason kowa yaji, kasan idan har wani a gidannan yasamu labari cewa zasuyi dama nacigaba da son nayi gasa da Amrah ne, sannan bazasu barni nacigaba bah, kuma idan har nasamu nayi wannan abun kafin wani yarigani nayi submitting dinshi a Council of members na Fada kafin daddy yasani nasan zasu ansa, zakuma su yarda a fada ma duniya ni nayi, kaga zamu samu UAE susan dani dan haka Aure na da Ridwan bazai yuba”.
Gyada kai yayi sannan yace “ Gaskiya hakan nada kyau, kinyi tunani mai kyau sannan kinsan bazan fadawa kowabah. Abu daya dazance shine bana tunanin littafin nan shine zaizama sanadin hakan, kinko san shekaru nawa mutane dasuke tunda suka tashi har mutuwarsu sunyi rayuwarsu ne dan su gano kan littafin nan? Gaskiya ni a ganina Samran salim ta haukace lokacin data rubuta wannan littafin. Indai ba hakaba babu yanda za’ayi ace fiye da shekara dari babu wanda ya iya gane menene abu nafarko data rubuta barema ace wani abu”.
Dan sunnar da kanta tayi tanajin maganganun daya fada. Tabbas tana sane da hakan. Saidai taada yakini cewa zata iya, domin koda bata samu ta iya gano menene a cikin littafin ba toh atleast ta gwada. “ Faryal banida wata hanya inba wannan ba, idan har inada rabo to lallai zan iya nayi hakan, sannan in banida rabo Allah zai bani wani hanyar dazai fiye mun alkhairi. Amma a yanzu zanyi duk abunda zan iya dan naga na cinma burina. Saina nunawa Mamah da Daddy ni yar halak ce sannan Amrah bata fini da komai ba, ita kanta Amrahn datake mun gani gani zan nunamata bata fini da komai ba. Yanzu kawai abu daya zaka mun shine ka dauki wannan jakar ka maida mun ita har cikin closet dina dan