Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
iska ya turoshi face dinta tabi ta side dinshi zata raba ta wuce. A fusace yakara tare mata gaba yana maimaita mata ba’a parking anan saidai tay kamar batajishiba, dan acewarta tafi karfin tay magana da security guard. Dago wayarta tay zatai kira saikuma ta tuna bazata iyaba, ranta dayafara sosuwa bawai dan security guard din daya hanata shigaba, no sai dan inconvenience da rashin iyayin anfani da wayarta datake yi. Chief security guard dinne ganin taki matsawa yayo inda suke, cikin professional voice danshi yagane wace ita yace “ princess Alina kozaki bada key na motar a kaimiki ita parking lot?”. Da kamar zaice mata ba’a parking a entrance saikuma ya tare kanshi, dan yasan indai yace mata ba’ayi toh lallai saita yishi. Saidai cikin rashin sa’a shima kallo kawai ta bishi dashi sannan tace “ anan nay niyyan parking motar, dan haka ku bani guri nawuce komuma bazaku ji dadin abunda zai faru idan hakan bata kasance bah”. Dan Tsayawa chief securityn yayi kaar mai tunani, saikuma chan yayima dayen security guard din alaman ya bata guri ta wuce. Yabe baki tayi aranta tana fadin ‘da baku matsaba dakunga abunda ba’ayi kuwa yau’ tay shigewanta cikin building din. Receptionist tagani a reception, straight gurinta ta nufa fuskarta babu annuri kwata kwata ta tsaya a gaban desk na receptionist din. Mace ce irin yan matan nan Latino mai black curly hair tana zaune a chair a bayan table. Professional Smile tayma Alina sannan cikin harshen turanci tace “ welcome to Qatars communication Regulatory Authority , how may i help you”. Kamar bazatai magana ba saikuma ta tabe baki tace “ i want to see your CRA asap( as soon as possible)”. Ta fada a British English accent dinta. Dan bude baki receptionist din tayi tana kallon Alina, dan batay kamada wanda zasuzo ganin CRA na Qatar gabadaya bah, bakowa ke samuh yaganshi bah, saidai bata nuna bah tace “ Miss do you have an appointment?”. No tafurta mata tana kallonta ido cikin ido. “ miss am sorry but sai kinada appointment, idan kinason booking appointment zakiyi filling form ki jira ayi approving, zuwa nanda 3-5 months zaki samu ki ganshi idan anyi approving na appointm…”. Bata jirata ta karasa ba ta juya kawai tabi hanyar elevator ta shiga. Dan batada abun tsayawa taji daga gurinta. Har ita Alina za’a kalla ace tajira 5months dantaga wani, lallai bataga waye ya isa yaymata wannan a duniya bah, dan wlh ko minti 30 bazata jira waniba bare watanni. Last floor ta danna wanda tasan nanne office dinshi yake. Cousin dinta ne sannan shine CRA na qatar wanda duk wani abu na communication sai yazo takanshi yasa hannu sannan za’a aywatar. Dan yayan Rayyan ne Aisha. Tana isa first floor dinkuma taga securities din kowa a post dinshi suna zagaye babu wanda yay takanta. Alaman sunsan da zuwanta kenan, aranta tasan wannan receptionist dince ta kira tafada. Dukda batasan wannene office din nashiba a cikin kifofin datagani guda biyar a jere kawai ta nufi wanda yake a tsakiya ta bude ta shiga. Zaune ta ganshi a seat bayan office desk dinshi yana kallon kofar kamar dama jiranta yakeyi. Batayi ko sallama ba tawuce direct inda yake a kujeru biyun dake gaban desk din taja daya ta zauna tana daura kafa dayakan daya ta daura idanunta akanshi face dinta a tamke. Shima face dinshi babu alaman wasa yake kallonta dawani irin kallo da zaka iya fassarashi da kallon so kona tsana, kokuma biyun ne suka hade guri daya, kana ganinshi kasan yaro ne dan bazai wuce 35 years bah full arab yatara saje da gemu. Babu wanda yay magana cikinsu har wajen 10minutes, ganin bafa zata yi magana bane dan yasan halinta yasa yace “ ke meya kawoki nan kuma? Ko girman kan naki ya tafi ne tunda mulkin dakike takama dashi an kwace?”. Cikeda zafa yay maganan. Murmushin gefen baki tayi tana kara kallanshi, cikin voice da kanaji kasan bata daukeshi serious bah tace “ hmm, Abdul kenan, kai kana tunanin mulki ko sarauta yasa nake abunda nakeyi, no sam bahaka bane, dan ni Alina nakai ne nakeyi badan wai wani nawa nada wani abuba, sannan meyasa za’a yi banning mun sim da accounts dina? Bayan kunyi freezing bank accounts dinmu har sims zakuyi freezing? Kuna tunanin banda zanda zanyi daku ne tunda mulki baya hannunmu yanzu”. Wata yar iskan Dariyar ya kwashe da ita harda rike ciki, sannan ya tsagaita yace “ lallai Alina yau na yarda ke yarinyace, bada abunki mekike dashi dakike takama bayan mulkin Rayyan? Yanzu Rayyan bashida mulki a hannunshi, an koreku daga fada, kowa ya juya muku baya babu abunda kike dashi daya rage banda kyan fuska da jin kai dabazai kaiki ko inaba. Idan da kinyi kin zauna lafiya yanzu baki isa kiyi bah, da haka ki tashi ki fitarmun daga office yanzu kafin nakira securities akanki amiki fitar wulakanci”. Fuzar da nunfashi tayi dan ba karya abun ya tabata, saidai a fili bat nuna komaiba infact kara daga face dinta sama tayi tana gyara zamanta, cikin ko in kula tace “ kaga abdul kokasa a gyara mun sim kokuma zanyi dakaina, inkuma nayi bazaka ji dadin abunda zai biyo baya bah, saina tada hankalin kowa a Qatar saina hana kowa bacci. Mikewa yayi ya zagayo inda take, tana kallonshi yana kallonta a bayanta ya tsaya dab da ita, bata juya kai ta kalleshi ba yadan duko kasa yasa kanshi daidai kunninta, “ idan kinaso nayi miki wani abu kona bude miki wani accouts da sims dazakiyi anfani dasu batareda kowa yasani bah toh ki biya mun bukatuna yanzu basai anjima bah”. Yana fadan hakan kuma yana dauro hannunshi kan kafadarta yana shafawa… For more information ga wattsapp mumber na 09157578540 Game of puzzle (Wasan sarƙaƙiya). By Aryaah Riyad.. Stars Talent Writers… Book one 1…. Chapter 11… Tanajin hannushi akan kafadarta yasa tayi saurin mikewa daga chair din, tareda kai mishi mari jikake tass takara daukeshi da wani marin a dayen kuncin. Wani irin shiru ne yadau dakin yakasa fitowa daga shock daya shiga, bai taba tunanin zata iya marinshi ba. Kamar tay amai haka takeji ta tsani a taba mata jiki, cikin bacin rai tace “ Abdul kai harka isa ka daga hannu ka tabani? Lallai bakasan wace Alina bah, zan cire maka duk wani rashin hankali dake dawainiya dakai”. Tana gama fadin hakan kuma ta juya ta fice daga office din tabarshi tsaye kamar gunki rikeda kuncinsa yama kasa magana. Koda ta fita a inda ta ajiye motarta taganta, security daya tsareta dazu yana balla mata harara. Abun dariya yabata yasa kawai ta daga mishi hannu tareda yi mishi wannan sexy smile din nata. Kamar wanda aka sumar haka ya tsaya yana kallonta baki sake, bawon Allah anga madarar kyau. Motar ta bude tashiga tereda barin gurin a guje. Tafiya tafara yi akan titin mai tsawo dan tun tana ganin gidaje har yakoma sai daidaiku dakuma daji ake gani. Wani hotel ta tsaya a gabanshi dan madaidaici bazakace na masu kudiba bakuna zakace na marasa karfi bane. Parking tayi sannan tafito, straight ciki ta shiga babu kowa a reception din banda warin disinfectant babu abunda ke tashi, floor na biyu tahau ta stairs dan ba elevator, a room 8 ta tsaya sannan tay knocking sau biyu. Ba’a ansa ba saida tay wajen 5 minutes saidai bata kara knocking bah, tasan yana ciki. Bude kofar akayi ahankali kamar wanda keciki na tsoron wani abu, baka ganin waye ya bude kofar dan tabayan kofar aka tsaya. Shiga Alina tayi ciki tana sallama ciki ciki, kofar aka rufe wani saurayi ne dogo irin black Americans dinnan hannunshi rike da gun AK-47 yayi pointing dinshi directly akan Alina. Harara ta wurga mishi tana juya manyan idanunta, cikin voice na ko in kula tace “ drop it malan, ko am not welcomed ne?”. No ya ansa mata dashi sannan ya sauke gun din yakoma kan karamin bed dake dakin ya zauna yana binta da kallo. Ganin baice tazauna bane yasa kayi kan chair dake adan gefen bed din tana karema dakin kallo. Gyaran murya yayi sannan yace “ Princess meya kawoki gurina yau kuma? I thought Abbinki yahanaki zuwa inda nake”. Yi tayi mara bata gane meyake nufi ba, dukda tagane sarai bawai yanason harka da ita bane tun bayan rabasu da daddy yayi tun suna level 100 yakuka sa aka koreshiba school din. “ Michael don't mind Ummi’s husband, kasan dai babu yanda zanyi dashi ne yasa harna yarda nadena nemanka, amma bagashi yanzu nazoba”. Tafada dukda tasan ba gaskiya bane, yes da dafarkon da Abbi ya rabasu tayi kokarin suci gaba da magana a boye, saidai Rayyan yasanta sarai dan haka saiyasa aka kori yaron daga school din amma yabashi scholarship a wata makaranta a UK, saidai bai tafi chan ba yazauna anan. Shima bawai ya yarda bane saidai tuna shiri dakuma taimakonshi datakeyi tun suna secondary school yasa kawai ya gyada kai, sannan cikin kausashiyar murya yace “ yanzu mekike so? Dan nasan bazaki taba zuwa kawai dan ki ganni bah, sannan naji labarin abunda yafaru daku ina muku jaje”. Dan tabe baki tayi dan bawai tanason ana maganan Abbi bane. “ Michael dama laptop nakeso, dakuma waya sabuwa da sim cards, sai bank accounts zan bada cash asamun a ciki, sannan banason kowa daya wuce kai yasan da hakan”. Dan jim yayi kafin cikin sanya yatambayeta nawa zata biya, ta ansa mishi da yayi naming price dinshi konawa ne zata bashi. Kai tsaye yace mata 250k dollars, da ok ta ansa sannan tace “ ammafah ayau nakeso, infact yanzu. Sannan banason kowa yasan nazo nan, kar nasaka a problem dan ina cikinta tsumu tsumu”. Dan murmushi yayi sannan yace mata ok bari yaje yasamo mata. Kuwait….. A bangaren Yazrin kuwa book din tasa a bag dinta sannan ta juya ta fice bayan tayimai sallama. Bata koma gida bah tace drivern ya kaita east wing na cikin masarautar. Gurine na shakatawa da suke zuwa in sunason shan iska. Kamar gidan zoo haka gurin yake, an zagayeshi ciki flowers ne kala kala ta ko ina, ga kanshi dayakeyi da bishiyu, ta chan gefe kuma animals ne basuda yawa a katange banda dawisu dake yawo a kasar gurin. Kujeru ne kamar na zuwa beach a jere a jere ata gefe daya, nan ta nufa bodyguard din na bayanta yasamu guri daga chan gefe ya tsaya itakuma tahau kan daya faga cikin chairs din mai recliner kamar gado ta kwanta akai. Babu kowa a cikin gurin dan shiyasa ma takeson zuwa, da wuya ka tarar da wani a ciki, dukda cewa iyakar yan gidansu sai kuma su faryal dakuma wasu close cousins dinsu kadai ke zuwa, bandasu babu wanda aka yarhe mawa suzo gurin Jin rana nadan dukanta yasa tayi ma bodyguard dinta alaman yazo, a hanzarce ya karaso cikin sanyayyiyar voice dinta tace “ please a kawo mun umbrella rana na damuna”. Ok ya ansa sannan ya juya ya nufi wata hanya a ciki, ba dadewa yadawo hannunshi rike da umbrella katuwa yazo ya kafa mata ita a daidai saitin kanta. Thank you tace mushi ya koma inda yake ya tsaya. Hannu tasa zata dauko book din daga bag dinta, saikuma tay tunanin kada wani ya shigo ya ganta saita fasa. Maida idonta tayi kan dawisu dasuketa yawonsu a gurin tana kallo, tanason animals a rayuwanta. Jin kaman bacci nason kamata yasa tay shirin tashi Dan takoma gida, batason tay bacci anan. Bata karasa mikewaba taji alamun taku, dago idonta tayi straight sai cikin idon Hajiya Marwa maman Faryal. Bata taba tunanin zata sameta anan ba, dan datasan hakan da batazoba dan batason matar wlh. Karasowa inda take Hajiya Marwa tayi tana tafiya a hankali daidai da daidai kamar batason taka kasar. Ga kuyangu wajen guda 10 a bayanta duk kansu a kasa suna biye da ita, bayanta kuma bodyguards ne sunkai wajen 15. Batada tsawo kokadan dan marabanta da dwarfs kadan ne, gata dai kamar Arab kamar ba arab ba, bazakace mummuna bace bakuma zakace tanada kyauba, sannan tanada kiba sosai dan koda take sanye da alkyabba data rufe jikinta amma zakaga yanda jikin ke rawa idan tana tafiya. Fuskar nan nata babu annuri kwata kwata a tamke take tamau, ga uban kwalli data sa saitai kamada wata boss irin na games dinnan. Kallonta yazrin takarayi tanajin gabanta na faduwa, dan ganin matarnan a inda ba cikin fada ba ba alkhairi bane. Tana karasowa inda Yazrin take kawai ta dauketa da wani azababben mari da saida taji ta dauke wuta. Bodyguard dinta ne yay saurin karasowa zai shiga tsakaninsu nata bodyguards din suka rikeshi, dayake sarkin yawa yafi sarkin karfi babu abunda yasamu yayi suka danneshi a kasa. Kafin Yazrin ta dawo daga shock data shiga takara kai mata wani marin a dayen kuncin da saida taji hakwaranta sun ansa kamar wani abu ya fashe a cikin fuskanta. A zabure ta tashi bama ta ganin inda take, Hajiya Marwa tay saurin damke hannunta tana mayarda ita inda take, cikin zafa da muryarta kamar na yan daba kanaji kasan tana busa hayaki tace “ kehar kin isa ki shiga gonata kice zaki aurin mun miji, lallai yau zaki ganema aya zakinsa, dan wlh ba Abduljabbar ne babanki bah, ko sarkin duniya ne akan mijina babu abunda bazan iyaba, yau idan nanuna miki iya haukata da bakinki zaki fasa auren, banda abun ridwan ma mezaiyi da mai kama da aljanu ma kamarki”. Tunda tafara Yazrin kejin maganganun wani sama sama, dan kunninta yay wani dum dakyar takeji dan inda ba dakarfi take maganarba vama zataji bah. Bude baki tayi tanaso tay magana saidai babu abunda yafito, tanajin jini daya taru a bakin nata tasamu ta hadiye shi dakyar, face dinta na wani radadi kamar an kunna mishi wuta, jikinta na karkarwa hankalinta duk ya tashi tarasa yanda zatayi. Hajiya Marwa dake huci kana ganinta kasan kan ba dadi ta juya tama kuyanga alaman tamiko mata abu, wata shaudediyar bulala ce irin na dukan dawakan dabasa tankwasuwa ta dadi ta mika mata ta ansa ta dagata tafara zubo ma Yazrin su a baya. Ihu Yazrin tayi jin kamar ana dukanta da garwashi, a haukace ta mike tanason ta rike bulalan amma ta kasa, duk yanda taso ta tsere ma Hajiya Marwa takasa infact sawa tayi kuyangu suka cire mata alkyabba suka bar mata yar cikin tareda rike mata ita ta rinka zubamata su, tun tana ihun azaba har ta gaji ta daina. Saida tay mata jina jina sannan ta sa aka saketa, tana kallon yanda take a zube a kasa jikinta duk jini daya rina golden rigar data rage a jikinta. Juyawa tayi ta fice a gurin batareda ta juyo ba, bodyguards dinta suka saki na Yazrin sannan suka bita a baya. Da sauri ya mike yataho gurinta. Saidai ganin halin datake ciki ga idanunta a rufe kamarma bata nunfashi yasa a razane ya dauketa yay waje da ita. Cikin mota yasata sannan ya shiga mazaunin gaba yana kallon hannushi daya jika da jininta, kirar emergency watar gida yayi yace a sanar dasu Mamah ga halin da Yazrin ke ciki. A mahaukacin guje yay tukin suna shiga cikin gidan ya kashe motar batareda yayi proper parking ba, daidai nan mamah ta fito tana nufosu face dinta cike da damuwa. Dr. Katherine ne a bayanta itama ta nufo su. Bude bayan motar bodyguard yayi sannan ya cirota daga ciki. Hannu mamah takai baki tana kwalalo ido ganin halin da Yazrin ke ciki, da sauri Dr Katherine tace a shigar da ita ciki. Har ward room ya kaita sannan ga fito Dr tafara dubata. Qatar A bangaren Alina kuwa tana zaune a dakin Michel har wajen 1hr kafin ya dawo hannunshi dauke da wani katon kwali. Yana shigowa tazo ya ajiye su akan bed sannan yay mata alaman tazo. Bude kwalin yayi ya ciro waya latest iPhone a kwalinta ya mika mata. Ansa tayi tana kallonshi dan ita batace ya chanzo mata waya bah, tafisoj wayarta sim kawai takeso. “ Micheal nifa ba waya nakeso bah, sim nace maka”. Gyada kai yayi sannan yace “ gashinan saikiyi synching da naki wayar, duk wani abu dake kai zai kuma wayarki, tanada E-sim so zai zo wayarki batareda yadawo gabadaya bah, saboda idan akazo tracking baza’a ga komai a wayarki bah saidai a ita wannan wayar, sannan ga laptop nan shima kiyi syncing da wayar saiki fara anfani da ita, Accounts shima na bude miki, yarage kikawo kudin da za asa a ciki, zakiga sunan account din amsa Fatima, shima idan akayi tracking bazai nuna ke kike anfani dashi bah”. Sauke ajiyar zuciya tayi tana daukar wayar, sannan ya ciro laptop Hp latest edition ya mika mata a kwalinta. Ansa tayi sannan tace mishi thank you, sannan ta tambayeshi yaushe zaizo ya ansa kudin. “ Alina ai ke zaki kawomin kudin bani zanzo na ansa ba, bazan shiga matsalarki bah gaskiya so ni bazanzo inda kikeba”. Hade rai tayi tana kallonshi, itafa batason rainin wayau zaice mata ita zat kawo mishi, soyake takara biyoshi har nan? Cikin dajin nan? Aiko bai isa bah. Daukar kwalin laptop din tayi dana wayar ta mike ta dauki nata wayar ta nufa kofar fita yana binta da ido, cikin no nonsense voice tace “ Zan turo maka da address dazaka zo ka ansa kudinka zuwa anjima”. Sannan ta murda kofar ta fice. Sauka tayi har kasa saidai babu motarta babu dalilinta, kalle kalle tafara yi tadaisan anan ta ajiye motar, amma yanzu bata ganta bah. Wata hargitsasiyar dariya tayi tanajin takaici na saukar mata, daga wannan sai wannan, takuma sani motar ta tafi kenan dan sace tah akayi. Kwafa tayi tana tunanin yanzu yazatayi takoma gidah kenan? A tsakiyan dajin nan ga hotel din bata tunanin akwai sunada transport. Titin kuma babu kowa. For more information ga wattsapp number na 09157578540 Wasan sarƙaƙiya ( Game of puzzle) By Aryaah Riyad.. Book one 1…. Chapter 11… Stars talented writers.. Dr. Katherine ta dubata akayi bandaging, Allah yasoma bayanta ne kawai dukan yasamu, tayi treating dinshi tayi mat allurai har akayi aka gama bata tashi bah. Mamah ce ta kalli Dr. tace mata “ Dr yanaga bata tashi bah? Kardai akwai wani abun bayan dukan da akayi matah”. Girgiza kai dr Katherine tayi sannan cikin professional voice tace “ No babu komai, shock ne tasamu kinga dama jikinta bashida kwari, nanda safiyar gobe zakiga ta tashi, dan nayi mata allurai na bacci, ciwukan ma basu zama deep ba dan haka nanda sati daya zasu warke”. Gyada mata kai mamah tayi sannan Dr Katherine ta fice daga dakin. Mamah ma fita tayi straight dakinta ta koma ta dauki waya ta kirah Daddy. Ringing uku ya dauka bakinshi daukeda sallama, mamah ce ta bashi labarin abunda ya faru, murya cikeda bacin rai yace “ wani me Audacity ne da bayason ranshi zai taba mun ya?”. Dan jim mamah tayi sannan tace “ Hajiya Marwa ce, kasan halinta dai akan miji”. Katseta daddy yayi yana fadin “ Au dayake kawarki ce shine kika boye sunanta da farko? Take so ta illata miki yarinya amma kike bata excuses, toh wlh saita gane kuranta, zan nuna mata bazatayi abunda taga dama a cikin masarauta ta takuma zauna lafiya bah”. Yana gama fadin hakan ya katse wayarshi. Mamah tsaki tayi jin yanda ranshi ya baci, kwata kwata bataso wannan abun bah, suna good time sosai da Hajiya marwa, dan haka bawai tanason wani abu ya shiga tsakaninsu bane tun suna yan mata suke tare, yanzu idan daddy yayi mata wani abun dolene kawancen dake tsakaninsu ya ruguje, duk yazrin taja mata wannan bala’in wlh. ( jama’a kuji karfin hali. Ina ruwan yazrin kuma? Yarinyar da batason ridwan din kukuka hada abunku yanzu kuma wai yazrin taja miki). Numbern Hajiya marwa ta dannawa kira harta gama ringing ba’a dauka bah. Kar kira tayi sannan aka dauka. Babu ko sallama hajiya marwa tace “ yane matar Abduljabbar yau kin tuna danine? Kokin kira kiji menayi ma yarki ne?”. Dan dariya mamah tayi sannan tace “ A’a ko kadan ai kece bakya nemana, tun Friday fah bamu kara neman junaba, yau sati daya. Dama nakiraki ne nace miki daddyn amrah wlh ranshi ya baci, abunda kikayi baki kyauta bah kini raina ya sosu, kinsan yanda yarinyar nan take ba lafiya gareta bah, yanzu tanachan rai a hannun Allah. Tun wuri ki nemi yanda zakiyi dan wlh yanda kika taba mishi ya abunda zaiyi ba karami bane”. Katseta Hajiya Marwa tayi tana fadin “ kefah akwai ki da tsoro, yarinyar takima daba sonta kikeyi bah. Yarinyar da tunda kika samu cikinta kika nuna baso kikeyi bah, kika haifeta ina tunawa a labor room kika ki koda daga idone ki dauketa, yanzu zakizo ki nuna wai kin damu da ita, sannan shima iban yar ai yasan basonta yakeyi bah, ba nunawa yayi bayason wahala bah datake rashin lafiyar nan? Koba shi yace a sawwaka mata rayuwarta ba tana shekara biyu?”. Sauke ajiyar zuciya tayi tana hade ranta guri guda “ Marwa nasha fada miki banason kina tunamin da wannan abunko? Abu yariga ya wuce sannan koba komai yatace daga cikina tafito, sannan kinsan halin Abduljabbar da izza, bazaiso koyaya ne a taba mishi ya ba, dolene zai dauki mataki akanki, kindai san dokar masarauta, kuma ita yazrin ba ita tace tanason ridwan bah, shi da daddynta sukayi abunda sukayi”. Tsaki Marwa tayi “ ke nifa akan mijina komai za’ayi saidai ayi, kuma karki sake fadin hardashi a cikin maganar nan, bazai taba yuwuwa yaso wanda baniba, zanyi maganinshi shima sai anjima banida magana dake”. Tafada tana katse wayarta. Tashi tayi jikinta ba kwari takoma ward room da yazrin ke ciki. Still bacci yazrin keyi saidai kana ganin yanda take baccin kasan a wahale take yinshi. Kallonta ta tsaya yi harga Allah bawai tanajinta a cikin zuciyanta bane, saidai ganinta a hakan yasa taji babu dadi sosai. Shafa kanta tayi sannan ta gyara mata bargon da aka rufa mata sannan ta kashe lights ta fice. Qatar… A bangaren Alina kuwa tsaye take gaban hotel din tana tunanin yanda zatayi, tuna cewa anyi mata sabon sim ne yasa ta dauko sabuwar wayar. A bude take sabuwa gal tayi setting dinta up sannan tayi downloading Doha Metro transport app tayi booking ride. Saida tayi wajen 40 minutes sannan motar ta karaso. Motace honda accord da drivern yay parking gabanta. Shiga tayi tana dari dari bata bari hannunta ya taba wani abu daya wuce kofar motarba. Tunani takeyi irin mutane nawa ne suka shiga motar kafin ita, tana karemata kallo kozataga wani abun kazantar saidai batagani bah. Dukda hakan kuma a dar dar take dan mugun kyankyami takedashi, inba dole ba da bazata taba shiga public transport bah. Drivern nata juyowa yana kallonta ta mirror, dataga kallon yaki karewa saita kura mishi ido itama ta mirror din tan kallonshi. Ganin haka yasa ya juya yakalli gabanshi. Kallon hanya takeyi ganin baya mata sauri tay tsaki tana kara gyara zamanta duk ta kagu yayi ya sauketa saidai a wani hankali yake tafiyar. A kule cikin no nonsense voice tace “ Malan kakara sauri mana kayi ka saukeni haba. Idan bakada abunyi ni inadashi”. Sakin baki yayi yana kallonta, a muryarshi dake dan rawa yace “ Princess ayimin afuwa, bazan iya kara guduba saboda doka”. Tsaki tayi sannan tace “ malan ka kara gudun ka kaini inda zani, babu ruwana da wata doka”. Gyada mata kai yayi sannan yakara gudun, dukda bawai gudun yamata bane amma batada time dinshi kawai yasa ta rabu dashi ta rufe idonta. Sotake ta jinginar da kanta amma kyankyami ya hanata. Sunkai wajen 1hr sannan ya sauketa a gaban gate na gidanta. Tariga tasan mutane sunsan anan suke shiyasa bama ta damu bah. Sauka tayi tay knocking kofar ba dadewa Henry ya bude mata. Shiga tayi tana zuwa ta tarar da Ummi a palour tana bacci, Laya na kwance akan jikin Ummi still uniform ne a jikinta, Raya kuma na zaune a kasa tana cin abinci takeout. Tana ganin Alina ta mike da sauri tazo tay hugging dinta. Hugging dinta back Alina tayi tana shafa kanta, cikin yar tausassiyar murya tace “ Raya su ummi tun dana tafi basu tashi daganan bah?”. A yar jaramin voice Laya tace “

Chapter 8 of 11