Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
dari uku da saukarta a mulki amma babu wanda zaice bai santa ba kokuma tarihinta, saidai iya abunda mutun daya yasani shi zakaji wani ya fada, babu wanda yasan meya faru sarakunan dasukayi zamani daya da ita suke rashin lafiya datayi silar ajalinsu. Ganin tunanin bazai bulle mata bane yasa ta mike tareda maida book din inda yake, sannan ta dauko wani da aka rubuta “ the process of life”. S3- Bata karasa inda take zama ba aka bude kofan, wani dattijo ne sanye da white jallabiya da black alkyabba irinta sarauta, bazai wuce shekara 45-48 hakaba. Mutun hudu ne manya manyan gabza gabzan maza majiya karfi a bayanshi, suna sanye da suit bakake idanunsu da shades black, fuskokinsu babu annuri kwata kwata. Dago mata hannu mutumin yayi, sannan ya nufo inda take, itama tafiya tafarayi a nutse tana nufanshi, dayake libraryn akwai girma sosai so saida suka dan taka sosai kafin su iso inda junansu suke, sannan tundaga shigowanshi idanuwanshi ke kanta baikoda kyafta ido ba. Dab daiya ya tsaya da saida tadan ja baya tsabar closeness dinsu, tana jin kallonshi akanta wanda yake mata tundaga sama har kasa saidai bata nuna tasan yanayi ba dukda babu dadi datake ji a jikinta. Wani classy murmushi ta sakin mishi sannan tadan yi kasa da kanta alaman respect. Ido cikin ido yake kallonta dan kusan tsawonsu daya ma da yazrin, still bai bude baki yayi mata magana ba dukda sunkai almost two minutes a tsaye. Yazrin ma kallonshi tayi shima cikin ido sannan cikin polite sexy voice dinta ta gaishe shi gaisuwa irinta masarauta da akeyima manyan mutane, sannan ta kalli bodyguards dake dan bayanshi ta furta “ sheikh ridwan, bodyguards aren’t allowed in here”. Kaman bai jita ba dan baiyi alaman yamasan tana magana ba, saima mayar da kallonshi zuwa cute lips dinta dayayi sanda take magana. Abun kwata kwata bai dameta ba dan bayau ya fara mata irin hakaba, shiyasa sam batason hada hanya dashi, dan idanda ba nan library din yazo ba toh bazata ma kulashi ba indai bashi yayi mata magana first ba, saidai duk abunda za’ayi sai ayi, amma dayake library yazo kuma itace in charge of libraryn, dolene tayi engaging dinshi, dan yana daya daga cikin four National Assembly members na kuwait, wanda daga sultan, sai amir wato babban dan sultan, sai kuma su a matsayi da power, sannan yaya mata na sultan. Kaman bazaiyi magana ba saikuma yayi musu alaman su tafi, ba musu suka juya sukayi waje. Cikin voice irin na dattawa dasuka ci duniya kana ganin kodaga idonshi kasan baya ji, ya kalleta yana fadin “ babyn sultan, kin girma, in bansanki ba dasai nace gudu na kikeyi a masarautar nan, ko nayi miki laifi ne?”. Ya fada still idonshi nakan ta. Wani smile din tadanyi dukda baikai zuciba, tasani sarai yasan gudunshi takeyi, toh inma bata gujeshi ba ai ya tambayi kanshi, still bata bar face dinta ya nuna komaiba ta tambayeshi me yakeso, sai ya cemata kawai yazone yaga libraryn sannan yadan zazzagaya ko zaiga wani abunda zai dau hankalinshi. Da ok ta amsa mishi aranta tana raya dama tasan babu wani abunda ya kawoshi, kawai bashida inda zai ganta ne sai anan din, takuma sani sonta yakeyi, dan kowa a masarautar yasan da haka, hatta sultan dakuma mamah sunsani, sannan shi sultan ma bai nuna rashin son abun ba, hasali ma nunawa yayi ai babu komai, mamah ce ma take basar da maganan alaman bata supporting, dan haka yazrin dole takw biye mishi dukda bata nuna mishi tasan meyakeyi, maidashi takeyi kaman mahaukaci yayta borin kunyan isa da sarautar nashi, dan ita baka ma isa wai ta nuna maka tasan me kakeyi ba, duk rainin wayan dazakayi mata tasan tayanda zata bullo maka cikin ruwan sanyi. Shiyasa koda suka fara zagaya livraryn yanata dan janta da hira cikin basaja saita datseshi itama, kokuma idan yay magana akan rashin ganinta ran fridays a gurin sauka da akeyi saitace mishi tana tareda matanshi. Hakan sosai yake bata mishi rai dan yanada hankali dakuma wayau har yakai matsayin da yake a yanzu, dan haka yagane sarai abunda yazrin kemai. Sunkai wajen two hours still basuyi rabin libraryn ba, yazrin tafarajin jikinta na saki, hannayenta sun fara kyarma idanunta na sauya kala zuwa jaja jaja, dama ita sam jikinta baya daukan wahala, abu kadan zatayi zataji jikinta ya saki, gashi bashida alaman gamawa. Sosai takeso ta zauna dan kafafunta kaman tana taka wuta takejinshu, ga nunfashinta dake zuwa da karfi da karfi dakyar take janshi, saidai bata nuna ba ta cigaba da binshi tana addua allah yasa ya gaji yace su koma, tana cikin hakan kuma taga ya tsaya, wanda bata luraba ta cigaba da tafiya saida ya kira sunanta wajen sau uku, da sauri ta juyo da kanta zuwa inda ya tsaya dan har tadanyi nisa. Gani tayi ya kure ta da ido yana kallonta alaman yanaso yaga meke damunta, saidai tayi saurin hada nutsuwanta tareda juyawa ta koma inda yake “ yazrin ya inata miki magana baki ansani ba sannan kika cigaba da tafiyarki?”. Ya fada ranshi babu dadi. Dan tabe baki tayi dan yanda take jinta bama zata iya biye mishi ba, kawai yazo ya gajiyar da ita sannan zaiyi kamar tamishi laifi dan bata ansa shi ba akan dai yar magana daya “ oh sorry fah, tunani nashiga yi shiyasa”. Bai ansa ta ba sai irin kallon mamaki dayake mata irin lallai yarinyar nan ce zata mishi magana ahaka harda tabe baki, kana kawai ya juya ta hanyar dasuka biyo ya koma. Binshi da ido tayi harsaida ya bace daga ganinta sannan ta sauke wani nannauyar ajiyar zuciya, zubewa tayi anan kasan epoxy floor irin na da dinnan dayake a tsaftace tsaf dan kullun sai an share ankumayi moping round biyu. nunfashinta tahau ja tanason daidaita shi, sannan ta mikarda kafafunta datakejinsu kaman dutse a jikinta, duk jikinta yayi tsami kamar wacce akayi ma duka. Takai wajen 1hr a zaune kafin tadanji dama dama, sannan a hankali ta mike ta juya ta koma lounge din, tanayi tana tsayawa dan ta huta. Koda ta koma lounge din bajewa tayi akan comfy chair din tana salati, tasan yanzu lokacin sallah yayi amma batada wani energy yin sallah saita huta. Kara gyara kwanciyan tayi jin baimata dadi ba, ga tunanin ko mai zaine yacema sultan akanta yanzu, dan daduk alamu ranshi ya baci, mutun ne maison a girmama shi dan haka dolene irin yanda tayi mai maganan ya bata mishi rai, allah dai yasa karya ballo mata ruwa. Jin kaman tunani zai fasa mata brain ne yasa ta mike tareda daukan phone dinta ta nufi waje, tareda dagawa librarian din hannu alaman ta tafi. Bodyguard dinta dake tsaye yana jiranta tayi gaba yana binta a baya, kaman tasa kuka jin yanda kafanta ya cigaba da zafi. The drive back zuwa mansion din was so peaceful kamar kar yakare, tana sa kafanta cikin front door dinkuma wani depressing feeling yazo mata, batasan meyasa ba kwata kwata bata samun nutsuwa a cikin gidan, shiyasa kullun indai bata library toh tana school, sosai take tana avoiding zaman gidan. Danne feeling din tayi ta wuce dining, babu kowa a ciki dan haka cookies kawai ta deba a dessert plate guda uku sannan ta juya ta tafi dakinta. Glass of water dakuma wani luxury dispenser da inba ace make dispenser bane bazaka zata shineba ta debi ruwa sannan ta koma bed dinta ta zauna tana sha tareda cin cookies din a hankali. Takai wajen ten minutes sannan ta gama ta mike. Straight toilet ta nufa ta cire kayan jikinta ta kaisu laundry room daka attached to toilet, sannan ta kunna ruwa a wani giant two persons jacuzzi ta wurga rose scent bath bomb a ciki sannan ta sa shower cap akaanta dan batada energy wanke shi ta shiga. Jikinta dayayi tsami ya fara saki sakamakon zafin ruwan dake shiganta har bones dinta takejinshi. Wayarta data saka a phone holder dake daidai kusada jacuzzin ta dauka tareda kunna wakan central cee ‘Band for Band’ tana miming tana jujjuya kanta face dinta cike da annuri. Voice dinta is so soft and silky kwata kwata bai dace da rap music ba, wakan daban voice din nata daban. Yana gama playing kuma ya shiga kendrick lamar “ not like us”. Yana playing tana miming, jikinta yayi dadi kamar ba itace dazuba, tana cikinji kuma wakan ta tsaya ringing din kira ya shigo, tsaki tayi dan yanda tayi relaxing dinnan kawai za’a kama ana wani kiranta, kaman bazata dauka ba saikuma ta sa hannu ta dauki wayan, lokacin harya gama ringing. Bude wayan taso tayi saidai bata samu ta bude ba saboda santsi na ruwa dake hannun nata, hakan yakara bata mata rai dan bataso ta tashi yanzu, saidai tunanin kowani important abu ne tunda banda yan gidansu mutun dayace wato bestfriend dinta ke kiranta, dan haka daurewa tayi ta mike ta dauko towel ta nede jikinta. Sannan ta dauki wayan ta fito. Closet ta nufa ta dauko body moisturizer dinta ta shafa adan sauri sauri sannan ta duba time, ganin kusan 7pm na yamma ya kusa yasa ta daukan kayan baccinta kawai dan lokacin dinner yakusa kuma tana ci bacci zatayi. Riga ce silk button up da wando dabaikai gwaiwa ba, yanada fadi and its so comfy dan kusan duk pyjamas dinta irinshi ne. White alkyabba rufaffiya ta dauka wanda takeda all white beadwork da fine stones an jera ta kasan dakuma wuyan sai yan blueish green suma andan watsa su saiyayi kaman ocean dayasa eye color dinta yayi popping sosai. Sannan ta cire shower cap din ta saki gashinta ya zubo yayi waves sai shining yakeyi, alkyabbar batada hula so dan scarf mara fadi tayi folding ta daura a kanta ta saman gashin ya zuba ta baya. Fita tayi sannan ta dauki wayan danta duba miss call din, sunan mamah tagani a screen din tana kara kira, da sauri ta dauka tana fadin “hello mamah sorry wanka na shiga”. Ta fadi hakan batareta jira mamah tayin magana ba. Da ok mamah ta ansa mata sannan tace “ yazrin come down for dinner, karkisa mu jiraki kaman dazu”. Tana fadin hakana kuma ta katse wayar. Dan jim tayi jin kaman taji hayaniya a inda mamah take, ko su waye oho. Harta nufa bed dinta dan tadan huta kafin ta sauka saikuma wani tunani ya fado mata, kodai azlan ne ya dawo?. Wani tsalle tayi tareda ihu so excited ta juya ta gudu tana sakin wayan a kasa ta fice daga dakin. Direct dining tayi nan kuwa tana zuwa ta tabbatar da zatonta. Tsaye ta ganshi… Game of puzzle (Wasan sarƙaƙiya). By Aryaah Riyad.. Book one 1…. Chapter 2….. Kuwait, Bayan Palace…… ( masarautar kuwait). Aiko hakan ne takasance dan tana shiga dining din ta ganshi a tsaye yajuya bayanshi yana magana da wani dabatama tsaya ganin wayeba tayi kashi tana dan ihu tareda tsalle tay hugging dinshi ta baya so tightly. Yin baya yayi kaman zai fadi dan yanda tayi kashi tay tsallen duk nauyinta ta sakinmai, hakan yasa tayi sauri ta sauka daga jikin shi dan ita tama manta bashida lafiya murnar ganinshi ya mantar da ita. Daidai bayanshi ta tsaya still hannayenta na zagaye dashi, saidai shi bai juyo ba bai kuma nuna yasan da ita bah, dan cigaba da magananshi yayi da wanda ke gabanshi. Sunkai wajen two minutes a haka sannan ta sake shi tareda zagayowa ta gabanshi dan taga me yahanashi ya juyo yayi mata magana, saidai bata karasa zagayowan ba suka hada ido da wanda ke gabanshi, a zaune yake a chair dake kusada na daddy a left side wanda hakan ya hana ta ganinshi tun shigowanta sai yanzu data juyo, saidai dukda a zaune yake bazai hanaka ganin cewa dogo ne sosai ba, full arab ne irin hadaddun UAE arab guys dinnan, eye color dinshi brown gashinshi kuma baki sidik yasha gyara daya gyarashi wasu sunyi baya wasu kuma sun zubo har gaban goshin shi, jikinshi is built da muscles dukda suit ne a jikinshi bazai hanaka gane hakan ba. Dauke idonahi yayi daga kanta ya cigaba da magananshi dayakeyi da amrah dake gefenshi a chair din tadan rungumoshi ta side sun hade kujerun nasu guri daya, tana magana, shima brothernta ayaan dayake kusan kamanninsu daya da azlan saika zata yan biyu ne saidai shi ayaan gashin kashi wavy brown ne, tsaye yana dan ansa musu sama sama, gakuma mamah dake opposite dinsu itama tana dan tofa musu.. Danne abunda taji yazo mata zuciya tayi sannan tasa smile a face dinta ta kalli ayaan tace mishi “ welcome back big brother, an dawo lafiya? Ya hanya? Yazu anty?”. Ta fada voice dinta yadanyi kasa. Juyowa yayi ya kalleta yadanyi mata smiling sannan yace mata lafiya kana yadanyi hugging dinta ta side for a split second kaman wanda kejin tsoron ta shafa mishi wani abu. Sannan ya koma side da mamah take ya zauna kusa da ita. Maida hawayen dataji suna kokarin zubowa tayi sannan ta juya kan azlan da yake gefen amrah tace mishi “ welcome back cousin”. dago ido yayi ya kalleta tundaga sama har kasa sannan yadan gyada kanshi alaman amsawarshi, itama bata juya ta kalleshi ba bare ta jira ansar datasan bazata samu bah. Kusada mamah ta zauna saidai tabar sit daya tsakaninsu wanda ayaan yazo ya zauna anan din, sannan ta sauke kanta kasa tareda dauke hannayenta dake rawa ta daurasu a laps dinta dan bataso wani yaga halindatake ciki. Sunkai wajen 5minutes suna hira a junansu babu abunda kakeji sai kashin expensive turaren wuta dakuma garlic and paprika spices dake tashi sai dariya dasuke yi sunata hirarsu. Babu wanda ya tuna kokuma ya nuna yasan da yazrin a gurin. Shigowan daddy ne ya fitar da ita daga tunanin datakeyi. Yana zuwa straight head of the table seat ya zauna batareda sun gaisa da su azlan ba, da alamun sun hadu kenan kafin su shigo nan. Sannu da zuwa yazrin tayi mishi tanajin yanda kanshin turarenshi yanadan tadamata da zuciya, dukda yana mata dadi on normal days amma indai zata fara ciwo da shi take ganewa, dan koyaya kanshin turare yake indai bana incense ba irin na gida toh saiya fara tada mata da zuciya. Sama sama ya ansa ta ba yabo ba fallasa sannan aka fara cin abinci. Yauma kamar kullun amrah ta tashi tayi serving kowa banda yazrin, yazrin ta tashi ta dauki falafel mai beef and cheese fillings da chicken salad ta zuba ta fara ci kwata kwata batada appetite dan har daci daci takejin abuncin na mata. Hira suka fara tsakaninsu ayaan na basu labarin yanda ya gudu daga dubai yatafi russia batareda sarauniyar dubai ummin azlan ta sani ba, dan idan har kaje gidanta toh baka isa kabar kasan kaje wata kasar ba saidai idan ka dawo gidanku sunganka sannan ka juya ka tafi inda zaka, dan mugun tsoro ne da ita especially na tafiya, shiyasa hardly zakaga tabar dubai taje wata kasar. So yana basu labarin yanda yatafi russian, mamah ce kuma ta tambayeshi gurin wayaje a russia, bai bata amsa ba, daidai nan wayanshi tafara ringing. Amrah ce tai saurin daukan wayan nashi, tana juyoma kowa da screen din dan suga wake kira tana dariya kaman ba itaba. Face time ne ake kira video call an rubuta my fav cousin a jiki da heart and padlock dakuma ring emoji a gaba. Harara ya wurga mata sannan ya mika mata hannu alaman ta bashi wayan, ba musu ta mika mishi tana maida mai da hararan cikeda zolaya, lokacin har wayan ta tsinke. Dan typing yayi a wayan sannan ya mayar ya ajiye. Daddy ne ya juyo inda yake sannan yadan gyara murya alaman zaiyi wata magana mai muhimmanci kenan. Yazrin da hankalinta kechan wani guri kaman bata cikinsu tayi saurin dago da idanunta ta kalleshi, hakan yasa dan kwallan dake gefen idonta tun dazu ya zubo. Sauri tayi tasa hannu ta goge batareda wani yaga halin datake cikiba dan kusan kowa ma ya manta da ita a cikin dakin. Daman idan har kaga yazrin tana cikinsu ana hira da nishadi to tsakanin amrah ko ayaan waninsu bayanan, indai ko duk sunanan gakuma azlan toh mantawa akeyi da ita, abun na mugun taba mata zuciya dan nuna mata sukeyi kaman ita ba cikinsu takeba. Cikin no nonsense voice daddy yafara magana “ ayaan yaushe zaka fito da mata ne? Idan bason yarinyan nan adaab kakeyi ba kafito ka gaya mana sannan ka nemo wata ko mu nemo maka, kai ba yaro bane shekarunka 30 a duniya, sannan azlan nayi magana da abbanka nanda 1month zamuzo ayi engagement party naku kaida amrah, a ranan za’a daura aure saidai bazaku tareba harsai ta gama university nanda 6months kenan, ke kuma yazrin, na yanke shawara nida mamanki zamu hadaki da amrah, ridwan zaizo gobe yaganki, sannan kada nasakejin abu makamancin wanda yafaru tsakaninku yau, idanba hakaba zaki ansa hukunci kamar yanda tsarin masarauta ta tanadar”. Wani irin sarkewa nunfashinta yayi jin irin kalaman da daddy ya furta, she can’t believe it . Kodai kunninta kemata gizo? Dan bata taba tsammanin daddy zai iya mata hakaba. Meyasa zaiso ya hadata da mutumin daya kusan haifanta, mai yaya da mata duka duka shekaranta 17, dan ridwan na farko faryal shekaranshi 17 shima, infact class dinsu daya a school. Kodai daddy ya manta da alkawarin dayayi mata ne?, kokuma ya mata cewa matar sa cousin dinsu ne?. Baki ta bude tanaso tayi magana amma ta kasa, kanta yayi mata wani irin nauyi, dakyar ta daga ido ta kalli mamah wanda ta sauke kanta tana yanka beef walington dake plate nata, babu wani reaction a fuskanta alamun tasan da maganan kenan. Wani sharp pain ne ya daki kirjinta daseda tayi kara, kowa a table din saida ya dago kallonta, tayi saurin dafe kirjinta tareda kokarin tashi ganin idon kowa na kanta. Dan layi tayi kaman zata fadi dan saurin mikewan datayi, saidai batai wata wataba ta nufi hanyan fita dakin tanajin dariyan amrah. Straight waje ta fice bata ko ganin inda take bi dakyau dan dishi dishi idonta keyi. Wajen palace din tayi tana tafiya a hankali tana dan tangal tangal kaman wanda tasha wani abun bugarwa. Takai wajen 1hr tana tafiya a haka batayi ko rabin fita daga fadan ba, wata mota blue ferrari ta tsaya gabanta. Glass din mazaunin driver dake side dinta aka bude, wani hadadden saurayi ne bazai wuce 17-18 years ba a ciki, face dinshi yayi kama dana amrah sosai hatta eye color dinsu da eye shape dinsu iri daya ne kaman twins. Cikin voice dinshi wanda dakaji kasan irin shagwababbun yaran nanne masuji da mulki, skin dinshi har wani glowing yakeyi kana ganinshi kaga dan hutu. Cikin voice dinshi da kanaji kasan yana vaping a wani hankali yayi mata magana cikeda zolaya “ yazrin baby an koreki daga gida ne? Ko kina missing dina ne kika fito?”. Tsayawa chak yazrin tayi jin muryan bestfriend dinta kuma cousin dinta, da sauri ta juyo suka hada ido ya wani juya mata ido kamar mace, nan take kuma taji zuciyanta tadanyi sanyi. Zagayawa tayi passenger seat kafinma takai kofan ta bude authomatically, shiga tayi kofan ta rufe yaja motan tana sauke nunfashi da karfi da karfi. Sunkai wajen 10minutes suna driving motan tayi tsit bakajin komai sai karan AC dakuma kanshin turarenshi saint lauren, sannan suka fita daga masarautar. Sai a lokacin taji hankalinta yadan kwanta sannan kuma gajiya ta fara saukan mata. Dan reclining kujeran tayi tana gyara zaman ta, sannan ta daga kafafuwanta dasuke mata zugi ta daura akan saman kujeran tana rumgume gwiwoyinta. Juyowa faryal yayi yana kallon yanda jikinta kedan rawa ta rungume kanta, mayafin abayan datasa ya sauko wuyanta gashinta datayi parking dinshi into a bun a waje. Gaban Wani katon high rise golden building suka tsaya an rubuta zeyz massage palour. Parking lot suka shiga yayi parking motan a vvip section sanna ya juyo ya kalleta. Idanunta ta a rufe tashiga tunani kaman mai bacci da alaman batamasan anyi parking motan ba. Hannu yasa ya ja kumatunta cikin zolaya, dasauri ta dago rinannun idanunta ta daura akanshi. Wani cool smile yayi mata yana fadin “ whats up babygurl, an daura aurenki da oldman dina ne?”. Yan fada yana kyalkyalewa da dariyan mugunta. Kafa mishi ido tayi tana kallonshi, tama rasa mezata fada, take hawayen dake bayan idonta suka zubo. Dariyan dayakeyi ya tsayar yana kallon yanda take kuka, saikuma cikin serious voice yace “ don’t worry, munada time ai, sai nanda 3months kafin nan we will figure out yanda zakiyi, bazan bari ki auri wanda bakya so ba, besides idan kika auri oldman dina dole nace miki anty, kuma kinsan hakan bazai taba yuwuwa ba, nagirmeki ko kinaso ko bakyaso, dan haka ki kwantar da hankalinki”. Yana fada yana shafa kanta kamar wata yar baby. Hugging dinshi yazrin tayi tanajin kalaman daya fada, a bangare daya hankalinta yadan kwanta jin cewa sunada time kuma yana bayanta, saidai kuma tasani sarai cewa tunda akayi maganan nan tsakanin daddy dakuma ridwan to lallai yan fada sunsan da maganan, sannan sarki baya magana biyu so kotanaso kobata so dole ayi auren. Rumgume shi tayi koba komai atleast tasan akwai wanda kebin bayanta, shima hugging dinta back yayi. Cikin voice daya shake tadan dago kanta daga jikinshi “ kasan bazasu chanza magana ba, dan haka dolene auren nan, saidai idan guduwa zanyi”. Kallonta yayi sannan yace “ toh ki gudu kije ina, duk inda kikaje zasu nemoki, kinkuma san hakan ne zaisa a tsaurara miki, abu biyu zakiyi dazaisa daddy ya yarda ya barki kiyi making decisions dinki dakanki, na farko shine ki fara ciwo, ki bari ciwonki ya dawo sosai to the point bama za’a iya maganan yimiki wai abu banda magani ba, saidai kinsan hatsarin ciwonki, daga haka zaki iya rasa ranki, sannan kuma kina warkewa za’a sake tada maganan, dan oldman mugun sonki yakeyi bakuma zai hakura ba”. “ “ na biyu kuma shine kisamu wata masarautar suyi proposing aure, kinga dole sheikh zai yarda tunda idan bai yarda ba za’a samu rabuwan kai a tsakanin masarautun Middle East. Amma matsalan shine sai dole a cikin masarautun Middle East, sannan saikin samu prince da bashida aure sannan kuma zaki iya auren shi, amma wannan bashine mai wahalan ba, dan akwai su dayawa saikin zaba, mai wahalan shine yanda zamuyi mu samu attention dinsu, indai ba azlan zaki kwace ba, tunda dama chan ke kika fara cewa kina sonshi kafin amrah”. Ajiyan zuciya ta sauke tana sakinshi tareda komawa ta jinginada seat din, laushin kujeran na karamata nutsuwa tareda solutions dinda faryal yakawo. Kusan minti biyar tana tunanin meyakamata tayi, options dinta biyu ne kadai, saidai option nafarko bata tunanin zaiyi aiki “ faryal option na farko fah bazai yi ba, dan kasan idan har nabari nakara ciwo mai tsanani koda kadan ne zai kara sawa ana kallona kaman wanda bazata iya komai da rayuwanta ba sai abunda aka yanke mata, sannan daddy zai kwace position dina a library yaba amrah, idan hakan ta faru kuma babu wani abu dazan karayi a masarautar, dan haka nida banza daya nake, daddy da mamah sunfison amrah da ayaan, dan gani sukeyi banida amfani bakuma na kara komai a cikin masarautar, shiyasa ma suka bawa ridwan aure na, dan na tabbatar idan amrah ce bazasu taba yimata hakaba”. Tafada cikin kunan zuciya. Dan sunnar da kanshi yayi bama yaso ya rarrasheta, dan baisan mezai fada mata ba, da yanada yanda zaiyi bazai taba bari yaganta a cikin wannan halinba, saidai rayuwa yanda tazo maka haka zaka bita. Amrah tayi sa’a, tanada kyau, ga ilimi da hankali, takuma iya harka da mutane kamar hawainiya haka take. Dan haka tun tana karama kowace masarauta da manyan yaran shugabannin kasashe da iyayensu kowa burinshi ace danshi ya auri princess amrah, gashi Allah ya bata farinjini, daddy da mamah kuma sunmata training mai kyau, sannan duk wani abu na masarauta musamman a harkar bincike da history tasani, sannan taci manya manyan competitions na duniya ba saudaya ba basaubiyu bah, dan haka duniya tasanta, gashi batada tsoro tanada courage sosai dake burge mutane, duk abunda tasa kanta yi saitayishi, har fan pages gareta tanada millions of followers a instagram, da fan accounts dake posting dinta, da irin fashion din datakeyi, da

Chapter 2 of 11