Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Taji fitowanshi sarai da tsayawanshi. Hada ido sukayi ta sakinmai wani sassanyar murmushi. Mayar mata da murmushin yayi sannan yace “ Alina yau kece a gidan namu? Ai nazata kin manta da kawar takine”. Bata chanza fuskartaba still da smile din a face dinta tace “banida time ne kasan yanda abubuwa suke. Amma yanzu gani nazo. Tun last month nayi mata alkawarin zanyi finding time nazo”. Gyada kai yayi sannan yace bari yaje yayi sallah ya dawo. Da ok ta ansa mishi sannan ta dauke idonta daga kanshi takoma danna wayarta. Bai tafiba immediately saida yakusa 1 full minute yana kallonta sannan yafice daga palourn. Tanajin fitarshi ta dago daga kallon wayar datakeyi tana sauke ajiyar zuciya. Daman tasan hakan zata faru dan ba karamin mutun bane dole zai gano da wani abu a kasa dukda bai nuna ba amma zuwanta gidan bayan wajen shekara daya rabonta dazuwa dole kobakayi dogon tunani ba kasan da wani abu. Daga kafadunta tayi aranta tana fadin toh seme? Itadai tasan dole plan dinta yayi working, ko akan wane kuwa. Saita tozarta Hussain tamishi abunda bai taba tsammani ba. Bakuma wanda zai iya mata wannan sai Daddyn Tariha. Da alama kuma bazata sha wahala akan hakan ba dan kwallonta tariga tashiga raga. Kuwait…. A bangaren Yazrin kuwa bacci ne ya kwashe ta saidai a wahale tayi baccin. Koda ta tashi still kata baibar ciwo ba infact karuwa yayi ga bayanta dake zugi kamar an saka mata shocking. Kamar tay kuka haka ta tashi daga kwanciyan datake tanajin jiri na dibanta. Dakyar tasamu jirin ya lafa tafara tafiya zuwa toilet dan wanka takeson yi. Tuna tanada ciwo a baya ne yasa ta komawa ta dauki watarta sannan ta danna wa Dr. Katherine kira. Saida takusa tsinkewa sannan ta dauka. Gaisawa sukayi sannan ta tambayeta zata iyayin wanka? Yes ta ansa mata saidai tace kartayi anfani da ruwan zafi sosai. Kashe wayar tayi batareda ta ansata ba ta shige wanka. Bata dadeba ta fito ta sa wata pure cotton night dress doguwa har kasa sannan ta fita daga dakin don yin exercise. Waje ta fita kanta dake ba dankwali gashinta a sake ya barbazu dadan danshi a jikinshi bata tsaya tayi drying dinshi sosai bah. First floor ta sauka sannan ta fice daga cikin mansion din gabadaya tayi left. Hanya ce sambal dake zagaye da flowers da short short trees babu security ko daya a gurin dan guri ne dasu kadai ke zuwa dantin trecking sudan motsa jiki. A hankali take tafiyar tanajin jikinta na saki sabanin dazu dayawani rike. Takai wajen minti goma tana tafiyan tana tunanin wannan riddle din data karanta last, wani tunani ne yafado mata shin kodai ansar nacikin rubutun ne? Kokuma …. Tayi nisa cikin tunanin bata ankara ba kawai taji an bangaje mata kafada. Wani juyowa tayi cikeda bacin rai tana kallon wanda tasan inba itaba babu wanda zai mata hakan a gidan. A harzuke tana tamke fuska kamar ba itaba tanuna Amrah tana fadin “ Amrah ni zaki buge? Duk girman gurinnan bai miki ki wuce ba saikin bigeni zaki wuce”. Tana fada tana nuna kanta. Tsaki mai sauti Amrah tayi itama face dinta a tamke ba annuri ta ballama Yazrin harara cikin wannan voice din nata mai bakanta ma Yazrin tace “ Oh. Dukana zakiyi kike daga mun murya? Idan nace zanbi takanki nawuce akwai wanda ya isa ya hanani ne? Kokuwa kina ganin kin samu tsoho zaki aura wato yanzu kin girma ko? Har kun fara fadan kishi kamar mahaukata kinje ana dukanki a banza zakizo ki huce a kaina toh idan kin manta waye Amrah zan tuna miki yau basai gobeba ki bata mun rai kigani”. Jin maganganun tayi suna wani sukanta batareda tayi wani tunani ba tafurta “ Kiyi abunda zakiyi Amrah. Duk rashin mutuncin dakike ji dashi ki rike shi inda kike karki kawoshi gurina ki kama girmanki”. Kafin tarufe baki ji tayi kawai Amrah tayi wani ihu tareda zubewa a gurin…… For more information ga wattsapp number na 09157578540. Game of puzzle (Wasan sarƙaƙiya). By Aryaah Riyad.. Book one 1… Chapter 17… Stars talented writers….. Kafin ta rufe baki ji tayi kawai Amrah tayi wani irin ihu tareda zubewa a gurin Tana rike ciki tana jujjuya kai. Sakin baki Yazrin tayi tana kallonta. Tama rasa mezatayi a gurin ganin iskancin da Amrah keyi. Sanin cewa matsala takeson ja mata yasa kawai ta juya batareda takara kallon inda Amrah take kwance ba ta koma sama zuwa dakinta cikin dan sauri sauri tasa lock ta rufe kofar. Anan kasa ta baje gurin book shelf tana cire tunanin abunda zaije ya dawo dan tasan dole yau tana cikin bala’i tunda Amrah tafara wannan rashin mutuncin bazai wuce zataje tace ta daketa a ciki bah su daddy subi bayan Amrah su bata mata rai gaba daya. Inda sabo ta saba dan haka kawai ta cire tunanin a ranta tafara jero words na riddle din tana furtasu a fili. Da wani sauri ta mike ta nufi bed side drawer dinta ta dauki phone dinta tareda shiga safari tayi searching shekarar haihuwar dan samrah salim na farko. A shekarar kuma mahaifiyarta ta rasu wanda idan har ta alkantashi da riddle din zaizama ansar shi na nufin rashi baya hana samu. A kuma yanda akayi structuring dinshi ansar bazata zama hakaba. Kara karantoshi tayi tana tauna kalaman, gadai ansar tasamu amma bashi bane. Saitayi anfani dashi zata gane menene gaskiyar ansar. Magana ce cikin magana. Komawa tayi tana karanta history din lokacin a wayarta, saidai babu wani ishashen bayanai dazai ansa mata. Sosa kanta tafarayi dukda ba kaikayi yake mataba. Wani irin sara mata yakeyi kamar ana buga mata guduma. Nunfashinta na zuwa da karfi da karfi saidai bata tsaya bintakan hakan ba dukda irin azabar dayake mata. Ajiye wayar tayi ta jingina kanta dayayi nauyi a book shelf din. Tunaninta ya hade gabadaya ga Amrah data kasa fita daga cikin ranta tasan nan bada dadewa ba za’azo nemanta. Takai wajen 1hours a zaune a haka ideas na running a kanta kafin ta dauki notebook data fara rubutu a ciki tana kallon ansarta na farko dana biyu. Ansa ta biyu take kallo. Indai ansar yazama Power to kenan samu da rashi zai zama sai kayi sacrificing wani abu sannan zaka samu wani. Da sauri kuma ta rubuta hakan kamar mai tsoron a kwace mata. Ajiyar zuciya ta sauke tana rufe book din dan bama zata iya kara wani abu yanzu ba. Kwankwasa kofar dakinta da akayi da karfi yasata zabura kanta ya bugu da wood na shelf din. Dan kara tayi tana dafa gurin jin ya tsananta mata ciwon kai datakeyi. Da sauri kuma ta mike saidai bata ansa ba. Kara kwankwasa kofar akayi kamar za’a ballata muryar Daddy na shigowa ta waje. “ Yazrin idan baki bude kofar nanba saikinyi regretting abunda zanmiki wlh”. Jin muryar shi babu alamun wasa kwata kwata a ciki yasa taja nunfashi sannan a hankali tana jan kafafunta dasukayi mata nauyi ta bude kofar hannunta nadan rawa. Aranta tana ayyana dama bata tsaya ta kula Amrah bah duk ciwon nanne ya dagula mata lissafi batamasan sanda ta mayar mata da maganganunba. Bata karasa bude kofarba aka turo ta ta waje saiji kawai tayi an dauketa da wani azababben mari da saida ta dauke wuta gabadaya. Zubewa tayi a kasa tana dago hannunta dake rawa tareda rike kuncin ta tana dago rinannun idanunta dasuka cika da kwalla tana kallon daddy. Tunda take Bata taba tunanin daddy zai iya daga hannu ya daketa irin hakaba. Idanunta datake ganin dishi dishi ta kura mai tana mai wani irin kallo da saida yaji kallon a zuciyarshi. Saidai tuna yanda yaga Amrah yasa ya rufe idanunshi kawai ya karaso cikin dakin. Mamah ce bayanshi saidai bata shigo bah kawai bakin kofa tasamu ta tsaya tana binta da kallon bacin rai. Daddy yasa hannu ya dago ta tamike tana kawar da kanta, cikeda bacin rai dawani murya da sau daya tataba jinta a rayuwarta lokacinda alakarsu da Amrah ta lalace yace “ Yazrin kina abubuwan dakika ga dama a gidan nan narabu dake yaushe nace kada ki kara fita batareda niqab ba kinji magana na? Kina abubuwa kina boye boye kina tunanin idan muka duba bazamusan mekikeyi bah? Yanzu kuma Yar uwar taki kike son ki kashe? Kinada cikakken hankali zaki dauki daga kafa ki buga mata a ciki? Kinsan cikinta ba lafiya gareshi bah shine kikeso ki karasata koh? Itama tazama irinki mara anfani tadawo ta zauna mana a gida daga wannan magani sai wancen?”. Saukan maganganun nashi takeji a cikin kokon kanta. Irin zafi da radadi dasuke mata bata tabasanin akwai ciwo mai azabar hakaba. Mara anfani! Mara anfani! Shine abunda yeketa yawo a cikin kwakwalwarta tanajin yanda zuciyarta ke radadi. Hannunta ta daura kan kirjinta saboda azaba, ga kai saita rasa dame ma zata ji. “ Ana tausayinki ana komai kinsan irin azabar danaso nayima Matar Ridwan Marwa akanki? Na nunawa kowa cewa ke yata ce babu wanda ya isa ya taba mun ya yazauna lafiya? Kinsan irin zafin danaji abunda tayi miki shine zaki zo kiyima yar uwarki irin wannan aika aikan? Toh daga rana irin tayau duk abunda wani zai miki saidai yayi miki babu abunda zanyi akai. Kije ke da bakin zuciyarki nacire hannuna a lamarinki”. Cigaba da masifa Daddy yayi yana gaya mata maganganu masu zafi cikeda bacin rai. Mamah na tsaye bata sa baki a ciki bah. Yakai wajen 10minutes yanayi yazrin harta soma dena jinshi Ayaan ya shigo dakin. Hakuri yaba daddy dakyar dai yajashi suka fita maah tabi bayan daddy. Dawowa yayi dakin yasa hannu ya dagota tana zube a kasa jikinta duk ya saki. Kan bed ya ajiyeta sannan ya shafa kanta murya kasa kasa yace “ Yazrin abunda kikayi baki kyautaba, kema kinsani dan haka duk abunda daddy yayi miki bakida hujjar nuna anmiki wani abu ba daidaiba, ki gyara halinki kiso yar uwarki amrah duk fushin dayayi saikiga ya sauka. Kije ki ba Amrah hakuri sannan kiba Daddy da Mamah hakuri ko kyasamu abubuwa su daidaita kafin kibar gidannan. Kada ki kafi gidan miji da fushin iyaye akanki”. Gyada mishi kai kawai tayi dan so take kawai ya fita ya bata guri. Babu wani abu dazasu fada mata. Shima bai zauna ba yajuya ya fita a dakin tareda rufe mata kofa. Kanta ta daura kan kwaiwoyinta tana jin yanda hawaye ke zarya daga idanunta zuwa kan fuskarta. Wato babu ma wanda ya tambayeta meya faru? Basu jira ansartaba bama sa bukatar ji daga bakinta. Babu kokwanto a cikin zukatarsu cewa zata iyama Amrah haka. Kokuma ma Amrah tayi mata wani abune ta rama. Bama sa wannan tunanin so dasuke ma Amrah ya rufe musu ido sun kasa ganin laifinta sai nata. Qatar…. A bangaren Alina kuwa Tahira ta kawo mata tea tadan sha dukda batayi breakfast ba amma batajin yunwa ko kadan so kawai dan sipping tayi ta ajiye. Tahira ta tasata da kallo kamar ta samu TV ganin dan shan datayima tea din yasa a shagwabe tace “ Sis Alina dan shan dazakiyi kenan dama? Kinsan wahalar danasha kafin nasamu na dafa miki tea dinnan? Dan Allah ki kara banason ki zauna da yunwa. Ko baimiki dadi bane na hado miki wani?”. Dan girgiza mata kai Alina tayi tanajin Surutun Tahira na damunta. Shiyasa bata cika son hada abubuwa da yarinyarba tacika surutu, ita kuma abunda bataso kenan a duniya hayaniya da surutu. Saidai jin bazata iya yimata basaja bane bakuma zata iya tace mata dama ba yunwa takeji ba kawai so take su hadu da daddynta sannan bataso Tahira ta kasance a gurin dan bazata barshi yasa attention dinshi issashe a kanta ba yasa tace ta hado mata tea kawai ta dauki cup din takara sipping ahankali tareda ajiyewa. Tahira ganin dagaske basha zatayi ba yasa kawai ta dauki cup din Alina ta kurbe shi tunda bawani yawane dashi ba duka duka karamin cup ne dan dama tasan batacin abinci da yawa yasa ta zubo matashi dan kadan haka. Surutu tafara mata akan school tana cikin yi kuma takoma kan friends dinta. Bata karasa ba takoma bata labarin saurayinta sai blushing takeyi tana kada kafa kamar tana ganinshi a gurin Alina kamar tasa ihu takeji sosai surutan ke damunta saidai bata nuna a face dinta ba. Infact tanama ansa mata dan dama tasan da hakan. Indai Tahira ce to dole kagaji da surutunta duk sonka da magana dajin hira kuwa. Agogon hannunta ta kalla ganin yanzu yaci ace zun idar da sallah yasa ta gyara zaman Alkyabbar a jikinta cikin dabara sannan tadan matsa gefe akan kujerar datake kai yanda idan ya shigo koda Tahira ta mike bazata kareta daga ganinshi ba sannan shima yana shigowa ita zai fara gani. Ba dadewa ya shigo cikin palourn yana bakinshi dauke da sallama. Ansa mishi Alina tayi cikin style da saikayi da gaske zaka tantance shi daga muryarta nayau da kullun saidai yanda zai sauka a cikin kunnin mutun dole hankalinshi ya dawo kan mai maganar, ga Allah ya bata murya takuma iya anfani da ita. Tunda yashigo idonshi ke kanta ga yanda ta ansa mishi sallamar shidai bazaice bahaka maganarta ko sautin muryarta yake ba bare yace iyayi take mishi saidai kuma sosai yakejin duk wani motsinta dakuma magana datakeyi har cikin zuciyarshi. Astagfirulla ya furta tuna cewa yanada mata har biyu ga yarshi dake sa’ar ita Alina bai kamata ace yanajin irin wayannan abubuwan akan wannan karamar yarinya dabai wuce ya haifeta ba, so yayi kawai idan ya dawo ya hayewanshi sama batareda yabi takanta ba jin yanda ta dagula mishi lissafi a gurin sallah saidai kara ganinta dayayi irin zaman datayi mai daukar hankali, ga lips dinta dayasha bold red lipstick na daukar hankalinshi, idanunta kuwa basai an fada ba sunfi komi rikitashi, ga alkyabbar ta zauna a jikinta kamar a jikinta aka dinka yanda take haka idan ka shigo falon baka isa ka kalli wani abun da ba ita bace sai kyalli takeyi kamar tauraruwa. Hin bazai iya daurewa bane gakuma dama matanshi duk suna Uk daga shi sai Tahira a gidan yasa kawai ya karaso inda suke. Tunani yakeyi meya kawo Alina gidanshi yau yasan tanason Tahira amma idan Alina daya sani ne toh lallai saidai ta kira Tahira a waya ita taje inda take, badai Gimbiya Alina Bin Rayyan ta tako har inda takeba dasunan gaisuwa. Wani tunani ne yafado mai toh ko gurinshi tazo? Saidai baiyi kan tunaninba tunda mezatazo tayi gurinshi, indai akan Hussain ne yasan bazata taba tambayar wani taimako ko wani abu makamancin hakan ba, yarinya ce mai mutumar jida kanta da baka isa wai tazo ta nemi taimako a gurinka ba, duk irin halin da zata shiga kuwa. Opposite Alina ya zauna yana kallon kirjinta dake walwali yashi glitters gashi fari tas har wani pink pink yakeyi. Alina na kallonshi duk wani motsi dayakeyi, tun daga kan yanda ya shigo ta ansa mishi sallama yanda yadan dakata da tafiyar dayakeyi kafin yacigaba, dakuma yada yake tafiyan a hankali kana gani kasan tunani yakeyi. Takuma lura da yanda ya shigo yanda ya karkata kana gani kasan baiyi niyyan zuwa inda suke ba, saikuma ya juyo ya nufo su. Murmushi tayi aranta dabai samu damar fitowa waje ba. Tayi tunanin zata sha wahala kafin tasamu kanshi ta aiwatar da abunda take shirin yi, saidai ga mamakinta kuma saitaga komi na tafiya smoothly. A kasan zuciyanta kuma tunani takeyi anya baiga cikin plan dinta ba? Dan ba karamin mutun bane. Dan duk mutumin dazata sauke kanta tazo inda yake hartayi mishi basaja toh ba wanda zakayi ma wayau cikin sauki bane batareda ya gane wasan naka ba tun kafin ka farashi kuwa, dan indai plan dinta yayi yanda takeso toh nanda kwana 5 zatayi tagama. Zata kwatar ma daddy yancin shi, sarautarsu tadawo hannunsu, ta tozarta hussain sannan tasa a ratayeshi a tsakiyar gari, shikuma daddyn tahira zatasan yanda zatayi dashi bayan tagama anfani dashi don cinma burinta. ( toh fah. Akwai chakwakiya. Me kuke tunanin Alina ke shirin yi? Wani plan take nufin aiwatarwa sannan anya Daddy tahira bazai ganota bah?). for more information ga wattsapp number na 09157578540 End of book An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 11 of 11