Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
gane mene ya faru, indai kwakwalwan ta bai fada mata karyaba kenan uncle Hussain yaudaranta yayi, kenan dama documents din dayasa ta dauko wannan abun zaiyi?, dukda batason daddynta amma batayi mishi tsanar dazaisa har tasa hannu akan lalata miahi rayuwa ba, dan kuwa tunda aka kamashi to yagama yawo, bincike zaayi sosai akanshi kuma duk kankantan laifi in aka sameshi dashi babu makawa sai an zartar mishi da mummuna hukunci, hukuncin ma na sarakuna dan nasu yafi na sauran mutane tsauri. Idanuwanta ta mayar kan kuyangu dake tsaitsaye suma alaman abun ya tabasu sannan ta janye, koda babanta bashida gaskiya bai kamata Hussain yayi mishi irin wannan cin mutuncin nan ba, amma indai yakasance sharri akayimai to lallai bazata yardaba, zata kwato mai hakkinshi zakuma ta tabbatar ta dandana ma uncle Hussain kudarsa, dan lallai Hussain baisan wace Alina ba. Karan kukan Ummi da taji ya katse mata tunaninta, da sauri tayi hanyan inda tajiyo kukan, a hallway ta sameta ta zauna ta saka kanta tsakanin gwiwoyinta tana kuka, ga wasu kuyangu nan sun zagayeta duk sunyi cirko cirko sun rasa yanda zasuyi. Da sauri ta karasa gurinta ta tsugunnan tana tambayanta ya akayi. Cikin raunin murya Ummi ta dago ta fuskanci Alina “lina daddy yace babu ruwanshi da harkanmu, yace kar na kara kirashi, mommy taki daukan wayan, Sheikh Abduljabbar yace kada na sake kiranshi, bazai sa kasarshi cikin wannan rikicin ba, bamuda kowa!, kowa ya juya mana baya lina mun shiga uku”. Wani irin tukin bakinciki Alina taji ya tsaya mata a makogwaronta, dama shiyasa kwata kwata bata son shiga harkar familyn su, duk tasan basonsu sukeyi ba, yanzu gashi tun ba’a kai ko inaba an juya musu baya. Daurewa tayi ta dago ummi sannan ta nufi hanyan daki da ita, saidai kafin su karasa wasu sojoji suka tsayar dasu. “ madam order daga sama, an baku 10 minutes ku fito kubar cikin palace dinnan, sannan ba’a yarda dayanku yaje wani properly dayake under sunan Rayyan ba, bakuma zaku dauki wani abu dake cikin gidannan ba koda kayan sawa ne, your time starts now”. ( toh guys, ga Alina… yakuke ganin wasan zata kaya? Shin sharri akema Sheikh Rayyan kokuma ya aikata wani abun ne ? Sannan Alina zata yarda a koresu daga gidan dasuka tashi a ciki?)… yanzu wasan yafara… For more information ga wattsapp number na 09157578540. Game of puzzle (Wasan sarƙaƙiya). By Ayraah Riyad… Book one 1… Chapter 7…. Kuwait, Bayan Palace….. ( masarautar kuwait). A bangaren Yazrin kuwa kwankwasa kofar da akayi yay mummunan razanata, kardai ace har yaga wayar? Karkarwan da jikinta keyine ya tsananta, saidai jin an kara kwankwasa kofar yasa tayi tunanin kodai ba daddy bane, dan idan har shine bazai tsaya kwankwasa kofar dakinta ba tuni yashigo. Saurin gyara face dinta tayi ta goge hawayenta sannan taje ta tashi ta bude kofar dakyar tsabar rawan da hannunta yakeyi. Wata kuyanga tagani tsaye a bakin kofar da tray a hannunta, sai plates da aka zuba mashed potatoes and stirred garlic beef a gefe da cup of water, gaisheta tayi sannan ta dukar da kanta batareda ta kara kallonta ba. Nannauyiyar ajiyar zuciya ta sauke sannan tadanyi mata smiling tace ta shigo ta ajiye, tana ajiyewa ta fice ta rufe kofar. Kallon abincin tayi kan side drawer dinta, bawai tanajin yunwa bane dan bata jin zata iya cin abincin saidai tasan idan bataciba dole za’a zargi wani abu, dan haka kawai saita koma bed din ta zauna sannan ta dauki plate din. Tana daga plate din taga wannan bakar envelope din kasan. Waro idanunta tayi tana maida idonta a sukwane kan kofar. Da sauri ta tashi da gudu gudu ta bude kofa tay waje, saidai ina bataga kuyangan data zoba. Kamar ta bita saikuma ta tuna ai tasanta, inkuma tabita dole mamah zata tambayeta metaje yi part na kuyangu a darennan, dan haka komawa dakin tayi tana buga tsaki. Envelope din ta dauka ta ciro takardar dake ciki ta bude. Kamar yanda akayi wancen rubutun haka akayi wannan, saidai wannan layi uku ne a ciki. “ Idan Bakyason Abduljabbar yaga wayarki, idan time yazo kada kiyi shaida, idan kin aminta ki mayar da paper ki ajiye, idan kuma baki aminta ba ki yagata ki zubar”. Tadade tana kallon takardar, tama rasa mezatayi, me suke nufi da shaida? Wani lokaci? Wakuma zata shaida? Sannan waye ke turo mata. Brain dinta nakara bata Ayaan ne saidai kuma tasan bazai taba yuwuwa ace shine ba, bashida dalilin yin hakan, sannan mesuke nema a gareta? Idan taje ta shiga abunda zai lalata mata rayuwa fah? Sannan tasan idanta fara abubuwannan bazata iya fita ba. Dan da dukkan alama wanda ke wannan abun ba wanda zata iya bugawa dashi bane, wanda zai shigo har cikin gidansu, yakuma san duk wani motsi datake yi, sannan taya sukasan tabar wayanta a office na daddy? Dukda cameran shiga a kashe take, sannan tanada tabbacin cewa babu camera a ciki saboda bayanan sirri dake ciki. Lallai akwai rikichi. Saidai tuna cewa duk wannan na nuna daddy baiga wayarba tukunna yasa taji hankalinta yadan kwanta. Batareda tabari wani tunani yashige ta ba kawai ta ninke takardan ta mayar cikin envelope ta ajiye, ta dauki meshed potatoes din tafara ci, da duk wani abu dazai biyo baya yanzu bashine a gabanta ba, dan gwara komai akan daddy yasan ta shiga cikin office dinshi. Tana gama ci ta hada da beef din ta cinye gabadaya ciki ta ya cika sosai da dakyar tasha ruwa ma sannan ta mike ta nufi toilet tay wanka sannan ta saka pjs white. Fitowa tayi tanajin yada jikinta yay dadi dukda batada wata cikakkiyar nutsuwa. Tuna haryanzu batayi checkup dinta ba yasa kawai ta dauki abaya tasa ta fita babu ko dankwali ta saki gashinta dake kyalli yayi wasu inconsistent messy waves daya kara mishi kyau. First floor ta nufa dining room nan ta iske su kowa da kowa akan dining din, harda Azlan datake tunanin yatafi saidai banda Daddy, bata ganshi a ciki bah. Gurin Ayaan taje ta dauki wayarshi dake ajiye akan table kusada plate dinshi. Dago kashi yayi ya kalleta, sakin mishi murmushi tayi sannan tamika mai wayar alaman ya bude mata. Ganin kowa na kallonta ne yasa ta dago itama tana binsu da ido tareda daga gira alaman yane. Mamah ce ta girgiza kanta tanabinta dawani kallo da kai tsaye bazaka kirashi da kallon banza ba, cikin kausasshiyar murya tay magana “ yazrin sai yanzu ake saukowa yin dinner? Bazaki taba chanza halinki kizama mai hankali cikakke ba, kullun sai ana binki yi wannan yi wanchan, baki ganin Amrah ne? Bazakiyi koyi da itaba?”. Sakin baki tayi tana kallon mamah, ita maganan ma bai bata mata raiba, infact mamaki kawai yabata. Yanzu zasu gane cewa yanda suka daurata haka take tafiya ne? Sun hanata yin komai, duk wani abu daya kamata subata tayi sun dauka sunbaiwa Amrah, yanzu kuma tazo tana mata complain. Itama hada rai tayi sannan ta furta “ mamah ai yanda kuka tasardani kenan. Inbaki manta ba duk wani abu dayakamata kubani dan nasan rayuwa hanani kukeyi ku dauka kuba favorite dinku Amrah, ni bazan iyayi ba, sannan kuma yanzu ku….”. Kasa karasawa tayi sakamakon wani zafi da zuciyanta yamata. Amrah ce tamata wani kallon rainin hankali, cikeda izza tafurta mata “ kinsan zaren ba kalan yadin bane, na chanchanci abani shiyasa aka bani, wani kuwa koda anbashi babu abunda yai iyayi akai, so ki fitar dani daga cikin bakinki, niba sa’ar yinki bace”. Tana gama fadin hakan ta juya tacigaba davin abincinta. Cije bakinta tayi tanajin wani zafi tundaga kanta har zuwa kafanta, batareda ta kara hada ido da wani ba ta ansa wayar da Ayaan ya miko mata ta shiga contact ls dinshi ta kira Doctor Katherine. Ringing uku ta dauka. Barin gurin tayi sannan tasa wayar a kunni, daga cikin wayar muryar wata dattijuwar mata ne tana fadin hello. Yazrin ta ansa ta sannan ta tambayeta tana ina? Ansa maya tayi dacewa tana gida amma bari ta karaso gurin Yazrin din yanzu sannan sukayi sallama. Mayar mishi wayar tayi still batabi takan kowaba ta juya ta fice. Main palour taje sannan ta shiga wata kofa, hanyace sambal hallway ta kunna fitila tashiga. Tadanyi tafiya kadan sannan saiga wasu kofofi guda biyu. Na hannun damanta ta bude ta shiga. Daki ne kamar ward na hospital, gado ne irin na mutun daya fari an shimfidamishi white bedsheet, bagon dakinma fari da wani katon wardrobe mai drawers aciki, gefe kuma sofa ce doguwa dazata iya daukan mutun 8. Sofan ta nufa ta zauna tana kishingida, maganan da Amrah tayi mata suna dawowa brain dinta. Saurin turesu tayi tadawo da tunaninta kan abunda yakamata tafara dashi. Dan tana bukatan tafara aikin nan da wuri tun kafin amrah tarigata, sannan babu time sosai so tasan amrah zatayi iya bakin kokarinta ta gamashi a wata daya, dan tafara shirye shiryen engagement din. Shigowan mutun cikin ward din ya fidda ta tunanin datakeyi, kobata duba ba tasan Dr Katherine ce, dan a cikin masarautar take kusada su, itace family doctorn su babbar likitace sosai tasan metakeyi. Har inda yazrin take tazo sannan tayi mata wani polite smile tace ta taso ta hawo gadon. Ba musu ta tashi taje gadon ta kwanta tana kallon Dr Katherine din, kana ganinta kasan ta manyanta dukda bawai sosaiba, zata kai wajen 50 years, American ce saidai anan take zama, tana sanye da white short sleeve tshirt dakuma tight mini skirt, gashinta dayake blonde ta daureshi bawani makeup sosai a face dinta very professional. Fara dubata tayi, tanayi tana mata tambayoyi akan jikin nata wannan month din, sosai Yazrin kebata ansa, tana fadamata komai datasan taji a month din, bayan tagama tace mata “ ok everything is good, zuwa nanda gobe za’a aiko miki da magani, ina tunanin a chanza miki ne tunda kince kinajin kamar zai tashi koh?, saidai ina tunanin saboda kindau kwanaki har uku baki sha maganinba shiyasa. Gyada mata kai Yazrin tayi sannan cikin zolaya tace “ Dr nifa naji sauki, maganin nan bawai dadinshi nakeji ba infact kwana ukun nan dabansha maganinba naji dadin jikina sosai naji kaman ya kara kwari”. ba karya tayi ba, dukda cikin zolaya kawai tayi maganan amma dagaske jikinta yayi mata dadi, dan ko dazu databi ta stairs daga part na Daddy bataji wani gajiya sosai ba, da normal day ne datuni kafanta nanan na zafi, saidai tunanin kodan tsorata datayi ne yasa jikinta baima dauki hakanba. Wani iri face din Dr Katherine yayi kafin tayi saurin gyara face din, cikin professional voice kuma tace “ dama magani haka yake, saiya bari ka saki jiki saiya dawo maka, sannan idan ya chapke ka bazakaji da dadi bah dan zai ninka nada”. Gyada kai Yazrin tayi sannan ta mike, itama Dr ta kwashe abubuwan dasukayi gwaje gwajen dashi tana disposing wanda ba’a kara using, sannan ta maida sauran bayan tayi sterilizing dinsu. Sallama yazrin tayi mata ta koma dakinta. A kan bed ta tarar da wayarta tareda…… Qatar. A sukwane Alina ta juyo tana kallonsu, rai a bace ta nufeta tana fadin “ ban ganeba, what type of nonsensical fucking nonsense is this, gidan namu za’a tashe mu, kunsan me kuke fada kuwa, bazamu fitaba karfi ya fitardamu, and you know what? fuck you”. Ta danna nata zagi tareda juyawa ta bi inda ummi ta nufa. Dakin Ummi ta nufa nan ta sameta akan gadonta sai sharar kuka takeyi tana jujjuya kai face dinta yay ja abunka da farar fata, “ Ummi stop crying kuma ki tashi kidauki duk wani abu mai mahimmanci dakike dashi a gidannan, and kar ki biye musu na cewa kada mu dauki komai dayake na daddy, ki dauka duk abunda zasuyi saidai suyi, amma kidena kukan nan ki tashi, nasan dole zasu koremu daga gidannan, nikuma zan tafi part na daddy zan debi cash iya yanda zan iya dan zasuyi suspending accounts dinmu, zan kuma zo na daukan mana kayan sawa, kiyi sauri pls”. Jiki ba kwari ummi ta tashi tafara aiwatar da abunda Alina tace, itakuma Alina ta juya ta fita, harta fita ta dawo tazo ta dauki akwati kato a walk-in closet na Ummi sannan ta zuba wasu ababu a ciki ta fita, cikeda izza take taku dai dai kamar wata model tazo ta wuce sojojin da aka zuba a gidan tashiga elevator ta nufa 5th floor, tana shiga ta tarar babu kowa ciki dukda tayi zaton zataga sojoji, direct study room din daddyn ta tashiga ta bude wani katon safe dayake ta wani gefe, kudade ne jibge a ciki dollers rafa rafa kaman kaya, akirge bazasu kirguba. Cire abayun dake akwatin tayi sannan ta fara jera kudaden a ciki, saida ta kusan cika akwatin tam sannan ta Daura abayun akai ta rufe ta ja handle din akwatin ta rufe safe din tayi waje. Daidai tazo fita saiga wasu sojoji maza dayawansu sunshigo cikin part din, tsayar da ita sukayi sukace bazata fitaba, bata tanka musuba tayi gaba zata fice. Da sauri suka rufe hanyan fitan tareda tsayawa a gabanta, babu tsoro ba komai tasa hannu ta zaro gun daga cikin riganta, gun ce ta gaske The SIG Sauer P365 model, cikeda izza irinta yayan sarakuna tafara musu magana “ koku matsamun koma harbi kaina, kunsan kuma ku zance, and kunsan sauran idan har akace kun harbeni, so kindly make way for this pretty girl, nasan baku taba ganin pretty girl kamana ba, kwa samu na rubutawa a diary yau ranar tarihi ”. Tana gama fadan haka ta bangaje na jikin kofan tayi ficewanta, binta da kallo sojojin sukayi, basu taba ganin mutun haka rayuwarshi an ruguza ta cikin seconds amma ko gezau batayiba. Direct dakin Ummi ta nufa wanda ta sameta harta harhado takardunsu da wasu cash dazasukai 2million Qatar dollars. Sai gwala gwalai data cika wasu katon akwati dasu, ga wasu diamonds ma da yawa sosai duk a ciki. Beautiful face dinta daya kumbura duk ga busassun hawaye nan akai ta dago tana kallon Alina, sannan ta tambayeta a ina zasu tafi. Kai tsaye Alina tace mata a motanta, dama ba kowa yasai mataba, da kudinta ta siya kuma sunanta ne a jikin takardun motan, dan haka babu wanda ya isa yace bazasu dauki motanba. Wasu akwatin suka debo sukasa kayansu a ciki, sannan suka fito waje, tunkafin ma a fitardasu, gwara su tafi da izzarsu. Fita sukayi har waje duk masarautar an cikata da sojoji, sojojin masarauta kuma dole aubi umarnin sama, dan haka suma umarni sukebi. Cikeda izza Alina ke tafiya tareda gangaro akwatina har uku, suna fitowa kuma reporters suka biyosu suna daukar su hotuna tareda tambayansu tambayoyi, saidai basuyi ta kansu ba, bodyguard din Alina ne yataho inda suke da sauri, shi kadaine a gidan ya bujire ma umarnin sama, yanason Alina kamar familynshi take, tun tana da shekara 10 yake a bodyguard dinta haryau, bazai taba yarda wani abu makamancin haka ya hadasu ba. Dan murmushi Alina tayi ganin yataho inda suke, babban sojane sosai, yakai matakin lieutenant yabar aikin yazo yana tsaron Alina, dukda yarinyan bataji amma baitaba jin wai ya tsaneta ba, tana annoying dinshi lokaci zuwa lokaci amma banda hakan sosai yake jinta a zuciyanshi. yanada yarinya kamarta itama bataji kusan halinsu daya da Alina, shiyasa intayi abu saiyaga kaman yarshi ce tayi, amma dukda hakan kuma Alina yarinyace mai tausayin mutane, bartadai da rashin kunyanta. Aiko tana ganinshi ta saki akwatunan tayi tafiyanta zuwa gurin mota, inda akayi parking mata motocin ta guda biyu, daya ferrari ce pink colour, daya kuma pickup truck ce katuwa itama pink color, tana kamada hilux saidai tafi hilux kyau dakuma tsada. Gurin ferrarin ta tsaya tana jiran bodyguard din daya tsaya kwaso akwatinan sannan yazo inda suke, key din motocin ya ciro ya mikamata na ferrarin alaman ita zatayi driving, sannan ya bude mata motan ta shiga ya dawo ya budema Ummi sit din baya itama ta shiga tabar akwatin a waje. Kwashe akwatinan duka yayi ya zubasu a cikin truck din sannan ya bude ya shiga. Jan motan yayi suka nufi waje Alina na biye dashi a baya, ita kanta batasan inda suka nufaba kokuma ina zasuje, kawai binshi sukeyi, har a lokacin idon Ummi bai dena zubar hawaye ba, takasa believing wai yau su akayima wannan irin korar karen, tunda take bata taba tunanin watarana wani abu makamancin wannan zai faru dasu ba sai yau, lokaci daya komai ya tabarbare musu, yanzu batasan inda zasusa kansu ba. for more informatin ga wattsapp number na 09157578540. Game of puzzle (Wasan sarƙaƙiya). By Ayraah Riyad… Book one 1… Chapter 8… Qatar.. Basu tsaya ko inaba sai a kofar makarantar Qatar British School, Henry yay parking motar sannan ya sauka. Sai a lokacin Alina ta tuna cewa sisters din twins Raya da Maya. Kamar reporters sunsan nan suka nufo dan wasu ma bin bayansu sukayi tundaga palace din, gakuma wasu a bakin gate na school din, saidai dayake school din duk yaran masu fada aji ne a kasar yasa security basu barsu sunshiga ciki ba. Zagaye motocin sukayi kowanne da cameras sakale a kafadunsa, wanda suka samu suke daidai jikin motan sai kwankwasa glasses na motan din sukeyi suna musu tambayoyi dabama ji sukeyi dan motar soundproof ce. Alina dake zaune mazaunin driver tana daddanna waya kaar batasan dawasu a waje ba, saidai jin kukan Ummi yasata jan tsaki tana maida idonta kan gate din ko zataga Henry suyi su tafi saidai hakan bai samu ba sakamakon reporters din dasuka zagaye motar harta gaba babu abunda kake gani sai kawunansu da cameras suna daukan hoto. Ta mirror ta kalli Ummi dake sharbar kuka, dan girgiza kai tayi tana juya ido, cikin sexy voice dinta tace “ Ummi kiyi shiru mana haka, ni baga abun kuka a wannan lamarinba, Hussain ne nakuma san yanda zanyi dashi, saidai kuma idan mijinki kike ma kukan, wannan tsakaninku, tunda indai bawai kinsan yayi wani abubane meye na irin wannan kukan kaman anmiki mutuwa”. Dan tsagaita kukan Ummi tayi tana kallon Alina da still daddanna wayanta takeyi, face dinta bai nuna komai ba alaman itafa bata dauki wannan abun da muhimmanci bah. Tabbas yanzu ta kara gane cewa Alina yarinya ce, “ lallai Lina da sauranki a duniya, kina tunanin yanda suka kama Abbinki zasu sakeshi ne? Sannan mekike dashi dazakiyi tunanin zakiyi nasara akan Hussain, ki tuna duk wani family ko friends sun juya mana baya, dole nayi kuka Lina bamuda wani abunda zamu iya akan hakan”. Tafada tana kara fashewa da wani sabon kukan. Yi tayi kaman bata jitaba dan ita ba yarda tayi ba, babu abunda zai daga mata hankali a duniyan nan, bare wani Hussain da saiyayi anfani da ita zai samu ya aiwatar da kudirinshi. Ba dadewa Henry ya fito rike da hannun wasu yara guda biyu mata bazasu wuce 12 years ba, suna mugun kamada juna da inba kagansu tareba bazaka taba yarda ba mutun daya bane. Suna kuma kama sosai da Alina dakuma Sheikh Rayyan, suna sanye da uniform white tshirt da black mini flowy skirt da black tights a ciki, kansu ba dankwali sun saki gashi baki daya nata har gadon baya daya kuma iya kafadunta ya tsaya. Reporters dinne suka juya yawancinsu suka nufe su, Gun Henry ya ciro yana musu alaman su matsa, bamusu suka matsa suka bashi hanya still suna daukan hotunan suna kuma musu tambayoyi da babu wanda ya amsa musu ciki. School bags dinsu ya ansa sannan ya bude musu bayan motar Alina da Ummi ke ciki suka shiga ya rufe ya shiga SUV truck din yaja motar Alina na binshi a baya. Saida sukai wajen tafiyan minti 30 sannan suka isa wani hadadden district kana ganin area kasan na manyan mutane ne saboda shirun dakuma maka makan tsararrun gidaje dakuma security. Gaban wani gida ya tsaya a tsakiyan district din gidane babba tsantsararre gate din auto matic ta wayarshi ya bude sannan suka shiga. Babu compound sosai a cikin gidan sai gurin parking na motoci uku, building dinne irin turkish style dankarere dan shiya mamaye rabi da kwatan gidan yay parking. Yazrin ma parking din motar tayi sannan ta bude kofa ta sauko. Bata bi takan su Ummi ko waniba tay hanyar entrance din gidan, gidan da Hussain yabata ne for her birthday last year, dan haka tasan yanda gidan yake. Shiga tayi palour ne zaka fara tararwa hadadde sannan yanada girma sosai komai na ciki brown da red ne. Kan doguwan sofa 3seater ta sauka ta kwanta, tareda cigaba da daddanna wayarta. Ummi ne suka shigo itada yaran. Henry na biye dasu da Akwatinan su daya kaisu chan karshe palour sannan ya juya ya fice. Daya daga cikin yaran ne mai gashi iya shoulders tay tsalle ta sauka akan Alina. Rintse idanu Alina tayi sakamakon bugun da kashinsu yayi, ta dago hannunta da zafi zafi kamar zata tureta saikuma ta saukesu. Tsareta da ido yarinyan tayi sannan cikin wata silly voice mai dadin sauraro tace “ Sis Lina me mukeyi anan? Wai dagaske reporters keyi an kama Abbi?”. Ta tambaya kamar zatayi kuka. Kamar bazata ansata ba saikuma ta dago ta kalleta, “ Laya kin cika tambayoyi, and yes an kama Abbi amma zan kwato miki shi kinji”. Tana fadin haka tanakai kallonta kan dayar mai dogon gashin sannan tace “ Raya kema ina fatan kinji, kafin yanzu inji dayanku yafara mun kuka hadaku zanyi na kora”. Bata ko gama rufe bakiba Laya ta fashe dawani irin shagwababben kuka “ Sis Lina i want my daddy, ni gaskiya saina bishi bazan zauna anan ba”. Kallonta Alina keyi, cikin zafa ta mike tareda tureta daga jikinta, ta maida idonta kan Raya da itama kukan takeyi saidai ita hawaye ne kawai ke zuba, dakuma cute lips dinta data chuno su gaba, gakuma Ummi itama kukan takeyi silently. Girgiza kai Alina tayi tana kara binsu da kallo, ganin idan ta zauna haukata ta zasuyi yasa tay hanyar stairs kawai tana jan akwati daya, Maya tay saurin mikewa tabita a baya tana kara sautin kukan nata tana kiran Abbi Abbi da karfi a kuma shagwabe. Juyowa tayi tamata wani mugun kallo, cikin no nonsense voice tace “ wlh Maya idan kika sake kika biyoni saina zaneki, ni nadau miki Abbin naki dazaki zo kinamun kukan shagwaban nan naki na banza? Kije ki nemi wanda ya daukeshi yadawo miki dashi baniba”. Sannan ta cigaba da tafiyanta sama. Bedroom dake a farko kana hawa stairs din ta bude ta shiga. Shima kamar palorn komai na ciki brown ne, da Royal king sized bed a tsakiyan room din. Ajiye akwatin tayi a tsakiyan dakin sannan ta wuga wayarta ka bed din daga nan inda take ta nufi toilet cikin shower ta kunna ruwan zafi. Wanka kawai tayi amma saida ta shafe wajen 1hour a ciki sannan ta fito, kan bed ta hango Maya tana zaune tana fuskantar toilet din tafara bacci. Tsaki tayi tana dauke idonta daga kanta. Aranta tana fadin shagwabbabiyar yarinya kawai. Kan mirror ta nufa da nufin ta dauko lotions dinta, saidai wayam babu komai a kai. Dafe kanta tayi tana tunanin meyasata manta lotions dinta, gashi babu damar komawa daukowa. Bed tanufa ta dauki wayarta sai kuma ta juyo ta gyara ma Maya kwanciya sannan ta shiga website din companyn lotions da body care datake using danta yi order, saidai tana saka ordern yadawo mata as error. Kara trying tayi saidai a error yadawo. Wani shu’umin murmushi ta saki, wato Hussain a shirye yake, tayi underestimating dinshi wato banning komai kenan? Bama accounts kawai ba. Kuwait A bangaren yazrin kan bed ta tarar da wayarta tareda wata takarda white a gefenta. Karasawa tayi ta dauki papern, babu komai a ciki, daukan wayar tayi ta haska paper ta baya saidai babu wani abu a jiki. Window dakin ta nufa sannan ta budeshi ta wurga papern sannan ta rufe tadawo kan bed ta kwanta da kayan jikinta tanajin wata muguwar gajiya na saukar mata. Bude wayar tayi tana dudduba abubuwanta. Komai daidai yake kamar ba’a taba ba. Sauke ajiyar zuciya tayi tanajin bacci na fizgar ta, batayi ko 5minutes ba baccin ya dauketa. After 3hours… Bude idanunta tayi tanajin baccin na sakinta a tsanake, saidai kafin ta ankara jin hannu tayi a makwogwaronto ana dannawa. Shaketa akayi da karfin gaske kanta da wuyanta na dannuwa a

Chapter 6 of 11