banason zamanta anan karma wani yakara kokarin budewa”.
Girgiza kai yayi sannan yace “ No Yazrin. Bakida time dinnan. Indai har dagaske kikeyi toh tun yau yakamata ki fara abunda zaki fara. Ko kina tunanin cewa kinada time harki warke ne kafin a gane littafin baya cikin library din? Koba yanzu kika cemun sati daya kike dashi ba yanzu har kinci kwana biyu?”.
Dafe kai Yazrin tayi ita hartama manta. Daidai nan Mamah tadawo itada Dr. Katherine. Alama Faryal yamata dan tayi sauri ta gyara yanda take. Da sauri ta kama cikinta ta rike tareda rintse ido tana jujjuyawa.
Juya ido faryal yayi ganin abunda tayi. Wato ta manta dazu kai ta kama yanzu ta rike ciki gashi har sun riga sun karaso ciki bare ya gyara mata. Mamah ce take binta da kallo ganin ta koma ta rike ciki, tunani takeyi data fita yanzu ai kai ta rike ya kuma yanzu yakoma ciki?.
Dr. Katherine ce tazo tareda danna cikin nata dan taji meke faruwa. Mamah ce tazagayo inda daidai kan Yazrin tana kallonta nayan sakanni sannan ta daga ma Dr. Katherine hannu tana fadin “ Dr. ai inaga taji sauki hakanan koba hakaba Yazrin”. Tayi tambayar tana kallon cikin idanun yazrin data budesu.
Gyada mata kai Yazrin tayi tana janye hannunta dagakan flat tommynta data rike ganin anriga an ganota. Shiyasa batason hada abu da mamah duk yanda kayi saita gane idan kana boye wani abu.
( niko nace ai kece da matsalar yar karyan nan ma ba iyawa kikayiba).
Mamah ta juya inda faryal yake sannan tace mishi “ Toh faryal a gaida mamah da ridwan kaji”. Yanajin hakan yasan korarsa takeyi sai kawai ya gyada mata kai sannan yayma yazrin sallama ya fice.
Juyowa Mamah tayi tana kallon Yazrin datayi tsuru tsuru dukda iya kokarinta datayi don Tayi appearing normal amma kana ganinta kasan batada gaskiya. A gefenta mamah ta zauna tana mata wani irin kallo mai wuyan fassarawa. Cikin kausasshiyar murya tafara “ Yazrin kinsan nina haifeki, sannan nina raineki infact kinfi kowani yaro dana haifa samun lokaci na saboda ciwonki, bayan haka tun kina karama har girmanki bakida kawaye ko wani abu har saida kika kai wajen 15 sannan kuka fara shiri da Faryal, a gidannan nasanki farin sani. Nasanki kamar yanda nake taunar abinci, sawa kawai nake a baki zanyi taunar basai nace ma hakwara na ga yanda zasuyi ba, toh haka nasanki basai nayi tunanin wai ga abunda kikeyi bah tukunna zan gane halin dakike ciki. Dan haka duk abunda kike boyewa nasan bakida gaskiya zan gano shi, idan kinga dama tun wuri ki ajiyeshi ko kizo ki fada, inkuma kingiso naganishi da kaina toh shima hakan yayi. Duk daya ne”.
Tadan ja nunfashi sannan ta cigaba “ Wai a gidanna Yazrin yaushe kika fara karya? Harni zakima karya a gidannan wai ki daga mun hankali kina wani tari da rike kai na munafurci dan na fita daga dakin kiyi magana da Faryal koh? Sannan har kinada zarrar da zan dawo ki manta inama kika rike kikoma ciki kina wani juye juye na banza da hofi. Zanyi maganinki a gidannan karkiga yanzu kin girma kin kawo karfi har ana maganan Aurenki, har yanzu baki wuce nazauna na hukuntaki a gidan nan ba”.
Rufe idanunta Yazrin tayi tanajin zafin maganganun da mamah ke fada. Bawai tayi regretting karyan datayi mata bane saidai yanda mamah ke fadin maganganun kamar ba yar cikinta bah. Nunfashi ta sauke tana goge hawayen dake zuba. Sotake ta mayarma mamah da maganganun data mata itama ta bata ansa saidai tana tsoron abunda zai biyo baya.
Mamah na kallonta abun ya bata mamaki ganin Yazrin bata dago ta bata hakuri bah. Da on a normal day ne yanda tayi mata fadan nan zata dago ta bata hakuri saidai yanzu tay shiru infact tama rufe ido karma tayi tunanin zata bata hakurin kenan.
Bude idonta tayi tasasu cikin na mamah sannan tace “ Mamah a samo kuyangu su tayani nakoma dakina. Nagaji da zaman ward room dinnan”. Wani irin murmushi mamah tayi da saida Yazrin taji cikinta ya kada saidai ta dake sannan tadan dago da jikinta. Bayan yadena mata zafi sosai alaman maganin na aiki sosai. Tana jinshi bawai batajinshi ba amma baikai yanda zaisa ta kasa tashi bah kamar dazu.
Tashi mamah tayi ta fita babu dadewa saiga wasu kuyangu su hudu sunshigo dakin. Gaisheta sukayi ta ansa sama sama suka gunguro wata wheelchair suka kawo bakin gadon sannan suka tayata mikewa ta zauna akan wheelchair din. Cema dayansu tayi ta dauko mata jakarta ta miko mata. Ta dauko ta kawo mata ta rike abunta tana kara kallon fuskokinsu aiko tayi sa’a harda wanda take nema akan maganar letter dinnan.
Murmushi tayi tana tarayo questions da zatayi mata. Gungurata sukayi har zuwa elevator sannan biyu suka shiga ciki da ita harda wanda takowa mata Abincin sauran kuma suka juya. Dakinta straight suka shiga bayan sun sauka a floor dinsu sannan suka tayata hawa gadon ta kwanta tanajin bayan nakara zafi alaman bayason jagwalgwalo.
Kallon dayew kuyangar tayi sannan tace mata taje ta hado mata tea datakesha da garlic bread ta kawo mata. Fita tayi yarage daga ita sai dayar kuyangar. Tambayarta tayi me sunanta tace mata Halima. Gyada kai tayi sannan tafara mata tambayoyi “ Ranan da kika kawomin abinci sama shekaranjiya kenan waye ya hada?”.
Dan jim tayi kamar mai tunanin wani abu sannan tace “ Ni na hada ranki ya dade”. “ babu wanda ya tayaki koya taba lokacin dakike hadawa?”. Ta ansa mata da yes babu.
Saida tadan dauki yan lokaci sannan cikin serious voice tace “toh akwai wanda yabaki wani abu ki kawomin ranan?”. Ansa mata tayi da yes akwai wanda ya bada abu abata.
( toh kuna ganin zamu samu mu gano wanda ke turo da letter nan? Sannan mekuke tunanin abunda yaturo na karshe cewa kada tayi shaida idan lokaci yayi? Mene zatayi shaida daya hanata?).
For more information ga wattsapp number na 09157578540.
Game of puzzle (Wasan sarƙaƙiya).
By Aryaah Riyad..
Book one 1…
Chapter 15..
Stars talented writers……
Dan waro ido Yazrin tayi dan batayi tunanin zata samu answer cikin sauki hakaba. Dadan sauri takara wurga mata tambaya “ ok waye sannan menene aka baki ki kawo?”. Dan juyawa kuyangar tayi sannan tadan rage murya tace “ ranki ya dade bansan wayeba gaskiya. Nidai kawai naga an ajiye a kan tray daa hada so nayi zaton prince Ayaan ne ya ajiye a kawo miki tunda shi ya umarta dana hada miki abincin ranan”.
Dan batarai Yazrin tayi dayasa kuyangar sauke kanta kasa dan ita batamasan meta fada daya bata mata rai ba. Alama Yazrin tayi mata akan taje shikenan dan bataga anfanin cigaba da mata tambayoyin ba. Aranta tana tunanin anya ba Ayaan dinne ke turo lettern ba? Saidai kuma tunawa da cewa Ayaan bashida hanyar dazai sa tashiga har office na Daddy batareda an ganta bah harya sa a dauko mata wayarta daga ciki.
Ajiyar zuciyata sauke sannan ta dauko jakar tabude ta cito littafin. Kwankwasa kofa akayi tayi saurin maida book din tana tambayar waye? Kuyangar dazuce tadawo tace mata ta shigo. Cinnamon Tea din ta kawo mata da garlic bread take dakin ya bude da kanshin garlic da cinnamon.
Ajiyewa tayi sannan ta juya ta fice bayan yazrin ta sallameta. Tashi tayi a hankali dan karta fama bayan sannan ta dauki tea din tafara sha. Sai a lokacin tatuno bataci abinci ba kwata kwata tunda ta tashi yau babu wanda yabata abinci taci. Bama tasan tanajin yunwa ba saida tafara cin abincin. Saida takusan shanye tea din ta ajiye ta dauki garlic bread din tafara ci yaji butter sanda aka gasa shi so bata ko shafa mishi buttern dake a wani mini bowl dake a plate din bread dinba.
Guda daya kawai ta chinye sannan ta ajiye shi a gefe ta kurbe ragowar tea din tana godewa Allah. Dauko book din takarayi tana budewa. A maimakon ta bude page na farko saita budeshi ta karshe tana kara kallon wayannan symbols da aka rubuta a ciki dabatasan ma’anar suba.
Komawa tayi first page takara karantashi still bata gane me poems din keyi a cikin diary ba kawai tayi gaba. Saida tayi wajen 10 pages duk poems ne sannan saiga riddles ( bansan me ake cema riddles da hausa bah, amma nakusa dashi ko nace ana kiranshi da kacici kacici ko wasan kwakwalwa, toh shine a cikin wannan bangare na wannan littafin da Yazrin ke karantawa. Zan rubuta shi da turanci sannan zan rubuta da hausa).
“I am a story told in scattered pieces,A game where confusion never ceases,Until you see how each part belongs.Then all the chaos becomes a song.What am I?”
Ni labari ne da aka warwatse guda guda,
Wasa ne da rudani ba ya ƙarewa,
Har sai ka ga yadda kowane yanki ya dace
Sannan duk hargitsi ya zama waƙa.
Me nake?”
Tun bata karasa karantawa ba tagane menene. Dan tun lokutan datake karanta littafin indai tazo inda akwai riddles to saita san yanda tayi tagano menene. Yana nufin kacici kacici ne, kokuma riddles. Sosai takeson yanda aka sa riddle din yazama ansar shi shine kanshi.
Wani smile ne ya ziyarci face dinta a take batareda tamasan tayiba tana jin dadin yada ta gane wani abu daga cikin book din, cikin excitement kuma ta bude page na gaba..
“I am a journey of many steps,
Where some ascend and some grow less.
The healthy climb me without thought,
But for the weak, each step is fought.
I measure strength in how you rise,
Or show your fall before all eyes.
What am I?”
“Ni tafiya ce mai matakai da yawa,
Inda wasu suna hawa wasu kuma suna raguwa.
Masu lafiya suna hawa ba tare da tunani ba,
Amma ga marasa ƙarfi, kowane mataki yaƙi ne.
Ina auna ƙarfi ta yadda kake hawa,
Ko kuma ina nuna faɗuwarka a gaban kowa.
Me nake?”
Kara karanta shi tayi dan koda take karantawa a baya bata taba bashi ma’ana ba. Jitake kamar da ita akeyi idan ta karantashi. Saida ta tattaro nutsuwarta sannan takara karantashi. Tunaninta na farko shine Power. Idan mutun na neman power ko mukami dole yabi matakai mabanbanta. Wasu nasamu su cinma burinsu wasu kuma basa iyawa.
Saidai kuma inda akace masu lafiya ke hawa batareda tunani ba. Sosai taji maganar a cikin zuciyanta dan harsaida taji kwalla ta cika mata ido. Gani take kamar dan ita aka rubuta dan a nuna mata bazata iya komai ba. Dan a nuna mata ita bata cika tayi abunda masu lafiya keyiba.
Danne zuciyarta tayi dan batason kananan abubuwa haka na damunta. Karasa karantawa tayi tana kara tunani akan medame yake nufi. Wani tunanin ne ya fado mata kodai yana nufin Stairs ne? Tunda ai shima matakai ne. Sannan mara lafiya shima a wahale yake hawa.
Mikewa tayi a hankali ta nufi katon book shelf dinta daya mamaye bangon dakin guda tayi sliding glass slide daya rufe shi sannan ta dauko note book daya a ciki ta dauki wani pink pen ta rufe ta dawo gadon ta zauna tanajin yanda bayan ko ciwo bai mataba.
Rubuta answern na farkon tayi sannan a nabiyun ta rubuta ansa biyu data samu. Acewarta idan ta ansa nagaban duk abunda tasamu tana yakinin zai nuna mata wanne ne a ciki.
Na ukun ta shiga karantawa kanta tsaye tun daga farkonshi har karshe. Layi ukune babu yawa. Saidai duk wani abu datake tsammanin zata gani bashi bane. Ba tsarin magana bane, bakuma magana bace cikin magana kokuma boyayyiyar ajiya a ciki. Smile dake face dinta ya bace bat kamar wanda aka goge. Girarta suka hade idanunta nadan warowa akan kalmomin.
Karatun datakeyi a sirrance yafito fili tana maimaitashi kanar hakan ne zaisa tagane me ake nufi. Saidai tafi kowa sanin bazata iyama kanta karya ba.
Hannayenta dasuke rikeda littafin suka saki littafin ya fadi kan gadon. Kai hannun tayi zata dauko shi saikuma ta fasa. Wannan ba kamar sauran yakeba, bazaka ce zaka chanki abunda aka rubuta ba, kokuma kace bashida ma’ana gaba daya, saidai a yanayin da akayi rubutun dakuma tsarin a da kalmomin suke zai nuna maka ba abune dazaka ansashi kai tsaye ba, hakan ma idan kasamu ka iya ansawar kenan.
Nite book din ta dauka ta rubuta kalma daya saikuma ta cancelling dinshi. Wani takara rubutawa tareda kara cancelling shima. Tayima pen din wani irin riko kamar yayi mata laifi. Guara zamanta tayi tareda dauko littafin kamar tana daukar wuta ta dora shi a laps dinta tareda kara budewa tana karanto kalmomin a hankali over and over again.
Tunaninta na tsere a cikin kwakwalwanta, ideas na zuwa suna wargajewa kafin ma tasamu tabasu ma’ana. Yanzu tagane meyasa nafarkon yazama haka. Wato nunawa yakeyi cewa lallai littafin riddle ne, nabiyun kuma na nuna mata cewa bazata taba samun answer ba kenan? Tunda koda tasamu answern batasan takamaimai wannene a ciki ba. Gakuma na ukun yanzu bama tasan tayanda zata farashiba.
Duk wani farinciki datunanin cewa yanzu tafara gano littafin yabar kwakwalwar ta. Dan maimakon hakan ta faru yanzu tagane meyasa babu wanda ya iya bawa littafin ma’ana. Dukta inda ka bullo mai anan zai barka. Kana gabane kana tunanin kasan mekakeyi, saikaje wani point zai nuna maka duk wani abu daka sani akai bahaka bane.
Wani jiri neyafara debanta tanajin bugun zuciyarta har cikin kanta. Hannu tasa tana rike kanta jin kamar zai fashe dan ciwo.
Qatar…
A bangaren Alina kuwa Jiki a sanyaye ta fice daga Office na doctorn takoma inda aka ajiye Ummi har lokacin bata farfado bah. Henry tasamu a gurin taredasu Raya sunyi chirko chirko a gurin. “ Henry dauketa mutafi”. Haka kwai tace sannan tajuya ta nufi waje Laya nabinta dagudu Raya kuma na tsaye gurin Ummi.
Waje gabadayensu suka hadu aka bude bayan mota Henry yasata Raya ta shiga ciki ta zauna tareda daukar kan Ummi ta daura aka cinyarta Alina ta shiga gaba itada Laya suka nufi gida. Suna kaiwa suka sauko Henry ya dauko Ummi yakaita sama dakinta ya ajiyeta sannan ya dawo Alina ta mika mishi tsohuwar wayarta datayi list a ciki tace yaje ya siyo musu abubuwan data rubuta tareda breakfast su Raya suci.
Ansa yayi tahada mai da cash masu mugun yawa ya ansa yatafi ba dadewa ya dawo motar cikeda kayayyaki. Shigo dasu duka yayi palourn kasa ya ajiye Alina ta dauki Cosmetics da kayan shafe shafenta ta nufi sama. Raya ta kira tace taje ta anso musu breakfast a kasa suci daganan ta shiga wanka.
Bata wani dade a wankan ba ta fito tazo ta bude lotions ta shafe jikinta tas sannan ta bude akwatinta ta dauki last abaya data rage mata white ce da akayi mata wani mahaukacin royal design da silver bedding ta samanta, sannan ta dauki wata silver Alkyabba da itama itace kadai ta dauko yarage babu wani kaya datake dashi yanzu ta zura su sai a lokacin tagane batada wasu underwears suma.
Silver alkyabbar tayi mata kyau sosai dan har kasa take ja, ga kyalli datakeyi kamar wata sarauniyar kyau dukda batasa komai a face dinta bah. Make up products ta ciro daga wani shopping bag tayi yan shafe shafenta. Bold red lipstick tasaka tasa glitter a chest area dinta da wuya dake dan bude. Sannan ta dauki shafa kwalli ta zana eyeliner tafito kamar wata siren.
Dan heel ta dauko mara tsawo sosai ta saka sannan kalli kanta ganin tayima kanta yanda takeso tayi wani mayen kyau kamar irin vampires dinnan sannan ta dauko wani cat eye glasses ta saka. Turare ta dauko shima a cikin seperate shopping bag ta feffeshe shi ta dauko dayen dake ciki takara fesawa dakin yadau wani sanyayyar kanshi me sauke gajiya. Wani shu’umin dariya tayi kasa kasa sannan ta fita ta shiga dakin Ummi.
Still bata farkaba tacema Raya dake cin abinci “ Raya na fita, idan Ummi ta tashi ki fadawa Henry zai kirani, sannan duk abunda kukesu kifada mishi, a kasa idan kungama cin abincin ga kayachan an siyo muku da mayika kuyi wanka kusaka anjima zan dawo”. Sannan ta kalli Laya dake zaune itama tana cin abuncin tace “ Laya karnaji kinyi wani abun a gidan nan koki damesu da kuka, Raya idan tayi wani ahun ku fadamun idan na dawo”.
Fita tayi ta shiga motarta ta bata wuta ta fice a guje tanajin kanta nadan sara mata saidai batabi takan hakanba ta cigaba da figar mota kamar zata tashi sama.
West bay lagoon district ta nufa unguwa ce datagi kowanne tsada dakuma wuyan samun a Qatar. Beaches ne dakuma water falls takowani bangare ka kalla. Gidajen cikinta maka maka kana gani kasan mostly family houses ne very luxurious.
Daya daga cikin gidajen ta tsaya a bakin gate din authomated security ne yayi scanning na motar tukunna gate din ya bude. Wani sabon titi ne a ciki zagaye da bishiyu ta shiga tafiya adan hankali sannan ta karaso wani gate din.
Wasu securities ne suke patrol a gurin sunkai wajen su 50. Suna ganin motar batareda sun tsaya sunyi checking waye a ciki ba suka bude mata gate din ta shiga. Yanzu idan nace zan tsaya baku labarin iya girma da haduwan da gidan yakedashi harmu gama book dinnan bazamu karasa ba.
A gaban mansion na gidan wanda securities ke patrol tayi parking motar. Saida tadauki time sannan ta bude kofar ta zuro kafarta a hankali kafin ta zuro dayer ta fito gaba daya.
A hankali tafara takawa zuwa front door na gidan daya bude Authomatically ta shiga tana takawa dai dai cikeda izza.
( ina kuke ganin Alina tabar Ummi a gida tazo? Mekuma zatayi?).
Wasan sarƙaƙiya ( game of puzzle).
By Aryaah Riyad..
Book one 1…
Chapter 16…
Stars talented writers……
Palourn gidan ta shiga babu kowa a ciki sai kanshin turaren wuta dake tashi ko ina tsab tsab. Ga wani haduwa da palourn yayi komai ciki purple ne da red an zuba mishi kaya everything was so exaggerated.
Bata tsaya nanba ta wuce Elevator dake chan gefe a palorn tashiga ta danna button na third floor cikin minti daya ya kaita ta fita. Shima nan wani palor ne komai naciki purple ga animated characters an mammanna a bango da hotunan su Henry cavil, leonerdo decaprio da sauransu hollywood celebritys da anime characters.
Bin palorn tayi da kallo tana tuna rabon da tazo gidan yau wajen shekara daya kenan. Daga gefe wasu kofofi ne ta nufi gayan cikinsu ta bude ta shiga batareda tayi knocking bah yanda takeyi kamar gidanta take shiga.
Shimadakin purple ne da princess bed yahadu sosai saidai yafi kamada dakin yara akan na manya. Wata budurwar yarinya ce kwance akan princess bed ta kifa cikinta akan gadon ta dago kafafunta sama face dinta akan wani lallaisar pillow tana danna wayarta dake cikin purple case. Kunninta da headphones shima purple mai gashi gashi tana kada kai kana gani kasan tana cikin nishadi.
Dan tsayawa Alina tayi tana kallon yarinyar yanda take kada kai abunta batamasan an shigo dakin bah. Dan sallama tayi ciki ciki saidai ina bata jitaba tanachan duniyar waya.
Karasawa ciki tayi batareda ta tufe kofarba ta zagayo har gabanta ta zauna amma still bata lura da itaba. Hannu tasa ta janye headphones din daga kunninta a firgice yarinyar ta dago kai tana kallonta. Tunda suka hada ido Tahira ke kallon Yazrin kamar taga aljana. Ta waro manya manyan doll eyes dinta akan Alina cute pink lips dinta a sake alamardai bata taba tsammanin zataga Alina bah.
Ta dade a haka Alina ma bata dauke idanunta ba tana kallonta kafin Tawani zabura ta mike kamar wanda aka chakama allura tana sakin ihu. “ O.M.G Sis Alina.. nooo i can’t belieeeve this wallahi kece dama”. Tawani yi maganar a wata shagwababbiyar murya tanajan words din voice dinta so cute kamar na yara.
Dan smiling Alina tayi mata tana daga mata gira daya alaman yes itace. Wani fadowa tayi jikin Alina ta rungumeta gamgam kamar zata ballata. Alina ma rungumeta tayi kafin ta cireta daga jikinta jin tana nema taballa mata kasusuwa.
Sakinta Tahira tayi sannan ta koma ta zauna a gefenta tana cire Headphones din daga kanta gabadaya tareda wurgashi gefe akan bed din. Voice dinta cikeda farinciki da excitement tace “ OMG Sis Alina wallahi i missed you so much. Kin dena zuwa gurina tun last year fah baki kara zuwa gidannan bah, gashi konaje gidanku saidai ace mun kin fita kullun, jiya nakiraki ma wayarki bata shiga nace daddy yasa a kaini gurinki yace mun wai baisan inda kikeba”. Takarasa kamar zatayi kuka.
Murmushi ta sakin mata tanajin a ranta babu dadi ganin genuine farin cikin Tahira a yanzu, bataso tayi anfani da ita saidai tuna halin dasuke ciki yasata danne tunanin a zuciyanta.
Cikin tausasahiyar murya wanda inba Ummi bah babu wanda kesamun wannan murya daga gareta tace “ Tahira baby i miss you too. Kinsan yanda abubuwa suke a cikin masarauta so banida time sosai amma gashi yanzu nazo. Ya school?”.
Guada mata kai tayi face dinta cikeda annuri kafin ta tabe baki tana fadin “ Bayan kin tafi kin barni? Wai ya akayi aka yarda kika gama degree dinki a shekara biyu mukuma sai munyi hudu? Sannan kikaki ki rokan mun daddy nayi ko shekara uku ne kikayi graduation kika barni Allah banji dadi bah yanzu banida friends tunda kika tafi”.
Murmushin gefen baki Alina tayi mata sannan tace “ Kinsan nima kawai dan Ummi tasa baki ne aka barni nayi shekara biyu. Kekuma bacewa kikayi bazaki dauki extra courses ba sunmiki yawa? Ni year one da year two a lokaci daya nayisu sannan level 3 da 4 shima a lokaci daya nayi kokin manta ne?”. Ganin an kamata yasa Tahira ta kara turo baki tana fadin itadai babu ruwanta wlh kawai dai anmata wayau ne fan ta wuce ta “ ai nima nanda 3 weeks zanyi graduating, dan haka na yafe miki”.
Abun dariya yaba Alina wai ta yafe mata. Kowa ya tambayi yafiyar ta oho halin Tahira sai ita. Duba agogon hannunta Alina tayi ganin yanzu time na masallaci yayi na sallar azhar kuma tasan lallai yanzu Daddy Tahira zai gita masallaci dake anan cikin gida yasa tajuya kan Tahira tace “ Tahira am hungry banci breakfast bah”.
Tsalle tayi ta dira daga kan bed din tana fadin “ am so sorrry my Alina. Murna ya hanani tuna manners dina bari nasa a kawo miki”. Wani iri Alina tayi da face dayasa Tahira yin saurin fadin “ sorry na mantaaa. Bakyacin abincin mutane muje dakaina zan dafa miki”.
Da ok Alina ta ansa sannan ta mike suka fita. Kasa first floor suka sauka Tahira tayi hanyar kitchen. Har tayi gaba kuma tajuyo tana kallon Alina data zauna a kan daya daga cikin luxurious red sofa dake palourn. “ Sis Alina bazakizo bah? Kinsan nifa ba iya girki nayiba, kuma bansan me zakiciba har yanzu banana pancakes ne favorite dink…”.
Bata bari ta karasa ba tace kawai ta hado mata tea mai honey shikenan. Da ok Tahira ta amsa sannan ta juya ta nufi kitchen din da sauri sauri gudu gudu.
Alina kuwa kalonta ta mayar zuwa elevator dan kujerar data zauna yana kallon elevator din directly, sannan ta daura kafa daya kan daya tana gyara zaman alkyabbarta tayi wani irin sexy yet casual zama mai daukar hankali.
Da biyu tayi hakan dan sotakeyi yana saukowa ya tarar da ita tana kara kallon time ganin lokacin tabbas yayi amma bataga saukowanshi bah. Tunani tafara Allah yasa bai riga ya tafibah datayi zuwan banza, saikuma ta tuna koda ya fita ai zai dawo, kawai dai zata kara bata lokacinta ne dan batayi niyyan zama sosai bah.
Tana cikin tunanin kuma taji karan elevator ya bude. Face dinta dayake ba yabo ba fallasa ta mayar kan wayarta dake hannunta data bari a bude tafara daddannawa.
Fitowa yayi daga elevator din a sannu yana sanye da Farar Kaftan. Dogo ne saidai ba chan sosai ba, kyakyawan arab man yana kama sosai da Rayyan da Tahira. Sumar kanshi dabai rufeta ba baki sidik bashida tsawo sosai an gyarashi baya.
Kanshi a kasa ya fito yana dan sauri haryayi nisa jin kanshin turaren wanda yasan mutun daya yasani dashi yasa ya dago kai zuwa inda yaji kanshin. Wani tsayawa yayi yana kallonta ganin yanda tawani kame.
Saida tadau lokaci sannan tadan dago kanta daga danna wayar datakeyi tsab