Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
wannan lettern? Gashi ba suna a jiki ko post office address, sannan menene a office din Daddynta da zata bukata?. A tunaninta ko Ayaan ne? Dan shine kawai a gidan zai iya supporting dinta, shima babu tabbas. Kokuma Faryal ne? No ta furta dan tasan Faryal bazai turo mata da letter ba. Idan har daya daga cikinsu ne taya zasu ce mata karta damu da cctv camera? Alaman a kashe take kenan . Abun daure kan shine lettern babu signature, ba return address, babu phone number kokuma wani abu dazai sadaka koya nuna ma daga inda ya fito. Envelope din ta dauka tana kara jujjuya shi dan taga tambarin maybe tagane shi, saidai hakan bai yu ba dan batasan wata masarauta ko kungiya mai tambarinba. Wayarta ta dauko tayi hoton tambarin danta turama Faryal kozai sansu. Saidai tuna alkawarin datayi ma kanta yasata fasawa. Ganin ba samun answer zatayi ba yaza tafara tunanin abunda aka rubuta. Ko taje office na Daddy ne dan taga menene take bukatan kamar yanda lettern tace, saidai kuma tafi kowa sanin ko mamah bata shiga office na Daddy, shikadai yake shiga kayanshi, bai yarda wani ya shiga ba, sannan akwai tsaro sosai dan yanada password dake chanza kanshi duk lokacin daya shiga, don haka koda kaga password din idan yasaka toh bazai maka anfani ba, dan yariga ya chaza kanshi. Dauko takardar tayi tana kara kallonta, kozataga wani abu bayan rubutun. Ganin yanayin takardar daɗan kauri yasa tayi wani tunani. Wayarta ta dauko ta kunna flash light ta haska takardan ta baya. Kaman yanda tayi harsashe haka abunya kasance, dan numbers ne 6-digit sukayi appearing a bayan takardan da aka rubuta su da silver ink maidan kyalli wanda bazaka ganiba harsai ka haska shi. Dan smiling tayi, kenan wannan ne password din? Taya wanda ya turo mata yasan password din bayan tasan babu wanda yasani wanda ba Daddy ba, shi daya a duniya yake shiga office dinshi. Sannan idan taje password din yariga ya chanza fah?. Kamar dai bazata jeba, saikuma tayi tunanin inbata jeba taya zatasan menene? Idan kuma ya kasance abunda zai cika mata burinta fah, inbatajeba ta rasashi kenan. Tunani tafarayi akan yaushe yakamata taje kenan? Shin intaje yanzu ai suna part na Daddy, so bazata iya zuwa yanzu ba, amma kuma idan tajira lokacin dinner za’a nemeta, saidai kuma banda time na dinner batada wani time dazata shiga part na Daddy baya ciki. Idan tace zata jira sai gobe kuma Daddy bayanan, so part dinshi a rufe yake, dan haka yaune kawai takeda damar zuwa batareda an kamata ta shiga ba. Duba time tayi ganin saura baifi ten minutes lokacin dinner yayi ba, dan haka kawai ta kwanta tana jira time din tayi. Tana kwance har barci yaso yafara kwashe ta, ganin yaka yasa ta duba time. Ganin time din yama wuce da wajen 20 minutes yasata mikewa tayi waje. Tasan dole yanzu kowa na dining. Call din Ayaan ne ya shigo wayanta daidai tahau elevator, saida ta kusa tsinkewa sannan ta daga batareda tayi magana ba. Kiranta yayi ya fada mata tazo dining ana jiranta, dan marairaice murya tayi kamar mai bacci tace “ big brother bacci nakeyi, amma bari na tashi zan sauko yanzu”. Da ok ya ansa mata yana sannan ya tambaya “ ko insa a kawo miki daki ne?”. No tace mishi sannan ta tabbatar mishi zata sauko taci batajin ci a daki sannan suka kayse wayan. Tana isa part na Daddy ta tura kofar ta shiga. Babu kowa a palourn, daga bangaren hagu wasu dofofi ne guda biyu nan ta nufa. Ta farkon ta bude hallway ne da kofofi guda uku a zagaye da juna, na tsakiyan ta nufa idonta nakai kan cctv camera dake jikin kofan, ganin datayi bata kawo wannan jan haskenba alaman a kashe yake ne yay mugun daga mata hankali, duk yanda akayi wanda yaturo lettern ba karamin mutun bane, dan babu yanda za’ayi a kashe cctv cameran office na Daddy, wanda shine gurin dayafi kowanne sirri dakuma muhimmanci a part din. Tsoro ne yafara shiganta, shin metake shirin sa kanta a ciki, kodai ta koma ne kafin ta shiga abunda bazata iya fitar da kanta bah. Wani barin na zuciyanta kuma na raya mata kawai ta shiga, dukma abunda yafaru wannan taji dashi daga baya. Daidai inda ake shigar da security digits din ta tsaya a gefen kofan. Sannan ta saka numbers din data rike daga lettern, bawai ta gama yarda zai budu bane. Da mamakinta saiga kofar ta bude. Danne feeling din tsoro dake kara tashi a zuciyanta tayi kawai ta fada ciki. Office ne sosai kaman na shugaban kasa, yanada girma gakuma fadi, a ta ciki idan ka shiga kujeru ne sofas kaman na palour, bayansu kuma office desk ne da chair, dayen bangaren kuma kofofi ne guda biyu. Bata taba shiga office dinba, dan haka saita tsaya binshi da kallo. Saidai tuna batada issashen time yasa tayi saurin karasawa ciki batareda ta tsaya rufe kofanba. Desk din ta nufa cikin hanzari, tana kaiwa tafara kallon abubuwan kan desk din. Files ne tili akai batamasan me zatayi ba. Nan kuma taji gabanta ya fadi, dan sai yanzu tam gane meta aikata. Lettern bata fada mata menene zata bukata ba, sannan bata fada mata inda zata duba ta dauko ba, dafe tanta tayi tanajin wani ciwon kai ya diran mata, yanzu saita fara neme neme? Sannan menene zata nema din. Ganin batada wata mafitar daya wuce tafara neman abubuwa kawai yasa ta sauke ajiyar zuciya tareda jan nunfashi, file na farko dake kan wasu files din akan table ta daga, budeshi tayi dan taga menene a ciki. File ne akan wannan project na maida library museum, kaman ta ajiye dan tariga tasan menene saikuma wata zuciyan tace mata ta karanta mana kotaga menene suka shirya. Fara karantawa tayi tana budewa page by page, takai wajen 4 pages page na biyar yadau hankalinta. Project ne akan littafi guda daya wato ‘ The Diary Of Queen Samran Salim”. Wanda shine favorite littafinta. Project ne akan yanda za’a mayar da littafin yazama littafin tarihi na kasar kuwait, littafi ne da mutane keson sanin menene a ciki, dan ba kowa ne yasamu karantashi ba, saidai wayanda suka karanta sunfi kowa son susan menene littafin ya kunsa, saboda kai tsaye bazaka gene mene littafin ya kunsa ba. wasu suna tunanin cewa akwai wani abun al’ajabi a tattare da rayuwanta dakuma abubuwan dasuka faru a lokacinta da idan hakan ta fito fili zai iya ruguza kasar kuwait gabaki daya, wasu kuma suna tunanin cewa itadin ba mutun bace, aljana ce kuma matsafiya, shiyasa littafin nata babu wanda ya iya gano menene ainihin abunda ke ciki, saidai yawancin mutane sunfi karkata dacewa haukacewa tayi, a hauka tayi mulkin shiyasa diary dinta baka gane komai kaman wanda ya rubuta bayida cikakken hankali. A file din kasashe dayawa daga ciki harda kasar America dakuma china dasuka yi donating manyan kudade a sunan book din, duk suna jiran a fitarda abundake cikin littafin. A kasan file din kuma sunan Amrah akayi sighing, alaman itace wanda zatayi project din. Sauran kuma bayanai ne sosai akan book din da ragowar history dai dazai anfana mai binciken. Wani iri yazrin taji, saidai bata bari tazama sad ba, dan tagama jin wannan emotion din, sannan tasan lallai wannan ne abunda lettern ke mata magana akai, dan tabbas wannan abune dazata bukace shi, idan har tayi solving wannan abun tariga amrah yinshi to dole Daddy zaiga anfaninta, zaikuma ga cewa yanzu tawuce duk wani limitations dasuke daukanta dashi, sannan duniya zata shaida itama yace sannan princess data ansa sunanta. Wayarta ta dauko tayi snapping hotunan pages na file din, sannan ta ajiye wayar akan desk din tacigaba da bude wasu files din kozataga wani abun anfanin, jin karan tafiya ta daya daga cikin kofofin yasa da wani irin sauri dabata masan zata iya irinshi ba tayi arranging files din suka koma yanda suke kaman ba’a taba ba sannan ta juya da gudu ta fice daga office din ta jawo kofa, daidai lokacin a gefen idonta taga an murda handle na daya daga cikin kofar dake ciki kofan shiga office din na karasa rufewa, Allah yaso ma bata kara. Cikin rudani kar wanda ke ciki datake da tabbacin Daddy ne ya fito ya kamata kawai ta nufi stairs, ta tabbatar idan tabi ta elevator zai kamata tunda shima zai iya yanzu zai tafi dining din. A floor dinsu ta sauka sannan kawai ta nufi dakinta, tana shiga ta rufe kofa tareda sauke nunfashin dabata masan tana rike dashi ba. Kirjinta sai bugawa yake dum dum, ga gumi dake kwararo mata, jikinta na karkarwa. Ganin yanda take a hakan tasan bazata iya sauka a hakan ba, kan carpet ta zauna ta jingina da gadon tana maida nunfashi. Wayarta tay niyyar daukowa dan ta kira Ayaan tace akawo mata dinnern daki kawai, saidai wayam bataga waya ba. Hannayenta ta dago dan ta tabbatar wa da kanta babu wayar a gurinta. Gashi ita ba aljihu ba bare tace ta ajiye a ciki. Wani bugawa da kirjinta yayi saida brain dinta ta amsa, tashin hankali, watarta, wayarta ta bari akan table na office na daddy. Kwalla ne masu zafi suka ciko idanunta, zau kashinta ya bushe, dan dole daddy zaiga wayar nan, a fili ta ajiyeta, gashi babu damar komawa, shin idan ta koma tanada tabbacin daddy bai riga yaga wayar ba? Sannan batada password na kofar koda ta koma, kofar ta riga ta chanza code din yanzu. (Toh fah.. ana wata ga wata… , mekike tunanin zai faru idan daddy yaga wayar, shin zaiganta kokuwa bazai ganta ba?) Bari mu leka wani bangare a cikin labarin namu…, Qatar. Wani hadaddiyar villa ne data gaji da haduwa, bawani abubuwa aka cikama villa dinba saidai kana ganinshi kasan na manyan kai ne, komai na gidan white ne. Wasu motocine suka kutso kai su uku, kana ganin motocin kasan na royal house ne, dan ga tambarin royal house dinnan dakuma flag na qatar yar karama a jikinsu. A katafaren parking space na gidan dazai iya daukan motoci 30 banda wayanda aka jerasu kaman gurin saida motoci duka bana karamin mai arziki, suma wasu cikinsu akwai tambarin royal house din wasu kuma tambarin sojoji ne a jiki, alaman mamallakin su soja ne kuma yanada sarauta. Motar gabane dana baya suka bude kofofinsu suka fito, bodyguards ne masu sanye da white and maroon kaya, dakuma tambarin royal house an rubuta Qatar Emirate Palace a gaban rigan kaman yanda akasa a jikin motocin. Biyu cukinsu ne suka nufa motar dake tsakiya tareda bude kofar baya, saida aka dauki wajen 2 minutes kafin ta zuro kafanta dake sanye da high heels sannan ta fito, doguwace sosai sannan batada jiki, yar daidai take amma a cike take, tanada shape sosai coka cola shape, tana sanye da doguwan riga abaya brown da mayafin ta yadan yafashi akai ana ganin gaban gashinta dayake blonde hair. Farace sosai full balarabiya, bazata wuce 18 years old ba, kyakyawa ce ta wuce misali, idanuwanta dasuka kasance blue manya manya cat eye, ga hancinta dogo dan karami, lips dinta masu dan fadi saidai full ne, gasu pink sosai kaman tasa lipstick. Sai yatsine face din nata takeyi ta fara tafiya a hankali, alkyabban ta daya daga cikin bodyguard din ya dauko ya buyota dashi, sukuma sauran basu biyota ba, shikadai ya bita. Wani hadadden catwalk takeyi kaman batason taka kasa, daga ganinta zakasan jinin sarauta ya ratsa jikinta. Cikin gidan suka shiga da itada bodyguard din dake biye da ita. Wani hadadden makeken luxurious palour suka shiga, shima komi cikinshi white ne da cream, bodyguard din bai bita cikin palour dinba, a wajen ya tsaya ta karasa ciki, wani kyakyawan arab dattijo ne zaune kan kujera ya daura kafa daya kan daya, kyakyawa ne sosai sunyi balain kama da yarinyan. Tana ganinshi ta wani kumbura face tayi kanshi ta fada jikinshi. Cikin muryanshi mai dadi ya furta mata “ my baby Alina, yau waya taba mun ke? Tell me pls kinsan I hate seeing you like this ko”. Yafada yana shafa face dinta. Kaman zatayi kuka tace “ ba daddy bane, uncle nina gaji da wannan abun wlh, baya taba barina nayi abunda nakeso, kullun saiya nemi abunda zaimun fada akai, i swear am tired”. Ta fada cikin zazzakar muryanta mai long pitch. Kara rungumeta yayi sannan yace “ Lina baby i always tell you to have patience, komai zaizo ya wuce, and your daddy only wants tge best for you, shiyasa yake matsa miki, dan nasan abunda yayi ma saboda ke yayishi”. Dago da dara daran idanunta tayi akanshi tana mishi wani irin kallo, irin ban gane dinnan ba. Ganin haka yasa yakara hade ranshi snnan yace mata ba komai, saidai tasan tunda yayi haka lallai akwai abunda yake boye mata. “ uncle mekake boyemun, you know i trust you so in akwai wani abu kawai kafadamun, and mekake nufi da abunda yayi saboda ni yayi”. Ta fada cikin serious tone. Ganin bazai iya boye mata bane yasa yace “ Alina i want you to do something for me, inaso ki shiga study room na daddynki, akwai wasu documents danakeso ki dauko mun, sunada matukar amfani a wajena, bazan fada miki namenene kuma banaso ki tambayeni, kinsan bazan cutardake ko daddynki ba, in lokaci yayi zakigani menene da idonki”. Shiru tayi tana kallonshi, yes ta yarda dashi sosai tasan bazai cutardasu ba, babanta twin dinshi ne, itakuma kamar ya take a gareshi, saidai kawai taji maganan bai kwanta mata araiba, yauce rana ta farko da taji ta fara kokwanto akanshi, bayau ta fara dauko mishi documents ba a study na daddynta ba, saidai yau kawai taji gabanta na faduwa daya fada mata hakan. A bangaren Hussain kuwa bayan fitanta wani shuumin dariya ya saki, danyau burinshi ya cika, yau basai gobe ba zai aiwatar da abunda yake buri tun shekara wajen talatin dasuka wuce, yau zai tsige Hassan daga karagar mulkinsa na sarkin qatar, sannan yasashi a prison, dan yanda yazauna yayi shirinshi baiga abunda zai wanke hassan ba, dan har saka hannun na hassan dinnan saidai kawai shi hassan baisan meyasaka ma hannun ba. Dan kyabe baki yayi yana tuno yanda Alina jikinta duk yayi sanyi, babu karya idan yace yaji zuciyanshi babu dadi dan abunda ya tanadar musu daga Alinar har iyayen nata saiya yimusu abunda koda karene bazai juraba, saiya sa sunji mutuwa tafimusu wannan rayuwan, zaisa suji duniyan batasu bace, dan har ruwansha saiya tabbatar ya gagaresu, qatar kuwa tashice sai yanda yaga dama dasu, dan wayannan takardun duk zaiyi approving dinsu, dan shiyasa aka kawo mishi su, dan gani yakeyi talakawa sun fara mishi yawa a garin, dan haka dole a ragesu dan kungiyan su suna bukatan jini, yakamata ya zabar da jini sosai indai har yanaso yakai matsayin dayakeso. …… Lokacin da Alina ta isa gida har wajen karfe shabiyu na dare, basai na tsaya fadamuku haduwar palace dinba, kunsan dai masarautar Qatar dai, inbaku sani ba kuje a baku labari dan girmanshi da haduwanshi bazai faduba. Shima komai white ne sai wasu abubuwa kuma red and green. Har harabar main house aka kaita, saidai bata sauka ba tacema driver din yakaita har kofa, bai amsata ba bai kuma motsa ba, dan tasani kuma ya sani cewa dokace ba a yarda a wuce nan harabar ba da mota, dokar masarauta ce kuma babu wanda ya isa ya tsallaketa. Ganin bai matsa ba yasa tabuga mishi tsawa akai “ malan i said ka karasa dani chan ko, bazan sauka anan ba, tunda ba gidan ukanka bane”. Ta fada a gadarance, kaman ba yar gidan sarauta ba take zage zage. Shidai driver din bai motsa ba, bodyguard dinta ma dayake zaune a gaban motan bai motsa ba, saidai ganin abun ya fara wuce misali ne yasa ya sauko daga motan yaxo ya bude mata kofan alaman ta sauko, kwata kwata Alina bataganin girman nagaba da ita, drivern nan magidanci ne dan a haife ya haifeta, amma ta dura mishi wannan irin ashar din. Ranta a bace sai huci takeyi ta fito daga motan ta karasa kofan, ba wani nisa baifi minti dayaba tafiyan tsakanin harabar da kuma kofan shiga part din, amma take irin wannan iya shegen. Bodyguard dinne ya bude mata kofan ta juyo ta balla mishi harara ta shige ciki, alaman dai personal bodyguard dinta ne. Komai ya hadu iya haduwa, gidan yaci kudi kaman baa duniya kakeba, shi kanshi kasan ba tiles bane, lux touch flooring ne da inka kalla saika zata ruwane da mirrow a ciki, dan ko takawa kayi zakaga yana motsawa ta ciki kamandai yanda ruwa keyi. Straight dakin Ummi ta nufa, shima dakin wani aljannar duniyan ne, komai an ciki white ne, alamun dai white shine color na masarautar, wata dattijuwa ce zaune kan tsala tsala single sofas dake a gefen dakin, kyakyawan matace kana ganinta kaga mix, kyakyawa ce ajin karshe saidai tadan manyanta amma baiwani nunaba, zaka zaci irin yan 30 years dinnan ne idan kaganta, doguwa ce dukda a zaune take ga skin dinta so soft and shiny kana gani kasan ana kashe mishi kudi, kaman arab take amma jinin American yafi karfi a jikinta dan idanba kayi mata kallon kurilla ba bazakace tanada jinin arab ba. Eyes dinta blue ne masu mugun kyau, ga eye shape dinta masha Allah, kaman ka saceta ka gudu. Zaune take akan sofa ta daura kafa daya kan daya kana ganin zaman datayi kasan sarauta nabin jininta. Sanye take da French lace anyi mata doguwan Riga tight fitting ta kama jikinta ga wani slit a gefe wanda yasa legs dinta tundaga knees dinta zuwa kasa a waje. Fuskanta babu ko walwala kawai ta zauna ta daura face dinta akan hannunta tana tunani. Jin bugo kofan dakin da akayi ne ya dawo da ita daga duniyan tunanin data lula. Kobata ga wayeba tasan Alina ce, babu wani mara issahen tarbiya a yayanta sai wannan yarinyan, kwata kwata ta rasa yanda zatayi da ita. Hada ido sukayi sannan ta juyar da kanta takoma kallon tv dake opposite dinta wanda ball ne akeyi na barcelona da real madrid. Dan kyabe baki Alina tayi ganin yauma kallon kwallon takeyi, cikin shagwaba ta furta mata tareda karasowa inda take “ Ummi wai ba husband dinki ya hanaki kallon wannan abunba, kodayake nima bajin magananshi nakeba bare wata ke”. Tafada ko a jikinta. Sakin baki najla tayi tana kallon ta “ Lina bana hanaki fadin irin maganganun nan akan daddyn ki ba, ba’a isa a fada miki kijiba ko?”. “ nifa ummi kinsani daddy baya sona, kuma nima basonshi nakeyi ba, am sure yana dawowa daga fada zai shigo yafara mun fada akan abubuwan dabasukai sun kawoba, so kawai ni ki rabudani”. A harzuke ummi ta mike tana nunata hannunta har rawa yakeyi tace “ ni Alina kike fadawa bakison daddynki, lallai yanxu abun naki yafara wuce gona da iri, zan dauki mummunan mataki aka…..”. Bata bari ta karasa maganan ta ta mike ta fice a dakin tana dariya, irin abun ma bai dameta ba. Dafe kirginta ummi tayi tana kallonta har ta fice, wlh tagaji da halin Alina kowama ya gaji da ita, bata duba abunda zata fada, duk abunda yazo bakinta fada kawai takeyi babu boye boye, gashi yanzu tana nema ta sakamusu hawanjini, dan wlh inba dan dokokin masarauta ba aurar da ita zatayi kowama ya huta, amma yanzu sai dole tagama university, nanda shekara biyu kenan. A bangaren Alina kuwa tana fita daga room din Ammi study room na daddynta ta wuce, wanda wani part ne daban da saida tahau elevator ya kaita floor 5 sannan ta shiga, part na sarki ne komai ya fita daban a ciki, ba ayi wani kyalkyali bakuma ayi extravagant abubuwa a ciki ba, komai saffa saffa akayi amma kuma kana shiga kasan bana kananan mutane bane. Kanta tsaye ta nufi study room na daddynta wanda yake da kofa ta falo, makeken guri be sosai da aka kawata shi, saidai shi komai brown ne a ciki da fari, wurin wasu safe ta wuce wanda suke floor to seiling edge to edge na bango daya gabadaya. Direct wurin tsakiya ta nufa, inda yace mata suke, bubbudewa takeyi cikin natsuwa bata ko tsoron a kamata, saida ta bude wanda take tunanin sune a ciki dan yace mata a cikin wani safe suke, nufinsa kenan safe cikin safe. Daukan safe din tayi daga cikin babban safe din sannan ta rufe ta fito waje, har a lokacin babu alaman motsin kowa a gurin. Abunda yasa batayi wani dar dar ba saboda part din babu cameras ko daya, dan dokace ta masarautar ba a saka cameras a turakar sarki, babu kuma masu tsaron gurin dan tsaro na waje, baka isa ka ballo ka shigo ciki ba, duk tantirancin ka kuwa, kuma tasan babu wanda zAi zarge ta, inma za a zarga to saidai masu aikin part din. Tana fita dakinta ta koma sannan ta dauki waya ta kirashi cewa ta dauko, sai kawai yace mata ta tafi dining suje daddynta ya dawo zasuyi lunch, tabar safe din a kan bed dinta. Da ok ta amsa mishi dukda dai she’s confused akan meyakeyi, kome zaiyi da takaddun oho, gashi kuma yace kada ta tambayeshi, amma komadai menene tasan bazai cutar dasuba. Fita tayi daga dakin bayan tayi wanka ta chanza kaya zuwa pj riga da wando sannan ta nufi dining din. Zaune ta isko daddynta wato Sheikh Rayyan zaune a kan head table wanda dining din zaici atleast mutane 25, kamarsu daya da Hussain saidai yafishi cikar haiba da kuma kwarjini, kyakyawan full arab man ne dogo ga saje daya kwanta a fuskanshi baki sidik, ga wata burka black da golden daya daura akan white jallabiyan shi, ga white scarf da black roll na kai dasuke sawa, irin typical shigansu na manyan sarakunan larabawa. Kyakyawan fuskanshi ba yabo ba fallasa yakai kallonshi zuwa kan Alina data shigo dining room din bako sallama sannan ya dauke kanshi. Ummi ce zaune a gefenshi na dama, Alina taxo ta zauna a sit wanda yake dadan nisa dasu tana daddanna wayanta batare da tace uffanba. Wasu kuyangu ne mata su shida suka shigo kowannen su sanye da fari da kuma maroon dogayen riguna, kansu babu dankwali saidai sunyi parking gashinsu in a low bun. Warmers na abunci ne suka sugo dasu suka jera a kan table din, sannan hudu suka tafi biyu suka tsaya suka fara serving din abuncin. Basu kaida fara serving dinba suka farajin hayaniya na karade gidan, kafin cikin abunda baifi 30 seconds. Ba a banko kofan shigowa dining din wanda yasa daga Alina har Sheikh Rayyan da Ummi mikewa tsaye. Hussain ne sanye da kayan sojoji ya shigo da wasu zaratan sojoji cikin army uniform na Qatar dazasukai wajen su 70, wasunsu basu samu daman karasowa ciki ba. Karasowa ciki yayi yana kallon Sheikh Rayyan ido cikin ido, fuskanshi a murtuke, saida ya karaso dab dashi sannan yayi alaman daya daga cikin sojojin yazo, wani ne yazo sannan ya ansa handcuffs ya daga sama, sannan yace Sheikh Rayyan ya kawo hannunsa. “ you are under arrest Hassan Rayyan, banso nayi wannan aikinba, amma doka nakan kowa, duk wani bayani kuma zakajishi a court, dan haka we need your absolute corporation”. Shiru dakin ya dauka jin maganganun Hussain, bakin kowa a sake dan they can’t believe wai Sheikh Rayyan ake arresting ba, kuma twin brother dinshi, ina bazai taba yuwuwa ba. Ba musu Sheikh Rayyan ya mika ma sojan hannunsa duka biyu, har a lokacin kuma yana kallon Hussain wanda shima shi yake kallo. Yasan rana mai kamar tayau zatazo, saidai baiyi tunanin abun zaizo nan kusaba, yasan tabbas makiyan shi bazasu barshi yayi muklin nan ba, makiyan ma dasuka kasance wanda suka fi kowa kusanci dashi. Babu bata lokaci sukayi waje dashi, reporters da camerorin su a daidai waje sai daukan hotuna sukeyi sunaso suyi tambayoyi amma babu dama dan an zagayeshi da sojoji. Sai bayan fitarshi sannan Ummi ta farga, she can’t process what just happeneded, me suke nufi da cewa anyi arresting mijinta, mekuma yayi. Nooo… bazai taba yuwuwa ba, this can’t happen, da gudu ta juya ta nufi dakinta dan ta dauko wayanta tayi kiran gida dan a kawo musu agaji. Alina na tsaye kaman wanda akayima wankan ruwan sanyi, idonta nakan kofa da aka bari a bude har yanxu hayaniyan bai lafaba, takasa

Chapter 5 of 11