Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ba’a fada ba amma nasamu labari danayi bincike akanshi, sannan bazai iya rike kiba, bashida karfin zuciya sai abunda iyayenshi suka fada mishi. Shikuma prince Azaan dakika ji ance bashida mutunci kawai don yanabin ra’ayin shine, babu wanda yaisa yafada mai yayi inbaiga dama ba, kowaye kuwa, shine irin wanda yakamata ki aura. Sannan daddy bazai taba cemishi no bah so baki da wani option sai shi”. for more information ga wattsapp number na 09157578540 @ Aryaah Riyad. Game of puzzle (Wasan sarƙaƙiya). By Ayraah Riyad… Book one 1. Chapter 4 Kuwait, Bayan Palace.. ( masarautar kuwait). Da ok kawai ta amsa mishi sannan ta koma ta kwantar da kanta kan chair din tareda cire glasses na idonta tasaka a bag dinta. Girgiza kafanta tafarayi sannan ta daura hannayenta dasuma suka fara rawa akan laps dinta, sannan ta fara karanto adduoi narage damuwa. Idanunta data rufe suke dan rawa, nunfashinta nafita a katse a katse, komai yahade mata bataso tazama batada abun tunani sai wannan. Batason sa kanta cikin damuwa saidai tarasa yanda zatayi da wannan halin. Bataso ta auri ridwan, infact ko ganinshi batason yi bare wani abu, gakuma prince azaan kuma, shima basonshi takeyi ba, jiya da faryal yafada mata options din taji sauki a zuciyanta, saidai yanzu datayi tunani akai saitaga babu gwara a cikinsu. Da abu daya zuwa biyu prince azaan yafi ridwan, daya shine shekaru, shi azaan still yaro ne shekaranshi 30, shikuma ridwan 49, sannan prince azaan bashida mata ko yara, ridwan nada mata mara mutunci kuwa ga yara, infact ga danshi nan faryal a gefenta, sanna shi prince azaan koba komai zai kula da ita kodan saboda daga masarautar datake, saidai kuma faryal yace ba’a fada mai yaji, dan haka zai iya yuwuwa yay mata abunda yaga dama tunda bai damu da abunda zai biyo bayaba. Saidai shi ridwan dama kowa yasan bayada zuciya mai kyau, dan haka bazata taba jin dadin zama dashi ba, gakuma matarshi haukatar da ita zasuyi wlh. Rasa yanda zatayi tayi kawai ta fara hawaye, faryal dayasan za’ayi hakan kawai ya kada kanshi ya tada mota yaja. A gida ya ajiyeta ta sauka yayi mata bye bye ta shige ciki bayanta goge hawayen dake face dinta. Tana shiga kuma a main palor suka hade da mamah, wanda kaman jiranta takeyi dama dan bata cika zama a main palor bah. Cikin sanyin murya dukda tayi iya bakin kokarinta dan yin magana normal bataso mamah tagane akwai waya damuwa a tattare da ita tace mamamah tadawo. Da ok mamah ta ansa mata sannan tace tawuce guest lounge ana jiranta. Wani dum yazrin taji kirjinta yayi mata, kardai ace ridwan ne yazo. “ mamah ban ganeba waye ke jirana”. Mamah na daddanna waya batareda ta dago ta kalleta batace mata ridwan ne. Wani kullutun bakin ciki ne yazo mata dabatasan lokacin da tay tsaki a gurin ba, da sauri mamah ta dago da face dinta tana kallon yazrin cikeda mamakin jin tayi mata tsaki “ yazrin tsaki naji kinyi?” Ta tambaya kamar dai bata yarda da abunda taji ba. Rolling eyes dinta yazrin tayi dan ranta yayi mugun baci, a kufule tace “ mamah badake nakeyi ba, idan zanmiki tsaki danayi tun jiya banjira yau ba”. Tana gama fadin hakan kuma ta wurga bag dinta kan daya daga cikin kujerun ta nufi hanyar guest lounge din, dukda tasan cewa zaizo yau meyasa baizo 4pm daya fadaba? Dan ita bama zuwan nashine yafi bata mata raiba chanza time din dayayi ne. Kofan ta bude dadan karfi ta shiga. Face dinta babu annuri ko kadan. Palour ne babba saidai yafi kama da itin hotel dinnan, yasha decoration komai a ciki white ne da coffee brown. A kan one seater dake opposite wata one seater ya zauna, jin an bude kofar yasa ya juyo, daidai nan tana shigowa. Had ido sukayi da saida yaji gabanshi ya fadi, wato idan ranta babu dadi tasaka maka idanuwan nan nata dole gabanka ya fadi. Saidai bai bari hakan ya nuna ba ya sakin mata smile yana nuna mata seat na gefenshi akan tazo ta zauna. Dan dariya tayi irin na gefen baki, sannan tabi ta gabanshi taje kujeran take opposite dinshi ta zauna. Batace dashi uffan ba shima bai mata magana ba. Infact wayanta ma ta dauko tafara daddanawa aranta tana ayyana wlh yau bazata mishi magana afarko ba, idan ya gaji da rainin wayon nashi ya mata magana, intaga dama ta ansashi. Ganin tadauki wayarta babu alaman zatayi mishi magana yasa yadanyi kwafa ciki ciki yana cije lips, tana kallonshi ta side din idonta duk abunda yayi saidai bata nuna tasan yanayi ba. Cikin voice dinshi dake cike da izzar mulki yace “ yazrin haka ake karbar bako? Ko ba’a koya miki manners bane? Ko ciwon yafara hawa kai ne?”. Da sauri ta dago kanta ta kalleshi jin maganan daya fada, saidai ganin murmushin dayayi irin yasan yanda zaiyi yasamu attention dinta ne yasa taji dama bata dago kanba. Saidai tunda ta riga ta dago sai itama ta sakin mai murmushin tareda biye mishi, cikin sanyin muryan nan nata mai sosa brain tay magana “ oh gaskiya an koyamun, saidai kasan ciwon nata gaba yahau kan ne, kaga yanzu idan na manta cewa ba’a korar baƙi na koreka badaga ni matsalan takeba”. Tafada hakan tana kallonshi ido cikin ido. Baiji dadin yanda ta mayar mai magana cikin ruwan sanyi gashi bazai iya yace tamai rashin kunya ba, sai kawai ya sauya zancen. “ toh shikenan, yanzu ya school din naki? Nasa a anso miki leave zakije nanda 2months daganan kuma bazaki kara zuwaba sai bayan mun tare abubuwa sun lafa”. Yafada yana miko mata wani envelope. Kallon envelope din tayi sannan ta dago ta kalleshi, lallai ma mutumin nan nada tabin hankali, toh inbama tabin hankali ba mai zaisa ya kalleta yamata wannan irin zancen, wato harya anso takardar leave din, zatai maganinshi. Wato so yake ya rabata da karatunta Kenan, dan daganan idan harta bari tafita daga makaranta wlh bazata koma ba, karya yakeyi bazai barta ta koma ba, saidai tunda tasan batada yanda zatayi dashi kawai ta mike ta ansa envelope din, bawai dan tayarda zatai hakan ba, dan kawai ta nuna mishi cewa hakan bai dameta ba. Hira yafara mata akan shirin auren nasu da akeyi, cewa baza’a fada ba kawai daurawa za’ayi, tunda dama babu amfanin fadan dan batada Wanda zaizo yace zai aureta, dan haka sun yanke hukuncin barin zancen kawai a fada. Itakuma amrah za’a fada, babu dalilin boye nata. Infact duniya gabadaya saitasan ana auren amrah yar Sultan Abduljabbar sarkin kuwait tareda Azlan Prince na dubai. Tana jinshi bata cemishi kala, saidai inyayi yayi saita daga mishi kai kawai, dukda abun bayamai dadi yanda take shareshi amma bai nunawa, a cewarshi dan tana waje ne takemai abunda taga dama idan ya aureta zaiga yanda zatayi. “ sannan jiya kinfita ina niqab dinki? Kindena sawa ne? Daga yau banason kara ganinki a school dinnan ba niqab”. Daga mishi kai kawai tayi, shika badan ta yarda ba, dan kawo sotake yagama abundhi yatashi yabata wuri tagaji da surutanshi. Shima bai wani kara dadewa ba dan bayan haka bai sake magana kawai kallonta yazaunayanayi ko kyaftawa bayayi, sannan bayan 5min ya mike yace mata zai tafi. Daga zaunen datake tace mishi “ ok bye bye agaida mom faryal”. Take face dinshi ta chanza yawani hada rai sai kawai yasa kanshi ya fice daga dakin. Dariya yabata, dan tasan sarai meyasa tayi magananta, bayason wani abu dazai hada wata tayi maganan matarshi, dan yafi kowa sanin balain ta, dan tasan yau da matarshi tasan zaizonan zance gurinta wlh da bazai fita gidannan ba. Dan akwai ranan data taba sawa gidan wuta yana ciki saboda yace zai kara aure. Envelope din hannunta yazrin ta kalla sannan ta ciro papern dake ciki, saidai instead taga takardar leave na makaranta hotonshi ne akyi printing akasa a ciki. Tsaki tasaki tana ajiye su a kasa. Wato gwadata yayi yaga mezatayi idan yace tabar makaranta. Tasan dagaske yakeyi, saidai meyasa zai ki bata takardar? Kokuma yariga yayi signing mata basai tayi ba, shine zaiyi mata wasa da hankali. Kwafa tayi sannan ta tashi tanufi gurin daddy. Yau thursday dan haka tasan daddy na gida, ran Thursday babu fada. A floor 6 yake wanda shine highest floor na gidan, tana isa tayi ringing doorbell tajira 1min sanna ta shiga. Hadadden palor ne daga kashiga ya hadu iya haduwa komi na ciki white ne da blue, daddy ta hango zaune akan royal themed chair dinshi one seater yana karanta newspaper. Karasawa tayi inda yake sannan ta zauna a kujeran dake opposite dinshi. Dagowa yayi ya kalleta yana sakin mata smile, itama tayi mishi smiling sannan yayi mata alaman tazo. Hugging dinta yayi ta side sannan yasa bayan hannunshi yana taba wuyanta. Jin dazafi yasa yace “ yazrin bazaki amiki. Monthly checkup dinba ko? Tun jiya yakamata kije gashi haryau bakije ba”. Dan turo baki tayi sannan tace mishi zataje. Ta koma kujera ta zauna. Ganin yaki mata magana akan abunda yafaru jiya ne yasa ta danne zuciyanta ita zatai mishi, dukda tanajin babu dadin abunda yamata amma tanaso taji meyasa zaiyi hakan. “ daddy meyasa ka yanke hukunci irin wanda kayi jiya? Batareda kaji ta bakina ba?”. Muryanta nadan karkarwa tay maganan. Badan komi ba saidon bataso ta kullace shi. Bai kalleta ba saidai cikin dakakkiyar murya yace “ yazrin bazaki gane ba, keba kamar kowa bace, kinada bukatan me kula dake”. “ toh amma daddy ku bazaku kula dani ba? Meyasa sai dole ta hakan ne za’a kula dani, sannan kamanta alkawarin dakamun cewa bazaka sake yanke mun hukunci abunda yashfi rayuwata batareda kaji daga bakina ba? Ko ka manta waye matar ridwan? So kuke ku kasheni?”. “Dakata yazrin, ke yata ce amma bazan bari ina magana kinayi bah, decision nariga nayi making dinshi, banason sake jin wani complain”. Ya karasa yana daukar newspaper fin yacigaba da karantawa. Kwalla ce taciciko idonta saidai bata bari ta zubo bah, kallonshi kawai takeyi takasa banbance mema takeji a zuciyanta. Tarasa matsayinta a gidannan, minti daya su nuna mata so cikin kankanin lokaci kuma sununa mata basu damu da ita ba. Jiki a sanyaye ta tashi ta nufi waje, muryarshi ta isko ta yana fadin “ sannan nasamu labarin kinje school jiya ba niqab, dan freedom damuka baki kike dauka bazan iya komawa ina monitoring din duk wani abu dakikeyi ba ko?”. Bata ansa ba ta bude kofan ta fita, dan batada abun fada. Ta tsani niqab dasuke sata sawa, ta zaci tunda andena mata magana akan niqab din zata iya dena sawa, ashe suna sane da ita. Dakinta ta wuce ta shiga toilet tai wanka tasa kayan zaman gida silk gown kamar night gown saidai tafi nightgown kauri. Sannan ta kunna turaren wuta mai sanyin kanshi dakin ya bude da kanshi. Gado ta fada ta kwanta tanajin gajiya na saukan mata. Sotake taje tayi checkup din amma batada wani energy. Wayarta ta dauka sannan ta shiga chat dinsu da far yake I don’t know how yu. File din prince azaan ya turo mata, budewa tayi tafara karantawa. File ne sosai na duk wasu abubuwa dangane dashi, hatta irin abuncin dayakeci, da turaren da yake sawa kai harda lokacin dayake tashi barci akwai ciki. W Tadan jima tana karantawa kafin takai karshen shi, dan yana da yawa sosai. kasan hotunan shine wajen ten a karshen an daukesu from different angles. Guy din ya hadu sosai ita kanta yazrin ta shaida, gashi dogo sannan ya iya sa kaya. Saidai ayanda ta karanta file din gaskiya mutunne mai mugun wuyan sha’ani, infact yanzu bama ya kasarsu, yabar abu dhabi yatafi Russia, wai an hadashi aure da princess na bahrain shinr yabar kasar, acewanshi wanda suka gada auren sa auri yarinyan, shi baiyi niyya ba bakuma zai aureta ba. Ajiyan zuciya ta sauke, tanajin hope dinta na mutuwa, tunda har bai yarda ya auri princess na bahrain ba ita me zaisa ya yarda ya aureta. Kaman tayi ihu haka takeji, zanzu yazatayi. Message ne ya shigo wayan nata, faryal ne yayi mata message, kaman yasan metake tunani. “ babygurl karki damu da matsalar shi da bahrain, saboda tace tanasonshi shine yaki yarda, amma ke ai bacewa zakiyi kinason shiba ko?”. Yes ta tura mishi dan yanada gaskiya ita tanuna tana sonshi sannan suka tuntubi Abu Dhabi, wurgar da wayar tayi tana kifa kanta akan pillow. Wani razanannen kara ne ya daki dodon kunninta…. for more information ga wattsapp numberna 09157578540 Game of puzzle (Wasan sarƙaƙiya). By Ayraah Riyad… Book one 1. Chapter 5 Kuwait, Bayan Palace.. ( masarautar kuwait). A ruɗe ta mike tana kalle kallen daga inda karan yafito. Daga gefenta ta hango glass cup a fashe a kasa, alaman shiyayi karan. Dage kai tayi tana rintse ido, lallai yakamata taje checkup dinnan, dan abubuwa sunfara dagule mata lissafi, komi na jikinta yazama sensitive hatta kunninta, shiyasa duk kankantan kara saitaji shi har cikin brain dinta. Tashi tayi badan tanaso ba tadauko abaya ta zura a jikinta batasa mayafi ba ta shiga elevator. Part na daddy tayi niyyan zuwa dan ya kira mata doctor Katherine tazo tayi mata checkup abata magungunanta na month din kota samu tadanji dadin jikinta, saidai tuna abunda yafaru tsakaninsu sannan kuma bataso taganshi yanzu, dan zuciyanta naraya mata abubuwa marasa dadi akanshi, bakuma taso dan koma menene shi mahaifinta ne, bataso saboda abu daya yazama tazo tanajin zafinshi. Dan haka sai kawai ta wuce part na mamah. Yafita daban yanayin yanda gidan yake, dan kusan komai akwai color a jikinshi sabanin yanda gidan yake fari sai wani dan color din. Nata kawai kaloli ne kaman rainbow kujerun palour blue royal set, flooring dinkuma hardwood ne brown, curtains orange ga paint kuma red, gakuma hadadden kanshin bakhur dake tashi mai dan karfi. Wani iri colors din sukeyi a idon yazrin, dan batason colors musamman masu daukan ido, saitaji brain dinta nawayi dum kamar maijin barci. Straight dakin mamah tanufa tayi knocking, saidai babu wanda ya ansata. Kara karfin knocking din tayi dayasa hannunta fara ciwo ciwo, saidai still babu ansa. Tura kofar dakin tayi saidai batafa kowa bah. Dan hada rai tayi tana tunanin toh ina mamah take? Tadaisan yau babu wani abu da mamah keyi, dan daddy na gida so bata komai. Hannunta ta daura akanta tana juya idonta, meyasa ma batayi tunanin tana gurin daddy bah? Dan tsaki tayi ganin ta bata lokacinta abanza, sannan ta juya ta nufa part din daddy, aranta tana raya bama zata kalli daddyn ba bare taji wani abu. Part din ta nufa sannan ta murda kofan ta shiga. A palour ta gansu dady na zaune kujeran data barshi, mamah na wanda ke gefenshi two seater ayaan na zaune gefenta, sai amrah dake zaune a kasa ta jinginada kafar daddy, saidai bataga azlan ba. Kallon projector board sukeyi suna dan hira, face dinsu very serious, alaman suna wani abu very important kenan. Dan tsayawa tayi tana kallonsu, tanajin wani iri a zuciyanta ganinsu a tare batareda itaba. Gyara face dinta tayi sannan takarasa shiga ciki bakinta dauke da sallama. Mamah da ayaan ne suka dago da kallonsu gareta, mamah face dinta ba yabi ba fallasa ayaan kuma yayi mata smiling, while amrah da daddy basu nuna sunsan da itaba. Itama smiling tayima ayaan sannan tasanu chair dake kusada nasu ta zauna tana mayarda idonta inda suke kallo. Projector board ne anyi projecting wani project. Da mamakinta saitaga project ne akan libraryn kasar, her favorite guri a duniyan nan. Fadada smile din face dinta tayi tana kallon abunda ake projecting tanaso tagane menene sukeso suyi, dan a iya saninta libraryn lafiyanshi law baya bukatan wani gyara ko wani abu. Saida aka kusa gama playing abun tagane menene. Wato so akeyi a bude libraryn into a museum da manyan mutane da shuwagabanin da sarakuna za’ayi musu organizing dinshi yazama museum dayafi kowanne tarihi dakuma muhimmanci a middle east gaba daya, wanda a yanzu museum na egypt shine yake rike da wannan title din, so sunaso nasu yazama shine number one. Strategies suka fara discussing akan yanda za’ayi hakan a cikin wata uku, dan daddy naso yazama anyishi sannan an budeshi ranan engagement na amrah, so kowa na tofa albarkacin bakinshi dakuma bada shawarwari akan yanda za’ayi hakan cikin wannan kankanin lokacin. Yazrin ma tana ji sannan tana tunanin yanda za’ayi hakan, a kasan zuciyanta kuma tunani takeyi ya akayi ba’a fada mata dawuri bah? Infact inbata zo part dinba yanzu kenan baza’a fada mataba?. Saidai ta ture tunanin gefe dan ta dawo da hankalinta akan abunda suke fada dan yafi mata anfani yanzu. Ayaan ne ke bada shawaran a mayarda libraryn dakuma building na artifacts yazama guri daya, saboda komai yazama organized, sannan ba koma yakamata asa ba, abubuwan da suka fi komai dadewa a ciki za’ayi displaying, saboda anfi daraja abunda ya dade. Amrah kuma nabada shawaran no abar komai a inda yake, dan idan aka hadesu zaizama kaman an an hada ruwa da wuta ne, dan littafai basa haduwa da artifacts, musamman ma kuma da tun baya kowa yasan ba guri daya suke ba, dan haka za’ayi losing history idan aka rabasu, sannan kuma ayi displaying wayanda sukafi zama popular wanda anriga an sansu. Yazrin dake binsu da kallo kowa na kawo evidence dakuma dalilan dazaisa a dauki nashi shawaran. Saidai ita duk shawaran basuyi mataba. Idan akabi na ayaan aka hadesu guri daya zai zama babu anfanin rabasu tun farkon da aka wallafa libraryn daban dakuma vault( ginin da artifacts din suke) daban daban tun farko, sannan history zaizama ana badashi ne a inda ak wallafa abun, bazai yu kazo kana bada historyn abu ba bayan ka daukeshi daga inda historyn nashi ya wallafa. Sannan kuma idan akace za’a dauko abubuwa dasuka fi dadewa da gaskiyan ayaan mutane musamman manya sarakuna zasugi daraja shi, dan ko a mutane ne anfi daraja babba aka yaro, idan aka biye ma amrah aka dauko wanda sukafi zama popular sannan an riga an sansu zaizama babu abunda zai dauki hankalinsu a gurin, tunda sunriga sunsan komai a gurin. Baki ta bude dan ta bada nata shawaran, sai kuma tayi saurin rufewa tana kokwanton ko ta fada ko kawai tayi shiru., tasan ba lallai abi nata ba, saidai kuma tuna cewa kusan tafi kowa sanin kan library dakuma vault of artifacts din ne yasa ta cire kokwanton, voice dinta cike da confidence ta fara “ ni inaganin a bar komai a inda yake, saboda su kansu ma’ajiyar ai history ne mai zaman kanshi, sannan kuma kada asa abubuwan da aka riga aka sani suke popular, a dauki wayanda suka fo dadewa dakuma tarihi ayi displaying dinsu, saidai dole a nemi inda za’asa littafai dakuma documents dasuke ba kowa za’a bude yagani ba, dan bamusan waye kuma zaizama enermy dinmu nan gaba ba”. Ayaan ne ya daga mata hannu alamun tayi kokari, mamah kuma ta juya face dinta so yazrin bata ganin expression dinta, amrah ma dagowa tayi tana binta da wani kallo mai wuyan fassarawa, saidai yazrin tasan kallon meye, bataga dalilin da yazrin din zatayi magana bane harta nuna abunda tafada baiyiba. Daddy da baiyi magana ba shima ya juyo da kallonshi kan yazrin, fuskanshi dadan smile akanta, cikin voice na tausasawa yace “ no need yazrin karki damu, Amrah zataji da komai”. Nunfashinta ne yawani katse, kirjinta yawani buga da karfin gaske, tanajin words din na yawo a tsakiyan brain dinta, takasa yarda da abunda taji. Kara karanto words din tayi a cikin brain dinta, for a second tayi tunanin suma zatayi. Lumshe idanu tayi. Sannan ta bude tareda kafe idanunta akan hardwood floor na palorn, sotake ta bace ko ta nitse, komai ma akan ta dago ido ta kalli daya daga cikinsu. Bata taba sanin matsayinta dakuma yanda suka ajiyeta yakai wannan na rashin mutuncin ba saiyau, sotake ta bude baki ta tambayi daddy meya maida ta, meyasa zaiyi mata haka saidai babu abunda zai fito daga bakinta. Mikewa tayi a wani hankali still kanta a kasa, takasa tunanin komai kawai brain dinta ya kulle, kafafunta dabama ta jinsa a jikinta tafara ja ta nufi waje, tanajin yanda gwiwanta ya bugi kujera saidai bata tsaya kota nuna wani abuba, dan bama taji zafin hakanba. Dakinta ta nufa tana shiga ta rufe kofan ta zube a kasa. Wayarta ta dago daga hannunta tayi dialing numbern faryal. Ringing biyu ya daga yana fadin “ hello babygurl”. Kuka ta sakinmai dabatama san tana rikedashi ba. Tambayanta yafarayi meyafaru, saidai takasa tama bude baki tai magana. Saida tayi mai isanta sannan tasamu tafara bashi labarin meya faru. “ faryal daddy ya kwace role daya bani a library, za’a maidashi museum sannan yace amrah ce zatayi, yace basai nayi komai ba yaba amrah ragamar komai tayi. Faryal shikenan banida wani anfani a cikin wannan masarautar, banida anfani a cikin gidan mu, yanzu shikenan an shafe babi na daga wannan ranan, zasu aura min ridwan ne kawai dan su kawar dani banida wani anfani a gurinsu faryal basa sona, sunsan yanda libraryn nan yake a wajena banida wani abu daya fishi sannan suka dauka sukaba amrah”. Voice dinta har wani daukewa yakeyi nunfashinta na janyewa kaman mai asthma. Jikinta yadau zafi kawai jira takeyi taji maizai cemata, dan shiru yayi sannan ya tambayeta ya akayi har akazo kan hakan. Tun daga farko har karshen abunda yafaru tafada mai tanajin yanda jikinta ke karkarwa, wayar ma dakyar ta iya riketa. Shiru yayi baice komai ba wajen 3 minutes, sannan cikin normal voice dinshi yace “ yazrin daddy nada point, kinyi abunda zakiyi kibar amrah tayi handling sauran, ke hutu kika samu yanzu”. Shiru tayi tanajin saukan words din, a batareda tasake cewa komai ba ta katse wayar, dan tagama jin abunda zataji. Yanzu dama kowa hake yake daukanta kenan, cewa bazata iya komai ba, cewa amrah tafita kenan, faryal datake ganin yasanta yakuma yi understanding dinta, faryal da shine mutun na farko datake nema idan tana bukatan a sanyaya mata zuciya abi bayanta idan kowa ya juya mata baya shima ashe a hakan ya dauketa. Sauke wata nannauyiyar ajiyar zuciya tayi. Shin ko dagaske hakan takene? Shin dagaske kowa yakeyi akanta kenan bazata iya wani abu bah? Baza a iya bata abu mai muhimmaci tayi ba. Girgiza kanta tayi takasa yarda da hakan, bazai taba yuwuwa ba, sannan zata nunama duniya cewa itadin zata iya duk wani abu dawani zai iya. Bataso tayi gasa da amrah, saidai abun kullun karuwa yakeyi, tana duk iya bakin kokarinta dan ganin cewa bata shiga abubuwan da amrah keyi, saidai hakan bazai cigaba da faruwa ba, zata nunama daddy da mamah dama kowa cewa amrah bata fita da komai ba. Nunfashi taja tana jin nunfashin na daidaituwa, mikewa tayi tanufa side drawer dan ajiye wayarta, harta ajiye wani abu yaja hankalinta ta juyo, karamar envelope ce baka kaman wanda ake sa letter a ciki irin nada, anyi sealing dinshi da red wax, jikinshi anyi zanen maciji, kallon lettern tayi tana kokwanton kota dauka kokuma karta taba dan bata san daga ina yakeba, sannan tambarin dake jiki na maciji baiyi kamada wanda ta sani ba, toh waye zai iya yashigo har dakinta ya ajiye mata letter bayan kowa nagidan na part na daddy, azlan kuma tanada tabbacin baya masarautar dan da yananan dazata ganshi a part na daddy, toh waye ya ajiye wannan lettern kuma menene a cikinshi?….. ( toh fah, waye ya ajiye lettern? Babu kowa dai a gidan banda su, sannan kuyangu basa hawo musu part indai ba tare suke da daya daga cikin yan gidan ba, koda kuwa sun hawo dakunansu sunada facial recognition system da idan ba daya daga cikin yan gidan ba babu wanda kofar zata budewa). for more information ga wattsapp number na 09157578540 Game of puzzle (Wasan sarƙaƙiya). By Ayraah Riyad… Book one 1. Chapter 6 Kuwait, Bayan Palace.. ( masarautar kuwait). Daukan envelope din Tayi hannunta nadan rawa ta bude. White paper ne a ciki ba’a ko ninkata ba, handwritten note ne layi biyu, an rubuta da jan ink “ Sheikh Abduljabbars private office, zaki samu abunda kike bukata, don’t worry about the cctv camera,”. Kara karanta words din tayi, sotake tagane waye zai aiko mata da

Chapter 4 of 11