Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
tafiyanta, mutun dayane tafita fans da abubuwa itace princess of Qatar princess Alina bin malik. a dayen bangaren kuwa yazrin tunda aka haifeta bata tabayin lafiya ba, cutar field disease aka haifeta dashi wanda itace mutun na uku a duniya daya taba yin cutar, cuta ce mai kashe garkuwar mutun a hankali harsai ta kashe shi, sanna kwanansu kadan ne a duniya, basa dadewa, wani lokacin har brain dinsu take tabawa. Dan haka tunda aka haifeta babu wanda yasanta a duniya, a kasar ma kowa dai yasan matar sarkin kuwait ta haifi ya amma babu wanda ya ganta, sannan tsananin rashin lafiya saida tayi shekara bakwai bata mike tayi tafiya kokuma magana ba, infact saida tayi shekara goma sannan ciwon ya lafa tasamu aka fara koya mata karatu a gida, yau lafiya gobe babu, a haka har tayi 15years , dan Allah yayi tanada brain sosai dan haka bama zaka taba gane bataje school ba, saidai mu’amalan ta da mutane zaka gane bata saba da mutane ba, dan da bama ta iya dogon magana da mutun, saida tayi 16 years harta kusa 17 shine daddy ya yarda ta shiga university, shima saida ya hadata da faryal dakuma securities dan bai yarda tana mu’amala da mutane ba, indai ba faryal ba da wasu cousins din, a cewar shi zasu iya mata wayau tafada musu sirrin masarauta. Sannan baya bari tana shiga harkar masarauta, shiyasa babu wanda yataba zuwa dacewan yana sonta kokuma masarautar dasuka nuna sha’awan sunaso dansu ya aure ta, dan koda aka santa bayan ta fara zuwa school, media sun dauki hotunanta tayi trending sosai harta samu title din most beautiful girl and princess in the world, mutane na fadin cewa tafi amrah kyau dakomai, saidai banda kyau babu abunda zata nunama amrah, dan amrah tafita komai, sannan masarautu basa auren kyau, auren jafi sukeyi, yanda zasu amfana da juna, shiyasa babu mai maganan yazrin dan a ganinsu bazata kara musu komai ba, dan wayanda suke zuwa domin neman auren amrah idan aka fada musu cewa an riga an bawa azlan aurenta saidai yazrin basa kara dawowa. Yazrin ma kawai tunanin yanda rayuwanta zai kasanse takeyi, ringing din wayan faryal wanda muryan yazrin ne tana fadin ‘faryal why are you not answering my phone tun jiya? Zan biyoka gidanku fah’. Kanaji kasan AI generated ne, juya idonta tayi jin yauma ya chanza ringing tone din nashi, bashida aikinyi sai amfani da voice chat dinta yana sawa a ringing tone, yau yasa wannan gobe yasa wanchan. Wayan ya ciro daga cikin pocket dinshi yana kallon mai kiran, an rubuta “prince ayaan”. Juyawa yazrin wayan yayi ta kalli mai kiran sannan ta juya kanta gefe tana kallon waje, shikuma ya dauki wayan yasa a speaker. Gaisawa sukayi da ayaan sannan ayaan ya tambayeshi ina yazrin, a take yace mishi gatanan, ya tambayeshi a ina suke yace mishi suna zeyz massage palour, “ ok ku juyo ka kawo yazrin gida nanda 40minutes ina jiranku”. Da ok ya ansa sannan ya katse wayan yana tada mota, basu kara magana ba har saida sukayi kusa rabin tafiyan sannan yazrin ta juyo takalleshi “ lets go with the second option, ka bincika mun princes din ka kawo mu zaba, zanyi tunanin abunda zanyi”. Gyada mata kai yayi. A daidai gate na shiga part dinsu suka tsaya akayi security checks sannan aka bude musu, goge face dinta tayi sannan ta gyara mayafinta, yana parking motan ta sauka, batako juyoba harta kai kofar shiga, sannan still batare data juyoba ta daga mishi hannu sannan ta shiga ciki. Direct dining ta nufa dan tasan nan tabar wayanta, saidai koda ta shiga babu wayan a inda ta zauna, babu kuma kowa a dining din. Tasan waye zai daukan mata waya, ayaan ne ba kowaba, dan haka fitowa kawai tayi ta nufa room dinta. Tana shiga straight toilet tayi ta watsa ruwa a jikinta sannan ta wanke face dinta ta fito daure da white soft towel a jikinta, ayaan ta gani kwance kan bed dinta yana daddanna wayarta, jin an bude kifan toilet ya dago ya kalleta, da sauri ta dauke kai ta shige walkin closet sannan tasa pj white a jikinta. Koda ta fito kallo daya yayi mata yacigaba da abunda yakeyi, itama batabi ta kanshi ba saima kara hada rai takeyi, danma yasan ranta a bace yake. Gaban mirror ta tsaya ta shafa moisturizers a jikinta sannan ta kunna AC a dakin jin yayi zafi dayawa, dan bata cika son AC bah. Bed ta nufo ta dayen side din da yake tahau ta kwanta tareda juyamai baya, ta dago silk bed wrap ta rufe jikinta tana karanto addu’an bacci. Muryan ayaan ne ya katse mata adduan datakeyi “ yazrin yau bazaa mun magana bane? Nima nazama amrah ne? Toh ga wayarki tunda bacci zakiyi, gobe da daddare zan fita dake outing mu zaga gari saimuyi hira koh? Saiki fadamun menayi miki ake share big brother”. Hannu ta mika mishi yasa mata wayan sannan ya sauko ya zagayo inda take ya manna mata kiss a goshi yana fadin good night baby sis. Cikin yar karaman voice kaman wanda bata iya magana ba tace “ good night to you too”. Sannan ta daura bargon har a kanta. Jin an kashe fitilan dakin tareda bude kofa da rufewa yasa tayi saurin ciro kanta daga wrap din dan harya fara sarke mata nunfashi, bata iya shiga kanta cikin bargo saboda nunfashi, da gangar taki mishi magana dan ya bata mata rai, takasa gane wani irin wasa da hankali suke mata daga shi har mamah da daddy, yau su nuna suna sonta kaman duniya ta tashi, gobe kuma su shareta suyi mata abunda sukaga dama, abun yana mugun damunta sosai, da kullun hakanta faru saita zauna tana kuka, amma yanzu yabi jikinta. Notifications akayi mata a wayanta ta dauka danta gani, daga instagram ne an rubuta princess Aryaa, budewa tayi ta shiga, page ne na princess din Qatar, kyakyawan yarinyace ajin farko bazata wuce shekara 18bah, tafi kowace princess ko prince followers a duniya, tanada wajen 300m followers a instagram kadai, sannan itace akaba title na most beautiful princess infact woman in the world sannan amrah. Post tayi na invitation zuwa ga anniversary celebration na yarjejeniyar zaman lafiya da akayi a tsakanin Iran da Qatar, na wajen shekara dari kenan. Fita yazrin tayi jin bacci nadan fizgarta. Ta ajiye wayan tareda rufe idanunta bacci yay awon gaba da ita. 4hours later…. Jin baccin na sakinta ne yasata bude ido tareda daga hannunta dan tayi mika tareda bude bakinta domin karanto adduan tashi daga bacci, saidai banda bude idanunta babu abunda ya yuwu a ciki, nandanan kuma dakin ya dauki wani duhu dayasa taji gabanta yawani fadi ras dan tasan meke shirin faruwa. Sanyi dakin yafara dauka tareda fara haske dan saida hasken yafara yima idonta yawa saidai takasa koda ta rintse idon ne, wasu irin halittu ne suka fara forming masu ban tsoro, bazakace ga suffan suba dan basuda ita, saidai duk wanda yay arba da koda dayansu ne mawuyaci ne hankalinshi bai gusheba, dan bawai hallitar ne abun tsoratarwar ba gaba daya, abunda sukeyi da mutun ne abun tsoratarwa. Matsowa kusada ita suka farayi su uku ne amma sun cika dakin gabadaya, ga tsananin hasken da dakin yayi yasa kake ganinsu tartar gasu bakake wul. Daidai bakin gadonta suka tsaya, nandanan kuma dakin gabadaya yakoma kaman irin manya manyan hotel dinnan ta baya gurin swimming area, ga swimming pool nan mantarere kaman kasa mutane dari a ciki, gakuma zagaye dashi mutane ne maza da mata suna zazzune akan beach chairs babu runfa dayake indoor pool be so ba rana. Kaman daga sama taji an dagata dukda bawani hannu kokuma alaman wani abune ya dagata, sannan aka wurgata cikin swimming pool din, razanannen ihu tasaka tareda kokarin dago jikinta dan tuni ta nitse, saiki taji jikinta yasaki tadawo tana iya motsa jikinta. Saidai kash, bata iya swimming ba, cikin kadewa tafara ihu a cikin ruwan saidai ba fitowa yakeyi ba tunda cikin ruwa take, dakyar ta dago da kanta tana kalle kalle da yunkurin komawa gefe danta fito, babu alaman dakinta ma dan gurin yakoma complete swimming area ne, mutanen gurin ne sukahau mata dariya suna chemata ta nitse, wasu na jifanta da coconut beach drink dinsu dayasa ta kara nitsewa, dakyar shima ta kara yowa sama da kanta tana ihun a taimake ta, saidai babu wanda yabi takanta. Tana cikin haka kuma taga face din Nara daga cikin mutanen tana mata dariya tareda motsa bakinta dukda bakajin sautin amma tagane metake fada ‘ki mutu yazrin kowa ya huta, bakida amfani a duniya’. Wani irin abu ne ya tokare mata a makwogwara ganin amrah, tuni kuma ta kara lumewa cikin ruwan, saidai a wannan karon bata iya tayo sama ba, tun tana iya rike nunfashinta tana kokarin yin sama harta kasa tuni ta shaki ruwa, wani irin ƙuna ne dayafara tun daga hancinta har zuwa makwogwaronta, kirjinta kuma kaman an daura mata dutsen dayafi kowanne girma da nauyi a duniya, idonta yafara sauyawa tanaganin duhu duhu, azaba ta cikata ta koina, kafin a hankali taji rai nafita daga jikinta. Dogon nunfashi ta sauke tareda mikewa zunbur, saidai jikinta dayayi mata nauyi yasata komawa ta kwanta babu shiri, jin wannan ƙunan a makwogwaronta da nauyin dake kirjinta tareda taste din ruwa me chemical yasata tuna abundayafaru, dasauri kuma ta fara bin dakin da kallo, ajiyan zuciya ta saki tareda sakin wani marayan kukan murna tasaki ganinta a dakinta kuma kan gadonta. Saidai murnar komawa ciki tayi jin an bude kofar….. for more information ga wattsapp number na 09157578540 @Aryaah Riyad. Game of puzzle (Wasan sarƙaƙiya). By Aryaah Riyad.. Book one 1…. Chapter 2….. Kuwait, Bayan Palace…… ( masarautar kuwait). Da wani azababben sauri ta juyarda kanta zuwa ga kofan harsaida wuyanta yay kara, saidai ba wannan ne gabanta ba, dan dishi dishi take gani amma hakan bai hanata ganin sarai waye a kofan ba, mamah ce ta bude ta shigo tana sanye da nightgown alaman yanzu ta tashi. Da sauri yazrin ta juyar da kanta, sotake tayi kaman tayi bacci amma tasan mamah ta ganta, dan haka sai kawai ta juyar da kanta tareda gyara kwanciyanta. Hasken dakin mamah ta kara dan wanchan babu wani haske sosai irindai na barci ne. Gabanta tazo ta tsaya tana kallon face dinta dayayi ja sosai gashi yayi chaba chaba da hawaye, rintse idanunta yazrin tayi jin kallon kurilla da mamah ke mata, addua kawai takeyi a zuciyanta kada mamah tagane cewa mafarkin nan takoma yi, dan babu abunda ke wuce idanun mamah kamar macijiya. Gefen ta mamah ta zauna sannan ta daura hannunta a face na yazrin tareda share mata hawayen fuskanta, kwace face dinta yazrin tayi tana bude jajayen idanunta akan mamah, batasan meyasa ba kawai ranta baci yayi ganin mamah yanzu, inatake jiya datake nemanta? Take neman wanda zai tsaya mata koya rarrasheta? Sai yau ne zatazo tawani nuna mata kulawa. Mamaki ne ya kama mamah ganin yazrin ta kwace face dinta, saidai tasan da dalili akan hakan, shiyasa ma batace komai ta ta mike tashiga toilet. Ruwan wanka ta hada mata mai zafi sannan ta fito harzata shiga closet kuma ta fasa ta juyo, dan yazrin bataso ana bata kayan da zatasa tun tana karama, sai wanda ta zaba. Kara dawowa inda yazrin din take tayi “ yazrin baby tashi ki shiga toilet kiyi brush kiy wanka saikizo kisha maganinki, naga jiya kwata kwata baki shaba gashi kindawo kina mafarke mafarken nan”. Wani yawu yazrin ta hadiye sannan cikin murya irinta safiya dakuma rashin son magana tace “ mabah niba mafarke mafarke nakeyi ba, abunda kuke shirin yi mun shiyasani a damuwa, dan banma samu nayi barci ba bare nayi wani mafarki, magani kuma kin manta yakare?”. Tafada ranta babu dadi kuma zaka gane hakan a yanayin magananta. Daga haka ta mike dakyar tanajin kasusuwanta na gogan juna, ga kirjinta da haryanzu nauyi yake mata dan dakyar ta iya mikewa straight. Toilet din ta nufa tana tafiya dadan sauri dan bataso mamah tagama karance ta, the last thing datakeso wani a gidan nan yasani shine batada lafiya ko tana mafarke mafarke, dan yanzu yanzu zasu hanata zuwa school dakuma library, wanda sukadai ne abubuwa datake yi a duniya tajita kamar cikakkiyar mutun yanzu. Toilet din ta shiga ta rufo kofa tareda sakin ajiyar zuciya, batareda ta cire kayan jikinta ba dan batada kargin yin hakan ta shige jacuzzin. Yanda ruwan zafin ke ratsa jikinta yake bata wani niima mai dadi. Jikinta nanan amma kunninta naga kofa, sotake taji ko mamah ta fice daga dakin, saidai babu sound ko daya, nanne ta tuna kuma cewa dakin soundproof ne, so bazataji komai ba. Tsaki taja aranta tana fadin who cares? Inma tananan inma tafita bata damu ba. Saida taji jikinta yamata dadi sannan ta mike ta cire pj din jikinta ta fito a jaccuzi din tareda draining ruwan ciki. Shower ta nufa ta kunna ruwan dumi sannan ta wanke jikinta ta fito daure da towel a jikinta daya kuma ta daure gashinta dashi, bata nuna tasan da zaman mamah dake zaune kan bed dinta bah. Gaban Mirror tazo ta zauna tayi yan shafe shafenta sannan ta saki gashinta. Har tsakiyan baya ya zubo mata tasa towel din tana gogeshi a hankali, mayukan gashinta na Augustinus bader & sisley, one of the most expensive haircare brand in the world, ta shashafa products din wajen guda 8, sannan ta taje shi. Scrunchie ta dauko ta daureshi a baya kaman donut sannan ta shiga toilet ta wanko hannayenta tareda dauro alwala ta fito ta tada sallah. Bayan ta idar ta mike ta nufi. Walk in closet ta dauko wata ocean green abaya mara kwalliya very plain, sanna ta dauki wata dark green alkyabba da akayi decorating dinshi ta gefe da gefe da rhinestones dakuma royal embroidery shima maroon and black color. White mayafi ta dauka irin na abaya da akayi mishi similar embroidery da alkyabbar a gefe da gefenshi ta yafa a kanta, yazamana kawai daura shi tayi batareda ta linkashi gefe da gefe ba, kawai ta sakeshi a gaban alkyabbar dan gaban gashinta dayake a cike a kuma kwance yasha gyara a waje yau bata rufe shiba. Sannan ta dauki ocean green loubotin heels ta saka tareda daukan black shades na dior ta sa a idonta, takuma dauki wrist watch dan siriri dazaka zata band ne, saidai watch ne tasa a hanun damanta. Fitowa tayi ta tsaya a mirror tana kallon kanta. Tayi wani fitinannen kyau kamar wata hurul ayn, idanka ganta saika ratse ba mutun bace, ga lips dinta da batasa ko janbaki ba banda lip gloss sai kyalli yakeyi yayi ja kaman tasa lipstick. Saida ta tabbatar tayi ma kanta kyau yanda takeso sannan ta koma ta dauko birkin bag dinta, a jere suke a side daya wajen guda 30 different colors, su a side daya kawai suke ga wasu sides din kuma wasu different designer bags dinne sunfi 50 a kirge, green birkin din ta dauko yahadu da kayanta sosai sannan ta fice. A tsakiyan dakin ta tsaya sannan ta juyo ta kalli mamah, “ mamah am off to school, idan na dawo nayi monthly check up din, ayi prescribing maganin na wannan month din”. Tana gama fadin haka kuma ta juya zata fice, jin mamah na magana yasa ta tsaya “ gobe ayi check up din, yau by 4pm ridwan zaizo, so ki dawo daga school da wuri”. Ti tayi kamar batasan me mamah tafada bah, ta juyo ta lalleta sau daya sannan ta bude kofa ta fice. Girgiza kai mamah tayi sannan ta mike ta fice itama daga dakin ta koma nata. Yazrin na saukowa suka hade da amrah, itama tayi gayu sanye da green alkyabba she’s dressed to the nines, saida yazrin tayi kasa da kanta sannan ta kalleta, dan dama tafita tsawo gashi kuma tasa heels, abun saikagani, wasu kuyangu ne su hudu mata a bayanta kowanne rike da tray yazrin na gani tasan azlan zataje kaima abinci. Rashin dadin yanda yazrin ke kallonta ta sama amrah taji, sam bambancin tsayinsu na kona mata zuciya, dan gani takeyi kaman yazrin din ta raina tane, gakuma wani irin kyau datakeyi koba kwalliya a face dinta, ta tsani taga wani yafita kyau ko Aura, ga ko yanda yazrin ke tsaye kaman wata high end model. Dason kular da yazrin din kuma saitayi murmushi tana fadin “ little sis, congrats fah, zaki auri daddyn bestie dinki, kinga shikenan keda faryal kunzama mom and son, zaku kara shakuwa kenan fiye da yanzu koh”. Tana gama fadin hakan kuma tabi ta saide din yazrin ta wuce, kuyanjin bayanta ma sukabi ta gefenta suka dan sunnar dakai alaman gaisuwa suka wuce biyeda amrah a baya. Yazrin bata bari face dinta ya chanza ba ta kura ma amrah ido, saidai amrah nagama fada ta wuce hakan yasa itama tayi wucewanta ta nufa dining. Babu kowa a dining din sai abunci kawai da aka jera. Usual tea dinta ta zuba ta dauki garlic bread da salted butter ta shafa a jiki ta fara ci ahankali. Saida tagama cin bread din sannan ta dauki tea din ta kurbe tana duba agogon hannunta, gani tayi still its 6:50am 7 am batayiba yasa ta fito main palour dayake makeke, set uku ne na kujeru a ciki kowanne a nashi side dib saiyayi kaman palour uku ne a cikin daya. Center set din ta nufa ta zauna akan leaning 3seater seat din white color tadan kwantar da kanta akan hannun chair din dan ta jira 7 tayi sannan ta tafi. Dan rufe ido tayi tanaso tadan maida bacci, saidai tana rufewa face din ridwan take gani, kokarin ture tunanin shi takeyi daga zuciyanta saidai hakan yaki yuwuwa, gashi yau dole zata ganshi, kawai hango ta takeyi wai ita za’a aurama wannan mutumin? No ina bazai yuwu bah wlh, ga matarshi maman faryal matan nan mugun kishi ne da ita, ga masifa da rashin tausayi dan kuyangu a part dinta guduwa sukeyi tsabar balain ta, sannan bata daukan masu kyau, dan a cewarta zasu kwace mata miji, shine su mamah sukeson chusata su hadata da mahaukaciyar matannan. Jin takasa cire tunanin daga zuciyanta gakuma ciwo da kanta keson farawa dan jiya batayi bacci da wuri bah gakuma mafarkin nan datayi duk sun hade mata ga tunani, kawai ta dauko wayarta ta shiga instagram. Page din amrah ta shiga tanada wajen 200m followers, following list ta shiga wanda amrah ke following, basufi mutun 20 take following back bah, tukkan su princesses ne da princes na Middle East, dan scrolling tayi zuwa inda princes din suke. Mutun daya zuwa biyu zata iya cewa zata aura, daya shine prince na UAE Abu Dhabi , na biyu kuma prince na bahrain. Sukadai ne idan har suka bukaci aurenta daddy zai fasa da ridwan, dan idan har bai basu bah za’a samu problem tsakanin su, tunda neman aure a gurinsu kaman yaki yake, idan kace yes toh shikenan za’a samu zaman lafiya, no kuma rabuwan kai dan zasuga kaman an rainasu ne. Saidai ita yanzu batasan yanda zatayi masarautar abu dhabi ko bahrain suyi proposing bah. Ringing wayanta yafara yi faryal ne ke kiranta. Dauka tayi tareda yin sallama. “ babygurl fito gani nazo daukanki, yau tare zamuje school inji oldman dina, yabani amanar ki”. Katse wayar tayi jin abunda ya fada. Wato shi ridwan harya fara shiga mata harkoki kenan? Zata gyara mishi zama ne bayaga daddy na bin bayanshi bah. Tsaki tayi sannan ta mike, waje ta fita a parking lot ta ganshi. Ferarri yauma ya taho da ita amma ba irin model din jiya bah, Ferrari 12Cilindri (Coupe & Spider) ce ya zoda ita white color, zagayawa tayi ta shiga ta rife yaja motan suka fice. Wajen 45minute drive ne daga palace din zuwa university dinsu, gashi da mugun gudu yake tafiya kaman bayason ranshi. Itadai yazrin adduoi take ta jerowa dan bata kaunar gudu, gashi tasan kotace yadena ba bari zaiyi ba, tasan halinshi sarai shiyasa bata binshi school dukdan course dinsu daya. Gaban university of kuwait(KU) suka tsaya, akyi security check sannan aka bude mishi gate ya shiga. Hadaddiyar university ce number 1 a kasar, tanada girma sosai dakuma students wanda duk top students ne a secondary schools, dansai marks dinka da grades sunkai wani level kafin ka samu admission a cikinta, bawai kawai dan kanada A’s ba, no sai kanada 90% a kowanni subject sannan. Gaban faculty of engineering suka tsaya yayi parking motarshi a parking space na staffs dan students basa shiga da motocin su cikin gurin faculties, saidai shi dayake babu wanda ya isaya hanashi shiga. Bude mata kofa yayi sannan ya sauka, ta dauki bag dinta da phone dinta ta fito. Students dayawa a gaban faculty din ana tsaitsaye kaman ana jiran wani, yawanci duk yan mata ne. Yazrin bata kalli kowaba tasa kanta gaba ta fara tafiya zuwa gurin entrance din, faryal nabinta a baya. Tasan taruwan menene, dan inda sabo ta saba indai tazo tareda faryal toh yan mata nanan na jiranshi kaman masu bara, kowa so yake yakalleta, saidai shima biye musu yakeyi yayitayi ya maidasu mahaukata. A hankali take tafiyan tanajin idanuwan yan matan akanta, babu dai cikinsu wacce tayi mata kallon banza ko wani abu dan sunsan sauran, saidai suyita binta da kallo, wasu idonau cikeda hassada wasu kuma cikeda admiration, dan indai zatazo guri toh idon kowa dole yadawo kanta, ko waye kuwa. Matsa mata sukayi ta shiga, faryal na bayanta yana ma ya matan smiling suna kiran sunanshi. Ta daidai bakin kofan ya rungume wata yar gajeriyar yarinya ce kana ganinta kaga America girl, siririyace irin sosai tasha uban fake lashes da red lipstick, tanada kyau ba laifi, tana mishi magana dawani fake voice kamar yar tsana. Second floor ta nufa inda department of Aerophysics and engineering yake, course din datake studying kenan su biyu ne kwata kwata a course din, daga ita sai faryal, danba kowa ke iya karatun shi ba. Exam room 1 suka shiga wanda yana chan ciki ne a floor din, already lecturer dinsu dake musu robotics na jiransu a ciki, yau test zasuyi. A gaba yace faryal yazauna sannan yazrin a chan baya, dan yasama faryal ido dakyau. A computer sukayi test din 2hrs, babu wanda yayi ma wani magana a lokacin har suka gama. Finalizing sukayi sannan sukai submitting, sannan suka fita. Mota suka shiga yaja su suka fice daga school din. Halfway through suna dan hiran test din tace ya tsaya a Burger king tasai chicken nuggets. Kin tsayawa yayi a cewarshi babu tsafta cin abuncin waje, rokonshi tafarayi akan dan allah ya tsaya, saidai baimabi ta kanta ba, yanda batada lafiyan nan koyaya taci wani abu daba tabbatar da tsafta dakuma ingancin abubuwanda aka sa a ciki ba, sai a samu matsala. Ganin dagaske bazai tsaya bane yasa tadan ciza lips dinta, aranta tana ayyana wlh saita rama, zaizo tamai wani abu shima. Yana kallonta yasan metake tunani saidai murmushi kawai yayi. A dan gaba yay parking motan sannan ya ciro laptop dinshi daga bayan motan ya kunna. Kallonshi tayi tanaso taga meyake son yi tadan matsa dan taga menene. Hoton wani arab guy ne hadadde dogo handsome guy, prince na Abu Dhabi ne UAE, sannan uncle din azlan ne. Faryal ya juyo yakalleta sannan yafara fadin “ ga target dinki, wannan file dinshi ne, zan turo miki file din, duk wani abu akanshi yana ciki classified information ne wannan nakashe kudade kan a samomin wannan abun. Within this 3months dole ne musamu yayi proposing, saidai fah ba karamin mutun bane dakike ganinshi, duk wani tactic dazamubi zai iya ganewa, dan haka dole ayi planning abunnan, kije kiyi studying file din sannan ki fada mun abunda kike ganin za’ayi, nima kuma zan fada miki”. Dan ajiyan zuciya ta sauke sannan ta kalleshi, “ faryal kaga ni hankalina yafi kwanciya da prince na bahrain, shifa wannan ya girmeni sosai wajen shekaranshi 30 fah, sannan ba taba ganinshi ba bansan halinshi ba, sannan naji azlan na fadama daddy cewa bashida mutunci kwata kwata, gaskiya banaso”. Tsaki faryal yayi a kufule yake fadin “ ke yazrin ina ruwanki da wannan? Shekaranshi 30 toh oldman shekaranshi 49, prince na Bahrain umar shekaranshi 26 amma an hada aurenshi da princess na qatar Alina,

Chapter 3 of 11