Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
WASAN SARKAKIYA 1

WASAN SARKAKIYA 1

by Ayraah Riyad ,

3 Hours
03, Feb 2026
Unknown group
09157578540
Free
245.45 kb
TXT
300+
244+
Last download 2 days ago

You cannot download this book until you log in, but you can read it.

Read Now

OR

Description

Kuwait, Bayan Palace..

( masarautar kuwait).

 

Tsaye take gaban hadadden floor to ceiling canadian mirror tan shafa Embryolisse Lait-Crème scented cream a jikinta dake daure da white towel.

doguwa ce sosai dan ko cikin mata ma kadan ne suke tsawo daya da ita, gata siririya sosai dan kana iya ganin kasusuwanta daga cikin towel din, saidai sirantan ba mara fasali ba dan shape dinta na figure 8 yafito sosai, hips dinta a cike suke daidai jikinta waist dinta is so slim and define, chest dinta ne kawai inda ba a cike yake ba a jikinta wanda inka kalla kaman na 13 year olds dukda tayi 17 years, farace sosai irin hasken russians mai daukar ido, ga glowing da skin dinta keyi kaman wanda ke wanka a cikin madara.

Slim long oval face gareta wanda yasa features dinta popping out, pink lips dinta dasuke round da wannan v curve din saman lips baiwani fito sosaiba, gashi dan karami amd full at the same time, gasu sunyi dan pinkish blue a bushe alaman dehydration, sai dogon cute nose dinta dan siriri dayakara ma face dinta wani 3D dimension saitayi kaman barbie doll saidai idanuwanta ne dasuke manya but looking very sharp and fierce yake sa kaganta kaman mulan instead of barbie, dan a wani irin sharp angle suke gadaisu manya manya saidai yanda sukayi wani unique curve ne yasa tai looking so sophisticated and alluring, ga color dinsu mix of hazel and blue, dan daga nesa zakaga kaman hazel ne saika matso kusa zakaga blue yafi karfi a idon, which is so unusual dan likitoci ma basuda explanation akai.

Gashin kanta kuwa brown color ne dayake wani irin kyalli da daukan ido, yanada haske sosai saidai bazakace mishi blond ba bakuma zai kasance brown sosai ba., ta daureshi a wasu french braids guda biyu side by side tasake su sunkai har tsakiyan bayanta da alaman danshi akansu. Inka ganta bazakace arab bace kai tsaye dan tana kama da irin mix race dinnan masu wuyan gane daga ina suke ne. 

Dakin babba ne sosai kaman bana mutun dayaba, kusan komai all white sai a pop of grey nan da chan, the only thing a dakin shine all white king sized bed, sai mirror da study table dayake a corner na room din, sai wani katon book shelf daya mamaye side guda na dakin cike da littafai na boko da addini, kana gani kasan mai dakin ma’abocin koyan ilimi ne. 

Daga gefe kuma kofofi guda biyu ne daya na leading to walk-in closet, daya kuma toilet, and dakin babba ne sosai saidai babu komai na decoration banda grey carpet dayake a zagaye da bed dinta, duk yanda akayi dai mai dakin minimalist ce dan ba ko alaman dan decoration ko abubuwa masu colors.

S1- knocking kofan dakin da akayi batare da ta dago kanta ba cikin wata sihirtacciyar murya mai rikita brain dan zaƙi ta furta “ come in”. 

Saida akayi wajen 2 minutes kafin a turo kafar, wata yarinya ce da bazata wuce 18-19 years ba ta shigo dakin da sallama ciki ciki, kyakyawa ce sosai ajin farko kana ganinta kaga russian arabian, saidai arabian side dinta yafi karfi a face din nata, tanada tsawo ba laifi saidai batakai yazrin tsawo ba, face dinta oval da manyan brown eyes, zara zaran eye lashes dinta ma brown ne kaman tayi dying dinsu, hancinta bashida tsawo sosai bashida gajerta kuma saidai bashida fadi lips dinta kuma sanye da pink lipstick sannan tanada haske sosai.

Sanye take da alkyabba irin na matan sarakuna dan ado dayasha, irin alkyabbar da baka ganin kayan da akasa a ciki ne dan shi kanshi abun kallo ne bare kuma kasa wani abu, kanta batasa dankwali ba hulan alkyabbar ta janyo yazo tsakiyan kanta dayasa ake ganin brown wavy shoulder length hair dinta dayasha gyara dan kallo daya kayi mai zakasan da hakan.

Kallo yazrin bata ishe taba dankuwa tana shiga bata nuna tasan dakin wani ta shiga ba tasamu gefe ta tsaya tareda fito da wayanta tana dannawa.

Itama yazrin bata nuna tasan da wani a dakin ba cikin natsuwa ta cigaba da shafa cream dinta, tasan meya kawo amrah dan bai wuce ance tazo ta kirata zuwa breakfast bane amma tunda bata kai ta bude baki tayi mata magana ba yasa ta koma gefe ta tsaya.

Itama dayake ba’a nuna mata sarautar sai bata nuna tasan da ran wani a cikin dakin ba ta cigana da shiryawanta, aranta kana jinjina irin shigan da amran tayi da sassafen nan, dukda gidan sarauta suke kuma yaran sarki dole ne su rinka sa kayan gani da fada amma kayan da amra kesawa ko mamah matan sarki bata sakasu ta fita waje bare kuma zaman gida.

Walk in closet dinta ta nufa wanda yake makeke dan zaiyi girman bedroom dinta sau biyu da wani abu, gashi cike makil da kaya dukkanin su designer ne kuma custom made dan sukadai akema kayan baka isa kasa kayan dasuke sawa ba.

Black abaya ta dauko mai embroidery design dabawani cika mishi designs din akayi ba sannan ta dauki turkish scarf white and black tasaka tareda saka home original fox fur sleepers sannan ta fito ta warware gashin kanta tareda sa brush ta taje shi yazama straight, har kasan waist dinta, pure castor hair oil ta shafa a gashin daya kara mishi kyau da kyalli sannan ta dauki scrunchies ta daure shi a tsakiyan kanta tareda daura scarf din. Sannan ta dauki wata black and red alkyabba wanda har kasa take ja, an mata designs irin na ancient rome dynasty bata cika kwalliya ba saidai intazo guri dole zaka kula da ita.

Sosai kyanta yakara fitowa dukda bawani gayu tayi ba amma kuma idanda zata shiga guri dik irin gayu da kwalliya da mutun zaiyi dole ido ya dawo kanta, dan abun ba a kayan bane.

Phone dinta ta dauka latest edition iphone ta nufi kofa bayan ta feshe jikinta da custom made turaren ta mai kanshi gaske.

Bata bitakan amrah ba tayi ficewanta ta nufi elevator zuwa 4th floor dan su a 5th floor suke, kana ganin yanda take tafiya da daukan kanta zakasa sarauta da mulki sunbi jikinta, dan ko a gidan babu wanda kasaita tabi jikinta kamar yazrin, bawai kuma yinshi takeyi ba, kawai a jininta yake ne. amrah bata shiga elevator dinba nagefen shi ta shiga wanda shima na yan gidan ne sai kuma guda daya na ma’ikata.

S2-  direct dining room dinsu ta nufa wanda already sultan sultan abduljabar bin malik ke zaune akan high chair, kyakyawan full arab dattijo ne face dinshi cikeda haiba, yaa sanye da jallabiya da bakar alkyabba irin dai wanda sarakunan arab nations ke sawa, kanshi sanye da Kaffiye da agal, suma kanshi a rufe sai saje daya tara baiwi tsawo sosai ba baikuma yi kadan ba. 

Gefenshi kuma ta hannun dama wata dattijuwa ce itama zaune wanda kana kallonta kamanninta da amrah kaman an tsaga kara, saidai amrah tafita kyau badan ita nasmah batada kyau ba saidai amrah kyanta tahada ne dana nasmah dakuma na sultan abduljabar, dan itace wanda mutane ke kira the most beautiful princess in the world, babu kuma musu akan hakan har saida girman yazrin da mutane suka fara ganinta, domin ita yazrin ba kowa ne yasan ita yar sarki abduljabar bace, domin ko school zata da niqab take zuwa sannan bata shiga cikin abubuwan masatauta bare mutane su ganta.

Shiga dining din tayi tareda nufan inda sultan abduljabar yake tana sakin murmushi daya karama face dinta kyau da annuri, kaman tauraruwa a ciki duwatsu. Hugging dinshi tayi tareda gaisheshi “good morning daddy, nayi missing dinka tun jiya da safe ban kara ganinka ba”. 

Hugging dinta back shima yayi yana murmushi irin nasu na manya sannan yace “ my baby ai kece bakya nemana, jiya a fada na wuni shiyasa ban dawoba, da daddare kuma kinyi baci baki jirani ba kuma banaso a tashe ki amma gashi yanzu kin ganni”. Yafada yana shafa kanta.

Turo mai baki tayi tana fadin “ nidai daddy kaine bakason ganina, kasan ka hanani zuwa fada tun ina karama ni yanzu banmasan hanyar taba, da dare kuma naje school na gaji shiyasa nayi bacci”. 

Bai kulata ba yayi mata nuni da kujeran ta dataje ta zauna, ba musu ta zauna tannan ta kalli nasmah tana dan sunkuyar dakai kaman mara gaskiya “ mommy good morning, antashi lafiya”. 

Murmushi mommy tayi mata sannan tace mata lafiya. Lokacin kuma sallaman amrah ta katse su, a nutse ta shigo sannan ta samu kujeran dake directly next to mamah ta zauna ita kuma yazrin tana gefen amrah. 

Ma aikatan masarauta ne suka fara shigowa matane su uku, a jere suka shigo kowanne su na sanye da abaya farare kal kal, shine uniform na masu girki da gyara domin hakan na nuna tsaftan su, dan koda dan datti ne akan kayan hakan na nuni dacewa tsafter su bata kai yanda akeso ba.

Abinci suka fara shigowa dashi wanda duk girman table din da zai dauki atleast warmers 30 saida suka cikashi cikin kakanin lokaci, kuma komi a layi suka sakashi babu wanda zaka gani a karkace.

Suna gamawa kuma suka fice bagareda sun tsaya serving dinsu ba. Turn turn ake dauka yau idan amrah tayi serving gobe yazreen zatayi, yau kuma turn din amrah ne so mikewa tayi sannan ta zubama daddy da mamah abunda suka bukata kanata zubawa kanta, saidai bata ko kalli inda yazrin take ba bare tasaka mata.

Itama bata damu ba dan dama ba zubamata takeyi ba, itama kuma bata Zuba matan, mikewa tayi sannan ta zuba cinnamon tea and da toasted garlic bread. Dama ita su takechi kullun babu chanji. Shiru dakin ya dauka banda kanshin abincika dake tashi dazai sanar maka da cewa akwai mutane a ciki dan babu koda karan utensils, dukda kuwa dasu sukeci saidai tsabar sanin dining etiquette bakajin maran chokula ko tauna. 

Kusan 25minutes sukayi sannan suka karasa cin abincin, sultan ne yafara mikewa sannan mamah ta tashi, sukai musu sallama suka fice.

Dago da kata daga daddanna wayan datakeyi amrah tayi tareda bin yazrin da wani irin kallon mai wuyar fassarawa.

Jin ana kallonta yasa yazrin dago dakai calmly tasama amrah hadaddun idanunta masu mugun kwarjini da kyau. Ajiyan zuciya amrah ta sauke “ you have grown sister, exactly like the princess you should be, making our parents proud”. Ta fada cike da izza tareda karemata kallo sama da kasa.

Dariya yazrin tayi aranta tana tunanin mekuma yakawo amrah ta kulata harda cemata ta girma, dan ita tun bayan abunda yafaru tsakaninsu bata tuna ranar da amrah tayi mata magana mai tsawo hakaba batare da wanine ya aikota gurin taba, saidai bata nuna komai a face dinta ba dukda kuwa zafi da zuciyanta yafarayi, saidai a face dinta bata nuna komaiba tayi mata dan smile na gefen baki tareda mayar mata da ansa “ dama ance girman dan adan ba wuya, saidai zan iya cewa kema hakance dan naga kaman kin manta shekara daya ne tsakanin mu”. Ta karasa tana siping tea dinta.

Dariya mai sauti amrah tayi saidai kana gani kasan baikai zuciya ba, yafi kama da dariyar rainin wayau. Bata ba yazrin ansa ba ta mike cikeda izza ta fita daga room din. 

Binta da kallo yazrin tayi tana son ta gano meyasa amrah zatayi mata magana yau, saidai ganin ba ansa zata samu ba yasa kawai ta sauke ajiyar zuciya ta mike tareda nufan waje.

First floor ta sauka sannan ta fice daga hadadden mansion din. Straight parking lot ta nufa wanda drivern ta na tsaye kusada wata black latest edition bentley, dattijo ne shima arab yana hangota ta bude mata kofan baya ta shiga. 

Shiga gaba yayi shima yaja motan suka fice a moderate speed. Gaisawa sukayi banda haka babu wanda ya karama wani magana. 

Masarautar kwata kwata bata kama da gidan masarauta saidai ace kaman gidan shigaban kasa dan instead kaga gininnikan da dakuma ancient architecture saidai kaga modern architecture da gininnika, ko ina an gyara shi yakoma kaman ba’a dade da ginata ba, sabanin masarautu dazakaga gini masu shekaru dasuka dade. 

Guri daya ne ba’ayi modernizing dinshi ba, shine ginin dayafi kowanne shekaru da tarihi kasar larabawa gabadaya bama a kasar kuwait kawaiba, yanadaga gabas na masarautan wanda yake rabe gida uku. Gini ne irin na masarautu nada saidai babu alaman tsufa ko gazawa, buildings ne guda uku dasuke dan nesa da juna, na tsakiyan bashida tsawo sosai bazai wuce 3-4story building ba, gefe da gefen kuma sunfishi tsawo zasukai 6story.

Zagaye suke da fence dogo da akayishi da zallan karfe, ba norma karfe da kake gani yauda kullun ba, no irin karfen dayasha wuta da bugu to the point that baka isa ka yankashi ko ka malkwayashi ba dukda kuwa ba fadi ya cika ba. 

Gate ne ta tsakiyan karfen motan ta nufa, wasu security na masarautar sanye da white and brown kaya sunkai wajen 20 a jere a bakin gate din kadai, ga wasu kuma dazasukai 100 a cikin building din suna kaiwa da dawowa kowannen su da guns tareda wasu weapons din a hannu.

Sauka drivern yayi sannan ya bude wa yazrin kofa ta sauko a hankali batareda ta wani bata lokaci ba

Daya daga cikin security dinne yataho inda suke tareda sunnar da kanshi kadan alaman gaisuwa ga yazrin, sannan drivern ya mika mishi key na motan yana matsawa yazrin tayi gaba yana binta a baya. Gate din aka bude musu suka shiga da kafa dan babu mai shiga cikin harabar gurin da mota, saidai ka aje motanka a chan waje, yaran sarki da sarki kashi sai wasu manya masu fada aji a masarautar kadai ake bari suyo gurin gate sannan su bada key na mota akwai special parking space ba nisa sosai daga gurin sai akai musu, dan ba kowa ake bari yana shiga gurinba.

Gurine dayafi kowani giri tarihi da muhimmanci a kasar kuwait bama masarautar ba, dan kuwa idan har sirrikan dakuma abubuwa na tarihi dake ciki suka fito toh lallai kasar kuwait zata fadi, dan kuwamaƙiyansu zasuyi anfani dashi wajen kawo karshenta. 

Building dake tsakiya library and artifacts ne a ciki, duk wani littafi da bayanan sirri na kuwait dama wasu kasashen ma zaka sameshi anan. 

Na gefen hagu kuma inda ake duk wata meeting da tattaunawa na abundaya shafi masarautar dakuma kasar gaba daya. Na dama kuma a rufe yake babu wanda yasan meke ciki sai daidaikun mutane, wanda yazrin bata cikinsu.

Na tsakiyan dayafi faɗi dakuma tsaruwa ta nufa, tana tafiya ahankali cikeda class tafiya mai daukan hankali dukda baka ganin shatin jikinta, kanta a ɗage cikeda confidence. Sundan taka sosai dan daga gate zuwa gurin akwai dan nisa.

Babban kofa ne irinta da wanda saika rantse gate ne dan yamafi wanj gate din tsawo, kofofi ne biyu a hade, security biyu ne gaban kofan da sukayi hazarin bude mata kofa tareda sunnar dakansu alamar gaisuwa, dan karamin polite smile tayi musu tareda shiga drivern ta nabiye da ita. 

Hallway ne dogo sosai da kofofi manya manya a gefe da gefenshi, a dama kawai kofofin sunkai 50 a jere sannan akwai dan tazara a tsakanin kowanne wanda hakan zai gasgata maka girman gurin. Babu paint a jikin bangon iya cement ne irin na da wanda ba ja ba bakuma ash ba, saiya bada wani greanish white color kaman a horror movie, gashi girin koda magana kayi saiya ansa, hakan na tsorata mutane dake zuwa gurin sosai indai baka saba ba, gashi babu haske sosai saina candles manya manya wasu kaman girman mutun suna ci.

Tafiya takeyi dai dai kaman bazata taka ba, irin tafiyan iyayi dakuma mulki da yariga ya zaman mata a jiki, drivern na biye da ita har suka kai wajen kofan tsakiya, tafita daban daga sauran kofofin dan tafi girma tareda faɗi, sannan tazaranta da kofan dake gefe da gefenta akwai tsawo sosai dan zakai tunanin babu wata bofa bayan ita idan kazo inda yake saboda tazaran dake tsakaninsu.

Tsayawa tayi daidai tsakiyan kofan, scanning dinta kofar tayi tundaga sama har kasa sannan a hankali ta bude, shiga tayi drivern bai bita ba ya samu guri a waje ya tsaya, alaman bodyguard dinta ne ba driver kawai ba.

Library ne irin ancient one dinnan da girman shi da fadin shi bazai misaltu ba, gakuma miskilin kyau dayake dashi sai wanda yagani kawai, ko ina littafai ne da scrolls da makamantansu.

Wani dan guri ne a gefe da alama reception ne dan table da kuma kujera tareda wani zaune akai zai tabbatar maka da hakan. Gurinshi ta nufa wani arab guy ne bazai wuce 40-50 years ba, idanunshi sanye da medical glasses yana kallon waya kaman yanda mutanen da keyi wayar na hannu daya suna dannata da dayen hannun.

Tana karasawa inda yake tadan saki murmushi tareda tapping table din, dagowa yayi suka hada ido ta kara fadada murmushin face dinta dayayi mata matukar kyau ya karama face dinta annuri wanda shima murmushin ya sakin mata tareda ajiye wayanshi a gefe.

Cikin murya irin na manyan mutane da suka ci sukabar duniya ya furta mata “nur yau dawuri haka? Ai nazata sai anjima zakizo, ince lafiya dai ko?”. Ya fada da damuwa a face dinshi.

Kujeran dake na guest ta zauna akai tana kallonshi, saida tadanja time wanda ya saba da hakan kafin ta bashi ansa cikin nutsuwa “ bakomai fah, kawai babu abunda zanyi ne yau babu school babu assignments, sannan mamah tanada zama da matan fada so kawai na taho yanzu”. 

Gyada mata kai yayi alaman gamauwa da abunda tace, sannan ya daura da fadin, yau munada guests dazasuzo library zaki zauna dasu duk abunda suke bukata saikiyi musu.

Mamaki abun ya bata saidai tadanji dadi sosai, dan sai takai wajen 1-3 months babu kowa dayake zuwa libraryn, sannan bata aikin komai dama kawai bata matsayin ‘keeper of the library’. Saidai babu abinda takeyi sai tazo ta zauna ta karanta books ta tashi ta tafi gida, domin sultan abduljabbar ya hana ana bata access na bayanan sirri na masarautar, dan yace bata isa ta rike wannan matsayin ba, wanda hakan sosai yake ci mata rai tunda anbar amrah ita.

Da ok ta amsa mishi batareda ta tambayeshi waye zasuzo ba, dan tasan bazai gaya mata ba, mutun ne shi mara yawan magana, so idan ta cika tambayanshi banza zaiyi da ita, 

Mikewa tayi sannan ta wuce lounge inda take zama tayi karatunta, chairs ne very comfy ones masu laushi tahau kai tareda daukan book dake kai wanda dama ita tabar abunta akai, an rubuta ‘the diary of Queen samran salim’. Littafi ne akan matar sarkin kuwait ta farko wanda za’a iya cewa su suka gina kuwait suka kawota inda take yanzu. 

Cikakkiyar balarabiya ce, wanda a lokacin ake harsashen cewa iyayenta sunyima sarkin asiri ya aureta, dan yanada wata matan dasuka yi soyyaya sosai kafin lokacin daya kwaci kasar, amma ko shekara goma basuyi ba ya saki matar tashi ya auro ta, wanda take yar mai bashi shawara ne a masarautar, tanada shekara 13 shikuma yanada shekara 50 ya aureta, wanda tun daganan bai kara samun lafiya ba, daga karshe bayan shekara biyar ya mutu batare da ya haifi yaya daga gareta ba, saidai yaronshi guda daya dayake dashi da tsohuwar matarshi, shi ya amsa sarautar kasar ya kuma auri queen samran salim, hakan ya jawo cece kuce a kasar domin sabanin hakan a addinin musulunci, saidai shima ko kadan bai kara lafiya ba bayan aurenta, shekaranshi bakwai ya mutu.

Sosai aka samu rikici bayan mutuwarshi domin queen samrah salim ita ta amsa mulkin kasar, mutane sunki andan mulkin mace domin a cewarsu gazawa ne kuma addinin musulunci bai hallarta hakan ba, saidai ga wani ikon allah kuma ko shekara biyu ba ayi da ansan mulkin nata ba mutane suka chanza akalarsu suka sota, dan koda akaso yimata juyin mulki mutanen kasar su suka tsaya mata ta zauna. Shekara ashirin tayi tana mulkan kasar kuwait sannan tayi murabus tabawa danta data haifa tareda wani cousin dinta data aura, sannan ta kashe kanta bayan yan shekaru.

Littafin diary ne so zakayi zaton zaka ga rubutunta datayi na rayuwarta, saidai akasin hakan poems ne kawai ta rubuta a ciki, wasu zaka gane me suke nufi, wasu kuma shirme ne kawai, wanda hakan ya haifar da maganar cewa ta haulace bayan ta ansa mulkin kasar, shiyasa bayan ta sauka ta kashe kanta.

A page din karshe yazrin take, wanda rubutu ne akayi saidai bana larabci bane bakuma na turanci ba, dan bata gane yaren ba, mikewa tayi ta nufi inda librarian din yake tayi mishi sallama, dagowa yayi ya kalleta tayi mishi alaman ya kalla page din. Ansa yayi yadan duba sannan ya furta mata kalma daya “ symbolism”.

Guada mishi kai tayi sannan ta koma inda take ta zauna, sannan ta ajiye book din dan tasan ba ita karantawa zatayi ba, symbolism language ne wanda mutun yake kirkiran abunsa ta hanyar zana objects sannan ya basu ma’ana da shi kadai zai iya gane abunsa. Idan har kanason ka gane me aka rubuta saidai ka kaima cryptographers wanda aikinsu ne suyi understanding sannan kuma su gane me aka rubuta, saidai ita yanzu batada wannan knowledge da kuma time din. Dan saturday and sundays ne kawai take zuwa library, monday to Thursday school take zuwa sannan friday kuma sauka da karatu akeyi a masarautar dan haka bata zuwa ko ina.

Sosai takeso tasan me aka rubuta a page din, domin tanason history na samrah salim, matace mai mugun wayau da abubuwan al ajabi, dukda kuwa shekaru wajen dari uku da saukarta a mulki amma babu wanda zaice bai santa ba kokuma tarihinta, saidai iya abunda mutun daya yasani shi zakaji wani ya fada, babu wanda yasan meya faru sarakunan dasukayi zamani daya da ita suke rashin lafiya datayi silar ajalinsu.

Ganin tunanin bazai bulle mata bane yasa ta mike tareda maida book din inda yake, sannan ta dauko wani da aka rubuta “ the process of life”. 

S3- Bata karasa inda take zama ba aka bude kofan, wani dattijo ne sanye da white jallabiya da black alkyabba irinta sarauta, bazai wuce shekara 45-48 hakaba. Mutun hudu ne manya manyan gabza gabzan maza majiya karfi a bayanshi, suna sanye da suit bakake idanunsu da shades black, fuskokinsu babu annuri kwata kwata.

Dago mata hannu mutumin yayi, sannan ya nufo inda take, itama tafiya tafarayi a nutse tana nufanshi, dayake libraryn akwai girma sosai so saida suka dan taka sosai kafin su iso inda junansu suke, sannan tundaga shigowanshi idanuwanshi ke kanta baikoda kyafta ido ba.

Dab daiya ya tsaya da saida tadan ja baya tsabar closeness dinsu, tana jin kallonshi akanta wanda yake mata tundaga sama har kasa saidai bata nuna tasan yanayi ba dukda babu dadi datake ji a jikinta. Wani classy murmushi ta sakin mishi sannan tadan yi kasa da kanta alaman respect.

Ido cikin ido yake kallonta dan kusan tsawonsu daya ma da yazrin, still bai bude baki yayi mata magana ba dukda sunkai almost two minutes a tsaye. Yazrin ma kallonshi tayi shima cikin ido sannan cikin polite sexy voice dinta ta gaishe shi gaisuwa irinta masarauta da akeyima manyan mutane, sannan ta kalli bodyguards dake dan bayanshi ta furta “ sheikh ridwan, bodyguards aren’t allowed in here”. 

Kaman bai jita ba dan baiyi alaman yamasan tana magana ba, saima mayar da kallonshi zuwa cute lips dinta dayayi sanda take magana. Abun kwata kwata bai dameta ba dan bayau ya fara mata irin hakaba, shiyasa sam batason hada hanya dashi, dan idanda ba nan library din yazo ba toh bazata ma kulashi ba indai bashi yayi mata magana first ba, saidai duk abunda za’ayi sai ayi, amma dayake library yazo kuma itace in charge of libraryn, dolene tayi engaging dinshi, dan yana daya daga cikin four National Assembly members na kuwait, wanda daga sultan, sai amir wato babban dan sultan, sai kuma su a matsayi da power, sannan yaya mata na sultan.

Kaman bazaiyi magana ba saikuma yayi musu alaman su tafi, ba musu suka juya sukayi waje. Cikin voice irin na dattawa dasuka ci duniya kana ganin kodaga idonshi kasan baya ji, ya kalleta yana fadin “ babyn sultan, kin girma, in bansanki ba dasai nace gudu na kikeyi a masarautar nan, ko nayi miki laifi ne?”. Ya fada still idonshi nakan ta.

Wani smile din tadanyi dukda baikai zuciba, tasani sarai yasan gudunshi takeyi, toh inma bata gujeshi ba ai ya tambayi kanshi, still bata bar face dinta ya nuna komaiba ta tambayeshi me yakeso, sai ya cemata kawai yazone yaga libraryn sannan yadan zazzagaya ko zaiga wani abunda zai dau hankalinshi.

Da ok ta amsa mishi aranta tana raya dama tasan babu wani abunda ya kawoshi, kawai bashida inda zai ganta ne sai anan din, takuma sani sonta yakeyi, dan kowa a masarautar yasan da haka, hatta sultan dakuma mamah sunsani, sannan shi sultan ma bai nuna rashin son abun ba, hasali ma nunawa yayi ai babu komai, mamah ce ma take basar da maganan alaman bata supporting, dan haka yazrin dole takw biye mishi dukda bata nuna mishi tasan meyakeyi, maidashi takeyi kaman mahaukaci yayta borin kunyan isa da sarautar nashi, dan ita baka ma isa wai ta nuna maka tasan me kakeyi ba, duk rainin wayan dazakayi mata tasan tayanda zata bullo maka cikin ruwan sanyi.

Shiyasa koda suka fara zagaya livraryn yanata dan janta da hira cikin basaja saita datseshi itama, kokuma idan yay magana akan rashin ganinta ran fridays a gurin sauka da akeyi saitace mishi tana tareda matanshi. Hakan sosai yake bata mishi rai dan yanada hankali dakuma wayau har yakai matsayin da yake a yanzu, dan haka yagane sarai abunda yazrin kemai.

Sunkai wajen two hours still basuyi rabin libraryn ba, yazrin tafarajin jikinta na saki, hannayenta sun fara kyarma idanunta na sauya kala zuwa jaja jaja, dama ita sam jikinta baya daukan wahala, abu kadan zatayi zataji jikinta ya saki, gashi bashida alaman gamawa. 

Sosai takeso ta zauna dan kafafunta kaman tana taka wuta takejinshu, ga nunfashinta dake zuwa da karfi da karfi dakyar take janshi, saidai bata nuna ba ta cigaba da binshi tana addua allah yasa ya gaji yace su koma, tana cikin hakan kuma taga ya tsaya, wanda bata luraba ta cigaba da tafiya saida ya kira sunanta wajen sau uku, da sauri ta juyo da kanta zuwa inda ya tsaya dan har tadanyi nisa.

Gani tayi ya kure ta da ido yana kallonta alaman yanaso yaga meke damunta, saidai tayi saurin hada nutsuwanta tareda juyawa ta koma inda yake “ yazrin ya inata miki magana baki ansani ba sannan kika cigaba da tafiyarki?”. Ya fada ranshi babu dadi.

Dan tabe baki tayi dan yanda take jinta bama zata iya biye mishi ba, kawai yazo ya gajiyar da ita sannan zaiyi kamar tamishi laifi dan bata ansa shi ba akan dai yar magana daya “ oh sorry fah, tunani nashiga yi shiyasa”. Bai ansa ta ba sai irin kallon mamaki dayake mata irin lallai yarinyar nan ce zata mishi magana ahaka harda tabe baki, kana kawai ya juya ta hanyar dasuka biyo ya koma.

Binshi da ido tayi harsaida ya bace daga ganinta sannan ta sauke wani nannauyar ajiyar zuciya, zubewa tayi anan kasan epoxy floor irin na da dinnan dayake a tsaftace tsaf dan kullun sai an share ankumayi moping round biyu.

nunfashinta tahau ja tanason daidaita shi, sannan ta mikarda kafafunta datakejinsu kaman dutse a jikinta, duk jikinta yayi tsami kamar wacce akayi ma duka.

Takai wajen 1hr a zaune kafin tadanji dama dama, sannan a hankali ta mike ta juya ta koma lounge din, tanayi tana tsayawa dan ta huta. Koda ta koma lounge din bajewa tayi akan comfy chair din tana salati, tasan yanzu lokacin sallah yayi amma batada wani energy yin sallah saita huta.

Kara gyara kwanciyan tayi jin baimata dadi ba, ga tunanin ko mai zaine yacema sultan akanta yanzu, dan daduk alamu ranshi ya baci, mutun ne maison a girmama shi dan haka dolene irin yanda tayi mai maganan ya bata mishi rai, allah dai yasa karya ballo mata ruwa.

Jin kaman tunani zai fasa mata brain ne yasa ta mike tareda daukan phone dinta ta nufi waje, tareda dagawa librarian din hannu alaman ta tafi. Bodyguard dinta dake tsaye yana jiranta tayi gaba yana binta a baya, kaman tasa kuka jin yanda kafanta ya cigaba da zafi.

The drive back zuwa mansion din was so peaceful kamar kar yakare, tana sa kafanta cikin front door dinkuma wani depressing feeling yazo mata, batasan meyasa ba kwata kwata bata samun nutsuwa a cikin gidan, shiyasa kullun indai bata library toh tana school, sosai take tana avoiding zaman gidan.

Danne feeling din tayi ta wuce dining, babu kowa a ciki dan haka cookies kawai ta deba a dessert plate guda uku sannan ta juya ta tafi dakinta.

Glass of water dakuma wani luxury dispenser da inba ace make dispenser bane bazaka zata shineba ta debi ruwa sannan ta koma bed dinta ta zauna tana sha tareda cin cookies din a hankali. Takai wajen ten minutes sannan ta gama ta mike. Straight toilet ta nufa ta cire kayan jikinta ta kaisu laundry room daka attached to toilet, sannan ta kunna ruwa a wani giant two persons jacuzzi ta wurga rose scent bath bomb a ciki sannan ta sa shower cap akaanta dan batada energy wanke shi ta shiga.

Jikinta dayayi tsami ya fara saki sakamakon zafin ruwan dake shiganta har bones dinta takejinshi. Wayarta data saka a phone holder dake daidai kusada jacuzzin ta dauka tareda kunna wakan central cee ‘Band for Band’ tana miming  tana jujjuya kanta face dinta cike da annuri. Voice dinta is so soft and silky kwata kwata bai dace da rap music ba, wakan daban voice din nata daban. 

Yana gama playing kuma ya shiga kendrick lamar “ not like us”. Yana playing tana miming, jikinta yayi dadi kamar ba itace dazuba, tana cikinji kuma wakan ta tsaya ringing din kira ya shigo, tsaki tayi dan yanda tayi relaxing dinnan kawai za’a kama ana wani kiranta, kaman bazata dauka ba saikuma ta sa hannu ta dauki wayan, lokacin harya gama ringing.

Bude wayan taso tayi saidai bata samu ta bude ba saboda santsi na ruwa dake hannun nata, hakan yakara bata mata rai dan bataso ta tashi yanzu, saidai tunanin kowani important abu ne tunda banda yan gidansu mutun dayace wato bestfriend dinta ke kiranta, dan haka daurewa tayi ta mike ta dauko towel ta nede jikinta. Sannan ta dauki wayan ta fito. Closet ta nufa ta dauko body moisturizer dinta ta shafa adan sauri sauri sannan ta duba time, ganin kusan 7pm na yamma ya kusa yasa ta daukan kayan baccinta kawai dan lokacin dinner yakusa kuma tana ci bacci zatayi.

Riga ce silk button up da wando dabaikai gwaiwa ba, yanada fadi and its so comfy dan kusan duk pyjamas dinta irinshi ne. White alkyabba rufaffiya ta dauka wanda takeda all white beadwork da fine stones an jera ta kasan dakuma wuyan sai yan blueish green suma andan watsa su saiyayi kaman ocean dayasa eye color dinta yayi popping sosai. Sannan ta cire shower cap din ta saki gashinta ya zubo yayi waves sai shining yakeyi, alkyabbar batada hula so dan scarf mara fadi tayi folding ta daura a kanta ta saman gashin ya zuba ta baya.

Fita tayi sannan ta dauki wayan danta duba miss call din, sunan mamah tagani a screen din tana kara kira, da sauri ta dauka tana fadin “hello mamah sorry wanka na shiga”. Ta fadi hakan batareta jira mamah tayin magana ba.

Da ok mamah ta ansa mata sannan tace “ yazrin come down for dinner, karkisa mu jiraki kaman dazu”. Tana fadin hakana kuma ta katse wayar. Dan jim tayi jin kaman taji hayaniya a inda mamah take, ko su waye oho. Harta nufa bed dinta dan tadan huta kafin ta sauka saikuma wani tunani ya fado mata, kodai azlan ne ya dawo?. Wani tsalle tayi tareda ihu so excited ta juya ta gudu tana sakin wayan a kasa ta fice daga dakin. Direct dining tayi nan kuwa tana zuwa ta tabbatar da zatonta.

Tsaye ta ganshi…

Comments

Please log in to leave a comment

Login here