Kailubul Hasanru da Nuraiha sun sami shekara goma sha biyar da yin aure amma basu sami haihuwa ba, babu irin fokarin da ba su yi ba wajen neman haihuwar amma abu ya faskara, dole suka hakura suka rungumi kaddara.
Gaba daya mutanen birnin Daluza suna bautar wani gunki ne mai suna Sharks. Masana tarihi a birnin Daluza sun tabbatar da cewa tun da aka kafa birnin sama da shekaru dari hudu da suka gabata ake bautar gunkin Sharks, kuma an yi imani cewa shi ne yake kare birnin daga dukkan masifu domin ba a tafa yin fari ba, ba a tafa kawo musu farmaki ba ko hari na 'yan sumame. Haka kuma suna da kwanciyar hankali da koshin lafiya, abu ne mawuyacima mutum ya ga nakasasshe a birnin koda zai yini yana yawa. Abinci kuwa ya wadata a ko ina. A takaice dai babu talauci ko fatara ko kadan a birnin. Kai ko bako ne ya shigo cikin birnin sai yaji kamar ba zai iya tafita ba sabo da ni'imar garin gami da hala iyar jama'arsa ta karrama baki. Bugu da kari mazansu ya yi musu kyu na fuska da na surar jiki. Mafi yawan fataken dake zuwa birnin basa yarda su tafi ba tare da sun auri 'yar birnin ba.
---
**Page 4**
Ana nan a cikin wannan jin dadi da ni'ima sai kuwa aka wayi gari wani azzalumin Sarki da akc kira Barufa wanda ke mulki a wani birnni can yammacin Daluza mai suna Hilusa ya kamu da hassada da kuma kyashin arzikin mutancn Daluza.
Sarki Barufa ya kasance gwarzon mayaki kuma gawurtaccen matsafi wanda ya gagari dukkain sarakunan da ke makwabtaka da shi, domin haka kawai sai ya aikawa Sarki ya bashi dukiya mai yawa, idan sarki ya ki ba da dukiyar sai ya kaddamar da yaki a kansa ya kashe shi ya dora wakilinsa akan karagarsa, wato birnin ya zama karkashin daularsa.
Lokacin da Sarki Barufa ya sami labarin irin ni'imar dake cikin birnin Daluza da kuma karfin arzikin su sai ya sa aka rubuta wasika aka baiwa Sarki Kailubul Hasaru. Sa'adda wasika ta riskeshi yana zaune ne a fadarsa. Nan take ya umarci maga takardarsa da ya karanta wasika a fili kowa yaji abin da ta kunsa. A wannan lokaci kuwa fadar ta cika makil da jama'a har da fadawansa gaba daya.
Maga-takarda ya warware wasika ya
---
**Page 6**
9
da wasikar ta kunsa. Da sarki Kailubul Hasaru da dukkanin jama'ar da ke cikin fadar kuwa sai duk suka dimauce hankalinsu ya dugunzuma ainun, suka rasa abin da ke musu dadi a duniya. Nan fa fadar tayi tsit! Kamar mutuwa ta gifta. Sai da dakika kusan dari uku ta shude kowa ya fada tunani mai zurfi. Daga can sai Sarki Kailubul Hasaru ya kawo gauron numfashi ya ajiye, sannan ya dubi wakilin Gunki Sharkas wani boka da ake kira Mauzaru ya ce da shi. "Ya kai Mauzaru yanzu me ne abin yi? Ka sani cewa Sarki Barzufa ya fi karfinmu ta ko ina, domin ya fimu yawan mayaka da sanin yaki tunda mu bamu taba yin yaki ba ma, ya fimu karfin sihiri, tabbas idan ba mu bi umarninsa ba sai ya aikata abin da ya yi alkawari a garemu. Idan muka bi umarninsa kuma tamkar mun talauta kanmu ne, mun lalata arzikin kasarmui, kuma mun zama bayinsa."
Sa'adda boka Mauzaru yaji wannan tambaya daga bakin Sarki Kailubul Hasaru sai ya yi ajiyar zuciya ya ce, "Ya shugabana kayi sani cewa a halin yanzu bani da ikon yin bayanin komai face na tuntu6i Ubangiji Sharkas. Duk abin da ya ce
Shuraihu Usman
Mukhtar Kwalisa
Abdulaziz Sani Madakin Gini
Aliyu Abubakar Sharfadi
Mansur Usman Sufi
Abdulaziz Sani Madakin Gini
Abdulaziz Sani Madakin Gini
Shehu Usman
Abdulaziz Sani Madakin Gini
Abdulaziz Sani Madakin Gini
Khadija Muhammad Shitu
Abdulaziz Sani Madakin Gini
by Jamila Umar Tanko,Jamila Umar
by Jeedderh Lawals
by Rahma Hassan Zaria
by Nazir Adam Salih
by Abdulaziz Sani Madakin Gini
by Zahra Muhammad Mahmud Surbajo
by Unknown
by Mamuh Gee
by Mujahida Matar Malam
by Nana Khadijatu