lOKACIN DA ABIDATUL AZMAL ta zama tsuntsuwa ta tashi sama ta luluka a cikin gajimare sai aka kama su Zuhura aka tafi da su izuwa cikin kurkuku.
Dama an daure hannayensu da sarkoki. Nan take aka zubasu a cikin daki guda aka kullesu.
Shi du wannan kurkuku babu taga a cikinsa ko guda daya sai dai kofarsa an yi ta ne da wadansu murtukamurtukan sandunan karfe wadanda babu wani karfen da zai
iya saresu.
Bayan an kulle Zuhura, Kurbas, Hasilatul Kurbas,
Inmal da Lahura a cikin wannan daki sai gaba dayan su
hankalinsu ya dugunzuma ainun suka rasa abinda ke musu
dadi. Kurbas ne kadai fuskarsa ke da walwala. Babban
abinda ya fi daga musu hankali shi ne, ba su ga yadda za su
iya fita ba daga cikin wannan kurkuku sannan ba su san
inda aka boye jikokin Kurbas ba a cikin wannan fada ta
Abidatul Azmal. Bugu da karfi Dakarun da ke gadin
wannan fada yawansu ya wuce kima, kuma sun kasance
wasu irin manya-manyan dodanni ba mutane ba masu
tsananin kwarjini da muni.
Bayan dukkaninsu sun yi shiru izuwa tsawon lokaci
sai Zuhura ta dubi Kurbas cikin mamaki ta ce, "Ya kai
Abul Hasilat mene ne dalilin da ya sa na ga fuskarka da
walwala tamkar kana farin ciki da wannan hali da muke
ciki?"
Ya yin da Kurbas yaji wannan tambaya sai ya yi
murmushi ya ce, "Ya ke Ummul Maharaz kiyi sani cęwa na
fi kowa damuwa da wannan hali da muke ciki amma kuma
3
Taskar
ina farin ciki domin na san cewa wannan ce kadai dama
muka samo ta ceton rayuwar jikokina. Zuhura tayıa
zuciya ta ce, "Idan har muna son mu ceci rays
jikokinka dole ne da farko mu kwance sarkokin da
jikinmu sannan mu bude kofar wannan daki mu fita
sannan ne kuma zamu shiga neman inda aka boye jik
naka a.cikin wannan fada ka san kuwa wadannan aiyuk
masu sauki bane musamman ma artabun da zamu yi
wadannan dodannin Dakaru masu tsaron wannan fada.
Sa'adda Zuhura ta zo nan a'zancenta sai Kurbas ya
murmushi ya ce, "Ummul Maharaz shin kin manta ne ce
gaba dayan mu nan ma'abota addinin Musulunci ne, mu
yarda da Allah kuma mun yi imani da cewa babu abinda z
gagareshi, saboda haka mu nemi taimakonsa lallai zai bamu
sa'a bisa abinda muke son mu aiwatar".
Koda jin wannan batu sai fuskar Zuhura ta fadada da
murmushi ta ce, "Madalla da dan uwa mai tunatar da 'yan
uwansa abinda suka sha'afa da yi."
Koda gama fadin haka sai Zuhura ta mike tsaye ta
fuskanci Alkibla, take su ma su Kurbas suka yi koyi da ita
suka kama nafilfiloli da addu'o'i bisa neman taimakon
Allah akan halin da suke ciki. Ya yin da maigadin wannan
daki da suke ciki ya ga suna ta wannan ibada sai ya
kyalkyale da dariyar mugunta domin gani yake kamar
zautuwa suka yi.
Da yake Allah Ma ji rokon bawansa ne, lokacin da s
Zuhura suka dan jima suna ta yin addu'o'i sai kawai maigadin dakin da suke ciki ya kama gyan-gyadi dama a
zaune yake daf da kofar dakin bisa kujera. Kafin a jima barci ya saceshi bai sani ba har yana ta munshari mai karfi.
4
Taskar Tsafi = 5 Madakin Gini
Bayan su Kurbas sun gama addu'o'insu sai kawai sukaga maigadin nasu yana ta barci, al'amarin da ya jefasu cikinmatukar farin ciki ke nan.
Cikin sanda da lambo Kurbas ya mike tsaye ya zuro
hannunsa ta cikin kafar karafan da ke jikin kofar ya cirowadansu mukullai barkatai a cikin aljihun maigadin a
hankali. Koda yai nazarin makullan sai ya ga ashe kuba cе
ta bude wannan daki da suke ciki da kuma wasu mukullanna kwance sarkokin da aka faura musu su duka hudun a
hannayensu da kafafunsu. Cikin hanzari Kurbas ya budekofar dakin a hankali ya zo kan maigadin ya tsaya kawaisai ya daga hannunsa ya doki wuyan mai gadin da karfintsiya. Take wuyan mai gadin ya karye ya sulale kasamatacce. Cikin hanzari Kurbas ya janyo gawar mai gadinizuwa cikin dakin ya cire suturar da ke jikin maigadin yasanya akan tasa sannan yasa wadannan mukullai ya kwancesarkokin da ke jikinsu su duka suka fita daga cikinkurkukun suka janyo kofar ta rufc. Nan take suka yi gabasuna sanda. Kurbas ne akan gaba sannan Zuhura na biye dashi sai Hasilatul Kurbas, Inmal da Lahura.
Haka dai suka ci gaba da sanda labe-labe a cikinfadar, duk sa'adda suka hango dakaru za su gifta sai su yisauri su buya.
A haka suka yi ta kutsawa cikin fadar har suka isowani wuri inda suka ga kofofi guda uku. Nan fa suka tsayasuka yi cirko-cirko domin basu san kofar da ya kamata sushiga ba.
Su dai burinsu shi ne su gano dakin da aka boye suIzaima jikokin Kurbas. Nan fa duk su biyar din suka kamakallon juna suna tunanin dakin da ya kamata su fara shiga.5
Abdulaziz Sani Madakin Gini
Abdulaziz Sani Madakin Gini
Abdulaziz Sani Madakin Gini
Fareeda Abdullahi
Aliyu Abubakar Sharfadi
Abdulaziz Sani Madakin Gini
Mansur Usman Sufi
Hauwa Sarki Zaria
Sad Nass
Abdulaziz Sani Madakin Gini
Azeema D Aminu
Mukhtar Kwalisa
by Rashuna
by Abdulaziz Sani Madakin Gini
by Abdulaziz Sani Madakin Gini
by Khairat Up
by Siyama Ibrahim
by Aisha Muhammad Maman Shakur
by Asma Baffa
by Rasheeda S Director
by Abdulaziz Sani Madakin Gini
by Oum Amjad