Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
8 / 12
MACIJIYAR ta rinka daukar mutane tana jefawa bakinta tana hadiyewa. Sai hankali kowa ya tashi, mutane suka kama guje-guje suna Neman tsira da rayuwarsu. Nan da Nan Dakaru suka ruga suka Sanar da Sarki Zurmatu. Cikin tsananin fusata yayi Shirin yaki tare da Dakaru dubu Dari suka nufo wurin macijiyar nan. Da zuwansu suka iske tuni wannan Katuwar macijiyar ta hadiye sama da Mutane dubu bakwai, Amma idan ka dubi cikinta sai ka ganshi lakwaf tamkar wani Bai taba shiga ciki ba. Nan fa aka rasa hanyar da za'a bi a kashe wannan macijiyar saboda girmanta ya wuce misali gashi Kuma a duk bayan dakika Barnar da take masu tayi yawa. Nan take Sarki Zurmatu yayi addu'o'i a cikin zuciyarsa Yana Mai Kiran sunayen Allah tsarkaka tare da Neman Allah ya bashi nasara akan wannan Ala'marin. Koda gama wannan addu'o'in sai Sarki Zurmatu ya Karanta wata Addu'a ta musamman ya tofa akan takobinsa sannan ya kwallah kabbara da karfi, sai ya cilla takobin sama izuwan kan macijiyar. To daman a dai-dai wannan lokacin macijiyar ta rankwafo da rafkeken kanta da nufin yin Loma guda da su Sarki Zurmatu, Amma kafin kanta ya iso garesu tuni takobin da Sarki Zurmatu ya cilla sama ta fada cikin bakin macijiyar tana wurwurawa tamkar an makala takobin a Saman fankar jirgi. Nan fa wannan takobin ta rinka daddatsa jikin macijiyar tamkar ana daddatsa Albasa da wuka. Cikin tsananin mamaki kowa ya kurawa macijiyar idanu Yana ganin irin muguwar mutuwar wulakancin da take.. Domin takobin Dake daddatsa macijiyar tamkar wani ne ya rike ta yake Sarrafa ta, alhalin kuwa ba kowa ita kadai ce. Babban abinda yafi daurewa mutanen wajen Kai shi ne, ganin yadda takobin take da tsananin zafin nama gami da kaifin tsiya tamkar Reza. Kafin cikar dakika Dari da saba'in wannan takobin ta kammala daddatsa jikin macijiyar gaba Daya. Nan fa sassan jikin macijiyar ya taru himili guda tamkar Tsauni saboda tsananin girmanta. Ba zato ba tsammani sai akaga wannan takobin tana kammala wannan aikin ta dawo hannun Sarki Zurmatu, ya cabe ta. Nan fa mutane suka Kara cika da tsananin mamaki.. Nan da Nan Boka RAKUL ya rugo gaban Sarki Zurmatu ya zube Kasa ya kwashi gaisuwa, sannan ya ce ya Kai Sadauki uban sadaukai tabbas kayi gagarumar abin bajintar da ko matsafan duniya ba zasu iya ba. Amma tayaya akayi ka iya wannan aikin haka? Lokacin da Boka RAKUL yazo Nan a zancensa sai Sarki Zurmatu yayi murmushi sannan ya ce yakai RAKUL shin ka manta ne cewa mu a halin yanxu ma'abota Addinin musulunci ne? Kayi sani cewa ni kaina abin Nan yafi karfina domin bazan iya yakar wannan macijiyar ba, shiyasa na roki Ubangijina Allah akan ya taimakemu. Saboda haka duk wannan nasara da kaga mun samu to ba dabara ta ko kokarina bane, kawai Karfine daga wurin Allah madaukaki. Nan da Nan jama'ar Dake wurin suka sallamawa Ubangijin musulunci Kuma suka Kara sa imaninsa a zuciyarsu suka tabbatar lallai shi ne Addinin gaskiya Wanda yafi kowa da komai karfi. Ana cikin haka ne, Waziri Mikilas ya dubi Sarki Zurmatu ya ce, ya shugabana tabbas munyi Imani cewa Ubangijin musulunci shi ne Mafi daukaka, Kuma shi Mai Iko ne akan komai. Amma dai duk da haka Muna so ka bamu tarihin wannan takobi ta ka, domin mun lura cewa lallai wannan takobin akwai wani sirri a jikinta, domin tun kafin ka karbi addinin musulunci kake yaki da wannan takobi, Kuma duk abinda ka Sara da ita, to sai abun ya rabe gida biyu. Koda Jin wannan batu sai Sarki Zurmatu ya yi murmushi a karo na biyu sannan ya ce tabbas Waziri kayi gaskiya.. Labarin wannan takobi Yana da tsawo, saboda haka inaso yanxu kowa ya samu natsuwa sannan mu taru mu binne duk wadanda suka mutu a wannan yaki, Kuma ayiwa wadanda suka raunata magani. Sannan Kuma mu gyara duk Barnar da wannan macijiyar tayi mana. Idan Allah ya kaimu kowannenku ya zo fada, domin sanar daku sirrin da ke cikin takobi Mai albarka. Nan da Nan aka shiga aikin yiwa wadanda sukayi mutuwar Shahada jana'iza, sannan Kuma aka Debi sama da Mutane dubu uku aka nufi wurin magani da su. Nan dai aka kammala komai yadda ya dace, har kowa ya watse Yana tunanin yadda abubuwa suka faru yau kamar almara. Washe kuwa da sassafe kowa yazo fada, sannan Kuma bayan Waziri da sauran fadawa da jama'ar gari sunyi gaisuwa ga sarki. Daga Nan sai Sarki ya fara Basu labari kamar haka.... Ya ku jama'ar birnin BALLUS kuyi sani cewa, Asalin wannan takobi da kuke gani a wurina ta babana ce wato marigayi Sarki DURZASU, haka Kuma Shima kanshi mahaifina din Gadon takobin yayi a wurin babanshi, wato abin bi da bi ne har izuwa kaina. Asali mahaifina su biyu ne a wurin mahaifinsu, da shi da Dan uwansa ZULDARI. Mahaifina da yarima ZULDARI suna matukar kama da juna kasancewar su 'yan biyu ne. Lokacin da mahaifina suka girma sai halayen Yarima ZULDARI suka canza ya koma maketaci Kuma Azzalumi Wanda ba ya Jin bari. Domin kullum sai ya cikin gari yayi da cin zalin jama'a. Mahaifinsu yayi iyakar kokarinsa wajen Hana ZULDARI wannan Dabi'a Amma ya gagara. Shi kuwa mahaifina Sarki DURZASU sai ya zamo Adali Mai son Adalci da Kuma rikon Amana, bisa wannan dalili ne yasa ya samu farin jini sosai a wajen jama'ar gari da Kuma gidan sarautar gaba Daya. A dalilin hakane ma mutane suka Yanke shawarar cewa Koda Sarki yabar duniya to mahaifina suke son ya zama Sarkinsu. A sakamakon haka ne gaba Mai tsanani ta afku a tsakanin mahaifina da Kuma Yarima ZULDARI. Wanda a sanadiyyar haka yaki Mai tsanani ya rinka barkewa a tsakaninsu. A duk lokacin da suka kaure da yaki to sai tattaro Dakaru guda dubu arba'in wadanda suka kasance jajirtattun jarumai sannan suke iya tsayar da su. A sanadiyyar bakin cikin yakar junansu da suke yi ne, ya sa mahaifiyarsu ta hadiyi zuciya ta mutu Amma duk da haka Yarima ZULDARI Bai dena kokarin hallaka mahaifina ba. Wannan ne yasa Sarki ya fusata a lokacin Kuma ya Kori Yarima ZULDARI daga kasarsa akan cewa baya son ko bayan ransa ya Kara dawowa. Cikin tsananin bakin ciki Yarima ZULDARI yabar garin tare da kudirin cewa lallai Nan gaba sai ya dawo da gagarumin shiri ya karbe mulkin birnin daga hannun mahaifina. Tun daga lokacin da Yarima ZULDARI ya bar gida, sai ya fantsama cikin duniya ya rinka kashe mutane Yana kwace dukiyarsu, sannan Kuma ya rinka shiga kananun garuruwa Yana yakarsu ya mayar dasu bayinsa da karfin tsiya, da haka da haka har ya Samar da Katuwar rundunar mayaka Mai yawa. Nan da nan ya nufi wani babban birni a yankin da yake, ya yaki Sarkin dake Mulki a wannan birni Kuma ya kashe shi, sannan ya gaje gidan Sarkin da sarautarshi da duk dukiyar sa. Kuma ya tursasa jama'ar wannan Kasa suka rinka yi masa biyayyar dole. Koda Yarima ZULDARI yaga ya samu wannan gagarumar nasara, sai ya rinka ziyartar manyan Bokaye suna bashi sirrikan tsafi, cikin shekara Daya sai da ya Ziyarci bokaye Dari uku da arba'in da bakwai. A wannan lokaci tuni Yarima ZULDARI ya zama shahararre a bangaren tsafi, domin ya kusa ya gagari duk BOKAYEN Dake nahiyar gaba Daya. Koda ganin wannan nasara da ya samu, sai ya Yanke shawarar bincike akan birninsu domin gano hanyar da zai mallaki sarautar birnin BALLUS. Nan da nan ya shiga halwar tsafi ta kwana uku daga karshe ya kammala bincikensa inda ya cika da tsananin farin ciki. Ba komai ne ya binciko ba face, ya gano yanda zai kashe sarki da Kuma mahaifina DURZASU salin alin batare da wata wahala ba. Abinda Yarima ZULDARI ya binciko shi ne, dole ne zai kirkiri wata cutar sihiri sannan ya jefa ta akan Sarki ta yadda zai kwanta jinya tsawon lokaci, shi Kuma Dan uwansa DURZASU idan yaga halin da Sarki ya shiga, to babu makawa zai shiga duniya domin Nemo Masa magani. Ya tabbatar da cewa a kokarin nemowa Sarki maganin cutar da ta same shi ne zai hallaka a banza. Daga Nan shikenan sai yazo ya Haye KARAGARSA salin alin batare da Bata wahala ba, Kuma yayi irin mulkin da yake so na zalunci. Nan take yarima ZULDARI ya rufe idanunsa ya fara Karanta wadansu dalasiman tsafi da karfi. Faruwar hakan keda wuya sai akaga dakin ya kama girgiza kamar zai ruguje, kawai sai akaga wani murgujejen Aljani ya bayyana a gaban Yarima ZULDARI. Nan da nan Yarima ZULDARI ya dubi wannan Aljani Sannan ya ce, ya Kai GAMJAHUL FUTUL kayi sani cewa ba komai yasa na kira ba, face inason ka tafi can birnin BALLUS ka yanko min gashin Kan Sarki GURBAS wato mahaifinmu, da Kuma gashin kirjinsa sannan ka yanko min kadan daga jikin rigar sarautarshi ka kawo min Nan da cikar kwanaki biyu Ina jiranka. Cikin girmamawa Aljani GAMJAHUL FUTUL ya risina yace angama ya shugabana, Nan take ya bace. Bayan shudewar kwanaki biyu sai ga ALJANI GAMJAHUL FUTUL ya dawo dauke da wadannan abubuwan, cikin tsananin murna da farin ciki Yarima ZULDARI ya karbesu Yana Mai jinjinawa wannan Aljani. Nan take Yarima ZULDARI ya shiga daji ya kaso dabbar kurege da Kuma tsuntsun hankaka ya dawo, da zuwansa sai ya hada wadannan abubuwan da Aljani GAMJAHUL FUTUL ya kawo masa, da Kuma dabbobin da ya farauto. Nan take yayi wani wani sihiri da su, sai aka ga dukkansu sun manne a jikin junansu zuwa can Kuma sun rikide sun zama gudan jini. Sannan ya Kara hurawa da iska sai akaga wannan gudan jinin ya juye izuwa lafceciyar tsokar noma.. faruwar hakan keda wuya sai Yarima ZULDARI ya sake bushewa da dariya a karo na uku, Nan da nan ya sake Kiran ALJANI GAMJAHUL FUTUL ya fito, sannan ya Umarce da yaje ya samo Masa baqin kare Wanda babu ratsin kowace kala a jikinsa. Nan da Nan Aljani GAMJAHUL FUTUL yaje ya kawo wannan bakin Karen. Da zuwansa sai Yarima ZULDARI ya mikawa wannan Karen tsokar Naman Nan, shi kuwa kare ya kama tsokar Naman Nan ya cinyeta tass. Faruwar hakan keda wuya sai akaga wannan Karen yayi wata girgiza gami da wata Kara, sannan yayi tsalle ya dire. Cikin kyalkyala dariyar mugunta Yarima ZULDARI ya dubi wannan Aljani ya ce ya Kai GAMJAHUL FUTUL Maza ka dauki wannan kare ka biyo ni dashi. Nan da Nan Yarima ZULDARI yayi wani tsafi sai gani akayi sun bace bat daga wajen, Basu bayyana a ko'ina ba sai Saman tsaunin wani Katon Dutse. Nan da Nan Yarima ZULDARI ya umarci Aljani GAMJAHUL FUTUL da cewa ya shigar da wannan Karen izuwa cikin wani Katon kogo Dake Saman tsaunin, Kuma yaci gaba da kasancewa da wannan kare daga Nan har izuwa wani lokaci. Kuma ya rinka nemowa Karen Nan abincin da zai ci don ya rayu. Nan fa Yarima ZULDARI ya cigaba da gargadin wannan Aljani akan mayar da hankali wajen gadin wannan kare, Yana gama fadin haka sai ya zama Hayaki ya bace... Ala'marin su mahaifina kuwa, suna zaune a cikin fada ana tafiyar da harkokin Mulki kamar yadda aka Saba, kawai sai aka ga sarki GURBAS ya kurma ihu daga Saman KARAGARSA zuwa can sai yayi tsalle ya fado Kasa ya mimmike Yana aman jini. Nan da nan hankalin kowa ya tashi, akayi Maza aka shigar da Sarki GURBAS cikin turakarsa. Mahaifina DURZASU yayi Maza ya kira likitoci suka taru kan sarki domin ceto rayuwarsa Amma Abu ya faskara. Sai da aka kwana bakwai ana binciken lafiyar Sarki Amma an rasa gano ainihin cutar da ta kama Sarki Gurbasu. Nan fa hankalin kowa ya sake Dugunzuma tamkar su Dora hannu aka su rushe da kuka. Ana cikin haka ne Wazirin Sarki ya dubi mahaifina ya ce, ya Kai YARIMA kayi sani cewa Muna kyautata zaton cewa wannan ciwo da ya kama Sarki ba na likita bane, saboda haka ni a shawarata me zai Hana a kira Boka FADDA'UL ZULUK domin ya bincika ya gano mana irin cutar da ta kama Sarki. Nan da nan mahaifina yayi na'am da wannan shawara ta Waziri, Kuma ya aika aka kira Boka FADDA'UL ZULUK. Da zuwansa sai aka Kai shi wajen Sarki GURBAS domin ya duba halin da yake ciki, Yana zuwa ya Kalli Sarki sai ya dafe Kai, sannan ya ce yakai Yarima kayi sani cewa wannan Cuta ta mahaifinku sharrin sihiri ne. Kuma ba wani bane yayiwa mahaifinku asiri ba, face Dan uwanka Yarima ZULDARI. Ba don komai yayi Masa wannan sihirin ba sai domin ya hallaka Sarki kuma ya gaje KARAGARSA. Koda Jin wannan batu sai hankalin kowa yayi mummunan tashi Kuma aka rasa Wanda zai ce wani abu saboda tsananin mamaki. Daga can sai mahaifina ya dubi Bokan ya ce yakai BOKA FADDA'UL ZULUK to yanzu menene mafita akan wannan Ala'marin? Tayaya za'ayi Sarki ya samu lafiya? Koda Jin wannan batu sai Boka FADDA'UL ZULUK yayi shiru Yana tunani daga can, sai ya ce Ina zuwa. Nan take Boka FADDA'UL ZULUK ya runtse idanuwansa ya fara Karanta wadansu dalasiman tsafi sannan ya hade hannayensa wuri guda. Faruwar hakan keda sai akaga Jikin Boka FADDA'UL ZULUK ya kama karkarwa, cikin kankanin lokaci sai akaga jikinsa ya jike sharkaf da gumi bugu da Kari Kuma sai akaga Jikin Boka FADDA'UL ZULUK ya dume da zafi tamkar ana Gasa masara, su kansu su mahaifina suna iya Jiyo irin hucin da jikin Boka FADDA'UL ZULUK yake. Ba shiri Boka FADDA'UL ZULUK ya Bude idanunsa wadanda suka jike sharkaf da hawayen wuya. Cikin tsananin tashin hankali BOKA FADDA'UL ZULUK ya dubi su Yarima yayi masu jawabi kamar haka. Ya shugabana kuyi sani cewa shidai sihiri da aka yiwa mahaifinku, an hada da gashin Kansa da Kuma gashin kirjinsa da rigar sarautarshi akayi tsafi da su sannan aka ba wani sihirtaccen bakin kare su ya cinye. Bayan haka sai aka dauki wannan bakin Karen aka kaishi can wani Gagarumin tsaunin da duk duniya babu halittar da ta taba zuwa samansa Kuma ta dawo a raye. Sa'annan Kuma a Saman tsaunin sai aka wakilta wani shirgegen Aljani Mai suna GAMJAHUL FUTUL gadin wannan kare iyakar rayuwarsa. Saboda haka kuyi sani cewa muddin ana son a ceto rayuwar Sarki GURBAS daga wannan Cuta to dole ne aje wannan Tsauni a kamo wannan bakin Karen a kashe shi kafin cikar kwanaki saba'in. Idan aka kuskura aka Haura Koda kwana Daya ne akan saba'in din nan, to take Sarki zai mutu. BOKA FADDA'UL ZULUK yaci gaba da cewa, ya Shugabana kuyi sani cewa a yayin zuwa wannan Tsauni inda aka ajiye wannan bakin Karen, akwai wasu Dazuzzuka masu matukar hadarin gaske wadanda dole sai an bi ta cikinsu sannan ake Isa wannan Tsauni. Su dai wadannan Dazuzzuka sun kasance masu matukar ban tsoro gami da hadari ga rayuwar kowace irin halitta. Har ta Kai cewa fiye da shekaru tamanin baya ba a Kara samun Wanda ya keta ta cikin wadannan Dazuzzuka a Raye ba. Adadin wadannan Dazuzzuka guda bakwai ne, Kuma saboda tsananin bala'in da ke cikin kowane daji yasa, masana suka tabbatar da cewa ba'a taba samun mahalukin da ya iya tsallake Dajin farko ya shiga na biyu ba, face mutum Daya, ba kowa bane face marigayi kakanku Sarki DAHAMUL. Kuyi sani cewa tun bayan mutuwarsa har yau ba a Kara samun mahalukin da ya keta cikin wannan Dazuzzuka ba. Manyan jarumai da sadaukai da Bokaye sunsha yin gangami su tunkari wadannan dazuzzuka Amma komai yawansu da sunje daji na farko daga Nan baza'a Kara Jin duriyarsu ba har abada. Wannan shi ne abinda na sani dangane da yadda za'a karya sihirin da akayiwa mahaifinku. Cikin tsananin dimaucewa da tashin hankali, mahaifina ya dubi Boka FADDA'UL ZULUK ya ce, ya Kai wannan Boka inaso ka sanar Dani hanyar da zanbi domin wannan Tsauni, lallai Koda zan rasa rayuwata sai na nemowa mahaifina maganin cutarsa. Nan take mahaifina yaje turakar Sarki Gurbasu ya dauko sharbebiyar takobinsa yayi Shirin gagarumin Shirin yaki, Sannan ya dawo inda su Boka FADDA'UL ZULUK suke tsaye. Nan da Boka FADDA'UL ZULUK ya Ciro wata 'yar karamar laya a cikin aljihunsa sannan ya mikawa mahaifina, ya ce ya shugabana wannan ita ce zata rinka Yi maka Jagora a cikin tafiyarka. A duk lokacin da ka kauce hanya to zakaji wannan layar ta fizgi hannunka na hagu izuwa kan hanyar da kake bukata. Haka Kuma muddin kana tare da wannan layar, zaka rinka yin sauri a tafiyarka domin zaka iya yin tafiyar wuni guda a cikin sa'a biyu kacal. Cikin tsananin farin ciki mahaifina yasa hannu ya karbi wannan layar, sannan ya makaleta a cikin jikinsa ya yadda ba zata fado ba komai GUMURZU, sannan ya dubi BOKA FADDA'UL ZULUK yayi Masa godiya Mai yawa, Kuma yasa aka yiwa Boka gagarumar kyautar da ki tattaba kunnensa ba zasuyi talauci ba a duniya. Ba tare da Bata wani lokaci ba, mahaifina ya bar Amanar Kasar BALLUS da Kuma Amanar Sarki Gurbasu a hannun Waziri, Kuma yayi masu sallama ya kama dokinsa dauke da guzuri Mai yawa ya kama hanyar fita birnin. Tun ana iya hangoshi har ya bace.. Nan fa mahaifina yaci gaba da tafiya ba dare ba Rana, duk Inda ya gamu da wasu tsirarun 'yan fashi cikin kankanin lokaci yake ratattake su tamkar kwarankwatsa ta fadowa karmami. Haka mahaifina ya wanzu Yana tafiya har tsawon kwanaki bakwai, a cikin kwanaki bakwan ne ya shigo Dajin farko da BOKA FADDA'UL ZULUK ya bashi labari. Da shigarsa Dajin sai yasha jinin jikinsa, saboda yanda gaba dayan siffofin Dajin ta sha bamban da sauran Dazuzzuka. Itatuwan wannan Dajin sun kasance manya-manya tamkar Tsauni, sannan Kuma Duwatsun Dajin suna da tsananin girma da fadi. Haka Kuma duk Inda ya duba sai ya rinka ganin gilmawar wani abu Mai tsananin girma. Yana cikin tafiya kwatsam sai....... ME ZAI FARU A CIKIN WANNAN DAJI DA MAHAIFINA YARIMA DURZASU YA SHIGA? SHIN ZAI SAMU NASARAR TSALLAKE DUK MASIFUN DAKE CIKIN WADANNAN DAZUZZUKA GUDA BAKWAI? WANENE ZAI MALLAKI KARAGAR MULKIN SARKI GURBASU A TSAKANINSU? domin Jin Amsar wadannan tambayoyin sai mu hadu a littafin GASAR JARUMTAKA na bakwai 7 don Jin cigaban wannan Kasaitacce Kuma Kayataccen labari ✍️✍️👇 Wanda ni naku NAJIBULLAH MUHAMMAD marubucin littafin nake cewa ku huta lafiya ✍️♥️🥰🙏🙏🙏 JARUMTAKA** LITTAFI NA BAKWAI 7**GASAR JARUMTAKA** LITTAFI NA BAKWAI 7 PART A ✅♥️ MARUBUCI: NAJIBULLAH MUHAMMAD ✍️♥️ POSTING: Najibullah Muhammad 🥷🥷 Lokacin da mahaifina ya shigo cikin wannan Dajin sai yasha jinin jikinsa saboda yanda yanayin Dajin yasha bamban da sauran dazuzzuka. Gaba dayan bishiyoyin Dajin sun kasance manya-manya masu matukar tsawo da kauri, sannan Duwatsun Dajin sun kasance jibga-jibga tamkar Tsauni. Tunda mahaifina ya shigo cikin wannan daji Bai ji motsin komai ba, hatta bera Bai gani ba ballantana wata Dabba Mai cutarwa. Kwatsam Yana cikin tafiya sai ya rinka ganin gilmawar wasu manyan-manyan birirrika masu tsananin girma. Ana cikin haka ne, ya hango dandazon wadansu maka-makan birirrika kimanin su dubu goma sun diddiro daga Saman bishiyoyi. Kowannensu na rike da Katon Sangwami Wanda suke tare mutane da Aljanu suna kashewa da shi. Su dai wadannan birirrika sun kasance manya-manya Kuma jikinsu a murde yake tamkar duwatsu aka cuccura a cikin jikkunansu. Saboda tsabar girmansu da kadan bishiyoyin Dajin suka fisu girma. Bugu da Kari wadannan birirrika sun kasance a wannan daji tsawon shekaru Dari da arba'in da bakwai, Kuma asali da babu su. Wani bakon mugun Boka ne yazo giftawa ta wurin, shi ne ya samar da jinsin wadannan birirrika guda biyu domin a gaba su zama Annoba ga mutanen nahiyar gaba daya, su ne sukayi ta hayayyafa har sukayi wannan yawan. Kuma tunda suke Basu taba fita wajen wannan Dajin ba. A halin yanxu sun cinye gaba dayan dabbobin Dajin, ko bera babu ballantana sauran dabbobi. Sa'annan Kuma duk lokacin da tsautsayi ya kawo wani mahaluki inda suke, to idan suka kama shi, zasu daddatsa shi filla-filla su kaiwa Shugabansu Kan mutumen. Su Kuma su rarraba sauran Gangar jikin su cinye. Haka suke yiwa komai yawan runduna, ko Kasusuwan Basu bari sai sun cinye komai. A bisa wannan dalili ne yasa aka hakura da ratsawa da cikin wannan daji. Lokacin da wadannan birirrikan suka yiwa mahaifina Kawanya, suka zagaye shi suna huci da gurnani kamar masu jiran Umarni. Zuwa can sai sukaji wani irin mugun taku Sawun ya tunkaro inda suke. Nan da nan suka Buda hanya. Wani shirgegen gwaggon biri ne ya fito, Mai yamutsattsar Fuska tamkar an taka kashin shanu. Saboda tsabar girmansa har ma ya kere gaba dayan bishiyoyi da Duwatsun Dajin, Yana da jajayen idanuwa tamkar garwashin wuta aka lika a cikinsu. Jikinshi a murde yake tamkar jijiyoyin bishiyar kuka, a hannunsa na hagu ya daura wani Kambun karfe Mai launin jaa, sannan a hannunsa na dama Yana da wasu tafka-tafkan faratuna wadanda kome ya caka da su, sai abun ya ratattake tamkar an taka tumatur. Koda Shugaban birirrikan yazo wurin yaga mahaifina ya zare takobinsa Yana Mai gyara tsayuwa sannan Kuma ya kurawa shugaban birirrikan Ido, sai ransa ya Baci. Ba zato ba tsammani sai kawai aka ga shugaban birirrikan Nan ya cafko wata Katuwar bishiya Dake kusa da shi da hannu Daya, sannan ya tugo ta da dukkan karfinsa, sai ga jijiyoyin bishiyar a sama suna Lilo. Shugaban birirrikan ya cillawa mahaifina wannan bishiyar da nufin ta ragargaje shi, Nan take Yarima DURZASU ya daka wawan tsalle sama ya Kaftawa bishiyar Sara da dukkan karfinsa, sai gashi bishiyar ta rabe gida biyu duk da kasancewarta Mai tsananin kauri. Yarima DURZASU na dirowa, sai Shugaban birirrikan nan ya basu umarnin su afka Masa. Nan fa gaba dayan birirrikan nan suka Afkawa Yarima DURZASU, suka yanyameshi tamkar an jefa kwayar gero a tsakiyar gidan tururuwa. SADAUKI DURZASU ya kwarara uban ihu sannan ya kutsa cikinsu ya rinka saran birirrikan suna zubewa Kasa, su kuwa suka rinka kokarin cafko shi da hannu, wasu Kuma na Kai Masa mangari shi kuwa Yana zillewa, wasu na kawo masa mugun taku da kafa da nufin talitse shi, Amma cikin tsananin zafin nama ya rinka kaucewa harin nasu Kuma Yana zaftare masu sassan jikinsu. Duk da kasancewar Sadauki DURZASU na kashe birirrikan Amma sai yaga tamkar matattun ne suke sake tasowa, domin ko kadan basa raguwa. Yayinda gumurzu yayi gumurzu sai ramuka suka yawaita a Kasa, saboda mugun takun sawun da birirrikan suke kawowa SADAUKI DURZASU, Nan take ranshi ya Kara Baci sosai ya tuna irin gagarumin aikin da ke gabanshi, kawai sai akaga ya daka wani wawan tsalle sama ya haye Saman kan birirrikan Nan. Koda ganinshi akan kawunan birirrikan nan, sai ya rinka daddatsa kawunan birirrikan cikin tsananin zafin nama na gaban kwatance. Kafin kiftawar Ido ya Kashe sama da birirrikan guda dubu. Koda wadannan birirrikan suka ga haka sai suka fusata ainun, saboda haka sai suka rinka kaiwa SADAUKI DURZASU duka da wannan Katon Sangwamin da nufin su mako shi ya fado Kasa, cikin tsananin zafin nama ya rinka kaucewa harin nasu, suka rinka makawa kawunan 'yan uwansu Sangwamin. Duk birin da aka makawa wannan Katon Sangwamin aka sai dai kaga Kan ya fashe cus, kwakwalwa da jini sai kwararowa suke a Kasa suna tsiri a sama, sai dai kaga birin ya sulale Kasa matacce. Nan fa gawarwakin birirrikan suka yawaita a cikin Dajin, a cikin sa'a guda sai da Sadauki DURZASU ya kashe birirrikan dubu shida. Koda Shugaban birirrikan Nan yaga irin mummunar barnar da wannan jarumi yake masu, sai ransa ya Baci Kuma zuciyarsa ta harzuka. Cikin tsananin fusata ya cizgo wata zureriyar bishiya Mai tsananin tsawo, sannan ya kawowa SADAUKI DURZASU duka da ita da dukkan karfinsa. Nan fa DURZASU yayi iyakar kokarinsa wajen kaucewa harin shugaban birirrikan nan Amma ya Kasa, sai da wasu rassan bishiyar suka sargafo shi, sannan suka mako shi Kasa. Kafin ya Mike shugaban birirrikan yasa kafarsa guda ya rinka halba shi Yana gwaruwa da bishiyoyin Dajin Yana fadowa. Nan fa DURZASU ya fita daga hayyacinshi jikinsa yayi laga-laga ya zamana cewa dakyar yake iya Bude Ido ma. A wannan lokaci jikinsa yayi raunika masu yawa, saboda tsabar gwaruwa da bishiyoyin Dajin da yake. Sai da yazamana cewa DURZASU yayi male-male a Kasa yana numfashi sama-sama ya kasa mikewa saboda tsananin galabaita. Koda Shugaban birirrikan Nan yaga irin wannan nasara da ya samu, sai yayi wani irin ruri Mai tsananin razanarwa Yana Mai dukan kirjinsa, Nan take ragowarsa yaransa sukayi koyi da shi. Karar rurin birirrikan nan da Kuma dukan kirajensu ya cika Dajin gaba Daya. Bayan wani lokaci sai shugaban birirrikan ya tsuke bakinsa, sannan ya tako yazo inda DURZASU ke kwance magashiyan, sannan ya rike kugu Yana mamakin irin Jarumtakar wannan jarumi. Shi a saninsa tun Wanzuwarsu a wannan daji tsawon shekaru Dari da arba'in, sunyi karo da Jarumai kala-kala Amma babu Wanda ya iya kashe mashi Yara, face wannan hatsabibin jarumin. Nan take ya ayyana a ransa cewa zayyi Masa mummunan kisan gilla irin Wanda ba a taba yiwa wani irinsa ba. Koda gama ayyana hakan, sai shugaban birirrikan ya duko da kanshi Kasa sannan ya tallafo kan DURZASU da Dan yatsa guda, da nufin ya soka Kansa a cikin bakinsa ya gutsure. Ba zato ba tsammani cikin tsananin zafin nama na gaban kwatance Mai

Chapter 8 of 12