Huda jikinsu to na mamallakin makamin ne. Kuma Koda kayi Amfani da makamin Daya daga cikinsu domin yakarsu Nan ma bazayyi tasiri akansu ba, dole sai dai ka rinka kwace na kowannensu Sannan kana Amfani dashi wajen kashe Mai shi.
Koda ganin haka sai ganin haka sai ran sadauki MARGIM ya 6aci, kawai sai yayi jifa da wannan Addar, Nan take ya rinka tattara gaba dayan karfinsa wuri guda Yana sa gwiwar kafarsa Yana dukan hannuwansu da kafafunsu, Nan take Kasusuwan Dakarun suka rinka karyewa kamar ana sassabe a gona.
Nan fa ihun Dakarun da karajinsu ya cika filin Gasar gaba Daya.
Domin cikin kankanin lokaci ya karya Kasusuwan Dakaru bakwai daga cikinsu, Kuma duk Wanda ya karya sai kwace Addarsa Sannan ya fille Masa Kai.
Koda Shugaban Dakarun yaga wannan mummunar barna da Sadauki MARGIM keyi masu, sai zuciyarsa ta kama tafarfasa kamar zata kone, kawai sai aka ga shugaban Dakarun yayi tsalle daga inda yake tsaye, sannan ya cafko wuyan Sadauki MARGIM da hannu Daya, Nan da Nan ya rinka fyada shi da Kasa da hannu Daya, cikin kankanin lokaci Sadauki MARGIM ya fita daga hayyacinshi saboda tsananin karfin kayen da shugaban Dakarun ke Yi masa ya wuce misali.
A cikin dakika sittin kacal sadauki MARGIM ya Suma, sannan shugaban Dakarun ya sake shi, shikuma ya sulale Kasa ko shurawa bayayi.
Cikin tsananin fusata shugaban Dakarun ya ya zaro wannan Adda tasa, sannan ya laftawa Sadauki MARGIM wani lafcecen Sara a baya Sannan ya Kara lafta mashi Sara a ciki, sannan ya daka wani wawan tsalle ya duro akan Kafafunsa Nan take duka kafafun suka karye.
Cikin tsananin Jin zafi da Zogi sadauki MARGIM ya takarkare ya kwarara wani uban ihu Mai razanarwa.
A dai-dai wannan lokaci ne shugaban Dakarun ya daga wannan lafceciyar Addar sama da nufin ya fille Masa Kai.
Kwatsam sai aka ga SADAUKI MARGIM ya hada hannuwansa guda biyu Sannan ya Doki cinyar shugaban Dakarun, take cinyarsa ta karye ba shiri ya durkushe Kasa tare da Sakin Addarsa, cikin zafin nama Sadauki MARGIM ya dauki takobin ya fillewa shugaban Dakarun Kai da ita.
Nan take sauran Dakarun da suka rage guda biyu suka rugo gare shi, kawai sai gani akayi SADAUKI MARGIM ya bugi Kasa da hannuwansa duka biyun ya tashi sama kamar tsuntsu, Yana zuwa wajen ragowar Dakarun sai Doki makoshinsu a lokaci guda, Nan take duk su biyun sukayi mutuwar tsaye, sannan addunansu suka subuce masu, cikin zafin nama ya Suri addunan sannan ya fille masu Kai suka zube a Kasa matattu.
Faruwar hakan keda sai aka aka ga Shima Sadauki MARGIM din ya sulale Kasa a sume saboda tsananin Gajiya, ga Kuma wadannan manyan-manyan raunikan da Shugaban Dakarun yayi mashi, suna ta malalar da jini tamkar idon teku, bugi da Kari ga Kafafunsa duk sun kumbura sakamakon karairayewar da yayi.
Nan take Sarki ya bayar da Umarnin ayi Maza a daukeshi domin a ceto rayuwarsa.
Sannan Sarki yayiwa jama'ar filin Gasar jawabi cewa lallai kowannensu ya kasance cikin shiri, domin a yanzu za'aje hutun cin abinci kafin da yamma a dawo aci gaba da gudanar da wannan Gasa.
Sannan idan an dawo za a canza sabon jarumin Gasa Wanda zai fafata kafin SADAUKI MARGIM ya dawo hayyacinsa.
Lallai wannan Gasa bazata Dakata ba, daga Nan har sai munga Wanda zai lashe Kambun GASAR JARUMTAKA.
Yayinda SARKI ZURMATU ya gama wannan jawabin Sai ya sallami kowa tare da shaidawa kowa lallai da yamma za'a ci gaba da gudanar da wannan Gasa.
Nan take kowa ya watse Yana fadin albarkacin bakinsa.
Sarki Zurmatu da sauran sarakuna suka tashi daga Kan kujerunsu sannan suka nufi ainihin Babbar fadar Sarki suna tafiya cikin kasaita da izzar Mulki.
Dakaru na take masu baya.
ME ZAI FARU IDAN YAMMA TAYI AKA DAWO FILIN GASAR JARUMTAKA?
SHIN JARUMI MARGIM ZAI FARFADO A CI GABA DA FAFATAWA DA SHI?
WANENE ZAI LASHE KAMBUN GASAR JARUMTAKA?
WANE IRIN BAKIN GUMURZU ZA'AYI DA YAMMA A FILIN GASAR JARUMTAKA?
WANE IRIN SHIRI SU SARKI FALWAN DA YARIMA FAZAMAL SUKE YI DOMIN GANIN SUN LASHE KAMBUN GASAR JARUMTAKA?
Domin Jin wadannan Amsoshi sai ku biyoni a cikin LITTAFIN GASAR JARUMTAKA na biyu Wanda ni Najibullah Muhammad na rubuta Kuma nake kawo maku shi✍️✍️✍️
Ina yiwa kowa fatan Alkhairi tare da cewa sai mun sake saduwa🤝♥️♥️
**GASAR JARUMTAKA**
LITTAFI NA BIYU 2 ✍️
PART A ✅♥️
Marubuci:- Najibullah Muhammad 🥷🥷
Typing/posting Najibullah Muhammad legends of the century ✍️🙏🥷
Kafin muci gaba da littafin mu akwai mutane da yawa da suke tambayata number ta.
To ga ta...
08112778656
Email dina..
najibullahimuhammad405@gmail.com
_________________________
Lokacin da Sarki Zurmatu da mukarrabansa suka baro filin GASAR JARUMTAKA suka nufi fada.
Sai likitoci suka ciccibo Sadauki MARGIM suka wuce dashi dakin jinya don yi masa magani domin har yanzu jini na kwarara a wadannan manyan raunikan da Shugaban Dakarun yayi Masa.
Da shigar su dakin jinya, sai suka debo kayan aiki suka tube Masa Riga don dinke Masa raunikan da ke jikinsa da Kuma gyara Masa karayar Kafafunsa.
Kwatsam ba zato ba tsammani sai kawai aka ga Dakin ya kama girgiza kamar zai ruguje, sannan sai wata iska Mai tsananin karfin tsiya ta kutso cikin dakin.
Saboda tsananin karfin iskar sai ta rinka daukar likitocin Dake Shirin yiwa MARGIM magani tana makasu a bango suna fadowa a matukar galaibace.
Cikin kankanin lokaci duk suka gigice, suka dimauce saboda tsananin zafin kayen da iskar ke masu.
Bayan kamar dakika Dari da Ashirin da faruwar hakan, sai iskar ta tsaya cak, Kuma dakin ya dena girgiza.
Kwatsam sai aka ga wani Jan Hayaki ya nannade sadauki MARGIM sannan ya bace tare da shi.
Koda ganin wannan Ala'mari sai gaba dayan likitocin suka rude, cikin tsananin razana shugaban likitocin ya ruga fadar Sarki Zurmatu domin sanar dashi wannan bakon Ala'mari.
Ala'marin SARKI ZURMATU kuwa lokacin da ya Isa turakarsa sai ya tura aka kira Masa Waziri domin binciko Asalin wannan jarumin da ya fafata da Dakarun Sarki a filin Gasa.
Cikin kankanin lokaci Waziri Mikilas ya zo turakar Sarki, bayan ya samu natsuwa sai Sarki Zurmatu ya dubi Waziri ya ce, ya Kai Waziri kayi sani cewa dalilin dayasa na kira ka shi ne, domin muyi bincike akan Asalin wannan bakon jarumi da ya fafata yaki a yau din nan.
Ka sani cewa wannan jarumi yayi babbar bajintar da ba kowa zai iya yin kamarta ba, domin daga cikin jarumai dubu mawuyacin abu ne a samu biyar masu irin baiwarsa, don haka ya zama dole musan ko shi wanene kafin ya warke daga raunikan Daya samu a filin Gasa.
Sarki Zurmatu yaci gaba da cewa, Waziri kayi sani cewa kimanin shekaru Ashirin da biyar da suka wuce, a lokacin da nake Neman haihuwa ruwa a jallo ban samu ba, bayan na Ziyarci bokaye Dari da saba'in da bakwai Amma ban dace ba, har na fara yanke Qauna da samun Magaji.
Daga bisani ne naji labarin wani shahararren Boka a yankin Kasar BANBUS, Wanda ke rayuwa a bayan gari cikin kogon Dutsen BUKUL.
Na samu labarin wannan shahararren Boka ne a wurin Bokan karshe da na ziyarta wato na cikon Dari bakwai da saba'in da bakwai, bayan Bokan yayi bincike sai yayi murmushi ya ce ya Kai wannan Sarki ka sani cewa duk duniyar Nan babu Wanda zai iya baka maganin matsalarka face mutum Daya, ba wani bane face Boka RAKUL na Kasar BANBUS.
A halin yanxu duk duniya babu Bokan da ya kai shi karfin sihirin tsafi, domin shi ne Bokan da ya zagaye duniya Kaf! Ya tattara gaba dayan sirrikan tsafin da ke cikinta, sihiri Daya ne kacal ya rage Masa ya mallaka Wanda zai hada da nasa domin ya zama gagarabadau, da zaran ya mallaki wannan sihirin to bazai mutu ba sai ya cika shekaru dubu saba'in a duniya, Kuma tsawon wannan shekaru shi ne zai ci gaba da rike KAMBUN GASA NA SHUGABAN BOKAYEN DUNIYA.
Wannan sihiri da Boka RAKUL yake nema ba komai bane face Yana son a tattaro mashi jinin gaba dayan dayan Sadaukan Duniya na jinsin bil'adama da ALJANU Wanda zai hadasu da wasu Alkaluman tsafi sannan ya shiga halwar tsafi ta kwana saba'in don tabbatar da wannan babban sihiri..
Bincike ya tabbatar da cewa indai Boka RAKUL ya cika wannan burin na shi to zai zamana cewa tamkar Yana mulkin duka duniya ne, domin komai zai zama sai da umarninsa yake aiki.
A bisa wannan dalilin ne, Boka RAKUL ya dukufa binciken hanyar da zai cika wannan babban burin na shi, sai da yayi kwana Dari a cikin halwar tsafinsa Yana bincike ba ci ba Sha tsawon wannan lokaci, sannan daga bisani ya samu mafita.
Mafitar kuwa ita ce, yayi bincike a madubinsa yaga cewa burinsa bazai taba cika ba, face yayi Amfani da Sarki Zurmatu saboda kasancewar a wannan lokacin duk duniya babu inda ya Kai Kasar BALLUS girma da yawan Dakaru da Kuma arziki.
Saboda haka sai yayi Amfani da karfin sihirin tsafi ya juyar da mahaifar matar Sarki Zurmatu, ta yadda har abada bazata taba haihuwa ba har sai yazo gareshi Neman taimako daga Nan Shima sai ya kawo sharadinshi Wanda zai zamo sanadin cikar burinshi.
Koda gama wannan bincike da Boka RAKUL yayi sai ya tuntsire da mahaukaciyar dariya har kwallar farin ciki na shatata akan kumatunsa saboda ya gano hanyar da zai cika burinsa.
Ala'marin SARKI ZURMATU kuwa, bayan ya samu gamsassun bayanai akan Boka RAKUL da Kuma irin shahararsa, Sannan Kuma wannan Bokan ya tabbatar mashi da cewa Boka RAKUL ne kadai zai iya magance Masa matsalarsa.
Nan take ya koma birninsa ya kama Shirin tunkarar birnin BANBUS don ziyartar Boka RAKUL.
Bayan shafe tafiyar kwanaki arba'in bisa ingarman dawakai, sai Sarki Zurmatu ya iso kogon Dutsen BUKUL inda Boka RAKUL ya ke.
Koda zuwansu bakin kofar Kogon, sai kawai suka ga gaba dayan Dajin da kogon yake ya gauraye da tsananin duhun da ko tafin hannun mutum Bai Isa ya gani ba, bayan kamar Dakika sittin da faruwar hakan sai sukaji an kece da mahaukaciyar dariya wadda Amsa kuwwar ta ya cika Dajin gaba Daya, zuwa can sai dariyar tayi shiru sannan ta ce, " lale marhabun da Gwarzo Kuma SADAUKIN SARAKUNA wato Sarki Zurmatu IBN Turmadu, kayi sani cewa na San duk abinda ke tafe Dake Kuma tabbas kazo inda za a share maka hawaye, don haka ka shigo cikin wannan kogon Kai kadai kabar dakarunka a wajen Kogon.
Koda gama fadin hakan sai muryar ta dauke, sannan wani farin haske ya wanzu akan hanyar da za a bi aje inda Boka RAKUL yake, alhalin kuwa sauran Dakarun duk a cikin daji yake.
Nan take Sarki Zurmatu yayi ta bin duk Inda wannan hasken yake, Yana tafiya Yana ganin abubuwan al'ajabi.
Domin akan hanyar shigarsa kogon ne yayita ganin Kwarangwal din halittu iri-iri na kowace halitta gasu Nan birjik a sakale a jikin bango anyi masu wani irin nau'in rubuce-rubuce da harsuna mabambanta.
Haka dai Sarki Zurmatu yayi ta tafiya har tsawon sa'a biyu Sannan ya iso wata Babbar fada Mai tsananin girma da fadi da kawatuwa..
Gaba dayan kayayyakin cikin fadar komai Sarrafa kanshi yake da kanshi.
Hatta abinci da abin Sha, da zarar mutum ya zauna Kan kujera zasu kawo kansu da kansu a gaban mutum sannan su Rika zuwa dai-dai misali kusa da bakin mutum ya kama ci har ya koshi.
Tabbas wannan wuri ya cika Aljannar duniya domin an tanadi komai da komai na Jin dadin rayuwar duniya.
Sarki Zurmatu na cikin mamakin wannan kogon Dutsen ne ya hango wani mutum zaune akan iska sannan ya nannade Kafafunsa tamkar akan turba yake, Kuma ya rufe idanunsa Yana Karanta wasu abubuwan da ba a fahimta.
A hankali tsohon ya cigaba da tahowa cikin iska har ya iso kusa da Sarki Zurmatu, sannan ya zauna daf da Sarki Yana Mai Yi Masa murmushi tamkar Wanda yaga Dan uwansa na jini.
Har Sarki Zurmatu ya budi Baki da nufin magana sai Boka RAKUL ya dakatar da shi, Sannan ya ce ya Kai wannan Sarki ka kwantar da hankalinka na San duk abinda ke damunka ba sai kace komai ba.
Domin ba wata matsala bace ke damunka face matsalar haihuwa, Kuma sai da ka Ziyarci bokaye Dari da saba'in da bakwai Amma baka dace ba, daga bisani ka hadu da Bokan da ya baka labarina wanda har ka zo nemana.
Sarki Zurmatu ya dubi Boka RAKUL cikin tsananin mamaki ya ce tayaya duk Kasan da wannan Ala'mari alhalin akwai tazara mai yawa a tsakaninmu?
Koda Jin haka sai Boka RAKUL ya bushe da dariya sannan ya ce, ka kwantar da hankalinka yakai wannan Sarki.
Kayi sani cewa ni yanzu na taka wani matsayi da duk duniya babu Bokan da ya taka shi, don haka yanzun Nan zan nuna maka yadda Ala'marin ya kasance domin ka samu natsuwa.
Gama fadin hakan keda wuya sai Boka RAKUL yayi da hannunsa na hagu izuwa ga bangon dakin da suke, take hoton birnin BALLUS ya bayyana.
Nan take aka cigaba da Nuno hotunan irin matsalolin da suka rinka faruwa a dalilin rashin haihuwa har Sarki ya fara ziyartar Bokaye domin neman magani, aka ci gaba da nuna wuraren da Sarki yaje har izuwa Kan Boka na karshe, ana zuwa dai-dai Nan sai Boka RAKUL ya sake nuna bangon da hannun Hagu take hoton komai ya 6ace.
Koda gama ganin haka sai Sarki Zurmatu ya Kara kamuwa da tsananin mamaki Kuma ya Kara tsinkewa da al'amarin Boka RAKUL ya tabbatar da cewa ya cika Hatsabibi.
Boka RAKUL ya dubi Sarki Zurmatu yace yakai wannan Sarki Bukatar mai sauki ce, Amma mudin zaka yadda da sharudda guda biyu.
Sharadi na farko shi ne, idan bukata ta biya da shekaru Ashirin zaka shirya GASAR JARUMTAKA a cikin birninka wadda zaka gayyato gaba dayan Sadaukan Duniya domin shiga wannan Gasa da za'ayi.
Sannan sharadi na biyu shi ne, ya zama dole kaje Kasar RUM ka siyo wadansu Dakaru na musamman wadanda asalinsu sun kasance jinsin SAMUDAWA ne, wadannan Dakarun da zaka siyo da su ne zaka rinka Amfani wajen shirya GASAR JARUMTAKA da zaka shirya a tsakanin duk Jaruman da ka gayyato daga sassan duniya.
Kayi sani cewa makaman da wadannan DAKARUN da zaka siyo suke Amfani da su, na Saka masu wani babban sihirin da duk mahalukin da aka yiwa rauni da su to bazai wuce kwana biyu a duniya ba zai mutu.
Don haka inaso ya zamana cewa gaba dayan Jaruman Gasar da ka gayyato sun hallaka a sanadiyyar fafatawa da wadannan DAKARUN.
Idan har ka yarda da wadannan sharudda to yanzu take zan biya maka bukatar ka.
Koda Jin wannan batu sai Sarki Zurmatu ya kawo gwauron numfashi ya ajiye, daga bisani yace yakai wannan Boka mai abun mamaki kayi sani indai wannan zai sanyani cikar burina to na amince.
Koda Jin wannan batu sai Boka RAKUL ya tuntsire da dariyar farin ciki, Sannan ya ce nayi maka alkawari a cikin kwana bakwai matarka zata samu ciki, sannan lallai zata haifi abinda ke cikinta lafiya Kuma abinda zata Haifa zayyi suna, daukaka, da tsawon Rai a duniya.
Amma fa bayan wannan bazaka Kara haihuwa ba.
Batare da Bata lokaci ba, Boka RAKUL yayi tsafi sai ga wani kullin magani ya bayyana a hannunsa, sannan ya mikawa Sarki Zurmatu ya ce, karbi wannan yakai SARKIN SARAKAI idan kaje gida a cikin dakin da kuke barci da matarka ka turara wannan a cikin dakin tare da ita, a ranar da kayi wannan aikin a ranar zata samu ciki.
Don haka kuje na sallameku, sai bayan shekaru Ashirin zamu sake saduwa.
Yana gama fadin hakan ya bace bat tamkar Bai gaba wanzuwa a wajen ba.
Cikin tsananin farin ciki Sarki Zurmatu ya fito wajen Kogon, sannan ya tarar yanzu haske ya dawo ko'ina, suka hawo dawakansu suka dawo gida.
A ranar da Sarki ya aikata abinda Boka RAKUL ya bashi, a ranar matarshi ta samu ciki kamar yadda ya fada..
Koda Sarki Zurmatu yazo Nan a jawabinsa sai kwalla ta cika masa idanu, sannan ya kara da cewa Ina tsoron kada wannan Jarumi ya samu nasara akan wadannan Dakarun batare da na cika sharadin Boka RAKUL ba.
Idan kuwa haka ya faru to akwai gagarumar matsala, domin matsalar zata iya zama sanadiyyar tarwatsewar birnin Nan da duk wani abu Mai Rai na cikin birnin.
Koda Sarki yazo Nan a zancensa, sai Waziri ya cika da tsananin mamaki, har Waziri ya budi Baki da niyyar cewa wani abu, sai kawai suka ga Shugaban likitocin da Sarki yasa su ceto rayuwar JARUMI MARGIM ya shiga turakar a firgice, Yana zuwa gaban Sarki ya zube ya kwashi gaisuwa Yana haki kamar ransa zai fita..
Nan take shugaban likitocin ya kwashe duk abinda ya faru a cikin dakin jinya a kokarin yiwa SADAUKI MARGIM magani ya fadawa Sarki.
Koda Jin wannan batu sai Sarki da Waziri suka mimmike tsaye saboda tsananin razana da mamakin Jin wannan batu na shugaban likitoci, cikin fushi Sarki Zurmatu ya kwarara wani uban ihu Mai ban tsoro Wanda Amsa kuwwarsa ta cika fadar gaba Daya, kawai sai yayi nufin ya ruga izuwa dakin ganin da shi da Waziri domin su ganewa idanunsu sannan su San matakin da zasu dauka.
Kwatsam ba zato ba tsammani sai kawai suka ga SHUGABAN BOKAYEN DUNIYA WATO BOKA RAKUL ya bayyana Tsulum a gabansu cikin wata irin mummunar shiga Kuma fuskarsa a murtuke, gaba dayan jikinsa Gurayen tsafi ne da Layun tsafi....
Kash! Laifin dadi karewa.
Mu hadu a GASAR JARUMTAKA 2 B don Jin cigaban wannan Kasaitacce Kuma kayatacciyar HIKAYAR✍️✍️🙏**GASAR JARUMTAKA**
LITTAFI NA BIYU 2 ✍️
PART B ✅✅
Marubuci:- Najibullah Muhammad ✍️✍️✍️
Typing/posting Najibullah Muhammad 🥷🥷🥷
Whatsapp No. 08112778656.
CIGABAN LABARIN.....
Lokacin da su Sarki Zurmatu suka ga BOKA RAKUL ya bayyana Tsulum a gabansu, sai suka Kara gigicewa musamman ma Sarki Zurmatu domin ya tabbatar da cewa lallai dalilin dayasa Boka RAKUL zuwa a wannan lokaci ba karamin Abu bane.
Cikin tsananin damuwa Boka RAKUL ya dubi su Sarki Zurmatu ya ce tabbas akwai gagarumar matsala da take tunkaro mu wadda idan bamuyi dagaske wajen maganinta ba, to gaba dayanmu sai mun hallaka, hatta wannan birni naka sai ya zama tarihi cikin kankanin lokaci zai baje ya koma tamkar ba a taba yinsa ba.
Cikin kaduwa Sarki Zurmatu ya dubi Boka RAKUL ya ce yakai wannan hatsabibin Boka, Maza ka sanar Dani abinda ke Shirin faruwa domin muyi gaggawar daukar mataki tun kafin dare yayi mana.
Kafin wani daga cikinsu ya Kara cewa wani abu, tuni Boka RAKUL yayi nuni da hannunsa na hagu izuwa ga bangon dakin da suke, Nan take sai suka ga hoton dakin da aka shigar da SADAUKI MARGIM don yi masa magani, aka ci gaba da Nuno duk abubuwan da suka faru.
Kamawa tun daga Kan lokacin da dakin ya fara girgiza da Kuma yadda kakkarfar iskar Nan tayi ta wurgi da sauran likitocin har zuwa Kan lokacin da wani Jan haske ya nannade sadauki MARGIM sannan ya bace da shi.
Nan take Boka RAKUL ya Kara nuna wannan bangon da hannun Hagu take hoton komai ya bace.
Sannan ya fuskance su Yana Mai cewa, ya Kai wannan Sarki kayi sani cewa bala'in da yake tunkaro min yafi karfin duk yanda kake tunani domin za'a iya asarar milyoyin rayuka a kokarin magance wannan matsalar.
Koda Jin haka sai Sarki Zurmatu ya dubi Boka RAKUL ya ce, yakai wannan Boka na roke ka akan ka sanar abinda ke faruwa, domin a shirye nake na yaki koma wace irin matsala ce wadda take Shirin kawo mana barazana akan rayuwarmu, mulkinmu da Kuma mutuncinmu.
Don haka ni yanzu Kai kawai nake Jira domin daukar mataki.
Boka RAKUL yayi doguwar ajiyar zuciya gami da yake, ya ce " ya Kai wannan Sarki kayi sani cewa matsalar da ke tunkaro mu ita ce..
Akwai wani HATSABIBIN BOKA Dake nahiyar birnin SIN Wanda mukayi kunnen Doki dashi a bangaren ilimin tsafi, a bisa wannan dalili yayi bincike ya gano nufinmu akan Shirin mallakar duniya da duk abinda ke cikinta ta hanyar shirya GASAR JARUMTAKA, da Kuma Amfani da duk jinin Jaruman Gasar da aka kashe wajen kammaluwar bukatarmu.
Koda ganin faruwar wannan Ala'mari Shima sai yayi alwashin Hana cikar burinmu, ya kudurce a ransa cewa lallai dole ne ya dakatar damu domin a rayuwarsa ya tsani ya kasance a karkashin mulkin wani ana bashi Umarni tamkar BAWA.
Don haka Nan da Nan ya fara Shirin ceton duk jarumin da ya fafata a filin Gasa.
Boka RAKUL ya ci gaba da cewa, ya Kai wannan Sarki kayi sani cewa kamar yadda na fada maka a shekarun baya cewa wadannan miyagun makaman da DAKARUNKA suke dasu sun kasance tsafaffu ta yadda duk Wanda aka Sara ko yiwa rauni da shi, to bazai Haura kwana biyu a duniya ba zai mutu.
Duk Wanda ake so ya rayu bayan ya samu rauni da wannan makami to tabbas dole sai anje karkashin TEKUN ZALLUS dake bayan birnin SIN sannan an tsinko ciyawar KATUL an daka ta sannan an shafawa mutum a raunin da makamin yayi Masa kafin cikar kwanaki biyu, ana shafa Masa take zai warke tamkar wani abu bai taba samunsa ba, idan kuwa akayi jinkiri har zuwa kwana biyu to nan take zai mutu.
Boka RAKUL ya ci gaba da cewa, daga Nan zuwa birnin SIN inda wannan Hatsabibin Boka yake, tafiya ce ta Kwanaki Dari da tamanin bisa ingarman dawakai kosassu masu lafiya.
Yanzu haka wadansu Bakaken Aljanu ne BOKA GARGUS ya turo sukayi Masa wannan aikin.
Wadannan sun kasance jibga-jibga Kuma manyan sadaukai marasa Imani daga jinsin ALJANU, domin Hatta a duniyar Aljanu sun fitini kowa an rasa yadda za'ayi dasu saboda tsananin zaluncinsu da Kuma karfin da suke dashi wamda ya wuce misali, a bisa wannan dalili ne BOKA GARGUS ya gayyato gaba dayan jinsin wadannan Bakaken Aljanun domin su rinka yi masa aiki, bisa yarjejeniyar a duk bayan wata guda zai rinka shayar dasu jinin bil'adama guda dubu, da Kuma dabbobi guda dubu saboda kasancewar jinin bil'adama da dabbobi ne abincinsu.
Bugu da Kari wadannan Aljanun sun kasance masu tsananin karfin gudun tsiya tamkar kibiya, domin suna iya shafe sama da tafiyar wata guda a cikin sa'a guda kacal.
Koda Boka RAKUL yazo Nan a zancensa sai hankalin Sarki Zurmatu ya Dunguzuma ainun sannan ya dubi Boka RAKUL ya ce, wai shin wace matsala zata biyo baya yayinda BOKA GARGUS ya ceto rayuwar JARUMI MARGIM kafin nan da cikar kwana biyu?
Koda Jin wannan batu sai Boka RAKUL ya fashe da matsanancin kuka tamkar karamin Yaro, ya rinka tsalle yana faduwa Kasa kamar sabon mahaukaci, sai da su Sarki Zurmatu suka rirrikeshi sannan ya natsu.
Daga Nan ya ce yakai wannan Sarki kayi sani cewa muddin muka bari Koda rayuwar mutum 1 ta tsira daga cikin jaruman Gasar to Kuma ba zamu Haura wata guda a duniya ba zamu mutu.
Domin zamu rinka wayar gari ne sashen jikinmu Yana lalacewa Yana rubewa, a hankali- a hankali har tsutsotsi sun rinka fitowa a jikinmu suna cin Naman da ya zagwanye a jikinmu, da haka da haka mu rube gaba Daya kafin cikar kwanaki talatin, Kuma irin mutuwar da mukayi irinta gaba dayan mutanen birnin Nan zasuyi har kowa ya mutu.
Koda Jin wannan batu sai Sarki Zurmatu Waziri Mikilas suka kamu da tsananin tsoro, saboda yanda rayuwarsu ta kasance a tsakanin tsaka-mai-wuya.
Cikin tsananin damuwa kamar yayi kuka, Waziri Mikilas yace ya Sarkin Duniya, na rokeka akan muyi duk irin abinda zamu iya don rayuwarmu, Kasarmu da mulkinmu.
Cikin tsananin damuwa Sarki Zurmatu ya dubi Boka RAKUL ya ce yanzu menene mafita akan wannan Ala'mari?
Boka RAKUL yayi shiru daga bisani ya dubi Sarki Zurmatu ya ce, mafita guda Daya ce kacal.
Shi ne dole ne mubi bayan wadannan Aljanun da suka sace Sadauki MARGIM kafin su samu nasarar kaiwa BOKA GARGUS shi har ya warkar dashi.
Sarki Zurmatu ya Kara duban Boka RAKUL cikin damuwa yace, tayaya kake ganin zamu iya cimmasu kafin su Isa birnin SIN alhalin ka fada mana cewa duk duniya babu Aljanun da suka Kai su tsananin karfin gudu?
Sannan Kuma tayaya zamu iya samun nasarar kwato jarumi margim har mu hallakashi daga hannunsu?
Koda Jin wannan tambaya sai Boka RAKUL ya ce" hakane kamar yadda na fada maku cewa Aljanun da Boka GARGUS ya Aiko sukayi wannan aikin sun kasance masu tsananin karfin gudu tamkar kibiya, to kayi sani cewa har ila yau akwai wasu ALJANU na musamman wadanda suka kasance manyan IFIRITAI masu tsananin gudu tamkar na tauraruwa Mai wutsiya.
Su dai wadannan Aljanu guda dubu ne, Kuma dukkansu sun kasance manya-manya kamar Tsauni.
A tarihin rayuwarsu ba a taba samun aljanin da ya rigasu zuwa wurin da suka dosa ba, domin sau dubu saba'in suna lashe GASAR TSEREN GUDU da ake shiryawa a duk karshen shekara cikin fadar babban Sarkin Aljanu.
Saboda tsananin karfin gudunsu a cikin kwana guda kacal suna iya yawace duniya Kaf!
Wato su je karshen bangwayen duniya na bangaren gabas, Kudu,
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 2 Chapter of 12