aga karfin iskar Kai saran tana dukan bishiyoyin Dajin suna rangaji tamkar zasu zube Kasa.
Hakika DURZASU ya samu namijin horo na gaban kwatance ta yadda ko kallon siffar jikinsa kayi Kasan cewa dole ne ya kasance Sadauki uban sadaukai.
A cikin wannan lokacin gaba dayan jikinsa ya canza, jijiyoyin jikinsa sunyi burdin-burdin kamar igiyoyi ne aka makala a jikin nasa.
Gaba dayan kwanjinsa ya cika cif-cif tamkar duwatsu ne aka lillika.
Idan Yana tafiya bisa turba ana Jin Kasa na Amsawa tamkar tafiyar toron giwa.
Koda DURZASU yaga cewa ya samu karfi da kwarewar yaki fiye da daa, sosai.
Sai ya dauki takobinsa ya tunkari Dajin karshe Wanda daga shi sai tsuburin da Aljani GAMJAHUL FUTUL yake.
Sai da ya shafe wuni guda Yana tafiya sannan ya iso daji na bakwai.
A lokacin da ya riski Dajin dare ya soma yi, saboda haka had ya Yanke shawarar Kafa tantinsa a bakin Dajin inyaso idan gari ya waye sai ya shiga ciki, Amma sai wata zuciyar tace ai Bai kamata ace namiji kamarsa Yana shakkar shiga wani wuri a duniya da dare ba, saboda haka sai ya kunna Kai cikin Dajin.
Da shigarsa cikin Dajin sai yaga Dajin gaba dayanshi a haskeke yake da matukar haske Wanda ko allura ta fadi sai an ganta.
Haka Kuma sai ya ga Dajin a tsaftace yake babu abun kazanta a cikinsa ko guda daya.
Duk inda ya duba a cikin dajin sai dai ya ganshi Gwanin burgewa da ban sha'awa.
Haka Kuma ga koramu Nan suna gudana a cikin wannan daji masu dadi.
Ga 'yayan itatuwa nau'i-nau'i Nan birjik kamar ba a so.
Haka Kuma Dajin ba'a Jin sautin komai a cikin dajin, tun farkon shigowarsa Bai ji motsin komai ba, shiru kawai yakeji.
In Banda takun sawun kafarsa babu motsin komai.
Kuma hatta Kananan halittun kwaruka irinsu gyare da tsanya, da sauraye, babu kukansu a wannan daji.
Yana cikin tafiya cikin wannan daji, sai ya iso wani wuri da aka kawata da zallan lu'u-lu'u da Zinari Mai kyalkyali, sannan Kuma an gina wani matsaikaci Kuma kyakkyawan gida Wanda yafi gaban Ido ya iya kure kyan wannan gida.
Haka Kuma Baki ba zai iya misalta irin Jan hankalin da yake da shi ba.
Gaba dayan yanayin ginin gidan, irin gidan manyan sarakunan Aljanun duniya ne wadanda suka Amsa sunansu.
Gidan an jejjera Masa wasu fitilu masu dadin gani wadanda suke caccanza kala duk bayan rabin dakika.
Haka Kuma wani sauti Mai tsananin dadi da Jan hankali na tashi a gidan.
Koda DURZASU ya fara jiyo wannan sautin, sai hankalinsa ya karkata akan wannan gidan.
Ya ji a ransa cewa babu abinda yake sha'awa face shiga wannan gida domin ganin ma-mallakinsa da Kuma irin abubuwan da ke ciki.
Nan take ya tunkari kofar shiga wannan gida.
Da zuwansa sai ya iske kofar gidan a Bude Kuma har a sannan wannan zazzakan sautin na karuwa daga cikin gidan.
Koda shigarsa wannan gida, sai yaga ya tsinci Kansa a cikin wata tafekekiya Kuma Kasaitacciyar fada Mai tsananin girma da fadi.
Abinda yafi bashi mamaki da daure Masa Kai shi ne, daga nesa ana iya cewa yawan gidan bazai wuce daki guda ba.
Amma Kuma da ya shigo cikin gidan sai yaga fadin gidan yakai girman wani garin.
Domin ga dakunan Nan birjik wadanda adadinsu yakai dubu.
Daga cikin dakunan ne ya rinka jiyo sautin wannan kidan a cikin Daya daga cikin dakunan..
Kai tsaye ya tunkari wannan dakin.
Da zuwansa sai ya kunna Kai cikin dakin, shigarsa keda wuya sai yaci karo da wasu manyan-manyan gumaka rike da kayan kida iri a hannuwansu.
Babban abinda yafi bawa DURZASU mamaki shi ne, ganin yadda gumakan suke kada kayan kidan har sauti Mai dadi ke bazuwa a gaba dayan Dajin.
Nan take DURZASU ya tambayi Kansa a cikin ransa cewa tayaya akayi wadannan gumakan suke iya kada kayan kidan, alhalin basu kasance rayayyu ba?
Abinda Bai sani ba shi ne, duk wannan na daga cikin nau'ikan tsafi Kuma tuni ansan da zuwansa Kuma an tanadi abinda za'ayi Masa.
Shi dai wannan daji na bakwai ana kiransa da suna DARUL HUJUK.
Kuma babu wata halitta da ke cikin wannan daji face wani shedanin Aljani Wanda ya kasance Sarki ne daga cikin manyan sarakunan Aljanun duniya, Kuma ana Kiransa da suna BANGAHUL GURUS.
Shidai wannan Sarki ya kasance Mai tsananin karfin damtse na gaban kwatance, Kuma ya mallaki dubunnan rundunonin Dakarun aljanu masu tsananin naci da Jarumtaka ta ban Al'ajabi har guda Milyan uku.
Bugu da Kari Sarki BANGAHUL GURUS ya kasance Azzalumi Wanda ya fitini jinsin Aljanu gaba dayansu.
Saboda tsabar bakin zaluncinsa ne yasa gaba dayan bokayen Aljanu suka taru, sannan sukayi Amfani da alkaluman tsafinsu gaba daya suka yi wa Sarki BANGAHUL GURUS asirin halaka shi, Amma da suka ga bazasu samu nasarar hallaka shi ba, sai suka sake yi Masa asirin barin nahiyar da suke, domin tsira daga sharrinsa.
A wannan karon sun samu nasara, domin asirin da sukayi Masa ya kama shi.
Dare Daya yaji ya tsani nahiyar Aljanu, Kuma yaji babu inda yake sha'awar zama face a cikin daji shi kadai.
A bisa wannan dalili ne yasa ya tattara manyan dakuransa guda Milyan uku wadanda ya yarda da Jarumtakarsu, sannan sukayi kaura daga inda suke suka dawo wannan daji na DARUL HUJUK da zama.
Tun ranar da suka dawo wannan Dajin yasa aka kama gaba dayan dabbobin Dajin, da tsuntsaye da kwaruka da kowace irin halitta Dake rayuwa a cikin dajin.
Wannan dalilin ne yasa Koda za'a zagaye Dajin gaba Daya to ko sauro Daya ba za'a gani ba, ballantana wata Dabba Mai cutarwa.
Haka Kuma Sarki BANGAHUL GURUS ya kasance gawurtaccen matsafi Wanda ya shahara a harkar bokanci.
A bisa wannan dalili ne yasa ya sihirce gaba dayan Dajin DARUL HUJUK ta yadda ko tsuntsu Bai Isa ya keta ya cikin wannan Dajin ya wuce ba, batare da saninsa ba.
Bugu da Kari SARKI BANGAHUL GURUS ya tsafance sama da Aljanu Milyan Daya, duk sun zama bishiyoyi sannan ya rarrabasu izuwa sassan Dajin domin su rinka gadi.
A zahiri duk Wanda ya shigo dajin zai rinka ganinsu a matsayin bishiyoyi, Amma Kuma su suna ganin duk halittar da ta shigo, Kuma Umarnin Sarkin su kawai suke Jira domin rikidewa izuwa ainihin siffarsu su kashe abinda ya shigo dajin.
Tun tsawon shekaru Dari da arba'in da wannan Sarki da rundunarsa suka wanzu a wannan daji, Amma kawo i'yanxu babu halittar da ta taba ratsawa ciki ta wuce lafiya.
Komai hatsabibanci da Jarumtakar mutum indai ya shigo wannan dajin to sunansa gawa, domin ko duriyarsa ba'a Kara ji ballantana tarihi ya tuna da shi.
Tun lokacin da SADAUKI DURZASU ya shigo cikin wannan Dajin, Sarki BANGAHUL GURUS ke kallonsa a cikin tafin hannunsa ta hanyar sihiri.
Wannan dalilin ne yasa, ya shirya Masa tarko da wannan Kayataccen gida da Kuma sautin kida Mai dadin sauraro.
Lokacin da DURZASU ya tsinci Kansa a cikin wannan daki da gumaka ke Samar da kida Mai dadi, sai ya cika da tsananin mamaki.
Nan take yayi duba izuwa kan wani tebur Wanda aka ajiye abinci da abun sha da 'yayan itatuwa iri-iri.
Koda ganin haka, sai yaji tsananin kwadayin abincin ya kama shi.
Nan take ya tunkari inda teburin abincin yake, ba zato ba tsammani sai kawai yaga wani kyakkyawan Yaro Dan shekaru bakwai ya bayyana Tsulum a gabansa Yana murmushi.
Koda yayi arba da wannan kyakkyawan Yaro, sai yaji zuciyarsa ta buga da karfi.
Nan take yaji wannan Yaron ya burgeshi ainun.
Kawai sai ya Dora hannunsa da nufin tambayarsa labarin wannan gida.
Faruwar hakan keda wuya sai yaga Yaron Nan, ya kyalkyale da wata mahaukaciyar dariya mara dadin ji sannan ya juye izuwa wata mummunar siffa Mai matukar ban tsoron da ko a tarihi ba a taba Jin labarin irinta ba.
Koda fara wannan dariyar sai gaba dayan gumakan da ke cikin wannan dakin ruhi ya shiga jikinsu suka mimmike, sai gashi sun juye izuwa wasu murtuka-murtukan bakaken Aljanu masu mummunar siffa kowannensu na rike da zabga-zabgan takobi masu tsananin girma da kauri tamkar rassun Katuwar bishiya suka rirrike.
Faruwar hakan keda wuya, sai wannan Yaron ya dakawa wadannan Dakarun tsawa yace me ku ke Jira ne da shi?
Maza ku kama min shi da karfin tsiya.
Na rantse da darajar KARAGAR MULKINA sai na gana Masa azabobi guda dubu sannan na kaishi kurkuku na Dake karkashin Kasa.
Kafin Sarki BANGAHUL GURUS ya gama rufe bakinsa tuni wadannan Aljanun sun Afkawa SADAUKI DURZASU wadanda adadinsu ya Kai dubu.
Nan fa wuri ya yamutse, aka fara dauki ba dadi.
Sara da suka ya yawaita, karafkiyar takubba ya zama tamkar numfashi, duk Inda mutum ya duba sai dai ya rinka ganin giftawar takubba ana Kai Sara da su.
Hakika Sadauki DURZASU ya samu zafin nama ninkin na daa sau dubu, shiyasa yake iya kare hare-haren wadannan Aljanun.
Inba don haka ba, da tuni sun hallakashi a cikin dakika daya jal.
Domin a duk a cikin dakika guda gaba dayan aljanu dubun suna iya kawo Sara a lokaci guda.
Amma saboda tsananin jarumtaka, Sadauki DURZASU na iya kare dukkan saransu a cikin rabin dakika har ma ya mayar da martani.
A duk lokacin da takobin DURZASU ta hadu da ta wadannan Aljanun sai dai aga tsawa game da walkiya sun bayyana, har wani tartsatsin wuta ne ke tashi saboda tsananin azabar yaki..
A dai-dai wannan lokaci ne, na gaji ainun da rubutu.
Nake cewa mu hadu a GASAR JARUMTAKA part B don Jin cigaban wannan Kasaitacce Kuma Kayataccen labari ✍️♥️
Ina maku fatan Alkhairi ♥️♥️🥰**GASAR JARUMTAKA**
LITTAFI NA GOMA 10 ✍️♥️
PART B ✅
AUTHOR: NAJIBULLAH MUHAMMAD ✍️✍️
POSTING: Najibullah Muhammad 🥷🥷
Idan baku manta ba, a baya mun tsaya ne a inda SADAUKI DURZASU yake fafata kazamin yaki da Dakarun Sarki BANGAHUL GURUS wadanda adadinsu ya kai Milyan Daya.
Su dai wadannan Dakaru suna da matukar girma da tsawo, domin girman kowanne daga cikinsu ya ninka da DURZASU sau biyar.
Wannan dalilin ne yasa lokacin da sukayi Masa Kawanya suna Masa rubdugu ko hangoshi ba'ayi, domin sun lullube shi tamkar yadda kaza ke boye 'yayanta a jikinta.
In ba don Sadauki DURZASU ya kasance SADAUKIN GASKE ba Kuma Mai tsananin zafin nama da tuni sun dade da aika shi barzahu.
Lokacin da aka shafe dakika dari da arba'in ana fafata wannan kazamin yakin, sai ya zamana cewa ran wadannan Aljanun ya baci ainun.
Zuciyarsu ta harzuka saboda ganin yadda suka tarar wa mutum Daya kacal Amma sun Kasa hallakashi.
Bugu da Kari a zahiri suna ganin cewa sun ninka shi girma da karfi.
Domin Ido ba mudu bane Amma ya San kima.
Haka Kuma sun kasance jinsin Aljanu, shikuma bil'adama.
Nan take sukayi kururuwa a lokaci guda sannan suka daka tsalle sama suna masu daga Takubbansu da nufin tsire DURZASU.
Koda DURZASU ya fahimci nufinsu, sai ya Yi wata katantanwa a tsakanin kafafuwansu.
Cikin tsananin zafin nama juriya da bajinta ya rinka jujjuya takobinsa Yana laftawa kafufuwansu Sara suna gutsirewa.
Kafin wadannan Aljanun su samu nasarar caka Takubbansu a Kasa, kawai sai sukaji ana ta gutsirewa masu kafufuwa suna faduwa Kasa sumammu jini na Malala a Kasa Yana fantsama a sama.
A cikin dakika hamsin DURZASU ya samu nasarar guntile kafafuwan Aljanu dubu arba'in, sama da dubu Talatin daga cikinsu tuni sun zama gawarwaki, sauran kuwa suna Kasa male-male sun Kasa mikewa.
Koda Sarki BANGAHUL GURUS yaga haka sai ransa ya Baci, Nan take yasa hannun Hagu ya shafi bangon dakin.
Kafin kiftawar Ido gidan ya bace ya barsu a sarari, sai gashi sun wanzu a cikin surkukin daji Mai duhuwa.
Wurin ya zama tamkar wani gida Bai taba wanzuwa a wurin ba.
Faruwar hakan keda wuya sai yaga ragowar Aljanun Nan, sunyi hannu-hannu.
Ma'ana wannan ya rike hannun wancan, a haka suka rirrike hannun juna suna masu kewaye DURZASU.
Faruwar hakan keda sai dukkansu suka rikide izuwa wata murtukekiyar macijiya, wadda tayi wa DURZASU zobe da jelarta, sannan ta saddo da rafkeken kanta Kasa-kasa Mai kama da Katon Dutse.
Nan fa macijiyar Nan ta rinka fiddo harshe tana fesar da mugun bakin dafi.
Koda ganin wannan Ala'mari sai SADAUKI DURZASU yaji zuciyarsa ta buga da karfi.
Nan take ya fara tunanin mafita, domin yasan cewa Abu ne mawuyaci ya tsira da rayuwarsa a wannan karon.
Yana cikin wannan tunani ne ya lura da cewa, wannan macijiyar tana tsuke jelarta, tana so ta matse gam a jikinta yadda zata samu damar cinyeshi.
Koda ya fahimci nufinta, sai ya daka tsalle sama ya fado a saman jikinta.
Yana dirowa yaji jikinta da tsananin santsi, Yana Shirin sulalowa Kasa.
Cikin tsananin zafin nama ya daga falleliyar takobinsa iyakar karfinsa ya soka ta a jikin macijiyar.
Take Takobin ta lume, jini ya fara kwarara.
Nan take macijiyar ta kwarara wani uban ihu sakamkon tsananin zafi da zogin da taji, kafin DURZASU ya samu nasarar zare takobinsa a jikin macijiyar tuni ta kawo masa mugun duka da wannan rafkeken kan nata.
A lokacin DURZASU ya rike takobinsa da hannu biyu Sannan ya tattake macijiyar Yana ta kokarin jawo takobin.
Ba zato ba tsammani sai kawai yaji macijiyar Nan ta tafka Masa Katon kanta, Nan take yaji kamar wani murgujejen dutse ne ya fado Masa Saboda tsananin karfin dukan.
Sai da DURZASU yayi sama yaje ya gwaru da manya-manyan bishiyoyin Dajin guda saba'in sannan ya maƙale a cikin wasu sarkakakkun bishiyoyi, wadanda suka sassarke da junansu.
Idan Mutum yaga DURZASU a wannan wuri, sai ya kwana Yana mamakin ta yadda akayi har ya iya shiga wurin.
Domin saboda cunkushewar da bishiyoyin sukayi ko kwaro bazai iya shiga wurin ba.
Nan fa macijiyar Nan ta rinka hargowa tana doka kanta a jikin bishiyoyin Dajin suna ratattakewa su fadi Kasa tamkar an taka karmami.
Har a sannan jini na ta Malala daga jikin rauninta.
Shi kuwa DURZASU duk da kasancewarsa a Raye Amma sai aman jini yake ta famanyi saboda tsabar nauyi da karfin dukan macijiyar nan tayi Masa.
Kuma duk wannan bala'in har yanxu takobinsa na rike gam a hannunsa.
Sai da macijiyar nan ta baje gaba dayan bishiyoyin Dajin sannan ta samu nasarar kafar DURZASU da bakinta, ta daga shi sama Yana Lilo kamar gawa.
Koda DURZASU yaga macijiyar Nan ta wangame lafkeken bakinta da nufin ta sokashi ciki, sai ya takarkare cikin tsananin zafin nama ya juya ya lunawa idonta guda takobin.
Nan take tabokin ta lume a jikin idon, ji kake Cus ya fashe kamar an fasa Kwan jimina.
A dai-dai wannan lokacin ne, macijiyar ta Dora DURZASU akan harshenta ta cillashi a cikin bakinta, Amma duk da haka sai da ya fizgo takobinsa sannan ya wuce da ita izuwa cikin-cikin macijiyar.
Nan fa macijiyar ta haukace, ta kama tumuwa a Kasa tana birgima saboda tsananin bala'i da take Sha.
A wannan lokacin jinin macijiyar gaba Daya ya kusa karewa saboda yanda idonta guda da gangar jikinta suke bulbular da jini ba kaukautawa.
A duk lokacin da macijiyar ta buga kanta a Kasa, sai DURZASU yaji tamkar hakarkarinsa zasu karye, domin ji yake tamkar an rike Kafafunsa ne ana maka Gangar jikinsa a jikin bango.
Sai da DURZASU ya Suma sau Ashirin da biyar Yana farfadowa a cikin-cikin wannan Katuwar MACIJIYAR saboda bala'i.
A haka ya wanzu har tsawon dakika dari da arba'in, a sannan ne macijiyar jikinta ya lankwame ta fadi Kasa matacciya.
Faruwar hakan keda wuya sai jikin macijiyar ya rinka narkewa Yana komawa na ainihin bakaken Aljanun Nan.
A hankali gaba dayan sassan jikin macijiyar ya narke, sai ga Sadauki DURZASU a Kasa male-male cikin jini tamkar Wanda aka tsoma a Kogon jini.
Cikin tsananin karfin hali ya rinka bude idonsa a hankali, kawai sai yaga gaba dayan bakaken Aljanun nan sun zama gawa, babu dayansu da yayi saura a Raye.
A hankali Kuma sai gawarwakin suka rinka kamawa da wuta Kurmus tokarsu na tashi sama tabi iska.
A haka sai da gaba dayan Gangar jikin Aljanun suka kone kurmus sannan tokarsu ta bi iska.
Cikin karfin hali DURZASU ya mike zaune da kyar, sai yaga wadannan bishiyoyin da maciyar Nan ta ratattake duk sun juye izuwa wasu murguza-murguzan Aljanu na musamman, Amma dukkansu suna kwance a Kasa matattu.
Nan fa DURZASU ya cika da tsananin mamaki, Yana cikin haka ne yaga su ma wadannan gawarwakin sun kama da wuta sun kone kurmus.
A haka Sadauki DURZASU ya wanzu a cikin wannan daji Yana jinyar jikinsa har tsawon sa'a guda.
Sannan ya iya mikewa tsaye yaje bakin wata korama yayi wanka ya samu karfin jikinsa.
Ya rinka cizgo 'yayan itatuwa Yana ci.
Yana zaune tunanin abinda ya kamata yayi, kawai ba zato ba tsammani sai Tsulum yaga Sarki BANGAHUL GURUS ya bayyana a gabansa cikin mummunar shigar yaki tare da wasu guraye da layu murtuka-murtuka.
A wannan lokaci iya fuskar Sarki BANGAHUL GURUS kawai ake iya gani.
Fuskarsa a murtuke take ainun babu annuri ko kadan.
Cikin kakkausar murya Sarki BANGAHUL GURUS ya dubi DURZASU ya ce," Kai Yaro ka tabka babban kuskure da har ka ratso cikin fada ta, Kuma ka kashe min dukkan dakaruna da nake matukar ji da su.
A sakamkon wannan babban laifi da kayi min, na rantse da Karfin mulkina, sai na azabtar da Kai irin da azabar da ko a tarihi ba a taba yiwa wani mahaluki ita ba, sannan daga bisani na tsareka a cikin Kurkukun da duk duniya babu Mai iya fito da Kai, sai dai ka kare rayuwarka a can.
Cikin tsananin fusata DURZASU ya tari numfashin Sarki BANGAHUL GURUS Yana Mai daka Masa tsawa sannan ya ce," Lallai karyarka tasha karya ya Kai wannan raunanannen Sarki. Tayaya kake tunanin cewa zaka iya ganin bayana Kai kadai alhalin na Gagarin gaba dayan Dakarunka da kake matukar ji dasu?
To kayi sani cewa na rantse da burin zuciyata cewa Koda ire-irenka sun haura dubu, sai na yake su dukkansu Kuma nayi nasara.
Nan take ran Sarki BANGAHUL GURUS ya Baci ainun da Jin wannan martani da DURZASU yayi Masa, Nan take ya nuna DURZASU da takobinsa da hannun Hagu.
Kafin DURZASU yayi wani yunkuri tuni wasu sarkokin tsafi sunyi fitar burtu daga cikin takobin sun nufoshi da nufin kanannade shi.
Ai kuwa sarkokin na taba jikin DURZASU sai suka tsittsinke suka kama da wuta.
Koda Sarki BANGAHUL GURUS yaga haka sai yace, tunda kasha jinin jikin macijiyar Nan tsafina ba zai iya tasiri a jikinka ba.
To Amma duk da haka ka shirya ga Maza Nan bisa kanka.
Yana gama fadin hakan sai ya mayar da hular karfensa, sannan ya rike takobinsa da hannun dama, sai yayi tsafi da hannun hadu wata murtukekiyar garkuwa ta wanzu a hannunsa.
Kafin DURZASU yayi wani yunkuri tuni Sarki BANGAHUL GURUS ya falfalo da azababben gudu tamkar iska ya zo gareshi, da zuwansa yasa garkuwar hannunsa ya banke shi.
Saboda karfin dukan sai da DURZASU yaji kamar an janye shi da Kugiya yayi sama ya fado Kasa ya mulmula.
Cikin zafin nama ya Mike Yana Mai rike takobinsa dakyau, sannan Shima ya falfala da gudu izuwan kan Sarki BANGAHUL GURUS.
Suna haduwa suka kacame da sabon masifaffen yaki mai tsananin ban tsoro Wanda ko a tarihi ba'a taba Jin irinsa ba.
A duk lokacin da DURZASU ya kawowa Sarki BANGAHUL GURUS Sara da takobinsa, sai dai yaga ya bace bat ya bayyana a bayansa, Amma kafin ya kawo harin da zai cutar da DURZASU tuni har ya juyo sunci gaba da fafatawa.
Tabbas tsananin zafin naman DURZASU ya wuce misali, wannan yasa har yanxu Sarkin Aljanu BANGAHUL GURUS ya Kasa cutar da shi.
Amma duk da haka lokuta dayawa Yana samun nasarar naushinsa, saboda duk irin harin da ya kawowa DURZASU sai dai yaga ya kaucewa harin nasa, Kuma mayar da martani.
Shi kanshi BANGAHUL GURUS yayi matukar mamakin ganin irin gagarumar Jarumtakar da DURZASU keda ita.
Domin Bai taba haduwa da hatsabibin Sadauki kamarsa ba.
Inba don yana yawan bacewa ba, a yayinda suke fafata wannan Yakin da tuni DURZASU ya hallakashi.
Sai da aka shafe sa'a guda ana wannan dauki ba dadi Amma dayansu Bai samu nasarar komai ba.
Koda ganin haka, sai Sarki BANGAHUL GURUS yayi turjiya ya tsaya, sannan yayi jifa da takobinsa ya fuskanci DURZASU Yana Mai cewa, tunda mun kasa cutar da junanmu da takobi ai sai mu gwada 'yar Kashi ko?
Koda Jin wannan batu sai Shima DURZASU yayi karfin hali ya jefar da takobinsa, sannan ya fuskanci Sarki BANGAHUL GURUS ya ce muje zuwa ni da Kai a San gwani.
Wannan shi ne babban kuskuren da Sadauki DURZASU yayi a rayuwarsa domin Sarki BANGAHUL GURUS ya kasance Mai tsananin karfin damtse.
Wanda masana sun tabbatar da cewa duk duniya babu wani Sadauki da ya kaishi tsananin karfin damtse da Kuma iya fadan hannu.
Domin komai yawan ayarin mutane da Aljanu ba zasu iya Koda lakutar jikinsa ba, muddin da hannu za'ayi.
Bayan anyi kallon-kallo tsakanin su, sai DURZASU ya falfala da mugun gudu izuwa kan Sarki BANGAHUL GURUS.
Da zuwansa yayi wani tsalle da nufin yasa Kafa ya banke shi.
Kash! Hakika masu iya magana sunyi gaskiya da suka ce ta Yaro kyau take Amma bata qarko!
Cikin tsananin zafin nama kamar walkiya Sarki BANGAHUL GURUS ya cafki kafar DURZASU ya rinka hajijiya dashi a sama Yana kwala da shi da Kasa.
Sai da yayi Masa Kaye Dari uku da arba'in sannan ya jefar dashi kasa a sume.
A wannan lokacin tuni numfashin DURZASU na niyyar daukewa, domin dakyar yake iya shakar iska.
Koda Aljani BANGAHUL GURUS yaga ya samu nasara akan DURZASU sai murna ta kama shi.
Nan take ya cire sulken yakin da ke jikinsa sannan ya rinka kururuwa mai tsananin karfi Wanda amsa-kuwwarta ta cika Dajin gaba daya.
Nan fa ya shiga dukan kirjinsa Yana yiwa Kansa kirari da kambama Kansa, yana Mai cewa.
Sai ni sadaukin jarumi Mai dakawa Maza gumba a hannu.
Ni ne Sarkin sarakuna, Wanda bani da tamka.
Ina ki gudu ga sa Maza gudu?
Ni kadai ke korar Maza komai yawansu.
Ni kadai ke ganin bayan runduna komai yawanta.
Ni kadai ne me nasara Mai ganin bayan makiya..
Haka dai Sarki BANGAHUL GURUS yaci gaba da yiwa Kansa kirari Yana juyi da ihu, har tsawon dakika dari da tamanin.
A wannan lokaci tuni Sadauki DURZASU ya farfado daga dogon suman da yayi, Amma sai yayi lamo ya nuna kamar bai farfado ba, Jira kawai yake yaji ta inda za'a sake kawo masa farmaki.
Shi kuwa Sarki BANGAHUL GURUS Koda ya gama yiwa Kansa kirari, sai ya tunkaro inda DURZASU ke kwance magashiyan kamar gawa, Yana Mai cewa tabbas yanzun Nan zan cika alkawarin da na dauka akanka na cewa zan Kai ka kurkukuna Wanda zansa ayita gana maka azaba Mai radadi daga Nan har karshen rayuwarka.
Koda isowarsa sai ya Mika hannunsa da nufin ya cafko wuyan DURZASU.
Ba zato ba tsammani sai kawai yaji DURZASU ya shammace shi ya gabza Masa wawan naushi a Fuska da dukkan karfinsa.
Saboda karfin naushin sai da jini yayi tsartuwa daga bakinsa da hancinsa.
Nan fa Sarki BANGAHUL GURUS yayi baya taga-taga kamar zai fadi Yana layi, saboda tsananin wahala har taurarin wuya ya rinka gani.
Yana cikin wannan magagi ne, SADAUKI DURZASU ya Suri takobinsa Yana Mai daka tsalle sama tamkar an cillashi daga cikin baka, Yana zuwa ya dirka akan kafadunsa ai kuwa kafin yayi wani yunkuri tuni ya soka Masa wannan sharbebiyar takobin a cikin bakinsa.
Sai gashi takobin ta Burma kan burum, ta faso ta keya.
Nan fa jini da kwanya suka rinka tsiri a sama suna Malala a Kasa.
Kafin cikar dakika hamsin ya gama shure-shurensa ya sulale Kasa matacce.
Koda ganin haka sai SADAUKI DURZASU ya sa hannu ya zaro takobinsa daga cikin bakin Sarki BANGAHUL GURUS sannan yaje wannan koramar ya wanke takobin Kuma ya sake yin wanka.
A wannan Dajin na DARUL HUJUK ya zauna har tsawon kwanaki bakwai sannan yayi Shirin cigaba da tafiyarsa, saboda a yanzu yaji raunikan jikinsa sun warke, Kuma karfin jikinsa ya dawo.
A cikin kwana na bakwan ne ya bar wannan Dajin ya tunkari Tsibirin mutuwa inda Aljani GAMJAHUL FUTUL yake.
Sai da ya shafe sa'a biyar Yana tafiya sannan ya iso wannan Tsibiri.
Tun farkon isowarsa wannan Tsibiri, ya rinka cin karo da abubuwan ban tsoro a kame Basu motsi kamar gumaka.
Haka ya rinka keta su cikin dar-dar din a kowane lokaci zasu iya afko Masa.
Amma har yayi nisa Bai ga alamun cutarwa a garesu ba.
Haka ya rinka tafiya har ya iso inda wata matattakala take, wadda za'a tattaka a hau Saman Tsibirin.
Nan take batare da fargabar komai ba, ya rinka Hawa matattakalar Nan Yana tafiya izuwa Saman Tsibirin har tsawon sa'a guda sannan ya iso karshensa.
Koda yazo karshen Tsibirin sai yaga wata Yana Mai matukar kauri ta lullube wajen, Kuma ba a iya hango abinda ke Saman Tsibirin dole sai an yaye yanar.
Nan take yasa hannu da nufin yaye yanar.
Ba zato ba tsammani sai kawai yaji an gabza Masa wawan naushi a Fuska, saboda karfin naushin sai da hakoransa biyu suka fice fit daga cikin bakinsa.
Faruwar hakan keda wuya sai ya sulalo Kasa sumamme, ya fada cikin wani karamin tafki dake Kasan Tsibirin.
Bayan kamar Dakika sittin ya farfado sannan ya fito daga dogon suman da yayi.
Har a sannan jini na yoyo a cikin bakinsa.
Koda ya shafa bakinsa yaga jini, sai ransa
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 11 Chapter of 12