Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
10 / 12
Fuska. Nan take DURZASU ya farfado daga dogon suman da yayi. Koda yayi arba da wannan Dan mitsitsin Aljani Mai rafkeken Kai, sai jawo takobinsa Yana Mai cewa wanene Kai? Cikin girmamawa Aljanin ya risina ya ce, " ya shugabana ni sunana SAMFADU, Kuma na kasance bawa ne a gareka tun farkon fara wannan tafiyar taka. Aljanin yaci gaba da cewa, ya shugabana idan baka manta ba a lokacin da zaka baro birnin BALLUS shugabana Boka FADDA'UL ZULUK ya baka laya wadda zaka makala a wuyanka, domin ta rinka nuna maka hanya a yayin tafiyarka. To kayi sani ni ne a cikin wannan laya, domin dalilin dayasa shugabana ya dorani akan wannan aikin na yi maka jagoranci a cikin wannan tafiya taka shi ne, saboda duk duniya babu wani Aljani da ya San hanyar da za'a iya zuwa Tsaunin da ALJANI GAMJAHUL FUTUL yake face ni. Kuma babu Wanda yasan irin bala'o'in dake Kan hanya da Kuma yadda za'ayi maganinsu sai ni. A bisa wannan dalili ne shugabana ya dora ni akan wannan aiki. Cikin tsananin mamaki, SADAUKI DURZASU ya dubi Aljani SAMFADU yace, " to menene dalilin dayasa kayi sauri ka dauko ni daga wancan Dajin ka kawo ni Nan? Kuma meyasa tun da muka fara wannan tafiyar baka bayyana gareni ba sai yanxu? Kuma meyasa duk irin halin da zan shiga a kokarin fafatawa da halittun cikin Dazuzzukan da muka wuce, baka fitowa ka kawo min dauki? Koda Jin wannan batu, sai Aljani SAMFADU ya Kara risinawa a karo na biyu, sannan ya ce ka gafarceni ya shugabana. Kayi sani cewa na dauko ka daga wancan Dajin ne, saboda sanin cewa a dokar Dajin shi ne duk lokacin da aka kashe dabbobin Dake rayuwa Saman Dajin da tazarar dakika arba'in, to take Kasar Dajin take kama girgiza tana ruftawa, a cikin dakiku kadan dajin yake dulmiyewa cikin karkashin Kasa tamkar bai taba wanzuwa ba, idan kuwa hakan ta faru to komai dake cikin ya hallaka kenan har abada ba za'a sake Jin duriyarsu ba. Amsar tambayarka ta biyu ita ce, dalilin dayasa ban taba bayyana a gareka ba, tunda muka fara wannan tafiyar shi ne, shugabana Boka FADDA'UL ZULUK ya gargadeni akan cewa lallai kada na sake na bayyana kaina gareka har sai naga ka shiga hadarin da ka Kasa ceton kanka, Kuma muddin ban taimakeka ba to zaka hallaka. Saboda haka a yanzu ne kadai naga ka shiga halin da baka iya ceton kanka, Kuma kana gab da hallaka shiyasa na bayyana kaina gareka. Amsar tambayarka ta uku kuwa ita ce, dalilin dayasa bana iya kawo maka dauki bisa duk irin bala'in da kake fafatawa da shi shine, saboda duk halittun da kake fafatawa da su a cikin Dazuzzukan da kake wucewa sunfi karfina nesa ba kusa ba. Domin da zarar na futo waje da niyyar yakarsu zasuyi min kwaf daya na fadi Kasa matacce. Idan kuwa haka ta faru to kaima mutuwa zakayi, domin akwai wurin da dole ko ka samu nasara akan bala'in dake cikin Dajin, to kana cikin mayunwacin hali tsakanin rayuwa da mutuwa Wanda indai babu Wanda zai taimakeka da wuri to mutuwa zakayi. Saboda haka ya shugabana na Ceci rayuwarka karo na farko, Kuma daga yanxu ba zaka sake ganina ba sai Nan gaba idan irin haka ta sake faruwa. Gama fadin hakan keda wuya sai akaga ALJANI SAMFADU ya rikide ya zama wani bakin hayaki, sannan ya shige a cikin layar da ke daure a wuyan DURZASU, Nan take hayakin ya bace tamkar Bai taba wanzuwa ba. Cikin tsananin karfin hali SADAUKI DURZASU ya mike tsaye Yana tafiya dakyar yaje inda ruwan koramar Nan ke gudana, sannan ya duka yasha ya koshi. Nan take ya fiddo wani garin magani dake maƙale a jikinsa ya barbada wa raunikan jikinsa Dake zubar da jini. Faruwar hakan keda wuya sai duk duka kame Kam, suka dena zubo da jinin. A hankali ya rinka tafiya Yana tsinko 'yayan itatuwa Yana ci har ya koshi. Haka ya kasance a wannan wuri har tsawon kwanaki bakwai, a Wannan raunikan jikinsa sun warke, haka Kuma karfin jikinsa ya dawo dari bisa dari. A cikin kwana na bakwan ne ya harhada nasa'inasa yayi gaba izuwa daji na biyar..... ME ZAI FARU A CIKIN WANNAN DAJI NA BIYAR? SHIN SADAUKI DURZASU YANA IYA KETARE HADARIN DAKE CIKIN DAJI NA BIYAR DA SAURAN DAZUZZUKAN HAR YA ISA TSAUNIN DA ALJANI GAMJAHUL FUTUL YAKE? INA LABARIN SU SARKI GURBASU WANDA KE KWANCE AKAN RASHIN LAFIYA? A WANE HALI YARIMA ZULDARI YAKE, KUMA ME YAKE SHIRYAWA? YA LABARIN SADAUKI USAMA WANDA YA AURI 'YAR SARKI ZURMATU YA TAFI DA ITA KASAR SU TA NURUL HAYAT? A WANE HALI SARKI FALWAN YAKE, WANDA YA KARBI MUSULUNCI BAYAN AN KAMMALA GASAR JARUMTAKA? DOMIN sanin amsashin wadannan tambayoyi sai mu hadu a GASAR JARUMTAKA na tara don Jin yadda ta kaya..**GASAR JARUMTAKA** LITTAFI NA TARA 9 PART A ♥️✍️ AUTHOR: NAJIBULLAH MUHAMMAD ✍️✍️ POSTING Najibullah Muhammad 🥷🥷 Whatsapp Num.. 08112778656 Lokacin da SADAUKI DURZASU ya kunna Kai izuwa daji na biyar, sai ya rinka tafiya cikin Sanda a hankali Kuma ya Kasa kunnuwansa don Jin sautin da ke fitowa cikin Dajin. Dama tun farkon shigowarsa wannan Dajin yasha jinin jikinsa, domin shirun da ke cikin wannan Dajin tayi yawa. Hatta iska dake kada bishiyoyin Dajin suna rangaji, sunyi tsaye cak wuri guda iskar ta dena kada su. Haka Kuma ruwan koramu da yake gudana a cikin dajin ya tsaya cak wuri guda. Kai hatta sautin Kwari da sauran dabbobin Dajin babu, domin komai na cikin Dajin ya tsaya cak ga barin yin motsi. Babu sautin da Kunnuwa ke ji, face sautin takun sawun kafafun SADAUKI DURZASU. Bayan fara tafiyarsa ne da tsawon dakika dari da arba'in ya fara ganin wani hayaki Mai tsananin yawa ya turnuke tsakiyar Dajin. Hayakin sai Kara yawaita yake, Yana bulbulowa tamkar an Kona danyun itatuwa da tayoyi. Koda ganin wannan Ala'mari sai ya zare takobinsa a hankali, yaci gaba da tafiya a natse. Koda ya iso ainihin inda hayakin ke fitowa, ba zata ba tsammani sai kawai yaji wani irin mugun gurnani Mai tsananin Kara da razanarwa ya fito ya Doki kunnuwansa. Saboda tsananin razana bai San sa'adda ya saki takobinsa ta fadi Kasa ba, ya kama waige-waigen ko'ina domin gano inda wannan gurnani yake fitowa. Yana cikin wannan Hali ne, yaji an sure shi da Dan yatsa guda anyi sama dashi. Sai gashi DURZASU Yana Lilo a Saman Dan yatsan wannan halitta. Ita dai wannan halitta ba wata bace face, wani SHIRGEGEN DODO Mai mummunar siffa. Bugu da Kari Yana da tsananin girman da ya wuce misali. Duk Wanda Bai San da wannan dodo ba, idan ya hango shi daga nesa sai yayi zaton cewa wani Katon daji ne Mai shuke-shuke iri-iri saboda yanda jikin dodon ya kasance launi daban-daban. Fuskar dodon a yamutse take, tamkar fuskar gwaggwan birin da ya shekara dubu a duniya. Haka Kuma jikinsa a murde yake, tamkar jijiyoyin bishiya ne aka jejjera. Kwanjinsa sunyi burdin-burdin kamar duwatsu ne aka cuccura a ciki. Kan dodon rankwalele ne, tamkar na Katon Dutse, sannan a Saman Kansa babu gashi ko guda Daya, ya kasance tankwal tamkar zabira aka sa aka aske. Yana da kwala-kwalan idanuwa, Kuma jajaye tamkar lokacin da Rana ta zo faduwa. Kai komai dai dakewar zuciyar mutum Idan yaga irin yadda mummunar dodon nan take, dole ne ya tsorata ainun. Wani ma yana iya zaucewa Nan take ya haukace, ko ma ya rasa rayuwarsa gaba Daya. Lokacin da wannan dodo ya wannan dodo ya dauko DURZASU da Dan yatsa guda, sai ya saita shi dai-dai fuskarsa, sannan ya kura Masa idanu Yana mamakin irin kankantarsa. Shi kuwa DURZASU har a wannan lokacin zuciyarsa a razane take, Amma Koda ya tuna cewa shifa jarumi ne na gaban kwantace Wanda babu kamarsa a duk nahiyarsu. Kuma ya tuna cewa ai abun kunya ne, aga jarumi kamarsa ya tsorata har ya Kasa fafatawa da wata halitta Dake bayan Kasa. Kuma ya tuna a ransa cewa idan ma Bai yaki dodon nan ba, to babu makawa sai ya rasa rayuwarsa domin tun kafin aje ko'ina tsoron dake zuciyarsa zai iya hallaka shi. Gama wannan tunani keda wuya sai yaji zuciyarsa ta kekashe ga barin tsoro, Nan take yaji wani irin kwarin gwiwar tunkarar wannan dodo. Shi kuwa wannan Katon dodo, Koda ya gama nazarin irin kankantar jarumi DURZASU, sai yayi nufin yayi loma guda dashi ya cinye duk da kasancewar kantantarsa ta fiye yawa, Koda ya cinye shi ba zaiji komai ba. To Amma ganinsa da yayi yasa mugun kwadayinsa ya tashi, saboda idan ya hakura da cinye shi, sai yayi shekaru goma yana dalalar da yawun kwadayin Naman bil'adama. Shi dai wannan Dodo a Kalla yakai shekara Dari biyar da saba'in da bakwai a Wannan daji. Kuma tunda ya wanzu daji yake tare Aljanu da mutane Yana kashe su Yana cinyewa. Tun tsawon wadannan shekaru, har yau ba a taba samun Wanda ya iya wucewa ta cikin wannan daji batare da sunyi arba da wannan dodo ba. A tarihin wannan wannan dodo komai yawan ayarin mutane ko fatake, da zarar sun biyo ta wannan Dajin indai sunyi arba, to sunansu gawa. Hakika wannan dodo ya cika abun tsoro Kuma SADAUKI na gaske, domin Koda adadin Dakaru ya Kai dubu, hannu Daya kacal yake mikawa ya cafko su ya watsa bakinsa ya hadiye, tamkar yadda mutum ke jefa Aya ko gyada a cikin bakinsa ya taune. A iya rayuwar wannan dodo a cikin wannan daji ya kashe mutane da Aljanu bila'adadin Wanda ba a San iyakarsu ba, domin a Kalla sun haura Milyan uku. A bisa wannan dalili ne yasa gaba dayan siffar wannan dodo ta juye izuwa tsantsar rashin Imani, ta yadda zai iya kashe milyoyin rayuka batare da digon tausayi ya darsu a zuciyarsa ba. A Ka'idar wannan dodo idan yaji yunwa, yakan tattara jinsin ALJANU dubu dari da hamsin, ya cinye sannan yake koshi. Idan kuwa yaji kishirwa to akwai wata Katuwar teku da wutsiyarta ke makwabtaka Dajin. Can yake zuwa ya Kafa Kansa ya kwankwada iyakar ransa har sai ya koshi. A halin yanxu ya kusa Karar da ruwan tekun saboda tsabar Shan da yake Masa. Bayan dodon nan ya Yanke shawarar cinye DURZASU Nan take ya wangame wawakeken bakinsa Mai kama tafka-tafkan Tsaunika guda biyu, da nufin jefa DURZASU cikin bakinsa. Cikin tsananin zafin nama DURZASU ya daka wawan tsalle sama daga Kan Dan yasan dodon nan, ya surmuyo Kasa luu, sai da yayi tafiyar dakika dari biyu da tamanin saboda tsananin Nisan Dake tsakaninsa da Kasa, sannan ya fado bisa turba. Babban abun mamakin shi ne, tamkar akan sifirin ya fado. Kamar walkiya sai kawai aka ga ya Suri takobinsa ya sake daka tsalle sama, sannan ya hau Saman tafin hannun dodon. Nan fa ya rinka falfala azababben gudu na gaban kwantace tamkar ya tashi sama. Koda dodon nan yaga DURZASU ya tattake iyakar karfinsa Yana gudu a Saman tafin hannunsa sai ya fusata. Nan take ya cillashi sama da nufin ya fada cikin bakinsa ya taune. Cikin tsananin zafin nama DURZASU ya soka takobinsa a cikin dasashin hakorin wannan dodo na sama, take Takobin ta lume. Jini ya kama tsartuwa da Malala, Yana fantsama a sama. Ai kuwa Yana finciko takobin, sai gashi hakorin dodon guda ya fice fit daga cikin bakin. Nan fa jini ya rinka shatata Yana tsiri a sama. Cikin dimaucewa dodon nan ya takarkare yana kururuwa tare da ihu Mai tsananin razanarwa. Nan take ya rinka Kai duka da tafka-tafkan hannuwansa ya ko'ina domin ya mako DURZASU. Ana cikin hakane aka samu akasin lokacin da dodon ya kawo wawan mangari ne da lafcecen hannunsa shikuma SADAUKI DURZASU yayi tsalle da nufin dirowa Kasa, sai akayi akasin hannun dodon ya mangare DURZASU. Saboda karfin dukan sai da DURZASU yayi sama tamkar an cillashi daga cikin baka, har sai da ya bace aka dena hangoshi. A wannan lokacin iskar sararin samaniya ta sumar da DURZASU, Kuma tuni yabar yankin wannan Dajin, har ya fara shigowa yankin da Tekun Nan take, inda wannan dodo ke zuwa Yana Shan ruwa. Koda yazo dai-dai Nan wajen, sai ya fara juyowa Kasa. Ya taho luu tamkar gawa, sai da yayi tafiyar sa'a guda Yana sulalowa Kasa sannan ya fado tsakiyar tekun Nan. Abinka da Wanda ya Suma, Yana fadowa sai ya nutse a karkashin teku. Sai da yayi tafiyar dakika arba'in Yana nutsewa a karkashin ruwa, sannan sai ga wani SHIRGEGEN KIFI ya wangame tafkeken bakinsa Ya dana tarkon Kananan kifaye Yana Jira su afka cikin bakin ya cinyesu. Nan da Nan Kifin Nan ya hango DURZASU ya biyowa ta wajen da yake Yana Shirin Kara lumewa Kasa. Cikin tsananin zafin nama Kifin ya ruga ya riski DURZASU sannan yayi loma guda dashi ya rufe bakinsa yaci gaba da sha'anin gabansa.... A dai-dai nan na gaji da typing.. Sai mu hadu a GASAR JARUMTAKA part B don Jin cigaban wannan Kasaitacce Kuma Kayataccen labari Mai dadi da debe kewa.. Najibullah Muhammad ✍️✍️ Ina maku fatan Alkhairi ♥️❤️**GASAR JARUMTAKA** LITTAFI NA TARA 9 PART B ✍️💯 AUTHOR: NAJIBULLAH MUHAMMAD ✍️✍️ POSTING: Najibullah Muhammad 🥷🥷 Idan baku manta ba a baya mun tsaya ne a inda SADAUKI DURZASU ya fada cikin Katon tekun nan Wanda har kifi ya hadiye shi. Haka dai DURZASU ya wanzu a cikin-cikin wannan kifi har tsawon sa'a guda sannan ya farfado daga dogon suman da yayi. Koda farkawarsa sai ya tsinci Kansa a cikin wani dan karamin KOGI domin iya hangensa ruwa ne. Abinda Bai sani ba shi ne, a cikin-cikin wannan kifin yake. Tsananin girman Kifin ne yasa har yake ganin ruwan cikin Kifin kamar KOGI. Nan fa DURZASU ya fara iyo a cikin wannan ruwan domin ya samu ya Isa karshensa. Sai da yayi tafiyar dakika dari da tamanin sannan ya iso karshen ruwan. Da zuwansa sai yaga Ashe babu kofar fita. Nan fa ya tsaya yana tunanin mafita. Domin har yanzu Bai Gane cewa a cikin-cikin kifi yake ba. Bayan wani dan lokaci sai dabara ta fado Masa. Kawai sai ya laluba damararsa ta yaki, yaji wadansu kananun wukake masu tsananin Kaifi da tsini guda biyu. Ya zaro su, ya fara cakawa a jikin Kifin Nan. Cikin tsananin dimaucewa Kifin ya fara wutsil-wutsil a cikin ruwa saboda tsananin zafi da zogi da yake ji. Shi kuwa DURZASU ji yayi tamkar KOGIN na Shirin birkicewa Kasa da shi, domin ji yayi gaba dayan ya kama tambal-tambal kamar zai rufta a karkashin Kasa. Amma duk da haka Bai dena caka wadannan wukaken a jikin Kifin ba. Nan fa Kifin ya haukace, ya rinka ninkaya a cikin ruwa. Yayi gabas yayi yamma, yayi nutso ya taso sama Amma har yanxu ya Kasa lalata abinda ke yakusarsa a cikin cikinsa. Kai Koda Kifin Nan yaji azabar da yake Sha tayi yawa. Sai ya ruga izuwa bakin gabar teku, ya takarkare iyakar karfinsa ya amayo duk abinda ke cikinsa, sai gashi DURZASU ya biyo kananun kifaye da ruwan da yake gani a matsayin KOGI sun fado bakin gabar teku. Nan take Kifin ya juya ya koma cikin teku. Shi kuwa DURZASU sai da ya shafe dakika arba'in a bakin tekun nan, iskar sararin duniya ta ratsa shi sosai, hankalinshi ya dawo jikinshi. Sai a sannan ne ya fahimci duk abinda ya faru da shi. Koda yaga karfin jikinsa ya dawo sosai, sai ya tsaya yana tunanin hanyar da ya kamata yabi domin cigaba da tafiyarsa. Fara hakan keda wuya sai yaji wannan 'yar mitsitsiyar layar dake sagale a wuyansa ta fisgeshi izuwa bangaren yamma. Nan take yaci gaba da tafiya cikin sauri-sauri gudu-gudu. Bai gushe ba yana wannan tafiya har tsawon rabin sa'a sannan ya shigo Daji na shida. Da shigarsa cikin wannan daji sai ya rinka ganin yadda iska ke girgiza gaba dayan bishiyoyin Dajin. Haka Kuma ya rinka Jin wata irin Kara mara dadin ji, Amsa kuwwar Karar ta cika Dajin gaba daya tamkar ana buga Katon Dutse akan mulmulallen karfe. Sai da DURZASU yayi tafiyar dakika dari da arba'in a cikin wannan daji Yana keta bishiyoyi da kwazazzabo da koramai Amma Bai ga komai ba, sai dai wannan iske da Kuma Kara da ke gauraye Dajin. Koda yazo dai-dai wani wuri a cikin dajin, indai yafi ko'ina sarkakiya. Sai kawai ya hango daga nesa Kasar wurin ta kama girgiza tana tsattsagewa. Ba zato ba tsammani sai yaga wani murgujejen Abu ya keto da gudu a cikin karkashin Kasa Yana kifar da bishiyoyi suna fadawa cikin Rami. Duk inda halittar nan ta wuce sai dai aga Kasar wurin ta Yanke ta fada cikin wawaken rami. Sai da halittar da kayar da bishiyoyi dari biyu da arba'in sannan tayi fitar burtu daga cikin ramin ta dirko Kasa. Koda SADAUKI DURZASU yayi arba da wannan halitta sai ya razana ainun, zuciyarsa ta buga da karfi yaji kamar ya juya da baya ya gudu Amma sai ya kanne dai ya tsaya. Ita dai wannan halitta, tana da kawuna bakwai. Kuma kowane Kai daga jikinta wuyansa daban, saboda haka tana iya Sarrafa kowane Kai daga cikin bakwan, tamkar yadda mutum kan Sarrafa hannuwansa. Bugu da Kari halittar na da idanuwa dubu uku a ko'ina a jikinta. A bisa wannan dalili ne komai kankantar Bai Isa ya kawo Mata farmaki ba, batare da ganshi ba. Halittar tana da zako-zakon faratan hannu da kafa masu matukar Kaifi da tsini wadanda duk abinda aka caka mawa, take yake ratattakewa ya lalace tamkar wutace ya cinye shi. Wannan dalili ne yasa halittar take Amfani da hannuwanta da kafafuwanta wajen kwakule Kasa ta shige karkashinta har ma tayi doguwar tafiya a karkashin Kasar. Haka Kuma wannan halittar na iya tashi sama kamar tsuntsuwa Mai fuka-fukai tayi doguwar tafiya batare da ta fado Kasa ba. Lokacin da DURZASU ya gama nazarin wannan halitta, sai ya rike takobinsa dakyau Yana nazarin irin dabarar da ya kamata ya bullo mata domin ya samu nasara. Yana cikin wannan tunani ne kawai yaga wannan mummunar halittar ta dako wawan tsalle sama ta nufo shi, da nufin ta cafke shi ta cinye. Cikin tsananin zafin nama ya daka wani wawan tsalle ya haye can saman wata Katuwar bishiya. Koda halittar tazo ta bangaji bishiyar sai gashi bishiyar ta tunbuko har jijiyoyin ta sun rikito Kasa luu. Suna durowa Kasa suka kacama da sabon masifaffen yaki mai tsananin ban tsoro Wanda a kowane lokaci lahira na iya yin Bako. Shi dai SADAUKI DURZASU ya zage dantse iyakar karfinsa wajen kaiwa halittar mugun Sara da takobinsa cikin tsananin zafin nama. Amma abun mamaki ita halittar Dan yatsanta guda daya ta Sanya ta rinka Amfani da farcen hannun tana kare saran Kuma tana mayar da martani. A duk lokacin da farcen wannan halittar ya hadu da takobin DURZASU sai dai Kaji wata Kara Kal! Tamkar ana buga Dutse da gudumar karfe har tartsatsin wuta ne ke tashi sama. Sai da suka shafe dakika dari da tamanin suna artabu Amma dayansu Bai samu nasarar komai ba. A wannan lokacin DURZASU yayi iyakar kokarinsa don ganin ya gano Lagon wannan halittar Amma Abu ya faskara gashi har ya fara gajiya. Ana cikin hakane wannan halittar ta sauko da rafkeken kanta guda Kasa, sannan ta makawa DURZASU shi a kirji. Saboda karfin dukan sai da yaji tamkar Katon Dutse ne ya fado Masa. Ai kuwa Nan take yayi baya luu tamkar an janye shi da Kugiya ya fado Kasa a sume, sai gashi bakinsa da hancinsa sai zubar da jini suke. Koda wannan halittar taga haka sai ta dako tsalle sama ta diro a gaban DURZASU, da zuwanta sai ta 'yan yatsunta guda biyu ta cafko gashin Kansa. Sannan ta jawo shi sama ta nufin bakinsa da shi. Koda tazo dashi dai-dai bakinta, sai ta wangame Daya daga cikin Katon bakinta da nufin ta jefashi ta ciki, har ta fara zura shi a ciki. Kwatsam sai ya Farka daga dogon suman da yayi, Koda ganin abinda ke Shirin faruwa sai ya daga falleliyar takobinsa iyakar karfinsa ya soka ta a cikin bakin wannan halittar, sai gashi takobin ta lume a jikin harshen halittar. Ai kuwa bayyi wata-wata ba, ya finciko takobin, sai gani akayi harshen ya gutsire. Nan fa jini ya kama bulbulowa tamkar magunar ruwa ta balle. Nan fa halittar nan ta haukace, ta rinka Kai duka ta ko'ina tamkar mahaukaciya. Haka ta rinka tamola da DURZASU Yana gwaruwa da duwatsu da bishiyoyin Dajin Yana faduwa Kasa. A cikin wannan fafatawa da yayi da wannan halittar sai da ya Suma sau Ashirin da biyar Amma da zarar halittar ta cafke shi da niyyar cinyeshi sai ya farfado ya kwaci Kansa. Kai a wannan yaki ne ya samu karaya uku a jikinsa. Daya a hannun Hagu, Daya a cinya Daya a Kafa. Gaba dayan jikinsa ya kukkumbura saboda tsananin wahala da bala'i, har ma ya fitar da ran cigaba da rayuwa Amma sai yaga ya kubuta. Haka dai aka ci gaba da wannan Gumurzu tun DURZASU na iya kare Kansa, har ya gaji ya Kasa ya sulale Kasa sumamme. A dai-dai wannan lokacin ne Kuma jinin halittar ya gama zubewa Kasa gaba Daya, faruwar hakan keda wuya sai akaga wannan Katuwar halittar ta sulale Kasa matacciya gaba dayan idanuwanta sun farfashe rugu-rugu saboda tsabar Kai duka ta ko'ina da take. Tom Alhamdulillahi♥️♥️ ME ZAI FARU IDAN YA FARFADO DAGA DOGON SUMAN DA YAYI? SHIN DURZASU ZAI SAMU NASARAR TSALLAKE DAJI NA BAKWAI DA YA RAGE, HAR YA ISA TSAUNIN DA ALJANI GAMJAHUL FUTUL YAKE? INA LABARIN SU SARKI ZURMATU MAI MULKIN BIRNIN BALLUS? A WANE HALI SADAUKI USAMA YAKE ? Domin son Jin Amsar wadannan tambayoyin sai mu hadu a GASAR JARUMTAKA na Goma insha Allah.. Najibullah Muhammad ✍️✍️🙏🙏🙏 Naku har kullum wato NAJIBULLAH MUHAMMAD ke cewa ku huta lafiya ✍️♥️🥰**GASAR JARUMTAKA** LITTAFI NA GOMA 10 PART A 🙋✍️♥️ AUTHOR: NAJIBULLAH MUHAMMAD ✍️✍️ POSTING: Najibullah Muhammad u🥷🥷 Lokacin da wannan halittar ta sulale Kasa matacciya ne da tsawon dakika saba'in da bakwai, sai Sadauki DURZASU ya farfado daga dogon suman da yayi. A wannan lokacin tuni karayar dake jikinsa ta fara kumbura saboda tsabar gwagwarmayar da ya Sha batare da an daure wurin ba. Koda Bude idanunsa sai yayi arba da Gawar wannan halittar himili guda a kusa da shi tamkar Tsauni. Cikin tsananin zafin nama ya yunkara da nufin ya tashi zaune Amma sai ya Kasa, domin ji yayi tamkar an Dora Masa wani Katon Dutse. Bisa dole ya hakura, sannan ya rinka Jan jiki Yana tafiya har ya iso karkashin wata bishiyar inibi, wadda 'yayanta suka zuzzubo Kasa ga su Nan birjik ba adadi duk nunannu. Da zuwansu sai ya rinka daukar 'yayan itaciyar Nan Yana ci, sakamkon yunwar da ke addabarsa ta tsawon kwana bakwai. Sai da yaci 'yayan itaciyar nan sosai ya koshi, sannan ya jingina a jikin itaciyar Nan, ya fara tallafo hannunsa na hagu Wanda ya samu karaya, cikin tsananin juriya da mazantaka ya fara kokarin gyara wannan karayar. Haka DURZASU ya wanzu a wannan Hali Yana ta kwallara ihu a yayin gyaran karayar da yake, sakamakon tsananin zafi da zogin da ya ke ji. Bai gushe ba Yana gyaran karayar da ya samu duka, sai bayan shudewar sa'a guda da rabi. A lokacin da ya kammala gyara karayar karshe ce, wato karayar kwaurinsa ya yi Suma na goma. Kai! Hakika komai rashin Imanin mutum Idan yayi arba da irin halin da DURZASU ya tsinci Kansa a wannan wuri dole ne ya zubar Masa da hawaye. Haka dai DURZASU ya wanzu a wannan daji har tsawon kwanaki goma Sha hudu, a wannan lokacin gaba dayan karayar jikinsa ta warke sumul, domin har Yana iya tashi ya falfala da gudu. Koda DURZASU yaga cewa, a yanzu fa karfin jikinsa ya dawo, sai ya yanke shawarar tsayawa a wannan Dajin na tsawon kwana bakwai domin Kara ma Kansa horon yaki. Tabbas yasan cewa tunkarar wannan Dajin na karshe dole sai anyi babban shiri na musamman. Nan take ya fara bawa Kansa horon yaki Mai tsanani, irin Wanda ba'a taba bawa wani mahaluki ba. Nan fa DURZASU ya wanzu Yana Mai koyon naushi akan bishiyoyin Dajin. Tun yana dukan bishiyoyin hannunsa na sagewa har ya zamana cewa idan ya naushi bishiya, sai dai aga hannunsa ya lume a ciki saboda tsananin karfin naushin. Haka Kuma yaci gaba da bawa Kansa horon tsalle-tsalle tamkar dan biri. Saboda tsananin horon da ya samu a bangaren tsalle-tsalle har ma yafi birirrika iya hawan sama. Domin idan DURZASU na wasan tsalle-tsalle zai iya yawace Dajin kaf, Yana tsalle-tsalle akan bishiyoyin Dajin batare da Koda kafarsa Daya ta taka Kasa ba. Sai dai aga Yana tsalle daga Kan wannan bishiyar zuwa waccan, daga waccan zuwa wannan tamkar Dan biri. A bangaren Sarrafa takobi kuwa, sai da ya zama tamkar wani shedanin Aljani. Saboda tsananin iya Sarrafa takobinsa zai iya fille kawunan abokan gaba dubu a cikin dakika goma. Idan DURZASU na Sarrafa takobi mutum na iya rantsewa cewa ba mutum bane Aljani ne, saboda ganin yanda yake Kai komo da takobin tamkar yadda hannu ko jerangiya a tsakanin kwano da Baki 😋😋 Kai! Har sai da ta Kai cewa saboda tsananin zafin namansa idan Yana Sarrafa takobi ko ganinsa ba'a iya yi, sai dai a rinka ganin guguwarsa tana fille manyan rassun bishiyoyi suna zubewa Kasa. Saboda tsananin karfin saran sa kuwa, duk lokacin da ya Kai Sara Koda Bai samu komai ba, sai dai

Chapter 10 of 12