Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
7 / 12
su ga Sarkinsu da Kuma son Jin bayanin da Sarkinsu yake dauke da shi a garesu. Bayan shudewar rabin sa'a, sai aka hango SARKI ZURMATU, SADAUKI USAMA, BOKA RAKUL, SARKI FALWAN cikin shiga ta Alfarma sun tunkaro fadar cikin nishadi. Nan take Dakaru suka Buda masu hanya, suka wuce Kai tsaye izuwa cikin fadar. Da isar su Sarki Zurmatu ya wuce kan KARAGARSA ya zauna. Sannan yayiwa su SADAUKI USAMA nu ni da su zauna a wasu kujeru a na Alfarma. Bayan sun zazzauna kowa ta natsu, sai Sarki Zurmatu ya Mike tsaye sannan ya fuskancesu yayi masu gaisuwa da harsheMai dadi, suka Amsa Masa cikin biyayya. Batare da Bata lokaci ba Sarki Zurmatu ya kwashe gaba dayan labarin duk abinda ya faru a filin yaki da Kuma yadda akayi suka karbi addinin musulunci daga hannun Sadauki Usama har suka samu nasarar wannan yaki, ya sanar da jama'arsa. Koda yazo dai-dai Nan a jawabinsa sai gaba dayan mutanen wurin suka cika da tsananin mamaki, Kuma Nan take Mafi yawa daga cikin jama'ar garin sukaji cewa zuciyarsu ta fara natsuwa da wannan addini. SARKI ZURMATU ya ci gaba da cewa, ya ku jama'ar birnin BALLUS kuyi sani Addinin musulunci shi ne, Addinin gaskiya Kuma Addinin tsira daga halaka. Kuma tabbas mun gani da idanmu, Kuma ku ma dayawanku kunga irin karfin da Ubangijin musulunci yake da shi. Kuyi sani cewa tuni mun Bada gaskiya ga ubangijin musulunci da ni da iyalina da Kuma su BOKA RAKUL, SARKI FALWAN, SARKIN YAKI DURKUL.. Saboda haka Ina son ku ma ku bayar da Gaskiya ga ubangijin musulunci domin tabbatar da rayuwarmu cikin aminci da kwanciyar hankali. Nan take jama'ar wurin duk sukayi shiru aka rasa Wanda zai ce wani abu, daga can sai wani dattijo ya tako ya zo gaban Sarki ya tsaya. Sannan ce ya shugabana tayaya zamu bar abinda muke Bauta mawa tun zamanin iyaye da kakanni, sannan mu rungumi wani bakon addini Wanda bamu San asalinshi ba? Shin idan mun shiga wannan addini a Ina zamuga Ubangijin musulunci ballantana mu rinka Bauta Masa? Sannan idan Muna cikin bukatar taimako tayaya zamuga Ubangijin musulunci har mu roke shi, ya temake mu? Koda Sarki yaji wannan jawabi daga bakin wannan tsoho, sai yayi shiru daga bisani ya dago Kai ya ce bani da Amsar wannan tambayar taka Amma bari na kira SADAUKI USAMA ya bamu wannan Amsar tunda shi ya Dade a cikin wannan addini. Nan take SADAUKI USAMA ya fuskanci mutanen birnin BALLUS ya ce, " ya ku jama'ar wannan birni kuyi sani cewa. Addinin musulunci shi ne Addinin gaskiya akan dukkan sauran addinai. Kuma Ubangijin musulunci shi ne, Wanda halicci komai da kowa. Shi ne Wanda ya halicci Sammai da kassai, sannan ya halicci mutane da da Aljanu da dabbobi da ruwa da iska, da bishiyoyi Kai da duk abinda kuke iya gani a duniya da ma Wanda Baku iya gani. Kuma shi ne ubangijin da komai yake tafiya bisa ikonsa. Haka Kuma duk abinda kuka gani a wannan duniyar Sammai da kassai mallakinsa ne, Kuma bayinsa ne. Sannan Kuma Yana lura da duk halin da bayinsa suke ciki, Kuma Yana Amsa kiran duk Wanda ya nemi taimakonsa Nan take. Haka Kuma Ubangijin musulunci ya kasance Mai kashewa da rayawa, Kuma Mai Azurta Wanda yaso ya talauta Wanda yaso, Kuma ya daukaka Wanda yaga dama sannan Kaskantar da Wanda ya Saba Masa. Haka Kuma ya tanadi rahma da ni'ima da Jin dadi mara yankewa ga duk Wanda ya Bauta Masa yayi Masa biyayya, haka Kuma ya tanadi azaba Mai radadi ga mutane ko Aljanun da suka bijire Masa ta hanyar kin Bauta Masa shi kadai. Koda jama'ar birnin BALLUS sukaji irin jawabin da SADAUKI USAMA yayi game da Ubangijin musulunci sai gaba dayansu jikinsu yayi sanyi Kuma suka gamsu dari bisa Dari cewa lallai Ubangijin musulunci shi ne Mafi cancanta a Bauta Masa. Nan take gaba dayansu suka ce tabbas mun amince Ubangijin musulunci shi ne abun Bauta da gaskiya, Kuma munyi Imani da shi. Cikin tsananin farin ciki SADAUKI USAMA ya biya masu Kalmar Shahada suka maimaita a lokaci guda. Wayyo musulunci dadi!♥️♥️🥰🥰 Inda ace mutum na wajen a lokacin da jama'ar wannan birni suka karbi addinin musulunci Kuma suke maimaita kalmar Shahada a lokaci guda, da sai ya ji kamar ya narke saboda tsananin dadi da farin ciki. Ana cikin wannan hali ne, aka ga Shugaban likitocin Sarki Zurmatu ya rugo cikin fadar cikin tashin hankali. Yana zuwa yayi gaisuwa ga sarki sannan ya ce, ya shugabana a gafarceni saboda mun Kasa ceto rayuwar YARIMA FAZAMAL yanzu haka ya mutu. Nan take duk murnan da akeyi sai ta koma izuwa bakin ciki, saboda kowa yasan irin yadda SARKI FALWAN ke matukar kaunar dansa. Nan take SARKI ZURMATU da sauran jama'ar wurin suka shiga rarrashin Sarki har suka shawo Kansa. Batare da Bata lokaci ba aka shirya jana'izar YARIMA FAZAMAL za'a binneshi a birnin, Amma sai Sarki FALWAN yace Yana so a bari yaje da Yarima birninsa ya rufe shi a can, Kuma daga Nan zai musuluntar da jama'arsa Shima. Nan take aka yiwa SARKI FALWAN shiri na musamman, SARKI ZURMATU ya bashi kyautar Dakaru masu yawa kyauta, da kyauta dukiya Mai yawa wadda za'a raya Al'umma Kuma a daukaka Kalmar Allah. Nan dai sukayi bankwana suka rabu. Bayan tafiyar Sarki FALWAN ne Sarki Zurmatu ya sanar da jama'arsa cewa insha Allah a Gobe za'a daura auren GIMBIYA MARITA da Kuma SADAUKI USAMA domin tabbatar da Alkawarin da Sarki yayi. Nan da Nan aka shiga shirye-shiryen biki, aka gayyato mutane daga ko'ina domin halartar wannan gagarumin biki. Washe gari aka daura auren GIMBIYA MARITA da SADAUKI USAMA aka Sha shagalin biki Mai yawa. SARKI ZURMATU ya Baiwa SADAUKI USAMA kyautar wani katafaren gida Mai tsananin kyau da kawatuwa. Batare da Bata lokaci ba Ango ya tare da Amaryarsa a sabon gidan da Sarki ya Basu, suka ci gaba da more Amarcinsu cikin Jin dadi da kwanciyar hankali. Bayan kamar wata guda ne da bikin SADAUKI USAMA GIMBIYA MARITA ta samu ciki. Farin ciki a wurin SARKI ZURMATU da Sadauki Usama bazai misaltu ba. Haka Kuma SADAUKI USAMA yasa aka Bude Masa wani Katon Fili a tsakiyar birnin inda yake Tara mutanen birnin Yana koya masu ibadoji na Addinin musulunci. Cikin kankanin lokaci mutane suka kware a karatu da rubutu da Kuma sanin yadda za'a bautawa Allah yanda ya dace. Haka dai akaci gaba da rayuwa cikin farin ciki har lokacin da GIMBIYA MARITA ta haifi da namiji Wanda ya kasance kyakkyawa na gaban kwatance. Tun daga ranar da aka haifi wannan Yaro aka fara shagalin rada Masa suna, da sati ya zagayo aka Sanya Masa suna MAHARAJ. Mutanen birnin BALLUS suka wanzu cikin tsananin farin ciki da kwanciyar hankali. Tattalin arzikin kasarsu ya habbaka ainun, ya zamana cewa 'yan kasuwa da fatake da duk wani Mai arziki sun naje kolinsu a birnin ya zamana cewa a kowane lokaci hidimar Kasuwanci a ke. A sakamakon hakane yasa Addinin musulunci ya Kara fantsama a ko'ina cikin duniya saboda kasancewar bakin fatake da ke zuwa fatauci birnin, Kuma dayawansu suna karbar Addinin musulunci suna zuwa can kasashensu suna yada Addinin. Bayan kamar shekaru uku da faruwar wannan Ala'mari, sai wani babban bala'i ya rinka faruwa a birnin. A Arewa da birnin BALLUS akwai wani surkukin daji Mai duhuwa Wanda hatta mafarauta basa iya shigarsa saboda duhuwarsa. To a cikin wannan Dajin akwai wadansu jibga-jibgan ZAKUNA masu tsananin girma da karfi Kuma adadinsu yakai guda dubu. A kullum da dare wadannan ZAKUNAN suna shigowa cikin birnin BALLUS suyiwa mutane mummunar barna, Kuma su kashe mutane sama da guda dubu, sannan da zarar anzo yakarsu sai su zama haske su bace. Haka suka rinkayi har tsawon wata guda, a cikin wannan lokacin sunyiwa mutane mummunar barna. Nan da nan domin ya gano daga inda ZAKUNAN ne ke zuwa suna masu barna Amma ya Kasa. Nan fa hankalin Sarki ya dunguzuma ainun ya rasa abinda ke Masa dadi a duniya. Koda SADAUKI USAMA yaga halin da Sarki Zurmatu yake ciki, sai ya ce ka kwantar da hankalinka ya Kai Sarkin sarakuna, kayi sani cewa babu abinda yafi karfin Allah. Don haka ka Dogara gareshi Kuma ka kwantar da hankalinka domin Allah Yana tare damu. Yanzu ka bani daga Nan zuwa gobe zanyi Istihara domin na roki Ubangijina ya sanar Dani duk abinda ke faruwa. Nan dai sadauki Usama yayita rarrashin Sarki Zurmatu har ya shawo Kansa, sannan sukayi bankwana suka rabu. Da dare yayi Usama yayi Istihara sannan ya kwanta, cikin iKon Allah, sai Allah ya bayyana Masa duk abinda ke faruwa akan lamarin wadannan bakin zakuna masu Yi masu barna. Washe gari tunda sassafe SADAUKI USAMA yaxo ga sarki yayi gaisuwa Sannan ya sanar dashi abinda Allah ya gwada Masa kamar haka... Yakai wannan Sarki kayi sani cewa, wadannan ZAKUNAN sun kasance sihirtattu ne, Kuma suna daga cikin jinsin ALJANU marasa Imani wadanda adadinsu yakai dubu. Sannan Kuma babban Dan SARKI KALJUL ne ya turo su, domin su zo su hallakamu gaba dayanmu saboda ya dauki fansar ran Mahaifinsa da jama'arsa. Yanxu haka wadannan ZAKUNAN suna can Dajin wannan birnin Dake arewacin garin. Koda Jin wannan batu sai Sarki Zurmatu yayi Umarni da ayi Shirin yaki domin aje a Karar da wadannan zakuna masu cutar da su. Nan take SARKI ZURMATU SADAUKI USAMA da sauran JARUMAN birnin sukayi Shirin yaki suka tunkari wannan daji.... A dai-dai wannan lokaci ne littafi na biyar ya kare🥱🥱🥱Kuma alkalami na ya kafe saboda rubutun da yasha✍️✍️ ME ZAI FARU IDAN SU SARKI ZURMATU SUKA ISA DAJIN DA ZAKUNAN SUKE? SU WA ZASU SAMU NASARA A YAKIN DA ZA'AYI? WANE MATAKI ZA'A DAUKA TSAKANIN BABBAN DAN SARKI KALJUL DA SU SARKI ZURMATU? mu hadu a GASAR JARUMTAKA na shida don Jin cigaban wannan Kasaitacce Kuma Kayataccen labari ✍️♥️🥰**GASAR JARUMTAKA** LITTAFI NA SHIDA 6 PART A MARUBUCI: NAJIBULLAH MUHAMMAD ✍️✍️ POSTING: Najibullah Muhammad 🥷🥷 Lokacin da rundunar su Sarki Zurmatu suka tunkaro wannan daji Wanda adadinsu ya Haura dubu arba'in. Kowannensu yayi shigar yaki ne da ratsin jan launi a jikin sulken kayan yakin, sannan Kuma dukkansu sun rufe fuskokinsu da hular karfe inbanda idanuwansu babu abinda mutum ke iya gani, haka Kuma mutum dubu Ashirin daga cikinsu na rike da mashi Mai tsananin Kaifi da Kuma tsini Wanda duk abinda aka soka da shi sai ya lume ya bullo ta baya Koda kuwa bishiya ce Mai kauri, a dayan hannuwansu na rike da Kuma garkuwowi domin kare martani. Sauran mutum dubu Ashirin din kuwa na rike da zabga-zabgan takubba masu tsananin Kaifi da tsini irin wadanda duk abinda aka Sara da su sai abun ya rabe gida biyu komai girmansa. Bayan tafiyar 'yan sa'o'i suka iso bakin Dajin. Daji ne Mai matukar duhuwa da Kuma sarkakkun bishiyoyi irin wadanda suka harhade da junansu. Da shigarsu Dajin suka Sha jinin jikinsu saboda ganin yadda Dajin yake da duhu Kuma tun farkon shigowarsu suka fara Jin wani irin gurnani Mai matukar ban tsoro Wanda ka iya sa mutum ya sume ko ma ya haukace saboda tsananin rashin Jin dadin gurnanin. A cikin wannan tafiya SARKI ZURMATU, SADAUKI USAMA, BOKA RAKUL ne akan gaba, sai Kuma Sarkin yaki DURKUL daga bayansu Yana bawa sauran Dakarun Umarnin inda zasu bi. Sai da suka shafe tafiyar sa'a uku cur! A cikin wannan daji suna tafiya Amma Basu ga Koda kyankyaso ba. Har ma sun fara tunanin juyawa da baya saboda gani suke kamar ZAKUNAN sun bar Dajin ma. Ba zato ba tsammani sai suka ga wurin da suke ya haskake da matukar haske, irin Wanda ko allura ta fadi sai an ganta. Kuma sai suka ga duk surkukin dajin ya warware ya Samar da wani Katon Fili na musamman tamkar a tsakiyar Sahara suke. Faruwar hakan keda wuya sai suka hango wani murgujejen Zaki Mai tsananin girma da kauri ya tako a hankali ya tunkaro inda suke. Zakin ya rinka yin wata irin tafiyar kaisaita tamkar tamkar a cikin gidansa yake. Yana tafiya Yana fitar da wani irin gurnani mara dadin ji, har ya karaso inda su Sarki Zurmatu suke. Nan fa aka fara kallon-kallo TSAKANIN SU SARKI ZURMATU da ZAKIN. Zakin dai guda Daya ne to Amma Kuma girmansa ya kai na toron giwa, domin duk takun sawunsa guda dai-dai yake da na mutun Dari. Yana tafiya Kasa na Amsawa kamar zata rufta. Koda tsayuwar wannan Zaki gabansu Sarki Zurmatu sai dukkansu suka razana Kuma suka Sha jinin jikinsu, domin a tarihin rayuwarsu da Kuma yake-yaken da sukayi Basu taba gani ko Jin labarin Zaki Mai tsananin girma da kwarjini kamar wannan Zaki ba. Nan take gaba dayansu sukayi ajiyar zuciya sannan suka jin-jina Kai suna tunanin hanyar da zasu bi wajen Afkawa Zakin. SARKI ZURMATU yayi tunani a cikin zuciyarsa cewa, meyasa Zaki Daya ne kacal muga gani alhalin sadauki Usama yace min adadinsu ya Kai dubu? To kenan Ina sauran suke? Kamar SADAUKI USAMA yasan abinda Sarki ke tunani, kawai sai suka dubi juna da nufin yin magana Amma sai hakan Bai yiwu ba sakamakon ganin yanda Zakin ya zabura da tsananin gudu tamkar iska ya ratso cikinsu, ya rinka bankesu suna faduwa Kasa. Tsananin zafin naman Zakin ya wuce misali, cikin abinda Bai wuce dakika hamsin ba Zakin ya zubar da Dakaru Dari da saba'in kwance a Kas, cikin mawuyacin Hali. Nan take Sarki Zurmatu ranshi ya Baci Kuma zuciyarshi ta kama tafarfasa kamar zata kone saboda tsananin fusata, kawai sai akaga Sarki Zurmatu da Sadauki Usama sun ruga izuwa kan Zakin sun tare shi. Nan fa suka kacame azababben yaki a tsakaninsu, ya zamana cewa suna iya kare duk harin da Zakin ke kawo masu da Takubbansu Amma abin takaicin shi ne Koda sun Kaftawa Zakin Sara, da takobinsu sai suji tamkar sun sari Dutse domin ko Kwarzanewa bayayi. Nan fa suka yi iyakar kokarinsu wajen hallaka Zakin Amma Abu ya faskara. A zahiri dai gashi sun samu nasarar dakatar da Zakin ga barin kashe dakarunsu da yake yi, to Amma Kuma sunbi duk hanyar da yakamata su kashe Zakin Amma Abu ya gagara. Haka suka wanzu har sa'a guda ta shude, a wannan lokaci tuni sun fara gajiya Amma shi Zakin ko kadan babu alamar gajiya a tare da shi tamkar wutar lantarki aka zuba Masa. Koda Zakin yaga su Sarki Zurmatu sun fara gajiya, sai ya fara murna Kuma ya Kara kaimi wajen kokarin hallaka su. Nan take ya shammace su ya daka wani wawan tsalle da nufin ya bankesu da kirjinsa, cikin tsananin zafin nama suka goce suna masu mirginawa Kasa, suka kaucewa harin nasa. Koda kirjin Zakin ya samu wani Katon Dutse Dake wajen, kawai sai akaga Dutsen ya tsattsage zuwa can sai aka ga ya ruguje tamkar an baza danyar Kasa. Nan fa hankalinsu ya Kara mummunan tashi saboda ganin irin tsananin karfin kirjin wannan Zakin. Nan da Nan Zakin ya Kara juyowa a Fusace ya Kara kawo masu wani mugun hari da kafafuwansa na gaba, Nan fa su Sarki Zurmatu sukayi iyakar kokarinsu wajen kaucewa harin Zakin Amma Abu ya gagara. Nan take Zakin ya mangaresu da kafafuwansa, saboda karfin dukan sai da sulken yakin da ke sanye a jikinsu ya kakkarye Kuma sukayi baya luu tamkar an janye su da majaujawar karfe, suka gwaru da wata Katuwar bishiya. Kawai sa aka ga sun fado a sume ko motsawa Basu yi. Cikin tsananin farin ciki Zakin yayi wani yunkuri da nufin ya yagalgala su Sarki Zurmatu, Amma sai Sarkin yaki DURKUL ya kwalla kabbara ya tare shi ta hanyar gabza Masa naushi a gefen Ido, saboda karfin naushin sai da Zakin ya fado kasa Kuma ya mulmula sau goma sannan ya Mike tsaye. Nan fa Zakin yayi wani irin ruri, sannan ya dako tsalle sama da dukkan karfinsa da nufin ya cizgewa Sarkin yaki Kai, Amma sai Sarkin yaki yasa mashinsa ya soka a cikin bakin Zakin sannan ya wurgashi can gefe guda. Ba zato ba tsammani sai yaga Zakin ya Mike tsaye sannan ya kama mashin ya taune shi, tamkar Yana ciyawa. Zuwa can ya furzo da Karafunan mashin waje, sai ga Karafuna na fadowa Kasa filla-filla. Ala'marin da yayi matukar Baiwa Sarkin yaki mamaki kenan, Kuma ya tabbatar da cewa lallai wannan Zakin ya cika Hatsabibi. Kafin yayi wani yunkuri sai yaga wannan Zakin ya Kara dako tsalle sama ya runbabeshi sun fadi suna ta mirgineneniya a Kasa. Kowannensu na ta kokarin hallaka kowa Amma Abu ya gagara, cikin abinda Bai wuce dakika goma ba, Zakin yayiwa Sarkin yaki munanan raunika guda uku, Daya a Fuska, daya a kirji, dayan Kuma a hannu. Kafin a jima jikin Sarkin yaki ya rine da jini Nan da Nan jiri ya fara diban sarkin yaki sbd jinin dake bulbulowa daga jikinsa, Koda Zakin yaga haka sai ya Bude bakinsa da nufin ya cisge Masa Kai. A dai-dai wannan lokaci ne SARKI ZURMATU da SADAUKI USAMA suka farfado daga dogon suman da sukayi. Koda Bude idonsu suka ga abinda ke Shirin faruwa sai gaba dayansu suka kwarara kabbara ta musamman sannan suka daka tsalle daga inda suke, suna dira a kusa da Zakin sai kowannensu ya cafko Kafa guda ta Zakin sannan suka jaa iyakar karfinsu. Nan take aka ji Zakin yayi wani irin ruri Mai tsananin Kara, kafin Zakin yayi wani yunkuri tuni su Sarki Zurmatu sun raba shi biyu, sai gashi kowane ya jefar da barin Gangar jikin Zakin. Nan fa sauran Dakarun Dake wurin suka shiga Yi masu shewa da jin-jina bisa wannan gagarumar Jarumtaka da suka nuna. Ana cikin haka ne sai kawai akaga Kasar wurin ta kama girgiza kamar zata rufta, Sannan aka ji wani irin takun sawaye Mai tsananin yawa ya tunkaro inda suke. Nan fa kowannensu ya Mike tsaye sannan suka rike makamansu dakyau, sannan Kuma suka shiga Karanta addu'ar Neman tsari da Kuma Neman taimakon Allah akan wadannan miyagun zakuna. Faruwar hakan keda sai kawai sukaga sauran ZAKUNAN wadanda adadinsu yakai dari Tara da casa'in da Tara sun tunkaro su. Da zuwansu Basu tsaya wata-wata ba suka afka masu gaba dayansu da nufin su cinyesu. Nan fa wuri ya yamutse, aka kama dauki ba dadi da wadannan ZAKUNAN. A wannan lokacin sai Ala'marin yasha bamban domin su Sarki Zurmatu suna samun nasarar kashe zakunan cikin sauki saboda kasancewar sun nemi taimakon Allah. Wannan yasa su kansu sauran Dakarun suka rinka karkarshe zakunan, saboda suna yakin ne suna Karanta addu'o'in Neman tsari. A wannan lokacin sai sukaga yanxu hatta makamansu na yin tasiri akan zakunan, wato duk Zakin da suka Sara da takobinsu sai suka ga ta lume a jikinsa Kuma ya fadi matacce. Wannan yasa suka samu nasarar kashe zakunan gaba Daya a cikin abinda Bai wuce rabin sa'a ba. Kuma babban abin farin cikin ma shi ne babu Wanda ya rasa rayuwarsa, Amma akwai wadanda suka samu mugayen raunika. Koda ganin wannan nasara da sukayi sai suka cika da tsananin farin ciki Kuma suka yiwa Allah godiya bisa karfafarsu da yayi akan makiya. Nan da nan suka yiwa kansu magani suka juya da baya suka koma izuwa birninsu, suna tafiya suna wakar cin nasara. Tun daga nesa Dakarun birnin masu tsaron kofa suka hango su suna wakar cin nasara, sai Nan da nan aka buka Gangar cin nasarar yaki wadda Kararta ya cika birnin gaba Daya. Nan take aka kama shagali da murnan wannan nasara da aka samu. Bayan kamar kwana uku da faruwar wannan Ala'mari, sai Sadauki Usama ya Baiwa Sarki Zurmatu shawarar cewa ya shugabana. Ina ganin ya kamata ka ware manyan jarumai daga cikin jarumanka wadanda adadinsu zai Kai Milyan Daya, a rinka Basu horon yaki bisa jagorancin sadauki DURKUL. Ni Ina ganin Idan akayi haka to abokan gaba zasu rinka shakkar tunkarar wannan birni naka, haka Kuma Kai kanka zaka huta da fita yaki saboda kana da tarin mazajen da zasu iya tunkarar komai da kowa. Koda Jin wannan batu sai Sarki ya yarda da wannan shawarar, Kuma daga wannan Rana aka rinka zabar manyan sadaukai majiya karfi Kuma masu dakakkiyar zuciya har sai da aka ware guda Milyan Daya. Sannan aka ware wani tafkeken Fili a wajen garin inda ake Basu horon yaki kullum. Daga wannan Rana wani abu bai sake faruwa ba, har bayan wata biyar. A wannan lokaci ne Sadauki Usama ya kadaita da SARKI ZURMATU ya ce, ya Shugabana a halin yanxu inaso na koma Kasarmu saboda a halin yanxu na cika alkawarin da na yiwa mahaifina akan musuluntar da kasashe guda dubu, Kuma nasan yanxu haka ana can ana tsammanin dawowa ta. Saboda haka inaso insha Allah a goben Nan zan kama hanya da ni da matata da Kuma Dana MAHARAJ. Koda Jin wannan batu sai idanun Sarki Zurmatu suka zazzaro Kuma ya marairaice kamar zayyi kuka, sannan ya ce ya Kai wannan Dan Sarki Kuma jarumin jarumai kayi sani cewa na shaku da Kai, Kuma na Saba da Kai ainun tamkar ni na haifeka. Tayaya kake tunanin zanji dadin rayuwata idan babu Kai, Kuma babu 'yata da Kuma jikana? Cikin tsananin tausayin Sarki Zurmatu, Usama ya ce kayi hakuri yakai shugabana. Kayi sani cewa duk abinda kaga ya faru a wannan duniya to dama can Allah ya gama tsara hakan, kawai lokaci ake Jira. Don haka na yi maka alkawarin cewa daga yau duk bayan kowace shekara zan rinka tasowa da ni da matata da Dana Muna kawo maku Ziyara a wannan birni Mai albarka, sannan Kuma nagode sosai da wannan Qauna da ka nuna min wadda ta sa har ka mallakamin 'yarka. Nan take suka fashe da kuka sbd tsananin alhinin rabuwarsu. A haka dai suka kasance har SADAUKI USAMA ya shawo kan sarki Zurmatu. Daga Nan sukayi bankwana suka rabu. Washe gari tunda sassafe kowa Yarima USAMA, GIMBIYA MARITA, da dansu MAHARAJ, tuni sun gama shiryawa har sun fito kofar fadar Sarki sun tsaitsaya. Nan da nan mutanen birnin sukayi cincirindo domin yiwa Yarima USAMA bankwana akan komawa kasarsu da zayyi. Bayan kamar Dakika sittin sai ga SARKI da matarsa sun fito idanunsu sharkaf da hawayen bakin cikin rabuwa da su GIMBIYA. Nan take suka rungume junansu dukkansu sbd alhinin tafiya, a haka dai suka kasance har wani lokaci. Bayan sun gama bankwana da mutane sannan suka hau dawakansu suka nufi birnin fita birnin tare da Dakaru dubu goma 'yan rakiya gami da kuzuri Mai yawa. Haka dai suka ci gaba da tafiya ana daga masu ana zubar da hawaye har suka kule aka dena hangensu.. Daga wannan Rana Sarki Zurmatu ya mayar da hankali wajen musuluntar da sauran kasashen da ke makwabtaka da su. Ya zamana cewa ya zage dantse wajen fita JIHADI da shi da Dakaru dubu Dari daga cikin wadanda ake bawa horon yaki. A cikin iKon Allah sai ya rinka samun gagarumar nasarar yaki, ya rinka Kawar da tutar Kafirci Yana Kafa ta musulunci, a cikin wata uku kacal sai dai yaci kasance arba'in da yaki Kuma ya Kafa tutar musulunci a biranen. Nan fa sunan musulunci ya daukaka, ya zamana cewa a ko'ina mutane sun San da rundunar Sarki Zurmatu. Su dai wadannan Dakaru na Sarki Zurmatu ana Yi masu lakabi da SADAUKAN YAKI. Saboda tsabar karfin wadannan Dakaru sai da ya zamana cewa da yawan kasashe suna Mika wuya su karbi musulunci, tun gabanin su gwabza yaki da su. Sai da wadannan DAKARUN suka shafe shekara guda suna yakar kasashen Kafirai suna Kafa tutar musulunci. A wannan sunyi yaki sau Dari da arba'in, Kuma sun samu nasarar musuluntar da kasashe Dari biyu da tamanin. Wannan yasa Birnin BALLUS ya yawaita da samun bayi da Kuma dukiya Mai tsananin yawa a matsayin Ganimar yaki da ake samowa daga sauran kasashen da akaci yaki. Daga wannan lokaci mutanen birnin BALLUS suka ci gaba da zama lafiya cikin kwanciyar hankali batare da fargabar komai ba. Yau ma kamar kullum mutane suna tsaka da harkokin kasuwancin su, sai kawai aka ga Kasa ta kama girgiza kamar zata ruguje, koguna suka rinka fantsama suna ambaliya, bishiyoyi suka rinka karyewa, gidaje suka rinka rushewa mutane suka rinka faduwa suna Suma wasu ma na rasa rayuwarsu Sakamakon wata irin muguwar tsawa da girgizar Kasa. Nan da Nan birnin ya hau girgiza Yana tambal-tambal kamar zai ruguje, ba zato ba tsammani sai kawai akaga wata murtukekiyar MACIJIYA Mai tsananin kauri da tsayi, wadda ba a iya hango karshenta saboda tsawonta. Haka Kuma kawunta guda saba'in da bakwai dukkansu suna furzo da wani mugun dafi bakikkirin tamkar an kada lalle. Idanuwanta kwala-kwala ne masu tsananin girma kamar Katon Dutse. Idan ta Mike tsaye kanta kamar zai tabo giza-gizai saboda tsabar girmanta. Ba zato sai kawai aka ga wannan MACIJIYA ta wangame gaba dayan bakunanta ta dasawa mutanen wurin Wawa. Nan fa ta rinka daukarsu tana yin Loma guda dasu tamkar ana jefa 'yar mitsitsiyar tsakuwa a cikin Katuwar Rijiya. Kafin cikar dakika hamsin ta hadiye sama da mutum dubu......... A dai-dai wannan lokaci ne na gaji da rubutu. Na ke cewa mu hadu a GASAR JARUMTAKA na shida 6 part B don Jin cigaban wannan Kasaitacce Kuma Kayataccen labari Mai dadi da debe kewa✍️✍️✍️🙏🙏🙏**GASAR JARUMTAKA** LITTATI NA SHIDA 6 ♥️ PART B ✍️💯 AUTHOR: NAJIBULLAH MUHAMMAD ✍️✍️ POSTING NAJIBULLAH MUHAMMAD 🥷🥷🥷 Lokacin da wannan Katuwar

Chapter 7 of 12