Kimanin shekaru dubu uku da Dari uku da arba'in da bakwai da suka wuce, anyi wata kafceciyar Kasa Mai tsananin girma da fadi wadda ta bunkasa a bangaren tattalin arziki, karfin Mulki, Kasuwanci, jarumai da bokaye da matsafa, ana kiranta da suna BALLUS.
Birnin BALLUS na karkashin mulkin wani Gawurtaccen Sarki ne, Kuma SADAUKI UBAN SADAUKAI Kuma kyakkyawa na gaban kwatance Wanda shekarunsa Basu wuce hamsin ba, ana kiransa da suna ZURMATU.
Sarki Zurmatu ya kasance adalin Sarki domin kowa Yana Jin dadin yadda Sarki Zurmatu ke tafiyar da mulkinsa a Kasar, domin Bai yadda da zalunci ba ko kadan. Amma Kuma Yana da tsananin rashin Imani ga duk Wanda ya karya doka a garin. Haka Kuma Sarki Zurmatu mutum ne Mai son Nuna Jarumtaka, wannan yasa duk Wanda yake son samun kusanci da shi to dole ne ya kasance Gawurtaccen jarumi na gaban kwatance.
A rayuwar Sarki Zurmatu babu abinda yake bakanta Masa rai kamar yaga jarumin da ya fishi Jarumtaka, domin a dalilin haka ne yasa ya Ziyarci kasashe Dari bakwai da saba'in da bakwai domin koyon salon yaki iri-iri ta yadda zai zama Gawurtaccen jarumin da babu Wanda zai iya nasara akanshi.
Tun daga ranar da Sarki ya kammala karbar horon yaki a kasashe mabambanta, sai ya tattara gaba dayan 'yan majalisarsa akan bukatar cewa, Yana son a rinka shirya GASAR JARUMTAKA duk bayan kwanaki bakwai.
Batare da wata jayayya ba gaba dayan 'yan majalisar suka amince.
Nan take Sarki Zurmatu ya Mike yayi masu bayanin yanda yake son Gasar ta kasance..
Wato za'ayi shela akan ana gayyatar duk wani jarumi da yake ji da Kansa, da Wanda yake cikin birnin BALLUS da sauran jaruman kasashe masu makwabtaka duk ana gayyatar su.
YANAYIN GASAR ZAI KASANCE.
Da farko za'a ware jaruman Gasa gefe guda, sannan za a rinka Kiransu Daya bayan Daya suna Gwabzawa da wasu Dakarun Sarki na musamman wadanda aka tabbatar da cewa inbanda Sarki Zurmatu babu Wanda yakai su Jarumtaka a duk fadin nahiyar, domin komai tsananin Jarumtakar mutum indai ya hadu da su to cikin dakiku kadan suke yin fata-fata dashi.
Wadannan Dakaru suna da tsananin yawan gaske, domin musamman SARKI ZURMATU ya je har Kasar Rum ya siyo irinsu sama da guda Milyan goma, dukkansu sun kasance Karti majiya karfi, domin gaba dayan jikinsu a murde yake tamkar karafuna ne aka lillika a sassan jikinsu.
Sannan Kuma sun kasance jibga-jibga tamkar samudawa.
Hakika wadannan Dakaru sun cika jarumai kuma ababen tsoro, domin komai yawan abokan gaba da zarar sunyi arba dasu, Nan take suke sumewa wasu Kuma su haukace saboda tsananin razana.
Tun daga ranar da Sarki Zurmatu ya siyo wadannan Dakaru ya kawo su birninsa, sai ya sa aka Gina masu wani tafkeken gari tare da gine-gine masu tsananin kauri da kwari, babu abinda suke yi a cikinsa face bawa kansu horon yaki da Kuma zaman jiran Umarnin Sarki.
Musamman Sarki Zurmatu yayi tanadin wadannan Dakaru domin kawai wannan Gasa.
Sarki Zurmatu yaci gaba da cewa, za'a rinka Gabar da wannan babbar Gasa ce a babban filin Fadarsa Wanda a Kalla zai iya daukar sama da mutum Milyan Dari saboda tsananin girmansa, Kuma ba'a yarda da yin Amfani da tsafi ba a yayin gudanar da wannan Gasa, haka Kuma ba a yarda da shiga cikin filin Gasa ba, muddin mutum baya daga cikin jaruman Gasa..
Sannan gaba dayan Jaruman Gasar zasu kasance a bangare Daya ne, sa'annan Kuma za'a ware Dakarun Sarki guda Dari a gefe Daya.
Daga cikin guda Dari na Dakarun Sarki za'a ware guda goma su shigo cikin Gasa, sannan a kira jarumin Gasa guda Daya domin tunkararsu, idan ya samu nasara akan guda goman Nan, sai a karo Masa guda Ashirin, Suma idan ya samu nasara akansu sai a karo Masa guda talatin da haka da haka har ya gama da duka darin..
Duk jarumin da ya samu nasarar kashe wadannan Dakarun Sarki guda Dari to Sarki yayi mashi Alkawarin biya Masa dukkan bukatar da yake da ita, sannan Kuma zai mallaka Masa 'yarsa aure.
Yayinda sauran 'yan majalisar Sarki sukaji wannan Batu, gaba dayansu sai suka mimmike tsaye saboda tsananin razana, domin sun San cewa Koda za'a Tara gaba dayan Jaruman duniya su tarar wa wadannan Dakarun na Sarki, to tabbas cikin kankanin lokaci Dakarun Sarki zasu Karar dasu, to tayaya ake tunanin akwai jarumin da zai iya ganin bayan wadannan za6a66un Dakarun guda Dari?
Cikin girmamawa Waziri MIKILAS ya dubi Sarki fuskarsa cike da damuwa yace, ya shugabana shin kanason ayi ta asarar miyagun rayukan Al'umma ne haka kawai, domin na tabbata cewa duk jarumin da ya shiga wannan Gasa mutuwa zayyi, domin kowa yasan cewa karo da wadannan Dakaru naka tamkar mutum ya siyo mutuwa ne da kudinsa ya rataya a wuya.
Koda Sarki yaji wannan Batu na Waziri, sai ya kyalkyale da dariya sannan ya dubi Waziri ya ce, ya Kai Waziri kayi sani cewa duniya da fadi take haka ma abin cikinta yawa gareshi, tabbas Ina ji a jikina cewa akwai jarumin da zai iya lashe wannan Gasa, Kuma a halin yanxu babban burina shine nayi Ido biyu da wannan jarumi domin mu gwabza ni da shi domin ganin Wanda zai samu nasara.
Don haka na Umarce ka, da ka sa a baza sanarwa birni da kauye akan ana gayyatar duk Wanda ya amsa sunansa na Jarumi zuwa wajen wannan Gasa Nan da kwana uku, tare da sanar da kowannensu sakamakon da zai samu yayinda ya lashe wannan Gasa.
Koda gama fadin hakan sai Sarki ya sallami taro kowa ya kama gabansa.
Waziri MIKILAS kuwa tunda ya rabu da Sarki Zurmatu sai ya tattaro duk Dakarun da yake ji dasu, sannan ya rubuta masu takardu masu dauke da gayyatar duk Wanda ke son shiga wannan Gasa, tare da Umarnin cewa kowa yazo daga Nan zuwa kwana biyu.
Nan da nan wadannan Dakarun wazirin guda dubu goma suka fantsama cikin duniya kowane yayi bangaren shi domin isar da Sakon Sarki.
A yammacin Kasar BALLUS wato inda SARKI ZURMATU ke Mulki kuwa akwai wata tafkekiyar Kasa Mai madai-daicin girma wadda wani Azzalumin Sarki ke Mulki.
Shidai Wannan Sarki ana kiransa da suna FALWAN.
Sarki FALWAN ya kasance gabjejen Kato na gaban kwatance Kuma Mai mummunar siffa, Wanda mutum Kan iya amai idan ya cika kallon fuskarsa saboda tsananin muninta.
Kamar yadda fuskarsa take mummuna haka Zuciyarsa take, domin komai kankantar laifi idan Mutum yayi Masa to hukuncin kisa ne, ko Kuma daurin Rai da Rai a gidan wani bala'e'en kurkunsa Wanda ya Saka Sojoji guda dubu Dari domin tsaron fursunoni.
Duk Wanda tsautsayi yasa aka kaishi wannan gidan kurkukun to har abada ko Gawarsa bazata fito ba, sai dai a bar gawar Nan ta ru6e ta zagwanye har kasusuwan suyi kwarangwal sannan a kwashesu akai wani daki na musamman da akayi domin tsatsube-tsatsuben duk wani abu da ya shafi rayuwar Sarki da mulkinsa.
SARKI FALWAN na da wani hatsabibin Yaro wani yayi kaurin suna wajen Zalunci da bakar zuciya, bugu da Kari Kuma gashi Jarumi na gaban kwatance domin mutane gani suke ma kamar yafi mahaifinsa SADAUKANTAKA, musamman ganin yanda yake iya yin abubuwan al'ajabin da duk nahiyar babu Mai iya yin kwatankwacinsa.
Saboda tsananin Jarumtakar Yarima FAZAMAL IBN FALWAN shi kadai Yana iya tunkarar mayaka Dari batare da makami ba, Kuma duk ya samu nasarar kakkaryasu batare da Daya daga cikinsu ya samu nasarar Koda lakutar jikinsa ba.
A rayuwar Yarima FAZAMAL babu abinda yake so sama da 'yar SARKI ZURMATU wato GIMBIYA MARITA, domin tunda yake sau Daya ya taba yin arba da kyakkyawar fuskarta a cikin madubin matsafin Bokan mahaifinsa, Kuma tun daga wannan lokacin soyayyarta da Qaunarta da begenta sukayi dirar mikiya a cikin zuciyarsa, ya zamana cewa hatta barci baya yi balle cin abinci saboda tsananin Qaunarta da yakeyi.
Kuma ba komai ne ya kawo hakan ba, face tsananin kyawunta GIMBIYA MARITA Wanda ya wuce misali, domin komai taurin zuciyar mutum indai yayi arba da ita, to take yake kamuwa da tsananin Qaunarta.
Kai saboda tsananin kyawun GIMBIYA ne yasa Sarki ya Sanya mata matakan tsaron da duk duniya babu wani jarumi daga jinsin bil'adama ko aljanu da ya Isa yazo inda take, Kai hatta hadiman gidan sarautar Basu Isa su ganta ba, sai dai wasu kuyangi na musamman masu kula da ita.
Dalilin dayasa Yarima FAZAMAL yayi arba da kyakkyawar fuskar GIMBIYA MARITA shi ne, watarana ne SARKI FALWAN ya kira bokansa domin yayi Masa akan gano hanyar da zai bi domin ya samu nasarar kashe Sarki Zurmatu ya Haye KARAGARSA.
tuntuni Daman Sarki FALWAN bashi da babban burin da ya wuce ace yaci birnin BALLUS da yaki Amma Abu gagara kasancewar SARKI ZURMATU ya fishi dimbin mayaka da Kuma miyagun makaman da ko a tahiri ba'a ganin irinsu ba.
Haka Kuma shi kanshi Sarki Zurmatu masana sun tabbatar da cewa SADAUKI NE NA GASKE Wanda ake tunanin duk duniya babu Wanda ya Isa yayi gaba da gaba da shi na tsawon dakika Dari batare da ya kai shi Kasa ba, komai tsananin Jarumtakar mutum kuwa.
Haka Kuma a bangaren karfin sihiri Sarki Zurmatu na da wasu zakakuran bokaye wadanda duk nahiyar babu Wanda ya Kai su karfin sihiri.
To a cikin binciken da Bokan Sarki FALWAN ne, madubin matsafinsa ya hasko fuskar GIMBIYA MARITA, inda Bokan ya tabbatar masu da cewa akan su kwantar da hankalinsu, Nan gaba kadan SARKI ZURMATU sai shirya wata GASAR JARUMTAKA wadda akayi alkawarin duk Wanda ya lasheta to shi ne zai zamo mijin GIMBIYA MARITA.
Koda gama ganin wannan Ala'marin sai SARKI FALWAN ya tuntsire da mahaukaciyar dariya domin a tunaninsa ya gano hanyar da zai kwace mulkin Kasar BALLUS salim-alin batare da wata wahala ba.
Wato idan shi ko dansa Yarima FAZAMAL ya lashe Gasar sai ya aura Masa GIMBIYA shikuma ya Haye KARAGARSA sannan ya barwa dansa mulkin wannan Kasar yaci gaba da Mulki.
Bayan kamar wata bakwai ne da faruwar wannan Ala'mari, Sarki FALWAN na zaune akan KARAGARSA Yana gudanar da harkokin Mulki na rashin Imani, kawai sai aka ga badakaren Birnin BALLUS ya ratso ta tsakiyar fadar rike da wata takarda.
Nan take fadar tayi tsit kowa ya zuba Masa idanu har ya zo gaban Sarki, Sannan ya sauko daga Kan dokinsa ya fadi yayi gaisuwa Sannan ya ce, ya shugabana Sako ne daga Sarkin Duniya wato Sarki Zurmatu na birinin BALLUS Wanda yake gayyatar duk wani jarumi na birninka izuwa wata Kasaitacciyar Gasa ta musamman tare da sakamako Mai tsoka ga duk Wanda ya lashe wannan Gasa.
Sannan Kuma ya ce, duk jarumin da yake sha'awar shiga Gasar to lallai ya halarcin Birnin BALLUS Nan da kwana biyu.
Badakaren na gama fadin hakan sai ya kama dokinsa ya hau sannan ya juya da baya ya sukwane shi.
Koda Jin wannan Albishir da Sarki FALWAN yayi, sai ya kamu da tsananin farin ciki Bai San ma sa'adda ya tuntsire da dariya ba.
Nan take ya Bada Umarnin a shirya masu tafiya shida Yarima FAZAMAL tare da Dakaru 'yan rakiya guda dubu saba'in.
Nan da aka kama shiri, washe gari tunda sassafe ya barwa wazirinsa rikon Kasa sannan suka kama hanyar birnin BALLUS.
A can birnin BALLUS kuwa, tuni labari ya cika ko'ina akan gabatar da wannan Gasa, domin kowa ya kagara ranar da za'a fara wannan Gasar tazo domin ya morewa idanunsa kallon yadda jarumai ke gwagwarmaya.
Ai kuwa cikin kankanin lokaci birnin BALLUS ya cika makil da bakin jarumai masu sha'awar shiga Gasar.
Duk jarumin da yazo don shiga wannan Gasar to Nan take ake yi masa iso wajen alkalan Gasa domin ya biya kudin shiga Gasa sannan su rubuta sunanshi.
A cikin kwana biyu kacal sai da aka samu manyan jarumai mabambanta wadanda suka shiga GASAR JARUMTAKA guda dubu tamanin.
Gaba dayan alkalan Gasar sun mamakin yadda akayi Jaruman Gasar sukayi yawa haka..
Abinda Basu sani ba shi ne, da yawan Jaruman Gasar Sun kasance jinsin ALJANU da Kuma shahararrun bokaye, suka rikide izuwa jinsin bil'adama domin samun damar lashe wannan Gasa don mallakar GIMBIYA MARITA.
Kash! Hakika masu iya magana sunyi Gaskiya da suka ce, rashin sani yafi dare duhu.
Tabbas inda wadannan Jaruman Gasar sun San abinda zai biyo baya da basuyi gangancin shiga wannan Gasar ba, domin bala'in da ke cikinta yafi karfin tunkarar duk mutanen duniya ka yake su.
A cikin kwana na biyu ne, da yamma sai ga SARKI FALWAN tare da dakarunsa sun shigo birnin BALLUS, suna zuwa Sarki Zurmatu yayi masu iso cikin tsananin farin ciki.
Batare da Bata lokaci ba, Sarki Zurmatu yayi Umarni aka Kai su masaukinsu tare da Kai masu abinci da abun Sha iri-iri.
Nan da Nan Sarki FALWAN ya aiki wani badakarensa izuwa wajen alkalan Gasar domin ya biya masu kudin shiga Gasa da shi da dansa Yarima, da Kuma wasu zakakuran dakarunsa wadanda suka kasance manyan jarumai na gaban kwatance guda dubu.
Nan take wannan badakaren ya cika Umarni, cikin 'yan dakiku kadan ya dawo.
Kashe gari tunda sassafe kowa ya fara tahowa filin Gasa, cikin kankanin lokaci filin Gasar ya cikar makil babu masaka tsinke.
Ya zamana cewa in Banda da'irar da Jaruman Gasar zasu fafata sai Kuma kujerun da Sarkin Zurmatu da GIMBIYA MARITA da Kuma sauran SARAKAI irinsu FALWAN da Yarima FAZAMAL babu sauran wajen zama ko tsayuwa.
Nan da Nan batare da Bata lokaci ba, bayan Sarki Zurmatu da mabiyansa sun hallara sai ya Bada Umarnin a fara Gasa..
Nan take aka kira wani Gwarzon jarumi daga cikin tawagar Jaruman Gasar ana kiransa da suna MARGIM, sadauki MARGIM ya kasance jarumi ne Mai dakakkiyar zuciya tare da Jarumtaka ta ban al'ajabi, sannan Yana da tsananin sa'a da rabo bisa duk irin abinda yasa a gabanshi.
Koda sadauki MARGIM ya fito filin Gasa sai aka hau yi masa shewa da jin-jina kasancewar shi ne jarumi na farko da zai fara fafatawa.
Nan take aka kira wadannan Dakarun Sarki guda Dari suka shigo filin Gasa, sannan aka waro guda goma daga cikin su suka zo gaban sadauki MARGIM suka tsaya.
Koda mutane sukayi arba da wadannan DAKARUN NA SARKI sai suka firgitse, da yawan mutanen ji sukayi kamar su ruga saboda tsananin razana, Kai hatta dayawa daga cikin jaruman Gasar sai da sukaji hantar cikinsu ta kada saboda tsananin razana, Nan take sukaji nadamar shiga wannan Gasa tazo masu domin sun tabbatar da cewa sun sayi ajalinsu ne da kudinsu.
Koda sadauki MARGIM yayi arba da wadannan samudawan DAKARUN sai yaji zuciyarsa ta buga da karfi, Amma saboda dakakkiyar zuciya irinta mazan kwarai sai yaki nuna alamar Karaya a fuskarsa sannan ya zare takobinsa, ya fuskanci wadannan Dakaru guda goma..
Koda jama'a suka ga haka sai dayawa daga cikinsu suka fara kuka saboda tunanin irin kisan gillar da wadannan DAKARUN zasuyi Masa, domin Ido ba mudu bane Amma yasan kima.
Nan take Sarki Zurmatu ya Bada Umarnin a buga Gangar fara GASA.
Nan take aka buga wannan tafkekiyar ganga, Wanda Kararta ya cika filin Gasar gaba Daya..
Nan take wadannan Dakarun sukayo Kan SADAUKI MARGIM da nufin suyi gutsin-gutsin da sassan jikansa, Shima sadauki MARGIM sai ya tare su tun gabanin suzo gareshi..
Kaico hakika bala'i ba a sa masa rana kuma tashin hankali yafi gaban Yaro.
Yayinda wadannan Dakarun suka falfalo da gudu izuwa ga sadauki MARGIM sai suka daka wani wawan tsalle da nufin suna duruwa suyi Masa luguden duka farat Daya su halaka shi...
Kwatsam ba zato ba tsammani sai aka ga sadauki MARGIM ya................
Kash!! Laifin dadi karewa..
Abdulaziz Sani Madakin Gini
Shehu Usman
Abdulaziz Sani Madakin Gini
Abdulaziz Sani Madakin Gini
Abdulaziz Sani Madakin Gini
Abdulaziz Sani Madakin Gini
Abdulaziz Sani Madakin Gini
Fatima Rabiu Ummu Affan
Xeemat
Abdulaziz Sani Madakin Gini
Mukhtar Kwalisa
Abdulaziz Sani Madakin Gini
by Queen Meerah
by Binta Rabiu Ali Laraba Agege
by Nazir Adam Salih
by Maryamah
by Hafsat Sodangi
by Sayyada Tahir
by Khadijat Sani Gana
by Momyn Fareesa,Maman Fareesa
by Unknown
by Hafsat Sodangi