An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
**GASAR JARUMTAKA**
LITTAFI NA 1
PART A
Marubuci: Najibullah Muhammad legends ✍️
Typing/posting Najibullah Muhammad 🥷🥷
Note:- Wannan littafi ne kirkirarre Wanda ni Najibullah Muhammad na rubuta, Kuma Yana da Volume har guda 20.
Kowane volume Daya matsayin littafi daya yake.
Saboda haka ban yarda wani ko wata ya Sarrafa wannan littafi izuwa kowace siffa ba, batare da izinina ba.
Daga karshe Ina maku fatan Alkhairi tare da fatan Allah yasa littafin Nan ya Nishadantar, fadakar, ilimantar da amfanar da duk Wanda ya Karanta shi.
Muna fatan Allah ya taimakemu...
Kimanin shekaru dubu uku da Dari uku da arba'in da bakwai da suka wuce, anyi wata kafceciyar Kasa Mai tsananin girma da fadi wadda ta bunkasa a bangaren tattalin arziki, karfin Mulki, Kasuwanci, jarumai da bokaye da matsafa, ana kiranta da suna BALLUS.
Birnin BALLUS na karkashin mulkin wani Gawurtaccen Sarki ne, Kuma SADAUKI UBAN SADAUKAI Kuma kyakkyawa na gaban kwatance Wanda shekarunsa Basu wuce hamsin ba, ana kiransa da suna ZURMATU.
Sarki Zurmatu ya kasance adalin Sarki domin kowa Yana Jin dadin yadda Sarki Zurmatu ke tafiyar da mulkinsa a Kasar, domin Bai yadda da zalunci ba ko kadan. Amma Kuma Yana da tsananin rashin Imani ga duk Wanda ya karya doka a garin. Haka Kuma Sarki Zurmatu mutum ne Mai son Nuna Jarumtaka, wannan yasa duk Wanda yake son samun kusanci da shi to dole ne ya kasance Gawurtaccen jarumi na gaban kwatance.
A rayuwar Sarki Zurmatu babu abinda yake bakanta Masa rai kamar yaga jarumin da ya fishi Jarumtaka, domin a dalilin haka ne yasa ya Ziyarci kasashe Dari bakwai da saba'in da bakwai domin koyon salon yaki iri-iri ta yadda zai zama Gawurtaccen jarumin da babu Wanda zai iya nasara akanshi.
Tun daga ranar da Sarki ya kammala karbar horon yaki a kasashe mabambanta, sai ya tattara gaba dayan 'yan majalisarsa akan bukatar cewa, Yana son a rinka shirya GASAR JARUMTAKA duk bayan kwanaki bakwai.
Batare da wata jayayya ba gaba dayan 'yan majalisar suka amince.
Nan take Sarki Zurmatu ya Mike yayi masu bayanin yanda yake son Gasar ta kasance..
Wato za'ayi shela akan ana gayyatar duk wani jarumi da yake ji da Kansa, da Wanda yake cikin birnin BALLUS da sauran jaruman kasashe masu makwabtaka duk ana gayyatar su.
YANAYIN GASAR ZAI KASANCE.
Da farko za'a ware jaruman Gasa gefe guda, sannan za a rinka Kiransu Daya bayan Daya suna Gwabzawa da wasu Dakarun Sarki na musamman wadanda aka tabbatar da cewa inbanda Sarki Zurmatu babu Wanda yakai su Jarumtaka a duk fadin nahiyar, domin komai tsananin Jarumtakar mutum indai ya hadu da su to cikin dakiku kadan suke yin fata-fata dashi.
Wadannan Dakaru suna da tsananin yawan gaske, domin musamman SARKI ZURMATU ya je har Kasar Rum ya siyo irinsu sama da guda Milyan goma, dukkansu sun kasance Karti majiya karfi, domin gaba dayan jikinsu a murde yake tamkar karafuna ne aka lillika a sassan jikinsu.
Sannan Kuma sun kasance jibga-jibga tamkar samudawa.
Hakika wadannan Dakaru sun cika jarumai kuma ababen tsoro, domin komai yawan abokan gaba da zarar sunyi arba dasu, Nan take suke sumewa wasu Kuma su haukace saboda tsananin razana.
Tun daga ranar da Sarki Zurmatu ya siyo wadannan Dakaru ya kawo su birninsa, sai ya sa aka Gina masu wani tafkeken gari tare da gine-gine masu tsananin kauri da kwari, babu abinda suke yi a cikinsa face bawa kansu horon yaki da Kuma zaman jiran Umarnin Sarki.
Musamman Sarki Zurmatu yayi tanadin wadannan Dakaru domin kawai wannan Gasa.
Sarki Zurmatu yaci gaba da cewa, za'a rinka Gabar da wannan babbar Gasa ce a babban filin Fadarsa Wanda a Kalla zai iya daukar sama da mutum Milyan Dari saboda tsananin girmansa, Kuma ba'a yarda da yin Amfani da tsafi ba a yayin gudanar da wannan Gasa, haka Kuma ba a yarda da shiga cikin filin Gasa ba, muddin mutum baya daga cikin jaruman Gasa..
Sannan gaba dayan Jaruman Gasar zasu kasance a bangare Daya ne, sa'annan Kuma za'a ware Dakarun Sarki guda Dari a gefe Daya.
Daga cikin guda Dari na Dakarun Sarki za'a ware guda goma su shigo cikin Gasa, sannan a kira jarumin Gasa guda Daya domin tunkararsu, idan ya samu nasara akan guda goman Nan, sai a karo Masa guda Ashirin, Suma idan ya samu nasara akansu sai a karo Masa guda talatin da haka da haka har ya gama da duka darin..
Duk jarumin da ya samu nasarar kashe wadannan Dakarun Sarki guda Dari to Sarki yayi mashi Alkawarin biya Masa dukkan bukatar da yake da ita, sannan Kuma zai mallaka Masa 'yarsa aure.
Yayinda sauran 'yan majalisar Sarki sukaji wannan Batu, gaba dayansu sai suka mimmike tsaye saboda tsananin razana, domin sun San cewa Koda za'a Tara gaba dayan Jaruman duniya su tarar wa wadannan Dakarun na Sarki, to tabbas cikin kankanin lokaci Dakarun Sarki zasu Karar dasu, to tayaya ake tunanin akwai jarumin da zai iya ganin bayan wadannan za6a66un Dakarun guda Dari?
Cikin girmamawa Waziri MIKILAS ya dubi Sarki fuskarsa cike da damuwa yace, ya shugabana shin kanason ayi ta asarar miyagun rayukan Al'umma ne haka kawai, domin na tabbata cewa duk jarumin da ya shiga wannan Gasa mutuwa zayyi, domin kowa yasan cewa karo da wadannan Dakaru naka tamkar mutum ya siyo mutuwa ne da kudinsa ya rataya a wuya.
Koda Sarki yaji wannan Batu na Waziri, sai ya kyalkyale da dariya sannan ya dubi Waziri ya ce, ya Kai Waziri kayi sani cewa duniya da fadi take haka ma abin cikinta yawa gareshi, tabbas Ina ji a jikina cewa akwai jarumin da zai iya lashe wannan Gasa, Kuma a halin yanxu babban burina shine nayi Ido biyu da wannan jarumi domin mu gwabza ni da shi domin ganin Wanda zai samu nasara.
Don haka na Umarce ka, da ka sa a baza sanarwa birni da kauye akan ana gayyatar duk Wanda ya amsa sunansa na Jarumi zuwa wajen wannan Gasa Nan da kwana uku, tare da sanar da kowannensu sakamakon da zai samu yayinda ya lashe wannan Gasa.
Koda gama fadin hakan sai Sarki ya sallami taro kowa ya kama gabansa.
Waziri MIKILAS kuwa tunda ya rabu da Sarki Zurmatu sai ya tattaro duk Dakarun da yake ji dasu, sannan ya rubuta masu takardu masu dauke da gayyatar duk Wanda ke son shiga wannan Gasa, tare da Umarnin cewa kowa yazo daga Nan zuwa kwana biyu.
Nan da nan wadannan Dakarun wazirin guda dubu goma suka fantsama cikin duniya kowane yayi bangaren shi domin isar da Sakon Sarki.
A yammacin Kasar BALLUS wato inda SARKI ZURMATU ke Mulki kuwa akwai wata tafkekiyar Kasa Mai madai-daicin girma wadda wani Azzalumin Sarki ke Mulki.
Shidai Wannan Sarki ana kiransa da suna FALWAN.
Sarki FALWAN ya kasance gabjejen Kato na gaban kwatance Kuma Mai mummunar siffa, Wanda mutum Kan iya amai idan ya cika kallon fuskarsa saboda tsananin muninta.
Kamar yadda fuskarsa take mummuna haka Zuciyarsa take, domin komai kankantar laifi idan Mutum yayi Masa to hukuncin kisa ne, ko Kuma daurin Rai da Rai a gidan wani bala'e'en kurkunsa Wanda ya Saka Sojoji guda dubu Dari domin tsaron fursunoni.
Duk Wanda tsautsayi yasa aka kaishi wannan gidan kurkukun to har abada ko Gawarsa bazata fito ba, sai dai a bar gawar Nan ta ru6e ta zagwanye har kasusuwan suyi kwarangwal sannan a kwashesu akai wani daki na musamman da akayi domin tsatsube-tsatsuben duk wani abu da ya shafi rayuwar Sarki da mulkinsa.
SARKI FALWAN na da wani hatsabibin Yaro wani yayi kaurin suna wajen Zalunci da bakar zuciya, bugu da Kari Kuma gashi Jarumi na gaban kwatance domin mutane gani suke ma kamar yafi mahaifinsa SADAUKANTAKA, musamman ganin yanda yake iya yin abubuwan al'ajabin da duk nahiyar babu Mai iya yin kwatankwacinsa.
Saboda tsananin Jarumtakar Yarima FAZAMAL IBN FALWAN shi kadai Yana iya tunkarar mayaka Dari batare da makami ba, Kuma duk ya samu nasarar kakkaryasu batare da Daya daga cikinsu ya samu nasarar Koda lakutar jikinsa ba.
A rayuwar Yarima FAZAMAL babu abinda yake so sama da 'yar SARKI ZURMATU wato GIMBIYA MARITA, domin tunda yake sau Daya ya taba yin arba da kyakkyawar fuskarta a cikin madubin matsafin Bokan mahaifinsa, Kuma tun daga wannan lokacin soyayyarta da Qaunarta da begenta sukayi dirar mikiya a cikin zuciyarsa, ya zamana cewa hatta barci baya yi balle cin abinci saboda tsananin Qaunarta da yakeyi.
Kuma ba komai ne ya kawo hakan ba, face tsananin kyawunta GIMBIYA MARITA Wanda ya wuce misali, domin komai taurin zuciyar mutum indai yayi arba da ita, to take yake kamuwa da tsananin Qaunarta.
Kai saboda tsananin kyawun GIMBIYA ne yasa Sarki ya Sanya mata matakan tsaron da duk duniya babu wani jarumi daga jinsin bil'adama ko aljanu da ya Isa yazo inda take, Kai hatta hadiman gidan sarautar Basu Isa su ganta ba, sai dai wasu kuyangi na musamman masu kula da ita.
Dalilin dayasa Yarima FAZAMAL yayi arba da kyakkyawar fuskar GIMBIYA MARITA shi ne, watarana ne SARKI FALWAN ya kira bokansa domin yayi Masa akan gano hanyar da zai bi domin ya samu nasarar kashe Sarki Zurmatu ya Haye KARAGARSA.
tuntuni Daman Sarki FALWAN bashi da babban burin da ya wuce ace yaci birnin BALLUS da yaki Amma Abu gagara kasancewar SARKI ZURMATU ya fishi dimbin mayaka da Kuma miyagun makaman da ko a tahiri ba'a ganin irinsu ba.
Haka Kuma shi kanshi Sarki Zurmatu masana sun tabbatar da cewa SADAUKI NE NA GASKE Wanda ake tunanin duk duniya babu Wanda ya Isa yayi gaba da gaba da shi na tsawon dakika Dari batare da ya kai shi Kasa ba, komai tsananin Jarumtakar mutum kuwa.
Haka Kuma a bangaren karfin sihiri Sarki Zurmatu na da wasu zakakuran bokaye wadanda duk nahiyar babu Wanda ya Kai su karfin sihiri.
To a cikin binciken da Bokan Sarki FALWAN ne, madubin matsafinsa ya hasko fuskar GIMBIYA MARITA, inda Bokan ya tabbatar masu da cewa akan su kwantar da hankalinsu, Nan gaba kadan SARKI ZURMATU sai shirya wata GASAR JARUMTAKA wadda akayi alkawarin duk Wanda ya lasheta to shi ne zai zamo mijin GIMBIYA MARITA.
Koda gama ganin wannan Ala'marin sai SARKI FALWAN ya tuntsire da mahaukaciyar dariya domin a tunaninsa ya gano hanyar da zai kwace mulkin Kasar BALLUS salim-alin batare da wata wahala ba.
Wato idan shi ko dansa Yarima FAZAMAL ya lashe Gasar sai ya aura Masa GIMBIYA shikuma ya Haye KARAGARSA sannan ya barwa dansa mulkin wannan Kasar yaci gaba da Mulki.
Bayan kamar wata bakwai ne da faruwar wannan Ala'mari, Sarki FALWAN na zaune akan KARAGARSA Yana gudanar da harkokin Mulki na rashin Imani, kawai sai aka ga badakaren Birnin BALLUS ya ratso ta tsakiyar fadar rike da wata takarda.
Nan take fadar tayi tsit kowa ya zuba Masa idanu har ya zo gaban Sarki, Sannan ya sauko daga Kan dokinsa ya fadi yayi gaisuwa Sannan ya ce, ya shugabana Sako ne daga Sarkin Duniya wato Sarki Zurmatu na birinin BALLUS Wanda yake gayyatar duk wani jarumi na birninka izuwa wata Kasaitacciyar Gasa ta musamman tare da sakamako Mai tsoka ga duk Wanda ya lashe wannan Gasa.
Sannan Kuma ya ce, duk jarumin da yake sha'awar shiga Gasar to lallai ya halarcin Birnin BALLUS Nan da kwana biyu.
Badakaren na gama fadin hakan sai ya kama dokinsa ya hau sannan ya juya da baya ya sukwane shi.
Koda Jin wannan Albishir da Sarki FALWAN yayi, sai ya kamu da tsananin farin ciki Bai San ma sa'adda ya tuntsire da dariya ba.
Nan take ya Bada Umarnin a shirya masu tafiya shida Yarima FAZAMAL tare da Dakaru 'yan rakiya guda dubu saba'in.
Nan da aka kama shiri, washe gari tunda sassafe ya barwa wazirinsa rikon Kasa sannan suka kama hanyar birnin BALLUS.
A can birnin BALLUS kuwa, tuni labari ya cika ko'ina akan gabatar da wannan Gasa, domin kowa ya kagara ranar da za'a fara wannan Gasar tazo domin ya morewa idanunsa kallon yadda jarumai ke gwagwarmaya.
Ai kuwa cikin kankanin lokaci birnin BALLUS ya cika makil da bakin jarumai masu sha'awar shiga Gasar.
Duk jarumin da yazo don shiga wannan Gasar to Nan take ake yi masa iso wajen alkalan Gasa domin ya biya kudin shiga Gasa sannan su rubuta sunanshi.
A cikin kwana biyu kacal sai da aka samu manyan jarumai mabambanta wadanda suka shiga GASAR JARUMTAKA guda dubu tamanin.
Gaba dayan alkalan Gasar sun mamakin yadda akayi Jaruman Gasar sukayi yawa haka..
Abinda Basu sani ba shi ne, da yawan Jaruman Gasar Sun kasance jinsin ALJANU da Kuma shahararrun bokaye, suka rikide izuwa jinsin bil'adama domin samun damar lashe wannan Gasa don mallakar GIMBIYA MARITA.
Kash! Hakika masu iya magana sunyi Gaskiya da suka ce, rashin sani yafi dare duhu.
Tabbas inda wadannan Jaruman Gasar sun San abinda zai biyo baya da basuyi gangancin shiga wannan Gasar ba, domin bala'in da ke cikinta yafi karfin tunkarar duk mutanen duniya ka yake su.
A cikin kwana na biyu ne, da yamma sai ga SARKI FALWAN tare da dakarunsa sun shigo birnin BALLUS, suna zuwa Sarki Zurmatu yayi masu iso cikin tsananin farin ciki.
Batare da Bata lokaci ba, Sarki Zurmatu yayi Umarni aka Kai su masaukinsu tare da Kai masu abinci da abun Sha iri-iri.
Nan da Nan Sarki FALWAN ya aiki wani badakarensa izuwa wajen alkalan Gasar domin ya biya masu kudin shiga Gasa da shi da dansa Yarima, da Kuma wasu zakakuran dakarunsa wadanda suka kasance manyan jarumai na gaban kwatance guda dubu.
Nan take wannan badakaren ya cika Umarni, cikin 'yan dakiku kadan ya dawo.
Kashe gari tunda sassafe kowa ya fara tahowa filin Gasa, cikin kankanin lokaci filin Gasar ya cikar makil babu masaka tsinke.
Ya zamana cewa in Banda da'irar da Jaruman Gasar zasu fafata sai Kuma kujerun da Sarkin Zurmatu da GIMBIYA MARITA da Kuma sauran SARAKAI irinsu FALWAN da Yarima FAZAMAL babu sauran wajen zama ko tsayuwa.
Nan da Nan batare da Bata lokaci ba, bayan Sarki Zurmatu da mabiyansa sun hallara sai ya Bada Umarnin a fara Gasa..
Nan take aka kira wani Gwarzon jarumi daga cikin tawagar Jaruman Gasar ana kiransa da suna MARGIM, sadauki MARGIM ya kasance jarumi ne Mai dakakkiyar zuciya tare da Jarumtaka ta ban al'ajabi, sannan Yana da tsananin sa'a da rabo bisa duk irin abinda yasa a gabanshi.
Koda sadauki MARGIM ya fito filin Gasa sai aka hau yi masa shewa da jin-jina kasancewar shi ne jarumi na farko da zai fara fafatawa.
Nan take aka kira wadannan Dakarun Sarki guda Dari suka shigo filin Gasa, sannan aka waro guda goma daga cikin su suka zo gaban sadauki MARGIM suka tsaya.
Koda mutane sukayi arba da wadannan DAKARUN NA SARKI sai suka firgitse, da yawan mutanen ji sukayi kamar su ruga saboda tsananin razana, Kai hatta dayawa daga cikin jaruman Gasar sai da sukaji hantar cikinsu ta kada saboda tsananin razana, Nan take sukaji nadamar shiga wannan Gasa tazo masu domin sun tabbatar da cewa sun sayi ajalinsu ne da kudinsu.
Koda sadauki MARGIM yayi arba da wadannan samudawan DAKARUN sai yaji zuciyarsa ta buga da karfi, Amma saboda dakakkiyar zuciya irinta mazan kwarai sai yaki nuna alamar Karaya a fuskarsa sannan ya zare takobinsa, ya fuskanci wadannan Dakaru guda goma..
Koda jama'a suka ga haka sai dayawa daga cikinsu suka fara kuka saboda tunanin irin kisan gillar da wadannan DAKARUN zasuyi Masa, domin Ido ba mudu bane Amma yasan kima.
Nan take Sarki Zurmatu ya Bada Umarnin a buga Gangar fara GASA.
Nan take aka buga wannan tafkekiyar ganga, Wanda Kararta ya cika filin Gasar gaba Daya..
Nan take wadannan Dakarun sukayo Kan SADAUKI MARGIM da nufin suyi gutsin-gutsin da sassan jikansa, Shima sadauki MARGIM sai ya tare su tun gabanin suzo gareshi..
Kaico hakika bala'i ba a sa masa rana kuma tashin hankali yafi gaban Yaro.
Yayinda wadannan Dakarun suka falfalo da gudu izuwa ga sadauki MARGIM sai suka daka wani wawan tsalle da nufin suna duruwa suyi Masa luguden duka farat Daya su halaka shi...
Kwatsam ba zato ba tsammani sai aka ga sadauki MARGIM ya................
Kash!! Laifin dadi karewa..
Nima na gaji da typing..
Sai mu hadu a part B don Jin yadda zata kaya..
Daga naku Dan uwanku wato Najibullah Muhammad ke cewa ku huta lafiya🥰🥰🥰✍️✍️✍️🥷🥷🥷🥷🥷**GASAR JARUMTAKA**✍️♥️
LITTAFI NA DAYA 1 ✅
PART B 🤝
MAWALLAFI: NAJIBULLAH MUHAMMAD ✍️♥️
MARUBUCI: NAJIBULLAH MUHAMMAD ✍️♥️🥷🥷
*************************
Lokacin da wadannan samudawan DAKARUN sukayo tsalle da nufin yiwa sadauki MARGIM rubdugu, suyi Masa kisan farat Daya.
Koda Sadauki MARGIM ya fahimci nufinsu sai kawai aka ga ya bugi Kasa da kafarsa guda, yayi sama tamkar an cillashi sama da majaujawa, Nan take wadannan Dakarun suka duro Kasa a lokaci guda tare da Kai wani mummunan duka a Kasa, saboda karfin dukan sai da gaba dayan hannuwansu ya lume a cikin Kasa ya haifar da Rami zururu.
Koda wannan Ala'mari sai hankulan gaba dayan mutanen filin Gasar ya tashi, Kai hatta sauran jaruman Gasar sai da suka firgita ainun saboda sun tabbatar da cewa cin wannan Gasar ba karamin bala'i bane.
Shi kuwa SADAUKI MARGIM Bai Karaya ba, sai ma ya Kara rike takobinsa Kam, sannan ya fuskance su da nufin fafatawa da makami saboda yasan cewa sun fishi karfin damtse nesa ba kusa ba.
Koda wadannan Dakarun suka ga, sadauki MARGIM ya rike takobinsa Kam Kuma ya fuskance su, sai dukkansu suka kyalkyale da dariya domin a zatonsu cikin abinda Bai wuce dakika hamsin ba, zasuyi filla-filla da sassan jikinsa.
Nan take dukkansu suka zaro wadansu lafta-laftan adduna da ke sakale a bayansu, masu tsananin kauri da kaifi wadanda duk abinda aka Sara da su sai ya Rabe gida biyu Koda kuwa Dutse ne.
Kawai sai suka rugo gareshi suna ihu da karaji tamkar Zakin da ya kwana goma Bai ci abinci ba.
Koda ganin haka sai Shima ya tare su Yana Mai falfala azababben gudu, suna haduwa sai suka kacame da MASIFAFFE yaki Mai tsananin ban tsoro Wanda a kowane lokaci lahira na iya yin Bako.
Domin harin da suke kaiwa sadauki MARGIM ya wuce misali, domin kowannensu Yana iya kaiwa sadauki MARGIM Sara da suka sau biyar a cikin dakika goma kacal, Amma babban abinda ya Baiwa jama'ar filin Gasar mamaki shi ne, duk wannan hare-haren da suke kawowa sadauki MARGIM an rasa Koda mutum Daya daga cikinsu da zai iya lakutar jikinsa saboda tsananin zafin namansa da iya zilliyarsa tamkar walkiya.
Nan fa wadannan Dakarun suka tashi hankalin gaba dayan mutanen Dake wajen, domin Karar haduwar Takubbansu da na Sadauki MARGIM ya haddasa girgizar Kasa da kamawar wuta.
Sai da aka shafe sa'a guda da rabi batare da Daya daga cikinsu ya samu nasarar komai ba, babban abinda ya bawa DAKARUN SARKI mamaki kenan, domin a tarihin rayuwarsu Basu taba haduwa da hatsabibin jarumin da suka gagara hallakashi a Kasa da dakika hamsin ba, Amma yau gashi su goma kuma sama da sa'a Daya da rabi Amma sun Kasa hallaka mutum Daya.
Nan take dukkansu ransu yayi mummunan 6aci, suka yo kukan kura gaba dayansu suka afka Masa da nufin su yagalgala shi, Kawai sai aka ga SADAUKI MARGIM ya daka wani wawan tsalle yana Mai daga takobinsa sama, cikin tsananin shammace da zafin nama sai kawai aka ya laftawa shugaban Dakarun Sara a wuya da nufin ya tsinke Masa Kai.
Amma bisa mamaki sai yaga ko Kwarzanewa bayyi ba, domin ji yayi tamkar ya sari Dutse.
Kafin yayi wani yunkuri tuni shugaban Dakarun yayi Masa wani wawan mangari a Fuska, saboda karfin dukan sai da SADAUKI MARGIM yayi tafiyar dakika Dari biyar a sama sannan ya fado Kasa a wani mummunan yanayi Mai kama da na Suma ko shurawa baya yi.
Koda ganin haka sai shugaban Dakarun ya kyalkyale da wata irin mahaukaciyar dariya Mai nuna alamar nasara, kawai sai ya dubi Daya daga cikin yaransa yace yaje ya saro mashi Kan SADAUKI MARGIM.
Cikin tsananin zumudi wannan badakaren ya ruga da nufin cika Umarni, Yana zuwa kusa da Sadauki MARGIM sai ya daga falleliyar Addarsa da nufin fille Masa Kai.
Kwatsam ba zato ba tsammani, sai aka ga SADAUKI MARGIM ya yunkara cikin zafin nama sannan ya doke Kasa da hannayensa ya daga kafafunsa guda biyu ya bugi kirjin wannan badakaren, saboda karfin dukan sai da hakarkarinsa na hagu suka karye ji kake Kararas tamkar ana karya Kara.
Kawai sai aka ga SADAUKI MARGIM ya fizge takobin wannan badakaren sannan ya fille Masa Kai.
Nan fa filin Gasar ya rude da shewa da yiwa sadauki MARGIM jin-jina kasancewar yayi babbar bajintar da babu Wanda ya taba yin irinta.
Shi kuwa Sarki Zurmatu mamaki ne ya turnuke shi, saboda ganin yadda Sadauki MARGIM yake da tsananin Jarumtaka tamkar ba jinsin bil'adama ba.
Nan take hankalinsa ya dunguzuma domin Bai taba ganin sadauki Mai tsananin karfin damtse da zafin nama kamar sadauki MARGIM ba.
Nan take ya kudurce a ransa cewa lallai sai yayi zuzzurfan bincike akan Sadauki MARGIM domin sanin ko shi wanene.
Ala'marin SARKI FALWAN kuwa da Yarima FAZAMAL dukkansu fuskarsu babu annuri Kuma zuciyoyin su tafarfasa sukeyi saboda tunanin cewa kamar SADAUKI MARGIM na iya lashe wannan GASAR TA JARUMTAKA, saboda ganin irin tsananin sa'a da rabon da yake da ita.
Nan take suka kudurce a ransu cewa lallai kota wane Hali sai sunga bayan sadauki MARGIM, domin idan suka sake ya lashe wannan GASAR to shikenan duk burinsu ya rushe.
Ala'marin wadannan Dakarun Sarkin kuwa, cikin tsananin mamaki Basu San lokacin da suka tsaya cak, Sannan suka kurawa jarumi margim idanu ba.
Domin a tarihin rayuwarsu ba a taba samun wani mahaluki da ya taba yi masu irin wannan Barnar ba.
Nan take dukkansu guda Taran, suka takarkare suka kwarara wani uban ihu Mai cike da ban tsoro, Karar wannan ihu ta cika birnin gaba Daya.
Kawai Nan take suka rugo izuwa kan SADAUKI MARGIM.
Shima ya tare su rike da wannan Adda ta badakaren da ya kashe, suna haduwa sai ya dage iya karfinsa Yana saran Dakarun da wannan Addar, Amma abinda ya Kara bashi mamaki shi ne ko Kwarzanewa jikinsu baya yi.
Abinda Bai sani ba shi ne, wadannan Dakarun duk duniya babu wani makami da zai iya Huda jikinsu, duk makamin da kaga ya
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 1 Chapter of 12