Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
4 / 12
sai ya duro akan Daya daga cikin Aljanun Nan take Kaftawa Aljanin Sara a ka, take Takobin ta lume cikin Kan, ta faskarashi biyu sai gashi Aljanin ya sulale Kasa matacce ko shurawa Bai Kara Yi ba. Nan fa Sarki Zurmatu ya wanzu a tsakanin Aljanun Yana Mai Kai masu mugun Sara da suka cikin tsananin zafin nama juriya da bajinta tamkar na tauraruwa Mai wutsiya. Nan da nan Sarki Zurmatu ya wanzu Yana Mai Kai masu hari ta ko'ina cikin kankanin lokaci ya kashe sama da ALJANU Dari da Ashirin. A wannan lokaci kowa ya zubawa SARKI ZURMATU Ido don tsananin mamakin irin Jarumtakarsa, tabbas Basu taba tunanin cewa JARUMTAKAR SARKI ZURMATU takai haka ba, lallai ya cancanci a jin-jina Masa. A bangaren Shugaban Aljanun kuwa, Koda ya hango irin 6arnar da SARKI ZURMATU ke masu shi kadai sai ya fusata ainun. Nan take ya daka tsawa kowa ya Dakata sannan ya Tako yazo daf da Sarki Zurmatu yace, tabbas ka cika sadauki na gaban kwatance, to Amma kayi sani komai Sadaukantakarka ni ne Nan zan zare maka ruhin numfashi domin na gagari duk Jaruman duniya da duk Sadaukan Duniya. A gaban dayan nahiyar Aljanu ma sun rasa yadda zasuyi Dani ballantana ku bil'adama don haka tabbas a yau din zanyi maka mummunan kisan gilla ta hanyar ciccisge sassan jikinka Daya bayan Daya har kayi mutuwar wulakanci. Koda Jin wannan batu sai Sarki Zurmatu ya bushe da dariya Yana Mai daka ma shugaban Aljanun tsawa sannan ya ce " Kai wannan takadarin Aljani Ina Mai gargadinka da ka kiyayi bil'adama domin mun wuce duk Inda ku ke tunani. Na rantse da karfin mulkin KARAGATA komai jarumtakarka a yau sai na kawo karshenka. Koda gama wannan Batu sai shugaban bakaken aljanun Nan ya bawa sauran Dakarun Aljanun Umarni akan cewa lallai su Afkawa wadancan Jaruman Gasar su tabbatar sun hallaka kowa a cikinsu. Cikin zafin nama yayo Kan Sarki Zurmatu shi kadai, Nan take Shima Sarki Zurmatu ya tare shi cikin mugun nufi. Suna haduwa sai suka ruguntsume da masifaffe azababben yaki mai matukar ban tsoro suka wanzu suna masu kaiwa junansu Sara da suka cikin juriya da bajinta Kai kace jikinsu ba na jini da tsoka bane. Cikin kankanin lokaci suka tashi hankalin duk wata halitta Dake rayuwa a wajen. Domin yakin yayi Tsamari ainun, ta yadda ko hangosu ba'a iya yi sakamakon Kura da ta turnuke su, ba abinda ake gani face gilmawar makamai yayin Kai Sara da suka. Wohoho! Tabbas idan bala'i da masifa suka wanzu a wuri, to dole ne zaman lafiya ya tattara nasa'i nasa yayi kaura daga wurin. Yayinda bala'i yayi bala'i sai dukkansu suka ja da baya suna haki kowannensu na tunanin dabarar da ya kamata yayi domin ya samu nasara akan Abokin gwaminsa. Bayan shudewar wasu 'yan dakiku sai suka Kara yunkurowa da dukkan karfinsu da nufin ayita ta kare ko a mutu ko ayi Rai. Cikin mugun nufi kowane daga cikin su ya daka tsalle sama tare da kawo mugun hari da nufin su hallaka juna. Takobin Sarki Zurmatu ta nufi wuyan Shugaban Aljanun da nufin ya tsinke Masa Kai, cikin tsananin zafin nama na gaban kwatance ya kaucewa harin da dukkan karfinsa Amma duk da haka sai takobin ta Dan yankeshi a wuyansa. Shima Kuma ya kaiwa Sarki Zurmatu mummunan Sara a ciki da nufin ya tsarge shi gida biyu, SARKI ZURMATU yayi Amfani da dukkan zafin namansa ya goce Amma duk da haka sai da takobin tayi Masa rauni a Saman cibiyarsa. Ba shiri dukkansu suka rikito Kasa suna masu dafe inda suka yiwa junansu rauni. Koda kowannensu ya dafa jikinsa yaga jini, sai ransa ya Baci zuciyarsu ta harzuka, Nan da Nan suka sake ruguntsume da wani sabon masifaffen yaki mai tsananin ban tsoro. A bangaren Jaruman Gasar Sarki Zurmatu kuwa da sauran Dakarun Aljanun nan, bayan sun ruguntsume da masifaffen yaki, Nan da nan sai suka cakude suna masu kaiwa junansu Sara da suka, ya zamana kowa na Neman hallaka Abokin gwaminsa kota wane Hali. Duk da cewar Dakarun Gasar sun lillinka Aljanun yawa, Amma sai suka Kasa kashe Koda Daya daga cikinsu, domin Aljanun sun fisu zafin nama nesa ba kusa ba, kafin Daya daga cikinsu ya kawo Sara sau Daya to su sun kawo sau biyar. Kuma a duk sa'adda suka kawo Sara wani kare saran sai yaji tamkar an wurgo Masa wani Katon Dutse saboda tsananin karfin saran Aljanun, domin mutum har durkushe Kasa yake a yayin tare saran. Wannan yasa cikin kankanin lokaci ALJANUN suka kuntata Dakarun Gasar har suka gano lagonsu suka fara kashe su. Bayan kamar shudewar sa'a biyu cur sai gashi Aljanun sun kashe sama da DAKARUN GASAR guda dubu goma.. Wannan yasa Jaruman Gasar da Sarki FALWAN da Boka RAKUL suka hada karfi da karfe wuri Daya domin yakar Aljanun. Boka RAKUL ya rufe idanunsa Yana Karanta wadansu dalasiman tsafi ya tofa a hannuwansa na hagu da dama, Nan take sai wata zabgegiyar Adda ta wanzu a hannunsa na hagu, irin Addar wadancan DAKARUN GASAR JARUMTAKA na birnin BALLUS, a dayan hannun Damansa kuwa sai wata majaujawar karfe Mai fitar da wuta ya wanzu. SARKI FALWAN, BOKA RAKUL, DA SAURAN JARUMAN GASAR, suka hada karfi da karfe suka yiwa ragowar Aljanun Kawanya suna masu Yi masu kisan wulakanci. Domin a wannan lokacin an masu Taron dangi ta yadda kota ina hari ake Kai masu, duk Aljanin da Boka RAKUL ya kwala ma wannan majaujawar karfen aka sai dai kaga Kan ya dagwargwaje tamkar an taka tumatur. Cikin abinda Bai wuce sa'a Daya da rabi ba, suka samu nasarar kashe gaba dayan Dakarun Bakaken Aljanun, ya zamana cewa babu dayansu da yayi saura a tsaye face SHUGABANSU WANDA YAKE FAFATAWA DA SARKI ZURMATU. Tabbas su Boka RAKUL da Sarki FALWAN sun taka babbar rawa a wajen kashe Dakarun Aljanun nan, duk da Sarki FALWAN na goye da Yarima FAZAMAL a bayansa, Amma hakan Bai hanashi yaki ba, domin yadda yake Sarrafa jikinsa tamkar ma babu kowa a jikinsa. A bangaren su Sarki Zurmatu kuwa har yanzu suna nan suna ta fafatawa a tsakaninsu, duk da cewa Sarki Zurmatu yayi matukar gajiya ainun Amma hakan Bai hanashi yaki ba, sai da suka Kara shafe sa'a guda suna bakin Artabu Amma Basu samu nasarar juna ba, cikin bacin Rai da shammace Sarki Zurmatu ya yi tsalle sama ya kaiwa SHUGABAN Aljanun wani irin mummunan Sara aka da nufin ya tsargeshi gida biyu, kafin takobin takobin Sarki Zurmatu ta sauka akan shugaban Aljanun ba zato ba tsammani sai kawai akaga wani Jan haske Mai tsananin gudu ya taho daga sama ya Doki kirjin Sarki Zurmatu, saboda karfin dukan sai da Sarki Zurmatu yayi sama yaje ya gwaru a jikin wani Dutse, take hannunshi guda ya kare kawai sai ya fado Kasa sumamme. Cikin tsananin mamaki sai SARKI FALWAN da Boka RAKUL da sauran jaruman Gasar suka rugo domin kawowa SARKI ZURMATU dauki.. Ba zato ba tsammani kawai sai suka ga BOKA GARGUS tare da wasu gungun bakaken aljanun wadanda adadinsu yakai dubu Dari, yana Mai kyalkyala wata irin dariyar mugunta.. Kafin wani daga cikinsu yayi wani yunkuri tuni ya nuna Sarki Zurmatu da hannun Hagu, faruwar hakan keda wuya sai akaga wata sarkar tsafi ta kanannade Sarki Zurmatu ta matse shi tamau, kawai sai ya Kara nuna dai-dai inda Sarki Zurmatu yake Nan take wani Kejin tsafi ya wanzu tare da Sarki Zurmatu a cikinsa. Mu hadu a GASAR JARUMTAKA na 3 part B don Jin cigaban wannan Kayataccen labari Mai dadi, Wanda ni Najibullah Muhammad na rubuta Kuma nake kawo maku shi. Anan nake cewa ku huta lafiya ✍️✍️✍️👌👌🤝🤝🤝**GASAR JARUMTAKA** LITTAFI NA UKU ✍️✍️ PART B ✅✅ MARUBUCI: NAJIBULLAH MUHAMMAD ✍️✍️ POSTING NAJIBULLAH MUHAMMAD 🥷🥷 Lokacin da Boka GARGUS ya bayyana da wannan Dakarun Aljanun guda Dari, sai kawai akaga ya takarkare ya kyalkyale da wata mahaukaciyar dariya, sai da yayi Mai isarsa sannan ya dubi su Sarki Zurmatu da Boka RAKUL ya nuna su da dan yatsa sannan ya ce, " ya Kai wannan Sarki kayi sani tabbas ka tafka babban kuskure da har ka biyewa maganganun wannan Bokan naka domin gashi yanxu zanyi maka mummunan kisan gilla da Kai da wannan karamin Bokan naka Mai tunani irin na yara. Cikin fushi Boka RAKUL ya tari numfashinsa Yana Mai daka Masa tsawa sannan ya ce, Hakika masu iya magana sunyi Gaskiya da suka ce, in Ajali yayi kira to babu makawa sai anje, domin yanzu gashi kana zaman zamanka amma ka jefa kanka a rigimar da zaka hallaka kanka a banza a kokarin dakatar da Abunda duk duniya ba Wanda zai iya. Don haka tabbas yau babu abinda zai Hana bamu fitar maka da ruhin numfashi ba. Koda Jin wannan batu sai Boka GARGUS ya Kara kyalkyalewa da dariya a karo na biyu, sannan ya ce ya Kai wannan Boka wai shin da me kake takama ne? Shin bakaga halin da Sarkinku yake ciki ba? Ka tuna cewa a halin yanxu hannun Sarki Zurmatu guda karyayye ne, haka Kuma na tsare shi a cikin Taskar tsafi ta yadda duk duniya babu Wanda zai iya fitar da shi daga halin da na Sanya shi. Ya Kai wannan Boka tabbas ka tafka babban kuskure da har kake Neman ganin bayana, domin na wuce duk yanda kake tunani. Na rantse da Karfin Tsafi a halin yanxu duk duniya babu wani Hatsabibin Boka Kuma Shu'umi kamata, domin sai da na zagaye duniyar mutane da Aljanu na hada manyan sirrikan tsafin da duk duniya babu Wanda ya samu, a halin yanxu sihiri daya ne ya gagareni, wato wannan da kake kokarin mallaka. To kayi sani cewa kayi shuka akan idon makwarwa domin duk wani shiri naku akan tafin hannuna yake. Kuma yanzun Nan zan shafe tarihinku ta yadda har abada baza'a Kara tunawa da ku ba. Koda Boka RAKUL yaji wannan Batu daga bakin Boka GARGUS sai ya fusata, Nan take yayi nuni da Kejin tsafin da Boka GARGUS ya tsare Zurmatu da hannun Hagu da nufin ya tarwatsa Kejin, Amma bisa mamaki sai yaga tsafinsa yaki yin tasiri akan Kejin. Nan fa hankalinsa ya dunguzuma domin ya tabbatar da cewa tabbas Boka GARGUS ba karamin hatsabibi bane. Koda Boka GARGUS ya ga abinda Boka RAKUL yayi sai ya bushe da dariya sannan ya ce Ashe baka yarda da abinda na fada maka ba? Kayi sani cewa yakai wannan Boka nayi amfani manyan Sihiran tsafi wajen tsare Sarkinku wadanda ni ne na kirkiresu da kaina domin tanadin irin wannan Rana. Don haka Koda zaka gayyato duk BOKAYEN DUNIYA bazasu iya lalata wannan sihirin ba. Kafin Boka GARGUS ya gama rufe bakinsa tuni SARKI FALWAN ya tari numfashinsa ta hanyar daka Masa tsawa, sannan ya fuskance shi Yana Mai cewa tabbas faduwar gaba asarar namiji ce, kayi sani cewa duk irin sihirin tsafin da kake takama dashi bazaka iya nasara akanmu ba, Amma idan Kuma kana ganin zaka iya to ka jarraba mugani. Kafin wani daga cikinsu ya Kara cewa wani abu, tuni Boka GARGUS ya nuna wadannan Aljanun da yazo da su yace ku afka masu naga iyakar jarumtakarsu.. Cikin tsananin gudu tamkar na tauraruwa Mai wutsiya Aljanun suka ruga izuwa kan su Boka RAKUL a lokaci guda da nufin su talitse su. Koda ganin haka sai BOKA RAKUL, Sarki FALWAN Wanda ke goye da Yarima FAZAMAL da sauran jaruman Gasar suma suka rugo garesu tun gabanin su riskesu. Ana haduwa aka kacame da wani sabon bala'e'en yaki Mai tsananin ban tsoro da tayar da hankali. Lokacin da aka fara wannan bakin gumurzun sai wancan Shugaban bakaken aljanun Wanda ya tsira daga hannun Sarki Zurmatu, sai yazo gaban Boka GARGUS ya risina cikin girmamawa sannan sai ya sanya hannunsa a cikin wata battar tsafi Dake daure a kugunsa ya zaro sadauki MARGIM da 'yan yatsu biyu kacal sannan ya mikawa Boka GARGUS shi. Cikin tsananin farin ciki Boka GARGUS ya bushe da mahaukaciyar dariya tamkar Wanda aka mallakawa duniya da abinda ke cikinta, sannan ya dubi Shugaban Aljanun ya ce dakyau DURKAS tabbas kayi gagarumin aiki Kuma ka cancanci sakayya ta musamman, don haka zan jiyar da Kai dadin da baka taba ji ba, Kawai sai Boka GARGUS ya dafa kafadar DURKAS da hannunsa guda Yana Mai cigaba da kyalkyala dariyar farin ciki, Nan da nan suka rikide suka zama wani bakin Hayaki suka 6ace. Ala'marin Su Boka RAKUL kuwa, lokacin da wadannan rundunar Aljanun suka yanyamesu suna masu Kai masu Sara da suka da muggan makamai, sai suka wanzu sai na Mai kare saran nasu cikin zafin nama juriya da bajinta sai da aka shafe sa'a guda ana dauki ba dadi sannan ne Boka RAKUL ya Ankara da bacewar Boka GARGUS da Kuma Aljani DURKAS. Koda ganin haka sai ya tabbatar da cewa babu inda suka nufa sai kogon Dutsen Boka GARGUS domin ceton sadauki MARGIM, Nan take Boka RAKUL ya kwarara uban ihu saboda ganin cewa duk shirinsu ya lalace Kuma gashi mawuyacin abu ne su tsira da rayuwarsu daga wannan wadannan Aljanun. Lokacin da aka Kara shafe wata sa'a gudar ana yaki a tsakanin su Sarki FALWAN da wadannan Aljanun sai ya zamana cewa su Sarki FALWAN sun fara gajiya domin dakyar ma suke iya kare kansu. Da wannan dama ce Aljanun sukayi Amfani suka rinka kashe jaruman Gasar tamkar ana sassabe a Gona. Ala'marin Sarki Zurmatu kuwa lokacin da ya farfado daga dogon suman da ya shiga sakamakon buguwa da wannan Dutsen sai ya tsinci Kansa a cikin wani Kejin tsafi Wanda akayi Amfani da wasu mulmulallun Karafuna masu tsananin girma da kauri wadanda babu makamin da zai iya lalata su, kawai sai ya yi yunkurin dauko takobinsa da nufin saran wannan karafun Amma sai ya Kasa sakamakon Jin hannunsa a karye, cikin firgici Sarki Zurmatu ya kwarara uban ihu Mai tsananin razanarwa Amma Kuma babu Mai Jin Karar ihun daga waje. Nan take yayi duba a wajen Kejin domin ganin abinda ke faruwa, ba zato ba tsammani sai yaga wadansu Aljanu na musamman masu tsananin yawa da zafin nama na gaban kwatance sai kashe Jaruman Gasar sa sukeyi, domin sun kashe da guda dubu goma. Nan take kwallar takaici ta zubo daga idanun Sarki Zurmatu ya tabbatar da cewa shikenan dukkan burinsu ya Yanke domin mutuwa zasuyi. Lokacin da yaki yayi Tsamari sai maza suka fara ja da baya domin tsira da rayuwarsu, domin Aljanun sun masu yawa Kuma su ko kadan basa gajiya tamkar wutar lantarki ce jikkunansu. Ana cikin hakane kwatsam sai aka ga wani Mahayin Doki sanye da fararen kaya ya ratso ta tsakiyar Dakarun ya kutsa cikin rundunar Aljanun ya hau su da Sara da suka ba ji ba gani. Wohoho Nan fa labari yasha bamban, domin zafin Naman jarumin ya kasance tamkar walkiya domin duk Aljanin da ya Sara da takobinsa sai aga Aljanin ya kama da wuta ya kone kurmus. Nan take ya cigaba da kisan Aljanun tamkar GOBARA DAGA KOGI ya zamana cewa a gaba dayan Aljanun an rasa Wanda zai dakatar dashi domin ko lakutar jikinsa ma an rasa Wanda zayyi. Kafin a jima ya kashe sama da ALJANU dubu arba'in.. A wannan lokacin tuni SARKI FALWAN, Boka RAKUL da sauran jaruman Gasar sun wadanda adadinsu Bai wuce dubu sittin ba, sun koma gefe guda sun zuba idanu kawai suna kallon irin tsananin Jarumtakar wannan bakon jarumi da yake taimaka masu. Hakika wannan jarumin ya Sha gaban mutane domin Yana da Jarumtaka ta ban al'ajabi tare da tsananin karfin damtse na gaban mamaki, domin duk lokacin da ya naushi Aljani guda sai kaga Aljanin yayi wata irin katantawa a sama tamkar an janye shi da Kugiya, sannan ya banke Aljanu a Kalla guda Dari sun baje a Kasa matattu. Haka Kuma duk Aljanin da ya Sara da takobinsa to Nan take Aljanin yake kamawa da wuta Kurmus ya cinye tamkar an zubawa wuta fetur. Lokacin da aka shafe sama da sa'a uku sai gashi wannan jarumin ya Karar da sama da guda dubu casa'in na Aljanun ya zamana cewa wadanda suka rage Basu wuce dubu goma ba. Ana cikin wannan Hali ne sai kawai akaga Boka GARGUS ya bayyana Tsulum a gaban wannan jarumin cikin mummunar shigar yaki, cikin shammace ya daga wata lafceciyar takobinsa sama ya kaiwa wannan jarumin Sara a wuya da nufin ya fille Masa Kai, cikin tsananin zafin nama jarumin ya kare saran da dukkan karfinsa Amma sai da ya durkushe saboda nauyin saran, domin ji yayi tamkar an Dora Masa katon Dutse, kafin jarumin ya mayar da martani tuni Boka GARGUS ya Doki kirjin jarumin da Kafa, saboda karfin dukan sai da jarumin yayi katantawa a Kasa sannan ya baje a Kasa a matukar galaibace. Koda ganin haka sai Boka GARGUS ya kece da mahaukaciyar dariya sannan ya ce, tabbas ka tafka babban kuskure ya Kai YARIMA USAMA IBN MUSBAHU na birnin NURUL HAYAT. Kayi sani cewa Koda mutanen duniya Kaf zasu taru bazasu iya kwatar jarumi margim daga hannuna ba, gashi yanxu zaka rasa rayuwarka a banza a wofi akan abinda bazai Amfaneka ba ko kadan. Don haka yanzun Nan zanyi maka mummunan kisan gilla irin Wanda ba a taba yiwa wani irinsa ba, domin hakan ya zama izini ga duk mutane masu karambanin shiga abinda Bai shafe su ba. Koda Jin wannan batu, Sai YARIMA USAMA ya yaye mayafin Dake fuskar sa, Nan take hasken musulunci ya bayyana a fuskarsa. Sannan ya murtuke Fuska ya dubi Boka GARGUS a Fusace, ya ce ya Kai wannan Kasurgumin matsafi Wanda ya Bata gaba dayan rayuwarsa wajen koyon Shirka da barna a bayan Kasa, kayi sani cewa lokaci yayi da HASKEN MUSULUNCI zai mamaye ko'ina a fadin duniya. Don haka muddin ire-iren ku suna a doron Kasa to tabbas Shirka bazata gushe ba, don haka nayi rantsuwa da Ubangijina Allah madaukakin Sarki Wanda yayi ni yayi ku Kuma yayi dukkan halittun duniya cewa sai na ga bayan dukkan ire-iren ku saboda barin irinku ba karamin matsala bace a bangaren Addininmu. Yayinda BOKA GARGUS yaji wannan bayani sai takarkare ya kyalkyale da wata irin mummunar dariya Mai kama da kukan Jaki, Sanna ya ce" yakai wannan Jarumi kayi sani cewa duk duniya masu irin addininku ne kadai suka zamo min matsala wajen cikar burina, a bisa wannan dalili ne yasa na Yanke shawarar Karar da gaba dayanku domin cikar burina, Amma bazan samu wannan nasarar ba sai na fara dakatar da SARKI ZURMATU da Kuma BOKA RAKUL bisa ga Kudirinsu na mallakar duniya ta hanyar shirya GASAR JARUMTAKA. Don haka a yau ta kowane Hali sai na halaka ka! Kafin wani daga cikinsu ya Kara cewa wani abu, tuni sun zare zabga-zabgan takubban da ke sakale a bayansu sun falfalo da gudu cikin mugun nufi... Suna haduwa suka kacame da sabon masifaffen yaki mai tsananin ban tsoro Wanda ka iya hallakar da duk abinda ke kusa da su. Nan fa suka wanzu suna masu kaiwa junansu Sara da suka cikin juriya da bajinta tamkar jikinsu ba na jini da tsoka bane. Wohoho! Idan jarumta ta hadu da SADAUKANTAKA to dole ne a tashi hankali 'yan kallo. Nan fa Jaruman biyu suka tashi hankalin Dajin gaba Daya, ya zamana cewa saboda tsananin karfin harin da suke kaiwa junansu ya haddasa guguwa Mai tsananin karfin gaske wadda ta rinka daukar duk abinda ta ci karo da shi tana wurgi da shi. Idan takobin Boka GARGUS ta hadu da ta YARIMA USAMA sai tartsatsin wuta ya tashi, Karar haduwar Takubbansu ya haddasa tsawa a sararin samaniya tamkar hadari ya gangamo a lokacin damina. Nan fa Boka GARGUS yayi iyakar kokarinsa don ganin ya hallaka YARIMA USAMA Amma Abu ya faskara, haka Kuma duk irin tsafin da yake Amfani dashi domin hallaka Jarumi Usama baya tasiri. Sai da suka shafe sa'a bakwai cur suna GUMURZU Amma dayansu Bai samu nasarar yiwa kowa rauni ba, har Takubbansu suka dakushe suka zubar da su, suka ci gaba da naushin juna hannu da kafa. Nan da Nan suka hadawa junansu jini da majina ya zamana cewa dakyar suke iya Kai duka, har faduwa suke suna tashi saboda tsananin galabaita Amma saboda naci da juriya sunki yarda su fadi. Nan take YARIMA USAMA ya shiga Neman taimakon Allah Yana Mai Yi Masa kirari da sunayensa tsarkaka akan ya bashi nasara akan Boka GARGUS. Fara hakan keda wuya sai kawai yaji wani Gagarumin Karfi ya shige shi Kuma duk gajiya da galabaitar da yayi sun gushe. Ba zato ba tsammani sai akaga SADAUKI Usama ya cafko wuyan Boka GARGUS da hannu Daya sannan ya daga shi Yana wutsil-wutsil da kafafu tamkar an rataye bera, sannan sai ya kama hajijiya da shi a sama tamkar Yaro na wasa tsintsiyar laushi, sai da ya jijjiga shi sau arba'in a sama sannan ya fyadashi da Kasa. Saboda karfin kayen sai da sai da Kashin bayan Boka GARGUS ya karye, nan take idanunsa suka zazzaro ya fara kakarin mutuwa, Kawai sai YARIMA USAMA ya fito da wata sharbebiyar wuka ya saita ta dai-dai makoshin Boka GARGUS Sannan ya ce" yakai wannan mushiriki shin zaka Bada gaskiya da Ubangijin musulunci ko kuwa bazaka bayar ba? Cikin kakarin mutuwa Boka GARGUS ya ce na tsane ka da Kai da Addininka, Kuma har abada bazan taba bayar da Gaskiya ga ubangijin musulunci ba, Kuma Koda ka kasheni to akwai milyoyin mutane irina da zasu ci gaba da yakar musulunci da musulm.... Kafin Boka GARGUS ya kammala maganar da yayi nufi tuni Sadauki Usama ya Luma Masa wannan sharbebiyar wukar a makoshinsa, sai ga jini na feshi da Malala a Kasa tamkar magudanar ruwa ta balle.... ME ZAI FARU A TSAKANIN JARUMI USAMA DA SU BOKA RAKUL? SHIN SARKI ZURMATU ZAI KUBUTA DAGA KEJIN TSAFIN DA BOKA GARGUS YA TSARE SHI? SHIN ZA'A CI GABA DA GUDANAR DA GASAR JARUMTAKA? WANENE ZAI LASHE KAMBUN GASAR JARUMTAKA? domin Jin Amsar wadannan tambayoyin sai mu hadu a GASAR JARUMTAKA littafi na hudu Wanda ni Najibullah Muhammad legends🥷🥷 nake maku sallama tare da fatan Alkhairi ✅✅✍️✍️✍️✍️✍️✍️🙏**GASAR JARUMTAKA** LITTAFI NA HUDU 4 ✅ PART A 💯♥️ Wallafar NAJIBULLAH MUHAMMAD ✍️♥️♥️ POSTING NAJIBULLAH MUHAMMAD 🥷🥷🥷 GORON JUMA'A ♥️♥️🥰😍 Lokacin da Sadauki Usama ya Luma wa Boka GARGUS wuka a makoshinsa sai kawai wukar ta Burma makogoran ta bullo ta keyarsa, Nan take ya fara kakarin mutuwa ya fara shure-shure, kawai sai aka ga bakin Boka GARGUS Yana motsi Yana ta Furta wasu kalmomi da ba a fahimtarsu. Faruwar hakan keda wuya sai kawai aka ga SADAUKI MARGIM ya bayyana a sama cikin iska, wasu siraran igiyoyim tsafi sun daddaure shi tamau. Kafin wani daga cikinsu yayi wani yunkuri tuni wadannan igiyoyin tsafin sun tsittsika sassan jikinsa tamkar ansa takobi an sassara shi. Boka GARGUS na gama wannan aiki ne ya kyalkyale da dariya sannan akaga Kansa ya langabe idanunsa sun kakkafe jikinsa ya sandare ya zama gawa. Yana gama mutuwa sai kawai akaga wata iska Mai tsananin karfin tsiya ta Suri Gawar BOKA GARGUS da ta SADAUKI MARGIM ta luluka da su sama cikin gajimare, kafin a kifta Ido tuni sun bace saboda karfin gudun su. Bayan faruwar wannan abun sai YARIMA USAMA ya juyo ga su Boka GARGUS ya fuskance su Yana Mai cewa, yaku wadannan Dakaru kuyi sani cewa ni sunana USAMA BIN MUSBAHU Kuma ni ma'abocin Addinin musulunci ne, Kuma na baro Kasata ne domin na tallata addinina ga mutanen duniya saboda shi ne Addinin gaskiya Wanda babu Shirka da tsafi a cikinsa, don haka Ina so ku Bada gaskiya da Ubangijin musulunci ko Kun rabauta daga rahmarsa tun gabanin Azabarsa ta riskeku. Yayinda su Boka RAKUL sukaji wannan batu sai suka cika da tsananin mamaki, sannan suka ce" ya Kai wannan Jarumi kayi sani tabbas Addininka bakon addini ne a garemu don haka idan har kana so mu karbi Addininka dole sai ka kubutar da Sarki Zurmatu daga cikin Kejin tsafi da Boka GARGUS ya Saka shi, sannan Kuma dole sai dai ka bi mu can birnin BALLUS domin shiga GASAR JARUMTAKA Kuma ka zamo zakaran Gasar sannan ne zamu tabbatar da cewa lallai Addininka ne Addinin gaskiya, Kuma a take zamu karbe shi tare da dukkan jama'ar mu na cikin birnin da wajen birnin. Koda Jin wannan batu sai Yarima USAMA yayi shiru Yana tunani, daga can sai ya dubi su Boka RAKUL ya ce duk naji abinda kuka fada, Kuma tabbas wannan abu ne Mai matukar Sauki a wurin Ubangijina. To Amma tayaya zan tabbatar da cewa lallai zaku tabbatar da maganarku ba zaku yaudareni ba. Koda Jin wannan batu sai Boka RAKUL da su Sarki FALWAN suka dube shi suka ce munyi maka alkawarin tabbatar da maganarmu da zarar ka kammala wadannan abubuwan biyu da Boka RAKUL ya lissafa maka. Nan take SADAUKI USAMA ya yi murmushi sannan ya dubesu ya ce, to ai shikenan sai mu fara aikinmu ko na kammala ayyukan

Chapter 4 of 12