Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
6 / 12
tarihi... Ana cikin hakane Sarkin yaki DURKUL ya tattaro duk Dakarun yaki guda Milyan ARBA'IN suka shigo cikin filin Gasar.. Nan take Sarki Zurmatu ya bayar da Umarnin a Afkawa wadannan shedanun Aljanun... SU WA ZASU SAMU NASARA A CIKIN WANNAN YAKIN? WANENEN ZAI LASHE KAMBUN GASAR JARUMTAKA? DA GASKE BIRNIN BALLUS ZAI ZAMA BIRNIN MUSULUNCI? WANENE ZAI MALLAKI GIMBIYA MARITA? sai mu hadu a GASAR JARUMTAKA na biyar don Jin cigaban wannan Kasaitacce Kuma Kayataccen labari ✍️✍️**GASAR JARUMTAKA** LITTAFI NA BIYAR 5 PART A ♥️❤️ MARUBUCI: NAJIBULLAH MUHAMMAD ✍️✍️ POSTING: Najibullah Muhammad 🥷🥷 Lokacin da Dakarun Sarki Zurmatu suka Afkawa su SARKI KALJUL sai wurin ya yamutse Kasa ta kama girgiza saboda tsananin yawan mazajen da suke rubdugun yaki a samanta. Nan fa wadannan Bakaken Aljanun suka wanzu suna masu cisge kawunan Dakarun Sarki Zurmatu da bakinsu Mai tsananin Kaifi kamar Reza. Su dai wadannan Aljanu sun kasance manya-manya Kuma gaba dayansu kawunansu irin na tsuntsun hankaka ne, sannan daga wuyansu abinda yayo Kasa siffar bil'adama garesu, Amma Kuma suna da wata doguwar jela daga bayansa wadda har sharar Kasa take. A duk lokacin da wadannan Bakaken Aljanun suka Bude bakinsu sai aga wuta Mai tsananin zafi ta fito daga bakinsu ta dira akan abokan gaba guda Dari, sannan a hannuwansu suna rike da zabga-zabgan takubba masu matukar nauyi da kauri, wadanda duk lokacin da suka Kai Sara to suna raba kawunan bil'adama hamsin a lokaci guda, haka Kuma suna wurga jelarsu izuwa abokan gaba domin ta shako wuyan sama da mutum arba'in sannan su wurwura su sama da jelar, sai dai kaga mutane suna shawagi a sama tamkar iska na kwashe ledoji. Haka za a ga mutane suna fadowa akan Duwatsu da Saman bishiyoyi suna kakkaryewa. Nan fa Aljanun Nan suka wanzu suna masu karkashe Dakarun Sarki Zurmatu tamkar GOBARA DAGA KOGI wadda Bata da magani sai Allah. Cikin kankanin lokaci aljanun Nan suka kashe sama da mutum dubu arba'in. A bangaren Dakarun Sarki Zurmatu kuwa babban abinda yafi tayar masu da hankali shi ne, Koda sun samu nasarar saran Aljanun takobin Bata tasiri a jikinsu domin ji suke tamkar sun sari Dutse har sautin wani Kara ke fita, wannan yasa suna ji suna gani akayita karkashe su batare da sun iya kare kansu ba. Yayinda SARKI ZURMATU yaga irin mummunar kisan gillar da ake yiwa Dakarunsa sai ransa ya Baci zuciyarsa ta harzuka Nan take ya kwarara uban ihu Mai tsananin razanarwa, kawai sai akaga yayi fitar burtu daga inda yake ya falfala da matsanancin gudu tamkar kibiya, saboda karfin gudun nasa har tashi sama yake. Koda wadannan Aljanun suka hango SARKI ZURMATU ya tunkaro su, sai sama da guda dubu suka rugo gareshi domin suyi Masa rubdugu a lokaci guda. Koda ya rage Bai wuce saura taku biyar ba ya iso garesu, sai sama da aljanu arba'in suka Bude bakunansu da nufin su Narkar dashi da wannan wutar Mai zafi. Cikin tsananin zafin nama Sarki Zurmatu yayi tsalle sama ya kaucewa dukkan harin nasu, sannan ya takarkare iyakar karfinsa ya Doki Aljani guda da Kafarsa, saboda karfin dukan sai dai ALJANIN yayi baya baya luu ya Bazar da Sama da Aljanu Dari suka baje a Kasa matattu ko shurawa babu Wanda yayi. Nan fa SARKI ZURMATU ya wanzu Yana Mai Kai masu Sara da suka cikin tsananin zafin nama juriya da bajinta, Amma Koda ya lura cewa takobinsa Bata tasiri a jikin Aljanun sai yayi jifa da ita, ya hausu da naushi hannu da kafa ba ji ba gani. Duk Wanda SARKI ZURMATU ya nausa sai dai kaga yayi baya luu ya fada cikin 'yan uwansa sun baje a Kasa matattu. Nan fa SARKI ZURMATU ya wanzu Yana kakkarya Kasusuwan Aljanun Nan tamkar yadda Kura ke kakkarya Kasusuwan duk dabbar da ta kama. Cikin kankanin lokaci Sarki Zurmatu ya kashe sama da Aljanu Dubu Dari.. Yayinda SARKI KALJUL ya hango irin mummunar Barnar da Sarki Zurmatu ke yiwa Dakarunsa sai ransa ya Baci, Nan take ya dako wani wawan tsalle sama tamkar an cilloshi yayo Kan Sarki Zurmatu da nufin ya fille Masa Kai, a wannan lokaci tuni SARKI ZURMATU ya shagala wajen kashe wadannan Aljanun ko kadan Bai Ankara da harin SARKI KALJUL yayi Shirin kawo masa ba. Koda SADAUKI USAMA yaga abinda ke Shirin faruwa sai ya kwalla kabbara da karfi sannan yayi sama tamkar an janyo da Kugiya, sannan ya kaiwa SARKI KALJUL mummunan Sara a hannu, kafin Sarki KALJUL ya Ankara tuni SADAUKI USAMA ya tsinke Masa hannu. Sai gashi sun duro Kasa a lokaci guda, Dungulmin SARKI KALJUL yayi ta kwararar da jini kamar teku ta balle, Nan fa SARKI KALJUL ya kwarara uban ihu Mai tsananin Kara da firgitarwa. Nan take Sarki KALJUL yayi tsafi sannan jinin Dake shatata a Dungulmin hannunsa ya tsaya tsaf... A wannan lokaci tuni SARKI FALWAN da Boka RAKUL da Sarkin yaki DURKUL na can cikin tsakiyar dandazon Aljanun Nan suna ta fafatawa, Boka RAKUL yayi iyakar kokarinsa don halaka Aljanun Nan da karfin tsafinsa Amma a banza domin duk abinda yayi nufi watsa masu walau kibiya ko wuta ko macizai sai ya take sun narke sun zama tun gabanin su taba jikin Aljanun. Wannan ya dena Amfani da tsafi gaba Daya ya dage iyakar karfinsa Yana yakar Aljanun da Karfin damtse duk da cewa su Sarki FALWAN suna iyakar kokarinsu wajen yakar Aljanun Amma sai harin da aljanun suke kawo masu yayi masu yawa, domin dukkansu sun samu munanan raunika a sassan jikinsu. Cikin kankanin lokaci suka galaibata ainun ya zamana cewa dakyar ma suke iya kare harin Aljanun basa iya mayar da martani. Ana cikin wannan Hali ne, aka hango SARKI KALJUL ya kwarara uban ihu Mai tsananin razanarwa, saboda Karar ihun sai da ta sa kowa ya tsaya cak daga yakin aka kura Masa idanu. Kafin wani daga cikinsu yayi yunkuri tuni SARKI KALJUL ya nuna Sarki Zurmatu, Sadauki Usama, Sarki FALWAN, Boka RAKUL, da Sarkin yaki DURKUL da hannun Hagu, Nan kafin suyi wani yunkuri sai akaga wata murtukekiyar Sarkar tsafi ta daddauresu tamau, sannan wata iska Mai Karfi ta zuko su Sarki FALWAN tamkar an dauko su, ta hadasu tare da su sadauki Usama wannan Sarkar tsafin ta hada da su ta daddaure tamau. Nan take SARKI KALJUL ya bushe da wata mahaukaciyar dariya sannan ya sake nuni da hannunsa izuwa ga wani Fili sai ga wani Katon Kejin tsafi ya bayyana, sannan ya hura su Sarki Zurmatu da iskar bakinsa sai gani akayi sun bace sannan sun wanzu a cikin wannan Kejin tsafin. Cikin kyalkyala dariyar mugunta SARKI KALJUL ya zo kusa da Kejin tsafin ya tsaya ya Kalli su Sarki Zurmatu Dake daddaure da Sarkar tsafi ya sake bushewa da dariya sannan ya ce.. Ya ku wadannan Hatsabiban bil'adama tabbas kunyi kokari Kuma kunyi babbar bajintar da har abada baza'a taba mantawa daku ba, domin ku ne mutane na farko da suka iya yimin rauni a filin yaki. Kuyi sani cewa a rayuwata nayi yaki da kasashen manyan Aljanu a Kalla guda dubu goma da Dari bakwai da hamsin, Amma daga cikin duk yakokin da nayi ba'a taba samun mahalukin da ya iya Koda lakutar jikina ba, sannan wannan hatsabibin Yaro wato Sadauki Usama. A bisa wannan dalili ne yasa na Yanke shawarar cewa bazan kashe ku ba, zan daddaure ku ne na barku Kuna kallon yanda zaka kashe gaba dayan Dakarun ku, na baje gaba dayan birnin na kama duk matayen garin a matsayin bayina, sannan na kwashe gaba dayan dukiyarku a matsayin Ganima, ta yadda har abada baza'a Kara tunawa da wannan birni ba. Sa'annan Kuma bayan na gama da Kasar ka, sai na kwashe ku, ku biyar din nan na tafi daku har fadata, sannan na bar ku a cikin Kejin Ina kallonku Ina Jin dadi daga Nan har abada haka zakuyi ta zama har karshen rayuwarku. Yana gama fadin hakan sai ya sake bushewa da dariya a karo na uku, sannan har ya juya zai tafi sai ya ji an daka Masa tsawa daga cikin Kejin. SARKI KALJUL ya waiwayo cikin mamaki don ganin Wanda yayi Masa tsawa, kawai sai ya ga SADAUKI USAMA ya dube shi a Fusace ya ce, yakai wannan la'anannen Aljani Wanda yake Kan Bata na Shirka Mai Bautar wanin Allah, kayi sani cewa har abada burinka bazai taba cika akanmu ba, domin inaji a jikina cewa lallai Ubangijin kowa da komai zai kubutar damu daga sharrinka, Kuma har abada Gaskiya ita ke nasara akan Karya. Don haka Ina Mai shawartarka da ka ajiye duk wani zalunci da kake yiwa bayin Allah, sannan ka dena Bautar Gunki ka dawo Bautar Allah 1 Wanda ya halicci komai da kowa, domin shi ne Mafi cancanta akan kowa ya Bauta Masa saboda shi ne Mafi karfin Iko akan kowa. Idan kuwa kayi kunnen Kashi ga barin yi masa biyayya, to ka sani cewa Ubangijina Yana da hanyoyin azabtar da manyan Kafirai irinka, Kuma azaba Mai tsananin da duk duniya babu Mai iya kubutar da Kai. Yayinda SARKI KALJUL yaji wannan jawabi daga bakin SADAUKI USAMA sai ya sake bushewa da dariya a karo na hudu, sannan ya ce, " yanxu Ashe har yanxu kana tunanin kubuta daga wannan kamun da nayi maku? Yanzu Ashe har Kuna tunanin akwai abinda zai hanani samun nasara a wannan Yakin? Tayaya har kake tunanin zan Kasa aiwatar da nufina a Kanku? Na rantse da Karfin mulkina Koda duk mutanen duniya ne zasu taru anan Basu Isa su hanani aiwatar da abinda nayi nufi akan wannan birnin da ku Kanku ba. Idan Kuma Kuna ganin akwai abinda zai Hana to mu zuba mu gani.. Kafin wani daga cikinsu ya Kara cewa wani abu tuni SARKI KALJUL ya bawa gaba dayan Dakarunsa Umarnin cewa su gama da birnin gaba Daya.. Nan fa DAKARUN ALJANUN Nan wadanda adadinsu ya kai Milyan Daya da dubu Dari biyar suka ruga izuwa kan Dakarun Sarki Zurmatu.. Saboda tsananin yawansu har kura ta tashi ta turnuke sama, Kasa ta kama girgiza kamar zata rufta.. Nan fa Aljanun Nan suka yiwa Dakarun Sarki Zurmatu rubdugu suka wanzu suna masu datsa kawunansu daga ubanjikinsu tamkar ana datsa Tuffa da wuka. Nan fa jini ya rinka Malala da shatata daga jikin Gangar jikin. Cikin kankanin lokaci suka kashe sama da Dakaru dubu Dari biyu. Duk Inda mutum ya duba sai dai yaga gawarwakin Dakarun Sarki Zurmatu birjik a Kasa sun zama matattu. Nan da Nan Karnin jini ya cika gaba dayan birnin, jinin bil'adama ya dinga kwarara a Kasa kamar teku, kafin wani lokaci gaba dayan Kasar wurin ta rine da jini, domin har gudu yakeyi a Kasa. Su kansu Aljanun sai gaba dayan jikinsu ya rine da jini saboda tsabar tsinke kawunan bil'adama da sukeyi jini na feshi a sassan jikinsu Yana jikasu. Shi kuwa SARKI KALJUL sai ya rike kugu Yana ta kyakyata dariyar mugunta Yana ganin yadda ake yiwa Dakarun Sarki Zurmatu mummunan kisan gilla, ya tabbatar da cewa Nan da cikar sa'a biyar an gama da kowa na cikin birnin. Yayinda su SARKI ZURMATU suka hango wannan mummunar barna sai sukayi kamar su haukace saboda tsananin bakin ciki da takaici. Nan take Sarki Zurmatu ya kama cisgar gashin Kansa saboda tsananin fushi jini na zuba Amma Bai damu ba, har sai da su SADAUKI USAMA suka rirrikeshi sannan ya dawo cikin hankalinsa. Nan take SADAUKI USAMA ya dubi Sarki Zurmatu cikin girmamawa ya ce ya shugabana, Ina Mai Rokonka akan ka Bada gaskiya da Ubangijin musulunci da Kai da su Sarki FALWAN da Boka RAKUL da Sarkin yaki DURKUL domin muyi nasara akan wadannan miyagun abokan gaba. Cikin sanyi murya Sarki Zurmatu ya ce, haba yakai wannan Sadauki tayaya kake ganin zamu iya kubuta daga sharrin wannan hatsabibin Aljani Koda mun karbi Addininka? SADAUKI USAMA yace na tabbatar da cewa idan ku ka yi Imani da Ubangijin musulunci Kuma muka taimakonsa to cikin kankanin lokaci zamu kawo karshen wadannan Azzalumai. Kuyi sani cewa Ubangijin musulunci shi ne Mai Iko akan komai, don haka a kowane lokaci mabiyinsa shi keda nasara. Don haka lallai zaku gasgata zancena yayinda kukayi Imani da Ubangijin musulunci. Lokacin da su SARKI ZURMATU sukaji wannan Batu, sai suka ce to munji Kuma mun yarda cewa babu abinda abin bautawa da gaskiya sai Ubangijin musulunci Kuma daga yau mun sallama gaba dayan rayuwarmu wajen bin umarninsa da Bauta Masa, munyi alkawari bazamu taba hadashi da komai na a wajen Bauta. Cikin tsananin farin ciki SADAUKI USAMA ya biya masu Kalmar Shahada sannan suka maimaita.. Nan take SADAUKI USAMA yayi wadansu addu'o'i na musamman sannan ya tofa akan sarkokin tsafin da suka daddaure su, faruwar hakan keda wuya sai gani sukayi gaba dayan sarkokin tsafin da suka dauresu sun tsittsinke. Gaba dayansu suka mimmike tsaye cikin farin ciki Sannan cikin hadin Baki suka ce YA UBANGIJIN MUSULUNCI KA TAIMAKE MU, MUYI NASARA AKAN AZZALUMAI, SANNAN KA KARFAFEMU DA KARFIN DA ZAMUGA BAYAN MAKIYA. Suna gama wannan roko ne, sai dukkansu sukaji wani irin mummunan Karfi na musamman ya shige su, domin ji suke tamkar zasu iya nada gammo a Dora masu gaba dayan duniyar da abinda ke cikinta bisa kansu. Nan take suka kama Karafunan KEJIN TSAFIN da suke ciki suka 6a66alla su tamkar yadda ake babballa Kara a gona. Nan take BOKA RAKUL yayi godiya ga ubangijin musulunci da ya kubutar da su, sannan ya dubi su Sarki Zurmatu da Sadauki Usama ya ce, " ya Shugabana na roke ku akan ku bani izini domin naje nayiwa SARKI KALJUL mummunan kisan gilla yanzun Nan. Nan take Sarki Zurmatu ya ce jeka abinka yakai RAKUL kayi sani cewa Allah na tare dakai Kuma shi zai taimake ka. Nan take Boka RAKUL ya falfala da matsanancin gudu izuwa kan SARKI KALJUL da nufin yi masa farat Daya.. Koda SARKI KALJUL ya hango Boka RAKUL ya tunkaroshi a Fusace, sai ya cika da tsananin mamaki, Yaya akayi wannan hatsabibin Bokan ya kubuta daga cikin Kejin tsafin da na tsaresu? Ya tambayi Kansa a cikin zuciyarsa. Kafin ya bawa Kansa Amsa, sai kawai ya zare lafceciyar takobinsa da dayan hannun nasa Mai lafiyar. Boka RAKUL na zuwa inda SARKI KALJUL yake sai aka ga SARKI KALJUL ya daga falleliyar takobinsa sama ya kawowa Boka RAKUL mummunan Sara a ka, da nufin ya raba shi biyu. Ba zato ba tsammani sai kawai aka ga BOKA RAKUL yasa hannunsa guda ya kare saran batare da ko kwarzane ba, sannan ya finciko takobin daga hannun Sarki KALJUL kawai sai akaga ya cukuikuyeta tamkar Yana mutsittsike takarda ya jefar da ita Kasa. Kafin SARKI KALJUL yayi wani yunkuri tuni Boka RAKUL ya cafko wuyansa, kawai sai akaga ya daga shi sama da hannu guda Nan ya rinka fyada shi da Kasa tamkar ana fyadin dawa. Cikin dakika goma sai dai Boka RAKUL yayiwa SARKI KALJUL Kaye tamanin, a wannan lokaci tuni kashin bayan Sarki KALJUL ya karye Kuma har ya Suma. Nan take Boka RAKUL ya saki wuyan SARKI KALJUL sannan ya Suri kafafun Aljanin yayi kan Dakarun Aljanun SARKI KALJUL ya hau su da duka da Gangar jikin SARKI KALJUL, duk Wanda Boka RAKUL ya makawa jikin SARKI KALJUL sai dai aka ya kama da wuta ya kone kurmus. Koda ganin abinda ya faru a tsakanin Boka RAKUL da SARKI KALJUL sai Suma su Sarki Zurmatu da Sadauki Usama da Sarkin yaki DURKUL suka ruga cikin filin yakin domin Kai Masa dauki... A dai-dai wannan lokacine Nima na gaji da rubutu, nake cewa mu hadu a GASAR JARUMTAKA na biyar part B don Jin cigaban wannan Kasaitacce Kuma Kayataccen labari ✍️♥️🥰 Najibullah Muhammad ✍️✍️🥷🥷🥷**GASAR JARUMTAKA** LITTAFI NA BIYAR 5 PART B ✍️💯 MARUBUCI: NAJIBULLAH MUHAMMAD ✍️♥️ POSTING: Najibullah Muhammad legend🥷🥷 Lokacin da su Sarki Zurmatu suka hango irin mummunan Kisan da yake yiwa bakaken aljanun nan, sai suka cika da matukar mamaki ainun. Nan take suka tambayi kansu a cikin zuciya, cewa tayaya Boka RAKUL ya samu wannan gagarumin karfi haka? Amma da suka tuna cewa yanzu sun musulunta Kuma duk karfin da suka samu ba dabararsu ko hikimarsu bace, Ubangijin musulunci ne ya Basu domin tabbatar da Addinin musulunci a bayan Kasa, sai hankalinsu ya kwanta Kuma suka Kara sallamawa Ubangijin musulunci.. Nan take batare da Bata wani lokaci ba suma suka ruga izuwa kan abokan gaba. Koda Sarki Zurmatu, Sadauki Usama, Sarkin yaki DURKUL, Sarki FALWAN suka iso tsakiyar abokan gaba sai suka zama tamkar GUGUWAR ANNOBA domin duk Inda suka sa gabansu sai da aga kawunan Arna na zubewa Kasa tamkar busassun ganyayyakin da suke fadowa Kasa. A wannan yaki Sadauki Usama da Sarki Zurmatu sun fi kowa taka muhimmiyar rawa, domin tsananin Jarumtakar da suke nunawa ta ninka ta Aljanun ma. Su kansu sunyi matukar mamakin yadda suka samu karfi na musamman da yafi na su a wannan Yakin. Domin suna iya kama Aljani su tsinka shi biyu, kamar a tsinka rubabben tsuma gida biyu. Haka Kuma idan suka naushi Aljani a ka, sai dai kaga hannunsu ya Burma cikin Kan tamkar a buga Sanda a jikin kabewa. Kai saboda tsananin karfin damtsen da suke jinsu da shi, suna iya falfalawa da gudu a cikin rundunar Aljanun sai dai kaga suna bankesu da kirajensu suna faduwa Kasa matattu tamkar kanyar da babu dadi na fadowa Kasa. A cikin abinda Bai wuce sa'a guda ba kacal sai da suka Karar da sama da Aljanu Milyan Daya da dubu Dari uku. Har a wannan lokaci ko kadan babu alamun gajiya a tattare dasu. A bangaren Boka RAKUL kuwa sai da ya zamana cewa ya tabbatar duk wani Kashi dake jikin SARKI KALJUL ya karye rugu-rugu saboda tsabar dukan Aljanu da yake da shi. A sannan ne ya fyada Gawar SARKI KALJUL a Saman wani mulmulen dutse, Gawar tayi fata-fata tamkar kafar giwa ta taka Fura. A sannan ne ya cisgo kafar hagun Sarki KALJUL da karfin tsiya, jini yayi feshi da tsartuwa sannan yaci gaba da ragargazar Arna da ita. Ya zamana cewa duk Wanda ya makawa wannan kafar sai dai aga ya rabe gida biyu, tamkar da takobi aka sareshi. Hakika a wannan rana mutanen birnin BALLUS sunga tashin hankalin da Basu taba gani ba, Kuma sunga bala'i da masifa irin wadda ko a tarihi Basu taba Jin kamarta ba. Domin a wannan Yakin sai da akayi asarar rayukan bil'adama sama da Milyan biyar, hatta Aljanu sai da aka kashe guda Milyan biyu da dubu dari biyar. Duk Inda mutum ya duba sai dai yaga gawarwakin mutane da Aljanu birjik kwance a Kasa, tamkar kudaje. Saboda tsananin yawan gawarwakin dake zube a Kasa yasa babu hanyar da mutane rugawa izuwa gidajensu, sai dai suka rinka takawa ta Saman gawarwakin suna tafiya. Su kansu su Sarki Zurmatu a Saman gawarwakin mutane da Aljanu suka rinka yakin, domin gawarwakin sun rufe Kasar da yake yakin a kanta saboda yawansu. Lokacin da aka Kara shafe wata sa'a gudar sai yazamana cewa su SARKI ZURMATU sun Karar da gaba dayan BAKAKEN ALJANUN SARKI KALJUL, ya zamana cewa duk sun mayar da su matattu babu guda Daya rayayye. A wannan lokaci ne suka rinka hango 'yan uwansu, sai gaba dayansu suka rugo suka rungume juna saboda tsananin farin cikin samun nasarar wannan yaki. Nan take suka fashe da kukan farin ciki a lokaci guda, suna masu kankame juna a jikinsu. Hmmm! A hakika a wannan lokaci duk Wanda ya Kalli wadannan JARUMAN dole ne ya jin-jina masu Kuma ya tausaya masu, saboda ganin yanda kamanninsu ya sauya izuwa jini. Gaba dayan jikinsu ya rine da jini tamkar an tsoma su a cikin KOGIN JINI. Suna cikin wannan hali ne, suka ji Waziri Mikilas ya kwalla masu kira cikin tsananin farin ciki. Waziri Mikilas ya taho ne tare da Dakaru na musamman wadanda zasu yiwa su Sarki Zurmatu rakiya izuwa cikin fadar. Cikin matsanancin farin ciki SARKI ZURMATU, SADAUKI USAMA, BOKA RAKUL, SARKI FALWAN, SARKIN YAKI DURKUL suka rugo inda Waziri Mikilas yake tsaye. Nan take Sarki Zurmatu ya bawa wani Sadauki Umarnin cewa yaje ya tattaro Dakaru dubu Dari domin suzo su kone duk gawarwakin mutane da aljanun da aka rasa a filin yakin. Nan take wannan SADAUKIN ya ruga domin cika Umarni. Shi dai wannan Sadauki mataimakin Sarkin yaki DURKUL ne, Kuma sunansa MAHUSH ya kasance jarumi Mai tsananin karfin damtse na gaban kwatance, domin da kadan Sarkin yaki ya fishi Jarumtaka. Bugu da Kari Kuma Yana da rikon gaskiya da Amana a dukkan harkokinsa, wannan yasa ya kasance Amintaccen Sarkin yaki DURKUL, ya zamana cewa duk Inda Sarkin yaki zashi to tare suke zuwa. Lokacin da SADAUKI MAHUSH ya tafi debo wadannan Dakarun, sai su Sarki Zurmatu suka dunguma gaba dayansu izuwa gidan sarautar. Suna tafiya ana buga masu Gangar cin nasarar yaki, gaba dayan jama'ar gari suka jejjeru sahu-sahu suna yiwa SARKI ZURMATU kirari da yabo da jin-jina saboda samun wannan gagarumar nasara da sukayi. Nan fa aka cika birnin BALLUS da kade-kade da bushe-bushe bisa wannan nasarar yaki da sukayi. Bayan SARKI ZURMATU sun iso fada, sai yace da jama'arsa," yaku jama'ar birnin BALLUS kuyi sani cewa a yau Muna cikin tsananin farin ciki, ba don komai ba sai domin samun nasarar wannan yaki da mukayi Wanda a zahirin gaskiya tuni mun saduda cewa rayuwarmu ta xo karshe, Amma Kuma sai gashi mun samu nasara. Saboda haka inason kowannenku ya je gida ya huta gajiyar wannan yaki daga Nan zuwa gobe, kowa ya taru a kofar fada ta domin na sanar daku sirrin da ya sa muka samu nasarar wannan yaki, sannan Kuma har ila yau a goben zan tabbatar da Alkawarina akan SADAUKI USAMA. Saboda haka kowa ya tafi gida na sallameku. Nan take kowa ya watse ya kama gabansa, Sarki Zurmatu ya wuce Kai tsaye izuwa cikin turakarsa Yana zuwa ya wuce inda matarsa take wato sarauniya KALTISA. Koda KALTISA ta hango mijinta tafe, sai ta rugo ta rungume shi cikin tsananin farin ciki. Bayan wani lokaci sai ta dubi Sarki Zurmatu fuskarta cike da tsananin damuwa sannan ta ce, ya Kai mijina tayaya akayi kuka samu nasarar wannan yaki alhalin naji ance SARKI KALJUL ne tare da rundunarsa suka kawo mana harin bazato. Cikin tsananin murmushi Sarki ya ce, yake matata kiyi sani cewa samun nasarar wannan yaki da mukayi na dauke da wannan babban Ala'mari, saboda haka ki kwantar da hankalinki idan naje nayi Wanka na kintsa, zan sanar Dake komai. Nan take Sarki Zurmatu yaje ya fesa Wanka sannan ya Saka kaya masu matukar kyau da tsada irin na manyan sarakunan duniya. Sannan ya fito turakar sarauniya KALTISA inda ya isketa tuni ta gama jejjera Masa kayan abinci da Sha iri-iri akan wani Katon teburin Zinari. Zaman Sarki Zurmatu keda wuya akan kujera, sai ya ji kamshin abinci kala-kala ya Doki hancinsa. Nan take Sarki ya dubi sarauniya KALTISA ya ce, " yake matata ni da wa kike son mu cinye wannan abincin haka? Kiyi sani cewa Koda mutum hamsin zasu taru bazasu iya cinye abincin da ke kan teburin Nan ba. Cikin dariya sarauniya ta ce, saboda murnan dawowarka a raye ne, yasa ni da kaina nayi maka girki na musamman irin Wanda baka taba cin kamarsa ba. Nan take Sarki Zurmatu ya sa matarsa KALTISA akan ta aika a kira GIMBIYA MARITA domin suyi tattaunawa ta musamman. Nan take KALTISA ta kwalawa wata Jakadiyarta kira, nan da Nan Jakadiyar tazo ta durkusa a gabanta, KALTISA ta dubi Jakadiyar ta ce, je ki kira mana GIMBIYA yanxun Nan. Cikin sauri Jakadiyar ta fice don cika Umarni. Ba tare da Bata lokaci ba, Sarki Zurmatu ya hau abincin Nan da ci tamkar mayunwacin da yayi shekara guda Bai sa komai a bakinsa ba. Lokacin da GIMBIYA MARITA ta shigo cikin turakar, sai ta rugo ta rungume Sarki cikin tsananin farin ciki. Nan dai Sarki da iyalansa suka kasance cikin farin cikin kasance a wannan lokacin. Bayan Sarki ya kammala cin abincinsa, sai ya dubi KALTISA da GIMBIYA MARITA a natse sannan ya ce to ku saurara da kyau domin na Baku labarin duk abinda ya faru a filin yaki da Kuma yadda akayi muka samu nasara. Nan take Sarki Zurmatu ya kwashe gaba dayan labarin abinda ya faru ya bawa su GIMBIYA MARITA. Cikin tsananin mamaki gaba dayansu suka kurawa SARKI ZURMATU idanu Kuma suka rasa ma abinda zasu ce. SARKI ZURMATU yaci gaba da cewa, saboda haka a yanxu take nake so ku bayar da Gaskiya ga ubangijin musulunci saboda ta hakane zan iya jawo hankalin mutanen Birnina akan suyi Imani. Batare da Bata wani lokaci ba, gaba dayansu suka amince. Cikin tsananin farin ciki Sarki Zurmatu ya biya masu Kalmar Shahada suka maimaita. Haka dai su Sarki Zurmatu suka kasance cikin aminci, Kuma suka kwashi lokaci Mai tsawo suna fira har dare ya raba sannan kowannensu yaje ya kwanta. Kashe gari da sassafe bayan kowa ya kimtsa, sai gaba dayan mutanen birnin sukayi tururuwa a filin fadar Sarki Zurmatu. Cikin kankanin lokaci fadar ta cika ta batse da jama'a, saboda nuna farin cikin

Chapter 6 of 12