da ku ke bukata ku karbi musulunci.
Nan take Boka RAKUL ya nunawa SADAUKI USAMA Kejin tsafin da aka tsare Sarki Zurmatu ya ce, ga aikinka na farko.
Nan take sadauki Usama ya tunkaro inda Kejin yake, Yana zuwa sai aka ga ya rufe idanunsa sannan ya daga hannayensa sama Yana Mai yin addu'a ta musamman tare da yiwa Allah kirari da tsarkakan sunayensa akan ya bashi nasarar kubutar da wannan Sarki, bayan kamar shudewar dakika Dari da Ashirin da faruwar hakan sai sadauki Usama ya Bude idanunsa a hankali sannan ya dafa Kejin tsafin da hannunsa na dama, Nan take Kejin tsafin ya bat tamkar daukewar ruwan sama sai ga SARKI ZURMATU a tsaye shi kadai a filin rike da hannunsa na hagu, kawai sai Sadauki Usama ya kamo dayan hannun SARKI ZURMATU ya jawo shi suka taho wajen su BOKA RAKUL.
Cikin tsananin mamaki da Al'ajabi su Boka RAKUL da Sarki FALWAN da sauran jaruman Gasar da suka rage suka kurawa su Jarumi Usama idanu suna masu Bude bakunansu cikin tsananin mamaki, hatta shi kanshi Sarki Zurmatu sai dai ya bishi da Ido cikin tsananin mamaki.
Da isowar su Sarki Zurmatu a gaban su Boka RAKUL sai dukkansu suka zube Kasa suka kwashi gaisuwa ga SARKI ZURMATU saboda tsananin girmamawa.
Nan take wani irin bakin ciki ya turnuke Sarki FALWAN yaji kishi ya shige shi, yaji a ransa cewa Ina ma shi ne Mai karfin mulkin Sarki Zurmatu, kawai sai ya ayyana a ransa cewa lallai ko ta wane hali sai ya lashe GASAR JARUMTAKA ko don ya mallaki birnin BALLUS domin cikar burinshi sannan ya mallakawa dansa Yarima FAZAMAL auren GIMBIYA MARITA domin tabbatar da farin ciki a cikin mulkinsa.
Yana cikin wannan tunani ne sai SARKI ZURMATU yayi gyaran murya, sannan kowa ya dago Kai ya dubeshi.
Sarki Zurmatu ya fuskance su Yana Mai cewa yaku jama'ata Kuma manyan jarumai tabbas kunyi matukar kokari a wannan yaki da muka fafata da abokan gaba, Kuma Kun tabbatar da cewa Kun cika jarumai ababan alfahari, a sakamakon haka nayi alkawarin bawa kowannenku dukiyar da ko tattaba kunnensa ma bazasu iya Karar da ita ba.
Kuma har yanxu Alkawarina Yana Nan akan duk Wanda ya lashe Kambun GASAR JARUMTAKA.
Don haka lallai yanxu zamu dauki hanyar komawa birninmu domin cigaba da wannan Gasa.
Bugu da Kari Kuma naji duk irin yarjejeniyar da BOKA RAKUL yayi da wannan bakon jarumi da ya taimake mu, sannan Nima na amince da wannan sharadi.
Don haka yanzu sai Shirin komawa gida, Nan da Nan Sarki Zurmatu ya dubi Boka RAKUL ya ce yakai shugaban BOKAYEN DUNIYA tayaya zamu koma gida cikin abinda Bai wuce sa'a bakwai ba?
Nan take Boka RAKUL yayi murmushi sannan ya ce ai ta inda aka hau to ta Nan ake sauka, Nan take ya Kara yin wannan hayakin da yayi tun lokacin da zasu baro birnin BALLUS, faruwar hakan keda wuya sai aka ga wadannan manyan-manyan IFIRATAN ALJANUN sun Kara bayyana wadanda adadinsu ya Kai dubu.
Girman kowane daga cikinsu yakai na adadin bil'adama Dari biyar.
Boka RAKUL ya dube su yace, Ina so ku mayar damu birnin BALLUS inda ku ka dauko mu da gaggawa.
Nan take suka rankwafa Kasa sannan Sarki Zurmatu, sadauki Usama, Sarki FALWAN Mai goye da Yarima FAZAMAL, Boka RAKUL da wasu Jaruman Gasar guda Dari hudu gaba dayansu suka Haye bayan Aljani guda..
Sannan sauran jaruman Gasar wadanda adadinsu Bai wuce dubu sittin da biyar ba, suka ruga izuwa ga sauran Aljanun suna Hawa samansu tamkar tururuwa na Hawa Saman katon tsauni.
Bayan sun gama hayewa sai Aljanun suka Bude fuka-fukansu suka tashi da su sama, suna masu lulukawa a cikin gajimare tamkar tauraruwa Mai wutsiya.
Wannan shi ne abinda ya faru da su Sarki Zurmatu bayan sun fafata kazamin yaki da Dakarun Boka GARGUS inda suka samu nasarar hallakasu.....
A can birnin BALLUS kuwa Waziri Mikilas ne akan karagar Mulki ana tafiyar da harkokin Mulki kamar yadda aka Saba, yau kimanin kwanaki bakwai kenan da tafiyar su Sarki Zurmatu.
Kuma Waziri Mikilas Yana tafiyar da Mulki yanda ya kamata kamar yadda Sarki Zurmatu ke Yi a Kasar, wannan yasa Waziri Mikilas yayi matukar farin jini a wajen mutanen gari saboda son adalcinsa ga talakawa.
A yammacin kwana na bakwai ne ana tafiyar da al'amarin Mulki kawai sai aka ga hasken rana ya bace lokaci guda, Nan take gari yayi duhu dundum kawai sai akaji fadowar wasu abubuwa masu nauyin gaske a can babban Filin Gasar JARUMTAKA.
Ana cikin haka kuma sai hasken rana ya dawo, Ashe Daman fuka-fukan wadannan Aljanun ne suka rufe hasken rana yayinda suka zo giftawa ta garin, Kuma su ne suka sauka a filin Gasar suka ajiye su Sarki Zurmatu sannan suka bace bat.
Kafin a jima gaba dayan mutanen birnin sunyiwa filin Gasar tsinke don ganin ko menene ya fado a can..
Su Waziri Mikilas ne da mukarrabansa akan gaba, suna zuwa sai suka iske Jaruman Gasar tare da su Sarki Zurmatu a tsaitsaye a filin Gasar.
Koda ganin haka sai dukkannin jama'ar gari suka rude da shewa gami da yiwa Sarkinsu jin-jina akan nasarar yakin da sukaje.
Nan fa fadar ta rude da shewa kowa na fadin albarkacin bakinsa, har sai da Sarki Zurmatu ya daga hannunsa sama sannan kowa ya tsuke bakinsa.
Sarki Zurmatu ya fuskanci jama'ar sa fuskarsa cike da murmushi sannan ya ce, ya ku jama'ar birnin BALLUS kuyi sani cewa munyi matukar farin cikin samun nasarar wannan yaki da mukaje, Kuma muka dawo cikin koshin lafiya, haka Kuma a yayin tsaka da wannan yaki ne muka hadu da wani bakon jarumi Wanda ya shiga jerin Jaruman Gasar JARUMTAKA.
Kuyi sani cewa a halin yanxu zamu ci gaba da aitawar da Gasar JARUMTAKA daga Nan zuwa kwanaki Sha hudu, sakamakon karayar hannu da na samu.
Don haka yanzu inaso maza a kira min Sarkin madora domin ya gyara min karayar hannuna..
Nan da Nan Sarkin yaki DURKUL ya zaburi dokinsa izuwa gidan Sarkin madora, ai kuwa kafin shudewar dakika hamsin sai ga shi ya dawo tare da shi.
Nan take aka shiga gyara karayar hannun Sarki...
Nan fa jama'a suka ga tsananin juriyar Sarki Zurmatu, domin saboda dadewa da hannunsa yayi a karye batare da an gyara ba ya haddasa kumbura da tsamin Kashi, Amma duk irin zafin da Sarki ke ji a yayin gyaran karayar sa ko gezau bayyi ba, har aka gama gyaran aka shafa Masa magani.
Nan fa mutane suka cika da tsananin mamaki domin Basu taba ganin Wanda yake da juriyar Sarki Zurmatu ba..
A zahirin gaskiya SARKI ZURMATU ya cika namijin gaske ko ta wane fanni, Domin ko surar jikinsa ya Kalla yasan cewa dole ne ya kasance sadauki Mai tsananin karfin damtse na gaban kwatance.
A bisa wannan dalili ne yasa mutane suke ganin cewa a gaba dayan Jaruman Gasar ba lallai bane a samu Wanda zai iya nasara akan Sarki Zurmatu wato a karshen wannan Gasa.
Bayan kammala gyaran karayar Sarki Zurmatu, sai Nan take ya sallami kowa tare da sanar da su cewa lallai kowa ya taru anan bayan cikar kwanaki Sha hudu domin cigaba da aiwatar da Gasa.
Nan take kowa ya kama gabansa, Sarki Zurmatu ya tunkari cikin gidan sarautar, Boka RAKUL da Sarki FALWAN da Yarima USAMA suka tunkari cikin gidan da aka sauke su na musamman, Daman tuni SARKI ZURMATU yasa manyan likitocinsa na musamman sun Dauki yarima fazamal domin ceto rayuwarsa sakamakon mummunan saran da badakaren Aljanin yayi Masa a filin yaki.
Nan da Nan kowa ya watse Yana fadin albarkacin bakinsa..
Nan da Nan kowa ya daga shirya Kansa domin zuwan ranar cigaba da GASAR JARUMTAKA, ya zamana cewa Jaruman Gasar kullum Basu da wani aiki sai bawa kansu horon yaki na musamman tare da horon shanye juriya Mai tsananin yawa, ta yadda Koda za'a kwana ana Gwabzawa ba zasu gaji ba.
Haka zalika Kuma shi ma Sarki FALWAN kullum sai ya tafi filin Gasar ya iske Jaruman Gasar ya hade dasu domin bawa Kansa horon yaki na musamman, ya zamana cewa wani lokacin Yana sa Dakarun Gasa guda Hamsin su tarar Masa shi kadai, Amma su Kasa samun nasara a kanshi a karshe ma shi ne ke Bazar da su Kasa.
Tun Yana yaki da mutum hamsin har ya ninka izuwa Dari, a ranar da ya fara yaki da Jaruman Gasa mutum Dari ne fa ya gane kurensa domin dakyar da jibin goshi ya samu nasara a kansu bayan ya samu raunika biyar a sassan jikansa.
Washe gari bayan anyi Masa magani ya Kara sa mutum Dari su rufar Masa, a haka a haka dai har ya rinka iya samun nasara akansu batare da dayansu yayi Masa koda kwarzane ne ba..
Hakanne ya tabbatar Masa da cewa tabbas shi ne zai lashe Kambun GASAR JARUMTAKA..
A bangaren JARUMI USAMA kuwa, tunda ya kasance a cikin masaukinsa Bai taba fitowa waje ba, kullum bashi da wani aiki sai ibada da karatun Alqur'ani Mai girma tare da nafilolin dare da rana..
Haka ya wanzu a kowane lokaci..
A bisa wannan dalili ne yasa sauran jaruman Gasar suke ganin cewa da zarar an hada su Gwabzawa da JARUMI USAMA to cikin farat Daya zasu hallakashi, tunda Bai taba fitowa wajen karbar horon yaki ba, Kuma a halin yanxu jininsa ya kwanta.
Hmm rashin sani yafi dare duhu.
A bangaren Sarki Zurmatu kuwa kullum sai likitocinsa sunzo sun duba shi sau biyar a Rana Kuma sun bashi maganin da ya dace domin karayar hannun sa tayi saurin warkewa.
GIMBIYA MARITA da mahaifiyarta su ne da kansu suke jinyar Sarki domin bashi kulawa ta musamman.
Ya zamana cewa sun dakatar da duk hadiman da ke yiwa Sarki hidima, su ne suke yiwa Sarki duk irin hidimar da yake so.
Saboda tsananin kular da Sarki Zurmatu ya samu ne yasa hankalinsa ya kwanta ainun har karayar hannunsa tayi saurin warkewa a cikin kwana goma kacal.
Ya zamana cewa kashin ya hade Kuma Kumburin hannun ya bace, Nan take Sarki Zurmatu da iyalansa suka cika da tsananin farin ciki mara misaltuwa..
A kwana a tashi har ranar Gasa ta kewayo, Nan fa kowa ya taru makil a filin Gasar.
A gefe guda Kuma Jaruman Gasar ne wadanda adadinsu Bai wuce dubu sittin da biyar ba rike da muggan makamai cikin mummunar shigar yaki.
Bayan kowa ya hallara ne sai ga SARKI FALWAN da su sadauki Usama da Boka RAKUL sun taho filin Gasar. Suna isowa suka zazzauna a wuraren da aka tanadar masu.
Bayan wani Dan lokaci sai aka hango SARKI ZURMATU da Waziri Mikilas da sauran Dakaru masu tsaron lafiyar Sarki suka shigo filin Gasar.
Da isowar su sai gaba dayan mutanen filin Gasar suka duka suka kwashi gaisuwa, Nan take Sarki Zurmatu yaji wani dadi ya shige shi ganin yadda mutanen sa suke matukar girmama shi.
Batare da Bata lokaci ba Sarki yayiwa mutane bayanin cewa a yau ne za'a ci gaba da GASAR JARUMTAKA domin fidda zakara a cikinta, don haka Nan take Sarki ya dubi Sarkin yaki DURKUL ya ce yaje yazo da wadannan DAKARUN NA MUSAMMAN guda goma irin wadanda jarumi margim ya fafata dasu..
Nan da Nan Sarkin yaki ya cika umarni, shigowarsu ke da wuya sai kallo ya koma kansu domin wannan karon wadanda jibga-jibgan SAMUDAWA ne wadanda suka ninka wadancan na farkon girma da tsayi da komai.
Takun sawayensu ma kadai ya Isa ya firgita mutum, suna zuwa tsakiyar filin Gasar suka ware gefe guda suna huci kamar sa ci babu.
Nan take alkalan Gasar suka kira sunan jarumin da zai fafata a karo na biyu na wannan Gasa ana Kiran sa da Suna NURKIB.
Sadauki NURKIB ya kasance dogo Mai kirar SADAUKANTAKA Kuma Mai faffadan kirji irin na Zaki.
Yana rike da zabgegiyar takobi a hannunsa na dama, sannan a hannunsa na hagu ya rike garkuwa.
Sannan Kuma ya rufe fuskarsa da hular karfe, in Banda idanunsa babu abinda ake gani.
Bayan kammala duk wasu shirye-shiryen Gasa, sai Nan take aka buga Gangar fara GASA.
Wohoho Nan take Daya daga cikin SAMUDAWAN DAKARUN SARKI ya tari SADAUKI NURKIB suka ruguntsume da masifaffen yaki mai tsananin ban tsoro da tashin hankali tamkar zasu hallaka duk halittun Dake wajen.
Nan fa suka wanzu suna masu kaiwa junansu Sara da suka cikin juriya da bajinta tamkar jikinsu ba na jini da tsoka bane...
Wohoho!!
Mu hadu a GASAR JARUMTAKA part B don Jin cigaban wannan Kasaitacce Kuma Kayataccen labari Mai dadi 🥰🥰♥️
Ni ne naku NAJIBULLAH MUHAMMAD ✍️♥️🥰🥰 ke cewa ku huta lafiya 🙏🙏**GASAR JARUMTAKA**
LITTAFI NA HUDU 4 ♥️
PART B ✅♥️
MARUBUCI: NAJIBULLAH MUHAMMAD ✍️♥️
POSTING: NAJIBULLAH MUHAMMAD 🥷🥷
LOKACIN da Sadauki NURKIB ya tari wannan badakaren suka ruguntsume da masifaffen yaki, sai ya zamana cewa gaba dayan hankalin 'yan kallon ya tashi saboda ganin irin harin da suke kaiwa junansu.
Tabbas inba don Sadauki NURKIB ya kasance Mai tsananin zafin nama ba, da tuni wannan badakaren ya hallakashi saboda mugayen hare-haren da yake Kai Masa sunfi gaban kwatance tamkar ana ruwan kibau.
Tun NURKIB na iya kare saran da badakaren yake Kai Masa har ma ya gaji ya Kasa ya durkushe Kasa, kawai sai akaga wannan badakaren ya takarkare ya zabgawa NURKIB naushi a kirji, saboda karfin naushin sai da gaba dayan hakarkarinsa suka kakkarye Kuma yayi sama tamkar an janye shi da Kugiya sannan ya fado Kasa Yana aman jini, kafin cikar dakika goma ya mutu.
Nan fa filin Gasar ya rude da shewa, gami da tafi saboda irin nasarar da wannan badakaren ya samu cikin kankanin lokaci haka..
A bangaren SARKI ZURMATU kuwa, Banda farin ciki babu abinda yake faman yi tamkar Wanda aka yiwa bushara da cikar muradinsa..
Ba komai ne ya haddasa Masa wannan farin cikin ba, face ganin irin yadda DAKARUNSA suka Kara samun tsananin horon yaki, gami da zafin nama na gaban kwatance.
A yanzu Kam ya tabbatar da cewa duk cikin jaruman Gasar babu jarumin da zai iya hallakar da wadannan Hatsabiban DAKARUN har ya Kara da Sarki Kuma ya samu nasara a Kansa, ballantana har ya lashe KAMBUN GASAR JARUMTAKA.
Shi kuwa Sarki FALWAN ji yayi zuciyarsa ta buga da karfi, domin Bai taba tunanin cewa akwai karfin wadannan Dakarun ya Kai har haka ba, tabbas yasan cewa ko shi idan sukayi gaba da gaba da su to bazai iya samun nasara akansu ba, don haka ya zama wajibi ya ninka bawa Kansa horon yaki akan yadda ya Saba ko don ya samu nasarar lashe wannan Gasa.
Batare da Bata wani lokaci ba Dakaru masu tsaron filin Gasar suka kwashi Gawar NURKIB sukayi waje da shi.
Sannan Alkalan Gasar suka sake Kiran sunan Jarumi na uku Wanda zai fafata.
Nan take aka kira wani JARUMI mai abocin girma tamkar rikakken maraki, ya fito filin Gasar ya tsaya yana ta faman zare Ido tamkar mayunwacin Zaki.
Nan take shugaban Dakarun ya sake bawa wannan badakaren da ya kashe NURKIB Umarni akan yazo ya kashe wannan ma.
Nan da badakaren ya tunkareshi da gaggawa, Yana zuwa kusa da shi sai ya tsaya cak Yana jiran Umarnin alkalan Gasar.
Nan take aka buga Gangar cigaba da Gasa, kawai sai Jaruman biyu suka zare makaman su sannan suka Afkawa juna ba ji ba gani.
Ya zamana cewa suna kaiwa junansu Sara da suka ta ko'ina, Amma abun mamaki sai akaga wannan jarumin Gasar Yana iya kare duk harin da badakaren yake kawo masa kuma ya mayar da martani, abinda ya Baiwa badakaren mamaki kenan a ransa yake cewa yanxu Daman har akwai bil'adaman da zai iya kare dukkan hare-harena?
Nan take zuciyarsa ta Baci Kuma ransa ya harzuka, cikin fushi ya jefar da Addarsa gefe guda, sannan ya dunkule hannunsa ya Afkawa wannan jarumin, ai kuwa cikin kankanin lokaci ya hada Masa jini da majina kafin cikar dakika Dari da saba'in tuni ya Bazar da shi a Kasa sannan ya murde Masa wuya ya jefar da Gawarsa.
Nan fa jama'a suka Kara rudewa da shewa suna jin-jina ga DAKARUN SARKI, saboda ganin irin nasarar da suke samu a yau, domin har yanzu ko Daya ba'a kashe daga cikinsu ba.
Nan take aka Bada Umarnin cigaba da Gasa.
Batare da Bata lokaci ba Alkalan Gasar suka kira jarumin Gasa na uku, kawai sai akaga wani siririn mutum ya fito filin Gasar rike da wata siririyar takobi Mai kamar Sanda, a Saman kan mutumin babu gashi ko guda Daya, Kuma Yana da kwala-kwalan idanu masu kama da na mujiya.
Nan take mutumin ya fito daga cikin jaruman Gasar sannan ya nufi filin Gasar inda wannan badakaren yake.
Nan fa jama'ar filin Gasar suka cika da tsananin tausayin wannan mutumin domin sun San cewa tabbas hallaka zayyi, wasu ma har sun fara zubar da hawayen tausayi saboda tunanin irin mummunan Kisan gillar da za'ayi Masa.
A bangaren su Sarki Zurmatu kuwa dariya ce ta kwace masu a bisa ganin Wanda ya fito da niyyar tarbar wannan badakaren, domin sun San cewa wannan kawai ya gaji da rayuwarsa ne yake so hallakashi shiyasa ya shiga wannan Gasar.
Nan take alkalan Gasar suka buga Gangar cigaba da Gasa, ai kuwa ana bugawa sai wannan badakaren ya zare lafceciyar Addar sa sannan ya dako tsalle daga inda yake ya kaiwa wannan jarumin Gasar Sara a ka da nufin ya tsargeshi gida ba, abun da yaba kowa mamaki shi ne ganin yadda shi jarumin Gasar ko motsawa bayyiba ballanta ya kare Kansa, Nan fa mutane suka runtse idanuwansu saboda ganin yadda za'a raba wannan siririn mutumin biyu daga fara Gasa.
Ba zato ba tsammani Addar badakaren na Isa Kan siririn mutumin Nan, sai kawai akaji wata Kara Mai tsanani ta watsu a cikin birnin gaba Daya, Kuma Addar ta Kasa Koda kwarzanar Kan siririn mutumin.
Shi kuwa wannan badakaren ji yayi tamkar ya sari Dutse Mai tsananin tauri saboda tsabar karfin kan mutumin, ba zato ba tsammani Kuma sai akaga wannan hannun wannan badakaren ya bushe rakau tamkar an busar da danyen abu, a hankali gaba dayan sassan jikin badakaren ya cigaba da bushewa har sai da gaba dayan jikinsa ya bushe rakau, kawai sai akaga jikinsa ya fara tsattsagewa daga karshe ya tarwatse yayi bindiga sai ga sassana jikinsa yayi filla-filla a sama.
Cikin tsananin razana sauran Dakarun suka zare makaman su sannan sukayo caa akan wannan siririn mutumin da nufin su yagalgala shi, kawai sai akaga ya nuna su da dan yatsa, take wata iska Mai tsananin wari ta kanannade wadannan Dakarun suka Kam a wuri guda, ba zato Kuma sai akaga su ma jikinsu Yana bushewa kamar yadda na farko yayi, Nan da Nan su ma suka tarwatse sukayi filla-filla a sama tamkar an watsa Hoda a sama.
Cikin dimaucewa da razana SARKI ZURMATU ya Mike tsaye sannan ya dakawa Sauran Jaruman Gasar tsawa akan maza su kama Masa wannan mutumin..
Nan take gaba dayan Jaruman Gasar suka zare zabga-zabgan makaman su sannan suka rugo izuwa kan wannan siririn mutumin.
Sama da Jarumai dubu Hamsin ne suka yanyameshi tamkar an ajiye kwayar gero a tsakiyar gidan tururuwa.
Nan fa wannan wannan siririn mutumin ya wanzu Yana ta dukan Jaruman Gasar da wannan siririyar takobi Mai kamar Sanda, duk Wanda ya doka da ita sai a ga ya bushe rakau daga bisani yayi bindiga, shi kuwa Koda wani daga cikin jarumin ya samu nasarar saransa da takobi sai yaji tamkar ya sari Dutse, kai ko naushinsa akayi sai suji tamkar suna naushin bishiya domin hannunsu ma har karewa yakeyi.
Nan fa hankalin mutane ya Dugunzuma ainun domin an rasa Wanda zai iya dakatar dashi, Kuma gashi sai Kara ragargazar Jaruman Gasar yake.
Kafin cikar rabin sa'a ya kashe sama da Jaruman Gasar dubu arba'in.
Koda ganin irin wannan mummunan kisan gillar da wannan siririn mutumin yake yiwa Jaruman Gasar sai ya kwarara wani uban ihu Mai tsananin razanarwa, Nan take ya bawa Sarkin yaki DURKUL Umarnin cewa Maza ya tattaro gaba dayan DAKARUN YAKINSA cikin gaggawa suzo a tari wannan makiyin.
Kafin cikar sa'a guda siririn mutumin Nan ya Karar da gaba dayan Jaruman Gasar, ya zamana cewa ya kashe dukkansu babu mutum Daya a tsaye face shi, Kuma har yanxu babu alamar gajiya a tare da shi.
Nan take ran SARKI ZURMATU ya Baci ainun, domin jikinsa gaba Daya karkarwa yakeyi saboda tsananin fushi, Bai San sa'adda ya zare lafceciyar takobinsa ba, sannan ya daka tsalle da nufin tunkarar wannan siririn mutumin.
Yana dirowa Kasa, sai ya falfala da gudu inda wannan siririn mutumin yake Yana zuwa suka kacame da sabon masifaffen yaki na gaban kwatance, Nan fa SARKI ZURMATU da SIRIRIN MUTUMIN Nan suka tashi hankalin kowa da ke wajen.
Domin a ranar kowa ya tabbatar da sadaukantakar SARKINSU ta yadda yake iya yaki da wannan siririn mutumin batare da ya iya lakutar Koda jikinsa ba.
Tsananin zafin naman Sarki Zurmatu yafi gaban kwatance domin duk irin Sara da dukan da wannan siririn mutumin yake kawo masa Bai taba samun nasarar Koda lakutar jikinsa ba.
Hasalima Sarki Zurmatu Yana yawan samun nasarar saransa da takobi, sai dai saran baya tasiri domin ji yake kamar Dutse yake Sara.
Ana cikin haka ne wannan siririn mutumin ya shammaci Sarki Zurmatu ya Doki kirjinsa da kafar hagu, saboda karfin dukan sai da Sarki yayi baya tamkar an janye shi da Kugiya sannan ya baje a Kasa, cikin tsananin zafin nama siririn mutumin ya dako tsalle sama da nufin ya fillewa SARKI ZURMATU Kai, ba zato ba tsammani sai aka SADAUKI USAMA tamkar an cilloshi ya Doki siririn mutumin iyakar karfinsa, saboda karfin dukan sai da siririn mutumin yayi tafiyar taku biyar sannan ya turje.
Tabbas kowa a filin hankalinsa yayi matukar mummunan tashi saboda ganin irin Jarumtakar wannan siririn mutumin, domin a tarihin Jarumtakar SARKI ZURMATU ba'a samun jarumin da iya fafatawa dashi na tsawon dakika hamsin ba batare da yayi nasara akanshi ba, Amma yau gashi wani hatsabibin Bil'adama yayi gagareshi har na tsawon sa'a guda.
SADAUKI USAMA ya rike hannun Sarki Zurmatu ya tashe shi tsaye sannan ya risina yace ya shugabana inaso ka bani akan wannan Matsafin mutumin domin na kawo karshensa.
SARKI ZURMATU ya ce je ka na baka wannan damar, sannan ka sani cewa muddin ka samu nasara akan wannan siririn mutumin to Kai ne Wanda ya lashe KAMBUN GASAR JARUMTAKA, Kuma a take zan tabbatar da Alkawarina a gareka.
Nan take SADAUKI USAMA ya falfala da gudu ya tunkari wannan siririn mutumin suka kacame da sabon masifaffen yaki mai tsananin tashin hankali...
Ala'marin Boka RAKUL kuwa, hankalinsa ne yayi mummunan tashi a bisa ganin irin 6arnar da wannan siririn mutumin yayi musu.
Kuma yayi iyakar bakin kokarinsa don gano ko wanene wannan siririn mutumin Amma Abu yaci tura, domin yayi Amfani da dukkan sihirin tsafinsa donyi bincike a madubin tsafinsa Amma daga karshe sai ya ga madubin tsafin yayi bindiga ya tarwatse..
Sannan Kuma yayi iyakar kokarinsa don ganin ya shiga halwar tsafinsa Amma Abu ya gagara, domin da ya matsa da bincike ma sai yaji gaba dayan jikin ya dume da mugun zafi tamkar an tsoma cikin RIJYAR WUTA GABA DUBU, ba shiri ya hakura ya zauna cikin zullumi da tsananin razana.
Bayan SADAUKI USAMA ya tari wannan siririn mutumin sai suka kacame da masifaffen yaki mai tsananin ban tsoro...
Wohoho! Idan SADAUKANTAKA ta hadu da JARUMTAKA dole ne yaki ya zamo TURMUTSUSUN BALA'I.
Nan fa suka wanzu suna kaiwa junansu Sara da suka cikin tsananin zafin nama na gaban kwatance tamkar walkiya, duk lokacin da Takubbansu suka hadu sai aga tartsatsin wuta ya tashi yayi sama tamkar Batoyi Yana feshin wuta..
Yayinda bala'i yakai bala'i sai aka ga wannan siririn mutumin ya kumbura ya zama wani Katon mutum cikin zafin nama ya harba SADAUKI USAMA Nan take SADAUKI USAMA yayi sama sannan ya fado Tim! A matukar galaibace har idanunsa na gani dishi-dishi saboda tsananin wahala.
Ba zato ba tsammani sai aka ga wannan mutumin ya kyalkyale da wata mahaukaciyar dariya Mai kama da kukan beraye, sannan ya rike ya zama wasu gungun bakaken aljanu wadanda adadinsu yakai Milyan biyu, kowannensu rike da muggan makamai.
Sannan sai ga wani Gabjejen basamuden Katon Aljani ya fito gaba Sannan ya ce" SUNANA SARKI KALJUL Mai Mulkin BIRNI GIRWAL na jinsin bakaken aljanun Duniya.
Bincike ya tabbatar min da cewa babu wani Sarki Mai karfin mulkin ka a duniyar bil'adama kamar ka, sannan kafi kowane Sarki Jarumtaka a cikin jinsin bil'adama.
Ni Kuma Ina kishin naga Sarkin da ya hada duk irin siffofin da nake da su, wato Karfin Mulki da Jarumtaka.
A bisa wannan nake yaki da duk Wanda naga Yana Neman kwatanta irin IZZAR MULKIN da nakeyi.
A halin yanzu na kashe sarakuna DUBU HAMSIN DA BAKWAI masu irin wannan halayyar.
Don haka Kai ne na cikon Dubu hamsin da takwas, don haka babu wani bala'i da zai Hana ni ganin bayanka da ni da jama'ata.
Kuma tabbas sai mun shafe komai na wannan birnin ya zama
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 5 Chapter of 12