Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 12
yamma da Arewa. Boka RAKUL ya ci gaba da cewa Ina Mai tabbatar maka da cewa, muddin muka bi bayansu tare da wadannan IFIRITAI to zamu iya cimmasu kafin su Isa birnin SIN da ragowar sa'a biyar. Koda Jin wannan batu sai hankalin su Sarki ya fara kwanciya, sannan Waziri Mikilas ya dubi Boka RAKUL ya ce, to yanxu tayaya zamu iya samun nasara a kansu yayinda muka riski wadannan Aljanun? Koda Jin wannan tambaya sai Boka RAKUL yayi shiru Yana tunani Mai zurfi, bayan tsawon lokaci Yana tunani daga can sai ya dago Kai ya Kalli Sarki Zurmatu da Waziri Mikilas sannan ya kyalkyale da dariya tamkar babu wata damuwa a ransa.. Bayan yayi Mai isarsa, ya dube su yace ku kwantar da hankalinku domin na gano mana babbar mafitar da zamu jefi tsuntsu biyu da Dutse Daya. Sarki Zurmatu ya ce fahimtar damu mafitar domin muji. Boka RAKUL yace mafitar ita ce, dole na Kasa Sarkin yakin ka ya tattaro mana gaba dayan JARUMAN GASAR JARUMTAKA su zo mu hadu mu hau Saman wadannan IFIRITAI domin muje dasu inda zamu yaki wadannan Aljanun. Da zarar mun riskesu sai muyiwa sauran jaruman Gasar bayanin cewa duk Wanda ya samu nasarar Kwato jarumi Margim daga hannunsu to shi ne ya lashe wannan Gasa. Kunga kenan burinmu zayyi saurin cika, domin nasan mawuyacin abu ne wani daga cikin jaruman Gasar ya tsira da rayuwarsa daga bala'in wadannan ALJANU. Koda Jin wannan tsantsar hikima da hangen nesa irin na Boka RAKUL sai dukkansu ukun suka bushe da mahaukaciyar dariya kamar bazasu dena ba, domin a zatonsu babu abinda zai hanasu samun nasara. Nan take Sarki Zurmatu yayi gagarumin Shirin yaki sannan ya fito ya wuce fada Waziri Mikilas da Boka RAKUL na take masa baya. Yana zama Kan KARAGARSA sai ya aika aka kira masa Sarkin yakinsa Mai suna DURKUL, wani gabjejen basamuden Kato ne Mai kirar manyan sadaukai majiya karfi. Koda Sarkin yaki DURKUL yazo gaban Sarki sai ya risina ya kwashi gaisuwa. Nan take Sarki Zurmatu ya fadawa Sarkin yaki duk irin abinda yake so akan Jaruman Gasa, cikin girmamawa Sarkin yaki yace angama ya shugabana Nan take Sarkin yaki yaje masaukin sauran jaruman Gasar sannan ya busa wani Kaho na musamman, Wanda da an busa shi to kowa daga cikin jaruman Gasar yasan cewa ana bukatar ganinsu cikin gaggawa. Nan da Nan kowanne daga cikinsu yayi gagarumin Shirin yaki sannan suka fito filin Gasar suka tsaitsaya suna jiran Umarni. Batare da Bata wani lokaci ba, Sarki Zurmatu yasa aka Tara gaba dayan mutanen birnin. Dama tuni SARKI FALWAN da YARIMA FAZAMAL da sauran zakakuran dakarunsu sunzo fadar Sarki Zurmatu cikin gagarumar shigar yaki. Bayan kowa ya halarci fadar, sai Sarki Zurmatu ya Mike ya fuskanci mutanen birnin gaba Daya sannan ya ce, " yaku jama'ar birnin BALLUS Mai albarka, kuyi sani cewa bayan fara Gasar Jarumtaka a yau din nan, wata Babbar matsala ta tunkaro mu, wadda indai bamuyi maganinta ba to tabbas sai kowa ya halakka a wannan birni.. A bisa wannan dalili ne muka shirya akan zuwa magance wannan matsalar, Sannan Kuma za'a cigaba da gudanar da Gasar Jarumtaka a can inda zamu tari abokan gaba, bayan mun gama da su sai mu dawo gida domin karasa Gasar da Kuma tabbatar da Alkawarinmu akan Wanda yayi nasara. Don haka yanzu take zamu tattara namu'i namu domin muje mu tari makiya don jinkirin kadan na nufin hallakarmu gaba Daya. Nan da Nan sai fadar ta kaure da hayaniya saboda Jin bayanin da Sarki yayi.. Nan da Nan kowa ya shiga cikin tsananin tashin hankali, domin wasu Nan take suka fara yin kuka. Koda ganin yadda mutanen suka firgice suke ta kace nace, sai Sarki Zurmatu ya daka masu tsawa, Nan take kowa yayi tsit tamkar daukewar ruwan sama. Kawai sai ya dube su a fusace ya ce bamu da isasshen lokacin batawa, kuyi hakuri kawai kuyi fatan Alheri, lallai mu ne da Nasara. Don haka a yanxu zan bar Amanar Kasa ta a hannun Waziri Mikilas domin yaci gaba da tafiyar da al'amarin Mulki kamar yadda aka Saba kafin mu dawo. Batare da wani Bata lokaci ba, Sarki Zurmatu da su Boka RAKUL da su Sarki FALWAN sukayi bankwana da sauran jama'a suka nufi babban filin Gasar Jarumtaka inda zasu hadu da Jaruman Gasa domin a dunguma a tafi. Da zuwansu filin Gasar sai suka iske Jaruman Gasar a tsaitsaye kimanin su dubu Dari cikin mummunar shigar yaki. Nan da Nan batare da Bata lokaci ba Boka RAKUL yayiwa Jaruman Gasar bayanin komai, sannan ya fiddo wani garin magani da cikin aljihunsa, sannan yayi tsafi garwashin wuta ya kama sannan ya barbada garin maganin a sama, kawai sai wani bakin Hayaki ya rinka tashi Yana taruwa a gefe guda, sai da hayakin ya shafe dakika Dari arba'in Yana tsiri a sararin samaniya sannan akaga ya rikide ya zama wasu manya-manyan halittu masu matukar girma har izuwa Kaso guda dubu, sannan kowannensu Yana da fuka-fukai guda Dari biyu da tamanin. Cikin girmamawa wadannan gungun Aljanun sukayi gaisuwa a wajen Boka RAKUL, sannan suka Ce me kake da bukata ya Bokan duniya? Nan take Boka RAKUL yace inaso ku dauke mu mu duka kubi bayan Aljanun da suka zo har fadar Sarki Zurmatu suka sace Sadauki MARGIM, lallai Ina so kuyi iyakar yinku domin mu riskesu kafin su Isa BIRNIN SIN. Koda Jin wannan batu sai shugaban IFIRITAN ya bushe da dariya, sannan ya ce Ashe ma bukatar ku Mai sauki ce, na rantse da KARAGAR SARKIN ALJANUN DUNIYA zamu iya riskasu a cikin abinda Bai wuce sa'a bakwai ba. Nan take suka kwashi gaba dayan Jaruman Gasar da su Sarki Zurmatu suka yi sama dasu a cikin tsananin gudun da yafi gaban kwatance. Wannan shi ne abinda ya faru a birnin BALLUS bayan su Sarki Zurmatu sunyi gagarumar shigar yaki sannan sun tafi domin riskar abokan gaba. ******. ***** ***** ***** A yamma da Kasar birnin SIN Kuma akwai wata kyakkyawar Kasa ta musulmai Mai suna NURUL HAYAT, Ita dai wannan Kasa na karkashin mulkin wani Sarki Adali Mai rikon addini da son zaman lafiya ana kiransa da suna MUSBAHU. SARKI MUSBAHU ya kasance tsoho dan shekaru casa'in da biyu, Amma Kuma har yanzu jikinsa Daram yake. SARKI MUSBAHU ya kasance Yana da wani da guda Daya tal a duniya mai suna USAMA. Usama shi kadai ne daa a wurin SARKI MUSBAHU Kuma ya kasance Gawurtaccen jarumi mai tsananin karfin damtse da Jarumtaka ta ban al'ajabi, domin shi kadai Yana iya yakar gari guda na Kafirai ya kashe na kashewa ya raunata na raunatawa, sannan kame matansu a matsayin bayi, ya kwashe dukiyarsu a matsayin ganima. A halin yanxu shekarun YARIMA USAMA 35 a duniya, Kuma a Kalla ya yaki kasashe guda tamanin ya Kafa tutar musulunci. Domin tun Yarima USAMA na Dan shekaru 15 a duniya yake fita Jihadi a duniya Kuma Yana samun nasara sosai akan Kafirai sbd kasancewarsa Jarumi na gaban kwatance. Hakika wannan halayya ta Yarima USAMA ba karamin farantawa mahaifinsa Rai take ba, domin bincike ya tabbatar da cewa tun SARKI MUSBAHU na Dan shekaru Ashirin a duniya yake yaki da kasashen Kafirai da matsafa, Yana musuluntar dasu, domin izuwa yanxu ya yaki kasashe sama da guda Dari bakwai Kuma duk ya samu nasara akansu. Tabbas SARKI MUSBAHU ya Sha gwagwarmaya da manyan Kafirai, Amma da karfin musulunci ba a taba kaishi Kasa a filin yaki ba. Babban burin Sarki MUSBAHU shi ne ya zamana cewa musulunci ya mamaye ko'ina da Ina a fadin duniya, a dena Bautar gumaka da ALJANU da komai Wanda ba Allah ba, ta hakane sukaci gaba da yaki suna Kafa Kalmar musulunci har sai da suka ci gaba dayan kasashen dake nahiyar su da yaki. To daman Yana daga cikin al'adar Kasar cewa duk Wanda zai hau KARAGAR MULKI ta Kasar, to dole ne ya shiga duniya domin JIHADI, Kuma bazai dawo ba har sai yayi nasarar musuluntar da kasashe a Kalla guda Dari biyar. A bisa wannan dalili ne yasa YARIMA USAMA ya fara shirye-shiryen fita JIHADI, Kuma a halin yanxu saura uku ya fita. Tun a wannan lokacin Banda farin ciki da murna babu abinda SARKI MUSBAHU da matarsa FADILA wato mahaifiyar USAMA sukeyi saboda ganin cewa dansu sauran kiris ya fita daukaka Kalmar Allah, domin sun San irin dimbin ladar da ke tattare da wannan JIHADI, Kai hatta sauran mutanen Kasar suna yin Taya YARIMA USAMA murna, sunaji a ransu cewa inama su ne zasu fita wannan JIHADIN. Haka dai rayuwa taci gaba da gudana har kwana ukun suka shude, washe gari tunda sassafe jama'ar gari sun taru makil a fada domin yiwa Yarima bankwana bisa wannan fita da zayyi. Sai da Yarima ya shafe sama da sa'a Daya da rabi Yana yin bankwana da mahaifiyarsa sannan ya samu ta sallameshi dakyar sbd tsananin sabo da shakuwa Dake tsakanin da da uwa. Batare da Bata wani lokaci ba, Yarima ya fito fada sukayi sallama da Mahaifinsa sannan suka yi sallama da sauran jama'ar gari, ya kama dokinsa dauke da jikkar guzurinsa da battar ruwansha ya hau ya tunkarin hanyar barin garin. Koda fitowarsa wajen birnin sai ya tunkari hanyar BIRNIN SIN Kai tsaye..... Wannan shi ne abinda ya faru a birnin NURUL HAYAT bayan YARIMA USAMA ya fito duniya yada kalmar Allah. ***** **** **** **** Ala'amarin wadannan gungun Aljanun na BOKA GARGUS kuwa, lokacin da suka sato Sadauki MARGIM sai suka kasance suna tsala matsanancin gudu a sararin samaniya, suka rinka gifta gajimare tamkar kibiyar da aka harba ta.. Sai da suka shafe sama da sa'a shida suna tsala gudu batare da wata matsala ba.. Kwatsam ba zato ba tsammani sai suka hango wani bakin Hayaki ya turnuke a gabansu, Kuma ya cika hanyar daga sama har Kasa. Saboda tsananin yawan hayakin har tokarewa yake da sararin samaniya, Nan take wannan bakin Hayakin ya rikide ya zama wadannan gungun IFIRITAN masu dauke da su Sarki Zurmatu da sauran jaruman Gasa. Koda ganin haka sai gaba dayan Aljanun suka ja birki sannan suka sauko Kasa bisa turba, sai Suma su Sarki Zurmatu suka sauko daf da su. Kawai sai Boka RAKUL ya dubi wadannan Aljanun ya tuntsire da mahaukaciyar dariya wadda Amsa kuwwarta ta cika Dajin gaba daya, bayan yayi Mai isarsa sai ya dube su yace, " ya ku wadannan ALJANU tabbas Kun tafka babban kuskure da har kuke mafarkin rushe mana burinmu ta hanyar sato Sadauki MARGIM domin kaiwa SHUGABAN KU BOKA GARGUS. To kuyi sani cewa a yau zamu dandana maku azabar da tunda akayi duniya ba'a taba yiwa wani ba, domin babu dayanku da zayyi Rai. Koda Jin wannan batu daga bakin Boka RAKUL, sai wadannan Aljanun suka kyalkyale da dariya tamkar ana ruwan aradu, daga bisani sai shugaban bakaken aljanun ya nuna rundunarsu Boka RAKUL yace, yanzu ku a tunaninku iya ku kadai zaku iya kashe mu sannan ku kwace jarumi margim daga hannunmu? To kuyi sani cewa mun rantse da shugabanmu Koda yawanku ya ninka haka sau Dari ba zaku iya hanamu aiwatar da wannan aikin ba, don haka Muna masu shawartarku da ku kauce daga Kan hanyarmu domin mu cika aikin Dake gabanmu, idan ba haka ba Kuma dayanku bazai tsira daga kaifin takobinmu ba.. Koda Jin haka sai ran Boka RAKUL da na Sarki Zurmatu ya 6aci har ma zuciyarsu ta kama tafarfasa kamar zata kone, Nan take yace wa wadannan JARUMAN GASAR guda dubu Dari Maza ku afka masu Muga iyakar jarumtakarsu. Koda Jin wannan batu sai gaba dayan Jaruman Gasar Nan suka zare makaman su sannan suka ruga izuwa kan wadannan Bakaken Aljanun, Suma sai suka rugo garesu duk da cewa yawan Aljanun Bai wuce dubu tamanin ba.. Wohoho! Inda ace mutum na Nan lokacin da rundunoni biyu zasu hadu, da sai yayi tunani kamar tsakanin mutanen duniya da aljanun duniya ne za'a kafsa yaki saboda tsananin yawansu. Karar sawayen Jaruman Gasar da na Aljanun ya haddasa girgizar Kasa Mai tsanani, kururuwar mazaje ya haifar da dodewar dodon kunnuwan mutane Nan take wasu suka rinka kurumcewa. Yayinda wadannan rundunoni biyu suka hadu, Kaico! Bala'i ba'a sa masa Rana, Kuma tabbas idan kwana ya kare to dole ne sai anje, haka Kuma idan Kaji ance ga ki gudu, to sa gudu ne Bai zo ba.. Nan da Nan Aljanun Nan sukayiwa Jaruman Gasar Nan rubdugu da nufin su yagalgala su, sai dai kaga Aljani ya kawowa mutum caka da tsinin bakinsa, da zarar ya goce to duk abinda ya samu take yake kamawa da wuta ya kone kurmus Koda kuwa Dutse ne. Nan da Nan farmakin da aljanun suke kawowa Jaruman Gasar ya haddasa kamawar wuta a cikin Dajin gaba Daya, Amma har kawowa i'yanzu ko jarumin Gasa Daya Basu kashe ba. Domin Jaruman Gasar suna kaucewa duk harin da aljanun ke kawo masu. Sai da aka shafe dakika biyu cur ana fafatawa Amma ba Wanda ya samu nasarar komai, tabbas wadanda Jaruman Gasar sun kasance sadaukai na gaske, domin duk Wanda yaga irin harin da aljanun ke kawo masu Kuma suna kaucewa harin to dole ne ya ya jin-jina masu. Koda cikar biyu da rabi, sai shugaban bakaken aljanun yace kowa ya Dakata, Nan take kowa ya cak kawai sai ya dubi Jaruman Gasar yace " tabbas Kun tafka babban kuskure da har kuka yarda kuka sallama rayuwarku domin yakarmu, don haka idan Kun yi a wannan farmakin na farko bari Muga yadda zakuyi da na biyu.. Gama fadin hakan keda wuya sai aka ga shugaban bakaken aljanun Nan ya wangame bakinsa Yana Mai kyalkyala wata irin dariya ta musamman Mai hade da wata irin iska Mai matukar karfin tsiya.. Nan take sauran Aljanun suka rinka zama iska suka shigewa ta cikin bakinshi, yayinda iskar ta rinka surar Jaruman Gasar tana makasu a jikin bishiya, Nan da Nan iskar Nan ta galabaitar da sama da Jaruman Gasa dubu arba'in, a wannan lokacin tuni gaba dayan Aljanun sun gama s**GASAR JARUMTAKA** LITTAFI NA UKU ✍️✍️ PART A ✅✅ MARUBUCI: NAJIBULLAH MUHAMMAD 🧔 TYPING/POSTING NAJIBULLAH MUHAMMAD 🥷🥷 Whatsapp Number 08112778656 ************************* Lokacin da wannan jibgegen aljanin ya takarkare wajen kisan Jaruman Gasar, sai kawai yaji wani abu ya doke shi ta baya, saboda tsananin karfin dukan sai dai yayi tafiyar taku goma sannan ya samu dakyar ya turje. Cikin tsananin mamaki, sai Aljanin ya waigo don ganin Wanda yayi wannan gagarumin aikin, ba wani bane ya gani a tsaye rike da takobi cikin gagarumar shigar yaki ya rike kugu Yana murmushi face SARKI ZURMATU. Cikin tsananin mamaki Aljanin ya juyo ya Kalli Sarki Zurmatu yace, ya Kai wannan Sarki Ina Mai shawartarka da ka tattara sauran dakarunka ku koma gida domin bazaku iya kwatar jarumi margim a hannunmu ba. Koda Jin wannan tambaya sai Sarki Zurmatu ya ce, na rantse da girman KARAGATA Koda BOKA GARGUS dakanshi yaxo Nan to sai na hallakashi da karfin tsiya Kuma na kwaci Jarumi Margim. Koda Jin wannan batu sai ALJANIN ya bushe da mahaukaciyar dariya wadda ta sa gaba dayan Dajin ya hautsine da wata irin Kara tamkar ana ruwan kwarankwatsa a sama, sai da ya tsuke bakinsa sannan komai ya lafa, daga can ya dubi Sarki Zurmatu ya ce to ai sai an gwada akan San na kwarai muje zuwa ni da Kai a San Gwani. Kafin wani daga cikinsu ya Kara cewa wani abu, tuni SARKI ZURMATU ya falfalo da azababben gudu tamkar Mai Shirin tashi sama, yayo Kan wannan Aljani Yana ihu da Karaji. Shi kuwa Aljanin sai ya daga kafarsa guda da nufin ya talitse shi, cikin tsananin zafin nama na ban mamaki Sarki Zurmatu ya daka wani wawan tsalle ya hau Kan Saman tafin kafar Aljanin sannan ya rinka falfalawa da azababben gudu yana tsalle-tsalle a samansa tamkar Dan biri ya hau Katuwar bishiya. Nan da nan Aljanin ya rinka kawo mahaukacin duka a jikinsa da nufin ya mako Sarki daga jikinsa, Amma duk Inda ya Kai duka sai Sarki Zurmatu ya daka tsalle ya cigaba da falfala gudunsa.. Haka yayi ta yi har ya iso Kan Kafadarsa cikin bakin zafin nama ya daga falleliyar takobinsa ya soka ta a jikin wuyan wannan ALJANIN, Nan take Takobin ta lume a cikin wuyan tamkar an luma wuka a cikin kabewa. Kawai sai Sarki Zurmatu ya rike takobinsa Yana Lilo a sama, cikin hargowa da mamunga Aljanin ya cafko Sarki Zurmatu ya jayo shi tare da takobinsa sannan ya mangareshi da dayan hannun nasa, saboda karfin dukan sai da Sarki Zurmatu yayi katantawa a sama sannan ya mako a jikin wata Katuwar bishiyar Zaitun Mai tsawo da kauri har sai da jijiyoyin bishiyar suka tun6uko daga cikin Kasa sannan suka fado Kasa a tare da bishiyar. A wannan lokacin tuni SARKI ZURMATU ya Suma saboda tsananin dokuwar da yayi a jikin bishiyar, ya baje a Kasa wanwar ko shurawar kirki baya yi, Amma duk da haka takobinsa na rike a hannunsa. Koda su Boka RAKUL da su Sarki FALWAN da sauran Dakarun suka ga haka sai suka yo kanshi domin su ceto rayuwar shi. Ba zato ba tsammani sai aka wannan NARKEKEN ALJANIN yana wani irin ruri mara dadin ji, ga jini na kwarara a jikin wuyansa, Nan da nan ya haukace ya rinka Kai duka da taku tako'ina a cikin Dajin. Ya zamana cewa Yana Kai duka da hannuwansa, sannan Yana feshin wuta da bakinsa sannan Yana Kai mugun taku da kafufuwansa, cikin kankanin lokaci ya hautsina Dajin gaba Daya domin duk abinda hannuwansa suka buga Nan take abun yake ragargajewa tamkar mutum ya taka karmami, Nan da nan hargowa da yawace-yawacen da yake a cikin Dajin ya haifar da manyan ramummuka masu tsananin zurfi da fadi saboda mugayen takun da yake kawowa da Kafarsa, sannan Wuta ta kama bishiyoyi da Duwatsun Dajin, ya zamana cewa Dajin ya ya dume da wani irin mugun zafi Wanda ka iya Narkar da mutum saboda tsananin zafin Wutar. Nan da nan Boka RAKUL yayi tsafi sai ga wata Katangar tsafi ta bayyana a tsakaninsu da wannan rafkeken Aljanin, ya zamana cewa duk wannan zafin Wutar da girgizar Kasar basa ji daga inda suke. Bayan kamar faruwar hakan da kamar Dakika Dari biyu da sittin sai akaji Aljanin yayi shiru, sannan ya dena Kai duka da feshin wuta. Kawai sai akaga Aljanin ya wangame bakinsa sai gani akayi jikinsa nata narkewa Yana fadowa Kasa, Bai gushe ba Yana yin hakan har sai da gaba dayan jikinsa ya narke ya zama ruwa, Nan da sai ya sake rikidewa ainihin siffarsu ta Dakarun Boka GARGUS, sai gashi sama da ALJANU Dari uku daga cikin sun mutu sakamakon soka mashi takobi a wuya da Sarki Zurmatu yayi. Cikin tsananin bakin ciki Shugaban Aljanun yazo kusa da gawarwakin 'yan uwansa ya tsaya, yana zubar da hawayen bakin ciki da takaicin rashin su. Sannan ya dubi su Boka RAKUL ya ce, yaku wadannan mutane kuyi sani cewa fiye da shekaru dubu uku baya ba a taba samun wata halitta data iya kashe Koda guda Daya daga cikinmu ba, Amma yau gashi sarkinku yayi sanadiyyar Asarar sama da guda Dari uku. Don haka na rantse da gemun Sarkin Aljanu cewa dayanku bazai bar Dajin Nan a Raye ba, duk sai mun zare maku ruhin numfashi. Yanzun Nan zamuyi maku mummunan kisan gillar da ba a taba yiwa wani irinsa ba. Gama fadin hakan keda wuya sai gaba dayan ragowar Aljanun suka ruga izuwa kan su Boka RAKUL da sauran Dakarun dauke da muggan malamai don suyi masu mummunan kisan gilla, a lokacin lokacin gaba dayan adadinsu Bai wuce su Dari takwas ba. Da zuwansu sai suka hau Sara da Sukar Jaruman su Sarki FALWAN Nan da Nan suka fille kawunan mutane suka rinka shawagi a sama tamkar ana ruwan sama. Nan fa mutuwa ta baje kolin Kasuwarta a wurin, domin duk Wanda suka Sara da takobinsu sai dai kaga ya ragargaje daga karshe ya tarwatse yayi bindiga tamkar an cika balan-balan da iska. Cikin kankanin lokaci suka kashe sama da Dakaru dubu uku. A bangaren Boka RAKUL kuwa sai ya rinka Amfani da karfin tsafi wajen Kashe Aljanun, Amma bisa mamaki sai ga tsafin baya masu komai, walau wuta ko kibiyoyi ya watsa masu, Kai kome ya jefa masu, to da zarar yazo kusa da su sai abun ya narke ya fadi Kasa. Ala'marin da yayi matukar bashi mamaki kenan, kawai ya rinka kokarin kare Kansa da karfin sihirin tsafi. Abinda Bai sani ba shi ne duk abinda ke faruwa a filin wannan Yakin BOKA GARGUS na hangosu Kuma Yana bawa wadanda ALJANUN kariya ta musamman ta yadda babu tsafin da zai iya tasiri akansu. A bangaren su Sarki FALWAN da YARIMA FAZAMAL kuwa, sai suka kutsa cikin Aljanun suka wanzu suna masu Kai masu Sara da suka Amma duk Aljanin da suka Sami nasarar Sara a wuya ko a wani wuri sai suji tamkar sun sari karfe, ko kadan makaminsu baya tasiri a jikinsu. Ala'marin da yayi matukar Dugunzuma hankalinsu kenan ya zamana cewa har sun fara gajiya basa iya mayar da martani sai dai kokarin kare Kai kawai. Ana cikin haka ne wani BARDE daga cikin ALJANUN ya shammaci YARIMA FAZAMAL ya lafta mashi Sara a kirji, Nan take Takobin ta lume ta haifar da wani katoton rauni. Ba shiri jini yayi tsartuwa da feshi daga kirjin nasa, kawai sai Yarima ya kwarara uban ihu sannan ya sulale Kasa sumamme faruwar hakan keda wuya sai wannan barden ya daga takobinsa da nufin datse Kan Yarima gida biyu, Koda Sarki FALWAN yaga abinda ke Shirin faruwa sai dako wani wawan tsalle tamkar an cilloshi daga cikin baka, Yana zuwa sai ya dira a gaban wannan Barden cikin tsananin zafin nama na gaban kwatance yayi alkafira ta tsakanin Kafafunsa ya bullo ta bayansa, kawai sai ya sa takobinsa ya tsargeshi gida biyu, sai gashi kowane bangare ya fadi can gefe guda. Nan take Sarki FALWAN ya Suri YARIMA FAZAMAL da hannu guda tamkar shaho ya Suri 'yan tsaki, ya Dora shi a Kan Kafadarsa sannan ya falfala da guda izuwa cikin Dakarunsa sannan ya cire wani Jan mayafi Dake daure a kugunsa ya daure Masa inda ke zubar da jinin, Sannan ya sunkuya ya dauki yarima ya Goya shi a bayansa ya daure shi tamau, sannan ya fuskanci Dakarun Aljanun yaci gaba da fafatawa. A wannan lokaci ALJANUN sun kusan Karar da gaba dayan Dakarun Sarki FALWAN domin sun kasance sama da mutum dubu Tara da Dari bakwai, Wadanda suka rage Basu wuce Dari uku ba. Kai! Komai rashin imanin mutum idan yaga yadda aka salwantar da gawarwakin mutane birjik a Kasa tamkar kanyar da ba a so, dole ne ya tausaya masu. Domin duk Inda mutum ya duba gawarwakin Dakarun Sarki FALWAN ne fululu a kwance a mace, wasunsu kawuna aka fille masu, wasu Kuma an fafake masu ciki an fitar da gaba dayan kayan cikin, wasunsu kuwa an kashe su ne ta hanyar yi masu gutsin-gutsin tamkar ana daddatsa Albasa. Kai! A wannan Rana Kasa Tasha Azaba saboda tsananin yakin da aka kafsa a samanta hatta bishiyoyin dajin da Duwatsun Dajin duk sai da suka ragargaje suka ratattake tamkar an tattaka busassun Kasusuwa. A wannan lokacin akwai sauran JARUMAN GASAR sama da guda dubu Saba'in a can gefe sun zura Ido suna jiran Umarnin Sarki Zurmatu alhalin Kuma Sarki ya Suma Kuma gashi har an kusa Karar da Dakarun Sarki FALWAN Amma Bai FARFADO ba, Kuma tabbas sun San cewa muddin wadannan Aljanun suka kashe Dakarun gaba daya, to kansu zasu dawo. To kenan ya matsayin kasancewarsu a cikin GASAR JARUMTAKA? Suna cikin wannan tunani ne suka hango farfadowar Sarki Yana Mai caka takobinsa a Kasa sannan ya riketa ya dafa ya Mike tsaye. Koda mikewarsa tsaya Kuma ya kyallara Ido yaga irin mummunar Barnar da wadannan ALJANUN sukayi sai ya takarkare ya kwarara uban ihu Mai tsananin razanarwa, Wanda yasa aka tsayar da yakin cak, kowa ya waigo wajen Mai ihun. A wannan lokacin an kashe gaba dayan Dakarun Sarki FALWAN shi kadai ne yake fafatawa dashi sun Kasa samun nasara a Kansa, a gefe guda Kuma ga BOKA RAKUL can Yana ta Amfani da karfin sihirin tsafi wajen kokarin hallaka Aljanun Amma baya tasiri. Koda SARKI ZURMATU ya gama ganin wannan mummuna kisan gillar da ALJANUN Nan suka yiwa mutane, sai ransa ya 6aci zuciyarsa ta kufulo, saboda tsananin fusata har fuskarsa ke yin gatsine, Nan take jikinsa ya kama yin karkarwa saboda tsananin fushi jijiyoyin jikinsa suka yi burdin-burdin, Kwanjinsa ya kukkumbura tamkar an hurashi da iska. Bayan shudewar dakika Dari da saba'in sai aka ga SARKI ZURMATU ya falfalo azababben gudu saboda karfin gudun har wata karamar guguwa ke biye dashi, Koda ya zama tazarar shi da Aljanun Bata wuce taku goma ba, sai ya daka wani wawan tsalle yana Mai zare takobinsa, ai kuwa

Chapter 3 of 12