tsoro ya ja da baya ya tsaya, sannan ya ce suwaye ku, me ku ke nufi da ni? Maimakon su bashi Amsa sai gaba dayansu sukayi sujjada a gareshi. Babban cikinsu ya nuna wannan kambun tsafi dake jikin hannun LU'UMANU ya ce, gaba dayanmu nan bayi ne masu Bauta ga wannan kambu da ke hannunka. Lallai zamu kasance masu biyayya ga Wanda duk ya daura shi. Fadi bukatarka kowace iri ce yanzun nan mu biyata. Yayinda LU'UMANU yaji haka sai farin ciki ya lullube shi, ya dubi aljanun nan ya ce" inaso ku Kaini birnin da babu kamarsa a kyau da kawatuwa. Kafin ya gama rufe bakinsa tuni Aljanun nan sunyi sama da shi. Cikin abinda Bai wuce dakika dari uku ba suka ajiye shi a tsakiyar fadar birnin TEHRAN. A wannan lokaci ko Sarki MAHARAMU na zaune bisa karaga, fadawa sun kewayeshi ana tafiyar da harkokin mulki. Kawai sai LU'UMANU ya kama wuyansa ya murde ya yada gawarsa. Gaba daya fadar ta rude da ihu, Dakaru sukayi caa a Kansa. Koda ya daka masu tsawa sai duk suka tarwatse kowa ya tsuguna Kasa bisa gwiwowinsa. Wannan alama ce ta mubaya'a. LU'UMANU ya dubi fadawa, Dakaru, da sauran jama'ar gari ya ce" ni ne LU'UMANU IBN SAMFANU. Daga yau na zama sarkinku Wanda duk ya bini zai rayu, Wanda ko ya bijire min zai fuskanci Azaba mai radadi, Kuma shayar da shi dacin mutuwa. Gaba dayan jama'ar suka ce munji mun bi ka. Daga wannan rana LU'UMANU yaci gaba da mulkin birnin TEHRAN.
Watarana Sarki LU'UMANU a cikin madubin tsafinsa ya gano wata kyakkyawar mace. Wadda ta kasance Matar Sarkin FARISA ce ana kiranta Gimbiya FATISA. yayinda Sarki LU'UMANU yaga wannan kyakkyawar mace sai ya rude ya dimauce ya kamu da tsananin begenta. Take yasa aka rubuta wasika ya aikawa Sarkin FARISA sakon cewa..
Yana so ya bashi wannan mata tasa, idan ko yaki zai zo da Kansa ya yake shi ya tafi da ita da karfin tsiya. Yayinda wannan Sako ya riski Sarkin FARISA sai hankalinsa ya dugunzuma ya rasa abinda ke Masa dadi a duniya, domin ya Dade da samun labarin Sarki LU'UMANU Kuma ya tabbatar da cewa ba karamin shu'umi bane yafi karfinsa. Sarkin FARISA ya tara 'yan majalisar sa ya sanar da su halin da ake ciki, daga bisani ya nemi shawararsu. Wazirinsa ya Mike ya ce ya mai duniya masu iya magana sunce zama lafiya yafi zama dan Sarki. Kowa anan yasan cewa babu yadda zamuyi da Sarki LU'UMANU. Kuma idan fushinsa ya tabbata a kanmu zai zo da mayakansa ya shafemu. Ni Ina ganin zaifi kyau ka rungumi kaddara ka bashi Matar nan taka, don ka ceto jama'a daga masifar LU'UMANU.
08112778656 ( Whatsapp )
Najibullah Muhammad ✍️✍️
Yayinda Sarki yaji wannan Batu sai yayi shiru Yana tunani daga can sai hawaye ya xubo masa ya ce," na amince da wannan shawara. Nan take Sarki ya Mike ya shiga ya sanar da matarsa FATISA halin da ake ciki. Koda ta ji wannan bakin labari sai ta fashe da kuka saboda bakin ciki. Ba wani bane ya janyo haka face sanin cewa, Sarkin FARISA mijinta ne na farko Wanda aka yi masu auren saurayi da budurwa. Sai da suka share shekaru shida suna soyayya kafin yin aure. Lallai suna matukar Qaunar juna. Shi ko LU'UMANU tsoho ne ya manyanta. A matsayinta na mace mai karancin shekaru da tsagwaron kyawu bata dace da LU'UMANU ba. FATISA ta dubi mijinta ta ce, ni kam akan na Auri wani ba Kai ba, gwara na kashe kaina. Koda Jin haka sai Sarki ya ce aikuwa idan kikayi haka kinci amanar soyayyarmu. Idan babu ke a duniya Ina amfanin rayuwata? Na horeki da ki rungumi kaddara kamar yadda Nima na runguma. Inason ki amince ki zauna da LU'UMANU. Ki sani cewa shekarunsa sun tura, ba lallai ne bane ya Dade a duniya. Ni da ke ko har yanzu Muna da sauran kuruciyarmu. Da zarar LU'UMANU ya mutu sai ki dawo gareni muci gaba da rayuwa. Da wannan bayani jikin FATISA yayi sanyi ta amince aka tafi da ita izuwa birnin TEHRAN, ta zauna da Sarki LU'UMANU bisa dole ba don tana so ba.
Wannan shi ne Asalin tarihin tsafin Sarki LU'UMANU da Kuma yadda akayi ya mallaki macen da babu kamarta a duniya.
Yanzu Kuma sai ku saurara dakyau domin kuji irin MASIFUN da ke cikin fadarsa da Kuma yadda zamuyi mu kubuta daga sharrinsa.
Lokacin da Sarki LU'UMANU yaga ya mallaki Gimbiya FATISA sai ya fara tunanin lallai ya kamata ya Kafa matakan tsaro na musamman don kada watarana wani yazo ya saceta. A wannan lokaci karfin mulkinsa ya tumbatsa har ta Kai cewa Yana Kai hari ga duk Kasar da yaso ya ci ta da yaki. Wani lokacin sai ya kashe Sarkin garin. Wani lokacin Kuma sai ya kama shi ya kulle a kurkuku. A bisa wannan dalili ne yasa aka gina Masa wani kurkuku da ke karkashin Kasa Mai kofofi goma Sha biyu. A kowace Kofa akwai dakarun Aljanu guda dubu goma masu tsaro. Babu Wanda ya Isa ya shiga ko ya fita, sai da ixinin Sarki LU'UMANU. Fiye da shekaru arba'in baya duk fursunan da ya shiga cikin wannan kurkuku ya shiga kenan ba za'a Kara ganinsa ba. Ba ma mutum ba, hatta Aljanu suna Jin tsoron a shigar da su cikin kurkukun Sarki LU'UMANU, saboda tsananin irin azabar da ke cikinsa. Ita ko fadar Sarki LU'UMANU an kintsa ta da tsaron tsafi, yadda duk karfin sihirin mutum bai Isa ya ratsa ta cikinta ba yayi abinda ya so. Babu wani tsafi da zayyi tasiri a cikin fadar Sarki LU'UMANU sai nasa. Komai jatumtakar mutum da zarar ya hadu da bakaken Aljanun nan guda dubu hudu da arba'in da hudu sai dai buzunsa. Har yau har gobe ba a samu Wanda ya samu Lago a kansu ba.
Sa'adda Aljani DURFAS yazo nan a zancensa sai JAFARU ya ce," har yanxu dai magana kake Amma bakace komai ba, ka zayyana mana karfin sihirin LU'UMANU, ka gaya mana matakan tsaron gidansa Amma har yanxu baka fada mana yadda zamu iya shiga kurkukun ba mu wato Aljani MARKAHUSSABUS. DURFAS ya ce haba Yaro me kake ci na baka na zuba? Idan ka bini a Sannu zan warware maku zare da abawa. Kamar yadda na fada maku a baya cewa muddin Sarki LU'UMANU na tare da kambun tsafinsa babu Wanda zai iya samun nasara a Kansa. To ku sani cewa shi wannan kambun tsafi usulinsa ya fito ne daga hannun wani gagarumin matsafin Aljani Wanda ake kira SHAMHARU. wannan Aljani na can wani tsubiri da ake kira BAHARZUS a tekun FASHA. masana tarihi sun tabbatar da cewa tun farkon kafuwar duniya babu wani mahaluki da ya taba zuwa tsubirin BAHARZUS sai Aljani SHAMHARU. Shima tunda yaje Bai dawo ba. domin ance babu wani wuri mai dadin ni'ima kamar tsubirin BAHARZUS. A wannan wuri mutum na iya ganin duniya gaba dayanta da duk abinda ke cikinta. Tamkar yadda za a zuba ruwa a cikin Koko a ga iya zurfinsa. Akan wannan tsubirin akwai bishiyoyi guda uku, bishiyar farko ta dabino ce, ta biyu ta zaitun ce, ta uku kuwa turaren wardi ne. Da mutum ko Aljan zai samu iKon samo 'yayan wadannan bishiyoyin yaci, da ya samu iKon shiga fadar Sarki LU'UMANU batare da wadannan bakaken Aljanu sun iya tsayar da shi ba. Haka Kuma zai iya gaba da gaba da Sarki LU'UMANU su gwabza yaki har ya samu nasara a Kansa.
Kuyi sani cewa tsakanin tsubirin BAHARZUS da wannan jeji da muke ciki tafiya ce ta shekara dubu Daya. Koda Aljani DURFAS yazo nan a jawabinsa sai YALISA tayi tsaki ta ce Kai dakata haka. Mufa mun gaji da gafara saa har yanxu bamu ga kaho ba, kayi kidanka kayi rawarka bamu gane inda ka nufa ba. Kasan dai a cikinmu nan kaf, babu Wanda zai iya zuwa tsubirin BAHARZUS har ya samo 'yayan wadannan bishiyoyi uku. To yanzu tayaya zamu mallake su? DURFAS yayi murmushi ya ce, yawwa ai amfanin tambaya kenan. Dama ance matambayi baya 6ata, idan baku manta ba a baya, an bada labarin wadansu mutane da aka ce ma'abota wani Addini ne da ake kira musulunci. Tabbas wadannan mutane sunci 'yayan wadannan bishiyoyi. Inda zamu samu daya daga cikinsu yayi mana jagora izuwa fadar Sarki LU'UMANU da mun samu nasara a bisa bukatarmu. Koda Jin haka sai JAFARU ya ce, yanzu a Ina zamu iya ganin wadannan mutane? Kafin Boka SULBAINI ya umarceni da daukarsu Gimbiya sima, naga Daya daga cikinsu a can jejin SALMIN a bayan dutsen BUHUR Yana yin wata irin ibada. Da zaku amince da nayi mana jagora izuwa gareshi yanzu a cikin abinda Bai wuce sa'a Ashirin da hudu ba. Koda Jin haka sai Gimbiya sima ta ce Nikam na amince, ta dubi JAFARU da YALISA ta ce, ku fa? Muma mun amince. Suka Amsa cikin hadin Baki. ALJANI DURFAS ya dubi NARGAS, GULZUM da Qaddaru ya ce bana ta taku, ko ku amince ko Kar ku amince duk daya tunda dai iyayen gidanku sun amince. Yanzu ni kadai zan daukeku gaba Daya izuwa jejin SALMIN. Na umarceku da ku hau bayana. Kafin kowa yayi wani yunkuri tuni JAFARU da YALISA sun haye kan DURFAS, Gimbiya sima ce ta biyunsu sannan Qaddaru NARGAS da GULZUM. Cikin karfi Aljani DURFAS ya yunkura yayi sama da su gaba daya tamkar Bai dau komai ba. Lallai Gaskiyar masu iya magana da suka ce, wani kayan sai amale, hakika in banda Aljani DURFAS ya cika Kato Kuma SADAUKI da Bai Isa ya dauki wadannan halittu har guda bakwai ba shi kadai. Kamar yadda ya Furta haka Ala'marin ya kasance.
Wato a cikin awa Ashirin da hudu suka Isa jejin SALMIN da zuwa sai Aljani DURFAS ya sauka a Dutsen BUHUR. Wannan Dutse na BUHUR na da matukar tsawo fadi da girma, ba lallai bane Wanda ke kasansa ya iya ganin abinda ke sama. Dirarsu keda wuya sai suka hau dube-dube Amma Basu ga komai ba Kuma basuga kowa ba. JAFARU ya dubi DURFAS cikin fushi yace, kaga irinta ki? Ina mutumin yake, gashi munzo ba kowa a wajen. Babu mamaki ma shirgata kayi. Cikin fushi da kuncin Rai, DURFAS ya dubi JAFARU ya ce Kai YARO yanzu bakaji kunya ba, ka dubi tsoho kamata kace nayi maka karya? Kai in Banda darajar biyayyata ga Gimbiya ka Isa kayi min rashin kunya na kyale ka? Ai da tuni na mitsittsike ka na ru6urbusheka ka zama gari. Koda Jin haka sai sima ta ce ya Isa. Ba fada ne ya kawo mu ba. Yanzu a wancan lokacin a dai-dai Ina kaga mutumin? DURFAS yayi nuni da Kasan Dutsen, gaba dayansu suka matsa a karshen Kasan Dutsen. Bisa mamaki sai sukaga wani kyakkyawan saurayi sanye da fararen tufafi Kuma a zaune bisa buzu ya fuskanci Gabas, hannayensa biyu a sama Yana ta fadin wani Abu da ba a Ji.
Alhamdulillah....
Mu hadu a KUNDIN TSATSUBA na daya part M don Jin cigaban wannan Kasaitacce Kuma Kayataccen labari Mai dadi da debe kewa 🥰♥️♥️♥️
Anan ni Najibullah Muhammad nake cewa ku huta lafiya 🙏🥰**KUNDIN TSATSUBA**
LITTAFI NA DAYA 1 ♥️
PART M ✍️🔜
MARUBUCI:- ABDUL'AZIZ SANI MADAKIN GINI 👮
TYPING:- NAJIBULLAH MUHAMMAD ✍️✍️
POSTING:- Najibullah Muhammad 🥷🥷
Note:- comments da likes da share ya zama wajibi ga duk masu bibiyar wannan labari, domin ta hanyar hakane kadai zai tabbatar min da cewa lallai kuna nishadantuwa Kuma Kuna godiya da samun wannan littafin. Saboda haka ku ma ya zama wajibi don nunawa marubucin farin cikinku ga wannan littafin.
Ina yi maku fatan Alkhairi tare da yi maku barka da wannan rana Mai albarka wato JUMA'AT MUBARAK ♥️♥️🙏Muna fatan Allah ya taimakemu 🙏
08112778656 ( Whatsapp )
Marubucin yaci gaba da cewa......
Cikin murna da hanzari DURFAS ya nuna wannan saurayi yace yawwa gashi nan, ga Wanda nake Baku labari. Amma Ina ganin yana cikin yin ibadarsa tukunna mu bari sai ya hattama tukunna. Sannan muje mu gaya Masa bukatarmu. Tunda sa'adda Gimbiya sima tayi arba da wannan kyakkyawan saurayi taji duk duniya babu Wanda take so da Qauna tamkar shi. Nanfa ta Kura Masa Ido ko kauda Kai Bata yi, har Qaddaru ya lura da halin da ta shiga. Ala'marin da ya bashi mamaki Amma se ya basar. Bayan kamar kimanin dakika dari da arba'in wannan saurayi ya kammala ibadarsa sannan ya Mike tsaye, ya dauki buzunsa da nufin ya wasa sawayensa. Ba zato ba tsammani sai yaji dirar wani abu mai nauyi a bayansa. Saurayin ya juya a natse batare da Jin tsoro ba, don ganin ko menene. Kawai sai yayi arba da su JAFARU tare da su Aljani DURFAS. Munzo gareka da aminci Banda niyyar cutarwa ba, munaso ka taimake mu bisa wata bukata muhimmiya. JAFARU ne yayi wannan furuci. Kyakkyawan saurayin Bai ce komai ba sai bayan ya kare masu kallo Daya bayan daya. Koda yazo Kan Gimbiya sima sai gabansa ya fadi zuciyarsa ta fara daka don ganin tsananin kyawunta. Amma sai yayi ta Maza ya kau da Kai ga barin kallonta.
Sannan ya dubi JAFARU ya ce Ina sauraro da me ku ka zo gareni? Nan take JAFARU ya kwashe labarin su gaba daya tun daga farko har karshe ya zayyane Masa. Kuma ya sake Neman taimakon sa a bisa jagorancin da zayyi masu zuwa fadar Sarki LU'UMANU. Yayinda kyakkyawan saurayin yaji abinda ke tafe da su, sai yayi shiru yana tunani. Daga can sai yace zan iya taimakon ku bisa sharadi guda, sai dai akwai matsala guda. Matsalar kuwa ita ce, Kunsan har abada ruwa da wuta basa haduwa waje daya su zauna lafiya. Ni ruwa ne ku Kuma wuta ne. Tayaya tafiyarmu zatayi dadi? Koda Jin haka sai su JAFARU suka cika da tsananin mamaki sannan ya ce, ka jefa mu a cikin duhu bamu gane abinda kake nufi ba. Kyakkyawan saurayin yayi murmushi Wanda hakan tasa kyawunsa ya Kara bayyana fiye da da. Ya ce ni ma'abocin Addinin musulunci ne, ku ko ma'abota Addinin tsafi ne, lallai babu jituwa a tsakaninmu. Saboda haka rayuwata ba irin taku bace. Munsan da haka Amma Muna so kayi addininka mu ma muyi namu, Amma ka taimaka mana domin cikar burinmu. Gimbiya sima ce tayi wannan furuci yayinda take yi Masa wani irin kallo me dauke da alamar tambaya. Ni Kam na amince zan taimake ku Amma bisa sharadi kamar yadda na fada maku da farko. Sharadin kuwa shi ne, idan bukatar ku ta biya zaku Bada Gaskiya da addinina. Wai shin menene Addinin nan naka, Kuma wa kake Bauta mawa? JAFARU ne yayi wannan tambaya.
Kyakkyawan saurayin yace addinina shi ne musulunci. Bana Bautawa kowa sai Allah Sarki guda daya Wanda bashi da Abokin tarayya. Be haifa ba Kuma ba a haife shi ba. Shi ne ya halicci sammai da kassai, Kuma shi ne ya halicci mutum da aljan ba don komai ba sai don su Bauta Masa. Ubangijina shi ne Wanda ya wanzu tun babun babu, Kai tun babun ma ba a santa ba. Wanda duk yayi Imani da shi, zai rabauta duniya da lahira Wanda ko ya bijire masa zai dandana Masa Azaba me radadi. Yaku wadannan mutane da Aljanu Ina Mai rokonku da horo a gareku akan kuji tsoron Allah. Ku tuba gareshi ku dena tsafi da Shirka. Lokacin da kyakkyawan saurayin yazo nan a zancensa sai gaba dayansu sukayi shiru aka rasa Wanda zai ce Qala.
Daga can sai Aljani NARGAS ya ce idan har kana so mu karbi Addininka, to kayi mana jagora izuwa fadar Sarki LU'UMANU sannan mu yake shi mu kawar da shi Kuma ka fito mana da Aljani MARKAHUSSABUS daga cikin akwatun karfen da aka kulle shi. Saurayin yace duk zanyi abinda kuka fada da izinin Ubangijin musulunci. Amma inaso in sani, idan nayi hakan a gaban idanunku zaku Bada Gaskiya ga Ubangijina? Kwarai kuwa ai idan kayi haka ka tabbata me Gaskiya. Shikenan na amince. Ku dauke ni mu tafi izuwa birnin TEHRAN. Kafin mu tafi ya kamata ka sanmu mu sanka, JAFARU ne yayi wannan furuci. Ni sunana JAFARU wannan ko sunanta YALISA qawata ce, Kuma garinmu daya mun fito daga birnin Sin. Wannan ko sunanta Gimbiya sima a halin yanzu ita ke mulkin Kasar LAHARIM. Wannan guntun mutumen yarimanta ne ana kiransa Qaddaru. Wannan bawan YALISA ne sunansa GULZUM. Wannan sunansa NARGAS bawa ne ga mahaifin YALISA Boka JISHEN. Shi ko wannan Katon aljanin sunansa DURFAS shikuma bawa ne ga Boka SULBAINI na Kasar LAHARIM. Ka sani cewa DURFAS ne ya bamu labarinka yace kana daga cikin ma'abota Addinin musulunci, Kuma zaka iya taimakon mu yanzu sai ka gabatar da kanka a garemu.
Kyakkyawan saurayin yayi murmushi a karo na biyu ya ce sunana HUBAIRU IBN MAS'UD. Na fito daga wata Kasa da ake kira SHAMSIL KHAIR. iyayena musulmai ne Kuma an haifeni a cikin musulunci Kuma na girma a cikinsa. Bayan na samu isasshen ilimin Addini sai nayi sallama da iyayena na shiga duniya don yada Addinin Allah a doron Kasa. Nayi yawo gari-gari kasa-kasa wasu wuraren a karbeni hannu bibbiyu wasu wuraren kuwa sai a kyamaceni harma akan kamani ayita azabtar Dani, ko aso halakani ma, Amma sai Ubangijina ya taimakeni. Wannan shi ne takaitaccen tarihin rayuwata.
Bayan HUBAIRU ya gama wannan jawabi sai su JAFARU suka kebe gefe guda sukayi kus-kus sannan suka dawo gareshi. ALJANI DURFAS ya ce ya kai HUBAIRU mun amince da sharadin da ka gindaya mana, Amma muma Muna da namu sharadin da zaka kiyaye yayinda muke tafiya tare da Kai, sharadin kuwa shi ne lallai ka nisanci yin ibada ko ambaton Ubangijinka yayinda muke dauke da Kai. Idan har kana da uzurin yin hakan to ka sanar damu mu sauko dakai kayi duk abinda zakayi. Haka Kuma bamu amince ba kayi tallan Addininka ga dayanmu har sai bayan bukatarmu ta biya. Sa'adda HUBAIRU yaji haka sai yayi murmushi ya ce shikenan na amince mu tafi. Batare da Bata lokaci ba, Aljani DURFAS ya sake rankwafawa kowa ya haye bayansa harda HUBAIRU sannan ya Bude fuka-fukansa ya tashi sama.
Wannan shi ne abinda ya faru da HUBAIRU bin mas'ud wani kyakkyawan saurayi ma'abocin Addinin musulunci Wanda soyayya ke kokarin shiga tsakaninsa da Gimbiya sima.
A can birnin TEHRAN kuwa, a yau ne Sarki LU'UMANU ya wayi gari cikin tsananin fushi da tashin hankali ainun. Ba komai ne ya janyo hakan ba, sai binciken da yayi jiya a cikin madubinsa na tsafi. Binciken ya tabbatar Masa da cewa lallai akwai wadansu mayaka da ke Shirin afko Masa. Kuma idan har suka zo zasu samu nasara a Kansa har ma su kawar da shi Kuma su sallami dukkan fursunonin dake tsare a cikin kurkukun karkashin Kasa. Bisa wannan dalili ne Sarki LU'UMANU ya tara dukkanin dakarunsa mutane da Aljanu yayi masu mummunar huduba akan lallai kowannensu ya zauna cikin shiri, shiri ba na wasa ba domin a hallaka makiya masu zuwa. Kai a wannan rana dai sai da Sarki LU'UMANU ya tattaro duka dakarun kasarsa suka cika fadarsa taf ciki da waje. Sannan ya Kara matakan tsaro ninkin na da sau Dari. Anan aka zauna ana jiran isowar Abokan gaba.
Ala'marin su HUBAIRU kuwa, tunda suka fara tafiya a sararin samaniya babu Wanda yayi magana da wani har tsawon lokaci. Tunda aka fara tafiyar Gimbiya sima ta Kasa samun sukuni, da zarar ta kishingida ta rufe idanunta don tayi barci sai ta rinka ganin hoton Fuskar HUBAIRU a cikin zuciyarta. Da zarar ta bude idanunta sai ta dubi inda yake suna hada Ido sai kowannensu yayi sauri ya kau da Kai. Nanfa Ala'marin ya damesu gaba daya domin duk halin da ta shiga irin shi ya shiga. A gaba dayan wannan tawaga babu Wanda ya lura da abinda ke faruwa sai waziri Qaddaru. Tun a can jejin SALMIN Qaddaru ya lura cewa soyayya na neman shiga tsakaninta da bakon kyakkyawan saurayin Nan. To amma da farko sai ya fara tunanin ba so bane, kawai dai Ala'mari ne na ganin abinda babu zato. To amma da aka dauki hanyar birnin TEHRAN kuwa sai Qaddaru ya tabbatar da cewa lallai soyayya ce ke Shirin afkowa. Domin kallon da masoyan ke wa junansu ya wuce na rashin sabo, don Yana dauke da alamar tambaya. Koda Qaddaru yaga Gimbiya sima ta Kasa sakat, sai ya matsa kusa da ita ya ce ya Shugabata tunanin me kikeyi ne, tun dazu naga kin Kasa yin barci Kuma kin Kasa zaune ko tsaye? Yayinda sima taji wannan batu sai tayi murmushi ta ce ai dole ne kaga na shiga wannan hali. Domin Ina matukar tunanin abinda ke gabanmu. Hakika na tsorata da labarin Sarki LU'UMANU, Nikam Ina ganin idan muka Isa fadarsa babu Wanda zai tsira daga sharrinsa. Qaddaru yayi murmushi ya ce wannan shi ne kadai abinda ya dameki? Cikin mamaki ta dube shi ta ce sai Kuma tunanin halin da na baro kasata da jama'ata. Kwaraima kuwa kinzo da magana me karfi. To Amma me kike gani dangane da burin rayuwarki, shin har yanxu kina da qudurin cigaba da gwagwarmaya har izuwa lokacin da zamu samu nasarar Bude kundin tsatsuba, ko kuwa da zarar mun mallaki aljani MARKAHUSSABUS Zaki koma gida? Sa'adda Gimbiya sima taji wannan tambaya sai ta murtuke Fuska ta ce Kai Qaddaru tambayoyinka sun isheni haka, lallai ka tsuke bakinka ko fushina ya tabbata a kanka. Cikin girmamawa Qaddaru yace tuba nake ranki ya dade ayi min afuwa bazan sake ba. Daga nan yayi shiru be Kara magana ba har suka fara hango gine-ginen birnin TEHRAN.
08112778656 ( Whatsapp )
Najibullah Muhammad ✍️ ✍️ 🥷🥷🥷
Da yake magriba tayi a wannan lokaci, fitilun garin a haskake suke ko'ina ka duba haske ne fayau tamkar da rana. Birnin TEHRAN gari ne me manya-manyan gine-gine na zamani masu manyan benaye. Saboda kyawun garin ake Masa lakabi da dausayin Hutu. Birnin ya daukaka a bangaren Kasuwanci. Domin anyi ittifakin cewa duk duniya babu wata kasuwa da take ci sama da ta birnin TEHRAN. Bisa wannan dalili ne attajirai suka yawaita a cikin birnin. Amma yawansu babu Wanda ya kama kafar Koda farcen Sarki LU'UMANU a yawan dukiya. Kai saboda tsabar yawan dukiyarsa sai da aka rasa inda za'a ajiyeta, kawai sai dai kaga ana ajiye Zinari da lu'u-lu'u a ko'ina cikin gidan sarautar. Amma ko kuda be Isa ya sauka a kansu ba, saboda Karfin sihirin Sarki LU'UMANU.
Lokacin da aljani DURFAS yaga sun iso birnin TEHRAN sai yace to koya ya Shirya mun kusa gamuwa da gamonmu. Kowannenmu ya tanadi dukkannin sihirin da yake takama da shi, domin munzo gidan uban masu sihiri. Kowa ta tattaro iyakar karfin damtsensa domin munzo gidan SADAUKIN Sadaukan duniya. Yau ne ranar da karfi tsafi wayau da hikima ba zata kwaci daya daga cikinmu ba. Lallai ku sani cewa mun siyar da rayuwakanmu Kuma munyi kasada domin abin dogaron namu ba lallai bane ya iya tseratar damu. Koda Jin wannan batu sai kowa ya fara lalubar guraye da layunsa na tsafi Amma Banda HUBAIRU. Domin shi zuba masu idanu kawai yayi kamar me kallon tuburarrun mahaukata. Kawai sai kallonsu yake yana murmushi. Cikin alamun damuwa Gimbiya sima ta dubi HUBAIRU ta ce, ya Kai wannan kyakkyawa shin baka ganin yadda muke shiri don tunkarar wannan hadari? Muna ta gyara makamanmu meyasa kaima ba zakayi naka Shirin ba? Sa'adda HUBAIRU yaji wannan tambaya sai yayi murmushi me taushi a gareta, sannan ya ce ai ni tuni na gama nawa Shirin. Domin na sanar da Ubangijina bani da wani makami Wanda yafi addu'a. Ubangijina me Amsa addu'a ne a kowane hali Kuma a ko'ina.
HUBAIRU na gama rufe bakinsa kenan sukaga wasu gabza-gabzan Aljanu kimanin dubu Dari sunyi masu inuwa. Aljanun masu siffar jemagu ne amma suna da kawuna irin na shanu. Hannayensu kuwa irinna bil'adama ne suna da cako-cakon farata masu tsawo da tsini fadi da kauri, tamkar faskararren icce. Kafin su ankara tuni wadannan Aljanu sunyi masu rubdugu. Suna Kai masu sara da suka. Cikin zafin nama kowannensu ya zare makaminsa yana kokarin kare Kansa. Idan takobi ta hadu da hannun Aljani sai kaga ta karye gida biyu. Wannan dalili ne yasa hankalinsu JAFARU yayi mummunan tashi, cikin dakiku kadan aljanun nan suka galabaitar da kowa. A wannan lokacin Sarki LU'UMANU na kishingide bisa karagarsa acan