Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
4 / 11
ya wuce ace na mushe ne ko ragowar ciki, ma'ana Wanda akaci akayi aman sa. Haka dai ZARAZU ta ci gaba da tunani har rana ta kwalle, iyayenta suka Farka daga barcin. MASHAMU ta dubi ZARAZU ta ce, au ke har yanxu kina Nan Baki tafi farautar ba? To me kike Jira? ZARAZU tayi murmushi ta ce, ai zakunan nan da kuka kawo min ba karamin koshi nayi ba, Ina ganin bazan nemi abinci ba daga Nan har zuwa gobe sai dai nayi ta Shan ruwa. Wannan Batu ba karamin mamaki ya baiwa dodo KIRYANU ba da MASHAMU. Domin fiye da shekaru Ashirin baya, ba a taba Jin ranar da ZARAZU tace ta koshi ba sai yau. To ai shikenan ki huta. Bari mun cinye ragowar Naman nan, inyaso da yamma sai mu sake fita Neman wani. Haka kuwa akayi, suka cinye ragowar zakunan da yamma kuwa suka sake fita farauta. A sannan ne ZARAZU ta Bude tsohuwar rijiyar nan ya fiddo MARKAHUSSABUS, yaji kamar an tsamo shi ne daga karkashin teku an Dora shi bisa tsibiri saboda tsananin zurfin rijiyar. ZARAZU ta dube shi tana Mai yin hamma ta ce, kaga yanda nake azabtuwa da yunwa a dalilinka ko? Tabbas idan na fita na barka a cikin Kogon nan sai sun fito da Kai sun cinye. Domin kamshinka ya dame su. Idan ko Ina nan, zasuji kunyar su Bude rijiyar don cin kumallo na. MARKAHUSSABUS yayi ajiyar zuciya ya ce, ai babu abinda zan ce da ke face nayi godiya a dalilin kin ceci rayuwata daga halaka. ZARAZU ta bushe da dariya sannan ta ce, ba nj zaka gode mawa ba, sai dai ka godewa hikimarka ta ambaton samo min bil'adama dari. Na rantse da girman ubana ba don kayi min wannan Albishir ba da tuni ka Dade da narkewa a cikin cikina. Yanzu na San kaima kana Jin yunwa, me kake da bukatar ci na samo maka? MARKAHUSSABUS yayi murmushi ya ce, ai ni Nan da kike gani zan iya rayuwa tsawon kwanaki arba'in batare da ci komai ba. Ban damu da kaina ba, ke kawai nakeji. Tafdi jam lallai ku Aljanu cikinku ba ya walahar da ku. Ai ni bazan iya kwana biyu ba batare da na ci komai ba. Yanzu dai zan San dabarar da zan 6ullo da ita, tsawon kwanakin nan bakwai don Kar na azabtu da yunwa. Haka dai MARKAHUSSABUS yaci gaba da zama a cikin rijiya har tsawon kwana bakwai kullum idan su KIRYANU sun tafi farauta sai ZARAZU ta fito da shi su Sha firar su. Ranar da taji ba zata iya jure yunwa ba, sai ta roki KIRYANU akan a rufe Kogon a tafi farautar tare da ita. Haka Ala'marin ya kasance a Rana ta bakwai ranar da dodo KIRYANU zai hada sabon tsumi a kaskonsa ne gardama ta turnuke tsakaninsa da ZARAZU. Inda yake cewa shi fa kamshin da k e cikin rijiyar nan ya isheshi haka. Ya kamata a Bude rijiyar a kwashe abinda ZARAZU ta amayar a fitar da shi waje. Ita ko ZARAZU sai ta dage akan cewa ba za a Bude ba. Babu komai a cikin rijiyar sai doyin Kasusuwan da ke ciki. Sai da aka shafe sa'a guda ana yin wannan muhawara, a karshe dai MASHAMU ce ta taba gardama akan cewa, idan suka tafi farauta suka dawo suka sake Jin kamshin wannan Aljani ba makawa sai an Bude wannan rijiya an fito da duk abinda ke cikinta. ZARAZU ta ce ya amince. Sannan ne DODO KIRYANU da MASHAMU suka dauki kayan farautarsu suka fice daga Kogon ZUHURUM..... Mu hadu a KUNDIN TSATSUBA 1 part F don Jin cigaban wannan Kasaitacce Kuma Kayataccen labari ✍️♥️🥰🥰 Najibullah Muhammad ✍️✍️🙏**KUNDIN TSATSUBA** LITTAFI NA DAYA 1 ♥️ PART F ✍️✍️ MARUBUCI:- ABDUL'AZIZ SANI MADAKIN GINI 👮👮 Typing & Posting:- NAJIBULLAH MUHAMMAD ✍️🥷🥷 CIGABAN LABARIN..... Sai da ZARAZU ta tabbatar da cewa sunyi Nisa da tafiya, sannan Bude wannan rijiya ta fito da ALJANI MARKAHUSSABUS. Ta dube shi ta ce to yau ne ranar cika alkawarinmu. Yanzu zamu tafi izuwa inda zaka bani bil'adama Dari. Nan take ta sa Koko ta kamfato tsumin mahaifinta, ta zuba a cikin wata battar fata ta cika fal. Sannan ta daure bakinta tamau. MARKAHUSSABUS ya Miko hannunsa da nufin ya karbi battar, sai ta janye ta ce haba samari, ya za'ayi na baka wannan tsumin batare da ka bani bil'adama dari ba? Shin baka taba Jin an ce Dinyar makaho ta nuna a hannunsa ba? Idan kaga na baka wannan battar to ka tabbatar ka bani bil'adama dari. MARKAHUSSABUS yayi murmushin yake ya ce, to shikenan na amince sai mu tafi. Naji zamu tafi Amma inaso nasan Nisan tafiyar da zamuyi kafin mu Isa wurin da zaka bani bil'adaman. Kuma Ina so naje na dawo kafin cikar sa'a uku, ka sani cewa Nan da sa'a uku cif iyayena zasu dawo daga farautarsu. Kar ki samu damuwa tafiyar sa'a guda kacal zamuyi mu Isa wurin. Ni da kaina na 6oye bil'adaman a cikin wani kogo, Kuma na ajiye wani hadimina domin yayi min gadinsu. Lallai zamu je mu riskesu a wannan wuri. Koda Jin haka sai murna ta kama ZARAZU. Nan take suka fita daga cikin Kogon ZUHURUM. Suka nausa wani 6angare daban a cikin jejin, ma'ana ba bangaren da su KIRYANU suka bi ba. ZARAZU tana tafiya da kafafunta a bisa doron Kasa, hannunta guda na rike da battar tsumin. Shi ko Aljani MARKAHUSSABUS na samanta cikin iska Yana Yi Mata inuwa saboda Rana. Tunda suka fara tafiyar zuciyar MARKAHUSSABUS ta cika da sake-sake. Yayi ta tunanin hanyar da zai bi ya Rana ZARAZU da wannan battar fata. Tabbas yasan cewa wannan battar, ba zata kar6u ba da karfin tsiya. Gashi Kuma ya San cewa karya yayi Mata akan cewa Yana da bil'adama guda dari da zai bata. Shin yanzu tayaya zai raba ta da battar tsumin? Sannan ya kwaci Kansa daga sharrinsa. Tabbas yasan cewa idan ta fahimci yaudararta yayi, take zatayi Loma daya da shi. Haka dai aka cigaba da wannan tafiya batare da MARKAHUSSABUS ya samu mafita ba a cikin tunaninsa. Har suka shafe rabin sa'a. Kwatsam sai suka hango wani Katon tsauni a gabansu. Akan tsaunin Kuma akwai wani babban Kogon Dutse. Tsakanin Kasan tsaunin da hawa Kansa za'a iya yin tafiyar kimanin rabin sa'a. Koda MARKAHUSSABUS ya hango wannan tsaunin, sai zuciyarsa tayi fari ya dubi ZARAZU ya ce, Ina fata kina iya hango wancan tsaunin ko? ZARAZU ta ce kwaraima kuwa, ince Kodai ba a Kai kace ka ajiye bil'adaman ba? Ko shakka babu a cikin Kogon Dutsen da ke Kansa na ajiye su. Sai mu karasa don muje na sallameki. ZARAZU tayi duba izuwa Saman tsaunin har izuwa kasansa, tayi ajiyar zuciya ta ce, tabdijammmm tayaya zan iya Hawa Kan wannan tsaunin? Alhalin bani da fuka-fukai irin naku na Aljanu. Ya Kai wannan Aljani kayi sani cewa a halin yanzu ba karamar gajiya nayi ba, sakamakon wannan doguwar tafiyar da muka Sha. Lallai sai dai ka hau Dani Kan wannan tsaunin, ko Kuma na tsaya a Kasa ka kwaso min bil'adaman ka bani, ni ko na baka battar tsumin. MARKAHUSSABUS ya ce yanzu dai mu bar tunanin Komai sai mun Isa wajen tukunna. ZARAZU Bata Kara fadin komai ba har suka Isa gaban wannan tsaunin. Da zuwa suka tsaya cirko-cirko suna kallon tsayinsa. MARKAHUSSABUS ya dubi ZARAZU ya ce yake 'yar lele kiyi sani cewa bani da karfin da zan iya daukarki na hau dake bisa wannan tsauni, domin nauyinki ya ninka nawa sau arba'in. Kuma bani da karfin da zan iya kwaso bil'adama dari a lokaci guda na sauko da su nan wurinki. Idan kin amince zan hau sama yanzu, na rinka saukowa da bil'adama daya bayan daya har su cika Dari. Sannan ki bani battar tsumin kowa ya kama gabansa. Yanzu zan fara hawa Saman don na duba lafiyar bil'adaman da Kuma Mai tsaronsu. Inyaso sannan na sauko na sanar da ke halin da ake ciki. ZARAZU tayi murmushi ta ce na amince da haka. MARKAHUSSABUS ya Bude fuka-fukansa yayi sama har ya Isa kan tsaunin. Da zuwa ya shige cikin wannan Kogon Dutse yayi shawagi a ciki batare da ya ga komai ba, dama bayyi tsammanin zai ga komai din ba, domin karya ya shirgawa ZARAZU. Kawai sai fita daga cikin Kogon ya sauko Kasa inda ya bar ZARAZU ya ce mata na same su lafiya, to amma Abokan tafiya ta sun ce ki nuna masu battar tsumin don su hangota su tabbatar da akwai ta, sannan su sauko maki da bil'adama guda dari. Da jin haka ZARAZU ta dubi MARKAHUSSABUS cikin mamaki ta ce, au dama ba Kai kadai ka shigo jejin Nan ba? Meyasa tun farko baka sanar min ba? MARKAHUSSABUS ya ce ai Kinsan ba zanyi saurin sanar da ke sirrina ba, tunda bansan yadda zata kaya ba. Ke dai kawai kiyi abinda na fada. Yanzun Nan zakiga Abokan tafiyar tawa su leko. Batare da wata fargaba ba, ZARAZU ta fito da battar tsumin daga cikin aljihun rigarta ta daga ta sama ta ce," Ina Abokan tafiyar Aljanin Nan? Ku leko Kasa ku ga abun muradinku. Cikin abinda bai wuce rabin dakika ba, MARKAHUSSABUS ya yunkura cikin tsananin zafin nama da shammace ya fizge battar tsumin daga hannun ZARAZU yayi sama. Bai dira a ko'ina ba sai akan tsaunin. Kawai sai ya leko Kasa ya dubi ZARAZU ya kyalkyale da dariyar mugunta sannan ya ce," ke yarinya daga yau na koya maki hankali, domin na nuna maki cewa duk Wanda ya Riga ka kwana dole ne ya Riga ka tashi. Tabbas na Riga ki zuwa duniya, dole ne na fiki wayau. Yanzu zan tafi da tsumin mahaifinki domin shi ne abinda ya kawo ni jejin Nan. Batun bil'adama dari kuwa, karya na Shirya maki bani da su. Kafin ZARAZU ta Bude Baki ta ce wani abu, tuni MARKAHUSSABUS ya Bude fuka-fukansa ya tashi sama... Nan da nan ya luluka a cikin gajimare ya 6ace. Ala'marin da yasa ZARAZU mugun bakin ciki a zuci kenan, kawai sai ta daga hannuwanta biyu masu zako-zakon farata ta luma a cikinta, sai gashi farken cikin tumbinta ya fado Kasa. Take ta fadi Kasa matacciya ko shurawa ba tayi ba. Ala'marin ALJANI MARKAHUSSABUS kuwa, Koda yaga ya samu nasarar karbar battar tsumi daga hannun ZARAZU sai ya cika farin ciki ya Kara kaimi a wajen tafiyarsa. Yayi ta keta hazo cikin tsananin gudu da kwanciyar hankali. Koda ya tuna cewa alkawarin SA da Sarki LU'UMANU na kwana dari da goma Sha biyu ne. Gashi ya 6ata kwana bakwai a kokarin samo tsumin DODO KIRYANU. Sai hankalinsa ya tashi, domin baya son yaga ya gota wadannan kwanaki, batare da ya Isa fadar Sarki LU'UMANU ba. Nan fa ya shiga tunanin hanyar da zai bi ya Kara karfin gudunsa. Yana cikin tunanin ne davara ta fado Masa. A Ka'ida bayan kowane mako guda yake sauka ya huta Kuma ya ci abinci. Amma yanzu sai ya Yanke shawarar ba zai rinka saukowa Kasa ba, sai bayan mako biyu. Kuma Yana tafiya zai rinka kada fuka-fukansa da saurin gaske don ya Sha gaban lokaci. Haka dai Ala'marin ya kasance. ALJANI MARKAHUSSABUS ya Kara kaimi iyakar karfinsa wajen wannan tafiya. A ranar da kwanaki suka cika dari da goma Sha biyu cif-cif ne. SARKI LU'UMANU na zaune a fadarsa tare da 'yan majalisar sa. Da Kuma Bokayen Kasar sa da sauran jama'ar gari. Sai kawai akaga garin ya gauraye da hadari. Nan da nan Kasa ta kama girgiza, ba zato ba tsammani sai ga Aljani MARKAHUSSABUS ya ratso ya karkashin Kasa ya bayyana a tsakiyar fadar. Hannunsa na hagu na rike battar tsumin DODO KIRYANU. Koda ganinsa sai fadar ta rude da tafi da shewa... 08112778656 ( Whatsapp) Murna ta kama Sarki LU'UMANU ya Mike tsaye daga Kan karagarsa ya taho ga MARKAHUSSABUS Yana Mai cewa lale marhabun farin bako. Lallai ka cika alkawari akan lokaci, bani abun muradina. SARKI LU'UMANU ya Mika hannu da nufin kar6ar battar tsumin. Sai Aljani MARKAHUSSABUS ya janye ya ce," Haba ranka ya dade, Ashe ka manta da sharadin alkawarinmu? Ai ba zan baka tsumin DODO KIRYANU ba sai na fadi tawa bukatar ka biya min. Koda Jin haka sai Sarki LU'UMANU yayi murmushin sannan ya ce, fadi bukatar ka Muji indai bata sa6a sharadin da na gindaya ba kafin ka tafi, yanzu take zan biya ta. MARKAHUSSABUS ya numfasa ya ce," ya Kai wannan Sarki kayi sani cewa bani bukatar komai daga gareka, face ka mallaka min wannan mata taka wato FATISA. Koda Jin haka sai Sarki LU'UMANU ya murtuke Fuska, ya koma kan karagarsa ya zauna hankalinsa ya dugunzuma ya rasa abinda ke Masa dadi. Daga can sai ya dago Kai a fusace ya ce," Ashe baka da hankali? Ya za'ayi ka bukaci abinda na tura ka tafiya dominsa? Ina umartarka da ka fadi wata bukatar Amma ba wannan ba. Banda raina da mulkina ko menene zan mallaka maka shi. MARKAHUSSABUS ya yi ajiyar zuciya ya ce," ni Kam indai ba FATISA zaka bani ba, bana bukatar komai. Lallai zanyi tafiya da tsumin DODO KIRYANU, inyaso kowa yayi asarar bukatarsa. Cikin harzuka Sarki LU'UMANU yace," 6ace mana da gani ya Kai wannan Aljani. Daga yau na haramta maka shigowa Kasa ta, idan ko ka kuskura ka Kara zuwa, zan tabbatar da wancan hukuncin da nayi alkawari a kanka. Batare da mayar da wani martani ba, Aljani MARKAHUSSABUS ya 6ace, 6acewarsa keda wuya sai Sarki LU'UMANU ya shiga gida cikin tsananin fushi da bakin ciki. Nan dai fada ta watse kowa ya kama gabansa. A wannan Rana babu Wanda ya kusanci Sarki LU'UMANU saboda ganin irin tsananin fushin da yayi. Tabbas zai iya hargitsa garin gaba Daya idan aka fusata shi. Hatta iyalansa baya-baya suka rinka yi da shi a ranar, babu Wanda ya shiga turakarsa, sai masu yi Masa hidima. Su ma din a cikin dari-dari suka rinka aikinsu. Shi ko Aljani MARKAHUSSABUS bayan ya Isa karshen gari, sai ya zauna Yana ta tunani da bakin cikin wannan Abu da Sarki LU'UMANU yayi Masa. Ya tuno da alkawarin da ya daukarwa mahaifiyarsa cewa ba zai komo gida ba sai tare da FATISA. Nan take yaji zuciyarsa ta kekashe tsoro ya kau daga cikinta, kawai sai ya Yanke shawarar ya koma gidan sarautar Sarki LU'UMANU, ya sato Gimbiya FATISA batare da wani ya ganshi ba. Nan take MARKAHUSSABUS ya Bude fuka-fukansa yayi sama, ya nufi gidan Sarki LU'UMANU cikin tsananin gudun da bai ta6a yin irinsa ba. Kamar kiftawar Ido, sai gashi ya dira a tsakiyar gidan sarautar. Nan fa ya fara Neman inda Gimbiya FATISA ta ke. Duk ta inda ya bi, Koda bango ne, sai dai kaga ya ratsa ta cikinsa ta wuce, kamar yadda danshin ruwa ke tsattsafowa daga karkashin Kasa. MARKAHUSSABUS yayi ta shiga sako-sako daki- daki har ya iso bangaren da Gimbiya FATISA ta ke. A wannan lokacin dare ya raba, ga Dakaru Nan birjik suna gadi, Amma babu Wanda ya iya ganin MARKAHUSSABUS duk da cewa gaba dayan gidan sarautar a haskake yake da hasken fitilu manya-manya irin na sarauta. Sa'adda MARKAHUSSABUS ya shigo cikin turakar gimbiya FATISA, sai ya iske kuyanginta a kwakkwance suna ta sharar barci, kamar Basu da Rai. Nan ya tsattsallake su, ya wuce izuwa cikin kuryar dakinta. Daki ne Mai girman gaske Wanda aka kawata da kayan alatu iri-iri. Ko'ina ka duba shudin kilishi ne a shimfide mai tsananin laushi idan ka taka. A tsakiyar dakin aka girke wani Katon gado na Zinari Mai Tudun taushi, da labulen alharini da dajiyar Baki da zubardaji sai sheki da walwali yake yi. Gaba dayan dakin ya dume da kamshin turaren miski. Akan tsakiyar gadon gimbiya FATISA ce kwance cikin wata doguwar Riga Mai shara-shara. Yayinda MARKAHUSSABUS ya ganta a cikin wannan Hali sai ya gigice Kuma ya dimauce, Nan take ya Isa kan gadon ya zauna daf da ita. Zamansa ke da wuya, ta bude idanunta sukayi arba da juna. Maimakon ta rafka ihu, ko ta razana sai yaga tayi murmushi. Ala'marin da yayi matukar bashi mamaki kenan. Har ya bude Baki zai ce wani abu, sai ta tsohe bakinsa da tafin hannunta ta ce," Kar ka ce komai ya masoyina, nasan cewa zaka dawo gareni. Kayi sani cewa tun ranar da muka ga juna ka tafi ka barni cikin mayen begenka. Dare da Rana bana iya barci saboda tunaninka. Hakika mijina yaci amanarka bisa alkawarin da ku ka yi. Ina umartarka da ka hanzarta Tarawa Dani kafin ya San da zuwanka. Domin burinka da nawa ya cika. A dai-dai wannan lokaci kwatsam sai suka ji kofofin dakin guda takwas sun bubbude da karfi, Dakaru sukayi ta tuttudowa cikin dakin dauke da muggan makaman yaki. Cikin dakiku kadan suka yiwa dakin Kawanya. A wannan lokaci MARKAHUSSABUS da FATISA na rungume da juna suna tsaye akan gadon cikin firgici. Gaba dayan Dakarun suka tsaya kyam suna kallonsu FATISA kawai. Ba zato ba tsammani sai ga Sarki LU'UMANU ya bayyana Tsulum sanye da mummunar shigar yaki, fuskarsa a murkute babu annuri ko kadan, idanunsa sun kada sunyi jawur..... A dai-dai wannan wuri ne na gaji ainun, nake cewa sai wani karon idan ya Allah ya kaimu.. Mu hadu a part G don Jin cigaban wannan Kasaitacce Kuma Kayataccen labari ✍️♥️🥰🥰**KUNDIN TSATSUBA** LITTAFI NA DAYA ✍️ ♥️ PART G ❤️❤️ Na:- ABDUL'AZIZ SANI MADAKIN GINI 👮👮 Typing & posting:- Najibullah Muhammad ✍️🥷🥷 08112778656 ( Whatsapp) Comments da likes da share, na da matukar muhimmanci wajen saurin kawo maku cigaban littafin.... Marubucin ya ci gaba da cewa... Ana cikin haka ne sai kwatsam suka ga kofofin dakin guda takwas sun bubbude da karfi dakaru na ta tuttudowa cikin dakin dauke da muggan makaman yaki. Cikin dakiku kadan suka yiwa dakin Kawanya. A wannan lokaci FATISA da MARKAHUSSABUS suna rungume da juna suna tsaye akan gadon cikin firgici. Gaba daya Dakarun suka tsaya kyam suna kallonsu FATISA kawai. Ba zato Kuma sai ga Sarki LU'UMANU ya bayyana cikin shigar yaki. Fuskarsa a murkute idanunsa sun kada sunyi jawur. Cikin fushi ya dubi FATISA ya ce," kaiconki matata, hakika kin bani kunya. Kuma kin zubar da kimarki, ki sani kinyi babban lahani ga darajar sarauta ta, lallai yau dayanku bazai tsira ga azaba ta ba. Ina nufin ke da wannan la'anannen Aljanin. Na rantse da girman tsafi sai na kulle ku a cikin akwatunan tsafi Sannan a Kai ku kurkukun karkashin Kasa. Anan zakuyi ta zama har izuwa karshen rayuwarku. Koda Jin haka sai MARKAHUSSABUS ya bushe da dariya ya ce," karya kake, baka Isa kayi mana wannan wulakancin ba muddin Ina numfashi a doron Kasa. Koda Jin haka sai Sarki LU'UMANU ya dubi dakarunsa ya ce ku kama su, naga iyakar kokarinsu, sannan ku aiwatar da hukuncin da na yanke a kansu. Take Dakarun suka afkawa su MARKAHUSSABUS, Nan fa wuri ya yamutse aka fara dauki ba dadi. Bisa mamaki sai MARKAHUSSABUS yaga cewa wadannan Dakaru sun addabe shi, duk da cewa shi Aljani ne, su ko mutane ne. Abinda Bai sani ba shi ne, ba mutane bane, Aljanu ne 'yan uwansa. Kuma suna daga cikin jinsin bakaken Aljanu wadanda babu marasa Imani kamarsu a doron Kasa. Koda yaga Ala'marin yafi karfin saninsa sai ya fara jaraba karfin tsafi. Nan take Dakarun suka juye kamanninsu izuwa ainihin siffofinsu na bakaken Aljanu. Kawai sai suka rufe shi da duka. Cikin abinda Bai wuce dakiku kadan ba, sukayi Masa luguden wahala ya fadi Kasa sumamme. Ita ko FATISA suka kama ta da karfin tsiya suka tafi da ita izuwa kurkuku na karkashin Kasa inda aka Gina wani karamin daki na musamman. Anan ne aka Sanya MARKAHUSSABUS a cikin wata battar karfe ita Kuma battar aka jefa ta cikin wata akwatu aka kulle, sannan aka sa Katon kwado aka kulle. Kamar yadda aka yiwa MARKAHUSSABUS haka aka yiwa FATISA. Da yake ita bil'adama ce kwanan ta uku a cikin akwatun karfen ta mutu. Shi ko MARKAHUSSABUS har yau har kwanan gobe Yana Nan a kwance cikin koshin lafiya. Kullum bashi da aikin yi sai kuka da rera wakokin bege ga masoyiyarsa FATISA. Inda mutum zai shiga wannan wuri, ya je kusa da akwatun zai ji sautin kuka Kuma zai ga hawayen MARKAHUSSABUS na kwaranya daga cikin murfin akwatun Nan. Wannan shi ne dalilin dayasa aka kulle MARKAHUSSABUS a cikin akwatun karfe. Sa'adda Aljani LUHUMAS yazo Nan a labarinsa. Sai JAFARU da YALISA sukayi ajiyar zuciya. Sannan suka dubi juna aka rasa Wanda zai ce kala. Daga can sai JAFARU ya ce," yanzu kenan dole sai mun je jejin KALKIM mun dauko takobin SARJUS mallakar MUGULUS sannan zamu iya zuwa birnin TEHRAN mu yaki Sarki LU'UMANU mu kubutar da Aljani MARKAHUSSABUS, ko ba haka ba? LUHUMAS ya ce haka wannan zance yake. Dole sai Kun tuntubi Boka JISHEN mahaifin YALISA sannan zaku iya keta jejin KALKIM ku fita lafiya. Wannan batu yasa hankalin JAFARU da na YALISA ya tashi, wannan yasa suka natsu a cikin tunani. Daga karshe sai suka Yanke shawarar kawai suje su tuntubi mahaifin nata. Nan take YALISA ta dauki KUNDIN TSATSUBA tayi waje, JAFARU da Aljanu GULZUM suka bita a baya. Koda suka zo bakin kofar Kogon sai yanar nan ta nannade kanta kamar labule suka wuce. Sannan ta dawo ta rufe. Batare da Bata lokaci ba YALISA da JAFARU suka haye bayan GULZUM ya tashi da su sama suka nufi gidan Boka JISHEN. A can birnin LAHARIM kuwa magriba nayi waziri Qaddaru ya koma wajen Gimbiya sima, ya sanar da ita cewa shi Kam ya gama shiri Kuma yayi sallama da iyalansa don haka a shirye yake su tafi izuwa jejin FALWAS don su sadu da Boka SULBAINI. Dama tuni Gimbiya sima ta sa an Shirya masu guzuri. Da 'yan rakiya wasu dakaru guda dari hudu da sittin. Daga cikin wadannan 'yan rakiya harda galadima wani dattijon mutum da ake kira ABULAJIS. Ba don komai Gimbiya sima ta Shirya wannan tafiya tare da ABULAJIS ba, sai don ya zama wakilin jama'ar gari, Kuma idan ta kama ta bar masa rikon garin ta bashi. Batare da Bata lokaci ba Gimbiya sima, Qaddaru, ABULAJIS da sauran 'yan rakiya sukayi hawa suka fice daga cikin gari suka dau hanya suka nufi hanyar jejin FALWAS. Kwanci tashi su Gimbiya sima suka Isa jejin FALWAS. Basu tsaya ko'ina ba sai a bakin Kogon RUHIM. Da yake Qaddaru ne akan gaba, da zuwansa sai yaja linzamin dokinsa ya tsaya cak a bakin wannan kogo. Sannan ya sauko daga Kan dokinsa. Su kuwa su Gimbiya sima Basu sauko daga kan dawakansu ba, sai suka tsaya suna kallon abinda Qaddaru zayyi. Yayinda Qaddaru yazo daf da kofar shiga Kogon RUHIM, sai ya tsaya ya ce ya Sarkin Bokayen duniya, ya Kai fitila Mai haskaka duhun dare, ya magani Mai warkar da kowace Cuta, kayi sani cewa yau ga sarauniyarka Gimbiya sima ta tako da kafarta tazo gareka da wata babbar bukata. Kayi hakuri ya shugaban Bokayen duniya mun katse maka aiki ba don son zuciya ba, sai don bin umarnin sarauniya. Ga ta nan a tsaye tana sauraronka. 08112778656 ( Whatsapp) Najibullah Muhammad ✍️ Qaddaru na gama fadin hakan sai suka ji wata murya ta ce, lale marhabun da sarauniya. Lallai mu masu Bauta ne da Ahalin gidanku tun fil-azal. Bukatarku tamu ce, gamu Nan zuwa gareku don mu share maku hawaye. Koda muryar tazo Nan a zancenta sai gaba dayan Kogon na RUHIM ya tsage daga Kasa kamar an Bude tsakiyar littafi. Take wani dogon mutum ya bayyana Yana sanye da warkin fata, a hannunsa na hagu akwai wata siririyar sandar tsafi. A hannunsa na dama kuwa hisga ce. Babu takalmi a kafarsa. Damatsansa kuwa a cike suke da gurayen tsafi. Kansa fari fat ne, ko'ina furfurace ta lullube, babu silin bakin gashi ko guda. A Kalla shekarunsa sun haura casa'in. Jikinsa a murde yake, wato Yana da kirar karfi. Kai da ganinsa Kasan cewa daa can anyi jarumta. Mutumin ya tako a hankali har ya iso gaban Gimbiya sima, sannan yayi sujjada a gareta ya ce, gaisheki sarauniyar duniya. Kece tauraruwar taurari, ni ne bawanki Boka SULBAINI. Muna sane da bukatarki sauko ki biyomu cikin Kogo. Lallai akwai bayani Mai tsauri dake bukatar sauraro cikin natsuwa. Batare da wata fargaba ba Gimbiya sima ta sauko daga kan dokinta ta biyo Boka SULBAINI

Chapter 4 of 11