Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
7 / 11
ni zan bayar da Umarni ba dai ni a bani ba, Amma na Kasa samun nasara. Koda Jin wannan batu sai Aljani NARGAS ya kyalkyale da dariya ya ce amma fa ka bani mamaki. To yaushe aka haifeka ma har da zakayi kukan gajiyawa da Bautawa bil'adama? Dudu-du shekarunka ba zasu wuce dubu daya da Dari hudu ba. Nifa yau shekarata dubu Ashirin da uku a doron Kasa. Tun Ina shekara Tara nake Bauta ga bil'adama sai musayata ake yi kamar yadda ake musayar rigar sawa. Idan aka auna ni waccan nahiyar sai a auna ni wata nahiyar. Kaf kasashen duniya babu Kasar da banje ba nayi Bauta. Na zauna da bokaye a Kalla guda dubu Dari shida da saba'in da bakwai. Akwai wani gidan sarauta da na zauna sai da nayi shekaru dubu biyu inayi masu Bauta, tun iyaye da kakanninsu har sai da tattaba kunnensu suka gajeni. A karshe dai Zamani ne yasa dole na guje su. Domin wadansu kangararrun mutane ne sukaci Kasar da yaki, wadanda da na doshe su sai naji kamar zan Kone. Da Jin wannan batu sai Aljani GULZUM ya dubu NARGAS ya ce, su kuwa wadannan mutane wadanne iri ne Kuma meye abun takamarsu harda suka gagareka? Tom Alhmdllh mu hadu a part J don Jin cigaban wannan Kasaitacce Kuma Kayataccen labari Mai dadi da debe kewa.... Wanda ni Najibullah Muhammad nake kawo maku shi. Anan nake cewa mu huta lafiya sai wani karon idan da rayuwa mun sake saduwa ✍️♥️**KUNDIN TSATSUBA** LITTAFI NA DAYA 1 ♥️🥰 PART J ✍️✍️ MARUBUCI:- ABDUL'AZIZ SANI MADAKIN GINI 🪖🪖 TYPING:- NAJIBULLAH MUHAMMAD ✍️✍️ POSTING:- Najibullah Muhammad 🥷🥷 08112778656 ( Whatsapp) Note:- Kar a manta comments da likes da share na da matukar muhimmanci wajen saurin kawo maku cigaban littafin ✍️✍️👆👆 Bayan haka kafin muci gaba. Zanyi Amfani da wannan damar wajen Mika sakon ta'aziyya ta zuwa ga iyalai da dalibai da sauran musulman duniya bisa ga rasuwar babban malami Kuma jagora wato SHEIKH DAHIRU USMAN BAUCHI. Muna fatan Allah ya jikansa da rahma yasa Aljannah ce makoma 🙏 Kuma Allah ya Amfani abinda ya bari. Allah yasa lahira ta fi Masa duniya. Allah yasa yana daga cikin makusantan manzon Allah Sallalahu alaihi wasallam a ranar lahira ❤️ daga karshe Ina fatan mu ma Allah yasa muyi kyakkyawan karshe, Kuma Allah yasa Muna daga cikin 'yan Aljannah amintattu🙏🙏🙏 CIGABAN LABARIN... Akwai wani gidan sarauta da na zauna da su Ina yi masu Bauta. Tun iyaye da kakanninsu har sai da tatta6a kunnensu suka gajeni. A karshe dai Zamani ne yasa dole na guje su. Domin wadansu kangararrun mutane ne sukaci Kasar da yaki wadanda da na doshe su sai naji kamar zan Kone. Da Jin wannan batu sai Aljani GULZUM ya dubi NARGAS ya ce," su ko wadannan mutane wadanne iri ne Kuma meye abun dogaronsu har da suka gagareka? NARGAS ya ce," wadannan mutane ma'abota wani Addini ne da naji ana yi Masa lakabi da musulunci. Ya Kai GULZUM kayi sani cewa a halin yanzu duk duniya babu wani gari da zaka samu wadannan mutane sai birnin BAHAZIR wato wannan Kasa kenan da nayi Bautar shekara dubu biyu. Birnin BAHAZIR na can tsakiyar duniya. Ka sani cewa daga birnin Sin zuwa can tafiya ce ta shekara dari uku da arba'in da uku bisa sadaukan Aljanu kama ta. GULZUM yace Kash! Ai ba don nisan tafiyar ba, da sai naje naga wadannan hatsabiban mutane wadanda suka iya fatattakar ma'abota tsafi da karfin sihiri. NARGAS ya ce," uhm ai indai kana tare da wadannan hatsabiban mutanen biyu wato JAFARU da YALISA watarana sai sun Kai ka birnin BAHAZIR. Daga wannan batu NARGAS yayi shiru Bai Kara cewa komai ba, suka bar firar haka. Ala'marin Gimbiya sima da waziri Qaddaru kuwa duk firar da ta wakana dazu tsakanin JAFARU da YALISA sunji. Lokacin da ya ce," sai yayi Mata rakiyar Mike Kafa duk suna ji. Lokacin da JAFARU da YALISA suka nausa cikin jejin sai suma suka bi bayansu. Da yake su sima na tare da sihirin hijabin 6ata, su JAFARU Basu San ana biye da su ba. JAFARU da YALISA na tafe suna fira, inda ya bata labarin abinda ya faru a gidan nan na dodanni. Da Kuma Batun Gimbiya sima da waziri Qaddaru, wadanda suka 6ace Masa da gani ya neme su sama da Kasa ya rasa bayan ya ceci rayuwarsu. Koda Jin wannan Ala'mari sai YALISA ta cika da dimbin mamaki, ta kar6i KUNDIN TSATSUBA daga hannunsa tayi Masa kallon kurilla ta ce," lallai akwai ababen Al'ajabi tattare da wannan littafi. Kuma Ina kyautata zaton ko su kansu Bokayen duniya Basu San iyakar abinda ke cikinsa ba. Yanzu bamu da burin da yafi mu samu nasarar bude littafin nan, don musan iya sirrin dake cikinsa. Koda YALISA tazo nan a zancenta sai sukaga wata Guguwa ta faso daga karkashin Kasa ta kama katantawa da su. Kafin su ankara tuni su biyun sun sume. Da karfin tsiya Guguwar ta janyesu izuwa cikin karkarshin Kasa. Take wajen ya dawo dai-dai kamar yadda yake da, Kai kace babu abinda ya faru. Wannan Ala'mari gaba daya ya faru ne akan idanun Gimbiya sima da Qaddaru. Cikin tsananin tsoro da firgita Qaddaru ya ce," ranki ya dade zo mu bar wurin nan, don kada abinda ya faru garesu mu ma ya faru garemu. Yayinda Gimbiya sima taji haka sai ta dubi Qaddaru cikin fushi da harara ta ce," Amma ban taba sanin cewa Kai butulu bane sai yau. Ashe ka manta da lokacin da JAFARU ya ceci rayuwarmu a cikin gidan dodanni? Taimakon mai taimako wajibi ne, dole ne mu shiga inda suka shiga don mu Kai masu dauki Koda kuwa zamu rasa rayuwakanmu." Kafin Qaddaru yayi wani yunkuri tuni sima ta ja shi izuwa wannan wuri. Ai ko suna sa kafafunsu izuwa wannan wajen, sai Guguwar nan ta bullutso waje ta zuke su izuwa karkashin Kasa. Suna kwance a sume basu Farka ba, sai bayan dakika dari da arba'in. Yayinda suka farfado daga dogon Suman da sukayi sai suka mike da kyar. Kawai sai suka tsinci kansu a gaban wani gabjejen Gunki. Gunki ne Mai siffar mutum a zaune rike da wani abu mai kama da abun Saka littafi, ko dora wa akai don karantawa. Wannan Gunki na ajiye ne jikin wani Katon daki Mai manyan gini masu tsayin gaske da kaurin tsiya. Gaba dayan yanayin ginin irin tsarin mutanen Misra ne, wato irin gininsu na gado tun zamanin Sarki Fir'auna na Misra. Bayan JAFARU da YALISA sun Mike a gaban wannan gunki sai suka ga kwayar idanun gunkin sun kada, Kuma sai bakinsa ya Bude ya ce da su lale marhabun da JAFARU Bin RUZYAL tare YALISA bin JISHEN. Kuyi sani cewa wannan littafi da ke hannunku bai dace da ku ba, da ni ya dace. Saboda haka na umarceku da ku Dora shi bisa mazauninshi da ke hannuna. Inba haka ba kuwa yanzun nan zan dandana maku Azaba daga cikin irin azabobina guda dubu. Yayinda su JAFARU sukaji wannan batu, sai JAFARU ya dubi wannan Gunki a fusace ya ce," Kai Kuma waye har da zaka ce mu baka KUNDIN TSATSUBA? Alhalin munsha wahala a baya kafin mu same shi. Sannan Kuma bamu San iyakar wahalar da zamusha ba nan gaba kafin mu iya bude shi. Lallai karyarka ta sha karya, idan har kaga ka rabamu da wannan littafin to ka tabbatar bama numfashi a doron Kasa." Nan take sukaji Gunkin ya kece da wata mahaukaciyar dariya wadda ta sa har wani farin Hayaki ya rinka fitowa daga bakinsa. Take hayakin ya rikide ya zama igiyar karfe, ita Kuma igiyar ta kanannade JAFARU da YALISA ta matse su da karfi, suka rinka kwallara ihu saboda tsananin zafin da sukaji tamkar Kasusuwan jikinsu zasu ragargaje. Bayan sun galabaita sai igiyar karfen nan ta sake sua lokacin da idanuwansu suka cika da kwallah. Jikinsu yayi laushi kamar Basu da laka. Gunkin ya dube su ya sake kecewa da dariya a karo na biyu ya ce," na umarceku da ku Sanya KUNDIN TSATSUBA bisa wannan mazaunin nasa da ke gabana. Duk wannan Azaba da su JAFARU suka Sha Bata sa su JAFARU sun saki KUNDIN TSATSUBA ba, har yanxu yana maƙale da shi a hammata. Lokacin da Gunkin nan ya bashi Umarni sai ya Mike tsaye dakyar yaje ya aza KUNDIN TSATSUBA akan wannan Abu da ke gaban Gunkin. Yana Dora shi yaga ya zauna daram, kamar dama sai da aka auna abun da girman KUNDIN TSATSUBA. Faruwar hakan keda wuya sai gaba dayan fitilun dakin suka kama wadanda adadinsu yakai dubu. Gaba daya wajen ya haskake da matukar haske yadda Koda allura ce ta fadi sai an ganta. Shi kuwa wannan Gunki sai ya rikide ya zama wani gajeren mutum tsoho tukuf Wanda tsayinsa Bai fi rabin na waziri Qaddaru ba. Wato dukanshi bai wuce kamu guda ba, ko kwando aka aza rufe shi zayyi ruf. Guntun mutumen ya dubi JAFARU yayi murmushi sannan ya ce," naji dazu ka tambaya ko ni waye. Yanzu zan sanar da Kai matsayina da Kuma dalilin zamana a wannan jejin. Da farko dai suna na Boka HAFSUL HABAL. Ni mutum ne kamar ku Amma nafi Aljani shedanci. Na samu shekaru hamsin Ina Bauta a karkashin mulkin Sarki ZURKILU na birnin MASJUR. A duniya kaf babu wani Sarki Mai karfin sihirin tsafi kamar sa. Na fara Bauta karkashin wannan Sarki a lokacin da nake shekara goma da haihuwa. Bisa alkawarin zai yiwa mahaifina sarautar waziri, Kuma zai raba dukiyarsa gida biyu ya bani rabi, bayan na taimaka Masa ya biya wata muhimmiyar bukata. A wannan lokaci mahaifina ya tsufa sosai domin shekarunsa sun haura casa'in. Haka dai na dukufa Kan aikin Sarki ZURKILU dare da rana, don ganin bukatarsa ta biya. Amma ban samu nasara ba sai bayan shekaru arba'in da bakwai sannan wannan bukata ta biya. Na Sha wahala mai tsanani a cikin wasu dazuzzuka guda bakwai kafin bukatar Sarki ta biya. Kai a wannan tafiya ne nayi asarar yatsun kafafuna gaba daya. Koda HAFSUL HABAL yazo nan a zancensa sai ya janye doguwar rigar dake jikinsa, su JAFARU suka ga dungulmin kafafuwa. HAFSUL HABAL yaci gaba da cewa bayan na kawowa Sarki ZURKILU abinda yake so sai ya cika da farin ciki yace na tafi gobe da safe nazo fada don ya cika alkawarin da ya daukar min. Nan take nayi sallama da shi ba tafi gida cikin tsananin farin ciki. Ina ta sauri nazo na sanar da mahaifina yadda mukayi da Sarki. Koda na Isa gida sai na wuce dakin mahaifina Kai tsaye, Ina shiga na tsaya kyam jikina ya hau karkarwa. Idanuna suka ciko da kwallah na kama kuka. Ba komai ne ya jawo hakan ba face ganin mahaifin nawa kwance kan gado anyi Masa yankan rago. Gaba daya gadon ya malale da jini. Mamaki da bakin ciki suka rufe ni. Wanene ya aikata wannan danyen aiki ga mahaifina? Tambayar da bansan amsarta ba kenan. Kawai sai na juya a fusace na ruga izuwa gidana don na shiga dakin tsafina nayi bincike na gano Wanda ya kashe mahaifin nawa. Tun kafin na karasa unguwarmu na hango gidana na ci da wuta. Nan fa na kurma ihu na Kara gudu, Ina zuwa na iske Gawar matata da ta 'yayana biyu HAZARTU da 'yar Uwarsu LUSWAL kwance a Kasa wuta ta kone su kurmus. Jama'a sunyi dandazo an kewaye gidan kowa na fadin albarkacin bakinsa. Nan fa na haukace Ina tambayar jama'a waye ya bankawa gidana wuta? Jama'a ko suka tarwatse aka barni ni kadai Ina ta bambamina. Ina cikin hakane Dakarun Sarki ZURKILU suka zo gareni. Da zuwa suka afka min da duka. Nayi iya kokarina don na hallakasu da karfin tsafi Amma sai tsafina yaki aiki. Saboda duk abubuwan sihirina da nake takama da su sun kone su a cikin gida. Nan da nan Dakarun nan sukayi min lilis har na Suma sannan suka tafi dani kurkuku. Ban farfado ba sai can tsakiyar dare, sa'adda aka kwara min ruwa ba farfado. Ina bude Ido nayi arba da Sarki ZURKILU tare da wadannan Dakarun tsaitsaye a kofar wannan daki da aka kulle ni. Sarki ZURKILU ya dube ni cikin murmushi sannan ya ce,_ ya Kai wannan Boka ka sani cewa ba wani bane ya kashe mahaifinka ba sai ni. Haka Kuma ni ne na sa aka kone gidanka. Ba don komai yasa nayi haka ba, sai don sanin cewa yanzu ka Kai wani babban matsayi a ilimin bokanci. Domin abinda na tura ka ka samo min ya gagari gaba dayan Bokayen duniya shekara da shekaru. Idan na cika alkawarin da na daukar maka, ba shakka watarana sai ka kasheni ka hau karagata. Bisa wannan dalili ne yasa na Yanke wannan hukuncin a kanka. Yanzu zakaci gaba da zama a wannan kurkukun har tsawon lokacin da na yanke shawarar abinda ya kamata nayi da Kai. 08112778656 ( Whatsapp ) Najibullah Muhammad ✍️✍️ Sa'adda Sarki ZURKILU yazo nan a zancensa sai takaici ya turnuke ni. Bansan sa'adda na fashe da kuka ba nace," yakai wannan Sarki Ina sanar maka da cewa ka hanzarta halaka ni, idan ko ka ki na rantse da jinin mahaifina sai nayi maka kisan gilla kuma na Karar da dukkannin ahalinka. Koda Jin haka sai ZURKILU ya bushe da dariya sannan ya daka min tsawa ya ce," Kai tsohon banza, Ashe baka San cewa anyi sake dan Zaki ya girma ba? Wannan Abu da na tura ka ka samo min a cikin daji bakwai shi ne cikar tsafina. Na rantse da girman karagata babu wani matsafi da zai fini karfin sihirin tsafi a yanzu. Babu wani makami da zayyi tasiri a jikina. Haka Kuma babu Kasar da zan durfafa da yaki ban tarwatsata ba nai nasara. Yana gama fadin hakan ya juya ya tafi Yana cigaba da kyalkyala dariyar mugunta, dakarunsa na biye da shi. Sai da na kwana uku a cikin wannan kurkukun ba ci ba Sha, na galabaita iya galabaita. A wannan dare na uku ne Ina kwance magashiyan sai naji wata irin iska mai tsananin karfi ta keto cikin kurkukun sannan ta sureni tayi sama da ni. Take Saman ginin ya dare iskar tayi waje Dani. Nidai ban sake tuna komai ba sai ganina nayi a cikin wannan dakin da muke ciki a yanzu. A sannan ne Kuma hankalina ya dawo. Koda na Mike tsaye sai nayi arba da wata tsohuwar aljana sanye da fararen tufafi tsaye a gabana. A kanta akwai kahonni guda hudu, yatsun hannunta dogaye ne ababen tsoro, faratan ta kuwa masu tsini ne kamar allura. Aljanar ta dube ni ta ce, tashi tsaye yakai HAFSUL HABAL nasan baka Sanni ba. Amma ni na sanka Kuma kayi min abin arzikin da bazan taba mantawa ba. Wannan dalilin yasa na kubutar da Kai daga hannun Sarki ZURKILU. Kuma indai kana Nan wurin ka tsira ba zai iya yi maka komai ba. Zan taimaka maka har ka dauki FANSA bisa zaluncin da yayi maka. Lallai kaima sai ka kashe shi, kisan wulakanci sannan ka kashe duk iyalansa ka haye karagarsa. To Amma ka sani cewa ba zaka samu nasara ba har sai ka mallaki wani littafi da ake kira KUNDIN TSATSUBA. Duk iya nemanka ba zaka ga inda littafin yake ba, Amma idan kayi hakuri nan da shekara arba'in wadansu hatsabiban Yara zasu zo har nan da littafin ka raba su da shi. Ni yanzu zan barka a nan. Zan tafi izuwa wani gagarumin yaki a tsakanin jinsinmu da jinsin wadansu Aljanu ma'abota wani Addini da ake kira musulunci. Ba lallai bane na rayu har na dawo gareka ba, Amma ka sani cewa yanxu duk sihirin tsafinka ya dawo. Kuma na gargadeka da kada ka kuskura ka fita daga cikin karkarshin Kasar nan, idan ko ka fita batare da KUNDIN TSATSUBA ba zaka sake fadawa hannun Sarki ZURKILU. Sa'adda aljanar tazo nan a zancenta sai nayi ajiyar numfashi na ce," yake wannan aljana sanar dani sunanki mana, Kuma inaso ki tunasar dani abun arzikin da nayi maki har ya janyo kikayi min wannan babban taimako." Aljanar tayi murmushi ta ce," sunana HAMMATUL LUHURUS ni ce babbar 'ya ga Sarkin bakaken Aljanu na yanxu na duniya. A halin yanzu shekarata dubu tamanin da uku a duniya. Abun arzikin da kayi min kuwa shi ne, watarana ka shiga jejin SABAS kana Neman saiwar bishiyar LUKES don hada wani sihiri, sai kaga wata barewa kwance a Kasa Yana numfashi sama-sama sakamakon Harbin da akayi mata da kibiya Mai dafi. Take tausayin barewar ya kama ka, kaje gareka ka cire mata kibiyar ka Kuma shafa mata magani Wanda ya kashe karfin dafin kibiyar. Kana kallo barewar nan ta mike ta shiga cikin jeji abinta. To ka sani cewa wannan barewa ba Dabba bace 'yata ZARINA. wannan harbi da akayi mata kuwa wani manemin aurenta ne yaso ya halakata saboda an hanashi ita. Tun daga wannan lokaci na dauki alwashin sai na Saka maka da abinda kayi mata. Sa'adda aljana HAMMATUL LUHURUS tazo nan a zancenta sai tayi shiru tana dubana, ni ko tsananin mamaki ne yasa nayi shiru Ina juya Ala'marin cikin kwakwalwata. Daga can sai HAMMATUL LUHURUS tayi min bankwana ta 6ace. Wannan shi ne Asalin zamana anan yanzu gashi Kun zo min da abinda zai wanke min bakin cikin rayuwata. Lokacin da Boka HAFSUL HABAL yazo nan a zancensa sai JAFARU ya dube shi yace," yakai wannan Boka hakika munji labarinka Mai ban tausayi da Al'ajabi ne. Amma ka sani cewa idan ka rabamu da wannan littafi ba kayi mana adalci ba. Zai Fi kyau ka biyo izuwa jejin KALKIM don mu dauko takobin SARJUS sannan mu wuce birnin TEHRAN mu sato Aljani MARKAHUSSABUS Wanda zai iya samo mana kubar miftahuzzarbil domin mu Bude wannan littafi da ita. Koda Jin haka sai HAFSUL HABAL yace," wannan ai zancen banza kenan, ya za'ayi na tafi yawon banza na 6ata lokacina alhalin ga abinda nake nema shekara da shekaru yazo hannuna. Sai dai ku jirani na fara zuwa birnin MASJUR tare da kundin tsatsuba na dauko fansar abinda Sarki ZURKILU yayi min sannan na dawo maku da littafin ku ma kuje ku aitawar da taku bukatar. Haba-haba ai wannan renin wayau ne, ya za'ayi ka ganmu da abunmu Kuma kace zaka nuna mana fin karfi? Gaskiya ba zamu amince da haka ba. JAFARU yayi wannan furuci cikin fushi. Kafin ya gama rufe bakinsa tuni igiyar nan ta karfe ta Kara kanannade su shida YALISA tana ta matse su suka fara ihu. Ba zato sai HAFSUL HABAL yaga igiyar tsafin nasa ta karkatse kawai sai ga Gimbiya sima da waziri Qaddaru sun bayyana a gabansa. Qaddaru na rike da kwari da baka, ita Kuma sima na rike da takobi ta ja Layi tana jiran ya motsa ta afka masa. Cikin fusata HAFSUL HABAL ya dube su yace ku Kuma su waye? Sanin ko mu su waye Bai taso ba. Abinda nake bukata dakai kawai shi ne, ka baiwa yaran nan littafinsu su tafi, idan Kuma kaqi yanzun Nan zan halakaka. Gimbiya sima ce tayi wannan bayani cikin gadara. HAFSUL HABAL ya tuntsire da dariya sannan ya ce," Ina ganin Kuna da karfi, Me zai Hana ku jaraba karbar littafin ku Basu? Na rantse da darajar tsafi zan yake ku batare da nayi Amfani da Shirin tsafi ba. Domin na renaku na Rena iskar ku ma. Yanzun nan zanyi gunduwa-gunduwa da wannan kyakkyawar surar taki, Kai ko wannan Dan guntun duk da dai baka fini tsawo ba, sai na rugurguzaka kamar yadda Kura ke rumurmushe nama a Baki. Yana gama fadin hakan sai ya daga hannu sama sai ga wata zabgegiyar adda ta bayyana, addar ta fishi girma da nauyi Amma sai ya shiga kaiwa su Gimbiya sima sara da ita Yana sarrafata kamar Wanda ya rike tsintsiyar laushi. Nan fa wuri ya yamutse aka fara dauki ba dadi, ba shiri Qaddaru ya yadda kwari da bakansa ya zaro wani mashi Dake maƙale a bayansa yaci gaba da kaiwa HAFSUL HABAL suka Kuma yana kare saransa. Nan fa HAFSUL HABAL ya zame masu alakakai ya takure su ya hanasu sakat, JAFARU da YALISA Kuma sai suka zama 'yan kallo. YALISA ta dubi JAFARU ta ce Kai ammafa kyakkyawar budurwar nan ta burgeni dubi yadda ta iya fada, wannan ai Ko a fagen yaki sai tayi 6arna. JAFARU yace gaskiya ne Amma fa ni guntun mutumen nan yafi burgeni gashi tsoho tukuf Amma sai kokarin tsiya. Ki dubi yadda ya addabesu shi kadai. To yanzu Kai shi kake so yayi nasara ko su? Haba qawata ya zanyi naso yayi nasara alhalin ya rabamu da kundin tsatsuba? Ai ni takaicina shine rashin iya yakina, da na iya fada da makami ai Kinga da saina temaka masu. An gaya maka ana koyon fada ne da Baki? Ai sai da jarrabawa ga wata takobi can dauki kaje ka jarraba. Koda JAFARU ya waiga yaga takobi ajiye a Kasa sai ya ruga ya dauka sannan yayi kururuwa ya afkawa HAFSUL HABAL. Da zuwa HAFSUL HABAL yasa Kafa ya mangareshi sai ga JAFARU yayi sama tamkar an cilla kibiya ya fado Kasa a sume daf da inda YALISA take. Mu hadu a KUNDIN TSATSUBA na daya part L don Jin cigaban wannan Kasaitacce Kuma Kayataccen labari Mai dadi da debe kewa 🥰♥️♥️ Anan ni Najibullah Muhammad nake cewa ku huta lafiya 🙏🥰**KUNDIN TSATSUBA** LITTAFI NA DAYA 1 ♥️ PART K 🔜👇 Author:- ABDUL'AZIZ SANI MADAKIN GINI 👮👮 TYPING:- NAJIBULLAH MUHAMMAD ✍️✍️ POSTING:- Najibullah Muhammad 🥷🥷 Note:- Comments, likes, share na da matukar muhimmanci wajen saurin kawo maku cigaban littafin 👇👇👇 08112778656 ( Whatsapp ) Marubucin yaci gaba da cewa... Sai ga JAFARU yayi sama tamkar an cilla kibiya ya fado Kasa a sume daf da inda YALISA take. Koda YALISA taga abinda ya same shi sai dariya ta kwace mata ta ce," lallai JAFARU ka cika sakarai, kawai daga na zuga ka sai kayi wauta? Ina Kai Ina fada da wancan tsohon mayakin? Jim kadan YALISA ta ga ko motsi JAFARU bayayi, Nanfa hankalinta ya tashi. Ba shiri ta fara jijjigashi tana Kiran sunansa, JAFARU dai bai motsa ba. Cikin rudewa ta cire wata karamar alkyabba da ta yafa ta rinka Masa fifita da ita. Nan take JAFARU ya farfado cikin ajiyar dogon numfashi. Har yanxu dai ana ta badakala tsakaninsu Boka HAFSUL HABAL da su Gimbiya sima. Babban abin mamaki shi ne duk cikinsu babu Wanda aka yiwa rauni, gashi suna yin fada cikin zafin nama ko alamar gajiya babu a tare da su. Ba zato ba tsammani sai kawai akaga wata irin iska mai karfi ta daga Boka HAFSUL HABAL ta fyadashi da Kasa take ya sume. Iskar ta rikide ta zama NARGAS da Aljanu GULZUM. Cikin sauri GULZUM ya daddaure HAFSUL HABAL da wata igiyar tsafi. Shi ko NARGAS ya tafi izuwa inda aka ajiye KUNDIN TSATSUBA da zuwa ya tsaya ya Karanta wadansu dalasiman tsafi, sannan ya dauki KUNDIN TSATSUBA salin-alin batare da wani Abu ya same shi ba. NARGAS ya matso gaban JAFARU ya Mika Masa KUNDIN TSATSUBA shi kuma ya karba. Kuzo mu tafi kada wankin hula ya kaimu dare, babu irin Neman da bamuyi maku ba Ashe kuna Nan. NARGAS ne yayi wannan batu a sannan ne Kuma ya samu damar yiwa su Gimbiya sima kallon tsaf. Wadannan Kuma su waye, meye gamunku da su? ALJANI GULZUM ne yayi wannan tambaya. JAFARU yayi farat ya ce nasansu domin na taba cetonsu a wancan jejin da muka yada zango. Yanzu Kuma su ne suka ceci rayuwarmu ni da YALISA anan. Lallai ba Abokan gaba bane. A wancan karon wannan kyakkyawar budurwar tayi min bayanin cewa ita ce Gimbiya sima Mai mulkin birnin LAHARIM, Amma bata gaya min dalilin dayasa ta baro kasarta ba. Koda Jin haka sai Aljani NARGAS ya ce," haba ni nasan biri yayi kama da mutum, lallai wadannan ne masu biye damu a baya. Kuma tabbas akwai sauran Abokan tafiyarsu Wanda ya kasance Aljani ba mutum ba. Dena zargin komai gani nan, ni ne Abokin tafiyar ta su. ALJANI DURFAS ne yayi wannan bayani yayinda ya bayyana Tsulum a gabansu. A dai-dai wannan lokaci ne Boka HAFSUL HABAL ya farfado daga dogon Suman da yayi sakamakon mugun kayen da Aljani NARGAS yayi Masa. Koda ya kyallara Ido ya gansa a daddaure da igiyar tsafi Kuma yaga kundin

Chapter 7 of 11