Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
10 / 11
fada Yana kallon duk abubuwan da ke faruwa tsakanin HUBAIRU da Aljanun a cikin madubin tsafinsa. Koda yaga aljanun sun galabaitar da su suna Shirin halaka su, sai ya kece da mahaukaciyar dariya sannan ya ce zancen banza, Ashema Kananan kwari ne Basu isa komai ba. Idan da nasan haka suke da na barsu sun karaso cikin fada ta. Inyaso sai nayi masu mugun kamu. Kafin LU'UMANU ya gama rufe bakinsa sai yaga HUBAIRU yayi kabbara da karfi ya Mike tsaye, kawai sai ya kama hannun Aljani Daya ya tsinke shi da karfin tsiya, take yayi Amfani da hannun a matsayin makami. Ya dinga dukan sauran Aljanun. Duk Wanda ya daka sai kaga ya ragargaje ya tarwatse. Koda ganin wannan Ala'mari sai Sarki LU'UMANU ya Mike zumbur daga Kan karagarsa cikin tsananin tsoro mamaki da dimaucewa. Kawai sai ya dubi sauran Dakarun Dake tsaitsaye a cikin fadar yace," Kar ku bar makiyana su iso Nan. Lallai yau abin nayi ne Ina zuwa. Kai tsaye LU'UMANU ya shige izuwa cikin dakin tsafinsa duk da cewa yasan kambun tsafi na daure a damtsensa sai ya shiga debo wasu layu da guraye Yana ta daurawa a jikinsa. Har sai da ya zamana in Banda warkin da ke kugunsa babu komai a duk jikinsa sai guraye da layun tsafi. LU'UMANU ya dubi Kansa sama da Kasa yayi wata kururuwa Mai tsananin razanarwa da karfi wacce kararta ta tsorata gaba dayan mutanen garin. Kasa tayi girgiza koramai suka fantsama. Kawai sai LU'UMANU yayi fitar burtu daga cikin dakin tsafinsa sai gashi yana yawo a Saman iska tamkar tsuntsu. Ala'marin su HUBAIRU kuwa, Bai gushe ba Yana kashe Aljanun nan masu siffar jemagu har sai da ya Karar da su gaba daya. Gaba dayan wannan Ala'mari ya faru ne a sararin samaniya ma'ana akan Aljani DURFAS. Lokacin da HUBAIRU ke ta faman halaka wadannan Aljanu sima jafaru Qaddaru gulzum da Nargas sunyi lamo akan Aljani DURFAS. Suna kallon abun mamaki da ba zato. Domin ganin Ala'marin suke tamkar Mafarki. Kowannensu jikinsa yayi sanyi suka razana da lamarin HUBAIRU. JAFARU ya dubi YALISA yace tabdijammmm wannan mutumin yafi Aljani shedanci, tunda nake ban taba ganin hatsabibi kamarsa ba. YALISA ta ce Uhm ai ko wajen Abbana ban taba Jin wani me irin siddabarunsa ba. Dubi fa yadda ya gama da dukkanin shedanun nan cikin kankanin lokaci. Na rantse da gemun ubana ko walkiya Bata fishi zafin nama ba. Ita ko Gimbiya sima tuni imaninta ya tafi ga HUBAIRU domin ya gama burgeta har sai ta ji kamar ta ruga ta rungume shi, don tsananin karuwar Qaunarsa a zuciyarta Amma sai ta danne zuciyar ta ta don kada ta tonawa kanta asiri. Bayan HUBAIRU ya tabbatar da cewa ya Karar da wadannan Aljanu, sai yayi Umarni ga Aljani DURFAS da ya tasarwa cikin birnin Kai tsaye. Batare da fargabar komai ba DURFAS ya tunkari garin. Koda suka bayyana a tsakiyar garin, sai ga Gungun wadansu dakarun daban, wadanda adadinsu ya ninka na wadancan. Su ko wadannan Aljanu masu siffofin mikiya ne, bakunansu kamar na zal6e ne. Wannan bakin nasu shi ne makaminsu. Duk abinda suka caka da shi sai ya hudo ta baya. Bayan da hubairu yaga wadannan sababbin Aljanu sunyi masu Kawanya, kawai sai ya koma ya kwanta ya dubi su JAFARU ya ce yanzu Kuma sai ku nuna min ababen dogaron naku, tunda na nuna maku nawa. Koda Jin haka sai JAFARU ya ce to kunji abinda yace saboda haka sai mu zage dantse, lallai mu ba mara da kunya. Koda yake ma na Rena wadannan Dakarun Ina ganin duk yawan nan nasu na banza ne zamu iya tarwatsa su cikin kankanin lokaci. Kafin JAFARU ya gama rufe baki tuni daya daga cikinsu ya kawo Masa suka da wannan dogon bakin nasa. Saura kiris ya huda Masa ciki, sai JAFARU ya sunkuya kasa cikin zafin nama duk da hakan sai da yayi Masa mugun yanka a cinya jini yayi tsartuwa. JAFARU ya kwallara ihu gami da faduwa Kasa jiri na dibarsa, Koda ganin abinda ya faru sai YALISA ta kwalla ihu ta fito da bulalar tsafi ta dinga dukan Aljanun nan da ita. NARGAS GULZUM sima da Qaddaru suka Taya ta wuri ya yamutse. Idan bulalar YALISA ta hadu da jikin Aljanun sai Kaji kamar an doki Dutse da gudumar karfe ko gezau basayi. Duk wannan dauki ba dadi da akeyi HUBAIRU na kishingide yaki ya Mike ya taimaka masu. Sa'adda aka Dade ana wannan turnuku sai karfin su sima ya kare, saura kiris ayi masu kisan gilla. HUBAIRU ya sake yin kabbara a karo na biyu. Dama har yanzu Yana rike da guntulallen hannun Aljanin nan, sai kawai yaci gaba da yin duka da shi. Cikin abinda Bai wuce dakika sittin ba, ya tarwatsa na tarwatsawa ya karya na karyawa ya kashe na kashewa masu gudu kuwa suka arce. Shin yanzu zakuyi Imani da Ubangijina? Kuyi sani cewa shi ne ya bani taimako na tseratar da rayukanku daga sharrin wadannan Aljanu. HUBAIRU ne yayi wannan furuci. Har sima ta Bude Baki zata ce wani abu, sai Aljani DURFAS ya tari numfashinta yace tukunna dai har sai ka fito da Aljani MARKAHUSSABUS sannan zamu Bada Gaskiya da Ubangijinka. Sa'adda HUBAIRU yaji haka sai yayi ajiyar zuciya ya ce, lallai shiriya na ga Allah. Shikenan muje zuwa da Sannu zaku Gane gaskiya. Nan take suka Kara kunna Kai cikin birnin har suka Isa fadar Sarki LU'UMANU. Har a sannan babu abinda ake face dauki ba dadi da bataliyar Aljanu da su HUBAIRU iri-iri. Har sai da sukayi fada da Aljanu kala dubu duk suka halakar da su, Amma duk HUBAIRU ne karfin samun nasarar su. Yayinda ake wannan gumurzu ne YALISA ta samu damar sa wa JAFARU magani ne a inda aka Yanke shi. Amma har yanxu JAFARU be farfado ba. Nan take hankalin YALISA ya dugunzuma tayi zaton JAFARU ya mutu, kawai sai ta rungume shi a kirjinta ta fashe da kuka. Tausayi ya kama Gimbiya sima, tazo daf da YALISA ta ce Ina dalilin wannan kuka naki? YALISA ta ce yake wannan sarauniya kiyi sani cewa na shaku da JAFARU har ta Kai cewa abotarmu ta Kai matsayin so da Qauna. Na rantse da darajar tsafi tun sa'adda muka baro kasarmu naji sonsa ya kwarara a cikin zuciyata. Kuma tuni na ayyana a raina cewa indai muka girma shi ne zai zamo mijina..... Tom Alhmdllh. Mu hadu a KUNDIN TSATSUBA na daya part N don Jin cigaban wannan Kasaitacce Kuma Kayataccen labari Mai dadi da debe kewa 🥰 ♥️ ♥️ Naku har kullum wato Najibullah Muhammad ke maku sallama tare da fatan Alkhairi 19/12/2025.**KUNDIN TSATSUBA** LITTAFI NA DAYA 1 ♥️♥️ PART N ♥️🔜 MARUBUCI ABDUL'AZIZ SANI MADAKIN GINI 🪖 TYPING:- NAJIBULLAH MUHAMMAD ✍️✍️ POSTING Najibullah Muhammad 🥷🥷 Note:- comments da likes da share ya zama wajibi ga duk masu bibiyar wannan labari ✍️ 08112778656 ( Whatsapp ) Marubucin yaci gaba da cewa.. YALISA ta ce yake wannan sarauniya kiyi sani cewa na shaku da JAFARU har ta Kai cewa abotarmu ta Kai matsayin so da Qauna. Na rantse da darajar tsafi tun sa'adda muka baro kasarmu naji sonsa ya kwarara a cikin zuciyata. Kuma tuni na ayyana a raina cewa indai muka girma shi ne zai zamo mijina. To yanzu gashi ya tafi ya barni Ina amfanin rayuwata a doron Kasa? Wannan batu yasa tausayi ya Kara baibaye Gimbiya sima. Kawai sai ta Kara hancinta dai-dai na JAFARU, Koda taji alamun fitar numfashinsa sai tayi murmushi ta ce kwantar da hankalinki Kanwata. JAFARU na raye be mutu ba. Kamar hadin baki kuwa sai idanun JAFARU suka bude a hankali. Koda ganin haka sai farin ciki ya lullube YALISA ta sake rungume shi. A dai-dai wannan lokaci Aljani DURFAS ya sauke su a bakin kofar shiga fadar Sarki LU'UMANU. Dirarsu keda wuya dakarun bil'adama sukayi ta 6ullowa ta ko'ina kamar tururuwa sukayi masu Kawanya. Gaba dayan Dakarun na rike da muggan makaman yaki iri-iri, adadin dakarun ya wuce a kidaya su. Daga Nan inda su HUBAIRU ke tsaye suna iya hango Sarki LU'UMANU tsaye a tsakiyar fadar tasa rike da kugu, fuskarsa a murkuke idanunsa sun kada sunyi jawur saboda tsananin fushi har wani irin huci yake irinna mugun maciji. Gaba dayan jikinsa daure yake da layu da gurayen tsafi. Ko takalmi babu a kafarsa. Bayan anyi kallon-kallo tsakanin HUBAIRU da Sarki LU'UMANU, na 'yan dakiku. Sai LU'UMANU yayiwa dakarunsa Umarni da su afkawa su Hubairu. Nan take wuri ya yamutse aka hau dauki ba dadi. A wannan lokaci JAFARU ne kadai a kwance baya iya ta6uka komai. Amma kowa na zubar da iyakar kwarewarsa a iya fada da tsafi. Da yake wannan fada da mutane ake ba da Aljanu ba, sai lamarin yasha bamban. Hakika Gimbiya sima Qaddaru NARGAS GULZUM da DURFAS sun taka muhimmiyar rawa a wannan yaki, Amma ko kadan basuyi rabin kwazon da HUBAIRU yayi ba. Sai da aka samu sa'a uku cur ana ruguntsumi. Yayinda HUBAIRU yaga wankin hula zai Kai su dare, ma'ana gashi dai suna kashe Dakarun Amma kamar matattun ne ke tashi. Sai ya Kara kaimi ya shiga tsakiyar Dakarun ya shiga sara da suka. Idan ya shiga bangaren sai ya dangana da karshen bango, sai dai kaga gawarwaki na zubewa Kasa kamar ana ruwan sama. Haka ma idan ya doshi yamma sai ya dangane da bango. Cikin abinda Bai wuce rabin sa'a ba HUBAIRU ya Karar da dukkanin Dakarun da ke cikin fadar nan gaba Daya. Ya rage saura Sarki LU'UMANU kadai a tsaye, zuciyarsa na tafarfasa kamar zata tsaga kirjinsa ta fito, saboda tsananin fushi da fusata. Yayinda Gimbiya sima ta ga wannan gagarumin aiki da HUBAIRU yayi, sai ta hau yi Masa tafi, su JAFARU ma sai suka taya ta. Bayan sun dena tafin ne sai sima ta shiga yiwa HUBAIRU kirari. Koda sima ta gama yiwa HUBAIRU kirari, sai ya waigo yayi Mata murmushi mai taushi Wanda yasa taji farin ciki ya lullube ta. Bata San sa'adda itama ta mayar Masa da martanin murmushin ba. Kafin jarumi HUBAIRU ya juyo, ya dubi inda Sarki LU'UMANU yake. Tuni LU'UMANU ya tashi cikin iska ya dira a gaban HUBAIRU, take ya cafki makoshinsa ya daga shi sama yayi hajijiya da shi da hannu daya ya fyadashi da jikin bango. Kawai sai gani akayi kan HUBAIRU ya fashe jini Yana kwarara. Gangar jikinsa ko ta sulale Kasa ko motsi bayayi. Ala'marin da yasa JAFARU da YALISA Gimbiya sima suka kwalla ihu cikin tsananin firgicewa. Sima ta ruga inda Gangar jikin hubairu ke kwance ta rungume shi tana kuka. Sarki LU'UMANU ya kyalkyale da dariyar mugunta sannan ya shiga yiwa Kansa kirari. Sa'adda Sarki LU'UMANU ya gama yiwa Kansa kirari sai ya juya ga Gimbiya sima ya kama gashin Kanta ya fincikota jikinsa, sannan ya dube ta da kyau ya kyalkyale da dariya ya ce" yau na samu me maye gurbin FATISA. Kece Zaki maye gurbin matata. Wadannan Abokan tafiyar nan naki kuwa, yanzun nan zan Sanya a kaisu kurkuku na da ke karkashin Kasa. A sanyasu cikin akwatunan karfe a kullesu a Raye, kamar yadda na yiwa Aljani MARKAHUSSABUS. Cikin matukar karfin hali, sima ta dubi LU'UMANU ta ce Kai la'ananne bakin kare, kayi kadan na zama matarka. Na rantse da darajar karagata sai dai ka Auri mushe na. LU'UMANU ya sake bushewa da dariya a karo na biyu sannan ya ce, yarinya bari sumbatu da surutan banza tuni aikin gama ya gama. Nan take ya murza kambun tsafin nan dake hannunsa sai ga bakaken Aljanun nan guda dubu hudu da arba'in da hudu sun bayyana. Su duka sukayi sujjada a gareshi suka ce me kake bukata damu ya Sarkin duniya? LU'UMANU ya ce inason ku kama wadannan Kananan kwarin ku shigar da su cikin kurkukuna ku Saka su cikin akwatunan karfe ku kulle su. Kamar yadda ku ka yiwa Aljani MARKAHUSSABUS da Gimbiya FATISA. Aljanun suka Amsa an gama ya mai duniya. Caraf suka damke JAFARU YALISA GULZUM da NARGAS da DURFAS kamar yadda mutum ke kama kaza, suka nutse da su izuwa karkashin Kasa. Shi ko Sarki LU'UMANU sai ya juya ya nufi dakin tsafinsa rike da Gimbiya sima. Ba zato ba tsammani sai yaji an daka Masa tsawa. Cikin firgici LU'UMANU da Sima suka waiga bayansu. Ba wani bane sai jarumi HUBAIRU yana tsaye bisa duga-duginsa har yanzu jini na zuba ta Kansa. Take yayi nuni da Dan yatsansa izuwa Sarki LU'UMANU yace Kai azzalumi tsohon Mushiriki, kayi sani cewa Ubangijina ya rayani ban mutu ba, yanzu ne zamuyi fito na fito da Kai. Da yardar Ubangijina sai naga bayanka daga yau an dena Bautar wani ba Allah ba a cikin kasarka. Yau ne ranar da gaskiya zata Kore karya. Kuma yau ne ranar da haske zai mamaye duhu a wannan birni. Duk da cewa Sarki LU'UMANU yayi matukar mamaki da yaga HUBAIRU ya Mike, Amma sai ya sake kyalkyalewa da dariya ya ce Kai yaro karya kake, ba a haifi wani da a doron Kasa ba, da zayyi galaba a kaina. Yanzun nan zanyi maka kisan gilla a gaban wannan kyakkyawar yarinya me tsananin Qaunarka. Take LU'UMANU yayi wurgi da Gimbiya sima ta fadi can gefe guda. Cikin tsananin zafin nama ya zare takobinsa yayi tsalle sama ya kurma wani wawan ihu, ya kaiwa HUBAIRU wani mugun sara da nufin ya tsarge shi gida biyu. Cikin zafin nama Hubairu ya goce, da yake takobin ta tsafi ce sai ta fasa ginin fadar ta nutse cikin karkarshin Kasa. Take LU'UMANU ya zare takobin da hannu daya ya sake kaiwa HUBAIRU sara, a lokacin da tuni Shima ya zare tasa takobin gami da Furta Kalmar kabbara, ya kare wannan sara. Koda takubban suka hadu sai tartsatsin wuta ya tashi. Nan fa suka cigaba da kaiwa juna sara da suka ba kaukautawa... Idan Hubairu ya samu nasarar jikin LU'UMANU sai yaji kamar ya gaftari dutsen wuta. Sai dai Kaji takobinsa tayi Kara ta ce Kal. Shi ko LU'UMANU idan ya samu nasara sai dai kaga jini na zuba a inda ya sari Hubairu. Ana cikin haka ne LU'UMANU yayiwa Hubairu kyakkyawan sara guda uku, daya a cinya Daya a kirji Daya a ciki. HUBAIRU dai be San sa'adda ya saki takobinsa ba ta fadi, Shima ya Yanke jiki ya fadi. Koda ganin haka sai sima ta sake fashewa da kuka. LU'UMANU yayi tsalle ya dira a gaban Hubairu yana Mai kyalkyala dariya. A wannan lokaci idanun Hubairu na rufewa da budewa yana ganin LU'UMANU. Yayi kururuwa yayi ihu irin wanda Mazaje ke yi a filin daga yayinda suka samu nasara akan Abokan gaba. Kawai sai ya daga takobin da hannu biyu da nufin ya caka a cikin Hubairu. Kafin hakan ta faru tuni Hubairu ya kira sunayen Allah tsarkaka guda uku, kawai sai yaji wani irin sabon karfi ya shige shi, cikin zafin nama yasa tafin hannunsa ya tare tsinin takobin LU'UMANU Wanda ke Shirin Burma cikinsa. Koda tafin hannun ya hadu da tsinin takobin sai ta dakushe, Hubairu ya rike takobin gam da hannunsa, ya matsa ta sai ko ta lauye. Take Hubairu ya dukunkuneta tamkar yana dukunkune takarda, yayi jifa da ita. Ala'marin da yayi matukar firgita Sarki LU'UMANU kenan ya ja da baya ya murza kambunsa na tsafi, sai ga bakaken Aljanun nan sun bayyana. LU'UMANU ya dube su ya ce ku kamashi kuyiwa yadda kuka yiwa 'yan uwansa. Aljanun nan sukayi Kan jarumi HUBAIRU gaba Daya da nufin zartar da Umarni. HUBAIRU ya nuna su da yatsansa, sai yaga wani irin Jan haske ya lullube su. Kawai sai suka kama da wuta suka kone kurmus sai tokarsu. Faruwar hakan keda wuya sai kambun tsafin nan dake jikin damtsen LU'UMANU ya cire Kansa ya 6ace. Nan fa Ido ya rena fata, LU'UMANU ya fara ja da baya-baya Yana Shirin gudu. Koda jarumi HUBAIRU ya fahimci nufinsa sai ya daka tsalle ya cacimeshi ya shiga bugunsa hannu da Kafa shima ya fara mayar da martani. Idan LU'UMANU ya naushi Hubairu sai yaji kamar ya naushi icce ko gezau baya yi. Shi ko idan yayi Masa naushi guda sai yayi tsalle sama ya rabu da Kasa, sai dai kaga ya gwaru da bango ya fado Kasa. Duk wannan Abu da ke faruwa Gimbiya sima na zaune a Kasa tana kallo cikin tsananin mamaki. Bayan Hubairu ya gama galabaitar da Sarki LU'UMANU, sai ya hau ruwan cikinsa ya tallafo Kansa da hannu biyu, ya ce zaka Bada Gaskiya da Ubangijin musulunci ko kuwa na hallaka ka? Koda Jin wannan batu sai Sarki LU'UMANU yayi murmushi ya ce haba Yaro da na karbi wannan Addini naka, ai gara na mutu a jeji Tsuntsaye su tsattsageni. Ai abun kunya ne ace ni Sarki LU'UMANU, ace anzo har kasata an cini da yaki Kuma nayi mubaya'a ga Yaro kamarka. Ina tabbatar maka da cewa Koda zakaqi kasheni sai na kashe kaina. Ni da musulunci sai gaba marar iyaka. LU'UMANU na gama fadin hakan, Hubairu ya murde Masa wuya ya yada gawarsa Nan. Ita ko Gimbiya sima sai ta Mike zumbur ta ruga gareshi suka rungume juna tana mai cewa nayi Imani da Ubangijinka, tabbas Addinin musulunci shi ne Addinin gaskiya. Koda Jin wannan lafazi sai farin ciki ya lullube Hubairu, nan take ya biya Mata Kalmar shahada ta maimaita. HUBAIRU ya dube ta ya ce Ina sauran Abokan tafiyarmu? Sima ta ce ai bakaken Aljanun nan ne suka shigar dasu kurkukun karkashin Kasa inda aka ajiye Aljani MARKAHUSSABUS. Koda Jin haka sai jarumi Hubairu ya ce bakomai ai da izinin Allah yanzun nan zamu Isa garesu. Kawai sai ya daga hannunsa sannan ya roki Allah akan ya kaisu wannan wuri. Take Kasa ta Bude wanwar, kamar yadda za'a bude tsakiyar littafi, sai gasu a cikin wannan kurkukun. Hubairu da sima sukayi arba da bakaken akwatunan nan manya-manya guda bakwai, kowace an garkameta da Katon kwado. Daya daga cikin akwatunan nan an kebeta a waje guda, a samanta an rubuta sunan Aljani MARKAHUSSABUS. Koda suka matsa daf da akwatun sai sukaga ruwan hawaye na zubowa ta cikin wata siririyar Kafa. Kuma suna iya jiyo saurin murya daga cikin akwatun. Suka Kasa kunnuwa, sai sukaji Ashe Aljani MARKAHUSSABUS ne yake rera Waka. Koda jarumi HUBAIRU ya gane cewa wannan me Waka Aljani MARKAHUSSABUS ne, sai ya Kai hannu da nufin Bude akwatun. Sima tayi wuf ta rike hannun ta ce dakata Sarkin jarumai. Ai bai kamata ka fara fito da Aljani MARKAHUSSABUS ba, shin ka manta ne cewa su JAFARU sun ce ba zasu Bada Gaskiya ga Allah ba, har sai sunga ka fito da shi a gaban idanunsu? Jarumi Hubairu yayi murmushi sannan ya ce kwarai kuwa kinyi gaskiya ya sarauniyar kyawawa. Wannan kalami ba karamin dadi ya yiwa Gimbiya sima ba a Rai, don ji tayi kamar an bada sarautar duniya. Jarumi Hubairu ya matsa kusa da sauran inda akwatunan suke, ya sake yunkurawa don ya bude ta farko. 08112778656 ( Whatsapp ) Najibullah Muhammad ✍️ KATSINA👆♥️ Sai sima ta sake rike hannunsa ta ce dakata jarumi uban jarumai. Kafin ka fito da Abokan tafiyarmu inason muyi wata magana ta sirri. Ina da tambayoyi guda uku a gareka, Kuma da fatan zaka bani amsarsu tsakaninka da Allah. Cikin mamaki Hubairu ya ce fadi tambayarki ni ko zan baki Amsa iyakar Gaskiya da abinda Allah ya sanar da ni. Tambaya ta farko ita ce, shin ka taba yin soyayya? Tambaya ta biyu ita ce, menene babban burinka a Nan duniya? Tambaya ta karshe wane Abu ne yafi burgeka fiye da komai? Sa'adda jarumi Hubairu yaji wadannan tambayoyin daga bakin sima sai yayi mamaki, kawai sai ya dube ta ya ce, amsarki ta farko ita ce ban taba yin soyayya ba. Amma Kuma yanzu na fada a cikin koginta na nutse a ciki na Kasa fitowa. Amsarki ta biyu kuwa ita ce, Bani da wani babban buri duniya Wanda yafi naga musulunci ya rinjayi Kafirci. Abinda yafi burgeni a duniya shi ne, ganin mace kyakkyawa Mai kyam hali da zuciyar tsoron Allah kamar ki. Da Jin haka sai murmushi ya kwacewa sima ta ce, na rantse da Ubangijin musulunci ni ce me tsamoka daga cikin wannan kogi da ka fada. Ya Kai wannan jarumi tun farkon ganina da Kai Qaunarka ta disashe ji na da ganina. Bani da wani aiki sai tunaninka dare da rana. Yau gashi ka zama sanadin shiriya ta izuwa karbar Addinin gaskiya. Cikin farin ciki Hubairu ya ce hakika na karbi soyayyarki hannu bibbiyu irin karbar da uwa ke wa Dan da ta Haifa. Ina rokon Allah ya kaddara aure a tsakaninmu ki zama uwargidana ko a gidan Aljannah. Da Jin haka sai itama farin ciki ya lullubeta, tayiwa Allah godiya. Batare da Bata lokaci ba Hubairu yayi Bismillah ya cire kwadon akwatunan nan guda shida, ya bubbudesu. JAFARU YALISA Qaddaru NARGAS GULZUM DURFAS suka firfito daga ciki. Cikin tsananin mamaki su shidan suka dubi sima da Hubairu suka ce, ya akayi ku ka tsira daga sharrin Sarki LU'UMANU? Koda Jin wannan tambaya sai jarumi Hubairu ya kwashe labarin duk abubuwan da suka faru ya zayyane masu. Da ya kare sai yace to kunsan cewa akwai alkawari a tsakaninmu Kan zan fito da Aljani MARKAHUSSABUS daga cikin akwatun da aka kulle shi. Ku Kuma ku karbi addinina, ko ba haka bane? Gaba dayansu suka Amsa suka ce hakane. To yanzu zan fito da shi da izinin Allah kamar yadda na fito da ku Nan take jarumi Hubairu ya nufi inda akwatin Aljani MARKAHUSSABUS da nufin ya Bude ta. Kafin ya Isa gareta sai Aljani DURFAS yayi wuf ya mangareshi, sannan ya mangare sima da Qaddaru duk su uku suka fadi Kasa sumammu. Cikin fushi JAFARU ya ce saboda me kayi wannan Danyen aiki? Saboda idan muka Bada Gaskiya da addininsa har abada bazamu taba samun nasarar bude KUNDIN TSATSUBA ba. Maza ka sare kwadon akwatun MARKAHUSSABUS da takobin SARJUS domin mu daukeshi Mubar wajen nan da sauri. Batare da wata gardama ba JAFARU ya fito da takobin SARJUS daga cikin aljihun rigarsa ya sare kwadon sai akwatun ta Bude. Tana budewa sai sukayi arba da wata battar karfe a ciki. ALJANI DURFAS ya dauki battar karfen sannan ya Suri JAFARU da YALISA da GULZUM da NARGAS ya aza su a gadon bayansu, nan take yayi sama da su suka fice daga cikin karkarshin Kasar nan. Nan da suka luluka a cikin gajimare suka bace, suna tsala mahaukacin gudu. Bayan sun samu kamar sa'a uku suna tafiya a cikin gajimare batare da sunce kala ba, sai JAFARU ya ce Wai Kai DURFAS yanxu Ina ka dosa da mu ne? Koda Jin wannan batu sai DURFAS ya kyalkyale da dariya sannan ya ce babu inda na dosa da ku sai Kogon shugaban Boka SULBAINI. Domin duk abinda nayi bisa Umarninsa nayi. Cikin fushi YALISA ta ce haba, ai wannan zancen banza ne. Kana nufin kenan duk wannan wahalar da muka Sha ta tashi a banza, Kai a shugabanka zakuci gajiyar Kundin tsatsuba? Kwarai kuwa ko Kunqi ko kunso haka Ala'marin zai kasance tunda Baku da wani zabi. Idan ko kukayi min gardama sai na halaka ku na tafi da kundin tsatsuba da wannan battar karfen. Sanyawa zuciyarka ruwan sanyi ya Kai DURFAS. Ai baza'ayi haka ba. Duk yadda kake so haka za'ayi. Mu masu biyayyane a gareka da Kuma shugabanka Boka SULBAINI. ALJANI NARGAS shi ya fadi haka. Da Jin haka sai DURFAS ya kyalkyale da dariya ya ce Ashe dai Kunsan Gaskiya. Shin yanzu tafiyar kwana nawa zamuyi kafin mu Isa Kogon Boka SULBAINI? JAFARU ne yayi wannan tambaya. DURFAS ya numfasa ya ce, a Kalla zamuyi kwana sittin da uku. JAFARU ya ce kenan dole sai mun yada zango. Kwarai kuwa Kasan dole ne na rinka hutawa bayan kowane kwana bakwai. Domin Ina saurin gajiya kasancewar Ina dauke da rai hudu. Da fadin haka sai JAFARU da YALISA suka dubi juna, sukayi signa kamar zasu kulla wani munafurci. Kwanci tashi su JAFARU sukayi kwana bakwai a sararin samaniya. Da yammacin kwana na bakwai ne DURFAS ya sanar da su zai sauko Kasa ne domin yada zango. Nan take su JAFARU suka nuna amincewarsu. DURFAS ya rufe fuka-fukansa sukayo Kasa luu har suka iso Kan turba. Cikin wani jeji ne mai yawan duwatsu da bishiyoyi

Chapter 10 of 11