ya wannan Sarki, kawai mu tsaya bisa alkawari Banda tunanin nuna Isa ko iKo. Koda Jin haka sai Sarki LU'UMANU yayi murmushi mai nuna yadda da Kai. Sannan ya nuna Aljani MARKAHUSSABUS da Dan yatsa ya ce," Kai wannan Aljani Ina Mai gargadinka da ka kiyayi bil'adama domin hatsabibancinmu yafi naku. Ka sani cewa duk yanda kake tsammaninmu mun wuce haka. Na rantse da darajar karagata idan ka kuskura kayi ba dai-dai ba, zakaga iKona kuwa.
Sa'adda Sarki LU'UMANU da Aljani MARKAHUSSABUS ke wannan cacar bakin, tuni cikin Bokayen nan ya duri ruwa. In Banda Sarkin Bokayen babu Wanda jikinsa Bai kama kyarma ba don tsoron Kar MARKAHUSSABUS ya hallakar da garin gaba Daya.
Ba zato sai MARKAHUSSABUS ya tuntsire da dariya, sannan ya ce," ai shikenan lokaci zai bambace komai. Yanzu me kuke bukata da ni?
Sarki LU'UMANU ya sake yin murmushi a karo na biyu ya ce," bukatata da Kai kawai shi ne," ka tafi izuwa KOGON ZUHURUM ka debo min tsumin DODO KIRYANU.
Da zuwanka zan biya kowace irin bukata ka ambata.
ALJANI MARKAHUSSABUS yayi murmushi sannan ya ce, " na amince Kuma yanzun Nan zan tafi izuwa biyan bukatarka. Ba zan dawo ba sai bayan kwana dari da goma Sha biyu. MARKAHUSSABUS na gama fadin haka sai ga Matar Sarki LU'UMANU, FATISA ta shigo cikin dakin, tare da kuyangi suna take mata baya. Da shigowarta tayi arba da Aljani MARKAHUSSABUS.
Nan fa suka kurawa juna Ido, har sai da taje ta zauna dab da Sarki LU'UMANU tana waigensa. Shi ko MARKAHUSSABUS idonsa na tsaye a kanta ko kiftawa bayayi. Tuni ya tafi duniyar begenta saboda tsananin dimaucewa da kamuwa da Sonta. Bayan FATISA ta zauna sai ta dubi Sarki cikin murmushi sannan ta ce," wannan Kuma waye daga cikin Bokayen duniya?
Sarki yayi murmushi ya ce," ai wannan ba bako bane, Aljani ne. MARKAHUSSABUS kenan, shi ne Wanda zai yaye mana bakin cikin da ya addabi rayuwarmu tsawon shekara da shekaru.
FATISA ta sake yin duba izuwa ga MARKAHUSSABUS dakyau, ta ce, Kai Amma wannan Aljani da kyau yake. Koda Jin haka sai MARKAHUSSABUS yaji farin ciki ya lullube shi. Bai San sa'adda ya mayar Mata da martanin murmushi ba. Sannan ya ce," na rantse da darajar iyayena Kaf! Iyakar yawona a duniya ban ta6a ganin mace kyakkyawa irinki ba, Walau a cikin mutane da Aljanu.
Cikin fushi Sarki LU'UMANU ya dakawa MARKAHUSSABUS tsawa sannan ya ce," ya Kai wannan Aljani ka sani na sa hijabi tsakaninka da matata, ba Kai ba ita. Ban kirawo ka nan don kuyi hira ba. Na umarceka da ka 6ace min da gani.
Rufe Bakin Sarki LU'UMANU keda wuya, Aljani MARKAHUSSABUS ya bude fuka-fukansa Yana Mai dariya tare da dagawa FATISA hannu. Daga Nan Sarki ya sallami Bokayen SA da sauran jama'a kowa ya kama gabansa.
Ala'marin MARKAHUSSABUS kuwa, tunda yabar fadar Sarki LU'UMANU ya Kasa samun sukuni. Sakamkon tunanin Ala'mari guda biyu da suka addabi zuciyarsa. Abu na farko shi ne, wannan gagarumar tafiya da zayyi Kogon ZUHURUM don debo tsumin DODO KIRYANU. Tabbas yasan cewa wannan tafiya ba karamin hadari gareta ba. Domin bai ta6a yin tafiya Mai Nisanta ba. Kuma yasan cewa akwai abubuwan hadari akan hanyar Wanda Kan iya jawo asarar rayuwa gaba daya.
DODO KIRYANU 🥷🥷🪖
Tun MARKAHUSSABUS na Yaro karami yake Jin labarin dodo KIRYANU a wurin tsofaffin Aljanu. An tabbatar da cewa dodo KIRYANU yasha jinin Aljanu sama da dubu arba'in, bil'adama kuwa ba a lissafinsu. Da yawa jarumai da sadaukai sun rasa rayuwakansu wajen kokarin zuwa KOGON ZUHURUM don debo tsumin DODO KIRYANU. Shi dai wannan tsumi an ce Yana da sihiri dubu Saba in. Kuma ba a Sha sai an San Daya daga cikin sihiransa, sannan a Sha da wannan niyyar. A halin yanzu sihiri daya aka sani daga cikin sihiran, wato sihirin samun haihuwa.
Sauran sihirin kuwa babu Wanda zai iya saninsu face Wanda ya Karanta littafin KUNDIN TSATSUBA.
Bayan Aljani MARKAHUSSABUS yayi dogon tunani, sai ya Yanke shawarar ya koma gida ya sanar da mahaifiyarsa wannan gagarumar tafiya da zayyi. Ko ta taimake shi da abinda zai kiyaye Kansa daga abubuwan hadarin kan hanya. Nan take MARKAHUSSABUS ya juya da baya ya nufi kasarsu. Tsakanin birnin TEHRAN zuwa garinsu tafiya ce ta shekara arba'in. Amma a cikin sa'a hudu da 'yan dakiku kadan MARKAHUSSABUS ya shafe ta.
Yau shekaru biyu kenan rabon MARKAHUSSABUS da gida. Tun sa'adda yayi bankwana da mahaifiyarsa Kan cewa, ya tafi Neman aure ba zai dawo ba sai da mata. Mahaifin MARKAHUSSABUS ne wazirin Sarkin garin nasu.kuma ya mutu shekaru dari da hamsin baya. SAMARATU mahaifiyar MARKAHUSSABUS tana zaune a farfajiyar gidanta kuyangi sun zagayeta suna Bata labarai masu dadi, don debe Mata kewar danta.
Sai kwatsam suka ga MARKAHUSSABUS ya bayyana a gabansu. Cikin tsananin farin ciki SAMARATU ta Mike zumbur ya ruga gareshi suka rungume juna. Bayan sun natsu sai ta janye jikinta daga nasa, ta duba Gabas da yamma kudu da arewa Bata ga komai ba. Ya Kai dana Ina sirikar tawa? Ashe ba mun rabu akan cewa ba zaka dawo ba sai da Matar da zaka aura? MARKAHUSSABUS ya jinjina Kai ya ce," kinyi gaskiya ya ummina, hakika na gano matar da ta dace dani Amma mallakarta dai-dai yake da tashin yakin duniya. Batare da Bata lokaci ba ya kwashe labarin FATISA Matar Sarki LU'UMANU ya zayyane mata kaf! Da Kuma Batun zuwansa Kogon ZUHURUM.
Da ya kare sai yace ya ke ummina kiyi sani cewa na ayyana a zuciyata, babu abinda zan nema a wajen Sarki LU'UMANU a matsayin ladan aikina, face ya aura min wannan mata tasa wato FATISA. Idan ko yaki zan sace ta na taho da ita nan a daura mana aure. Na rantse da darajar sarautar gidan nan na kamu da tsananin son Gimbiya FATISA. Son da bazan iya rayuwa ba sai da ita. Kiyi sani cewa ban dawo gareki domin komai ba sai don ki taimaka min da Shirin da zan kare lafiyata yayin wannan tafiya.
Domin nasan kin gaji sihirai da dama a wajen mahaifina. Sa'adda MARKAHUSSABUS yazo nan a zancensa sai SAMARATU tayi shiru, gami da sunkui da kai Kasa Bata ce komai ba. Daga can sai ta dago Kai ya dubi dan nata, idanunta cike da kwalla ta ce ya Kai dana a cikin duniyar Nan kaf! Babu abinda nakeso sama da Kai. Kuma komai ka bukata a gareni indai Ina da shi, sai na baka. Kayi sani cewa wannan bukata taka, dai-dai take da masunci a cikin ruwa. Ma'ana idan ya jefa kamar sa Bai San abinda zai kamo ba. Tabbas zan taimaka maka, Kuma zaka samu nasarar debo tsumin DODO KIRYANU. Amma Ina jiye maka sharrin Sarki LU'UMANU. Lallai wannan mutum ba karamin hatsabibi bane, domin Yana iya sarrafa Aljani kamar yadda ake sarrafa kwayar hatsi a turmi. Bani da wani sihirin da zan iya kare ka daga sharrinsa. Hakika idan ka kusanci matarsa sai ya 6oye ka a cikin kurkukun da babu Mai iya fito da Kai. Kaga kuwa idan haka ta faru, shikenan an rabani da Kai har abada. Ina Mai baka shawara da ka cire son FATISA daga ran ka. Ka sake fita Neman wata. Ka sani cewa duniya fa, na da fadi. Babu mamaki ka gano wata wadda ta fita a wani bangaren daban.
08112778656 ( Whatsapp)
Yayinda SAMARATU ta zo nan a zancenta, sai MARKAHUSSABUS ya ce , ya ke ummina ki dena tsoron komai. Kiyi sani cewa ni MARKAHUSSABUS na Kai wani matsayin da Baki zato. Ina mai tabbatar maki da cewa babu wani bil'adama da ya Isa ya sarrafa ni yadda yake so a doron Kasa, sai dai Dan uwana ALJANI ko kuma irinsu dodo KIRYANU.
Na maki alkawarin babu abinda Sarki LU'UMANU zai iya yi. Kawai ki taimaka min nayi wannan tafiya lafiya. SAMARATU tayi ajiyar numfashi ta ce," to shikenan ai ance ba a kwace wa Yaro garma. Amma Wanda Bai ji bari ba, zai ji hoho." Yanzu ka zauna zan tafi jeji na samo wasu ganyayyaki da sauyoyi na jika su, su kwana a tsume sannan ka shanye. Indai ka Sha wadannan tsumin babu wani hadari da zai same ka yayin wannan tafiya. Ala'marin dodo KIRYANU kuwa bani da wani kariya da zan iya baka, sai dai karfi da hikimarka su kwace ka. Da Jin haka sai MARKAHUSSABUS yayi murmushi ya ce, na sani ummina Kuma na amince, kedai kawai ki tafi aiwatar da naki Shirin. Kafin ya gama rufe bakinsa tuni SAMARATU ta 6ace. Bayan kamar sa'a biyu sai ga SAMARATU ta dawo, dauke da wasu ganyaye da sauyoyi iri-iri birjik, wasu ma babu Wanda yasan kalar su. Da zuwa ta sa aka dauko mata wata Katuwar kwatanniya aka zuba a ciki. Sannan ta kawo ruwa ta zuba akai. Zuba ruwan ke da wuya, sai ganyayen da sauyoyin suka hau narkewa suna tafarfasa. Kai kace kwatanniyar a karkashin wuta take. Nan take ta kawo murfin kwatanniyar ta rufe, sannan ta dubi MARKAHUSSABUS ta ce," ya Kai dana jeka abinka kayi barci don ka samu Hutu daga Nan zuwa Asuba. Zan zo na tashe ka don kasha wannan tsumin.
Batare da wata gardama ba yake dakinsa ya kwanta yayi ta sharar barci har da minshari. Asubahin farko SAMARATU ta tashi MARKAHUSSABUS suka tafi izuwa tsakar gida inda aka ajiye kwatanniyar nan, da zuwa ta dube shi ta ce Maza ka dauki kwatanniyar nan ka shanye abinda ke cikinta.
Nan take MARKAHUSSABUS ya daga wannan kwatanniyar da hannu biyu, wadda nauyinta ya wuce karti dari su iya raba ta da Kasa. Kawai sai ya Kafa a bakinsa ya kwankwade ruwan ciki. Gaba daya zuka uku yayiwa ruwan a bakinsa ya kare. MARKAHUSSABUS ya ajiye kwatanniyar nan sannan yayi gyatsa. Faruwar hakan keda wuya yaji gaba dayan jikinsa ya dau, dumi. Kafin a jima zufa ta lullube shi tamkar ruwa ake kwarara Masa. Nan da Nan gumin jikinsa ya malala a Kasa ta taru.
Inda bil'adama zai fada cikin gumin, sai ya nutse ciki yaji kamar kogi ya fada. Bayan gumin jikin nasa ya Kafe, sai Kuma yaji wani irin sabon karfi ya shige shi. Tamkar zai iya daukar duniya bisa tafin hannunsa. MARKAHUSSABUS yayi girgiza ya daka tsalle gami da kururuwa wadda ta farkar da duk mutanen garin gaba Daya. Kowa ya tashi a firgice daga barci. Kawai sai ya dubi mahaifiyar tasa ya ce ya ke ummina hakika kinyi min kyakkyawan Shirin da zan iya tunkarar komai da kowa. Ina Mai godiya a gareki gami da Yi Maki sallamar cewa ni zan tafi izuwa ga Neman biyan bukatata. Amma na dauki alkawarin cewa bazan dawo gareki ba sai da matata Gimbiya FATISA. Koda Jin wannan batu sai hawaye ya zubowa SAMARATU ta rungume MARKAHUSSABUS ta ce, Ina maka fatan nasara Dana, lallai zan kasance cikin kewa da tsananin begenka, har sai naga dawowarka. Sannan take MARKAHUSSABUS yayi bankwana da mahaifiyarsa sannan ya Bude fuka-fukansa yayi sama, tana kallonsa tun tana hangensa har ya kule a cikin gajimare.
08112778656 ( Whatsapp)
MARKAHUSSABUS yasha gwagwarmayar gaske a dazuzzuka daban-daban kafin ya Isa Kogon ZUHURUM. Domin sai da yayi dauki ba dadi da mugayen Aljanu iri-iri da Kuma dodanni. Sai da ta Kai cewa yayi jinyar rashin lafiya sau sittin da biyar. Amma ko kadan bai tsaya da yin tafiyarsa ba. Ma'ana har iya Isa Kogon ZUHURUM Yana fama da rashin lafiya sakamakon raunikan da ke jikinsa. Shi Kansa ya fitar da ran rayuwa Amma bisa mamaki sai yaga Bai mutu ba.
Lokacin da MARKAHUSSABUS ya dira a bakin Kogon ZUHURUM tsakiyar dare ne, don haka dodo KIRYANU da iyalansa na kwance a cikin Kogon suna barci. Kogon ZUHURUM na da matukar tsawo fadi kaurin gaske. Kofar shiga Kogon zagayayya ce Kuma an rufe ta da wani Katon mulmulallen Dutse. Babu Mai iya janye wannan Dutse face KIRYANU da matarsa wadda ake wa lakabi da MASHAMU.
SA'ADDA MARKAHUSSABUS yazo ya iske wannan mulmulallen Dutse sai ya tsaya a bakin Kogon. Abinka da Mai takama da karfi sai ya kama Dutsen da hannu biyu da nufin ya dauke shi. Kawai sai yaji kamar Yana Shirin daukar sararin samaniya, take yaji kamar jijiyon hannunsa zasu tsittsinke. Ba shiri ya saki Dutsen. Daga can sai ya sake komawa ya Kara jarrabawa a karo na biyu. Abinda ya faru da farko shi ne ya sake faruwa.kai sai da MARKAHUSSABUS ya jaraba daukar Dutsen Nan sau bakwai Yana kasawa. Ala'marin da yayi matukar tayar Masa da hankali kenan ya rasa abinda ke Masa dadi a duniya.
Nan dai ya tsaya Yana tunani yace a ransa, bani da wata dama da tafi yanzu, domin a yanzu ne idan na samu damar shiga Kogon,sai na sato tsumin sali-alin nayi tafiya ta batare da ya ganni ba. Amma idan na kuskura gari ya waye yayi arba Dani, tawa ta kare. To yanzu ya zanyi tunda Kogon yaki budewa, Kuma me ya kamata nayi don kubuta daga sharrinsa? Wata zuciyar tace dashi kawai ka tafi cikin jejin Nan kawai ka 6uya a wani wurin har izuwa wani daren sannan ka dawo.
Babu mamaki kayi sa'a ka tarar ya bar kofar a Bude. Ai masu iya magana sun ce ba kullum ake kwana a gado ba. Yau da gobe tafi karfin wasa, dole ne watarana ya mance kulle kofar.
Da wannan shawarar MARKAHUSSABUS yayi Amfani, Amma sai da dare bakwai ya shude Bai taba zuwa ya tarar da wannan Kofa a Bude ba. Kullum jiya i'yau. Nan fa hankalinsa ya Kara dugunzuma, a wannan dare ne ya Kasa tafiya ya tsaya yana shawarwarin abinda zai fisshe shi. Shi Kam ya tabbatar da cewa tunda yazo wannan wuri ba zai koma ba sai da tsumin DODO KIRYANU, ko Kuma ya rasa rayuwarsa a wajen.
Haka dai yaci gaba da tunani iri-iri har Asuba ta doso Kai, Nan take ya Yanke shawarar ya samu wuri ya 6oye nesa kadan. Inda zai rinka hango Kogon, da zarar yaga KIRYANU ya fito sai yaje ya shiga ya debo tsumin ya kama gabansa.
MARKAHUSSABUS ya tashi sama, ya tafi can nesa kadan izuwa kan wasu bishiyoyi masu yawan ganyayyaki da duhuwa, ya 6uya. Yadda Yana iya hango Kogon ZUHURUM din. Yana Nan la6e har gari yayi shaarr rana ta fara hudowa. A lokacin ne gyangyadi ya fara daukarsa sakamakon gajiya bisa doguwar tafiyar da ya Sha, ta tsawon kwana dari da goma Sha biyu. Tun sa'adda ya baro gida kawo izuwa yanzu Bai runtsa ba. Lallai kuwa akwai tarin barci akansa ..
Ba zato sai barci ya sace shi, yayi ta kwarara barci abinsa Bai San abinda ke faruwa ba......
Nima a dai-dai wannan lokaci ne barci ya figeni nayi ta sharara barci sakamakon gajiyar da ta makalkale jikina tun dazu..
Saboda haka nake maku sallama tare da cewa sai mun hadu a 'KUNDIN TSATSUBA' na daya part E don Jin cigaban wannan Kasaitacce Kuma Kayataccen labari, Wanda ni Najibullah Muhammad nake kawo maku shi✍️✍️🙏🙏🙏🙏**KUNDIN TSATSUBA**
LITTAFI NA DAYA 1 ♥️♥️
PART E ✍️✍️
MARUBUCI:- ABDUL'AZIZ SANI MADAKIN GINI 👮👮
TYPING:- NAJIBULLAH MUHAMMAD ✍️🥷🥷
08112778656 ( Whatsapp)
CIGABAN LABARIN......
Jim kadan da fara barcin nasan ne, kofar Kogon ZUHURUM ta Bude. Sai ga dodo KIRYANU tare da matarsa MASHAMU da 'yarsu guda daya ZARAZU, sun fito waje suna masu yin hamma da Mika.
Kai da ganinsu Kasan cewa yunwar safe ce ta tashe su. Shi dai dodo KIRYANU ba karamin zabgegen Kato bane, Yana da manyan damatsa da Kuma rafkeken Kai, idan yayi tafiya sai Kaji Kasa na amsawa saboda karfin takun sawunsa.
Idan ko ya gifta wajen da bishiyoyi suke, sai kaga suna rangaji saboda tsananin hucin iskar hancinsa da bakinsa. Nan fa dodo KIRYANU ya shaki iska ya dubi matarsa da 'yarsa ya ce," Kai ku tsaya Anya kuwa bamu samu bako ba a jejin Nan? Nifa Ina iya Jin kamshin bil'adama. MASHAMU ta daga bututun hancinta mai kama da algaita ta shaki iska, sannan ta ce kwarai Mai gida Nima naji kamshinsa. Lallai yau Muna da kyakkyawan lagwada. Ina ganin rabonmu da cin bil'adama Ina ganin a Kalla za'ayi shakeru Ashirin. Sai dai Naman Aljanu kullum da shi muke kalaci, harma sun ginshe mu. Gara na ci Naman dabbobin dawa ma. Koda Jin haka sai ZARAZU ta bushe da dariya ta ce, lallai naga alama rikicin tsufa ya fara riskarku. Ya za'ayi kuji kamshin mutum a jejin Nan? Shin Kun manta ne cewa, babu inda labarinmu Bai je ba a duniya? Ai tuni bil'adama suka sallama wannan jeji, suka dena shigo shi. Ku dai Kara shinshinawa dakyau kuji. Ba mutum bane aljanine Amma kamshinsa na daban ne.
Take KIRYANU da MASHAMU suka Kara shakar numfashi cikin natsuwa, tsawon dakika biyar. KIRYANU yace aikuwa yarinya tayi Gaskiya. Yanzu menene abinyi? MASHAMU ta ce, abinyi kawai shi ne ni da Kai mu tafi farautar wannan Aljani, mu bar ZARAZU tsaron Kogon. Bana son ka tsaya rufe kofa har mu 6ata lokaci har Aljanin ya tsere. Koda Jin wannan shawarar sai KIRYANU ya amince. Nan take suka nausa inda MARKAHUSSABUS ke la6e. Suka bar ZARAZU a kofar Kogon tana Mai kai-kawo, tare da leke-leke ko zata hango inda bakon Aljanin yake.
Yayinda Aljani MARKAHUSSABUS ya hango su dodo KIRYANU sun durfafo inda yake la6e, sai tsoro ya kama shi har hantar cikinsa ta kama rawa. Bai San sa'adda ya dauke numfashi ba, saboda tsananin razana. DODO KIRYANU da MASHAMU suka iso daf da bishiyar da MARKAHUSSABUS ke Kai suka tsaya. Nan sukayi duba iya dubansu Amma Basu ga komai ba.
Ala'marin da yayi matukar Basu mamaki kenan. MASHAMU ta dubi KIRYANU ta ce, Kai abinnan da ban mamaki yake, kafin mu iso wajen nan Muna ta Jin kamshin Aljani, Amma Kuma Muna isowa sai naji kamshin ya dauke. Gashi babu irin duban da bamuyi ba Amma bamuga komai ba. KIRYANU ya ce hakika haka Ala'marin yake. Ina ganin Aljanin ya gudu ya bar wajen.
Zo mu Kara gaba watakila mu riske shi. Batare da wata gardama ba MASHAMU tabi KIRYANU a baya, suka nausa cikin jejin suna daga bututun hancinsu sama don su jiyo a inda kamshin Aljanin yake.
Abinda Basu sani ba shi ne, Aljanin na Nan a inda suke. DODO KIRYANU da iyalansa basa iya ganin Halitta muddin halittar Bata numfashi. Wannan shi ne dalilin dayasa basuga MARKAHUSSABUS ba. Domin sa'adda ya ganshi, ya firgita ainun har numfashinsa ya dauke, har ta Kai shi GA Dan karamin Suma.
Sai bayan tafiyarsu da dakika dari uku da arba'in sannan ya farfado. Koda farfadowarsa sai yaga ZARAZU na ta kokarin kama wani tsuntsu Amma ta Kasa. Tsuntsun ya tsaya a sama ya Kasa tafiya, sai wahalar da ita yake. Wannan tsuntsu kamanninsa irin na gauraka ne. Gashi yunwa ta addabi ZARAZU Amma ta rasa yadda zata iya kama tsuntsun.
Da zaran ta bishi sai ya kada wani wurin, haka yayita wahalar da ita har ta gani ti6is. Abinka da yarinya sai kawai ta zauna ta fashe da kuka. Wannan Ala'marin da ya faru yasa tausayi ya kama MARKAHUSSABUS. Kawai sai ya siyar da Rai, yayi fitar burtu daga inda yake boye kamar an cilla kibiya ya damko wannan tsuntsu ya karya Masa wuya, Sanna ya sauko Kasa gaban ZARAZU ya Mika mata tsuntsun.
ZARAZU ta fizgi tsuntsun ta jefa a baka, tauna uku kawai ta yiwa tsuntsun ta lankwame shi. Sannan ne fa aka fara kallon-kallo tsakaninta da MARKAHUSSABUS. Nan take yawun kwadai ya fara dalala daga bakinta. Kafin MARKAHUSSABUS ya Ankara tuni ta cafko shi da hannu daya, ai kuwa sai ta wangame bakinta da nufin ta gutsire Kansa ta taune. Cikin Karaji MARKAHUSSABUS ya ce, haba-haba 'yar lele, ya Zaki cinye Wanda ya taimake ki? Ki min Rai, ni kuwa na kawo maki sakayyar bil'adama Dari. Koda Jin haka sai ZARAZU ta fasa cinyeshi, ta ajiye shi a Kasa a hankali.
Sannan ta dube shi ta daka Masa tsawa ta ce, Kai karamin mayaudari ka sani cewa na San halinku na Aljanu Kun iya karya da munafurci. Na yarda zanyi maka rai Amma, ba zan sake ba sai dai mu tafi dakai izuwa inda zaka samo min bil'adama dari. Da jin haka murna ta kama MARKAHUSSABUS ya ce na yadda da wannan sharadi, Amma bisa uzuri guda. Fadi uzurinka naji don Ina da aiki a gabana. Ina son ki debo min tsumin mahaifinki na tafi dashi yanzu. Koda Jin haka sai ZARAZU ta zazzaro idanu cikin fargaba ta ce, tafdi jam. Nanfa Daya, ruwan tsumin mahaifina a kididdige yake, yasan adadinsa. Duk bayan tsawon kowane kwana bakwai yake cika kwatanniyar da yake tsuma wannan tsumin. Kuma sai yayi kwana bakwai Yana Sha. Kuma kullum kur6a bakwai yake yi ya koshi bayan yayi kalaci.
Idan na debo Koda cikin Kofi Daya ne zai Gane, idan ko ya Gane take zai kasheni. Domin ko mahaifiyata Bai yarda Tasha wannan tsumin ba. Idan kana son na debo wannan tsumin na baka, to dole ne ka zauna har tsawon kwana bakwai sa'adda zai hada sabon tsumin, ni Kuma sai na faki idonsa na kara yawan ruwan tsumin. Lallai Ina kwadayin na samu Naman bil'adama naci na more. Domin rabona da shi yau shekaru Ashirin kenan. Tabbas zan biya maka wannan bukata indai zaka samo min bil'adama dari.
Domin boye su zanyi a wani wurin na rinka tsakura dai-dai da dai-dai Ina ci har su kare.
Sa'adda MARKAHUSSABUS ya ji haka sai hankalinsa ya tashi ya ce, to yanzu tayaya zan iya zama a nan har tsawon kwanaki bakwai? Batare da iyayenki sun San da zamana ba? Ki sani cewa da zarar sunji kamshina zasu kama ni su cinye. ZARAZU ta bushe da dariya ta ce Kar ka damu, kamar yadda kazo min da hikima na fasa cinyeka, haka su ma zanyi masu hikima su Kasa ganinka har tsawon wannan lokaci. Kai dai abinda nake so dakai shi ne, duk abinda na ce kayi to kayi Kar ka Saba. Idan ko ka Saba sunanka halakakke. Ai ko zan zamo Mai biyayya ga dukkannin umarninki. Yana gama fadin haka suka jiyo Karar sawun dodo KIRYANU. Cikin hanzari ZARAZU ta dauke shi ta jefa a cikin wata tsohuwar rijiya da ke cikin Kogon ZUHURUM.
Sannan ta mayar da murfin rijiyar ta rufe. Kawai Kuma sai ta zurmuka Dan yatsanta guda a cikin Baki, ta fara kakarin amai. Tana cikin wannan Hali ne DODO KIRYANU da MASHAMU suka iso cikin Kogon. Da zuwa suka durkusa gaban ZARAZU suna masu tambayarta abinda yasa take kakarin amai. ZARAZU ta dago Kai ya dube su idanunta sunyi jawur ta ce, bayan tafiyarku na kama wani guntun Aljani na cinyeshi, sakamakon bakar yunwar da nakeji ne yasa ko kadan bai isheni ba, sai ya zamana ya tayar min da zuciya har amai ya taso min. Ina ganin haka sai na bude tsohuwar rijiyar can nayi aman a ciki, inda muke zuba Kasusuwan Aljanu da mutane.
Wannan shi ne dalilin dayasa ku ka dawo ku ka sameni a cikin wannan hali, gashi har yanzu zuciyata Bata dena tashi ba.
08112778656 ( Whatsapp)..
Najibullah Muhammad ✍️✍️
MASHAMU ta gyada Kai ta ce gaskiyane, domin gashi Ina iya jiyo kamshin Aljanin daga cikin rijiyar. To ai ga Naman dabbobin daji nan mun kamo, sai kiyi sauri kici ko zuciyar taki ta dena tashi. Nan take ZARAZU ta dubi Gawar wasu zakuna guda hudu da ke sakale a kafadar KIRYANU ta wafto guda da rabi ta hausu da ci. Kafin dakika dari da Ashirin ta gama cinyesu. Tayi gyatsa Mai karfi sannan ta dauki ruwa a cikin wata Katuwar tukunya, tayi Masa makwarwa hudu ta shanye. Koda ta ajiye tukunyar sai tace yawwa yanzu naji Dan dai-dai. In anjima Kuma sai ku fita kuyi mana farautar na Rana ko? KIRYANU ya dube ta a fusace ya ce, ke dai kin cika cin tsiya. Kullum mu kenan a cikin yi maki wahalar farauta? Dubi abinda kika cinye ke kadai, ko ni da Uwar taki ba zamu iya cinyewa ba.
To babu inda zamuje da Rana, sai dai kije kiyi farautar da kanki. Nan dai KIRYANU da MASHAMU suka sa Zaki biyu a gaba suka cinye.ya rage saura guda Daya da rabi. Bayan sun kare sai suka nemi wuri suka kwanta, don suyi barcin kailula.
Ita ko ZARAZU sai ta zauna tayi shiru tana tunanin zuci, inda ta ayyana cewa muddin ta kuskura ta fita daga cikin Kogon sai iyayenta sun Bude tsohuwar rijiyar nan sun fito da Aljani MARKAHUSSABUS sun cinye. Saboda kamshinsa