A birnin Sin kimanin shekaru dari da arba'in bayan zamanin Sarki Fir'auna na Misra.
Anyi wani balaraben mutum Wanda ake kira RUZYAL.
Asalin RUZYAL mutumen Misra ne Amma yawon duniya ne ya Kai shi birnin Sin.
Shekarun RUZYAL zasu Kai tamanin da biyar Kuma Yana da wani hatsabibin da guda daya Wanda ake kira JAFARU.
JAFARU Yaro ne Dan shekaru goma Sha biyu, Kuma ya kasance mai kunnen Kashi, domin baya Jin bari.
Sannan bashi da tsoro ko kadan.
Batun ta'adi kuwa ko 6era ya sallama Masa, dai-dai da dakika guda hannun JAFARU baya zama kyan, koyaushe a cikin 6uruntu yake.
Bugu da Kari JAFARU baya zama wuri Daya, tun safe sai ya wuni Yana yawo lungu-lungu sako-sako a cikin birnin Sin, Bai damu da yunwa ko kishirwa ba, muddin zai baiwa idanunsa abinci ta hanyar kalle-kallen abubuwan Al'ajabi da debe kewa.
Kyan da ya gaji Ubansa, kamar yadda JAFARU ke mutuwar son ganin ababen Al'ajabi, haka mahaifinsa yake.
Domin kuwa bincike ya tabbatar da cewa tun RUZYAL na Dan shekaru Tara a duniya yake bincike akan abubuwan Al'ajabi wadanda suka faru a duniya Yana rubutawa.
Musamman abubuwan da suka shafi tsafi jarumta da daukaka.
RUZYAL ya kasance Mai tafiye-tafiye kasa-kasa, yana ziyartar matsafa da sarakai suna bashi labarurruka, shi ko yana rubutawa Yana ajiyewa.
Lokacin da RUZYAL ya samu shekaru tamanin a duniya, sai ya tattaro labaran da ya rubuta ya shiga sake rubuta su a cikin wani Katon littafi Wanda akayi bangonsa da katako da Kuma jemammiyar fata, shafukan cikinsa na takarda mai kauri ne guda dubu daya.
Sai da RUZYAL ya shafe kwana dubu daya Yana mayar da tsohon rubutunsa a jikin wannan sabon Katon littafi Mai inganci.
a ranar da ya gama rubutun cikin dare ne, sulusainin dare kuwa.
Yana zaune a turakarsa shi kadai, dama a wannan lokacin matarsa Zuhura ta samu shekara guda da rasuwa.
Dansa JAFARU kuwa na can wani daki daban Yana barci.
Lokacin da RUZYAL yaga ya kammala wannan rubutu. Sai farin ciki ya lullube shi, nan take ya Mike tsaye da nufin ya dau littafin yaje ya 6oye a cikin akwatinsa.
Mikewarsa keda wuya sai wata irin iska Mai karfi Abar firgitawa, ta ratso cikin dakin.
Saboda karfinta sai tukwanen dake sagale a cikin dakin suka rinka farfashewa, Kai komai dai Dake cikin dakin sai da ya tashi sama Yana yawo a iska, har shi Kansa RUZYAL din.
Ba zato ba tsammani sai kawai yaga wani murgujejen ALJANI ya bayyana a gabansa, cikin mummunar siffa.
Ala'marin da yayi matukar tayar da hankalinsa kenan ya firgita, idanunsa suka zazzaro.
Aljanin ya kyalkyale da dariya sannan ya ce, " haba baban hikima, ya zaka fara aiki kaqi karasawa"?
Jikin RUZYAL na karkarwa ya dubi Aljanin ya ce, " ya Shugabana me ya rage a cikin rubutun wannan littafi, ai na gama komai."
Aljanin ya daka Masa tsawa wadda tasa ya Kara firgicewa, har ya saki fitsari a wandonsa.
Karya kake baban hikima, domin ko baka rubuta sunan littafin ba, Wanda zai zamo abun daukaka abun tsoro ga duniya gaba Daya.
Maza ka rubuta 'KUNDIN TSATSUBA' a jikin bangon littafin nan.
RUZYAL ya sake duban Aljanin cikin tsananin tsoro a karo na biyu sannan ya ce," ya shugabana ai alkalamina bazai iya rubutu a jikin bangon wannan littafi, domin ko na rufe littafin da jemammiyar fata ne."
Koda Jin haka sai Aljanin ya Suri RUZYAL da Dan yatsansa guda, Kuma ya yanki dan yatsan RUZYAL da kaifin farcen hannunsa, jini ya fara zuba.
Da karfin tsiya Aljanin ya dangwala hannun RUZYAL a bangon littafin, har sai da ya rubuta sunan littafin da jinin jikinsa kamar haka ' KUNDIN TSATSUBA ' take jinin ya daskare akan littafin.
ALJANI ya ce," ya Kai RUZYAL na umarceka daka kankare sunan wannan littafin yanxu-yanxu, cikin biyayya da fargaba RUZYAL yasa faratan hannunsa da nufin kankare rubutun, amma sai Abu ya faskara.
Koda ganin haka sai RUZYAL yaje ya dauko wuka, yayita kankarar rubutun har tsawon lokaci Amma ko Kwarzanewa bayyi ba.
RUZYAL ya tube rigarsa yaje ya dauko gatari yayi ta saran rubutun har sai da ya jike sharkaf da ji6i, Amma rubutun yaki saruwa.
Aljanin ya sake bushewa da dariya sannan ya ce, tsaya haka ya RUZYAL Baban hikima.
Ka sani cewa babu wani Abu da zai iya kankare wannan rubutu a duniya, Kuma wannan littafi ba zai yagu ba Kuma ba zai konu ba.
Ina horonka da kayi Masa ma6oya ta kirki, na rantse da gemun Sarkin Aljanu daga yau duk Wanda ya kuskura ya Bude wannan littafin to ya budewa duniya kofofin masifu iri-iri guda dubu Daya.
Koda Jin haka sai zuciyar RUZYAL ta buga, ya ce har abada bazan bari wani ya Bude shi ba ya Shugabana.
Shin zaka iya sanar da ni ko Kai waye? Kuma menene hikimar ka akan umarta ta da boye wannan littafi?
Aljanin ya bushe da dariya ya ce," ba zaka Sanni ba, sai ranar da wani mahaluki ya samu nasarar Bude wannan littafi. Hikimata kuwa akan boye wannan littafi shi ne, cikinsa akwai sirrikan tsafi guda dubu Daya.
Duk mahalukin da ya samu damar Karanta su sai ya mulki duniya gaba dayanta.
Kai kanka da ka rubuta littafin ai baka taba Karanta shi a lokaci guda ba.
Aljanin na gama fadin haka ya 6ace, shi kuwa RUZYAL sai yaga abun kamar a Mafarki. Amma da ya tuna irin gargadin da Aljanin yayi Masa, sai ya Mike zumbur ya kinkimi Katon littafin, Bai tsaya ko'ina ba sai gaban wata tsohuwar rijiya dake tsakiyar gidan.
Ita dai rijiyar zurfinta yakai kamu Dari biyu, musamman RUZYAL yayi matattakala a cikinta ta shiga. A cikin rijiyar Kuma ya Gina wani karamin daki, Wanda babu Mai shiga sai shi kadai.
RUZYAL ya shiga cikin wannan rijiyar har ya shiga cikin wannan dakin ya ajiye KUNDIN TSATSUBA sannan ya fito daga cikin rijiyar.
Murfin wannan rijiya anyi shi ne, da wani Katon karfe Wanda Koda karti tamanin zasu taru ba zasu iya dagashi ba.
Nan fa RUZYAL ya tsaya Yana tunanin hanyar da zai bi ya rufe murfin wannan rijiya, alhalin baya so jama'a su san da batun kundin tsatsuba.
Bisa mamaki sai yaga Aljanin nan ya sake bayyana, take yasa Dan yatsa guda ya dauki murfin ya rufe rijiyar sannan ya sake 6acewa.
RUZYAL ya juya da nufin ya koma dakinsa ya kwanta, kawai sai yayi arba da shi.
Ba wani bane face dansa JAFARU a bakin kofa ya rike kugu Yana murmushi, RUZYAL ya dube shi a cikin kaduwa ya ce," JAFARU me kakeyi a cikin dakin Nan har yanxu bakayi barci ba?
JAFARU ya sake yin murmushi sannan ya ce," Abba duk abinda ya faru a tsakaninka da wannan Aljanin na gani Kuma na ji. Ina tabbatar maka da cewa sai na Bude rijiyar nan na dauko KUNDIN TSATSUBA na Karanta, ko don ma naga irin MASIFUN da zasu 6arko duniya... 'hmmm karfa Yaron Nan ya jawo mana bala'i 🥺🥺""
JAFARU na gama fadin haka, sai RUZYAL ya rugo gareshi da nufin ya kama shi ya sa masa mari yayi ta tsaronsa, saboda yasan halinsa duk abinda yace zayyi sai ya yi shi komai wahalar sa.
Koda JAFARU ya fahimci nufin mahaifin nasa, sai yayi tsalle ya kama katangar gidan ya haura ya gudu.
Shi ko RUZYAL sai ya zauna a Kasa yayi tagumi cikin tsananin fargaba.
Nan ya shiga tunanin hanyar da zai bi yayi gadin wannan rijiya, dan lallai JAFARU zai dawo.
Haka dai RUZYAL ya kasance a cikin wannan Hali har Asuba tayi idanunsa garau babu alamar barci a tattare da su. Yayinda yaga barci ya kaurace Masa, sai ya Mike tsaye ya hau kai-kawo, zuciyarsa na ta sake-sake.
Kai a wannan Rana dai ko ruwa Bai Sha ba, balle ya ci abinci. Kirjinsa sai dukan uku-uku yakeyi.
Saboda tsananin fargabar yadda zai iya kare KUNDIN TSATSUBA, tabbas yasan irin hatsabibancin JAFARU ko tayaya sai ya shammace shi ya shiga cikin wannan rijiya ya sace kundin.
Sannu-sannu har magriba ta doso Bai Yanke shawarar abinda ya kamace shi ba, kwatsam sai ga Aljanin Nan ya sake bayyana a karo na uku.
Suna hada Ido RUZYAL ya zube a Kasa Yana tuba ya ce," ka gafarceni ya Shugabana, hakika bazan iya kare KUNDIN TSATSUBA ba, Ina rokon ka da ka dauke shi ka tafi dashi.
Yayinda Aljanin yaji wannan Batu, sai ya kyalkyale da dariya a lokaci guda Kuma ya tur6une Fuska ya ce," ai komai da ka sani na duniya Yana da muhallinsa, nan ne usulin KUNDIN TSATSUBA, Kuma babu inda za'a ajiye shi ya zauna cikin kwanciyar hankali da kyakkyawan tsaro sai nan din.
Ka kwantar da hankalinka ya RUZYAL, yanzun nan zanyiwa KUNDIN TSATSUBA makulli Wanda ba zai ta6a buduwa ba, face da wata kuba da ake kira MIFTAHUZZARBIL...
Najibullah Muhammad ✍️✍️
Kayi sani cewa ya Kai RUZYAL, ita dai kubar miftahuzzarbil wata kuba ce Mai joni uku, ma'ana ana iya rabata gida uku.
Ba zata taba yin aiki ba, muddin babu gida guda daga cikin ukun Nan.
Gida na farko shi ne Kai, Wanda aka kera shi da yakutu, gida na biyu shi ne Baki, Wanda aka kera daga shudin karfen jauhar, gida na uku shi ne tsakiyar kubar wato Gangar jikinta, Wanda aka kera da zubardaji ruwan dorawa.
Kayi sani cewa bayan na sanya wannan kuba na kulle wannan littafi, zan tafi da ita kubar na Kasa ta izuwa wurare uku da babu wani mahaluki da ya Isa yaje wajen ya dauko.
Wadannan wurare su ne, bangwayen karshen duniya na bangaren Gabas kudu da Arewa.
Kayi sani cewa zan dauki Kan wannan kubar na Kai shi bangon dake Gabas, sannan na dauki bakin kubar nakai bangon kudu, ita kuwa tsakiyar kubar zan Kai bangon Arewa ne.
Ya Kai RUZYAL daga nan birnin Sin zuwa wadannan bangwayen guda uku, tafiya ce ta shekaru dubu hanlmsin-hamsin.
Ma'ana kafin kaje kowane bango sai ka shafe shekara hamsin kana tafiya.
Ni kadai ne Aljanin da zan iya wannan tafiya a cikin kwanaki hamsin-hamsin.
Yayinda RUZYAL yaji wannan Batu sai murna ta kama shi.
Fuskarsa ta cika da murmushi ya ce," ya Shugabana Ina rokonka da ka hanzarta aiwatar da wannan shiri naka.
Domin ni dama tun jiya da ka tafi ka barni ban runtsa ba, saboda tsananin tsoron dana JAFARU.
A cikin sauri Aljanin ya tari numfashin RUZYAL ya ce," na San duk abinda ya faru a tsakaninku ba sai ka fada min ba, kayi sani yakai ma'abocin hikima ni nafika tashin hankali idan har danka JAFARU ya samu nasarar Bude wannan littafi, domin Shugabana ba zai barni da Rai ba.
Kai ko wanene wannan shugaba naka, da har ya Kasa ajiye KUNDIN TSATSUBA a muhallinsa ya barshi a hannun matsoraci kama ta?
ALJANI ya takarkare ya bushe da wata mahaukaciyar dariya wadda tasa gaba dayan gashin jikin RUZYAL ya mimmike tsaye saboda tsananin razana.
ALJANIN ya ce," sanin Shugabana dai-dai yake da Neman kunci da Azaba da bala'in da baya da karshe.
Da sanin Shugabana gwara kullum a rinka yi maka azaba kala dubu har izuwa karshen rayuwarka.
Tabdijammmm🥺🙆🙆
Kai nifa ba surutu nazo yi ba, bani wuri ka gani.
Kafin RUZYAL yayi wani yunkuri tuni Aljanin nan ya nuna murfin rijiyar Nan da hannu, kawai sai ya Bude da Kansa.
Take sai ga kundin tsatsuba ya fito daga ciki, ya zo ya dira a hannunsa..
Aljanin ya zaro kubar miftahuzzarbil daga cikin aljihunsa ya caka a tsakiyar littafin, kubar ta nutse ciki ta fitar da siffa Mai kofar ta, ta 6ullo karshen bangon sannan ya Murda ta, ta kulle ya zare.
Koda yin haka sai ya mikawa RUZYAL kundin, sannan ya ce jaraba budewa mu gani.
RUZYAL ya kama bangon littafin yaja da nufin ya Bude, Amma sai yaji tamkar an like shi ne da kafar kusoshi.
RUZYAL yayi iyakar kokarinsa Amma ya Kasa Bude littafin, sai ya dubi Aljanin cikin gazawa ya ce ya Shugabana na rantse da girman iyayena in duniya zata taru wannan littafin bazai budu ba.
Sa'adda Aljanin yaji haka sai ya kyalkyale da dariya sannan ya karya kubar miftahuzzarbil gida uku, ya ce yanzu zan tafi na ida aikina.
Yakai ma'abocin hikima Ina Mai umartar ka da ka mayar da kundin tsatsuba cikin waccan rijiyar.
Kuma Kar ka samu damuwa Koda danka ya samu damar sace shi, domin har abada bazai iya dauko sassan wadannan kubar ba a inda zanje na boye su.
RUZYAL ya ce," an gama ya Shugabana Amma Ina Mai rokonka a karo na biyu da ka sanar dani sunanka da na shugabanka."
Maimakon Aljanin ya sake cewa wani Abu, sai ya bushe da dariya sannan ya ce," idan har zakaji Amsar wannan tambayar sai idan har danka JAFARU ya samu nasarar hada wannan kuba ta miftahuzzarbil tare da mallakar littafin, to a sannan ne zaka Sanni ka San Shugabana.
Yana gama fadin haka ya 6ace 6at.
Shi ko RUZYAL Bai San sa'adda ya tuntsire da dariyar farin ciki ba, don shi a zatonsa ya rabu da tashin hankali kenan har abada. Abinda Bai sani ba shi ne, yanzu ne ma zai shiga mugun tashin hankalin da Bai taba shiga irinsa ba a rayuwarsa.
ALA'MARIN JAFARU kuwa tun sa'adda ya gudu sai ya tafi wurin wani Sako, inda babu Mai ganinsa ya fito da madubinsa na tsafi ya fara binciken hanyar da zai bi ya samu Damar sato kundin tsatsuba a cikin wannan rijiya ta mahaifinsa.
Sai da ya shafe sa'a guda cur! Yana bincike Amma Bai samu nasara ba, daga bisani sai ya gano cewa babu Mai taimakonsa a cikin wannan Ala'mari face YALISA.
YALISA wata karamar yarinya ce kyakkyawar gaske 'yar shekaru goma Sha Daya, Kuma 'ya ce ga shugaban bokayen birnin Sin Wanda ake wa lakabi da Boka JISHEN.
Tsakanin YALISA da JAFARU ba a ga-maciji, domin duk sa'adda suka gamu sai ta azabtar dashi ta hanyar Amfani da karfin tsafi.
Wani lokacin ta Kan daga shi sama, tayi ta hajijiya da shi har sai ya fita daga hayyacinsa.
Ita kuwa tana mai kyalkyala dariya. Ko Kuma tayi ta Zane shi da bulalar tsafi mai 6acewa har sai ya vey, ya tuba ya bi ta, sannan ta ke kyaleshi.
wani lokacin ma sai ta mayar dashi jakinta Yana tafiya da ita cikin rarrafe.
Kai wani lokacin Kuma sai ta rinka Daura Masa igiya a wuya, tana cewa ga Karen ta.
Wulakanci dai iri-iri babu Wanda ba tayi Masa ba, saboda bakin cikin hakane yasa JAFARU ya shiga bin bokaye don ya samu sirrin da zai rama abinda YALISA ke Masa, Amma kullum a banza domin har yau Bai samu sirrin da yafi na ta karfi ba.
Gabar JAFARU da YALISA ta samo Asali ne tun watarana da suka taba haduwa a gindin wata rijiya don Shan ruwa.
A wannan lokacin ruwan Sha yayi Karanci sosai a birnin Sin, sakamakon wani mummunan yaki da akayi.
A wannan lokaci YALISA ta debo ruwa dakyar ta cika tulunta, sai ga JAFARU ya zo. Koda zuwansa ya dubeta ya tabbatar ya fi ta karfi, kawai sai ya kwace tulun Kuma ya mangareta ta fadi Kasa.
Kawai sai ya juya da nufin ya tafi abinsa, ba zato sai kawai yaga tulun ya bar hannunsa ya dawo gareta.
Duk da cewar yayi mamakin faruwar hakan, sai ya juyo a fusace ya dubi YALISA yace au rashin kunyar taku irinta 'yayan bokaye har tazo kaina? To yau zanyi Maganinki, yadda har abada ba zaki sake rena wani ba.
Kawai sai JAFARU ya tunkareta ya daga hannu da nufin ya shara mata Mari.
Wai ance rashin sani yafi dare duhu, inda JAFARU yasan abinda zai biyo baya da bayyi nufin hakan ba.
Koda yaje dab da ita, sai hannunsa ya kage ya Kasa motsa shi, JAFARU yayi iya kokarinsa don ya motsa hannun Amma ya Kasa.
Ba zato Kuma sai ya hau Marin Kansa da Kansa, har sai da ya mari kuncinsa sau arba'in.
Bai San sa'adda idanunsa suka ciko da kwallah ba ya fara kuka.
Ita ko YALISA sai ta bushe da dariya har ta fadi Kasa, daga can sai ta dubi JAFARU ta ce," daga yau mun kulla gaba ni da Kai har abada, zaka San cewa ka tabo tsuliyar dodo. Na rantse da gemun mahaifina duk sa'adda na hadu da Kai sai na wahalar da Kai."
Tana gama fadin haka ta dafa tulunta ta bace.
JAFARU ya nemeta sama da Kasa ya rasa.
Aliyu Abubakar Sharfadi
Ismail Abdullahi
Abdulaziz Sani Madakin Gini
Abdulaziz Sani Madakin Gini
Basiru Aliyu Harande Zuru
Abdulaziz Sani Madakin Gini
Ismail Abdullahi
Shehu Usman
Mansur Usman Sufi
Abdulaziz Sani Madakin Gini
Abdulaziz Sani Madakin Gini
Mansur Usman Sufi
by Umar Muhammad Sangaru
by Sumayya Abdulkadir Takori
by Aisha Mohammad Sani (Xayyishatul Humaira)
by Yar Gatan Huda
by Rahmatullah Muhammad
by Halima Musa Leemat
by Billy S Fari
by Abdulaziz Sani Madakin Gini
by Chamsiya Laouali Rabo,Mrs Sadauki
by Aisha Ali Garkuwa