Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
TASKAR TSAFI 3

TASKAR TSAFI 3

by Abdulaziz Sani Madakin Gini ,

0 Hours
26, Jan 2026
Unknown group
Not Inserted
Free
58.04 kb
TXT
40+
31+
Last download 1 hour ago

You cannot download this book until you log in, but you can read it.

Read Now

OR

Description

Lokacin da aka ruguntsume da azababben
yaki tsakanin tawagar gimbiya Abidatul
Azmal da mutanen birnin Nurul Kalbi, sai dakarun
Abidatul Azmal suka lulluße garin gaba daya,
tamkar kudan zuma akan kwason da ya sa zubi. Nan
fa aka ci gaba da fafatawa, inda aljanu, dodanni, da
dakaru marasa adadi suka yiwa mutane kalilan
rubdugu. Amma saboda karfin addu'a, sai gashi
kalilan mutane na taka muhimmiyar rawa. In banda
Karar karafa, ihun mazaje, da kururuwar aljanu babu
al in da mutum ke ji a wajen. Idan Musulrni ya sari
kafirin aljani da, takobinsa, sai ka ga aljanin ya
kama da wuta ya kone kurmus. Haka kuma idan
suka sarki dodo ko mutum, sai ka ga ya darc biyu.
Ana cikin wannan ruguntsumin fadane
gimbiya Abidatul Azmal ta hango Himal, sadaiki
Kurbas, da Hasilatul Kurbas suna ragargazar
jama'ar ta. Nan takoe ta fusata, ta bayyana a
tsakiyar su, ta afka musu da sara da suka. Su ukun
suka rufar mata, amma sai ta zame musu annoba.
Abidatul Azmal ta sami nasarar kaftawa
kowanne su sara da dai-dai, ta zub da su kasa,
kowannen su na murkusus a kasa ya kasa motsi.
Abidatul Azmal ta tsaya akansu tana murmushin
mugunya. A wannan lokaci sarki Maharaz na can
3
Taskar Ts
tsakiyar abokan gaba sun lullube shi yana ta
ragargazar su.
Abidatul Azmal ta dubi su sadauki Kurbas
daya bayan daya, ta bushe da dariya, sannan ta ce,
"Ashe har kuna tsammanin zaku iya bijire mini ne,
kuma ku tsira daga sharrina? Kun yi kuskure babba,
kuma yanzun nan zan zare muku ruhin numfashin
ku".
Koda gama fadin haka, sai ta yunkura da nufin
ta sare musu kawuna. Kawai sai taji an tari
takobinta da wata. Ba kowane ya kawo wannan
agaji ba face sarki Maharaz.
Nan fa suka fara mugun artabu shi da iya cikin
tsananin zafin nama, juriya, bajinta, da kwarewa.
Duk su biyun suka wanzu suna kaiwa juna sara da
suka tamkar jikinsu na karfe ne ba na jini da tsoka
ba.
A wannan lokacin ne su sadauki Kurbas suka
sami kwarin gwiwa suka mike tsaye suka ci gaba da
yaki.
Sai da aka sami sa'a tara ana wannan yaki.
Amma mutanen Abidatul Azmal ba su sami nasarar
balla katuwar kofar da za su shiga inda aka bоуе
yara da mata da tsofaffi ba.
Haka kuma mutanen birnin Nurul Kalbi sun
kasa karar da koda kaso daya daga goma na
dakarun Abidatul Azmal, gashi kuma kowanne
4
Taskar Tsafi-3 Abdul'aziz S. M/Gini
bangarc sun fara gajiya. Amma aljanun da dodannin
ko kadan babu alamar gajiya a tare da su.
Yayin da aljani Marwanul Hasanu ke taka
muhimmiyár rawa a wannan yakj. Sai ya fuskanci
cewa jama'ar sarki Maharaz na cikin mugun hali,
domin kuwa idan aka sake samun sa'a uku ana
wannan gumurzu za su iya gajiya a cisu da yaki, tun
da su aljanun da dodannin basa gajiya. Kuma gashi
kashe su ake ta yi, amma kamar dada karuwa suke.
Nan take Marwanul Hasanu ya sulale ya gudu daga
wannan filin yaki, ya nufi wani babbar birni na
jama'ar aljanu ma'abota addinin Musulunci, wanda
ake kira Baitul Asmar. Daga birnin Nurul Kalbi
zuwa birnin Baitul Asmar tafiya ce ta kwana biyar,
amma sai Marwanul Hasanu ya dage iya karfinsa,
ya dinga tsala hudu yana mi kada fuka-fukansa da
sauri, domin ya isa wannan birni a cikin kwanakin
da ba su haura uku ba.
Burin sa shi ne a kawowa su sarki Maharaz
dauki kafin a ci karfin su.
***
A can birnin Nurul Kalbi kuwa, yaki ya kara
tsamari ainun. Musamman kaurewar Abidatul
Azmal da sarki Maharaz, wadda ta haddasa
rugujewar gine-gine da dama da kuma kamawar
5
Taskar Tsafi-3 Abdul'aziz S. M/Gini
wuta bisa tsananin karfinsu, da kuma amfani da
karfin sihirin da Abidatul Azmal ke yi.
Sai dai duk tsafin da take yi ya ki ya yi tasiri
akan sarki Maharaz, kasancewar shima yana ta
karanto addu'o'in neman tsari.
Ana cikin wannan dauki ba dadine daya daga
cikin dakarun Abidatul Azmal ya gano cewa an
boye mata da yara, da tsofaffi a cikin wani gida na
Karkashin Kasa. Koda gano haka, sai yaja tawagar aljanu suka durfafi kofar wajen, wacce ta kasance
Katuwar gaske ta bakin karfe.
Aljanun na zuwa bakin kofar, sai sadauki
Kurbas ya hangosu, kuma ya gane nufinsu. Ai kuwa
sai ya falfala da gudu izuwa wajen. Kafin ya karasa
ya daka tsalle ya dirga a gabansu ya hausu da sara. Suma suka rufar masa, amma sai gashi yana tarwatsa su suna konewa. Amma saboda naci, da
taurin zuciya, wasun su nė suka yi ta tattudowa. Sai da aka sami sa'a guda Kurbas na ta ragargazar aljanun nan. Shi kađai ya zame musu alakakai, ya hanasu 6alla wannan kofa.
Ana cikin haka ne wani shaidani ya ja wasu daga cikin aljanun suka kewayo ta bayan' Kurbas suka shammace shi suka sure shi izuwa sama, har takobinsa ta subuce daga hannunsa, kuma wani daga cikinsu ya watsa masa wata laka a baki ya kasa ci gaba da addu'a.
6
Taskar Tsafi-3 Abdul'aziz S. M/Gini
Koda ganin sun sami wannan nasara, sai wani
daga cikin su ya taso sama daga kasa rike da
takobin haske irin ta su ta tsafi, da nufin ya sare kan
sadauki Kurbas.
Ba zato ba tsammani, sia aka ga wata mace
wadda ta rufe duk jikinta, har da fuskarta ta rugo da
gudu rike da zabgegiyar takobi tana mai karanta
wadansu addu'o'i a bakinta. Kawai sai ta yi tsalle ta
dinga taka kan abokan gaba tana kara yin sama, har
ta riski wanda ke shirin hallaka sadauki Kurbas, ta
tsarga shi gida biyu, ya zama gawayi. Sannan ta
tarwatsa wadanda ke rike da Kurbas, duk suka
watse, sannan ta tallafo Kurbas a hannu kamar ta
riko karamin yaro, ta sauko kasa kamar tsuntsuwa
ta dira a hankali, ta dire Kurbas a kasa. A lokacin
Kurbas ya furzar da lakoar da ke bakinsa, ya dubi
wadda ta ceci rayuwar cikin tsananin mamaki, ya
ce, "Wace ce ke?".
Maimakon ta bashi amsa, sai ta yaye mayafin
da ke fuskarta, suka yi arba da juna. Ba wata bace
face gimbiya Zuhura, mahaifiyar sarki Maharaz.
Nan fa mamaki ya turnuke sadauki Kurbas ya kasa
cewa komai.
Zuhura tayi murmushi a gare shi, sannan ta yi
wuf ta tsugunar da shi kasa, takobin abokin gaba ta
wuce ta saman kansa. Kafin ya yi wani yunkuri ta
soke abokin gabar da takobin ta, ya sulale kasa.
7
Taskar Tsafi-3 Abdul'aziz S. M/Gini
A lokacin ne kuma wasu abokan gabar suka yo ca! a kansu, aka ci gaba da dauki ba dadi.
A bangaren sarauniya Abidatul Azmal da
Sarki Maharaz kuwa, al'amarin yafi gaban kwatance, domin wannan karon masifaffen yakin da suke yi ya ninka wanda suka yi a farko gamuwar su sau dari.
Saboda bala'i, sai da suka bar kusa da birnin suka koma can gefe daya suna faffatawa, suna yaki irin na su na manyan sadaukai.
Lokacin da gumurzu yai gumurzu, ya zamana gaba daya makaman Maharaz da na Abidatul Azmal
sun lallace, sun kakkarye, sai suka ajiye batun tsafi da addu'a, suka kaure da matsanaicin sabon fada,
suna naushi da bugun juna hannu da kafa.
Wohoho! Hakika duk wanda bai ga wannan turnukun ba ya yi asarar kallo, domin a wannan fada ne mutum zai tabbatar da cewa sadaukantaka baiwa ce. Babu abin da zai baiwa mutum mamaki
face irin yadda karfinjaruman biyu ya zo daya. Hatta juriya, bajinta, da kwarewar ma duk iri daya ne. Duk wanda ya sami nasarar naushin wani, kafin ya ankara dayan ya rama naushinsa. Sai da suka sake shafe sa'a uku suna laftar juna, sannan suka rabu da kansu, kawai sai suka fara ja da baya-baya. Sai da suka yi nisa da juna, kimanin taku arba'in a tsakanin su, sanan suka sake
8
Taskar Tsafi-3 Abdul'aziz S. M/Gini
rugowa ga juna, kowannensu zuciyarsa cike da
mugun nufi. Koda ya rage saura taku goma kacal su hadu, sai duk suka daka tsalle a lokaci guda, suka hadu a sama suka yiwa juna gware da ka, fuskokinsu suka manne. Al'amarin da ya janyo
kowannensu ya fita daga hayyacinsa, suka fado
kasa a sume, kowannesu jini na zuba a hancinsa.
Nan fa suka baje a kas kamar matattu. Bayan
dan lokaci sai iska ta kada, Abidatul Azmal ta fara
farkawa. Koda ta bude idanunta ta ga Maharaz a
kwance, sai tayi murmushin farin ciki. Nan take tayi
tsafi, wata takobi ta bayyana a hannunta, kawai sai
taje kan Maharaz ta tsaya, sannan ta daga takobin
sama da nufin ta caka masa a kirji. Amma sai ta
tsay kyam ta kasa.
A dai-dai lokacin ne Maharaz ya farka. Koda
ya bude idanunsa ya ga Abidatul Azmal tsaye
akansa rike da takobi ta kasa caka masa, sai ya cika
da tsananin mamaki. Tsawon 'yan dakiku suka
kurawa juna ido, sannan ya ce, "Me ya sa kika kasa
kasheni, alhali kin sami babbar dama?".
Abidatul Azmal ta yi ajiyar numfashi, sannan
ta ce, "Kai kadaine sa'an fada na, idan na kasheka
da wa zan yi? Rayuwa in ba makiyi babu abokan
gaba ai ba dadi!".
Sa'adda Maharaz yaji wannan batu, sai yayi
murmushi, ya yi mata kallo mai nuna rashin yarda
9
Taskar Tsafi-3 Abdul'aziz S. M/Gini
ya ce, "Kunne yaji abin da kika fada, amma zuciya
ba ta gamsu ba. Kiyi sani cewa ni da ke babu abin
da zai tsai da gabar mu face fitar ruhin numfashi,
domin har abada babu sulhu tsakanin wuta da
ruwa".
Abidatul Azmal ta yi murmushi ta ce, "Kwarai
kuwa. Amma na tabbata cewa bayan na yi wannan
yaki gabarmu ta kare".
"Idan kika ga gabar mu ta kare, sai idan kin
daina tsafi, ki karbi addinin gaskiya, in kuwa ba
haka ba, to ki tabbata cewa bana numfashi a doron
Kasa, shine kadai dalilin da zai sa ki ci birnin Nurul
Kalbi da yaki".
Kafin Maharaz ya gama rufe bakinsa, tuni
Abidatul Azmal ta kawo masa wawar suka a ciki da
wannan takobin tsafin.
Cikin tsananin zafin nama ya goce, amma duk da
haka sai da takobin ta huda rigar jikinsa. Maharaz
ya yi wata irin katantanwa kamar an murza mazari,
ya doki hannun Abidatul Azmal mai rike da
takobin. Take takobin ta yi sama, taje ta tsire kanta
a can saman wata bishiya mai tsawon gaske.
Nan fa suka ci gaba da sabon turnuku da
ruguntsumi.
A can birnin Nurul Kalbi kuwa, masifa ta kai
masifa, domin suma dakarun Musulunci an fara yi
musu barna, domin an kashe sama da mutum dari
10
Taskar Tsafi-3 Abdul'aziz S. M/Gini
biyar, saboda azababben nacin aljanun da dodannin,
wanda ya hadda sa rudewar wasu dakarun suka kasa
ci gaba da yin addu'a.
A wannan lokaci kuwa, Hasilatul Kurbas,
yarima Himal, gimbiya Zuhura, da sadauki Kurbas,
sun tsare bakin kofar nan inda za'a shiga a riski
mata, tsofaffi, da kananan yara, sai dauki ba dadi
ake yi da su a wajen.
Dakarun Abidatul Azmal sun ci gaba da
nacewa akan sai sun balla kogar sun shiga wannan
gida na karkashin kasa, su kuma su Kurbas suka
hanasu, aka ci gaba da cinikin rayuka a wajen.
Haka dai aka ci gaba da wannan bala'i, har
tsawon kwana da yini. Ba ma mutane ba, su kansu
aljanu da dodannin da basa gajiya, sai da suka kagu
a tsaida wannan yaki, saboda ganin yadda ake kaşhe
'yan uwansu tamkar ana zubo ruwan gawa daga
sama.
Su kuwa Dakarunun Musulunci, kishirwa da
yunwa ce ta fara galabaitar da su.
A 6angaren manyan zakuna kuwa, wato
gimbiya Abidatul Azmal da sarki Maharaz,
al'amarin ya wucea gaban kwatance, domin sai da
suka sake suma har sau biyu, wato ya zamo kenan
sun suma sau uku.
Yayin da Abidatul Azmal ta farfado a karo na
ukun, sai tayi tsafi, wani kaho ya baiyana a
11

Comments

Please log in to leave a comment

Login here