An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
SKAR TSAL
ALLIRL
MAjej
MUHD
tag
Not for stic
ABDUL'AZIZ SANI M/GIN
Taskar Tsafi-3 Abdul'aziz S. M/Gini
TASKAR TSAFI-3
Lokacin da aka ruguntsume da azababben
yaki tsakanin tawagar gimbiya Abidatul
Azmal da mutanen birnin Nurul Kalbi, sai dakarun
Abidatul Azmal suka lulluße garin gaba daya,
tamkar kudan zuma akan kwason da ya sa zubi. Nan
fa aka ci gaba da fafatawa, inda aljanu, dodanni, da
dakaru marasa adadi suka yiwa mutane kalilan
rubdugu. Amma saboda karfin addu'a, sai gashi
kalilan mutane na taka muhimmiyar rawa. In banda
Karar karafa, ihun mazaje, da kururuwar aljanu babu
al in da mutum ke ji a wajen. Idan Musulrni ya sari
kafirin aljani da, takobinsa, sai ka ga aljanin ya
kama da wuta ya kone kurmus. Haka kuma idan
suka sarki dodo ko mutum, sai ka ga ya darc biyu.
Ana cikin wannan ruguntsumin fadane
gimbiya Abidatul Azmal ta hango Himal, sadaiki
Kurbas, da Hasilatul Kurbas suna ragargazar
jama'ar ta. Nan takoe ta fusata, ta bayyana a
tsakiyar su, ta afka musu da sara da suka. Su ukun
suka rufar mata, amma sai ta zame musu annoba.
Abidatul Azmal ta sami nasarar kaftawa
kowanne su sara da dai-dai, ta zub da su kasa,
kowannen su na murkusus a kasa ya kasa motsi.
Abidatul Azmal ta tsaya akansu tana murmushin
mugunya. A wannan lokaci sarki Maharaz na can
3
Taskar Ts
tsakiyar abokan gaba sun lullube shi yana ta
ragargazar su.
Abidatul Azmal ta dubi su sadauki Kurbas
daya bayan daya, ta bushe da dariya, sannan ta ce,
"Ashe har kuna tsammanin zaku iya bijire mini ne,
kuma ku tsira daga sharrina? Kun yi kuskure babba,
kuma yanzun nan zan zare muku ruhin numfashin
ku".
Koda gama fadin haka, sai ta yunkura da nufin
ta sare musu kawuna. Kawai sai taji an tari
takobinta da wata. Ba kowane ya kawo wannan
agaji ba face sarki Maharaz.
Nan fa suka fara mugun artabu shi da iya cikin
tsananin zafin nama, juriya, bajinta, da kwarewa.
Duk su biyun suka wanzu suna kaiwa juna sara da
suka tamkar jikinsu na karfe ne ba na jini da tsoka
ba.
A wannan lokacin ne su sadauki Kurbas suka
sami kwarin gwiwa suka mike tsaye suka ci gaba da
yaki.
Sai da aka sami sa'a tara ana wannan yaki.
Amma mutanen Abidatul Azmal ba su sami nasarar
balla katuwar kofar da za su shiga inda aka bоуе
yara da mata da tsofaffi ba.
Haka kuma mutanen birnin Nurul Kalbi sun
kasa karar da koda kaso daya daga goma na
dakarun Abidatul Azmal, gashi kuma kowanne
4
Taskar Tsafi-3 Abdul'aziz S. M/Gini
bangarc sun fara gajiya. Amma aljanun da dodannin
ko kadan babu alamar gajiya a tare da su.
Yayin da aljani Marwanul Hasanu ke taka
muhimmiyár rawa a wannan yakj. Sai ya fuskanci
cewa jama'ar sarki Maharaz na cikin mugun hali,
domin kuwa idan aka sake samun sa'a uku ana
wannan gumurzu za su iya gajiya a cisu da yaki, tun
da su aljanun da dodannin basa gajiya. Kuma gashi
kashe su ake ta yi, amma kamar dada karuwa suke.
Nan take Marwanul Hasanu ya sulale ya gudu daga
wannan filin yaki, ya nufi wani babbar birni na
jama'ar aljanu ma'abota addinin Musulunci, wanda
ake kira Baitul Asmar. Daga birnin Nurul Kalbi
zuwa birnin Baitul Asmar tafiya ce ta kwana biyar,
amma sai Marwanul Hasanu ya dage iya karfinsa,
ya dinga tsala hudu yana mi kada fuka-fukansa da
sauri, domin ya isa wannan birni a cikin kwanakin
da ba su haura uku ba.
Burin sa shi ne a kawowa su sarki Maharaz
dauki kafin a ci karfin su.
***
A can birnin Nurul Kalbi kuwa, yaki ya kara
tsamari ainun. Musamman kaurewar Abidatul
Azmal da sarki Maharaz, wadda ta haddasa
rugujewar gine-gine da dama da kuma kamawar
5
Taskar Tsafi-3 Abdul'aziz S. M/Gini
wuta bisa tsananin karfinsu, da kuma amfani da
karfin sihirin da Abidatul Azmal ke yi.
Sai dai duk tsafin da take yi ya ki ya yi tasiri
akan sarki Maharaz, kasancewar shima yana ta
karanto addu'o'in neman tsari.
Ana cikin wannan dauki ba dadine daya daga
cikin dakarun Abidatul Azmal ya gano cewa an
boye mata da yara, da tsofaffi a cikin wani gida na
Karkashin Kasa. Koda gano haka, sai yaja tawagar aljanu suka durfafi kofar wajen, wacce ta kasance
Katuwar gaske ta bakin karfe.
Aljanun na zuwa bakin kofar, sai sadauki
Kurbas ya hangosu, kuma ya gane nufinsu. Ai kuwa
sai ya falfala da gudu izuwa wajen. Kafin ya karasa
ya daka tsalle ya dirga a gabansu ya hausu da sara. Suma suka rufar masa, amma sai gashi yana tarwatsa su suna konewa. Amma saboda naci, da
taurin zuciya, wasun su nė suka yi ta tattudowa. Sai da aka sami sa'a guda Kurbas na ta ragargazar aljanun nan. Shi kađai ya zame musu alakakai, ya hanasu 6alla wannan kofa.
Ana cikin haka ne wani shaidani ya ja wasu daga cikin aljanun suka kewayo ta bayan' Kurbas suka shammace shi suka sure shi izuwa sama, har takobinsa ta subuce daga hannunsa, kuma wani daga cikinsu ya watsa masa wata laka a baki ya kasa ci gaba da addu'a.
6
Taskar Tsafi-3 Abdul'aziz S. M/Gini
Koda ganin sun sami wannan nasara, sai wani
daga cikin su ya taso sama daga kasa rike da
takobin haske irin ta su ta tsafi, da nufin ya sare kan
sadauki Kurbas.
Ba zato ba tsammani, sia aka ga wata mace
wadda ta rufe duk jikinta, har da fuskarta ta rugo da
gudu rike da zabgegiyar takobi tana mai karanta
wadansu addu'o'i a bakinta. Kawai sai ta yi tsalle ta
dinga taka kan abokan gaba tana kara yin sama, har
ta riski wanda ke shirin hallaka sadauki Kurbas, ta
tsarga shi gida biyu, ya zama gawayi. Sannan ta
tarwatsa wadanda ke rike da Kurbas, duk suka
watse, sannan ta tallafo Kurbas a hannu kamar ta
riko karamin yaro, ta sauko kasa kamar tsuntsuwa
ta dira a hankali, ta dire Kurbas a kasa. A lokacin
Kurbas ya furzar da lakoar da ke bakinsa, ya dubi
wadda ta ceci rayuwar cikin tsananin mamaki, ya
ce, "Wace ce ke?".
Maimakon ta bashi amsa, sai ta yaye mayafin
da ke fuskarta, suka yi arba da juna. Ba wata bace
face gimbiya Zuhura, mahaifiyar sarki Maharaz.
Nan fa mamaki ya turnuke sadauki Kurbas ya kasa
cewa komai.
Zuhura tayi murmushi a gare shi, sannan ta yi
wuf ta tsugunar da shi kasa, takobin abokin gaba ta
wuce ta saman kansa. Kafin ya yi wani yunkuri ta
soke abokin gabar da takobin ta, ya sulale kasa.
7
Taskar Tsafi-3 Abdul'aziz S. M/Gini
A lokacin ne kuma wasu abokan gabar suka yo ca! a kansu, aka ci gaba da dauki ba dadi.
A bangaren sarauniya Abidatul Azmal da
Sarki Maharaz kuwa, al'amarin yafi gaban kwatance, domin wannan karon masifaffen yakin da suke yi ya ninka wanda suka yi a farko gamuwar su sau dari.
Saboda bala'i, sai da suka bar kusa da birnin suka koma can gefe daya suna faffatawa, suna yaki irin na su na manyan sadaukai.
Lokacin da gumurzu yai gumurzu, ya zamana gaba daya makaman Maharaz da na Abidatul Azmal
sun lallace, sun kakkarye, sai suka ajiye batun tsafi da addu'a, suka kaure da matsanaicin sabon fada,
suna naushi da bugun juna hannu da kafa.
Wohoho! Hakika duk wanda bai ga wannan turnukun ba ya yi asarar kallo, domin a wannan fada ne mutum zai tabbatar da cewa sadaukantaka baiwa ce. Babu abin da zai baiwa mutum mamaki
face irin yadda karfinjaruman biyu ya zo daya. Hatta juriya, bajinta, da kwarewar ma duk iri daya ne. Duk wanda ya sami nasarar naushin wani, kafin ya ankara dayan ya rama naushinsa. Sai da suka sake shafe sa'a uku suna laftar juna, sannan suka rabu da kansu, kawai sai suka fara ja da baya-baya. Sai da suka yi nisa da juna, kimanin taku arba'in a tsakanin su, sanan suka sake
8
Taskar Tsafi-3 Abdul'aziz S. M/Gini
rugowa ga juna, kowannensu zuciyarsa cike da
mugun nufi. Koda ya rage saura taku goma kacal su hadu, sai duk suka daka tsalle a lokaci guda, suka hadu a sama suka yiwa juna gware da ka, fuskokinsu suka manne. Al'amarin da ya janyo
kowannensu ya fita daga hayyacinsa, suka fado
kasa a sume, kowannesu jini na zuba a hancinsa.
Nan fa suka baje a kas kamar matattu. Bayan
dan lokaci sai iska ta kada, Abidatul Azmal ta fara
farkawa. Koda ta bude idanunta ta ga Maharaz a
kwance, sai tayi murmushin farin ciki. Nan take tayi
tsafi, wata takobi ta bayyana a hannunta, kawai sai
taje kan Maharaz ta tsaya, sannan ta daga takobin
sama da nufin ta caka masa a kirji. Amma sai ta
tsay kyam ta kasa.
A dai-dai lokacin ne Maharaz ya farka. Koda
ya bude idanunsa ya ga Abidatul Azmal tsaye
akansa rike da takobi ta kasa caka masa, sai ya cika
da tsananin mamaki. Tsawon 'yan dakiku suka
kurawa juna ido, sannan ya ce, "Me ya sa kika kasa
kasheni, alhali kin sami babbar dama?".
Abidatul Azmal ta yi ajiyar numfashi, sannan
ta ce, "Kai kadaine sa'an fada na, idan na kasheka
da wa zan yi? Rayuwa in ba makiyi babu abokan
gaba ai ba dadi!".
Sa'adda Maharaz yaji wannan batu, sai yayi
murmushi, ya yi mata kallo mai nuna rashin yarda
9
Taskar Tsafi-3 Abdul'aziz S. M/Gini
ya ce, "Kunne yaji abin da kika fada, amma zuciya
ba ta gamsu ba. Kiyi sani cewa ni da ke babu abin
da zai tsai da gabar mu face fitar ruhin numfashi,
domin har abada babu sulhu tsakanin wuta da
ruwa".
Abidatul Azmal ta yi murmushi ta ce, "Kwarai
kuwa. Amma na tabbata cewa bayan na yi wannan
yaki gabarmu ta kare".
"Idan kika ga gabar mu ta kare, sai idan kin
daina tsafi, ki karbi addinin gaskiya, in kuwa ba
haka ba, to ki tabbata cewa bana numfashi a doron
Kasa, shine kadai dalilin da zai sa ki ci birnin Nurul
Kalbi da yaki".
Kafin Maharaz ya gama rufe bakinsa, tuni
Abidatul Azmal ta kawo masa wawar suka a ciki da
wannan takobin tsafin.
Cikin tsananin zafin nama ya goce, amma duk da
haka sai da takobin ta huda rigar jikinsa. Maharaz
ya yi wata irin katantanwa kamar an murza mazari,
ya doki hannun Abidatul Azmal mai rike da
takobin. Take takobin ta yi sama, taje ta tsire kanta
a can saman wata bishiya mai tsawon gaske.
Nan fa suka ci gaba da sabon turnuku da
ruguntsumi.
A can birnin Nurul Kalbi kuwa, masifa ta kai
masifa, domin suma dakarun Musulunci an fara yi
musu barna, domin an kashe sama da mutum dari
10
Taskar Tsafi-3 Abdul'aziz S. M/Gini
biyar, saboda azababben nacin aljanun da dodannin,
wanda ya hadda sa rudewar wasu dakarun suka kasa
ci gaba da yin addu'a.
A wannan lokaci kuwa, Hasilatul Kurbas,
yarima Himal, gimbiya Zuhura, da sadauki Kurbas,
sun tsare bakin kofar nan inda za'a shiga a riski
mata, tsofaffi, da kananan yara, sai dauki ba dadi
ake yi da su a wajen.
Dakarun Abidatul Azmal sun ci gaba da
nacewa akan sai sun balla kogar sun shiga wannan
gida na karkashin kasa, su kuma su Kurbas suka
hanasu, aka ci gaba da cinikin rayuka a wajen.
Haka dai aka ci gaba da wannan bala'i, har
tsawon kwana da yini. Ba ma mutane ba, su kansu
aljanu da dodannin da basa gajiya, sai da suka kagu
a tsaida wannan yaki, saboda ganin yadda ake kaşhe
'yan uwansu tamkar ana zubo ruwan gawa daga
sama.
Su kuwa Dakarunun Musulunci, kishirwa da
yunwa ce ta fara galabaitar da su.
A 6angaren manyan zakuna kuwa, wato
gimbiya Abidatul Azmal da sarki Maharaz,
al'amarin ya wucea gaban kwatance, domin sai da
suka sake suma har sau biyu, wato ya zamo kenan
sun suma sau uku.
Yayin da Abidatul Azmal ta farfado a karo na
ukun, sai tayi tsafi, wani kaho ya baiyana a
11
Taskar Tsafi-3 Abdul'aziz S. M/Gini
hannunta. Take ta busa kahon, sautinsa ya cika
dodon kunen komai. Hatta halittar da ke nesa da
birnin Nurul Kalbi kimanin tafiyar sa'a goma sai da
ta jiyo sautin kahon.
Ana cikin tsakiyar yaki, sa Dakarun Abidatul
Azmal suka jiyo sautin wannan kaho. Kawai sai duk
suka daina yakin suka dinga tashi sama suna barin
wajen yaki. Kafin kiftawar ido sun yi dandazo a
can gaban Abidatul Azmal sun kewayeta a tsakiya
ita da sarki Maharaz tamkar tsibiri a tsakiyar teku.
A wannan lokaci sarki Maharaz ya farfado.
Koda ya ga kansa a tsakiyar dumbin Dakarun
gimbiya Abidatul Azmal, sai ya mike zumbur, yayi
tsayuwa irin ta jaruman gaske ba tare da wata
alama ta tsorata ba.
Abidatul Azmal ta sa hannu ta share jinin da
ke diga a hancinta, sannan ta dubi Maharaz cikin
murmushi ta ce, "Gaishe ka namijin duniya, sarkin
sadaukai. Ka yi şani cewa babu wanda zai yake ka
anan, kuma kada kayi mamakin ganin dukkanin
mayakana anan, ni ce na tsaida wannan yaki izuwa
wani dan lokaci kadan, domin damu da ku, kowa ya
sami lokacin hutu da kuma. sake tattaunawa da
mayakansa bisa shawarar samun nasara".
Gama fadin haka ke da wuya, sai tayi nuni da
hannunta izuwa ga bayan Maharaz, take dakarun
suka da re gaba daya suka ba da hanya. Abidatul
12
Taskar Tsafi-3 Abdul'aziz S. M/Gini
Azmal ta nuna hanyar ga Maharaz ta ce, "Ka tafi
izuwa jama'ar ka, na baka kwana daya, ku sakc
sabuwar damara, domin duk abin da aka yi yanzu
share fage ne"
Maharaz ya maida mata martanin murmushi ya
cc, "Ko zamu shckara muna wannan yaki ba za ki
sami nasara akan mu ba, domin mun kasance haske,
ku kuwa duhu ne. Lallai ko yaushe gaskiya na bisa
karya, ina tabbatar miki da ccwa Ubangijin mu ba
zai bari muji kunya ba albarkacin Manzon Allah
(S.A.W.), wanda'yai duniya da lahira dominsa".
Yana gama fadin hakan yabi ta tsakiyar
Dakarun ya kama tafiya. Sai da yai sa'a biyu yana
tafiya a cikin su, sannan kuma ya sakc yin sa'a
guda yana tafiyar, ya isa kofar birnin Nurul Kalbi.
Tun daga nesa ya hango hayaki tsibi-tsibi na
tashi, sakamakon wutar da aka karkashc.
Gawarwaki kuwa, gasu nan birjik kamar an watsa
tsakuwoyi a sahara. Nan fa ya fara jiyo kukan mata
da yara kanana, wadanda suka rasa danginsu a
wannan yaki. Al'amarin da ya karya zuciyar Sarki
Maharaz kc nan, tausayi ya dabaibaye zuciyarsa.
Haka dai ya ci gaba da wuce gawarwaki har ya
iso tsakiyar gari, inda ya iske gaba ſaya Dakarunsa
a tsaitsayc sun yi cirko-cirko, a gefe daya kuma
sadauki Kurbas, yarima Himal, Hasilätul Kurbas, da
13
Taskar Tsafi-3 Abdul'aziz S M/Gini
gimbiya Zuhura nc a tsayc, kowannen su jikinsa ya
rune da jini.
Cikin tsananin mamaki Maharaz ya karaso
gaban gimbiya Zuhura, ya kama hannunta ya jata
gefe guda, inda babu mai jin abin da zai fada, sanna
ya dubeta ta ce,"Ya ke Ummi na, shin ba kin cc ba
za ki sake yin yaki ba a rayuwar ki? Wane dali ne
ya sa yanzu kika sauya shawara?".
Yayin da Zuhura taji wannan tambaya, sai tayi
ajiyar zuciya, ta ce, "Ya kai dana, ka sani cewa
tunda aka kafa birnin nan namu bamu taba ganin
tashin hankali ba irin na yau. A yau na gha mayaka
masu tsananin yawan da suka ninka Dakarun mua
sau ba adadi. Na ga yadda 'yan uwana Musulmi ke
ta yin shahada. Ba zan iya zuba ido ba kawai ina
kallon wannan bala'i, dolc ne na bada gudunmawata
ko dan saboda ma na samu rabon shahada a cikin
wannan gagarumin yaki."
Lokacin da gimbiya Zuhura ke wannan
magana da dan sarki Maharaz, shi kuwa sadauki
Kurbas ya Kurawa Zuhura idanu kawai yana mai
tunani da mamakin dalilin da ya sa ta sai da rayuwar
ta ta cete tasa. Haka kuma kyawunta ya kara jefashi
cikin kogin begenta da kaunarta.
Bayan Maharaz ya gama jin hujjar Zuhura ta
wannan yaki, sai ya baro inda Zuhura ke tsayc уа
laho gaban Dakarunsa, ya hau kan mumbari, sai
14
Taskar Tsafi-3 Abdul'aziz S. M/Gini
suka yi ta matsowa gaba, har sai da aka taru a wajc
guda, gaba daya mutanen birnin, kuma aka yi tsit
kamar mutuwa ta gifta.
Sarki Maharaz yai gyaran murya ya ce, "Ya ku
'yan uwana, ku yi sani cewa ba a gama wannan yaki
ba, yanzu ne ma aka fara shi. Ina ma kira a garemu
da mu sallama al'amarin mu ga Allah, madaukakin
sarki, wanda shi ne masanin yau da gobc. Kada mu
yarda muji tsoron kafirai, saboda a yawansu da
yawan makamansu, ko kuma saboda karfin
sihirinsu. Lallai wanda ya yarda da Allah ya mika
wuyansa garc shi, Allah na tare da shi.
Da wannan furuci nake sallamar kowa domin muje
mu binne 'yan uwanmu wadanda suka yi shahada.
Bayan nan kuma ina kira ga dukkanin Malaman
Kasar nan da mayakanmu da su taru a fada domin
mu tattauna bisa hanyar da zamu bi mu sami nasara
a wannan gagarumin yaki".
Ba tarc da bata lokaci ba aka shiga dibar
gawarwaki, sannan aka binnc su, tare da yi musu
addu'a.
Bayan an kammala ne Malamai da Dakarun
yaki suka taru a fadar Sarki Maharaz..
Sa'adda Sarki Maharaz ya ga kowa ya hallara,
sai ya mike tsaye ya cc, "Ya ku madafar birnin
Nurul Kalbi, kuyi san cewa abokiyar gabarmu
gimbiya Abidatul Azmal ta tsaida wannan yaki ne
15
Taskar Tsafi-3 Abdul'aziz S. M/Gini
izuwa tsawon kwana daya rak domin kowanc
Bangare ya sami damar hutawa da yin shawara 6usa
tadda zai samu nasara. Yanzu a cikin ku wayc zai
bamu shawara mafi inganci bisa yadda zamu sami
nasarar wannan yaki?".
Koda jin wannan tambaya, sai kow ayai shiru,
aka rasa wanda zai cc wani abu, har izuwa tsawon
lokaci. Ba zato ba tsammani sai aka ga kofa ta
bude, gimbiya Zuhura ta shigo ratayc da takobin
mijinta marigayi sarki Makawi, kuma ta sha lullubo.
Zuhura ta wucc taje har inda sarki Maharaz ke
tsayc ta tsaya kusa da shi, sannan ta yayc mayafinta,
sai ga kwalla a cikin idanunta. A lokacin ne ta hada
idanu da sadauki Kurbas, ta saki tattausan
murmushi a garcshi, wanda ya jefashi a cikin
dimauya da rudewa har yaji kamar ya fashe da
dariya dan murna, amma sai ya kannc.
Zuhura ta matso hawayc daga idanunya,
sannan ta sa hannu ta share shi, ta cc, "Ya kai dirkar
birnin Nurul Kalbi, kayi sani cewa a yau ni gimbiya Zuhura, ina zub da hawaye saboda tunowa da namijin duniya, wato maigidana, kuma mahaifin sarkin ku.
Idan baku manta ba, har sarki Makawi ya bar duniya ba'a taba cin kasarsa da yaki ba.
Wannan takobi da ke ratayc a kafadata, ita cе takobin da Sarki Makawi ya yi yake-yakensa da ita.
16
Taskar Tsafi-3 Abdul'aziz S. M/Gini
Ni matarsa zan danka wannan takobi ga wanda ya
cancanta ya mallaketa."
Tana gama fadin haka, ta juya ta mikawa sarki
Maharaz. Cikin sanyin jiki Maharaz ya karbi
takobin, sa'adda hawaye ya subuce masa, sannan ya
rataya takobin a kadadarsa.
Zuhura ta dube shi ta cc "Da ikon Allah
wannan takobi za ta zamo sanadin nasarar mu а
wannan yaki.
Ya kai dana, a iya kwarewata da sanin tuggun
yaki, shawarar da zan bayar guda daya cc. Lallai a
bude kofar nan ta can bayan gari a sirrancc,
dukkanin matayen mu, yara da tsofaffi su fita ta
cikinta su bar cikin birnin nan a daren yau, dimin
idan abokan gaba suka dawo mana bala'in da za 'ayi
sai ya ninka wanda aka yi a baya. Ina tabbatar muku
da ccwa duk ginin da ke tsayc a birnin nan sai yajc
kasa, kuma sai an kone komai namu ya zama toka.
Mu tura mutanen mu izuwa can birnin Nurul Salam,
in ya zo mu bar mayakan mu zalla anan aci gaba da
fafatawa.
Kun snai cewa birnin Nurul salam ya kasance
hada ka ta Musulmai da kafirai, duk da cewar suna
zaman amana da juna ba za'a rasa wakilan gimbiya
Abidatul Azmal ba, dan haka ina mai da ba shawa
rar idan matan mu, tsofaffin mu, da yaranmu za su
17
Taskar Tsafi-3 Abdul'aziz S. M/Gini
tafi can din, a hadasu da wadansu manyan Dakarun
mu su yi musu rakiya".
Koda gimbiya Zuhura ta zo nan a zancen ta,
sai gaba daya Malaman goma suka yi kabbara,
kuma aka yaba da wannan shawara ta ta,
Nann fa aka fara tunanin jaruman da ya
kamataa zaba su yiwa makaskantar rakiya izuwa
birnin Nurul Salam, sai gardama ta karke. A Karshe
sai gimbiya Zuhura ta ce, "Babu wadanda suka dace
da yin wannan rakiya fa ce ni da sadauki Kurbas.
Dalilina anan shi ne, mu kadai ne shekarun mu suka
fi na sauran sadaukan mu, su kuwa sauran sadaukan
sun fimu karfi da kuruciya, su ya kamata su tsaya
suyi babban yakin".
Yayin da manyan Malamai goma suka ji
wannan shawara ta biyu, sai suka sake yin na'am da
ita.
Nan takc aka bada umarnin aje a fara shirycshiryc. Nan fa kowa ya watse daga fadar, aka bar
sarki Maharaz shi kadai a zaunc, inda ya shiga
sabon tunani. Kawai sai ya fara tunano abubuwan
da suka faru tsakaninsa da gimbiya Abidatul Azmal,
tun daga farkon haduwar su da ita, kawo i yanzu.
Sa'adda ya zo kan lokacin da ta sami damar
kashc shi, amma taki, sai ya dada cika da mamaki,
yana mai tambayar kansa cikin zuciya, ya c, "Wai
shin mene ne dalilin da ya sa Abidatul Azmal taki
Taskar Tsafi-3 Abdul'aziz S. M/Gini
kashe ni, alhali ta sami dama, kuma na kasance
babban makiyinta a duniya?".
Maharaz ya tunano da wani lokaci, sa'adda
Abidatul Azmal ta yi masa wani irin kallo mai
tattare da alamun tambaya. Tabbas irin wannan
kallo baya rasa nasaba da kamuwa da kauna.
"Idan dai har Abidatul Azmal ta kamu da
kaunata, dan me take yakin neman rayuwata? Mе
zai hana ta daina tsafi ta karbi addinin Allah?"
Haka dai Maharaz yai ta tunani iri-iri, ya kasa
samun amsoshin tambayoyin da yakc yiwa kansa.
Wata zuciyar kuma sia ta ce da shi, "Hakika ya
kamata kayi aurc ya kai Maharaz. To amma fa babu
macen da ta dace da kai fa ce Abidatul Azmal.
Domin a fegen kyau sai dai kuyi kunnen doki. Haka
ma fagen jarumta da sadaukantaka.
Koda Maharaz ya zo nan a zancen zucinsa, sai
yaji zuciyarsa ta kamu da kaunar gimbiya Abidatul
Azmal. Nan takoe cikin fushi ya mike ya dakawa
kansa tsawa, ya ce, "Kai Maharaz, ka shiga hankalin
ka! batun soyayya babu shi a tsakaninka da
Abidatul Azmal har abada, babu sulhu tsakanin baki
da fari, domin duk wanda ya sami dama zai disashe
dayan ne.
Wannan shi nc abin da ya faru ga sarki
Maharaz bayan an gama shawara fadarsa bisa yadda
za'a bullowa wannan gagarumin yaki.
19
Al'amarin sadauki Kurbas da gimbiya Zuhura
kuwa, suna fitowa daga cikin fadar sarki Maharaz
suka yi ta shiga gida-gida suna fito da mata, tsofaffi,
da yara, tare da kayayyakinsu suna dora su akan
dawakai da kekunan doki.
Sai.da suka shafc sa'a shida suna wannan aiki,
sannan suka kammala. A lokacin ne Sarki Maharaz
da Hasilatul Kurbas suka zo garesu dan yin sallama
da su, wanda ta kasance tamkar bankwana, tun da
babu wanda ke da tabbacin zai sake saduwa da
wani.
Hasilatul Kurbas ta dubi mahaifinta sadauki
Kurbas tana kuka, ta cc, "Ya kai Abbana, kayi sani
ccwa yau ne karo na biyu da zan yi rabuwa da kai, irin waccc ba zan taba mantawa da ita ba.
Rabuwar farko ita ce ranar da aka daura min
aurc da mijina Himal, na bar gidanka. Yau kuma gashi zamu rabu bisa Jihadi, dan daukaka kalmar Allah. Wata Kila wannan rabuwa za ta zamo ta karshe a tsakanin mu. Idan har hakan ta faru, ina mai rokonka da ka gafarce ni bisa duk irin laifukan da nai maka na fili da na 6oye".
Koda jin wannan batu, sai hawayc ya zubowa sadauki Kurbas, ya ce, "Ya ke 'yata, ki yi sani ccwa baki taba yi mini laifi ba tun ma kina karamar ki
20
Taskar Tsafi-3 Abdul'aziz S. M/Gini
kawo izuwa yanzu. Idan ma kin yi mini ban sani
ba, to na yafe miki duniya da lahira.
Ina yi