Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 3
miki fatan cikawa dą imani, tare da samun sakamakon aljanna". Wannan kalami ne ya jefa karayar zuciya ga sarki Maharaz, har shma ya ruga ga gimbiya Zuhura. Duk su biyun suka kama kuka a lokaci guda. Nan takc suka yiwa juna addu'o'in nasara, sannan suka yi bankwana suna ta zub da hawaye. Ba tare da 6ata lokaci ba aka bude kofar sirri ta bayan gari, sadauki Kurbas, gimbiya Zuhura da sauran makaskantan birnin gaba daya suka bi ta cikinta suka bar birnin Nurul Kalbi. Bayan kulewar su, Sarki Maharaz suka ci gaba da shiryc-shiryen yaki, aka yi ta fito da sabbin makamai, kuma aka fara kirkiro sabbin dabaru,w adanda suka hada da kera katuwar majaujawa mai cilla dutsen wuta, wanda idan aka jefashi kan makiya ya fashe zai haddasa gagarumar wuta. Haka dai mutancn Nurul Kalbi suka wanzu suna ta wannan aiki tambar ba za su daina ba. Rashin snai yafi darc duhu. Hakika in da su sarki Maharaz sun san irin shirin da su Abidatul Azmal ke yi da sun san cewa na su wasa ne. Domin abin yafi gaban kwakwalwar bil'adama. Da farko dai, a shawarar da suka yanke, akwai batun tabbatar da cewa an bajc birnin Nurul Kalbi Taskar Tsafi-3 Abdul'aziz S. M/Gini ya zamo babu wani gini a tsayc a cikinsa, sannan kuma dole ne a konc komai na cikinsa, ya zama toka a wannan karon, ko ta wanne hali. Aljanu suka ce lallai sunc da alhakin ruguje birnin. Su kuma dodanni suka ce sune za su konc shi. Su kuwa bil'adama suka ce sune da alhakin kashe dukkanin wani abu mai rai na cikinsa. Suka yi rantsuwa da cewa ba za su bar koda kiyashi guda daya ba. Koda gama yanke wannan shawara, sai aka shiga kcra sabbin muggan kayan yaki, inda aljanu suka dinga kwakule manyan duwatsu suna cusa makamashin wuta a ciki, tare da danyan mai. Su kuma dodanni suka kcra kiboyoyin wuya masu mugun yawa. Su kuwa bil'adama takubba, masu, da sauran makamai sukayi ta tanada. Sai da sa'a biyar ta shude ana wannan shiryeshirye cikin tsananin gaggawa da basira, sannan aka kammala. Bayan an gama sai farin ciki ya lullube gimibiya Abidatul Azmal. Ta dubi dakarunta gaba dayan su, ta ce, "Kowa ya zauna cikin shiri, lallai gobe da asuba za mu afkawa birnin Nurul Kalbi mu kawar da shi tamkar bai taba wanzuwa ba a doron Kasa." Wannan shi nc abin da ya faru dangane da kowannc bangarc na abokan gaba. 22 Task Abdul BZIZ S. M/GINI *** Al'amarin su sadauki Kurbas kuwa, lokacin da suka jagoranci tsofaffi, yaram da dukkanin matan birnin Nurul Kalbi, suka fita ta boyayyiyar kofa da ke bayan garin, sai suka ci gaba da tafiya a cikin daji ba sassautawa. Da yakc an basu karin dakaru dari, sai suka rabasu kaso uku. Kaso guda suka tsaya a farkon jama'ar. Kaso na biyu a tsakiyar su. Su kuma kaso na uku a can gabansu, dan tabbatar da tsaro. Sadauki Kurbas da gimbiya Zuhura kuwa, su ne akan gaba, kowannen su akan doki yana duban gaba da baya. Sai da suka shafe fiye da rabin daren suna tafiya, sannan suka fuskanci cewa jama'a fa sun gaji ainun. Tsawon wannan lokaci Zuhura da Kurbas basu yi magana da juna ba. Nan take Zuhura ta daga hannunta sama, alamar a tsaya. Ai kuwa sai Dakarun da ke kan gaba suka ja tunga. A sannan ne ya dubi sadauki Kurbas, ta ce, "Ya kai abal Hasilat, yanzu mene ne abin yi? Hakika idan muka ci gaba da wannan tafiya mutanen mu za su gaji su shiga mugun hali. Haka kuma idan muka tsaya anan har aka ci gaba da yaki a can birnin Nurul Kalbi abokan gaba za su iya 23 Taskar Tsafi-3 Abdul'aziz S. M/Gini gano ccwa bama can, dan haka za su iya biyo sahun mu su cimmana". Yayin da sadauki Kurbas ya ji wannan tambaya, sai yai shirus yana tunani. Daga can sai ya dago kai ya dubi gimbiya Zuhura ya cc, "Ya kc Ummul Maharaz, in dia haka ne, dole ne mu nemawa mutanen mu maboya mai kyau yadda koda abokan gabar mu sun biyo sahun mu ba za su gan mu ba". Zuhura ta ce, "Kwarai kuwa, hakika ka zo da shawara mai kyau". Nan take suka raba wasu dakaru su goma, suka ce su tafi neman kogon dutse mai zurfi da duhu, ko kuma babban rami, wanda ke cikin boyayyen sako. Nan yake dakarun suka bi umarni. Suma sai suka tafi laluben tare suka bar jama'ar a kar kashin tsaron sauran dakarun. Bayan kamar sa'a hudu, daf da gabatowar asuba, sai Kurbas da Zuhura suka gano wani tsohon kogon dutse a cikin wasu bishiyoyi masu duhuwas. Saboda duhun wajen, sai da suka kunna fitilar wuta,s annan suka iya haska hanya suka shiga cik. Abin takaici kuma shi ne, suna shiga cikin kogon sai suka ga ashe karamin kogo ne, wanda baifi mutum ashirin su shiga cikin sa ba. Ba zato kuma, sai suka ga wata tsohuwar rijiya a cikinsa, 24 Taskar Tsafi-3 Abdul'aziz S. M/Gini wadda aka rufeta da wani katon mummulallen murfi na karfe. Sadauki Kurbas ya sa hannaycnsa biyu da nufin ya daga murfin rijiyar ya janyc shi,amma sai yaji ya kasa. Al'amarin da ya matukar bashi mamaki kenan, domin da farko ya raina nauyin murfin, kuma ya sha daga wadanda suka fi wannan girma da nauyi. Dan haka sai ya dubi gimbiya Zuhura ya cc, ta kawo masa agaji. Nan fa suka hada karfi su biyun suka kama murfin dan su daga, amma sai yaki daguwa. Mamaki ya kara turnukc su su duka. suka dubi juna, kawai suka yi shiru suna tunani. Daga can sai Zuhura ta dubi Kurbas ta cc, "Muyi bisimillah, da izinin Allah zamu bude rijiyar nan". Ba tare da yin gardama ba, Kurbas ya bi umarninta, suka yi bisimillah a tarc. Ai kuwa suna gama karfi suka daga murfin cak, wanda duk jikinsa yana cc ya lullubc, suka ajiyc shi a gefc guda. Koda suka haska cikin rijiyar, sai suka ga ashe ma matattakala ce ciki. Nan takc suka kunna kai ciki, suna masu karanto addu'o'in neman tsari. Ai kuwa suna sauka karshcn matattakalar sai suka ga ashe wata katuwar fada ce a ciki ta wani boka, da gani ya dade da yin zamanin sa shckaru aru-aru da suka gabata. Babu komai a cikin fadar fa cc kayayyakin tsafc-tsafc. Girman fadar ya kai girman birnin Nurul 25 bdul'aziz S. M/Gini Kalbi. Nan fa Zuhura da Kurbas suka cika da mamakin ganin girman wannan waje da yadda aka gina shi a cikin karkashin kasa. Gaba daua abubuwan da ke cikin fadar sun kamc sun zama gunki, kuma yanah ta lullubc shi. Koda su Zuhura suka gama nazarin cikin fadar, suka tabbatar ccwa babu wani mugun abu a ciki, sai suka fita da sauri, suka je suka taho da dukkan sauran,jama'ar tasu, suka sake shiga cikin wannan rijiya. Da yake Zuhura da Kurbas ne suka shiga daga karshc, sai suka sake yin bisimillah suka janyo murfin rijiyar suka rufe ruf, tamkar ba'a taba budcwa ba. Nan fa gaba dayansu suka duru a cikin rijiyar, suka isa karshenta, suka bayyana a cikin wannan tsohuwar fada. Koda tsofaffi, yara, da mata suka tsinci kansu a cikin wannan wuri, sai suka shiga kalle-kale cikin ta'ajibi. Anan dai kowa ya sami wuri ya kwanta saboda gajiya. Cikin 'yan dakiku kadan jama'a suka kama barci. Kurbas da Zuhura nc kadai idanunsa kekashc sun kasa rintsawa. A lokacin suna zaune nesa kadan da juna, sai wannan ya kalli wannan kawai suna murmushi, an rasa wanda zai cc kala. 26 Taskar Tsafi-3 Abdul'aziz S. M/Gini Daga can sai Kurbas ya mike tsaye daga inda voke zaune. va je kusa da Zuhura ya zauna, sannan ya ce, "Ya kc wannan babba jaruma, wadda ta ceci rayuwata, ina mai gödiya garcki bisa sai da ranki da kika yi saboa ni". Koda jin wannan batu, sai Zuhura ta yi murmushi ta ce, "Babu bukata ka yi miní godiya, domin wajibi ne a gareni na ceto rayuwar babban mayakin addinin Allah. Ba karamar asara ba ce mu rasa irinka a cikin mu". Kurbas yayi murmushi, sannan ya ce, "Amma kuma naji danki ya cc kin yi alkawarin ccwa ba za ki sake yin yaki ba a rayuwa ki. Shin me yasa kuma kika yi yanzu?", Koda jin haka, sai Zuhura ta cika da tsananin mamaki, dan haka sai ta cc, "Ya aka yi kaji wannan zance, alhali a sirrance mu ka yi shi ni da dana?". Kurbas ya sake yin murmushi, sannan ya cс, Allah ya bani wata irin baiwa, wacce koda rada kayi a kusa dani ina iya jin abin da aka fada. Haka kuma idan mutum na tafiya ncsa daga inda na ke tsawon zura'i dubu, idan na aza kunne na akan Kasa ina iya jiyo sautin sahun tafiyarsa, kuma ina iya sanin lokacin da zai iya izuwa inda na ke". Koda gama fadin haka, sai Zuhura ta yi ajiyar zuciya, gami da kabbara, sannan ta ce, "Hakika Allah shi ne mabuwayi mai bayar da kyauta ga duk 27 Taskar 1safi-3 Abdul'aziz S. M/Gini wanda ya so. Tabbas kana daga cikin bayin Allah masu baiwa. a Ya kai wnanan sadauki, y sani cewa ba komai ne ya sa na ce na daina yaki ba, sai domin yaki ne na rasa babban masoyina, kuma mijina uban dana Maharaz sarki Makawi. A duk sa'adda na ga ana yaki sai hankalina ya dugunzuma na tuno da shi na yi ta kuka. Domin na san cewa na rasa wanda har abada babu mai maye min gurbinsa a zuciyata. Bisa wannan daliline na diana yaki, kuma na ke tsoron na ga yaki. Lokacin da yaki ya zo mana bakatantan, kuma na ga irin kokarin da kakc yi a yakin na kare Musulunci da Musulmai, sai na ga komai na ka irin na mijina nc. Hatta yadda ya kc rike takobinsa, da kuma salon yakinsa. Nan take naji sonka ya kwarara a zuciyata, har na ji na gamsu cewa za ka iya mayc mini gurbin tsohon mijina. Saboda haka ne na sallama rayuwata dan ccto taka, ina fatan zaka bani matsuguni a cikin zuciyarka?". Koda gimbiya Zuhura ta zo nan a zancenta, sai farin ciki ya turnukc Kurbas, ya cc, "Ya kc wannan sarauniyar kyawawan duniya, ki yi sani cewa ranar da na fara ganin ki na karyata kaina na tabbatar da ccwa matąta margayiya kyawunta kalilan ne daga cikin naki. Alhali a zamaninta babu wata mace man kyanta a garin mu. Ina ganin ki na ji gaba daa 28 Taskar Tsafi-3 Abdul'aziz S. M/Gini begen da na ke ma ta ya dawo kanki. Dan haka tun tuni kina da matsuguni a cikin zuciyata". Koda jin wannan batu, sai hawayen farin ciki ya zubowa gimbiya Zuhura, taji kamar ta rungume sadauiki Kurbas, amma sai ta kanne. Haka dai suka ci gaba da hirar soyayya cikin nishadi da nutsuwa har alfijir ya keto. Wannan shi ne abin da ya faru tsakanin gimbiya Zuhura da sadauki Kurbas bayan sun buya cikin fadar wani tsohon boka da ke karkashin kasa, wanda yai zamaninsa shekaru aru masu yawa. a *** Acan Nurul Kalbi kuwa, alfijir na ketowa sai aka ga sararin samaniya ta kece da ruwan duwatsun wuta. Nan fa duwatsun suka ringa fadowa kan ginin gidaje suna rushesu. Sannan kuma sai ruwan kibiyoyin wuta ya biyo bayansu. Kafin kiftawar ido duk wnai gini da ke tsaye ya baje kasa, kuma wuta ta kama ko ina, sai ci take ganga-ganga, tamkar an yi ambaliyar gobara. Allahu Akbar! A wannan lokaci sama da Musulmi dubu dari bakwai ne suka yi shahada. In ba dan su sarki Maharaz sun kwanta a kas ba, sun rufe jikinsu da garkuwoyi ba, da tuni sun halaka 49 Taskar Tsafi-3 Abdul aziz S. M/Gini gaba daya. Duk da hakan ma sai da wadansu daga cikinsu da yawa suka hallaka. Babbar dabarar da su Maharaz suka yi, ita ce, sai suka yi lam6o kamar sun mutu gaba daya. Saboda haka, bayan abokan gaba sun daina sako ruwan kibbau,sai suka sauko kasa cikin tsananin farin ciki, su duba gawarwakin da ke wajen, wacce ba ta mutu ba su karasa ta. Ai kuwa suna saukowa sai su Maharaz suka mike aka kaure da sabon azababben yaki. A lokacin ne gimbiya Abidatul Azmal ma ta sauko kasa. Koda ta hango sarki Maharaz yana karkade dakarunta tamkar mai sassabe a gona. Sai ta cilla kanta tamkar an harba kibiya daga cikin kwari, ta dirga a gabansa, ta tare shi suka fara masifaffen yaki. Nan fa wuri ya kara hautsinewa, in banda ihun maza, karar karafa, da karajin aljanu da dodanni babu abin da mutum ke ji. A wannan rana Hasilatul Kurbas da yarima Himal sun yi gagarumin aiki, domin duk inda suka sa gabansu sai dai ka ga kafirai na zubowa kasa, babu mai iya tsai da su. Suma sauran mayakan Musulmai sun yi rawar gani ainun, domin duk wanda ka duba sai ka ga zuciyarsa a tafarfashe taje, banda kisa babu abin da yake, saboda sun fusata sosai bisa ganin muguwar Garnar da aka yi musu, ta baje wannan babban birni 30 Taskar Tsafi -3 Abdul'aziz $. M/Gini da kone shi, da kuma asarar dumbin rayukan 'yan'uwansu. A Gangaren gimbiya Abidatul Azmal da sarki Maharaz kuwa, abin yafi gaban kwatance, domin a wannan karon babu abin da Abidatul Azmal ke kokarin yi masa face ta kama shi ta daure, domin a tunanin ta ta gama cin wannan yaki, tun da ta gama rushe birnin, kuima ta kashe da yawan dakarunsa. Abidatul Azmal ta yi ta jefawa Maharaz tarkuna irin su raga da kejin karfe na tsafi, domin ta kama shi, amma sai ya yi ta lalata su da takobinsa bisa taimakon addu'a da kuma tsagwaron-jarumtakarsa. Lokacin da aka sami sa'a uku a haka, ba ta sami nasarar kama shi ba, sai ta tabbatar da cewa lallai abin na yi ne, domin tsafi ba zai taba nasạra ba, sai dai ta yi amfani da tsagwaron karfin dantse. Nan take Abidatul Azmal ta yi jifa da duk makamanta na yaki, ta rugo kan Maharaz, shi ma sai ya yi watsi da na sa makaman ya tare ta, suka fara naushi da dukan juna cikin fusata, zafin nama da juriya. Nan fa al'amarin ya sauya, domin wannan karon kowannensu na wahala ainun. Nan da nan suka hadawa kan su jini da majina. Kai tun suna bugun juna a tsaye, har ma suka fadi kasa suna numfashi da haki, suka kasa motsi. Koda suka huta, sai suka sake kaurewa da sabon azababben fada. A can bangaren su jarumi Himal kuwa, suma ba su daina ragargazar arna ba. To amma fa da yake sarkin yawa yafi sarkin karfi, an dada kashe Musulmai sama da dubu dari hudu. Al'amarin da ya firgita su Hasilatul Kurbas kenan, suka tabbatar da cewa idan aka kara sa'a hudu nan gaba a haka za a iya Karar da dukkanin Musulman da ke taimaka musu, ya zama saura ita da yarima Himal kadai. Tabbas su biyu kacal ba za su iya ba da abokan gabar. Haka kuma sun hanga ko'ina ba su ga sarki Maharaz da gimbiya Abidatul Azmal ba. Al'amarin da ya dugunzuma hankalinsu kenan, suka rasa abin da ke musu dadi. Haka dai suka ci gaba da wannan yaki, zuciyoyinsu cike da fargaba. Ga shi a wannan lokaci rana ta fadi, gari ya soma duhu. 31 Daga can sai su Hasilatul Kurbas suka hangi Maharaz da Abidatul Azmal a can nesa da su kan wani katon dutse mai tsawo suna kwarmazuwa. Suna cikin fafan ne Abidatul Azmal ta yi duba izuwa sansanin yakin, ta ga sauran kiris jama'arta su gama da jama'ar sarki Maharaz, kuma nan take sai wani tunani ya fado mata a rai. Ta tambayi kanta a zuciya ta ce, 'Wai shin ina mata, yara, da tsofaffin garin nan ne? Tun da aka fara yakin nan ban ga an kashe koda daya daga cikin su ba? Lallai duk yadda aka yi an foye su ne a wani wurin. Wai shin ma ina sadauki Kurbas yake? Shi ma tun da aka fara yakin ban ganshi ba. Kai duk yadda aka yi akwai tuggun da mutanen nan suka shirya, ya zama wajibi na je 'na taimakawa mayakana mu karar da makiyan can namu, sannan na juya kan Maharaz na nemi sa'a akansa ta kowanne hali." Abidatul Azmal na gama wannan tunani, sai ta tashi sama kamar tsuntsuwa, ta tunkaro sansanin yakin, ta baro Maharaz akan wannan dutse. Koda Maharaz ya ga haka, sai ya gangaro kasa daka kan dutsen cikin azababben gudu, domin ya san cewa idan bai yi sauri ya riski Abidatul Azmal a can ba, za ta yi mummunar Garna. Wata kila ma ta sami nasarar hallaka Hasilatul Kurbas da mijinta Himal. Abin ka da wanda ke tafiya a sana, kafin Maharaz ya isa sansanin yakin tuni Abidatul Azmal ia riga shi. Ai kuwa tana dira ta fkawa Hasilatul Kurbas da yarima Himal, suka fara mugun artabu. Ko dakika sittin ba a yi ba, Abidatul Azmal ta yi wa Himal wani mugun duka da kafarta a fuskarsa. Saboda karfin dukan sai da ya yi tsalle sama, sannan ya fado kasa a sume jini na zuba a hancinsa da bakinsa. Al'amarin da ya fusata Hasilatul Kurbas kenan, ta rusa uban ihu ta afkawa Abidatul A/mal da dukkanin karfinta, cikin tsananin fusata. Kafin Abidatul Azmal ta ankara Hasilatul Kurbas ta yi tsalle a sama ta jera mata duka tara da kafarta a kirji. Duk da juriya da sadaukantaka irin ta Abidatul Azmal, sai da ta yi baya taga-taga ta fadi da baya. 32 Taskar Tsafi-3 _Abdul'aziz Hasilatul S. M/Gini Kurbas ta diro kasa za ta sake dukan kirjin maida Abidatul Hasilatul Azmal. Kurbas Ai kuwa sai Abidatul Azmal ta sa kafarta ta Kurbas ta baya da karfin duka. Take Hasilatul ya lali da gudu da baya ta gwaru da wani dutse, har kanta fusho, A jini ya yi tsarluwa, ila ma ta sulale kasa sumammiya. daidai wannan lokaci ne sarki Maharąz ya įso sansanin yakin. Himal, Koda ya ga abin da ya faru ga Hasilatul Kurbas da yarima sai ya fusata ainun, ya afkawa Abidatul Azmal suka cigaba da azababben yaki. Abidatul Azmal kuwa, sai ta dinga gudu daga gare shi tana yawo a sama kamar tsuntsuwa tana girbar kawunan Musulmai, Al'amarin da ya dugunzuma hankalin sarki Maharaz kenan, domin shi kafai ne ya rage mai iya tabuka wani abų daga cikin Musulmai, tun da Himal da Hasilatul Kurbas sun suma. Ba zato, ba tsammani sai aka ga wadansu halittu kamar tsuntsayc sun durfafo sansanin yakin daga can sama. Koda suka matso kusa, sai sarki Maharaz ya ga ashe aljani Marwanul Hasanu ne ya taho da gudunmawar wadansu Musulman aljanu dakarun yaki, ga su nan birjik ba adadi. Koda ganin wannan runduna, sai farin ciki ya mamaye sarki Maharaz.. Ita kuwa Abidatul Azmal da jama'arta, sai hankalinsu ya dugunzuına, domin sun san cewa sabon yaki ya same su. Kafin kiftawar ido su aljani Marwanul Hasanu sun sauko Kasa sun afkawa dakarun Abidatul Azmal. Nan fa guri ya hautsine, ihu da karaji da sararraki suka cika dodon kunne. A wannan lokaci ne sarki Maharaz ya sami damar zuwa inda Hasilatul Kurbas da Himal suke, ya yayyafa musu ruwa suka farfado. Duk su ukun suka sake mikewa suka ci gaba da yaki suna taimakawa aljani Marwanul Hasanu. Abidatul Azmal ta wanzu a tsakiyar Muslman aljanu tana ragargazar su da takobinta. Su kuwa suka kasa hallaka ta, amma kuma suna ta hallaka aljanunta da dodanninta. 33 Haka aka ci gaba da wannan azababben zazzafan matsanancin yakin mai tsanani, yakin mutuwa, yakin bala'i yakin masifa, har dare ya raba, gari ya sake wayewa. Abin ka da jiki mai jini da tsoka, sai Abidatul Azmal da su Maharaz suka jigata, suka kasa ci gaba da yakin, dole suka zama 'yan kallo. yakin ya zamo na aljanu da dodanni kawai. Koda ganin haka, sai Abidatul Azmal ta yi tsali ta bace bat tare da ragowar dakarunta na bil'adama tsiraru. Koda ganin haka, sai hankalin su sarki Maharaz ya tashi, domin sun San cewa Abidatul Azmal za ta iya bin sawun su sadauki Kurbas la hallaka su gaba daya. Nan take Maharaz, Hasilatul Kurbas yarima Himal, suka nemi dawakai suka hau suka nausa cikn daji a sukwane, suka tafi neman su sadauki Kurbas. Su kuwa aljanu da dodanni da sauran bil'adaman Musulmi, sai suka ci gaba da yaki. Koda aka jima ana yi, sai aka karar da duk bil'adaman, ya rage saura aljanu da dodanni. Nan la yaki ya zamo sabo tamkar sannan aka fara. Sai da aka kwana ashirin da tara ana wannan yaki, sannan aka gama shi. Ya zama su aljani Marwanul Hasanu sun sami nasarar kashe dukkannin dakarun Abidatul Azmal. Bayan sun sha muguwar wuya, musamman aljani Marwanul Hasanu. wanda shi ne yafi kowa sara da yanka kimanin dari bakwai da tamanin da biyar. A karslie shi ma faduwa ya yi kasa a sume, sai da aka yi ta yayyafa masa ruwa, sannan ya farfado. In ka ganshi sai ka yi tsammanin a kogin jini aka tsamo shi. Nan dai aka shiga yi masa magani don a ceto rayuwarsa. Wannan shi ne abin da ya faru a birnin Nurul Kalbi, bayan an fafata kazamin yaki irin wanda ko a tarihi ba a taba jin kamarsa ba a nahiyar gaba daya. *** Al'amarin Abidatul Azmal kuwa, lokacin da ta bace bat daga sansanin yakin tare da tsirarun dakarunta, ba su bayyana а ko'ina ba sai a dajin da ke can bayan birnin Nurul Kalbi. 34 Taskar Tsafi-3 Abdul'aziz S. M/Gini madubin Bayyanar su ke da wuya sai Abidatul Azmal ta dauko Kurbas ya tsafi bayyana ta shafe shi da hannu. Nan take hoton su sadauki Kalbi, tun a ciki, su da tsofaffi, yara da matan Nurul daga lokacin da suka baro cikin birnin izuwa lokacin hoton da suka shiga kogon dutsen nan. Suna shiga cikin kogon sai cikin ya daukc. Abidatul Azmal ta cigaba da kokarin ganin kogon, amma sai abu ya faskara. Koda ta matsa, sai madubin tsafin ya yi bíndiga ya farfashe. Al'amarin da ya dugunzuma hankalinta kenan, ta takarkare ta kwarara uban ihu cikin tsananin takaici da bakin ciki. Daga cai sai ta yi ajiyar zuciya, ta ce, "Lallai wafannan mutane suna nan a cikin kogon tsafin boka Auradul Azagab, bokan da ya yi zamanínsa shekaru dubu biyu da dari hudu da suka gabata. Tun daga lokacin da ya mutu kawo i yanzu ba a sami wani mahaluki da ya iya shiga cikin fadarsa ba da ke cikin kogon. Ku zo mu je can kogon mu riski su Kurbas a can mu hallaka su." Tana gama fadin haka ta sake yin tsafi suka bace bat, suka bayyana a bakin kogon dutsen. Nan fa kowa ya ja da baya, aka rasa wanda zai shiga ciki, sai da aka ga Abidatul Azmal ta shiga. Sannan wasu kalilan suka bi bayanta. Da shigar su sai suka ga babu kowa a ciki, kuma suka ga tsohuwar rijiyar nan wadda yana ta lullube murfinta a rufe, babu alamar an bude ta. Abidatul Azmal ta kurawa rijiyar idanu, sannan ta lumshe idanunta tana karanta wadansu kalmomin tsafi. Kamar a mafarki sai ta ga hoton lokacin da gimbiya Zuhura da sadauki Kurbas suka hada karfi suka bude murfin rijiyar bisa taimakon karanta Bisimillah. Sannan suka shiga cikin rijiyar tare da mata, yara da tsofaffi gaba daya. Koda ganin wannan al'amari, sai Abidatul Azmal ta fara jarraba kokarin bude murfin rijiyar da karfin sihirin tsafi, amma sam sai abu ya faskara. Nan da nan ta hada gumi, ta jike sharkaf. Yayin da ta Kara matsawa sai ta ji kamar ana kona ta da wuta, ba ta san sa'adda ta kwala ihu ba ta fadi kasa magashiyan kamar ta suma. Al'amarin da ya dugunzuma hankalin dakarunta da ke 35 wajen kenan, suka rasa abin yi. Bayan Abidatul Azmal ta dawo cikin hayyacinta, sai ta mike tsaye ta sake yin tsafi, takardu da alkaluma suka bayyana a hannunta, nan take ta rubuta gajeriyar wasika ta dorata akan murfin rijiyar. Sannan ta sake yin tsafi ta Bace 6at tare da dakarunta. Lokacin da suk sarki Maharaz suka baro birnin Nurul Kalbi bisa dawakai su uku, suka nusa cikin daji. Sai da suka kwana bakwai suna neman su sadauki Kurbas, amma ko duriyar su ba su gani ba. Al'amarin da ya tayar musu da hankali kenan, har suka fara zub da hawaye, domin suna ganin cewa an hallaka su gaba daya. Sarki Maharaz ya tuna da yadda aka ruguje birninsa aka kona shi gaba daya, sannan ya tuno da dumbin jama'arsa wadanda suka yi JIHADI a wannan yaki, kuma ya tuno, da mahaifiyarsa gimbiya Zuhura. Kawai sai ya fashe da kuka. Nan take tausayi ya kama Himal da Hasilatul Kurbas, suka shiga rarrashinsa, da.kyar dai suka lallashe shi, ya daina kuka. Sannan suka mike suka hau dawakansu suka cigaba da neman da ba su da tabbaci, domin sun gama karaya. Sai da suka shafe kwana tara a cikin daji suna neman su Kurbas, amma shiru babu alamunsu. A yammacin kwana na goma sha shida ne suka ga sawayen kafafun mutane izuwa cikin kogon boka Auradul Azagab. Cikin sauri suka sauka daga kan dawakansu suka ruga cikin kogon. Ai kuwa suna shiga sai sarki Maharaz ya yi arba da wasikar nan wacce Abidatul Azmal ta rubuta ta ajiye akan murfin rijiyar nan. Cikin hanzar Maharaz ya dauki wasikar ya ware ta, sannan ya fara karantawa kamar haka: "Sako a gare ka ya kai sadauki Kurbas, ka yi sani cewa ni gimbiya Abidatul Azmal ban san cewa kana cikin wannan rijiya tare da mata, yara da tsofaffin birnin Nurul Kalbi ba. Tabbas ba zan iya shigowa cikin wannan rijiya ba na riske ku. To amma ina yi maka tuni da cewa jikokinka guda biyu, wato 'ya'yan 'yarka Hasilatul Kurbas na tare da ni a can fadata. Idan har kana son rayuwar jikokinka lallai ka zo mini da 36 Taskar I safi -3 Abdul'aziz S. M'Gini dukkanin wana wannan jama'a da ke tare da kai. Na ba ka wa'adin talatin, idan ba ka zo ba zan kashe jikokin naka. Sarauniya Abidatul Azmal." Koda gama karanta wannan wasika, sai hankalin Hasilatul Kurbas da ma yarima Himal ya dugunzuma, suka fara kwalla. Nan dai suka hadu su ukun suka fara kokarin bude murfin rijiyar, amma sai suka kasa, sai da suka shafe sa'a uku a wajen suna ta yi dabaru iri-iri dan su bude rijiyar, amma babu nasara. Har sai da suka saduda suka zauna suka yi tagumi. Kowannensu ya yi zugum yana tunani. Daga can sai Maharaz ya mike tsaye ya nufi rijiyar cikin harzuka, sai kuwa su Himal suka bi shi da kallo kawai, suna mamakin abin đa yaké son yi, ålhali babu

Chapter 2 of 3