abin da ba a yi ba a baya, babu nasara. .
Koda Maharaz ya je kan rijiyar, sai ya yi Bismillah da karfi, ya sa hannu daya ya dauke murfin rijiyar cak, ya ajiye shi
gefe guda.. Koda ya leka cikin rijiyar, sai ya ga duhu. Sai ya
umarci su Hasilatul Kurba da su kunna fitilar ice. Cikin gaggawa
suka bi umarninsa. Ai kuwa suna haska cikin rijiyar, sai suka ga
ashe matattakala ce a ciki. Cikin sauri suka bi matattakalar suka
kunna kai ciki. Suna zuwa karshen matattakalar suka yi arba da
sadauki Kurbas da gimbiya Zuhura tsaye rike da takubbansu
cikin shirin kafsawa, dan suna zaton abokan gaba ne suka shigo
ciki.
Koda aka gane juna, sai farin ciki ya turnuke su gaba
daya. Maharaz ya ruga ga Zuhura mahailiyarsa ya rungume ta,
suna kukan murnar sake haduwa. Ita ma Hasilatul Kurbas sai ta
ruga wajen mahaifinta Kurbas, suka rungume junansu. Gaba
daya matan nan da yara da tsofaffi suka kama tsalle da murna,
saboda ganin su sarki Maharaz a raye.
Bayan kowa ya nutsu, sai Maharaz ya fiddo wannan
wasika wacce gimbiya Abidatul Azmal ta rubuta ya sake
karantawa a fili. Yana gama hankalin kowa ya sake dugunzuma.
Nan take hawayc ya zubowa sadauki Kurbas. Ya dubi Maharaz
ya ce "Ya kai sarki mai adalci, ka yi sani cewa akan rai biyu ba
37
za mu salwantar da rayukan dubunan jama'a ba. Tabbas a hakura da wadannan jikoki nawa, lallai bá zan bi umarnin sarauniya Abidatul Azmal ba." Koda jin haka sai Maharaz ya tako ya z
gaba Kurbas, ya dafa kafadarsa ya ce, "Ya kai wannan sadauki ka yi sani cewa, daidai da dakika guda ba za mu saurarawa sarauniya Abidatul Azmal ba. Lallai za mu je mata da wadannan jama'a da ta bukata, kuma da izinin Allah za'mu ceto rayuwar jikokinka, kuma sai mun ga bayanta." Cikin alamun shakka Kurbas ya ce, "Na san babu abin da zai gagari Allah, amma fa dole ne muma mu yi tunanin mafita." Maharaz ya ce, "Kar ka damu, abin da nake so da kai kawai ka yi duk abin da na ee."
***
Abidatul Azamal na zaune a fadarta tare dukkanin sarakunan Kasashenta. Sannan kuma ga dukkanin mayakanta wadanda suka yi saura, an kewaye ta ana sauraron abin da za ta ce, domin yau ne cikar wa'adi na talatin da ta bai wa sadauki Kurbas ya zo da jama'ar birnin Nurul Kalbi, ko kumata kashe jikokinsa. A bangaren hannunta na dama, sarki Asmarrne a zaune. A
hannun hagu kuwa, jikokin Kurbas ne a daure jikin kujera da sarkoki, sai kuka suke yi. Abidatul Azmal ta mike tsaye cikin Kasaita da izza, ta dubi gaba daya talakwan garin da ke gabanta ta ce, "Ya ku jama'ar birnin Kusa, ku yi sani cewa yau ne zan kashe wadannan yara, domin wa'adinsu ya cika, jininsu zaí zamo fansa ga jinin dukkanin mata, yara da tsofaffin birnin Nurul Kalbi. Mutanen da sune kadai suka bijire mini a cikin kasata, kuma na kasa kawar da su."
Abidatul Azmal na gama fadin haka sai ta dubi wani shirgegen bakin bawa wanda ke rike da zabgegiyar adda, ta ba shí umarnin ya je ya sare kan jikokin Kurbas. Nan take bakin bawa ya je kansu ya tsaya. ya daga addar sama da nufin sare kawunan yaran. sai aka ji magana da babbar murya daga bakin kofar shigowa fadar. ta ce, "A tsaya!"
Nan fa kowa ya waga ya dubi bakin Kofar, sai aka ga ashe sadauki Kurbas ne bisa doki yana jagorantar gaba dayan yara, mata
38
da tsofaffin birnin Nurul Kalbi. Koda ganinsa sai farin ciki ya Jullube Sarauniya Abidatul Azmal. Cikin gaggawa dakarunta suka zare makamai suka yiwa su Kurbas kawanya, a lokacin da suke ta shigowa cikin fadar. Sai da suka gama shigowa sannan Abidatul Azmal ta sauko daga kan karagarta ta zagaye su kaf tana nazarinsu, amma ba ta ga Sarki Maharaz ba a cikinsu. Kawai sai ta dubi Kurbas ta ce, "Ina su Maharaz?". Kurbas ya ce, "Ai ke zan tambaya inda suke, tun da a can Nurul Kalbi na baro su kuna
kafsawa." Koda jin haka sai ta kyalkyale da dariya, sannan ta murtuke fuska ta ce, "Ko ka fada mini inda suke ko kuma yanzun
nan na hallaka jikokinka, sannan na hallaka gaba daya...." Kafin
Abidatul Azmal ta gama rufe bakinta sai aka ga ginin saman fadar
ya kama tsattsagewa yana ruftowa kasa. Nan fa fadar ta rude,
jama'a suka kama ihu da guje-guje. Kafin su Abidatul Azmal su
ankara sai ga su aljani Marwanul Hasanu na ketowa ta cikin ginin
saman dauke da su Sarki Maharaz. Nan fa yaki ya turnuke aka fara
dauki ba dadi. Abidatul Azmal ta tari Maharaz suka hau fafatawa.
Shi kuwa Kurbas, Hafisatul Kurbas da gimbiya Zuhura sai suka
taimakawa su aljani Marwanul Hasanu aka ci gaba da ragargazar
arna. Yarima Himal kuwa sai ya ruga inda 'ya'yansa ke daure da
nufin ya kubutar da su. Kawai sai ya ga Sarki Asmaru ya sha
gabansa da takobi yana shirin afka masa. Himal ya dubi Asmaru
idanunsa cike da kwalla ya ce, "Ya kai Abbana yanzu kai ne kake
son ka hallakani da hannunka?" Asmaru ya bushe da dariya ya ce,
"Ya kai wawa, shashasha, Ka sani cewa na tsaneka kamar yadda
na tsani mutuwata, tun da baka son abin da ke so". Kafin Himal ya
kara cewa wani abu tuni Asmaru ya kai masa wawan sara. In ba
dan ya goce ba da tuni ya tsargashi gida biyu. Nan fa yaki ya ci
gaba da kai masa sara, shi kuwa ya yi ta kokarin karewa, amma ya
ki mai da martani, dan baya son ya kashe mahaifinsa da hannunsa.
Suna cikin wannan fadan ne Asmaru ya sami nasarar kaftawa
yi masa mummunan yanka. Himal ya Himal takobi a cinya, ya
kwala ihu ya fadi kasa magashiyan. A dai-dai wannan lokaci ne
mahaifiyar Himal, wato Lahura ta rugo da gudu cikin fadar tana
mai kwalawa Himal kira, gami da yi masa bushara ta ce, "Ya kai
39
Himal maza ka kashe Sarki Asmaru, domin ba shi ne mahaifinka
ba, shi ne dai wanda ya kashe mahaifin naka".
Koda jin wannan batu sai Himal yaji wani sabon karfi ya zo
masa, tamkar babu rauni a jikinsa. Nan take ya daka tsalle sama
rike da takobinsa. Kafin ya diro kasa ya fille kan Sarki Asmaru, sai
ga gangar jikin ta sulale kasa tana shure-shure. Al'amarin da ya
fusata Abidatul Azmal ke nan, ta kara kuntatawa Maharaz da
dukkanin karfin dantsenta, domin ta kai kan Himal, amma abu ya
gagara. A wannan rana dai, gaba daya sirrikan tsafin Abidatul
Azmal ba su yi tasiri ba, sabo da karfin addu'ar Musulmai.
Ammam fa duk da haka ta yiwa musulmai mummunar barna.
Kuma ita da Maharaz sai da suka suma sau biyar-biyar sabo da
bala'in fada. Duk me ran da ke cikin wannan fada a wannan rana
sai da ya zama gawa face Husilatul Kurbas, Kurbas, gimbiya
Zuhura, Izaima da Uhairu 'ya'yan Himal, Himal, Iahura, Sarki
Maharaz da kuma Abidatul Azmal. Ya yin da a karshe Abidatul
Azmal ta ga an kashe dukkanin jama'ar ta saura ita kadai sai ta yi
garkuwa da su Izaima. Bisa dole suka yarda makamansu. Abidatul
Azmal ta dubi gawarwakin jama'arta, ta dubi yadda aka lalata
karagar mulkinta, ta tuno da duk wahalar da ta sha a baya dan ta kawar da musulunci da musulmai, amma ta kasa, kawai sai ta fashe
da kuka. Ta dubi Maharaz ta ce, "Duk abin da zan yi nayi domin
na ga bayanku amma na kasa. To ku saurareni anan gaba zanje nayi wani sabon shirin wanda daga shi ba wani. Dole ne na ga bayanku". Koda gama fadin haka sai Abidatul Azmal ta doki kasa da kafarta ta shige izuwa cikin karkashin kasa tare da su Izaima suka bace bat. Nan fa hankalinsu Maharaz ya dugunzuma suka ma rasa abin da za su yi. WANNE IRIN SHIRI MAHARAZ ZAI YI DAN KARE KANSA DAGA MUGUN KUDURIN ABIDATUL AZMAL?
BURIN ABIDATUL AZMAI YANA CIKA NA GANIN
BAYAN SU MAHARAZ?
INA LAΒARIN SOΥΛΥΥAR SADAUKI KURBAS DA MAHAIFIYAR HAIMAN?
Mu hadu a littafi na hudu don jin karshen wannan labari. ABDUL'AZIZ SANI M/GINI.
40
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels