Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
TASTAR TSAFI 1

TASTAR TSAFI 1

by Abdulaziz Sani Madakin Gini ,

0 Hours
26, Jan 2026
Unknown group
Not Inserted
Free
52.79 kb
TXT
53+
35+
Last download 4 hours ago

You cannot download this book until you log in, but you can read it.

Read Now

OR

Description

kimanin shekaru dubu daya da dari K
daya kafin zamanin Sarki lamarudu
na birnin KUSA an yi wata
mashahuriyar sarauniya kuma babbar matsahfiya
j'yar ta'addanci mai suna ABIDATUL AZMAL.
Abidatul Azmal ta kasance kyakkyawar
buqurwa 'yar shckara ashirin da biyar kuma ta gají
sarauta ne da tsafi a wajen mahaifinta Sarki Azmal
bin Taufid wanda a zamaninsa babu wani sarki a
duniya mai karfin mayaka da karfin sihiri kamarsa.
Sai dja ya zamana gaba dayan sarakunan duniya da
matsafa na matukar tsoronsa.
A lokacin sarki Azmal bashi da wani buri
wanda ya fi ya mulki duniya gaba dayanta don haka
sai da ya-ci manyan kasashen duniya da yaki guda
dari bakwai da tamanin, wannan dalili ne ya sa
sarakuna da dama suka dinga gudu daga cikin
birancnsu suna buya a cikin dazuzzuka saboda idan
Sarki Azmal ya riskesu a cikin kasarsu yana yi
musu kisan gilla tarc da duk iyalansu. Sarki Azmal
na kan wannan sharafi nasa ne Allah ya jarrabeshi
daj wata irin cuta mai muni, ya zamana naman
jikinsa na rubewa da kadan-kadan, har sai da ya
zamo abin gudu ga dukkanin iyalansa da hadiman
sa domin kuwa jikinsa doyi yake, fuskarsa ma sai
da ta zagwanye ta yi muni abin firgitarwa, magani
3
Taskur Tsafi Abdul'aziz Sani M/Gini
babu irin wanda ba a yi ba amma a banza.
A gaba dayan iyalan Sarki Azmal Abidatu ce kadai ba ta gujeshi ba saboda tsananin kaunar da take masa amma mahaifiyar ta ma gudu ta yi ta bar shi sai da ya zamana darc da rana kullum Abidatu
na zaunc a gaban Sarki Azmal tana rusa kuka kuma ita cc ke yi masa komai.
Wata rana Abidatu na tare da Sarknal
tana dura madsa abinci a baki tana zub daaye kamar yadda ta saba kawai sai ta ga ya dubeta ya kama murmushi. Al'amarin da ya matukar ba ta mamaki kenan, ta share hawayenta ta ce "Ya kai Abbana ina dalilin wannan murmushi nake alhalin
yau watanka uku kcnan rabonka da yin murmushi? Sarki Azmal ya sake yin murmushi a garcta a karo
na biyu sannan ya bude baki da kyar ya cc "Ya ke 'yata ki yi sani ccwa ba komai ne ya sani wannan murmushi ba face na hango cewa ke ce za ki gajeni, lallai za ki yi shuhura a duniya kamar yadda na yi kuma za ki dade akan karagar mulki har ki tsufa har zuwa ajalinki. Hakika ke kadai cc ki ka nuna mini so da kauna fiyc da kowa tunda ba ki gujeni ba a
sa'adda kowa ya gujeni haka kuma ba ki kyamace ni ba a lokacin da kowa ya kyamace ni." Sarki Azmal ya daga hannunsa da kyar ya yi nuni izuwa wata bakar akwati sannan da Abidatu "Je ki ki dafa saman akwatin can da tafin
4
Tuskur Tvafl Abdul'azi: Sani M/Gint
hannunki."
Cikin sanyin jiki da rashin fahimta Abidatu
ta mike ta je ta dafa akwatin, ba zato ba tsammani
sai ta ga akwatin ta rikide ta zama kofar wani katon
kogo, mai duhün gaskc wata irin iska mai karfi na
fitowa daga ciki tana kokarin zukcta. Ta kc iskar ta
haddasa mikewar gashin kan Abidatu, rigar dake
jikinta kuwa ta dinga kadawa kamar za ta fita daga
jikinta, ba don Abidatu ta tokare kofar kogon da
kafafunta ba da hannayenta da tuni iskar ta zuketa
izuwa ciki.
Abidatu ta rusa ihu ta waigo ta dubi
mahaifinta fuskarta cike da tsoro ta ce "Ya kai
Abbana yanzu ba ka ceceni ba kana gani zan hallaka?"
Azmal ya ce "Ya ke 'yata ashe duk tsawon
zamana dake ba kı amince dani ba. Saki jikinki ki
kwantar da hankalınkı ki bari wannan iska ta zukeki
domin za ta kai ki ne inda za ki samu irin matsayin
da na samu kuma za ta kai ki inda wani mahaluki
bai taba zuwa ba, kuma daga ke har izuwa mutumin
karshe na duniya wani ba zai je ba."
Koda Abidatu ta ji wannan batu sai hankalinta ya kwanta ta saki jikinta wannan iska ta zuketa izuwa cikin kogon. Take kogon ya rikide ya
zama wannan bakar akwati, Sarki Azmal ya kurawa
akwatin idanu har tsawon rabin sa'a sannan akwatin
5
Taskar Tsafi Abdul'aziz Sani M/Gini
ta sake rikidewa ta zama kogo, sai ga Abidatu ta fito
daga ciki fuskarta cike da annuri wani irin haske ya
baibaye jikinta gaba daya. Tana fitowa daga cikin
kogon sai kogon ya zama bakar akwatin a daidai
lokacin ne Sarki Azmal ya fara wani irin kakarin
mutuwa. Al'amarin da ya dugunzuma hankalin
Abidatu kenan ta ruga izuwa kan gado da Sarki
Azmal ke kwance, ta zaunc daf da shi ta kura masa
idanu tana kwalla ta ce "Ina ma'anar wannan kakari
naka?"
Azmal ya ce "Ya ke 'yata ki yi sani cewa
lokaci ya yi da zamu yi bankwana. A halin yanzu
kin ziyarci inda gaba dayan sirrikan tsafin duniya
yakc,w anda ni kadai na mallakesu kuma yanzu sun
barni sun koma gareki. Wannan wuri da ki ka je shi
ake kira TASKAR TSAFI. Shin za ki iya bani
labarin abubuwan da ki ka gano a cikin Taskar
Tsafi?"
Abidatul Azmal ta kada kai ta ce "Ya kai
Babana ka yi sani cewa harshe ba zai iya bayanin
abin da na gani ba, idanu ba su isa su ga abin da na
gani ba, abin da zan iya cewa kawai shi ne na je
inda babu irinsa a duk fadin duniyar nan kuma na ji wani sirri a cikin jinin jikina, Kashina, bargona da fatar jikina irin wanda ban taba ji ba. Ka yi sani ccwa
azata

bisa
ina ji kamar zan iya daukar duniyar nan na tafin hannuna."
6
Taskar Tsafi Abdul'aziz Sani M/Gini
Ko da jin haka sai Sarki Azmal ya yi guntun murmushi cikin karfin hali a lokaci guda kuma ya hadiyi miyau na karshe. Take idanunsa suka kafe, gaba daya gangar jikinsa ta sandare komai ya daina motsi, koda ganin haka sai Abidatul Azmal ta
rungumc gawar Sarki Azmal ta fashc da matsanancin kuka har da ihu al'amarin da ya
haddasa durowar gaba dayan dakarun gin sarautar
izuwa cikin turakar Sarki Azmal. Duk wanda ya shigo ya ga Abidatu rungume da gawa sai jikinsa ya yi sanyi ya kame kawai.
Cikin kankanin lokaci labari ya bazu izuwa
sauran kasashe dake makwabtaka da birnin kusan
cewar Sarki Azmal ya mutu, ai kuwa nan fa jama'a
suka cika da farin ciki domin sun san cewa sun huta
dulkin zaluncin da ake yi musu sun manta da
cewa an kashe maciji ne ba a sare kansa ba, domin
akwai magajin Sarki Azmal wato 'yarsa Abidatul
Azmal.
A yammacin birain Kusa akwai wani babban
gari da ake kira Babila. Sarkin dake mulki a Babila
sunansa Asmaru bin Ufila.
Kafin Sarki Asmaru ya hau kan karaga Sarki
Zuwadu ne ke mulki amma sai Sarki Azmal ya
kaudashi da karfin tsiya ya dora Asmaru.
Sarki Asmaru na da da guda daya wani
kyakkyawan saurayi kuma jarumin gaske mai suna
7
Himal.
Taskar Tsafi Abdul'aziz Sani M/Gini
Himal ya kasance adalin mutum kuma ga tausayi da jin kan talakawa. Wadannan halayc na sanc suka sa bai shaku da mahaifinsa ba Sarki Asmaru domin shi Asmaru ya kasance cikakken azzalumi, makctaci. A ragowar Sarki Asmaru babu
abin da ya ke so sama da cin zali, kisa da kwatar
dukiya ko macc mai kyau. Ita kanta mahaifiyar
Himal asalinta matar wazirin Sarki Asmaru ce. A
ranar da Sarki Asmaru ya kyallara idanu ya ganta ya
jc har gidan Wazirin nasa ya yi masa kisan gilla ya
daukota da karfin tsiya ya aurcta bisa dolc.,
Wannan abu ya faru ne kimanin shekaru ashirin da
biyar baya kuma har yanzu Yarima Himal bai taba
jin wannan labari ba, domin mahaifiyarsa ba ta bari
ya sani ba.
Sa'adda Yarima Himal ya fuskanci cewa
ra'ayinsa da na mahaifinsa sun bambanta sai ya ja
da baya ja cikin harkokin sarauta ya zama kamar ba
dan Sarki ba. Kullum ba shi da tunanin hanyar da
zai bi ya hana zalunci a doron kasa to amma fa ya
san cewa bai isa ba, domin ko ba komai Sarkin
yawa ya fi sarkin karfi. Tabbas idan ya ce zai shiga
cikin irin harkokin mahaifinsa na hanashi aiwatar da
zalunci, mahaifin nasa zai iya sawa a hallaka shi,
tunda dai babu wata kauna da kyakkyawar alaka a
tsakaninsu.

Comments

Please log in to leave a comment

Login here