Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
DAKARUN MUSULUNCI 5

DAKARUN MUSULUNCI 5

by Abdulaziz Sani Madakin Gini ,

1 Hours
19, Jan 2026
Unknown group
Not Inserted
Free
106.04 kb
TXT
96+
82+
Last download 1 hour ago

You cannot download this book until you log in, but you can read it.

Read Now

OR

Description

 Duk sa'adda Huzaifa ya sami nasarar saran jikin katon mutumin ko ya sokeshi da takobinsa sai yaji kamar dutse ya doka ko kwarzanewa jikinsa baya yi sai dai kaga tartsatsin wuta na tashi.
   Wannan barandami na mutumin kuwa, duk abinda ya sama dashi sai ya rabe gida biyu walau dutse ko karfe.
   Duk irin zafin naman Huzaifa da tsananin jarumtakarsa sai yaga duk sun zama na banza domin katon ya ninkashi a komai.
   In ba don ma yana da mutukar kwarewa ba da iya yaki da tuni katon yayi masa kwaf daya.
   Suna cikin wannan bakin gumurzu ne katon ya shammaci Huzaifa ya gabza masa naushi fuska.
   Saboda karfin naushi sai da Huzaifa yayi sama ya gwaru da jikin bango a lokacin da wani gudan jini yayi fitar burgu daga cikin bakinsa ya fado kasa a mutukar galabaice takobinsa ma sai ta subuce daga hannunsa ta fado kasa.
   Koda ganin abinda ya faru sai aljani huraisul Marwas ya fusata ainun ya bude fuka fukansa ya kawowa katon mutumin suka a kirji da wani mashinsa na yaki.
   Kawai sai katon ya tare sukar da tafin hannunsa.
   Take mashin ya narke ya kama diga kasa tamkar ya kwana dari a cikin wuta yana damuwa.
   Cikin zafin nama katon ya kaiwa hurusul Marwas mangari da hannunsa guda, ai kuwa sai yayi Saar samunsa a fuka fukinsa na hagu.
   Kamar an cilla tsakuwa haka hurusul Marwas ya fada can baya ya gwaru da bango ya fado kasa sumamme sakamakon karyewar fuka fukinsa.
   Koda katon ya ga wannan nasara da ya samu sai ya bushe da dariya mugunta sannan ya juya izuwa kan yarima Huzaifa yaje kansa ya tsaya ya raba kafafunsa kuma ya sunkuyo da nufin ya kama kan Huzaifa ya murde masa wuya.
   Ashe a dai dai wannan lokaci hunzalu na ta yiwa Allah kirari yana neman ya karfafeshi da karfin da zai iya taimakon su Huzaifa.
   Ai kuwa nan take yaji wani gagrumin karfi ya shiga jikinsa, kawai sai gani yayi ya daka tsalle daga inda yake ya dira akan wannan garjejen kato.
   Kafin katon ya kamo kan Huzaifa da hannayensa tuni hunzalu ya naushi gadon bayansa.
   Saboda tsananin karfin naushi take gadon bayan katon ya burme, sai ga hannun hunzalu ya Faso ta cikin katon.
   Yana zare hannunsa sai katon ya sulale kasa matacce, ji kake Tim! Tamkar giwa ce ta fadi.
   Shi kansa hunzalu bai san saadda ya kame ba kamar gunki saboda tsananin mamaki bisa ganin wannan gagarumar jarumta da yayi. Kawai sai yaji tsoron Allah da kaunarsa sun karu ainun a cikin ransa, bai san saadda idanunsa suka ciko da kwallah ba suka fara zubar da hawayen murna.
   Huzaifa da aljani hurusul Marwas kuwa, kasa motsawa sukayi saboda tsananin alajabi sai bayan yan dakiku sannan Huzaifa ya mike tsaye ya dubi hunzalu cikin murmushi yace, ya kai hunzalu kayi sani cewa wanda duk ya yi imani da Allah kuna ya dogara da shi bisa dukkan lamuransa to fa babu abinda zai gagareshi a doron kasa.
   Tabbas imaninka da tsoronka ga Allah ne suka sa ka sami wannan gagarumin karfi har ka sami nasarar kashe wannan katon ka ceto rayuwarmu.
   Ni da hurusul Marwas kuwa ajizanci ne irin na dan Adam yasa muka shaafa da ci gaba da neman taimakon Allah, a lokacin da muke yin yaki da wannan kato, shi yasa muka masa samun nasara a kansa.
   Koda Huzaifa yazo nan a zancensa sai yaji ana ta kiran sunansa a bayansa.
   Koda ya waiga da sauri sai yaga ashe ba wasu bane face dakarun garinsu wadanda ke cikin wannan daki a kulle, su duka sun zo bakin kofar dakin  sun tsaitsaya wacce take a kulle da katon kwado kuma an yi tane da sandunan karfe mai kauri.
   Nan take Huzaifa ya sunkuya ya dauki takobinsa ya tofa mata wata addua sannan ya dagata sama ya sare kwadon mukullin da aka rufe kofar da shi.
   Take kwadon ya fadi kasa kofar ta bude, sai dakarun suka fito waje gaba dayansu cikin tsananin farinciki suna yiwa Allah godiya gami da yiwa Huzaifa jinjina.
   Nan dai aka dunguma da nufin a fice daga cikin kurkukun gaba daya amma sai Huzaifa ya tsaya cak! Sakamakon  aljani hurusul Marwas a kwance yana nishi ya kasa tashi.
   Cikin kaduwa Huzaifa ya ruga gareshi ya durkusa a gabansa yace, ya kai dan uwanavv menene ya sameka ka kasa tashi kana ta nishi haka?
   Hurusul Marwas ya budi baki da kyar yace, shi baka ganin yadda fuka fukina na hagu ya kumbura bane?
   Ai na karye ne kuma ba zan iya koda motsawa ba daga nan face an gyara mini wannan karaya.
   Koda Huzaifa ya dubi fuka fukin ya ga yadda ya karye kuma ya kumbura sumtum! Sai hankalinsa ya dugunzuma domin bai san yadda ake DOA aljanu ba yayin da suka karye.
   Huzaifa ya dubi aljani hurusul Marwas yace, yanzu menene abinyi?
   Kaga dai inda zamu taru mu duka nan ni da dakarun nan da muka ceto rayuwarsu ba za mu iya daukarka ba sannan kuma bamu san yadda ake gyara karaya ba irin taku ta aljanu.
   Koda jin wannan batu sai aljani hurusul Marwas yayi murmushin karfin haki yace, ai batun gyaran karayarmu iri dayane da naku, kawai yanzu ku garzaya ku samo itatuwan bishiya masu kauri gami da danyar jijiyar bishiya kuzo ku gyara karayar da sauri kafin abokan gaba su zo su afka mana domin na san cewa nan da zuwa wani lokaci akilin sarki shaaran zai iya samun labarin halin da kurkuku ke ciki aboda tsegumi irin na yan uwana aljanu. Yanzu ma karfin addu'armu ne ya hana aljanun dake yaso munafunci zuwa kusa da nan bare su san halin da ake ciki.
  Koda jin wannan batu sai Huzaifa ya umarci wasu daga cikin dakarun na musulunci da su ruga suje u samo manyan itatuwa da danyar jijiyar bishiya.
   Nan da nan kuwa dakarun suka cika umarni. Lokacin da aka zo da abubuwa biyun sai aljani hurusul Marwas ya dubi yarima Huzaifa yace, ina mai baku shawara daku samo murtukekiyar sarkar karfe ku fara daure hannayena, kafafuna da wuyana  kasa cikin dirkoki in ba haka ba kuwa gyaran karayar nan ba zai yiwu ba.
   Koda jin wannan batu sai yarima Huzaifa yayi murmushi yace, hakika aikin mai shawara baya baci.
   Aaje a samo irin sarkokin da ake daure fursunonin aljanu a gidan nan, sannan vkuma ina son muci gaba da yin adduoi gaba dayanmu domin Allah ya hana abokan gabarmu zuwa nan harmu kammala duk abinda muka zo yi.
   Nan take kuwa akayi amfani da wannan umarni.
   Bayan an samo wata murtukekiyar sarkar karfe an daure hanaye, kafafu da wuyan aljani hurusul Marwas a jikin wadan su manyan dirkokin gini, sai hurusul Marwas ya sake bayar da shawara a toshe bakinsa da tsummokara a daureshi tamau.
   Wannan shawara ma ba ayi biris da ita ba,, koda aka fara gyara karayar fuka fukin nasa kuwa yaji wani irin mugun radadi da zugi sai ya yunkura cikin azabbaben karfi, ya kwarara uban ihu.
   Da yake bakinsa a toshe yake sai ihun ya zamo kamar an busa bututun algaita, amma duk da haka sai da karar sautin ta cika birnin shumbul gaba daya ta firgita komai da kowa.
   Motsawar da yayi kuwa, sai da gaba dayan ginin gidan kurkukun yayi girgiza kamar zai rushe.
   Cikin hanzari Huzaifa da sauran jamaarsa suka daka tsalle suka dira akan hurusul Marwas suna kokarin danneshi.
  Duk da haka sai suka kasa ladaftar da shi domin da zarar ya yunkura sakamakon zafin da yake ji na gyaran karayar sai kaga ya watsar da su kasa tamkar busassun ganyayen bishiya na zubowa kasa.

Comments

Please log in to leave a comment

Login here