ke shiryawa kullum a gidansa don jama'ar gari da baŕi, don lalle abincin ya isa jarin yaro.
To duk abin nan da Mairabgaja ya tara na banza ne, kuma abin da ya ke ma jama'a na banza ne don ba shi da magaji, ko ŝari ba a taŝa yi masa ba. Yayin da malamin nan ya zo nan, sai ya ga Nakowa yana kuka duk hankalinsa ya tashi. Malami ya nemi kai da ŝafar Nakowa ya rasa, ba abin da ya ke sai kuka. Sabo da'haka malamin ya fito ya tafi gidansa ya bar shi cikin wannan hali.
Al'adar malamin ce ba ya zuwa gun Nakowa sai dare ya kusa rabawa amma kashegari tun da afmur u ya zo, ya tarad da shi dai ba ya da wani sukuni, hankalinsa in ya yi dubu duk ya tashi. Malami ya tsugunna suka gajsa, sa'an nan ya duŝadda kansa ŝasa ya ce, "Ina so ka bayyana mani dalilin ŝacin zuci- yarka na jiya." Nakowa bai amsa ba. Da malamin ya nace masa da tambaya, sa'an n'an ya daga kai ya ce, "Ka sani ba ni da da ko diya, ni kuma na tambaye ka ka ba ni labarin wani ŝasa itaccen attajiri, don in ji irin dubarunsa ko na sami waŝan- da za su yi mini amfani." To, da farawa sai ka soma yi mani habaici, kana cewa, duk dukiyar da attajirin nan ya tara, ta banza ce, don ba shi da magaji, watau ni." Da malamin nan ya ji inda Nakowa ya nufa sai fa hankalinsa ya tuma, ya faŝi yana rantsre-rantsre gaban Nakowa, kan shi ko a zuci bai kawo haka ba. Da Nakowa ya ga malami da gaske ya ke, sai ya ce, "To, ai ba komi, ka san, zato zunubi ne ko da ya zama gaskiya ne." Ya nemi gafarar malamin, ya gafarta masa.
Sa'an nan malamin ya duŝa ya ce, "Abin da ya fi yanzu mu shiga roŝon Allah ni da kai, ko Allah ya amshi roŝomnu, ka sami haihuwa." Nakowa ya amshi shawara da hannu bib- biyu. Suka shiga roŝon Allah.
Ba su yi wata uku ba, sai Allah ya amshin roŝonsu, daya daga cikin matan Nakowa ta sami ciki. Da ganin haka' fa Nakowa murna ba sai an faŝa ba. Nakowa ya kira malamin nan ya yi masa kyauta mai yawa. Sa'an nan ya ce da shi, "Ina so mu roŝi Allah, matar nan tawa ta haifi da namiji, kuma Allah ya sauke ta lafiya." Malami ya amsa, sa'an nan ya ce, "To, bisa magana'da ka faŝa mani, kan wai ina yi maka habaici ne, don ba ka taŝa haihuwa ba, da zai zama habaicin ne, to da ko kowa ya nemi irin wannan habaici, wanda ŝarshensa ya zama hausabook.com
---
**Page 6**
alheri sabo da haka na hore ka da ka yi aiki da karshen al'amari kada ka dubi farkon shi, don akasari farkon al'amari ya kan zama mai kyau, amma karshensa-mummuna, shi ya sa ko mu- tum zai rika tunawa da lahira, don ko karshe can ne makomar- sa." Malami ya yi godiya ya koma gida.
Da Nakowa da malami suka shiga rokon Allah, kan Allah,ya sauki matar lafiya, ya kuma nufa ta haifi da namiji. A wani dare Nakowa na cikin roko sai ya ga dakin da ya ke ciki ya yi duhu, sa'an nan ya yi haske, ya duha haka gabansa sai ya ga wata irin halitta, Kafafun kamar tsinke jikin kamar runbu haKoran ko kamar kwabren itace, kan ko kamar na biri. Nakowa ya ga lalle wannan halitta aljani ne ga shi ba shi mafita, sabo da haka zuciyarsa ta dake, ko da ya ke da ma jarumi ne, ya ce, "Kai, me ya kawo ka dakina?" Aljani ya bugi Kirji da hannu ya zunguri Nakowa da haKori daya, ya ce, "Ni za ka nuna wa raini?" Nakowa ya warto takobinsa ya danKara wa Aljani har ya rabe biyu, amma da ya ke aljani ne, ya sake gamewa, ya dubi Nakowa ya haure shi da haKori, ya fadi har ya suma. Da ya farfado ya sake fada aljani suka yi ta dauki ba dadi har asuba. Da aljani ya ga Nakowa lalle ya isa duk inda jarumi ya kai ya kai, sai ya nemi su yi abota, suka yi abota. Aljani ya kawo wani takobi mai wani irin rubutu a jikinsa da larabci, ya ce, "Ka ga wannan in kana tare da shi, ko da Sarkin Aljannu ku yi fada, don ba irinsa duk duniya." Ya kuma yi masa alkawari ko wane mako zai zo su yi hira, daga nan sai ya bace. Ko wane mako yana zuwa.
Bayan wata tara matar Nakowa ta haihu, Allah bai amsa roKonsu ba ta haifi mace, wadda domin kyaw0 sai ka ce aljana. Ko da ya ke Nakowa bai samu cikkakiyar biyan bukata ba, amma shagalin da aka yi ran da ta haihu sai wanda ya gani. Aka yi sa'a kuwa ran nan aljani abokin Nakowa ranar zuwansa ce. Da aljani ya zo Nakowa ya ba shi labarin abin farin cikin da ya same shi. Aljani ya taya shi murna, ya yi alkawali zai zo suna tare da abokansa.
Da mako ya kewayo aka rada wa yarinya suna ZulRaratu. Nakowa ya sa aka yanka rago dari, raRuma arba'in, shanu hamsin, sha'anin abinci ko idan an tsaya a fada sai a cika littafi, a takaice dai duk garuruwa na kusa da Langeri sai da suka kwana bakwai ba su sai abinci ba. Tun daga safiyar suna a ke kade-kade da bushe-bushe, har wata safiyar.
---
**Page 7**
Yawaitar wannan shagali har abin ya kai ga Limamin garin, sai Liman ya aiko wa Nakowa a fada masa wannan bidia ta yi yawa, ya kamata a bari haka nan, im ba kuma an fita daga hanyar Allah ba ne. Nakowa ya aika aka sanad da Liman zai yi bakin koarinsa ya hana mutane, amma kuma Liman ya san wanda ya yi nisa ba ya jin kira, wannan mutane kafin a jawo hankalinsu su bar kada-kade da sauran sha'ani sai an yi da gaske. Nakowa ya aika wa jama'a a tashi daga biki haka nan, amma ina, ba wanda ma ya saurari abin da a ke fada.
Abin sha'awa da la'asar sai kurum aka ji kade-kade da bushe- bushe da waka daga sama ana kuma watso kudi da goro, ashe aljani abokin Nakowa ne ya zo taya shi biki, kamar yadda ya dauki alkawari. Wannan fa shi ya jawo tsofaffi da dattawa ana kokawa don kudi. Maganar kudi nan da nan ta bazu gari. Kafin a ce haka dattawa sun fi yawa gun bikin sai kokawa a ke da su.
Magana ta tafi har fada, da Liman ya ji haka, sai ya ce da Sarki, “Ashe da gangan na zargi Nakowa, ashe· abin na Allah ‘ne, kudi daga sama ai lalle baiwa ce daga Allah.” Sai Liman ya ce wa Sarki, “Ai ya kamata mu tafi mu sami abin da muka samu, don neman albarka.” Kafin a ce haka sai gun biki ya cika da sarakin gari da mahakunta. Da zuwansu ba wanda ya dube su ma, kowa yana ta kansa, ganin haka fa sai Liman ya ce, “Ai ba tsayawa za mu yi ba, gara mu shiga mu ga abin da za mu samu.” Kafin a ce haka sai ga Sarki da Liman da sauran manyan gari suna kokawa da yara, an ture masu rawani can rigunan an yi kaca-kaca da su.
Da Nakowa ya ji labarin zuwan manyan gari, sai ya fito a guje, ya duba bai gansu ba, duk sun saje da yara da sauran talakawa. Zuwa can ya ga Liman duk sajensa ya yi fura, bai ma sami wani abin kirki ba, ya fadi ya ce, “Allah ya gafarta mallam, lafiya haka?” Liman ya ce, “Ai mun zo har da Sarki ne don neman albarka”. Nakowa ya ce, “To wannan ai wani abokina ne, ya zo taya ni biki, shi ne mai zubo kudi daga sama”. Sai ku tafi gida in ba ku naku”. Nakowa ya aika masu nasu bayan sun je gida. Manyan gari duk kunya ta rufe su kan wannan abu.
Da Zulkaratu ta fara wayo sai Nakowa ya sa ta makaranta ta zama ko yarinya ce mai koari, kafin a ce haka har ta sau ke.
---
**Page 8**
Aka sa ta kuma karatun littattafai wanda za ta gane sha'anin addini, cikin lokaci kada'n duk ta iya su. ZulRaratu ba ta cika shekara goma ba sai da ya zama ta san abubuwa wadanda duk sa'arta ba ta sani ba game da ilmi, kai har ma manyan.
Da yarinya ta soma girma sai masoya suka yo ca, abin babu kama hannun yaro. Ya zamana daga Sarki sai dan sarki, don attajirai abin ya fi Farfinsu, ko da ya ke masu karanbani sun shiga, ka san wannan wuri su talaka rabonsu hange, don ba a anbata su ba.
To cikin manemanta akwai dan Sarkin garinsu, watau Langeri, ana ce da shi Yarima, yana son ta gaya, ko da ya ke ita ma ta fi sonsa da duk sauran manemanta. Yarima ya tabbatar shi zai aure ta.
Sabo da haka sai ya tambayi ubansa Sarkin Langeri, wata gona tashi, yamma da gari, ya amshikudi masu yawa, ya shiga gina gidan da za su zauna. Kafin a ce haka, ya gina gidan da ba a tafa ganin irinsa ba duk arewa. Aka kawo kilisai da ku- jeru na zinari da azurfa aka zuba, abin sai wanda ya gani. Koyaushe a nan su ke hira da ZulRaratu.
Akwai wani gawurtaccen Sarki gabas da Langeri a wani gari da ake kira Damas, wanda ya sami labarin ZulRaratu daga wani falke. Ya sa aka kira falken nan gidansa, Sarkin nan ya tambaye shi labarin ZulRaratu. Falke ya sanad da shi cewa ya tabbata duk duniyan nan babu matar da ta yi ya ZulRaratu a kyau, ga ta da fasaha da ilmi. Da Sarki ya ji haka sai ya fara shawara yadda zai yi ya sami ZulRaratu.
Kashegari sai Sarkin Damas ya yi shirin kayan duniya masu yawa, ya kira Falken nan ya gama shi da wani babban bafa- densa ya tura su Langeri, gun Nakowa su nema masa auren ZulRaratu. Falke da Bafade suka yi shiri, suka nemi sa'ar hanya suka tafi. A kwana a tashi har Allah ya kai su Langeri, suka je suka sauka, aka sauke kaya daga kan raRuma da aka labtawa.
Bayan sun huta, suka tafi don su gana da Nakowa, kuma su ba shi labarin abin da ke tafe da su. Aka yi masu sallama, Nakowa ya fito, bayan sun gama gaisuwa, suka ba shi labarin abin da ke tafe da su, da kuma irin baiwar da Sarki ya aiko su da ita. Nakowa bai nemi ko ya ga abin da suka kawo ba, sai
Abdulaziz Sani Madakin Gini
Umar Muhammad Sangaru
Abdulaziz Sani Madakin Gini
Abdulaziz Sani Madakin Gini
Abdulaziz Sani Madakin Gini
Abdulaziz Sani Madakin Gini
Ismail Abdullahi
Najibullah Ahmad
Sad Nass
Abdulaziz Sani Madakin Gini
Mansur Usman Sufi
Habibullah Muhammad Kabara
by Abdulaziz Sani Madakin Gini
by Yar Mutan Zazzau
by Mhiz Innocent
by Mrs Usman
by Khadijat Sani Gana
by Batul Mamman
by Mummy Minal
by Boyayyiyar Marubuciya
by Jidderh
by Jameela Jameey ƴar mutan Kankia