An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
以下是该 PDF 文档中提取出的文本内容(已按页面大致分段,保留原文格式):
---
**Page 1**
# TAURARUWAR HAMADA
By SA’IDU AHMED DAURA HAUSABOOK.COM
hausabook.com
---
**Page 2**
Tauraruwar Hamada
na
Sa’idu Ahmed Daura
The Northern Nigerian Publishing Company
Zaria
---
**Page 3**
Copyright © Sa'idu Ahmed Daura 1971
An fara bugawa 1971
ISBN 978- 169- 154- 9
Published by The Northern Nigerian Publishing Company Ltd. P.O. BOX 412. Zaria.
PRINTED BY GASKIYA CORPORATION, ZARIA
---
**Page 4**
hausabook.com
---
**Page 5**
ke shiryawa kullum a gidansa don jama'ar gari da baŕi, don lalle abincin ya isa jarin yaro.
To duk abin nan da Mairabgaja ya tara na banza ne, kuma abin da ya ke ma jama'a na banza ne don ba shi da magaji, ko ŝari ba a taŝa yi masa ba. Yayin da malamin nan ya zo nan, sai ya ga Nakowa yana kuka duk hankalinsa ya tashi. Malami ya nemi kai da ŝafar Nakowa ya rasa, ba abin da ya ke sai kuka. Sabo da'haka malamin ya fito ya tafi gidansa ya bar shi cikin wannan hali.
Al'adar malamin ce ba ya zuwa gun Nakowa sai dare ya kusa rabawa amma kashegari tun da afmur u ya zo, ya tarad da shi dai ba ya da wani sukuni, hankalinsa in ya yi dubu duk ya tashi. Malami ya tsugunna suka gajsa, sa'an nan ya duŝadda kansa ŝasa ya ce, "Ina so ka bayyana mani dalilin ŝacin zuci- yarka na jiya." Nakowa bai amsa ba. Da malamin ya nace masa da tambaya, sa'an n'an ya daga kai ya ce, "Ka sani ba ni da da ko diya, ni kuma na tambaye ka ka ba ni labarin wani ŝasa itaccen attajiri, don in ji irin dubarunsa ko na sami waŝan- da za su yi mini amfani." To, da farawa sai ka soma yi mani habaici, kana cewa, duk dukiyar da attajirin nan ya tara, ta banza ce, don ba shi da magaji, watau ni." Da malamin nan ya ji inda Nakowa ya nufa sai fa hankalinsa ya tuma, ya faŝi yana rantsre-rantsre gaban Nakowa, kan shi ko a zuci bai kawo haka ba. Da Nakowa ya ga malami da gaske ya ke, sai ya ce, "To, ai ba komi, ka san, zato zunubi ne ko da ya zama gaskiya ne." Ya nemi gafarar malamin, ya gafarta masa.
Sa'an nan malamin ya duŝa ya ce, "Abin da ya fi yanzu mu shiga roŝon Allah ni da kai, ko Allah ya amshi roŝomnu, ka sami haihuwa." Nakowa ya amshi shawara da hannu bib- biyu. Suka shiga roŝon Allah.
Ba su yi wata uku ba, sai Allah ya amshin roŝonsu, daya daga cikin matan Nakowa ta sami ciki. Da ganin haka' fa Nakowa murna ba sai an faŝa ba. Nakowa ya kira malamin nan ya yi masa kyauta mai yawa. Sa'an nan ya ce da shi, "Ina so mu roŝi Allah, matar nan tawa ta haifi da namiji, kuma Allah ya sauke ta lafiya." Malami ya amsa, sa'an nan ya ce, "To, bisa magana'da ka faŝa mani, kan wai ina yi maka habaici ne, don ba ka taŝa haihuwa ba, da zai zama habaicin ne, to da ko kowa ya nemi irin wannan habaici, wanda ŝarshensa ya zama hausabook.com
---
**Page 6**
alheri sabo da haka na hore ka da ka yi aiki da karshen al'amari kada ka dubi farkon shi, don akasari farkon al'amari ya kan zama mai kyau, amma karshensa-mummuna, shi ya sa ko mu- tum zai rika tunawa da lahira, don ko karshe can ne makomar- sa." Malami ya yi godiya ya koma gida.
Da Nakowa da malami suka shiga rokon Allah, kan Allah,ya sauki matar lafiya, ya kuma nufa ta haifi da namiji. A wani dare Nakowa na cikin roko sai ya ga dakin da ya ke ciki ya yi duhu, sa'an nan ya yi haske, ya duha haka gabansa sai ya ga wata irin halitta, Kafafun kamar tsinke jikin kamar runbu haKoran ko kamar kwabren itace, kan ko kamar na biri. Nakowa ya ga lalle wannan halitta aljani ne ga shi ba shi mafita, sabo da haka zuciyarsa ta dake, ko da ya ke da ma jarumi ne, ya ce, "Kai, me ya kawo ka dakina?" Aljani ya bugi Kirji da hannu ya zunguri Nakowa da haKori daya, ya ce, "Ni za ka nuna wa raini?" Nakowa ya warto takobinsa ya danKara wa Aljani har ya rabe biyu, amma da ya ke aljani ne, ya sake gamewa, ya dubi Nakowa ya haure shi da haKori, ya fadi har ya suma. Da ya farfado ya sake fada aljani suka yi ta dauki ba dadi har asuba. Da aljani ya ga Nakowa lalle ya isa duk inda jarumi ya kai ya kai, sai ya nemi su yi abota, suka yi abota. Aljani ya kawo wani takobi mai wani irin rubutu a jikinsa da larabci, ya ce, "Ka ga wannan in kana tare da shi, ko da Sarkin Aljannu ku yi fada, don ba irinsa duk duniya." Ya kuma yi masa alkawari ko wane mako zai zo su yi hira, daga nan sai ya bace. Ko wane mako yana zuwa.
Bayan wata tara matar Nakowa ta haihu, Allah bai amsa roKonsu ba ta haifi mace, wadda domin kyaw0 sai ka ce aljana. Ko da ya ke Nakowa bai samu cikkakiyar biyan bukata ba, amma shagalin da aka yi ran da ta haihu sai wanda ya gani. Aka yi sa'a kuwa ran nan aljani abokin Nakowa ranar zuwansa ce. Da aljani ya zo Nakowa ya ba shi labarin abin farin cikin da ya same shi. Aljani ya taya shi murna, ya yi alkawali zai zo suna tare da abokansa.
Da mako ya kewayo aka rada wa yarinya suna ZulRaratu. Nakowa ya sa aka yanka rago dari, raRuma arba'in, shanu hamsin, sha'anin abinci ko idan an tsaya a fada sai a cika littafi, a takaice dai duk garuruwa na kusa da Langeri sai da suka kwana bakwai ba su sai abinci ba. Tun daga safiyar suna a ke kade-kade da bushe-bushe, har wata safiyar.
---
**Page 7**
Yawaitar wannan shagali har abin ya kai ga Limamin garin, sai Liman ya aiko wa Nakowa a fada masa wannan bidia ta yi yawa, ya kamata a bari haka nan, im ba kuma an fita daga hanyar Allah ba ne. Nakowa ya aika aka sanad da Liman zai yi bakin koarinsa ya hana mutane, amma kuma Liman ya san wanda ya yi nisa ba ya jin kira, wannan mutane kafin a jawo hankalinsu su bar kada-kade da sauran sha'ani sai an yi da gaske. Nakowa ya aika wa jama'a a tashi daga biki haka nan, amma ina, ba wanda ma ya saurari abin da a ke fada.
Abin sha'awa da la'asar sai kurum aka ji kade-kade da bushe- bushe da waka daga sama ana kuma watso kudi da goro, ashe aljani abokin Nakowa ne ya zo taya shi biki, kamar yadda ya dauki alkawari. Wannan fa shi ya jawo tsofaffi da dattawa ana kokawa don kudi. Maganar kudi nan da nan ta bazu gari. Kafin a ce haka dattawa sun fi yawa gun bikin sai kokawa a ke da su.
Magana ta tafi har fada, da Liman ya ji haka, sai ya ce da Sarki, “Ashe da gangan na zargi Nakowa, ashe· abin na Allah ‘ne, kudi daga sama ai lalle baiwa ce daga Allah.” Sai Liman ya ce wa Sarki, “Ai ya kamata mu tafi mu sami abin da muka samu, don neman albarka.” Kafin a ce haka sai gun biki ya cika da sarakin gari da mahakunta. Da zuwansu ba wanda ya dube su ma, kowa yana ta kansa, ganin haka fa sai Liman ya ce, “Ai ba tsayawa za mu yi ba, gara mu shiga mu ga abin da za mu samu.” Kafin a ce haka sai ga Sarki da Liman da sauran manyan gari suna kokawa da yara, an ture masu rawani can rigunan an yi kaca-kaca da su.
Da Nakowa ya ji labarin zuwan manyan gari, sai ya fito a guje, ya duba bai gansu ba, duk sun saje da yara da sauran talakawa. Zuwa can ya ga Liman duk sajensa ya yi fura, bai ma sami wani abin kirki ba, ya fadi ya ce, “Allah ya gafarta mallam, lafiya haka?” Liman ya ce, “Ai mun zo har da Sarki ne don neman albarka”. Nakowa ya ce, “To wannan ai wani abokina ne, ya zo taya ni biki, shi ne mai zubo kudi daga sama”. Sai ku tafi gida in ba ku naku”. Nakowa ya aika masu nasu bayan sun je gida. Manyan gari duk kunya ta rufe su kan wannan abu.
Da Zulkaratu ta fara wayo sai Nakowa ya sa ta makaranta ta zama ko yarinya ce mai koari, kafin a ce haka har ta sau ke.
---
**Page 8**
Aka sa ta kuma karatun littattafai wanda za ta gane sha'anin addini, cikin lokaci kada'n duk ta iya su. ZulRaratu ba ta cika shekara goma ba sai da ya zama ta san abubuwa wadanda duk sa'arta ba ta sani ba game da ilmi, kai har ma manyan.
Da yarinya ta soma girma sai masoya suka yo ca, abin babu kama hannun yaro. Ya zamana daga Sarki sai dan sarki, don attajirai abin ya fi Farfinsu, ko da ya ke masu karanbani sun shiga, ka san wannan wuri su talaka rabonsu hange, don ba a anbata su ba.
To cikin manemanta akwai dan Sarkin garinsu, watau Langeri, ana ce da shi Yarima, yana son ta gaya, ko da ya ke ita ma ta fi sonsa da duk sauran manemanta. Yarima ya tabbatar shi zai aure ta.
Sabo da haka sai ya tambayi ubansa Sarkin Langeri, wata gona tashi, yamma da gari, ya amshikudi masu yawa, ya shiga gina gidan da za su zauna. Kafin a ce haka, ya gina gidan da ba a tafa ganin irinsa ba duk arewa. Aka kawo kilisai da ku- jeru na zinari da azurfa aka zuba, abin sai wanda ya gani. Koyaushe a nan su ke hira da ZulRaratu.
Akwai wani gawurtaccen Sarki gabas da Langeri a wani gari da ake kira Damas, wanda ya sami labarin ZulRaratu daga wani falke. Ya sa aka kira falken nan gidansa, Sarkin nan ya tambaye shi labarin ZulRaratu. Falke ya sanad da shi cewa ya tabbata duk duniyan nan babu matar da ta yi ya ZulRaratu a kyau, ga ta da fasaha da ilmi. Da Sarki ya ji haka sai ya fara shawara yadda zai yi ya sami ZulRaratu.
Kashegari sai Sarkin Damas ya yi shirin kayan duniya masu yawa, ya kira Falken nan ya gama shi da wani babban bafa- densa ya tura su Langeri, gun Nakowa su nema masa auren ZulRaratu. Falke da Bafade suka yi shiri, suka nemi sa'ar hanya suka tafi. A kwana a tashi har Allah ya kai su Langeri, suka je suka sauka, aka sauke kaya daga kan raRuma da aka labtawa.
Bayan sun huta, suka tafi don su gana da Nakowa, kuma su ba shi labarin abin da ke tafe da su. Aka yi masu sallama, Nakowa ya fito, bayan sun gama gaisuwa, suka ba shi labarin abin da ke tafe da su, da kuma irin baiwar da Sarki ya aiko su da ita. Nakowa bai nemi ko ya ga abin da suka kawo ba, sai
---
**Page 9**
ya ce, “ Na ji, na kuma gode, amma batun aure, ba ni iya ba da wannan yarinya nisan duniya har Damas don ba ni da kowa sai ita.” Ya kawo kyauta mai yawan gaske ya ba su, ya ce, “Ku gaida mani Sarki, bakin irin jawabina ke nan, amma ina masa godiya tun da ya ke ŝaunar diyata, ni kuma ina ŝaunarsa kuma tsakanina da shi sai amana da alheri. Nisan garin shi ne kurum ya sa ba zan ba shi ba.” Suka yi godiya suka fita. Da safiya ta yi suka yi shiri, suna masu baŝin cikin bukatar Sarki ba ta biya ba, suka kama hanya zuwa Damas.
Ran nan da magariba suka isa Damas, ba su doshi ko ina ba sai gidan Sarki. Da Sarki ya ji su ne suka dawo, sai ya fito. Suka kwash e labarin yadda duk suka yi da Nakowa suka fada masa da ja wabin da kyautar da Nakowa ya yi masu. Suka kuma ba shi labarin sun ji a cikin gari, wannan yarinya fa ba ta son kowa sai dan Sarkin garinsu, watau Yarima.
Hankalin Sarki fa duk ya tashi, ya sa aka tara hakiman Kasarsa duka da manyan fadawansa. Da aka taru Sarki ya ba su labarin Zulŝaratu da kuma aiken da ya yi da jawabin da aka yiw o masa, ya tambaye su yaya za a yi, don shi lalle ya sami wannan yarinya ko ta wane hali. Sai wani daga cikin hakimai ya ce “Allah ya ba Sarki nasara, ai kurum sai mu tafi, mu ciwo garin a kama yarinya”. Sai Wazirin garin ya ce, “A’a, tun da ga irin jawabin da ubanta ya yi, ga kuma kyauta da ya yi wa manzommu, to bai kyautu mu fada garin ba da yaŝi, sai dai mu yaudare su, mu sa a sato yarinyar allabashi in sun ce za a karŝe ta, kuma nan sai a yi duk yadda za a yi.” Sarki ya ce da Waziri, “Ta Raŝa za a sato ta?” Waziri ya ce, “Ai wannan ba wuya, zan zo mu shirya da almuru”. Sarki ya yarda da sha- warar Waziri, aka watse.
Da magari ba ta yi waziri ya tafi gidan sarki. Ya sami Jaka- diya, ya sa ta yi masa sallama da Sarki. Sarki ya fito, Waziri ya fadi ya yi gaisuwa, sa’an nan ya ce, “Allah ya ba ka nasara, bisa maganar yarinya da ka sami labarinta, akwai wani shaha- raran bara wo ana ce masa M. ‘Danye, ba ni shakka idan har muka shirya da shi zai sato ta ya kawo ta nan”. Sarki ya cc, “To ya ya za mu yi mu shirya haka, har mu sami wannan barawo?” Waziri ya ce, “In har dai ka yarda in shirya yadda zan zo da shi, ba za a cika wata ba duk inda ya ke mu same shi.” Sarki ya yarda.
---
**Page 10**
Da Waziri ya koma gida ya kira wani amintaccen yaronsa, ya sa shi ya nemo masa M. 'Danye, amma kada su shigo gari sai magariba ko sun zo da wuri.
Bayan mako biyu, yaro ya zo tare da M.'Danye, ya shiga ya ba Waziri labari sun zo da shi. Da Waziri ya fito bai ko tsaya ba, sai ya kira M.'Danye suka dunguma sai gidan Sarki.
Aka yiw o sallama da Sarki, ya fito. Waziri ya yi gaisuwa, sa- 'annan ya sanad da shi sun zo tare da M.'Danye. Sarki ya ce, "Ya shigo"
M. 'Danye ya shigo ya yi gaisuwa, Sarki ya amsa da murna da ban girma, sai ka ce wani hakimi. Sa'annan Sarki ya kwashe labarin Zulkaratu ya ba M. 'Danye, kuma ya fada masa abin da ya ke bukata ya yi masa kanta. M. 'Danye ya ce, "Ai don wannan ba komi ba ne, sai dai ina son dan lokaci don shlri" Sarki ya kawo kudi da tufafi masu yawa ya ba shi, ya kuma masa alkawari in har bukatarsa ta biya zai ba shi abin da zai ci har ya mutu. M. 'Danye ya roki Sarki ya ba shi wata daya don ya yi shiri, Sarki ya yarda.
Waziri ya fito M. 'Danye na biye da shi har gidan Waziri, da suka isa sai Waziri ya ce da M.'Danye, "To ta inda aka hau ta nan a ke sauka, kada ka dawo da yarinya ka nufi gidan Sarki, nau gidana za ka kawo ta, don ni zan tafi da ita, sa'an nan in kai ka ka yi gaisuwa, Sarki ya sallame ka, kuma ni ma in sallame ka". Ashe Waziri abin da ya sa ya ke son a kawo ta, ya riga Sarki samun labarinta, shi ma yana sonta gaya, wannan ma shi ne dalilin da ya sa ya Ri a karbo ta da yaRi. Ya kawo 'yar kyauta ya yi wa M. 'Danye don Rarin guzuri, ya gargade shi kada ya fada wa kowa, kuma in ya zo kada ya shigo gari sai dare ya raba. Nufin Waziri, idan: M. 'Danye ya zo da ita da dare ya kashe shi, ya amshi yarinyar. M. 'Danye ya yi sallama ya fita.
Da lokacin tafiya ya kusato, M. 'Danye ya tafi gun wani mashahurin Malami, ana ce masa M. Namuduka, ana yi masa laRabi da "Gobe-da-nisa" ya ba shi labarin ya zo ne don a ba shi taimako za shi Langeri, amma don ya sato ZulKaratu. M. Namuduka ya ce, "I, lalle muna jin labarin wannan yarinya, amma ga yadda mu ke jin yadda ta ke ga ubanta da fasahar ta, wannan al'amari naka mai girma ne, amma zan taimake ka, gobe ka zo mu ga Sarkin Aljannu."
Kashegari M. 'Danye ya dawo. M. Namuduka ya ce, "To
---
**Page 11**
ka iya ganin Sarki Aljannu, ba ka ji tsoro ba ?". M. Danye ya ce, "Allah ya gafarta Malam, na iya." M. Namuduka ya tashi ya shiga gaba M. Danye na biye da shi har bayan gari gindin wani dutse. Da suka isa, sai M. Namuduka ya d'auko turare da wafansu hakukuwa ya turara, ya yi wani karatu, sai kurum M. Danye ya ga dutse ya bude. Suka shiga cikin Dutse, sun kusa fadar Sarkin, sai M. Danye ya ga wanin tsohon aljani, fuskar kamar tsumma da gara ta ci, idon ko sai ka ce garwashin wuta, ha'oran a kan rasa zube, bakin kaman an yanka kabewa, kan ko rut. Da aljani ya gan su, sai ya kura wa M. Danye idanu da kallo, M. Danye ko da ya ga'shi ya ke duba sai ya yi baya. Mallam Namuduka yana tafiya abinsa bai san abin da ya auku ba, sai da ya juyo haka zai yi wa M. Danye gargadi, bai ga M. Danye ba, ya koma da sauri ya tarad da M. Danye har ya kai bakin kofa, ya ce, "A'a ha, yaya ka dawo ?" Ya ce, "Wani aljani da za mu wuce, ya harare ni ya ce in komo" M. Namuduka ya dai lallashe shi suka shiga da kyar.
Da suka koma suka isa fada, Sai M. Danye ya ga wani tsohon Aljani bisa Karaga duk jikin gashi ne, yana sanye da rigar fatar zaki, hularshi ta karfe mai siffar kan jaki, ga aljannu sun kewaye shi, tsoro duk ya kama shi. Sa'an nan Malam Namuduka ya sanad da Sarkin Aljannu abin da ke tafe da su. Da Sarkin Aljannu ya ji, sai ya fido wata 'yar laya ya ba shi, ya ce, "Wannan kada ya rabu da ita, ya je lafiya ya dawo lafiya, in ya kiyaye wafannan sharuda, ko ya gamu da mutum kada ya yi masa magana, kada kuma ya shiga ko wane gari, in ba garin da ya yi niya ba". M. Namuduka ya ba M. Danye laya, M. Danye ya sa hannu biyu ya amsa ya yi godiya, suka fito. Bayan sun fito M. Namuduka ya sallame shi ya yi masa addu'a, suka rabu, M. Danye yana cewa, ko kuma ba a sonsa da yin sa'ar ne.
Bayan sun fito, sai Sarkin Aljannu ya'ce, "Ya kamata mu aika a d'auko yarinyar nan, mu ganta, mu ga kuma irin abin da ya sa, har a ke son sato ta". Da dare ya raba, Sarkin Aljannu ya sa aka je Langere, kafin Riftawa da bissimillah aka kawo Zulkaratu ya dube ta da kyau, ya ce, "I, lalle gaskiya ne, ba mutum ba ko aljani ya yi kyawnn wannan yarinya, lalle ya isa mai kyau, to ba don, M. Namuduka yana cikin wannan magana ba da ba mu maida ta ba, amma sabo da shi mu, mun yi ha'uri, tun da
---
**Page 12**
sun riga sun zo har gare mu”. Ya sa aka mayor da ita nan da nan. Amma ita ba ta san abin da aka yi ba ma, balle halin da a ke ciki kanta.
Da lokacin da M.'Danye ya dauka gun Sarki ya cika, sai ya yi shiri, ya kama hanya tun da asuba ta cikon wata daya da ya d'auka gun Sarki, ya kama hanya mai zuwa Langeri ya yi ta yi. To a'binka da hanyoyin sahara, wani wurin hanya sai ta bace, rairayi ya rufe ta, ya yini yana tafiya har magari ta yi. Da magariba ya tsaya a wani fili wanda aka share shi babu rairayi sosai, ya ci abinci ya yi sallah, sai ya kishingida don