Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
5 / 9
nan ba ku ka zo, to duk yau sai wasu ba ku ba.” M. Danye ya ce, “Ai mu baKi ne, ba mu san ba’a zuwa nan ba.” Tsohuwa ta ce, “Wa nene ba ya da labarin Jamilatul’uhura duk duniyar nan.” M. Danye ya yi ta rantse-ranse inda ba’a san girman rantsuwa ba, kan su ba su sani ba. Tsohuwa ta ce, “To ku zo mu je in kai ku gunta, a kulle ku kafin mijinta ya zo a kashe ku. Ashe wan.nan gida da su M. Danye suka je, Sarkin Jafila ya sa aka gina shi lokacin da zai auri ita Jamilatul’uhura, ita ko dijar Sarkin Furkanzim ce, ya kawo ta han da duk kuyanginta baya zuwa ko sai mako mako, in ya zo kuma kwana uku ya ke yi, duk namiji da ya zo za a Rulle shi, in ya zo a je a kashe shi. Tsohuwa ta shiga da su M. Danye gun Jamilatul’uhura, suka fadi suka gaida ta. M. Danye ya dube ta da kyau, ya ce Allah Sarkin baiwa, na gode Allah ko da yanzu an sare mana kai. Jamilatul’uhara ta ce, “Mai ya sa ka fadi haka ?” M. Danye ya ce, “Ranki ya dade, na ji labarinki, tun daga Rasar Damas na fito don mu yi ido hufu, yau ko shekara ta hufu ke nan rabo na da gida, ba irin hadarin da wahala da ban shiga ba, ga shi yau. Allah ya sada ni da bukatata.” Ta ce, “Wane irin labarina kaji ne ?” Ya ce, “Na ji an ce ba kamar ki duk duniya, kuma wajen alheri ko Sarkin duniya ba zai yi ya taki ba.” Ta ce, “Ashe duk mutanen duniya sun sami labarina, kuma sun san alheri na.” M. Danye ya ce, “To wannan, ni da za’a kashe, ina zance haka ne, don na taso in zo in ga alheri, aka ce kuma kashe ni za’a yi, ban sami lafiya ta ba, bare ma alherin da ake fada.” Jamilatul’uhura ta ce, “Wa ya ce za’a kashe ka ?” M. Danye ya ce, “Wan nan tsohuwar” Sai ta fada tsohuwa da fada tana cewa wato har baŝina wanda suka tafo tun daga wata ŝasa --- **Page 39** don ni, su ma kashe su za’a yi, to na san zaman da muke yi da ku. Tsohuwa ta gamu da sharri M.‘Danye, ta fađi tana ta tuba kan ita bata sani ba. Aka dai kyale ta, amma ana yi mata fushi. Aka ba su M. ‘Danye đaki da shinđa irin ta sarakuna da abinci wani ma ba su ta ba ganin irinsa ba, ko a cikin yawonsu, suka yi ta kashe gararsu. Kullum da safe sai M. ‘Danye ya zo ya yi ta shara mata Rarya, ka san indai har za’a buđa bakia fađa ne, to su M. ‘Danye kafin su fađa ta ke da wuya, amma in sun shirya ta, sai ka đauke shi ta wata hanyar waliyi, wata hanyar ma sai ka ce baka son kowa duk duniya sai shi. Sabo da haka nan da nan ya samu shiga, har Jamillatul’uhura na cewa ba za ta yarda ba su koma gida sun zo ke nan. Ran san sai Sarki ya zo, wato makon zuwansa, Su M. ‘Danye suka ji kide-kide da bushe-bushe, fadawa na hargowa kamar duniya za a tashi. Sarki ya shiga gun Jamilatul’uhura. Bayan sun gaisa, a tambaye ta, “Ko akwai wadanda suka shigo, don a je a kaspe su yanzu ?” Dama al’ada ce, da Sarki ya shigo, sai a kawo’ maza wadanda suka shigo lokacin da baya nan, a tafi da su a kashe. Ko da su M. ‘Danye suka ji haka, sai hantarsu ta kada, cjkinsu ya yi kuka kulululu suna zaton ko Sarki zai ce lalle a kashe su. Sai ta ce masa, ”Akwai wadanda suka shigo, amma ba wadanda za’a kashe ba.” Ta ba shi labarin su M. ‘Danye, ta ce kuma kai na ke jira ka zo, don ba ni so su tafi, ina so su zauna tare da ni don su rika share mani kewa don sun iya labari. Sarki da ya ji wannan magana tata, sai ya gama fuska, ko da ya ke’ dai ba ya son bata mata, ya ce ”Ai bai kamata ba, a bar maza cikin mata don bada labari kawai, sai daiduk abinda ki ke so, in baki ki sallame su, su tafi.” Ta Ri wannan jawabi na Sarki. San nan Sarki ya ce da ita, ”To kafin in tafi, mu yi shawara mu san abin da za’a yi. ”Ta ce, ”To.” Sarki ya ce, ”To ai sai su zo in gansu.” Aka kira su M. ‘Danye da Dabo suka zo, suka yi gaisuwa. Sarki ya tambaye su labarin kasarsu. M. ‘Dan~ ye fa ya kunce masa bakin jaka, abin ba’a magana. Sarki ya yi ta mamaki da ya ji can ba su itatuwa kuma ba’a yin ruwan sama, bai wuce tsanani ba a yi sau daya a shekara. Da fa Sarki ya ji irin lafazinsu sai ya so su, amma fa bai yarda da ya barsu tare da Jamilatul’uhara ba. Sabo da jin dađin hirarsu Sarki sai da ya kwana bakwai, san nan ya tambayi Jamilatul’uhura yadda za su yi. Ta ce masa --- **Page 40** ”Ai ni bani da wata shawara sai ta a bar su tare da ni.” Sarki ya nace kan lalle dai a sallamesu su tafi, amma ta ŋi. Can Sarki ya tuna wata dabara, san nan ya ce mata to kin sani fa su ba su zo da niyyar zama nan ba, to yanzu ko mun ce mu tsaida su ba za su yarda ba, don ganinki suka zo kurum. Ta ce to a kira su a tambaye su mana. Aka kira su M.’Danye Sarki ya ce musu, ”Wai kuna so ku zauna a nan har abada, koko kuna son mu baku lokaci ku je gida ku shiryo, san nan ku dawo ?” To ka sani dama su M. ’Danye ga abin da ya tafo da su, wan nan dama dubarar su sami ransu ce suka yi, kuma basu bukatar kwana ko daya don dai a ce abin da suka fada gaskiya ne, sii ya sa suka dade h..ka. Sabo da haka suka ce,, ”I, janzu kam bamu zo da niyyar zama ba, sai dai in ana son mu je gida mu shiryo, mu dawo don zaman duniya to sai a bamu lokaci mu tafi mu dawo.” Da jin haka Sarki ya ce, ”To kin ji, sabo da haka tilas ta yarda da aba su lokaci su je su shiryo.” Aka basu shekara biyu da yake yanzu sun san hanya. San nan Sarki ya kawo dukiya mai yawa ya ba su ya ce duk sallamar matarsa ce, don gunta suka zo ba shi ba. Su M. ‘Danye suka yi sallama suka kama hanya suna farin cikia sun sami fita da ransu, ga shi sun sami isasshen guzuri ga kuma dukiya ko da ya ke dai bata da wani amfani gare su, don suma sun bar nasu a baya gun Faira’atu. ## M. DANYE YA RABU DA DABO Kwanci tashi har Allah ya kaisu wani kogi mai tsaw o da fadi wanda tilas su yi amfani da jirgi. Sabo da haka suka zauna bakin wannan kogi suna jiran masu jirgi. Kwana uku sai ga masu jirgi. Suka daga masu hannu suka tsaya, masu jirgi na zaton ko batattu ne. Suka je gun masu jirgi, suka yi lada suka biya kudi suka shiga, suka taras duk mutanen da ke cikin wannan jirgi ba mai jin harshensu. Amma suna taimakonsu da abinci. Kwana bakwai suna tafiya cikin ruwa, sai Allah ya yi ma jirginsu hadari, ya yi karo da dutse duk ya farfashe, da yawa duk suka nutse cikin ruwa, amma M. ‘Danye ya samu wani guntun allon jirgi ya markaye, ya ga kuma wasu da dama sun sami sa’a irin tasa, ya ce to Allah ya sa Dabo ma ya samu guntun allo kamar ni, ya yi kukan rabuwa da Dabo, ga shi bai san abin da zai afku kansa ba. Ya kwana biyu a kan wannan guntun allo, sai ya ga wani dogon sunduki yana yaw o bisa ruwa, --- **Page 41** da ya zo kusa da sundukin nan, sai ya saki allon ya kama shi, to sabo da babba ne kuma dogo, har ya zama yana iya zama bisa kansa, kamar jirgi. Ya kwana uku cikin wan nan hali, sai ya ga yunwa zata hal- laka shi. Har ya yi shawara ya fada ruwa ya mutu ya huta, sai Allah ya kawo shi, wani babban tsibiri. Ya rarrafa ya kama wannan tsibiri ya hau, ya jawo sundukinsa. Da hawa sai ya tarar ashe wannan tsibiri babba ne, har da garuruwa masu yawa, kuma ba ya iya ganin karshensa, ga jama'a ko ina. Ashe wannan tsibiri kasa ce guda makekiya, Allah ya yi masa gyafar dogo. Yana tafiya bisa tsibirin nan har ya isa wani dan rauye. Ya je gidan wani tsohon masaRi ya sauka. MasaKin nan ya amshe shi da girma, ya ce masa, "Hala jirgi ya yi hadari da ku ne?" M. Danye ya ce, "Ai kwanana kamar bakwai ina cikin ruwan nan, jirgi ne ya yi karo da mu wasu cikin 'yan uwana da yawa sun fada ruwa sun mutu." Bayan ya dan murmure, sai ya ce bari in buda akwatin nan in ga abin da Allah ya bani kuma. Ya jawo sunduRi ya buda, sai ya ga mutum a ciki, ya zaci matacce ne, har ya tsorata, sai ya dai daure, sai ya ga mutumin yana dan nunfashi. Ya jawo shi ya fitar ya ajiye, ya ga ya bude ido. Sai ya tafi a guje ya kira masaRi ya nuna masa wannan mutum, ya ba shi labarin yadda ya sami sanduRi. Suka yi ta jiyya har dai mutum ya wartsake. Bayan mutumin nan na sunduRi ya wartsake har ana zance da shi, sai M. Danye ya tambaye shi sunansa. Mutumin ya ce da M. Danye, "A yanzu ba abin da zance ma sai godiya, amma ina so bayan mun ci abincin dare, ni da kai da masaRi mu taru in baku labarina". Da magariba bayan sun ci abinci, suka taru a dakin masaRi. Mutumin ya ce, "Ni, sunana Mahiru, dan Sarkin Kurna. Ubana yana daga cikin manyan sarakunan da su ka yi yaRe-yaRe a kasar kudu suka ci garuruwa. Ubana ya zama ya na Raunata fiye da 'ya'yansa, ko da ya ke dai mu maza biyu ne, sauran ko duk mata ne. Duk yaRe yaKen da ya yi tare mu- ke zuwa, ina gabansa. To, kun san sha'anin fadawa, an ce mai hannu da shuni, shi a ke ba murjin zare, ko da ya ke dan uwana, shi ne babba na, to amma ganin yadda na ke ga ubana, sai ya zama kowa ni ya ke so, shi ko wana ba a bakin komi ya ke --- **Page 42** ba. Har mutane in an yi zancen shi cu kan ce, kai ku rabu da mahaukaci, ai wannan bai san abin da ya ke ba, ga shi ko ba abin da ya ke da shi na ri. Wata ran ubana ya yi niyyar kai yaRi ga Sarkin Burgaje, wani Rasaitaccen Sarki ne yamma da Rasarmu, ana shirin tafiya sai rashin lafiya ta same shi. Sabo da haka ya tara manyan maya- Ransa, ya sanad da su, shi ba zai iya zuwa ba, amma tun da ya yi niyyar zuwa ba za'a fasa ba, sai Mahiru da ya ke ya saba zuwa gun yaRi ya shugabance ku, ku tafi. Wan nan tafiya ta sa mutane wanda ya ke da wani abu a zuciya ya sakan mani, an tabbata ni zan gaji ubammu. To, ka san sha'anin sarauta, sai fa wana ya tashi tsaye kan lalle zai hallaka ni, ko da ya ke duk son da ubana ya ke mani bai sa na raina shi ba. Ya fa shiga Rulle-Rulle da munafukan fadawa, don ka san duk fada ba'a rasa irin wadannan, wanda za su yi ma zance don dadinsa kamar ka basu ranka, kai ko ka huta, wato don so dai, amma da zaka ga abin da ke zuciyarsu, sai ka sar- su da takobi nan take, duk yanda za'a yi da kai a yi. Sabo da haka sai ya shirya da wasu manyan mayaka kan in sun je gji yaRi su tada wata tarzoma wadda za su sami dama su kashe ri. ya kuma yi masu alkawali in sun aikata haka, ba shakka in ya yi sarki zai nada su hakimai, manyan hakimai ko, wato bayzi: mutuwar ubammu. Mutanen nan suka yi masa alkawali kai, sun yarda kuma za su cika alkawali. Bayan mayaka sun gama shiri, sai na wuce gaba muka je gun Sarki muka yi sallama kan Allah ya hada fuskokim mu gobe fiyama, don ka san wanda za shi yaRi irin wannan sallama ya ke, san nan muka fito muka ma sauran dangimmu sallama kowa dai zuciya duk a bace. To amma duk da haka manyan mayaka basu komi in za'a fita yaRi sai murna kan za su samo ganima, kowa sai kirari ya ke, kai abin ba dama. Bayan mun gama sallama sai na wuce gaban runduna, ma- kada da mabusa sai ba ni abincin duniya suke, ni ko a wannan lokaci ji na ke ba wanda ya yi yi ni duk duniyar nan, kuma da kowa mu gwabsa, amma bani da asirin abin da aka shirya mani kamar yadda mutum ke tare da ajali amma bai san ranar saukar- sa ba ya nata hauka. Muna tafiya Makada na Rara kambama ni ban gane ba, an hada mataccen itace da matacciyar fata, ga ni kuma ana zuga ni in zama matacce na uku, ba abin da na ke sai --- **Page 43** annashuwa, doki na sai hargowa ya ke ya ci ya Roshi, in kida ya shige ni, ni kan zabure shi kadan, fadawa ko sai kaji suna cewa hattara mai duniya, wato su har sun nada ni Sarki, ka ji sha'anin duniya. Muna cikin tafiya har Allah ya kawo mu gun wani kogi, to da la'asar ko muka isa, muka tarar kogin ya kawo, sabo da haka tilas ne, mu sabka sai ya ja. Muka sauka nan da nan, aka kafa mani tanti wuri ba wuya ya zama tamkar gari, sai fa fadanci a ke yi mani. Mutanen nan da wana ya Rulla da su, su kashe ni, sai na ga suna gama kai, ni ina zato zumunci ne na tafiya, ashe suna shawara kan kashe ni gare su, ba Karamin al'amari ba ne, sabo da haka sai suka yi shawara kan za su saka ni cikin kogin nan idan dare ya raba mutane sun yi barci. Kun san al'amarin duniya ba ya 6uya, to shirin duk da suka yi sai wani cikinsu ya zo ya bani labarin kan yadda suka yi da wana, amma bai sa- nad da ni ba ko sun yarda za su aikata ba, ko kuma ba za su aikata ba, ko kuma wan nan shawara tasu, ta su fasa ce ko ta su aikata ce, sabo da haka na zamna ina da shiri, to amma ban tsammani za su saka ni cikin kogi ba. Wannan akwati da kuka ganni a ciki akwati na ne da nake zuba kaya ciki. Da dare ina barci ka san abin da baka zato zai faru, na ji an dauke ni an saka cikin wani abu, amma Allah bai bani ikon magana ba, sai da aka rufe shi aka jefa ruwa sannan na yi karaji, amma ina, duk a banza wa ma zai yi zaton ni ne, mutane basu san abin da a ke ciki ba. Ka san an ce 'Zakaran da Allah ya nufa da cara ana shafo ana muzuru sai ya yi,' wannan babbar ishara ce gare mu, domin an tabbata sundukin nan zai yi Rasa, ni kuma ko da bai yi Rasa ba lalle in nutu ko don zafi da rashin iska. To amma da Allah ya nufa da sauran kwanana nan gaba ; sai Allah ya nufa ka sami sunduki da ni ke ciki ban riga na mutu ba, ga shi ka jiy- yace ni, ga shi ni ne har ni ke ba da labarin abin da ya afku kai- na, kuma watakila, zata yiwu mu yi ido hufu da su mutanen nan". M.'Danye da Masaf: suka yi mamakin wan nan al'amari. Suka san Allah shi kurum ke iya saukar da abu kan mutum. M.'Danye ya yi alkawali zai kai shi garinsu kafin ya wuce neman abin da ya tafo da shi. MasaRi ya sanad da su akwai jirgi mai zuwa kowane wata uku, amma a lokacin bai fi sauran wata ba ya zo, sai su sami zuwa har wajen Rasar su Mahiru. M.'Danye da Mahiru a nan suka koyi saRa, masaRin nan yana Raunar su gaya, yana kuma taimakon su da abinci isasshe, --- **Page 44** kullum M. 'Danye kan ba su labarin tafiye tafiyensa da kuma labarin yaron shi Dabo, yana juyayin abin da ya afku kanshi, don ya tabbatar ya mutu. Da wata daya ya cika sai ga jirgi. MasaKi ya shiga shirya masu guzuri, ya biya masu kudi suka shiga jirgi. Bayan sun yi ban kwana da masaKi jirgi ya tashi. kwanansu ashirin suka zo bakin kasar da Mahiru ya sani. Mahiru ya ce ka ga daga cikin wannan kasar ce wannan hadari ya same ni, idan masu jirgi suh sabke mu nan zamu iya samun hanya mai zuwa Kurna. Sabo da haka M. 'Danye ya yi magana da masu jirgi kan suna so su sabke nan. Jirgi ya tsaya suka sabka, san nan fa suka kama tafiyar kasa, to ka san Mahiru bai saba da tafiyar kasa ba, wannan shi ya bata masu lokaci mai yawa a hanya. Suna cikin tafiya har suka shiga kasar da uban Mahiru ke mulki, ka san tafiya kasa ga rana, wannan shi ya hana mutane gane Mahiru in sun je gari, ya kan nuna shi mai mulki ne, wai shi ne Mahiru, ga shi duk kasar an san shi amma jin Mahiru ya mutu, kuma wannan duk ya dafe ya yi baKi, ga shi a kasa, sai aka Ki yarda, ana wulakanta su. Ran nan da la'asar sai fa suka shiga Kurna, wato' birnin su Mahiru. Da jama'ar gari suka kyalla ido suka gan shi, ga shi duk ya yi baKi ga shi a kasa, to amma da ya ke garinsu ne, sai aka gane shi. Mutane suka yo ca kansa, don dama ga shi fa farin jini abin kamar za'a hadiye shi a takaice dai a ka ya isa gida. Labarin wan nan na Mahiru ko Sarki har ya yi haKuri da Mahiru, ya samo jan shi a jikinsa, shi ma ya samo miKe kafa, kuma dai ya tabbata shi zai gaji uban, sabo da haka mutanen gari da na kasa tilas ne su so shi. Sai katsam ya ji labarin Mahiru a gida, baKin ciki fa ba sai na fada ba. Sarki ko da ya ji hargowa bai san abin da ake ciki ba, sai ya zaci wani tashin hankali ne, sabo da haka ya yo waje da sauri, ya tambaya ko lafiya, aka ce masa ai Mahiru ne ga shi da wani bako sun zo. Ko da Sarki ya ji haka sai fa ya yi waje, wajensu, aka shigo da su Mahiru gida. Bayan sun gaisa, ya ba Sarki labarinsa duka da na M. 'Danye. Mutane fa suka yi ta zuwa, ana yi masa barka da arziki. To Mahiru yana da wani abokinsa Malami, wanda dama ko yaushe suna tare, Malamin nan tare su ka kwana da Mahiru ran nan, yana ba shi labarin abin da ya afku bayansa. --- **Page 45** Labarin kuma wafanda suka yi ma Mahiru wannan aiki ko da suka ji labarin ya zo, ka san an ce maras gaskiya ko cikin ruwa ya yi jibi, sai suka zaci Mahiru ya san sune suka aikata masa haka, amma ko an tabbata bai sani ba, wannan rashin gaskiyar su ce kurum da rufewa ta sa su zaton haka. Sabo da haka dukansu sai suka yi shiri da dare suka gudu, ga su ko sune manyan na gaban Sarki. Jin fa sun gudu dukansu, shi ya sa kurum aka gane su ne suka aikata haka ga Mahiru. Sabo da haka nan da nan Sørki ya sa aka bi su, kafin a ce haka aka tarad da su. Amma an sani tarad da su ba sassau kan abu ba ne don irin abin da suka aikata, bare tafo da su. Da manzonnin Sarki su ka tarad da su, sai suka ja daga suka ce duk wanda ya isa ban da shi. Aka yi ta dauki ba dadi, to amma Sarkin yawa ya fi Sarkin Rarfi, sabo da haka aka nuna masu Rarfi duk aka kame su. Aka taso su gaba har gun Sarki. Sarki ya sa aka tara jama'a bar da wan Mahiru. Bayan fada ta cika da hakimai da fadawa da jama'ar gari, sai Sarki ya ce yana so jama'a su yi shiru su saura- riabin da zai fada masu. Duk aka yi tsit kamar an mutu don tso- ron Sarki da a ke yi. Sa'an nan Sarki ya tashi tsaye ya ce, "Jama'a kun tuna kwanakin baya na shirya yaRi zuwa kasar Burgaje, Allah bai nufe ni da in je da kaina ba. Sabo da haka na wakilta Mahiru ya shugabanci yaKin. Na yi wannan shiri don Mahiru ya saba zuwa gun yaRi tare da ni, kuma yana da RoRari, ya iya kuma jimre duk wahalolin yaRi, ga shi kuma jarumi, to wan- nan shi ne dalilin da ya sa na wakilta shi, amma ba don ina nufin don ya gaje ni ba, don dai in an ce za a kai yaRi, to nasara ko ake so a samo, hanyar samunta ko ita za'a bi, amma ba don ina nufin don ya gaje ni ba, domin kun sani wannan abu ne na Allah, domin komin son da ni ke masa kan ya gaje ni, in Allah bai ba shi ba, ba yadda za'a yi ya samu, kuma komin Kin da zan yi masa, idan Allah ya ba shi ba yadda zan in hana shi. Wannan shiri da na yi, ashe wansa zuciyarsa ba ta so ba, kuma bai hangi Allah ne mai bayarwa ba, sai ya gamu da mugayan mutane suka yi shawara kan za su kashe shi a can. To shi ne da Allah ya nufa da sauran shan ruwansi suka dauRe shi suka saka a sunduRi suka jefa shi kogi. Kun san ban da Allah ya nufa yana da sauran ganin duniya, da wuya wanda aka yi ma haka ya rayu. --- **Page 46** San nan ya sa fadawan nan da suka aikatawa Mahiru haka suka tashi tsaye. Sarki ya ce da jama'a, "To wadan nan su ne wadan da na ba amanar dana su tafi da shi gun yaRi, sune kuma suka aikata haka gare shi." Jama'a ta kwasa 'Allah ya tsine maku albarka.' Sarki ya ce a yi shiru. San nan ya sa M.Danye ya tashi tsaye, ya ce da jama'a, 'To wannan yaro shi ya ku butad da shi daga wannan hallaka, ya jiyyace shi, ya kuma kawo shi gida.' Jama'a ta kwasa 'Allah ya shi masa albarka.' Sarki ya ce duk a yi shiru. Aka yi tsit. San nan Sarki ya ce, "To, bayan sun dawo daga ya Ri, sun kuma ciwo

Chapter 5 of 9