Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
6 / 9
nasara, sai suka nufo ni da kukan Rarya, suka ce da dare sun sabka bakin kogi sun ga Mahiru dare ya yi can ya tashi yana bin gabar kogi da safiya ta yi, ba'a gan shi ba. A ka yi ne- ma ba'a ganshi ba, suna zato ko kado, ko wani naman ruwa ya- kama shi. Ko da na ji wannan labari ban yarda da shi ba, sai don abin da ba ka nan aka yi kurum, wannan magana ta sa na yi haRuri. To kuma jama'a mai ku ka gani zan aikata ga wannan mutane." Jama'a kowa sai ya ce, 'Ai sai ran kasuwa a kai su kasuwa a tsire su, wasu su ce, a gama su da yara su jefe su, kowa dai ya yi ta fadin abin da ya fito daga bakinsa. Bayan an nutsa, sai Sarki ya ce, "To jama'a tun da dai Mahiru bai mutu ba, ga shi kuma ya dawo, su kuma amince masu tasa na gama su da shi, to ba abin da na gani sai su zaRi kofar da suke so, su da jama'ar su duka in sa a raka su." Kunya ma da suka ji yanzu ta ishe su in dai masu kunya ne." Jama'a ransu duk bai so ba suka yarda dai tilas, don ba don tsoron Sarki ba da sai su tsare su, su kashe. Bayan an natsa san nan Sarki ya ce, "To jama'a mai kuma ku- ka gani ya kamata in wa yaron nan da ya ku butad da Mahiru?" Jama'a suka ce baki d'aya, "Ai ba wani abu sai ka nada shi hakimci, domin su ma wadan da su ka nufi kashe shi, sun yi haka don a yi masu hakimci." Da M.Danye ya ji irin daular da za ta same shi, ya san kuma lalle in ta same shi bashi da halin ya tafi neman abin nan da ya ke so. Sabo da haka sai ya ce da Sarki, "Wan- nan abin da ka ce za ka bani, na ji, na kar ba, na kuma gode, amma yanzu ina da niyya'a zuciyata wadda za ta hana ni yanzu in tsaya in amshi wan nan abu da ka ke nufi, amma in na je na samu biyan bukata, zan zo in amsa in yi zaman duniya a nan. Kuma yanzu zan huta a nan kwana kadan san nan in wuqe." Sarki ya yi, ya yi da M. 'Danye kan ya fasa niyyar nan da ya --- **Page 47** yo, in don neman duniya ne, to ya same ta, amma M. 'Danye ya Ri. Aka sabki M. 'Danye a gidan wani dogari wanda suka yi amana gaya, ko da ya ke ko yaushe yana gidan Mahiru, can suke fira da Malamin nan abokin Mahiru. Da ya ke ka san M. 'Danye wajen a fadi magana ba shi da dama, nan da nan suka yi abuta da mutane da yawa, a ciki har da wani attajiri makwa- bcin mai masaukinsa, to attajirin irin attajiran nan ne wadanda ba su ci ba su sha, dama shi ma arzikin da ga sama ya same shi. Wata ran M. 'Danye yana fira da Malami abokin Mahiru, sai ya tambayi Malamin taimako sabo da ya samu sa'a kan niyyar shi. Malamin ya kawo wata laya ya ba shi, ya ce kuma ya nemi tunkiya ya yanka da dare, ya rataya mata layar, ya sayi likfani ya sanya ta, ya je ya gina kabari ya sanya ta ya rufe, amma duk da dare zai yi haka. Bayan sun gama fira M. 'Danye ya tafo gida. Ya zo cikin un- guwar da aka sabke shi, sai ya tarar da wata yarinya fuskar na kyalkyali don kyau sai ya zaci ma ko Jamilatul'uhura ce, tana tsaye a kofar gidansu. Ashe yarinyar kuturwa ce, har yatsunta na hannu sun gundile, ko da ya ke sauran jikinta daram ya ke. M. 'Danye da ya ganta sai ya tsaya ya tambaye ta sunanta. Ta ce masa sunanta Bulkisu. Ya tambaye ta sunan ubanta, ta ce masa Maharazu. Wannan yarinya duk ta daukema M. 'Danye hankali, ya tafi yana wasuwasi ko ma ya fasa tafiyar don ya aure ta, ba shi da asirin kuturwa ce. Da isar M. 'Danye gida, sai ya kira dogari ya ba shi labarin Bulkisu. Da dogari ya ji hanyar samu, sai ya fara yabon yarinya ko da ya ke ya san halin da ta ke ciki, ya kuma san ba yarinyar da ta fita kyau duk kasar, amma wan nan abu shi ya nakasa ta. Sabo da haka dogari, sai ya fara zuga M. 'Danye ya aure ta, wai don ya samu abin da zai samu cikin sha'anin buki, don ya san shi za'a a rika aika, sai ya ce da M. 'Danye, "Ai don yarinta ko yatsu bata fara ba". M. 'Danye bai fahinta da abin da dogari ya ke nufi ba, sai ya yi ta mamaki, yana cewa ashe a kan haifi mutum ba yatsu sai bayan an haife shi, san nan ya fara yi. Dogari ya ce, "Ai nan kasar in dai har mutum ya amsa kyau, to ba'a haifuwar shi da yatsu, sai bayan an haife shi ya yi." M. 'Danye ya ce, "To al'adarku ce nan kasar, duk mai kyau ba a haihuwarsu da yatsu." Dogari ya ce, "Mu ai haka ne." M. 'Danye ya yarda da --- **Page 48** maganar dogari, sai suka shiga shawarar neman aure. Aka sanad da da Sarki, to ka san Sarki na son M.‘Danye ya tsaya, jin zai yi aure, sai murna ta kama shi, ko da ya ke ya san yarin- yar kuturwa ce, amma hai fada ba don kada M.‘Danye ya ji ya fasa. Mahiru da Malami ma ba su fada ma M.‘Danye halin da yarinya ke ciki ba, don ganin lalle in ya yi aure zai zauna ke nan. Nan da nan maganar aure ta nuna, ka san an ce mai abin hannunsa in ya ce, yana son abu, sai ka ga mai badawa ya fi shi son ya ba shi, fiye da shi da ya bunta ya ke so, don in rashi ya same ka, to, duk gaskiyarka ma kanya ce gun mutane. Da ya ke bazawara ce, ba sai an sa ranar buki ba, sai nan da nan aka daura aure, amma duk abin nan ba wanda ya sanad da M.‘Danye halin da yarinya ke ciki. Bayan an daura aure Sarki ya ba M.‘Danye wani kangameman gida. Bayan kwana uku amarya ta tare, a ka yi shagali mai yawa don Mahiru shi ne abokin ango. M.‘Danye ya tara dukiya mai yawa. Bayan an nitsa sha’anin buki M. ‘Danye ya shiga gida don kuma su yi hira da amarya. Ya shiga dakin amarya ya zauna, amarya ta kawo abinci da ruwan sha da na wanke hannu ta ajiye masa, bayan ya ci abinci ya kimtsa ta zo ta đauke kwanu- kka. Ya kira ta ta kawo masa goro, ya fasa ya cika bakinsa, ya ce mata “To kuma sai mu shiga hira yau ba zan je gidan Ma- hiru ba”. Suna hira sai ya tuna maganar dogari ta ba ta da yatsu don kyau, ya duba hannunta haka sai ya ga ashe rashin yatsu na kuturta ne, ba kamar yadda dogari ya fada ba, sai duk abin duniya ya dame shi, sabo da haka ya yi shawara a ransa ba abin da ya fi sai ya yi tafiyarsa, amma wan nan abu ko dogarin bai nuna wa ba kan an cuce shi, sai dai in ya tuna kalmar nan ‘ko yatsu ba ta fara ba,’ ya nisa. Shawarar tafiya ta tsaya a zuciyar- sa, sai ya tafi gidan Mahiru, ya same su shi da Malamin ya sanad da shi, shi tafiya zai yi. Mahiru ya ce, “Af, to, amarya fa, ya ya za ka yi da ita ?” M. ‘Danye ya ce, “In ta yarda mu tafi tare, in bata yarda ba shi ke nan ta koma gidan su sai na dawo.” Ma- hiru ya ce, “To ai Sarki yana zaton ka yarda zaka zauna, da ran Juma’a za’a nada ka hakimi ma.” M. ‘Danye ya ce, “To, ai sai ka je ka sanad da shi zan yi gaba, kuma yanzu ina cikin shiri.” Kashegari M. ‘Danye ya tafi kasuwa don ya samo tunkiya da likafani don ya aikata abin da malamin nan ya fada masa. Ya --- **Page 49** sayi tunkiya da likafani bashi. Da dare ya tashi ya yanka tun- kiya ya sata cikin likafani kamar dai yadda malamin ya ce, sa'an nan ya dauko makara ya sanya ta ya ajiye. Can dare ya raba, ya san ba sauran mutane a waje, sai ya fita bayan gari ya gina kabari ya dawo gida ya tada matarsa ya ce mata, "Zo ki taimake ni, na kashe mutum mu je mu binne, don kada safiya ta yi asirina ya tonu. Ya yi haka don ya jarraba ta ne, ya ga ita ma ta iya rufa masa asiri, yadda ya rufa mata. Sai matar ta tashi da rawar jiki ta taya shi suka dauki gawa, su ka kai su ka binne tare, suka dawo gida. M.'Danye ya ga matarsa ko a fuska ba ta nuna wani abu ba, ya saurara ko ya ji ta fada wa wani, shiru bai ji ba. Wannan ya sa ya yarda da ita ya kuma karfafa masa ya tafi da ita, ta rika dauke masa kewa, tun da ga shi ya rasa Dabo. Da M. 'Danye ya gama Shiri, ya sa ranar tafiya, sai ya sanad da matarsa zai tafi, amma tare za su tafi. Da dai matar ta ji zai tafi sai ta da'ika, zai gudu ne, don ya kashe mutum. Sabo da haka da dare M. 'Danye suna tare da dogari kafin ya tafi gidan Mahiru, sai matar, ta zo ta ce masa tana so ta je gidansu. Ashe ita niyyarta, in taje ta fada mijinta ya kashe mutum, amma zai gudu, ya ce kuma wai ta shirya su tafi tare, watakila ya yi wan- nan shiri don kada ya barta baya ta fada a biyo shi. Ko da ya ke M. 'Danye bai san wannan niyya tata ba, sai ya Ki, ya ce ba zata je ba. Ta nace kan lalle ita sai ta tafi, ya ce ba zai bar ta ba. Ta sake cewa ita ko bai bar ta ba tafiya za ta yi. Sai M. 'Danye ya ce da ita, "Ashe ke mutuniyar bazna ce." Da ta ji haka, sai ta ce, "Ni ba mutuniyar bazna ba ce, ni har ka ce mini mutuni- yar bazna ; nan ka kashe mutum na rufa ma asiri, to dogari don Allah mutumin bazna ya rufa ma wanda ya kashe mutum asiri." Sai dogari ya ce mata, "Don Allah ki rufa mana asiri kada wani ya ji, dare ba shi da ido, amma yana da kunne." Dogari ya ba ta hafuri ta hafura ba ta je ba gidansu. Wannan ya kara wa M. 'Danye ilmi kada ka yi saurin yabon mutum sai ka tabbatar da al'amuransa. M. 'Danye da dogari suka fito suka nufi gidan dogari- M. 'Danye ya shiga gidan attajirin nan abokinsa, ma'wabcin dogari, suka yi 'yar hira, har ya sai wata taguwa yar shara ta sule da sisi a gunsa amma bashi. San nan ya fito ya tafi gidan Mahiru. --- **Page 50** Da dai dogari ya ga M. 'Danye ya tafi, sai ya fito ya garzaya sai gidan Sarki. Ya je ya iske sarkin gida a kofar gida. Sarkin gida ya ce masa, "Lafiya ka ke tafe yanzu ?" Dogari ya ce, "Ina fa lafiya so na ke lalle in ga Sarki yanzu, baRon nan ne abokin Mahiru ya kashe mutum, to ya ke niyyar ya gudu." Sarkin gida ya tura Jakadiya ta sanad da Sarki, Sarki ya fito da sauri. Dogari ya kwashe labari ya sanad da Sarki, Sarki ya ce, "To, je ka sai da safe." Da dogari ya tafi, sai Sarki ya aika gidan Mahiru aka kira M. 'Danye. Da M. 'Danye ya zo, Sarki ya tambaye shi labarin kisan kai. M. 'Danye ya kwashe labari duk ya fada masa, ya kuma ce ina so gobe in dogari ya zo, in an tambaye ni zan ce, i, na kashe mutum, to kai kuma ka ce a je a kashe ni, Sarki ya ce, "To shi ke nan." M. 'Danye ya yi sallama da Sarki sai ya nufi gidansa bai koma gun su Mahiru ba. Kashegari tun da safe dogari ya zo Rofar fada ya zauna, can Sarki ya fito, ya tashi ya yi gaisuwa. Sarki ya tambaye shi maganarsa, ya fada, mutane sai duk mamaki ya kama su, don ana son M. 'Danye, aka ga kuma yadda dogari mutuminsa ya yi masa. Sarki ya yi umurni a je a kira M. 'Danye. Aka je gidan M. 'Danye, da ma ya san maganar sabo da haka bai fita ko'ina ba yana jira. Da ya ji an yi masa sallama, sai ya sanya taguwar nan 'yar shara da ya saya gun abokin shi attajiri sule da sisi bashi ya fito. Da zuwa kofar gida sai ya ga ashe ko Manzon Sarki ne. Manzon Sarki ya fada masa ya je fada Sarki na kira. M. 'Danye ya ce, "Lafiya ?" Manzo ya ce, "Ai ban sani ba, ni dai an ce in kira ka, ko ka san ka yi wani abu ne ?" M. 'Danye ya ce, "A'a ban sani ba, amma bari in shiga in sawo riga ta, ta kirki." Manzon Sarki ya ce, "Ai cewa aka yi da na ganka kada in barka ko taki mu rabu." M. 'Danye ya ce, "To mu tafi." Manzon Sarki ya zo da M. 'Danye gaban Sarki. Sarki ya ce da dogari, "To zo ka fadi maganar ka." Dogari ya yi shiru duk kunya ta kama shi ya ga M. 'Danye. Sarki ya buga masa tsawa ya ce, "Yanzu na sa a kashe ka in ba ka fada ba, ko dama Rarya ce ka zo ka fada mahi, fadi maganar da ka zo ka fada mani jiya da dare da kuma yau da safe." Dogari ya saddad da kai Rasa ya ce, "Jiya ne, na je hira gidan M. 'Danye, suka yi yar hargowa da matarsa kan zuwa unguwa, har ya ce mata, mu- tuniyar banza, sai na ji ta ce, ita ba mutuniyar banza ba ce, --- **Page 51** tunda ta rufa masa asiri da ya kashe mutum, to na ke jin tsoro kada wani ya zo ya fada, a ce da ni aka gama baki aka kashe shi, shi ya sa na zo na fada, don M. 'Danye ya fada mani zai tafi, to ina jin tsoron bayan tafiyarsa." Sarki ya waiwayi M. 'Danye kan wannan magana. M. 'Danye ya ce, "I, jiya ya je hira gida- na, kuma matata ta tambaye ni zuwa unguwa na hana ta, na kuma ce mata mutuniyar banza da ta ce, ko ban bar ta ba za ta tafi, ita kuma ta ce wai na kashe mutum, wannan magana da dogari ya fada lalle haka aka yi jiya, Allah ya baka nasara." Sarki ya ce, "To a je a kashe shi tun da ya kashe mutum, amma in ya ce yana da magana a maido shi, kada wanda ya matsa masa." Jin yanda Sarki ya fada, sai mutane duk mamaki ya kama su, suka rika guna-guni. Aka fita da M. 'Danye za'a tafi a kashe, mutane duk ransu bai so ba, wasu daga zuci har zagin Sarkin suke. Suna cikin tafiya M. 'Danye ya ce, yana so a bi da shi wurin abokinsa attajiri don su yi sallama. Suka je, aka yi ma attajiri sallama ya fito. M. 'Danye ya sanad da shi abinda ya same shi, kuma yanzu tafiya za'a yi a kashe shi. Ko da attajiri ya ji haka, sai ya ce, "Ai ko ka kyauta da ka ce a biyo da kai ta nan, don cinikin da muka yi da kai na taguwa jiya ta sule da sisi ba ka biya ni ba, to, da an kashe ka da na yi asara, ga shi ko na yi sa'a ita ke wuyanka, ai sai ka tuBe ka bani." M. 'Danye ya ce masa, "To, yanzu sai bante'a gindi na in ka yarda sai ka yi haKuri, in an kashe ni su kawo ma." Attajiri ya ce, "Ai haka ba za ta yiwu ba, ga abin nawa ina gani, a ce kai da na ba sai ka mutu in amsa, kai tun da Allah ya yi mani gyafar dogo tuBe taguwa ta ka bani. kai kuma ka iya da abin da ya same ka." M. 'Danye ya ce da shi, "Ka tuna tsakani na da kai, don haka ta same ni, har ka guje ni sabo da taguwar sule da sisi, ka kuma tuna kana da dubun ta, kuma don ina jin ka a rainahar na ce a biyo da ni ta gunka in yi ma sallama." Attajiri ya ce, "Mine ne tsakanin- mu da kai, kai in kana tuBe taguwa ka bani, ka tuBe, kana Batawa su Hauni lokaci, yanzu ai da sun gama ma aiki sun dawo, kurum don karaya, ka tsaya kana jan guntuwar magana wadda baka da gaskiya cikin ta, ai kai ma ka san ba za'a gusa da kai ba sai ka tuBe mani taguwa ta ka bani." Da M. 'Danye ya ga attajiri ya tsananta sai ya ce masa, "To, biyo ni fada in baka, ku kuma ku maida ni gun Sarki, ina da magana." Atta- --- **Page 52** jiri ya ce, “Kan haRina ko’ina ka ce muje ai sai muje, mu tafi gun Sarkin.” Aka runtuma da Attajiri har gun Sarki. Da Sarki ya ga su M. Danye, ya ce, “Yaya akwai wata magana ne ?” M. Danye ya ce, “I, akwai, Allah ya baka na- sara.” Sarki ya ce, “To, fadi maganarka.” M. Danye ya ce da Sarki, “Ina so a aika a kira mutumin da na sai tunkiya gunsa, da wanda na sai likafani gunsa.” Ya yi ma wadanda aka aika kwantace da runfar da suke a kasuwa. Sarki ya tura nan da nan aka zo da su. Da suka zo M. Danye ya bada labarin yanda suka yi da Malami, ga ko Malamin yana nan a zaune gun Sarki. Malami ya ce, “I, lalle mun yi haka da shi.” Sannan M. Danye ya juya wajen wanda ya sai tunkiya gun shi ya ce, “Wannan kuma lokacin da na yi niyya zan yi gaba, don in aikata abin nan da Malami ya fada mani, gun shi na je na sai tunkiya, amma ban biya ba har yanzu, don ko na san lalle aikata haka da dare, za ta kai a yi zato tamkar yadda aka yi yanzu, shi ya sa ban biya ma kudin ba.” Aka tambayi mai tunkiya ya ce, “I haka ne, bai biya ni ba kuma har yanzu.” Sa’an nan ya juya wajen mai likafani, ya ce, “Shi ma wannan yadda muka yi da mai tunkiya haka muka yi, ban biya ba.” Aka tambayi mai Likafani ya ce, “I, lalle haka aka yi.” Sa’an nan M. Danye ya ce, “Ina rokon Sarki ya gama ni da mutane mu je gun kabarin da muka binne tunkiyar nan, ni da matata, don a ga tunkiya ce, ko mutum ne.” Sarki ya ce, “Ai sai mu tafi har da ni.” Sarki da duk jama’a aka tashi M. Danye na gaba, har gun kabari. Aka tona kabari aka fiddo da gawa, sai aka bude likafani, a duba haka sai aka ga tunkiya ta kumbura suntum. Jama’a kowa sai mamaki ya ke, ganin irin yadda M. Danye ya yi. M. Danye ya ce, “Dama na yi haka don in jarraba mata na ne, to ga ko irin abin da ya afku, dama ko an gargafe ni da kada in kuskura in auri bazawara, sai na shagalta na yi.” Da aka dawo fada, M. Danye ya ce, “To, da dogari ya zo ya ce, na kashe mutum, sai ya fadi wanda na kashe, don ba’a ce mutum ya kashe mutum ba kurum, amma ba a san sunan wanda ya kashe ba, ba’a ce ba wani ya bata ba.” Dogari ya yi shiru. San nan M. Danye ya sa aka kawo matarsa gaban Sarki. Ga ta ga dogari ga abokinsa attajiri ya ce, “To, ita dai matata, ba ni aurenta, daga nan kada ta koma gida na, kayanta ma a aike a dauko mata, san nan ya bada labarin abin da ya auku tsakanin --- **Page 53** 8hi da attajiri." Mutane sa suka yi ta tsine wa Dogari da Attajiri da matar M. Danve. Duk kunya ta kama su, suka ra sa abin da za su ce. M. Danve ya aika gida aka kawo masa riga, san nan ya tue'ya ba Attajiri tas. Attajiri ya Ri amsa. M. Danve ya ce, "Ai haka ba za ta yiwu ba, lalle ka amsa." Attajiri ya Ri. San den.M. Danve ya jeja, masa taguwa. Attajiri bai ko dube ta bare ma ya taba taguwar; ya duadada kansa kasa don kunya. San man M. 'Danve ya ce da Sarki, "To, ni kuma zan yi gaba, don ka ga irin abin da mutanenka suka Rulla mani, to, in an ce zan yi zaman duniya ne, har ina rike da wani muRami babba kamar hakimci, wa ya san abinda zai auku, wai don ni ba mutu- min kasarku ba ne, to na san ko dai, na yi, yadda kanyi, na kuma ga irin sakamakon da na samu a garin su Mahiru, na kuButo shi, ga shi ni kuma ana so a hallaka ni. To, gara tun gaban ba ta kai- ni ga hallaka ba in janye jikina in wuce abin da ya tafo da ni, don da ma ban zo garin nan da niyyar zama ba, kuma ma Raddara ce ta kawo ni". Jin fa wannan jawabi na M. 'Danve. sai hankalin Sarki da na Mahiru ya tashi, suka yi fushi mugun fushi. Sarki da Mahiru suka shiga lallashinsa, don kada ma wani kunne ya ji, ga irin abin da ya yi musu amma ga abin da aka Rulla masa a garinsu, kuma ya yarda ya zauna. M. 'Danve ya ce shi kam ba zai tsaya ba, har a ce an nada shi hakimi, tun da ya ga halin mutanen kasarsa, ya ko ga masu saka alheri da sharri ne. Da ya ke Sarkin wanda ya san ya kamata ne, ya san kuma alheri da mutuncin mutane, kuma ba mai nuna wannan nashi ne ba, wannan ba nashi ba ne, duk wanda ya ga cancanci abu gare shi ya ke, sai wannan magana ta kara tunzura Sarki. Ya ce da do- gari da attajiri da iyayen matar M. 'Danve duk su tashi su bar masa kasarsa, don M. 'Danve ya. gani, shi da ya ce, don baKo ne, to ga shi don shi baKon ya kori- yan gari. Suka nemi Sarki ya ba su kwana daya ma su shirya. Sarki ya ce, "Shi ko kwana daya bai yarda ba, yanzu zai sa a raka su, in ko suna wata jiji, zai sa a kashe su". Nan da nan suka shiga gama 'yan komatsansu. Kafin azahar duk sun kimtsa suna jiran maraka. Sauran danginsu suna kuka, can maraka suka zo. Suka ce wace hanya ku ke so mu fita: Suka ce a yi gabas da su. Maraka suka tasa su gaba suka yi gabas da su har suka kai su kan iyaka, da dare. Da

Chapter 6 of 9